shi.
Saboda dare ya yi ya sa a ka bar ma gobe har da safe sai da Mu'azzam ya sake kiran Nasir ya ce har yanzu bai ga Mansoor ba kuma shi ba zai tafi ya bar ɗan uwansa a wannan bakin gidan ba.
Nasir ya ce ina kada ya je ko'ina bari ya je can gidan ya gani, ai yana zuwa sai ya ji labarin tun safe Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna gidan Hajiya shima sai ya Nufi acan, can ɗin ma abun tausayi Mimi ta kwana kuka duk idanuwanta sun kumbura haka Hajiya ya iske Alhaji Hamza ya yi musu Bucking din jirgi zuwa Abuja har da Inna Meri da Baba Ɗanjuma za'a tafi, Inna Meri faɗi take yi"Sai ni naje na duka na bashi hakuri zan roƙe shi Allah ya sakar min Ƴaƴana ba su da kowa Allah ne gatan su."
Yaddiko na gidan itama duk daga baya take jin labarin abubuwan da suka faru. Amman abunda Yaya Kabiru ya aikata ya yi son rai, ba kyau ka wulakanta mutum.
A ranar suka bi jirgi zuwa Abuja daga filin jirgin suka hau taxi zuwa gidan su Mimi da ke Abuja Mommy ce kawai ta san da zuwan su domin itama ta ce ya kamata su zo gabaɗaya in ba haka Major zai kashe yaron mutane.
Yana Office Alhaji Hamza ya kira shi ya ce ga su sun zo har da Hajiya ma.Shi ya yi tafiyar sa ma ya bar yaron mutane sojoji na yi masa azaba, Mu'azzam kuma ya ƙi tafiya saboda tun jiya bai kara ganin inda a ka kai masa Dan'uwa ba, abinci ko ya kasa saka shi acikin cikinsa shima ya yi kuka ina zai nufa gida cike da sojoji shima yanzu su kamashi su yi ta ta duka Mommy ta aiko masa da abun kari ruwan zafi kawai ya iya sha yana jiran zuwan su Inna Meri tunda Nasir ya sanar da shi tare da su za'a taho.
Mu'azzam na haraban gidan tsaye su Inna Meri suka iso, wajen su ya nufa yana kuka ya rumgume su.
Mimi kuma tana kuka ta kwashi gudu zuwa cikin gida tana kiran sunan Mommy.
Inna Meri sai tambaya take yi Ina Baban Inna? Mu'azzam na kuka yana faɗin"Inna an kai shi wani ɗaki, ban kara ganinsa ba a sume su ka fita da shi. Jini na zuba ajikinsa."
Mu'azzam ya kara rushewa da kuka Inna Meri na salati da sallallami.
*Janafty*
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka.
*Zumar Matsi Guarantee 3500*
*Maganin sanyi komai nacinsa 4k*
*Zumar kacha kacha 2500*
*Zumar kiba 4k*
*Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki*
*Dahuwar kaza ta manyan mata 8k*
Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0
*Page 15*
Baba Ɗanjuma kuma sai maimaita faɗin" Innalillahi wa'inna ilaihirraju'un" kawai yake yi shi kan shi ba domin yana namiji ba tashin hankalin da suke ciki ba zai saka ya iya mallakan kansa ba. Ba shi ya haifi Mansoor ba amman da gaske yake yi ya karɓo amanarsa kuma yana jin sa kamar Mu'azzam ne shi a wajensa.
Tabbas Baban Inna ya janyo ma kansa fitinar da tafi karfinsa haka Inna Meri da Baba Ɗanjuma ke ta raya acikin ransu saboda ganin samudawan Sojojin dake tsaran gidan Major fuskarsu ba fara'a daga gani ba su san wani abu wai shi Imani ba sun fi gane yaren umarnin wanda ya ijiyesu.
Su kansu kafin Sojan dake tsaren get ya amince su shiga sai da Alhaji Hamza ya kira Yayan na shi da kansa ya yi masa mgana sannan ya kira wayar sojan sannan aka buɗe musu get suka shiga cikin gida.
Har da Yaddiko a ka zo sai ga su kowa ya yi zaman sanyi a cikin falon gidan Major Kabir, Inna Meri tana shan kuka lokaci ɗaya tana riƙe da hannun Mu'azzam, Mimi kuma ma na jikin Mami tana wani irin kuka mai ban tausayi. Hajiya kuwa girgiza jiki kawai take yi ta kasa mgana domin kunyar su Inna Meri take ji, tun bayan gaisawar da suka yi da Mommy ga shi an kawo musu ruwa da lemu amman zullumi ya hana kowa motsi.
Hajiya ta kalli Alhaji Hamza lokaci ɗaya tana faɗin" Wai ba ka ga ya ma Kabiru har da ni aka zo ba ne?.
Cikin ladabi ya ce" Na gaya masa Hajiya, ya ce ga shi nan tahowa."
Sai kawai ta jinjina kai wani abu na taso mata acikin kirjinta.
Murja ta kalla da ke rike da ƴarta itama daga gani ta sha kuka ba ta cikin natsuwarta. Cikin tsausayi Hajiya ta ce" Murja har ke Kabiru bai saurare ki ba ko? Kuma ba ki san inda ya sa a ka kai yaron mutane ba ko? Mommy ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce" Ba irin rokon da ban yi masa ba Hajiya ɗan uwansa ma yana kuka ya roƙonsa amman bai saurare mu ba, bai sa an fita da shi ba ya na nan acikin Kurkunsa na cikin gida, ba wanda ya isa ya sa su fito da shi sai in har shi ne ya ba su umarni Hajiya." Yaddiko ta yi kasaƙe kafin ta ce"Kai jama'a kurkuku kuma ?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce"Eh ya na da wani ƙaramin ɗaki da bai wuce tsawon gajerun mutum ba, sannan ba shi da faɗi kuma a ƙasan yake, akan sanya mutum a ciki in ya yi wani laifi domin a yi masa horo."
Gabadaya sai Inna Meri da Baba Danjuma su ka kara ruɗewa, Yaddiko ta saka salati Hajiya ta karishe ma ta shi ko Alhaji Hamza kai ya girgiza kafin ya ce" To duk me ya yi zafi? Wannan lamarin da duk an bi shi a hankali da an warware komai cikin sauƙi"
Inna Meri ta zube a kan kafafunta daga saman Kujera ta haɗa hannayenta waje ɗaya tana faɗin"Don girman Allah Hajiya kin yi min rai ki saka a saki Baban Inna wlh na yi miki alkwarin ko hanyar gidan ki bazan kara kallo ba har abada,ni dai ku saka ya sake shi kuma shima in sha Allahu ba zai kara kusantar Inda ƴar ku take ba, laifin yaro ne tunaninsa ba ya ba su abu dai dai in da ace yayi tunanin shi kanshi ba zai janyo ma kansa rigimar da ta fi karfinsa ba.".
Tana mgana tana kuka Mu'azzam na taya ta sai aka rasa mai lallashinta ballantana ya ce wani abu, Hajiya ke sharan kwalla a ɓoye Mommy kuma na tausayin ƴarta ne.
Ana cikin wannan halin sai ga Major kabir ya shigo cikin kakinsa na aiki wani Soja na mara masa baya. Yana shigowa cikin takunsa na zafin nama na cikakkun mazan jiya, sai ya ɗaga ma Sojan hannu fuskar nan ba rahama shi kuma sai ya juya ya fita bayan ya sara masa.
Baba Ɗanjuma kallo ɗaya ya yi masa shima tsoronsa ya kamasa sai ga shi shima zube kan kafafunsa kusa da Inn Meri ya na rawan jiki da na zuciya.
Ya ga Hajiya a zaune amman bai nufe ta ba sai ya samu wata kujera mai zaman mutum ɗaya ya zauna ya ɗora kafa ɗaaya kan ɗaya ya na ƙare ma mutanen falon kallo har ya sauke kan Hajiya cikin yanayin maganarsa ta Sojoji ya ce" Hajiya duk wannan taron na menene.? da kun yi zaman ku yaro zai yi wasa da gidan Soja ne shi ne nake so na koya masa hankali nan gaba ko sunan Soja ya ji an ambata sai ya yi fitsarin jini acikin Wandonsa." Kafin Hajiya ta samu zarafin mgana Inna Meri ta rarrafa tsakiyar falon kamar ta kwanta masa, ita ko iya kallonsa ba ta yi saboda firgici cikin roƙo kamar zai yi mata gafara ta fara faɗin"Don Allah ka yi masa aikin gafara ka yi hakuri ka yafe masa yarinta ke damunsa amman ina wuyan Baban Inna ya yi karfin da zai ja da kai? Ka yi masa rai don Allah ka sake shi."
Take faɗa tana kuka har da majina, A kaikace Major ya kalleta cikin wani irin Murya ya ce"Wace ce ke?
A razane ta ce"Ni ni mahaifiyarsa ce, ga mahaifinsa nan."
Ta faɗa ta na nuna Baba Ɗanjuma da shima ya ƙariso tsakiyar falon da jan gwiwa Mu'azzam ganin iyayensa duke kamar masu neman gafara ya sa shima ya rarrafa cikin jan gwiwa zuwa kusa da su ya durkusa ba zai bari kimar iyayensa ta zube ba, ko da ba shi da yarda zai yi gwara shima ya yi zaman neman gafaran tare da su. Sai da Major ya gama musu kallon wulaƙanci sannan ya yi wata irin sariya kafin ya ce"Ke ce uwar da kika ki haifi mara kunyar yaron da zai ja da ni? Kai kuma kai ne uban da ke rikon Agolan dake neman ja da Soja?
Ya karishe faɗa yana nuna kansa bayan kuma daga karshe ya nuna su ɗaya bayan ɗaya jikinsu na rawa kansu na kasa kamar sun ga wani mala'ikan mutuwa, kuma kowa ya kasa mgana Hajiya bakinta ne ya yi nauyi? Me za ta ce? Ko ta yi mgana ba zai taɓa Sauraranta ba tunda halinsa ne baya girmama maganarta a matsayinta na uwa a gare shi. Alhaji Hamza ne ya yi gyaran Murya ya fara mgana da cewa" Major.."
Sai kawai ya ɗaga masa hannu cikin kaushin Murya ya ce"Ya raina matsayina, yaron ya yi min tsurin ido bayan ya fara soyayyaa da ƴata ba tare da sanina ba, sannan ya zo har gidana ina mgana yana tsaye ina tsaye sannan wai ni zai nuna ma tsageranci? Sai ni kuma na nuna masa ba'a zuwa gidan Soja a yi taurin kai na ce su yi ta dukansa in har bai yi nadama ya ba da hakuri ba, ka da su barshi ko duka zai kashe shi"
Mimi ta saka wani irin kara ta miƙe tana faɗin" Abi."
"Ke sai na harbe ki, in kika kara mgana anan wajen nonsess kawai."
Ya faɗa cikin zafin nama har yana miƙewa da sauri Mommy ta mike da sauri ta maƙale ƴarta a bayanta tana rawan jiki, Hajiya ta yi yunƙurin mikewa dai dai sanda Inna Meri ke dukar da kanta a kasa tana haɗa Major Kabir Allah da Annabi ya saki Mansoor shi kuma ya ce ba yanzu ba sai ya san da wanda ya ke faɗa. Cikin yanayin ba da umarni Hajiya ta ce"Kabiru ni a matsayina na Mahaifiyarka na ce ka saki yaron mutane ka sake shi."
Cikin kallon Hajiya ya ce"Hajiya kinsan me ya yi min ne? Kama na kamar ni wannan yaron talakawan zai ja da ni?.
Da ƙarfi Hajiya ta ce"Ba na son ji komai, ka sa ka a saki yaron nan yanzun nan ban san zalunci."
Ta faɗa cikin bayyana bacin ranta har da hawayenta sai ya fara huci yana wani cijewa kamar zai kai duka.
Sai Hajiya ta fara kokarin dukawa tana Fadin" Ko nima sai na duka ne?.
Da sauri Alhaji Hamza ya mike ya isa ga Hajiya ya riƙe ta yana Faɗin" Haba Hajiya ai kin wuce haka a wajen Yaya zai yi abin da kike so yanzu ma kuwa"
Major Kabir ya kallah kafin ya ce" Major ka sa a saki yaron nan don Allah, ka duba darajan Hajiya ga kukan da rokon da iyayen yaron ke yi maka, ka yi masa afuwa ka saka a sake shi." Yadikko ma ta saka baki, sai da Hajiya ta fashe da kuka tana Fadin"Shike nan kabiru kada ka sake shi. Wlh in har wani abu ya sami yaron mutane ba zan taɓa yafe maka ba."
Jin haka yasa Alhaji Hamza ya ce" Major ka sarrafa fushinka, Hajiya ke mgana da kai fa."
Sai da ya fitar da iska daga bakinsa sannan ya ɗaga waya ya kira ɗaya daga cikin Sojojin ya ce a taho da wannan yaron zuwa falonsa ya na jiran su. Cikin lokaci kaɗan da bai gaza mintina goma ba sai ga shi sun shigo da shi kamar sun ɗauko wani cuta suna zuwa tsakiyar falon suka sake shi ya faɗi kasa warwas tunda ba shi wani kuzari, Kamar ma sun watsa masa ruwa ne ya farfaɗo tunda faran rigan jikinsa duk ya baci da jini, fuzkarsa ta kumbura idanuwansa sun shige ciki saboda tsabar duka bakinsa ya sumtuma da goshinsa.
Bai iya kuma motsa hannunsa na dama da kafarsa ta hagu ba, kallo ɗaya zaka yi masa ka san cewa ya bugu buguwa na sosai tunda har kammaninsa ya sauya.
Da wani irin sauri da kuka Inna Meri da Baba Ɗanjuma suka nufi Mansoor Mu'azzam ya tarairayo sa jikinsa yana ta kiran sunan shi amman ko iya buɗe ido ba ya yi saboda tsabar duka, yana so ma ya bude ido ko ya yi mgana ya kasa Allah ne ya yi kwanansa na gaba kwana suka yi suna dukanshi, shi kuma bakar zuciyarsa ta hana shi ya yi nadama. Inna Meri ta riko hannun da na dama da sauri ta ga ya janye hannu ya na cije leɓensa da duk ya fashe saboda duka cikin kuka Mu'azzam ya ce"Inna bar taɓa hannun kila ya samu gocewa ne."
Baba Ɗanjuma yana share ma Mansoor jinin goshinsa da haɓan rigansa lokaci ɗaya yana kiran sunan shi"Baban Inna buɗe idanuwan ka? Baban Inna, Baban inna" Haka yake ta kiran sunan shi yana jin su amman kuma ya kasa iya buɗe idanuwansa.
Mmi na leƙensa ta bayan Mommy tana kuka ta san in ta ce za ta karisa sai Abi ya saka bindiga ya ɗauke kanta Khadija ma tana falon amman itama ko motsi ta kasa, Hajiya kuwa sai kawai ta dukar da kai tana kuka faɗi ta ke yi
"Kabiru wlh ka ɗauki hakkin wannan yaron kuma in har bai yafe maka ba sai Allah ya isar masa"
Yaddiko sai salati ta ke yi ganin Yadda Sojoji su ka maida hallitar Mansoor.
Alhaji Hamza kuma ya ma kasa magana bai ɗauka rashin imanin Yayan nasa ya kai haka shahara ba, shi ko tsoron ya kashe shi ba ya yi. Hawayen Inna Meri da na Mu'azzamu na ɗiga a saman fuskar Mansoor su suka taimaka har ya iya buɗe likakkun idonsa guda ɗaya ya na kallon iyayensa suna kuka saboda halin da ya saka su, yunkurawa yake yi kamar ya tashi amman kuma ya kasa sai da Mu'azzam ya rike shi sannan ya iya tashi zaune, amman dauriya ce shi kaɗai yasan halin da yake ciki.
Major Kabir kuma sai mirmishin mugunta yake yi kafin ya ce"Zan kyale yaron ku saboda Hajiya amman ba domin haka ba da sai ya raina kansa, amman ko yanzu ya san karo da Soja ba wasa ba. Sannan akwai sharaɗin da zan kafa muku da in har ya tsallake su anan gaba sai dai shi ya mutu wlh." Inna Meri da Baba Ɗanjuma har suna karo da Juna wajen ƙara dukawa gaban Major Kabir, suna rawan bakin sanar da shi sun amince kuma Mansoor zai yi biyayya ga Sharaɗin sa.
Major Kabir ya nuna Mimi da yatsa kafin ya ce"Ba shi ba ƴa ta, ko kallonta ya kara yi in na sani sai na lalata rayuwarsa, sannan ya sani kada ya kara min wannan tsaurin ido Mimi tafj karfin talaka kamarsa wanda har ubansa ya bar duniya bai shigo birni ba, Kuma ni ba zan iya aura ma ƴata Agolan da rayuwarsa ba ta da wata mamora ba, daga yau sai yau na raba wannan alaqar ba shi ba ƴa ta ba rayuwata in kuma ya ki ji to Wlh a karo na biyu har ku mutu ba za ku kara ganinsa ba domin sai na ɓatar da rayuwarsa, Kuma ba zai bar wajen nan ba sai ya duka ya nemi gafara ta kamar yadda kuka yi yanzu in kuma har yanzu bai yi laushi zan saka shi ya yi laushin."
Ya faɗa ya na nuna Sojojin da ke baya sun kame, Inna Meri har tana rawan baki riko hannun Mansoor ta kamkame tana fadin"Darajar haihuwar ka da nayi Mansoor ka buɗe baki ka ba shi haƙuri saboda ka tsira da rayuwarka."
Mansoor kukan zucci ya ke yi zuciyarsa na wani irin suka, yana ji kamar ya zama asarrare mara amfani, duba yadda Mahaifiyarsa da wanda ya zame masa uba da ƙaninsa suke kuka saboda shi, kalli yadda suke duke gaban wani hallita na Ubangiji saboda shi , yau saboda shi an kira sunan mahaifinsa an zage shi da gorin ya mutu a kauye bai taba shiga birni ba, shi ba yana kukan dukan da ya ci ba ne da dai ya ba ma wannan mugun hakuri gwara ya kashe shi, Shi ko da wani suna zai iya kiran kalmar Soyayya? Tun jiya ya ke son yaji ya tsani Mimi acikin ransa amman ya kasa, ji yake yi kamar ya mutu baƙinciki da yake cikin zuciyarsa tunda ya zo duniya bai taɓa tsintar kansa aciki ba. Ba shi da niyar saduda ya so ne su bar shi ya kashe shin in dan har zai iya, Sai dai Kukan Inna Meri da na Baba Ɗanjuma tare da Mu'azzam suna masa magiyan ya bashi hakuri saboda ya tsira Inna Meri ta san halin abin da ta haifa yasa a fusace ta ce"Ko ka bashi Hakuri ko na ce sai ka biyani Nonona da ka sha"
Baba Ɗanjuma ya kira sunanta da karfi cikin tashin hankali.
"Meramu.."
Hajiya ma sai da ta kira sunanta ita kuma ta yi hakane saboda ya ba da hakurin ta san halin Baban Inna da kafiya sai yace sai dai a kashe shi. Kuma hakan da ta yi sai a ka samu masalaha domin Mu'azzam ya rike sa ya durkusa saman gwiwiyonsa tare da Iyayensa kansa na kasa ya na jin taruwan hawaye acikin idanuwansa, ko dukan da aka yi masa bai saka shi kuka irin wannan tozarcin ba muryansa ba ta fita ma sosai Saboda wahala ya furta" Ka yi hakuri..!"
Yana gama faɗin haka sai ya ji wasu hawaye masu zafi sun sauko masa.
Nan Major Kabir ya Koma ya zauna yana Faɗin"Good. za ku iya tafiya da shi amman ya kiyaye sharuɗɗana.
Inna Meri da Baba Ɗanjuma suna rawan jiki masa godiya su ka miƙe jiki na rawa Hajiya nauyi da kunya su ka hanata mgana Alhaji Hamza ne ya ce su tsaya mana a nema musu Jirgin komawa da sauri Baba Ɗanjuma ya ce"Mun gode da karamci ranka ya daɗe ya isa haka."
Hajiya ta yi saurin kallon Major kafin ta ce"Kabiru ka dubi halin da Binta ke ciki Hausawa su ka ce idan An ciza a hura watarana kada ka zo kana nadamar abunda ka aikata ma wannan yaron"
"Ni? Kamar ni Major Kabir My Daughter ta auri talaka Agolan da ubansu har ya mutu a can wani kauyen kurmus, uban rikonsa wanzami uwarsa yar aiki? Over my dead body Mimi za ta yi wannan auran ƙaskanci ba ta isa ba, ko za ta mutu bazan aura mata wannan talakan ba, jinin takalawa wanda bashi da wata kyakyan makoma ko anan gaba." Ya karishe faɗa a fusace kamar ba da Hajiya ya ke mgana ba, kawai sai ta girgiza kai kafin ta ce"Shike nan Allah ya hana mu jin kunya watarana."
Ta faɗa ta na kallon yadda Idanuwan Mimi suka kumbura saboda kuka, Mommy ma sharan kwallan take haka ma Khadija kowa kuma yasan ba'a kyauta ba, amman kowa yana tsoron ya yi mgana wanda bai girmama maganar uwar da ta haifesa ba ai ba wanda kuma ya isa ya yi masa mgana ya saurare shi.
Mu'azzam ya riƙo sa tunda ba ya iya tsayuwa gefe kuma Baba Ɗanjuma ya kama shi za su fita daga falon da gudu Mimi ta ƙwace daga jikin Mommy ta ƙarisa gaban Abi cikin kuka Ta ce.
"Abi ka yi hakuri Abi ina son shi don Allah kada ka raba mu da juna"
Cikin tsawa Ya ce" Sai dai ki mutu, amman Wallahi tallahi ba za ki auri wannan talakan yaron nan ba, ba shi da makoma mai kyau, ina tambayan ƙwalin karatun shi Hajiya na gayamin iyakarsa Secondary school. Soja yake son zama ire iren su ma ba su da wani rabo a duniya." Mimi ta katse shi cikin gunjin kuka tana kara faɗin.
"Abi ina son shi.."
"Ke yarinya ce Mimi, karatu nake so ki yi ba yanzu zan yi miki aure ba"
Ya faɗa shima bayan ya katseta cikin kaushin Murya.
"Abi Ina son shiiiii..."
Ta faɗa cikin wani irin karyayyen sauti kamar za ta shiɗe.
"Murja ki ɗauke min Mimi kada raina ya ɓaci na fasa kanta da bindigata"
Ya faɗa ya na kokarin sarrafa fushin sa domin ji yake yi kamar ya tokareta ta faɗi in ta na haɗa shi da wannan ƙasƙantaccen yaro nan mara makoma mai kyau.
Ba zai manta da wannan kukan da ta rika yi lokacin da mahaifiyarta ke rike ta ba, har gobe yana jin Sautin wannan kukan acikin kirjinsa. Ya tuna ta na miƙo hannunta Mahaifiyarta da yayarta khadija suka riƙe ta suka tafi da ita zuwa cikin wani ɗaki.
Yayi ƙokarin danne abin da ke taso masa amman sai ya kasa, kafarsa ya makaleta ya kasa tafiya da ya sa su Mu'azzam su ka tsaya su na kallonsa ba su san abin da zai aikata ba da ba su barshi ya kara yin mgana ba.
Sai juyawa kawai su ga ya yi ya na faman ɗingisa kafa idanuwansa a like ga kaya duk sun yage ba hula ba takalmi kamar wani almajiri cikin muryan da ta galabaita ya fara faɗin.
"In har ni Mansoor na haifu cikin uwata Meri da uba na Ibrahim ƴarka ko ita kaɗai ta rage a duniya nan sai dai ta mutu nima na mutu ban yi ba aure ba,"
Ya faɗa ya na sakin numfashi Inna Meri na kokarin toshe masa baki amman sai da ya ida sa faɗin abunda ke ransa a lokacin.
"Nayi alkwarin toshe kunnuwana daga jin ta da ganinta na yi alkwarin sauya duniyata daga duniyar ta na yi alkwarin sauya mattacen mafarkina a kanta, na kuma gode maka da ka fahimtar dani darasin rayuwar dana daɗe ana ga ya min ban ɗauka ba, na kuma fahimci akwai tazara mai kimanin kilomita tamanin tsakanina da ƴarka, na kuma fahimci matsiyaci kamata ya yi shisshigi wajen tusa kansa in da bai dace da shi ba, yadda ka saka iyayena kuka a kaina kai ma watarana sai ka yi kuka saboda ƴarka."
Yana gama faɗin haka ya juya kamar zai kifa saboda yanayin jikinta Major Kabir ya yi wani kayattacen mirmishi kafin ya ce" Ku ja ma ɗan ku kunne, na ga alaman tsageranci na damunsa sannan ku yi masa iyaka da ƴata domin ruwa ba sa'an kwando ba ne, zan sake shi na yanzu amman ko kallon Mimi ya sake yi sai na ɗaure shi da kakin jikina." Baba Danjuma bakinsa na rawa ya ce"Ba ma zai kara kallonta ba In sha Allahu ka yi hakuri."
Haka su ka fita da Mansoor a rirriƙe da shi saboda halin da ya ke ciki, kuma ba wanda ya bi bayan su. Shima Major ɗin mikewa ya yi a fusace ya shige cikin ɗakinsa har yana banko kofa Hajiya ta bi shi da kallo tana Sassauta fushinta domin kada ya zama masifa ga rayuwar Kabiru. Amnan ita ta so da aka Ciza sai a Hura saboda ba'a san abunda gobe za ta haifar ba.
Ko kwana ba su yi a Abuja ba Hajiya ta ce gida zata koma, Mimi kuma ta zauna wajen mahaifinta ba za ta kara amsar ta riko ba tunda ga abunda ya biyo ba, Mommy ta yi tayi Hajiya ta kwana Hajiya ta rantse ba za ta kwana ba. Hajiya na ba ta hakuri Mommy ma na ba ma Hajiya hakuri ta yi mirmishin takaici kafin ta ce"Bakomai Murja wata rana Kabiru zai yi nadama, sai dai ina fatan Lokacin da zai yi nadamar lokaci bai kure masa ba.
Alhaji Hamza a lokacin ya nema musu jirgi suka juya zuwa Gombe kuma har suka bar gidan Major bai fito daga ɗaki ba,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 26