awannan damunar dan gujewa kamuwarsu da damshi.inanan kano unguwar sharada ina tyra kayana ko ina a nigeria.08033627255
*Page 18*
Huci kawai ya ke saki shi kaɗai ransa in ya kai dubu ya ɓaci Inna ba ta kyauta masa ba, ba domin Baba Ɗanjuma ya ga fitowarsa ba, da anguwan zai bari dole ya yi alwala suka tafi masallaci tare ana idarwa saboda kada ma su Baba Sani su tare shi ya yi saurin tashi yana kara waya a kunne kamar yana waya Baba Ɗanjuma yana can yana musabaha da mutane Baba Sani da Baba Ɗanlami kuma ganinsa ya sa suke Allah Allah su fito domin su haɗu amman ko da suka fito ya bar haraban masallacin ma gabaɗaya.
Baba Sani ya jinjina kai kafin Ya ce
"Ɗanlami wai ka lura yaro nan yana gudun mu ne yanzu? Baba Danlami ya yi kayfci kafin ya ce"Wlh nima na lura, ka bar mutum kawai saboda kuɗin da yake ba mu ne duk wata sai ɗan taimako in ya taso, ba dole ya ganmu ya yi wucewarsa ba tunda ga yan maula." Baba sani ya yi shuru kafin ya ce"Laifin duk na Yaya Ɗanjuma ne, in da amana muma fa muna da hakki akan dukiyar yaron nan tunda ai gidan uban mu aka riƙe shi, amma ya tattare komai ko nuna masa matsayin mu ba ya yi yadda ake ba ni labarin kuɗin yan ƙwallon kafa wlh zai iya kai mu saudiya ma sannan ya siya mana manyan gidaje a garin Abuja da motoci."
Baba Ɗanlami sai da ya yi wata yar dariya kafin ya ce"Haba! to ai naga shi ma Yaya Ɗanjuma bai kai shi Saudiyan ba ma sannan bao sai siya masa mota ba, ya dai gyara gidan ya siya masa mashin itama tunda aka sace ai bai kara siya masa ba, kai ko uwarsa Meri ai ba kai saudiya ba mu kuma a suwa? Karan kaɗa miya."
Baba Sani zai yi mgana kenan sai ga Baba Ɗanjuma ya zo wajen sai ya yi shuru hannu ya ba suka yi yi musabaha daman tunda ya gan su yasan da wata mgana.
Baba Ɗanlami ne ya fara faɗin.
"Yaya Danjuma gaskiya ka yi ma yaron nan Mansoor mgana, kamar mu zai gani ya rika wulakantawa? Baba Ɗanjuma ya yi saurin cewa"Anya? Ko dai bai gan ku ba ne?
Baba Sani ya ce" Zencen kake so, ya fa ganmu amma sai ya ɗauke kai ya yi wucewarsa in ma saboda ɗan abin da yake ba mu ne ya ke ganin kamar ya na yi mana alfarma gwara ka gaya masa gaskiya muma muna da hakki a kansa tunda ya tashi a ƙarkashin mu, duk tsiya dai a gidan Wanzamai ya tashi kuma da gidan zai yi tutiya yau ko saudiya ya kaimu bai biyamu rikon da mu ka yi masa ba ahto."
Baba Ɗanlami ya ƙarishe da faɗin"Ka ji zencen gaskiya." Baba Ɗanjuma bai yi mamaki ba sanin halin ƴan uwan nashi kamar waɗanda suka taɓa tsinana ma Mansoor ɗin wani abu suna ta kumfar baki, baya son nana ta mgana ɗaya ya sa ya ba su hakuri yace zai yi masa mgana.
Ashe korafin na su ba ɗaya ba ne nan take Baba Ɗanlami ya kalli Yayan na shi yana faɗin" Shi kuma Mu'azzamu dai ya manta damu? Ko wancan zuwa ma bai bari mun haɗu ba, ina ga ko ya yi saƙo iya kai da Meri saƙon ke zuwa gare ku, domin ba na jin ko Magajiya tana samun wani abu aciki."
Sai alokacin ya buɗe musu ido cikin gargaɗi ya ce"Ko ni da na haifesu ban kwanta a gida na dogara da su ba, suma ai suna da na su uzurin rayuwar duk abin da kuka ga ba'a baku ba ba'a kawo ba ne, wani abun ma ba na sanin da shi ake ɗauka a baku ba yaran nan duka biyu daga Mu'azzamu har Mansoor ɗin ba sa yi min abu ba su yi muku ba ko da ɗinki ne na kaya domin ɗaya suke ɗaukan mu, kune da shigen zarge zarge da tsegumin ku da ya sa kuka kasa fahimtar komai ballantana ku godema Allah Bisa ni'imar da ubangiji ya yi muku."
Yana gama faɗin haka ya yi wucewarsa ya bar su su na raka shi da harara Baba Sani har ya na kwaikwayon maganar Yayan na shi Baba Ɗanlami ya ce"Dankari! Mgana fa ya faɗa mana wato ba ma gode ma Allah kuma sannan mu zuciyarmu ta mutu sannan har da gorim mu ƴaƴanmu su yi mana ɗin " Baba Sani ya yi tsaki kafin ya ce. "Kyaleshi akwai ranar maida martani."
Suna tafe suna ta faɗin mganganu.Suna zagin ɗan uwansu uwa ɗaya uba ɗaya da suke tunanin ya samu duniya zai wulakantasu Ahalin duk tarin alherin da sanadin su Mu'azzam suke samu har gobe ba su gani ba Ƴaƴan na su kowa na fama da rayuwa wasu ma ga iyalai ba aikin yi, shi fa babban yaron Baba Sani Direba ne yau ya na da mota gobe bai da shi, bai da ma takamammen mai gidan da zai ba shi mota saboda tsabar rigime rigimensa, sauran mazan na shi kuma duk ba wani mai ƙwakwaran Sana'a sai Hayatu kaɗai da ya ke sana'ar fenti amman kuma shi kanshi ya sani da iyalansa ko kaɗan ba shi da zuciyan taimakon iyayayensa da ga shi sai matar shi sai ƴaƴansa dangin matarsa kawai da ita suke shanawarsu.
Sauran matan kuma suna gidajen mazajensu suna ji da kansu, wasu ma suna nema ne, shi ko Baba Ɗanlami duk wannan Kumfar bakin da ya ke yi ya na da ya'yan amman ba su iya taimakonsa da komai, tunda Abdurrahim ɗinsa ya na sana'ar sai da kayan wuta, sannan ƴarsa Bara'atu tana auran mai kuɗi sai dai irin makokan nan ne, ita kanta ba ta ci ba ballatana ta kawo gida. Amman ba'a taɓa jin suna mgana kan ƴa'ƴansu ko samu suka yi ba su taɓa nunawa a gani bar su dai ko da yaushe idanuwansu na kan Mu'azzam da Mansoor gani su ke yi kamar suna kawo ma Baba Ɗanjuma wani duniyar ne su ba ya ba su, ko kuma suna ware su ba sa ba su kuɗi tunda su gani suke yi wani duniya Mansoor da Mu'azzam suka tara.
*******
Da bacin rai ya isa gidansa, daman kuma a mashin ɗin haya ya zo, motarsa ya kunna ta sai ta fara wani hayaki sai kawai ya barta sai ya kira bakanike mashin ɗin sa kuma ta yi kura sai ya kai wanki kuma yana jin kasalar zuwa sai kawai ya hau mashi ɗin haya zuwa can anguwar. Sai ga shi ya je ya ji abin da ya kusa saka shi kamar ya mutu saboda Haushi shiyasa ko jimawar da ya so ya yi bai yi ba ya yi tafiyarsa dalilin da yasa yana ganin su Baba Sani suna jiran sa kuma in ya tsaya a yadda ya ke jin ɓacin rai zai iya yi musu ba dai dai ba, in kuma ya yi musu mgana yana cikin fushi ya faɗi abunda bai dace ba sai su ji haushin shi shi ya sa ya yi tafiyarsa kawai.
Takaicinsa ɗaya wai Inna har da gayya ta yi na zuwa gidan to ina abun zuwa Allah ya jiƙan rai ga wanda ya kusa kashe miki ɗa Mu'azzam ya faɗo masa a rai daman ya san duk yana sane da duk abunda ke faruwa aiko sai ya ci masa mutumci. Sallar Isha'a a gida ma ya yi yunwa ya ke ji amman ɓacin ran da yake ciki ya hana shi ya sama ma kansa mafita. Mu'azzam ya doka ma kira ya na faman huci fushinsa tsab yake son ya huce a kansa.
Mu'azzam na tare da Matarsa Hibba suna yin Dinner sai ga kiran Mansoor ya ɗauka da zumuɗin sa sai dai zumuɗin ya koma ciki domin cikin faɗa da masifa Mansoor ya fara faɗin" Mu'azzam !Mu'azzam! Mu'azzam! Sau nawa na kira ka?
Yana jin haka ya san yau shi kuma sai ya sha masifa. Cikin sanyin murya ya ce.
"Sau uku."
"To ka kiyayeni wlh in ba haka ba sai na ɓata maka rai, bar ganin kana da kaki, kakin ka banza ne ni awajena ba ka wuce ƙanina da nake yi ma hukunci in ya yi ba dai dai ba."
Mu'azzam na shafa keyarsa yace"Me na yi ne yau kuma? Cikin kufuluwa Aji ya ce"Abunda ka san ka aikata ashe ba ka da kishin kai ban sani ba? Kai ne ka kira Inna ka na gaya mata wai su Mimi sun dawo ka sakata ta ɗauki su Walida suka tafi gidan wai sun je gaisuwa me ye haka? Me ye alaqar mu da su da har kake wani yaɗa sun dawo? Ba na son wawanci fa Mu'azzam ka sanni sarai." Mu'azzam ya yi shuru ya rasa na cewa in ya yi mgana sai maganarsa ta yi zafi sai kawai ya zaɓi da ya yi shuru haka ya zauna sai da Mansoor ya gama masa masifa da faɗa sannan cikin ladabi ya ce"Allah ya baka hakuri ba da wata manufa na faɗa ma Innar ba, kuma har ga Allah ni ban ma san za ta je ba domin ba ta faɗa min ba."
Mansoor ya yi ƙaramin tsaki kafin ya ce"Ni fa na daina yarda da kai, kai ma ka koma layinsu Nasir, nan ba har lambata ka ba ta ba? Mu'azzamu kada ka bari mu haɗu domin haɗuwarmu ba za ta yi mana kyau ni da kai ba." Daga haka ya katse wayar ya bar shi sagale da ita a kunne kafin shima ya sauke yana faɗin"Ikon Allah!
Ajiyar zuciya ya sauke kawai ya Cigaba da cin abincinsa Hibba ba ta yi mgana ba tana fama da Junoir ne ma a lokacin to ita ai ba ta isa ba wannan faɗan tsakanin Yaya da ƙaninsane, sai dai in bai yi masa wani abun da ya baɓa masa rai ba haka zai kirashi ya yi mishi faɗa ko Inna da Baba albarka.
Har mamakin masifar Yaya Mansoor take yi, shi abu kaɗan a wajensa na faɗa ne. Tana ta nazarin mijin nata ya na cin abinci yana mirmishi shi kaɗai, cikin mirmishin itama Ta ce.
"Me ya faru ne.? Na ga kana ta mirmishi kai kaɗai"
Kai ya kaɗa kafin ya ce"Ina son yayana, na tabbata duk duniya ba wanda zai kai sa kaunata wani abu na tuna kawai da ya sa naji zuciyata ta yi sanyi. Fata na nima wata rana na saka shi farinciki kamar yadda yake sakani." Ba ta matsa sai ta ji me ya tuna ba ta amsa da Amin Amin, sai da ya gama cin abincin sa sannan ya kira Inna bayan ta ɗauka sun gaisa ya faɗa mata yadda suka yi da yayan na shi cikin yar dariya Inna Meri ta ce"Kyale shi ɗan inna faɗan da ba zai iya yi min ba ne ya sauke maka, rabu da shi kada ya saurara ma kansa ya je bakar zuciyarsa ta hana shi zama lafiya da kowa."
Sun ji ma suna ta mgana da Inna, tana bashi labarin yadda Hajiya ta yi ta murna da ganinta amman ba ta faɗa masa mganar Mimin da Hajiya ta yi mata ba, amman ta faɗa masa Hajiya ta ba ta labarin Major ya so ya zo ya nemi gafaran Baban Inna kan lamarin da ya faru a baya sai dai Allah bai yi ba lokaci ya ƙare. Mu'azzam ya ce"Mu ai ba mu da matsala Inna, tuni mun yafe abunda ya faru matsalan daga Yaya Mansoor ne shi fa kamar ba ya iya yafiya ga wanda ya ɓata masa Inna."
Inna Meri tace"Allah shi ya ye masa wannan cutar, domin cuta ne ta bala'i da ya kamata a nema masa tsari wajen Ubangiji."
Mu'azzam sai da ya yi dariya jin abunda Inna ta ce itama sai ta biye mishi suna dariya ƙarshenta dai kafin su yi sallama sai da ya ba ma Hibba wayar suka gaisa da Inna Meri ta na tambayan Megidan ta Hibba ta ce ga shi a jikinta ya yi barci sannan suka yi ma juna sallama.
Yaya Amina washegari da ta zo gidan ta ji abin da ya faru ta yi ta dariyan Bintu da ta gudu cikin dariyan ta ce"Bintu ga tsoro ga ban tsoro."
Inna Meri ta ce"Ina za ta tsaya jiya nan ya warwareta, ɗan inna dai aka kira jiya aka yi ma borin." Walida ta ce"Inna ke ma fa jiya kin yi ma Yayanmu tsawa."
Inna Meri ta ce"Da ban yi mishi haka ba, da ba zai bar mganar ba, ni kaɗai nasan fitinar za ta faru ƙarkashin wannan maganar."
Yaya Amina ta ce"Gaskiya tunda shi dai ba zai gane abunda aka yi ba, Allah Sarki ashe ba ta manta damu ba."
Walida tace"Wlh ta ce duk a gaishe ku."
Yaya Amina ta ce"Mu na amsawa da Inna ta min mgana ai da tare za mu je."
Walida na riƙe dariyanta ta ce"To yanzu ma ba ta ɓaci ba, in za ki je ne ai gidan ba ɓoyayye ba ne."
Ita Kuma Yaya Amina sai ta ce sai dai in Walida za ta raka ta ita kuma ta ce ba da ita ba ya zo Baban Inna ya ji labari ya yi biji biji da ita. Inna na gefe ta na yi musu dariya kafin ta ce"Sai dai ya yi muku amman ni ai na kuna ba na tashin ƙauri ba yadda za'a yi dani sai hakuri."
Yaya Amina ta ce"Inna ke sha kumdun ne, ni kuwa sai ki sa ya kulla dani mu na yar mutumci da ɗan ƙanina,Halima har mamaki take yi in taga muna hira na kan ce ma ta tun tuni daman tamu ta zo ɗaya da Baban Inna" knna Meri na sakacen hakorinta ta ce"Ke ku rabani da halin Baban Inna, zuciyarsa har wani zaɓan wanda za ta yi mu'amala take yi, Allah dai ya ye mishi wannan cutar." Walida na kwasan dariya ta ce "Inna ba shi da lafiya ne?
Kai tsaye ta ce"Eh mana ai ciwo ne babba ma kuwa, ku yi ta masa addu'an Allah ya ye masa." Suna ta dariya Inna Meri na faɗin su daina dariya ba abun dariya ba ne.
Yaya Amina na gidan har bayan la'asar sai da su ka yi sallar sannan Amina ta ce Walida ta raka ta su je gidan Bintu.
Walida ta ce ita makaranta za ta je Yaya Amina ta ce to su je in ta rakata sai ta wuce makaranta daga nan.
Inna Meri na zaune ta na jan casbaha tace"Ku gaishemin da Bintu, ku ce mata nan fa ba gidan Baba Inna ba ne ta kwantar da hankalinta ya yi mana ma yaji."
Dariya ta kara ka ma su Walida su ka fita suna yi Inna na gimtse fuska,.Da ya ke yau Yaya Amina ita kaɗai tazo yara duk suna makaranta har sun fita Inna ta kira su, bayan sun dawo ta kalli Amina tana fadin"Amina ki shiga bangaren su Gaje ki gaishe su, sannan ki shiga ɗakin Magajiya itama ki gaisheta ba ta jin daɗi."
Yaya Amina ta amsa da toh Inna sannan su ka fita ɗakin Magajiyan su ka fara shiga ta na kwance Jummai ta zo gidan ashe tana ganin Amina ta washe mata baki su ka gaisa
Aminan ta gaida Magajiya ta amsa mata fuska ba fara'a Walida ma duk da ta shigo da Safe sai da ta kara yi mata ya jiki ta amsa ta na wani haɗe rai ita dai Magajiya ba ta san zaman lafiya ciwo ya rafketa Mariya na gidan Zuwaira ba ta dawo ba Inna Meri ke yin abinci yanzu ta ke ba ta kuma safe da rana da yamma Inna Meri za ta shiga ta duba ta amman ko da rana ɗaya ba ta taɓa gode mata ba. ita dai Inna Meri komai take yi domin Allah ne.
Hiran da Walida da Yaya Amina suka riƙa yi kenan a kan hanyarsu ta zuwa gidan Bintu, da suka shiga shashen su Gaje ma har ana faɗa musu mgana kiri kiri Gaje ta ce ma Amina ba'a ganinsu ko sun zo suna ɗakin uwarsu Meri to ka da su manta suma ɗaya suke da Meri a wajen su.
Walida ko ta bata rai a ranta ta ce ba ɗaya ba ne, Amina kuma sai ta ba ta hakuri Harira ce ma yar ba ruwanta ba kamar Gaje da kamar halinsu ya zo ɗaya da mijinta wajen kallon rayuwar wani.
Sun je sun iske Bintu ita kaɗai a gida su Hassan sun bi babansu gidansu, abokiyar zamanta ba ta nan suna biki a gidanu, ta yi murna da ta gansu sai ga shi ta kawo musu ruwa da zoɓo daman ta na saida wa.
Ta zauna kusa da Yaya Amina tana faɗin"ki ce yau a gida kika yini"
Yaya Amina na shan ruwa ba ta amsa ta ba, sai Walida ne ta ce"E, ke ai kin gudu jiya."
Bintu ta ce"Uhm na yi gudun gara ne Walida yau da safe Baban inna ya kirani a waya ya zazzageni Walida."
Walida ta zaro ido Yaya Amina kaɗan ta ƙware da ruwa ta ɗago tana faɗin"Kai! me ya ce miki kuma?
Bintu ta yi tagumi kafin ta ce"Kawai da safe muna cikin karyawa da Bashir sai ga kiransa ni fa tunda na ga kiran Baban Inna nasan ba na alheri ba ne na tashi na yi ciki ina ɗaukan waya ko gaisuwata bai amsa ba ya fara min masifa wai mu munafukai ne ni da Walida me ya sa da Inna ta ce ga inda za mu rakata ba mu kirasa a waya a ɓoye mun faɗa masa ba? da ina masa rantsuwan ni ma ban san inda za mu je ba ya dakamin tsawa yana faɗin duk sai yaci ubanmu me ya sa da ta ce mu rakata ba mu ce ba za mu je ba? Kuma sannan mun yi masa ƙarya da ya kira mu ka ƙi gaya masa in da mu ka je, yace wlh wannan ƙaryan da munafuncin da mu ka yi masa sai mun raina kanmu."
Walida ta yi fiki fiki da ido ta kasa mgana Yaya Amina ta ce"To ke ba ki ba sa hakuri ba ne?. Bintu ta ce" Wani hakurin? Ya tsaya ne ma ina cikin mgana ya yi tsaki ya kashe wayarsa walh Baban Inna ya cika masifa"
Yaya Amina ta ce"To ai jiya ma yazo zai yi ma Inna ta balbaleshi da masifa shi ne ya koma gida ya kira Mu'azzam ya sauke a kan shi."
Bintu ta ce"Kai jqma'a shi ya yi hakuri da rayuwa mana, ni fa ban ga wani abu acikin zuwa gaisuwan da muka yi ba"
Walida ta ce"To ni ma dai shi nagani."
Yaya Amina ta ce"To shi gani zai yi ba kwa kishinsa ban da abunsa da mai rai ake fushi ba da wanda ya mutu ba."
Nan su ka cigaba da tattaunawa Walida ta shantake ba ta je islamiyan ba Bintu na ba ma Amina labarin yadda Hajiya da Mimi da su ka yi ta rawan jiki da su ka gan su.
Yaya Amina ta ce"Allah Sarki Itama kila har yanzu ta na son shi."
Bintu tace"To daman mana, shi ma duk wannan kumfar bakin na Soyayar ne."
Gabaɗaya suka saka dariya ba su suka baro gidan ba sai shidda saura na yamma.
Suna komawa gida Inna ta ga Walida ta dawo da wuri cikin faɗa ta ce" Amman dai ba ki je makarantan ba ko?
Walida ta sosa kai ba ta yi magana ba Inna tace "Ya yi miki kyau."
Yaya Amina ke labartama Inna yadda Baban Inna su ka yi da Bintu sai da Inna ta yi dariya amman ba ta ce komai ba acikin ranta tana son ganin yadda lamarin zai kasance. Shi dai kahaifin Mimi da ya fara ja Ubangiji ya karɓi kayanshi sauran Baban Inna shi kuma sai ta tsaya ta ga ina wannan bakar zuciyar za ta kaisa.
Kamar Inna ta sani yaji ya yi musu sai da ya kusan kwana goma sannan ya zo gidan Sun dai ji kabarin ya na kaduna sun je buga wasa daga bakin Mu'azzam shi tuni har sun shirya kansu. Sai da ya dawo ya zo gidan shima bai daɗe ba, Walida daman tana nemansa nan ta gaya masa an fara biyan Jamb ta na so ta biya nan ta ke ya ba ta kuɗin har da na abun hawa ya ce kuma in akwai wata matsalar ta kirashi ta wayar Inna ta gaya masa.
Duk kuma wannan abun bai zauna ba ya na tsaye a kofar ɗakin Inna Meri.
Ita ko ta yi masa banza kamar ba ta gansa ba, har ya tafi kuma sai ya dawo ya kira Walida yana tambayanta ina Mariya? Ita ba za ta yi jamb ɗin ba ne? Domin suna aji daya ne SS3 Kuma tare aka biya musu kuɗin jarabawar fita.
Sai take faɗa masa Mariya ta daɗe ba ta nan ta na gidan Yaya Zuwaira, Inna ya kalla kafin yavce"Inna me ta je yi can kuma?
Inna na tankaɗen garin tuwo ta juyar da kai kafin Ta ce"Ina zan sani, shiga ɗakin Magajiya sai ta faɗa maka"
Cikin Kallonta ya ce" Innarmu."
Ko kara kallonsa ba ta yi ba sai kawai ya kaɗa kai ya fice bai kara magana ba ta bishi da kallon tausayi a ranta ta na masa fatan Allah ya yaye masa wannan bakar zuciyar.
Da daddare Mu'azzam ya kira wayarta yana faɗa mata Babanta ya kawo masa ƙaranta.
Tana mirmishi ta ce"Me kuma na yi ɗan Inna? Ckin dariyan shima ya ce" Ya ce ya zo kin yi kamar baki gan shi ba ,yana mgana kika yi banza da shi sannan ko abinci bavki ba shi ba." Inna Meri ta ce"Ban ba shi ba sai ya zo ya ƙwata, ko auransa na ke yi da zai zo ya tsaya a saman kaina yana min wani cin magani? Ɗan Inna rabani da Baban Inna ba na iyawa da fitinarsa."
Cikin magiya ya ce"Haba Innarmu maganin kukan mu, a yi masa afuwa in kina fushi da shi ina zai saka kansa Inna?
Ya faɗa cikin wani yanayi sai ta ji tausayin duka ya'yan nata ya kamata amman ba ta huce ba cikin gatse ta ce"To shi ba shi da bakin da zai zo ya ce in yi hakurin ne?
Mu'azzam sai da ya yi dariya kafin ya ce"Allah ya huci zuciyarki Inna"
Ta amsa mai da Amin bayan sun yi sallama ba jimawa Baba Ɗanjuma ya shigo.
Shima sai da ya yi mata mganar cikin Lallashi ya ce"Meri fushi da Baban Inna ba naki ba ne a wannan lokacin, ki yi hakuri ki fahimce sa don Allah."
Inna ta gyara zama kafin ta ce"Au kai ma ƙaran nawa ya kawo maka?
Kai tsaye ya ce"Ko ɗaya ni na fahimci yau ya na cikin bacin rai ya shigo gida ya fito ban gansa cikin yanayi mai daɗi ba, ki yi hakuri tunda har mu fahimcesa sai mu yi ma rayuwarsa uzuri kin ji ko?
Ba za ta iya yi ma mallam gaddama ba sai ta amsa masa. Shi ya sa bayan kwana biyu da ya zo Innar ta sakar masa amman ba sosai ba da kanta ta kawo masa abinci ya zauna yaci sosai tausayinshi ya kama inna har sai da ta ji taruwan kwalla acikin kwarmin Idanuwanta. Bai yi wani doguwar mgana ba da zai ta fi ya ijiye mata kuɗi yana faɗin "ki yi hakuri Inna."
Daga haka bai kara cewa komai ba sai ta ɗauki kuɗin tana saka albarka kafin ta ce"Ka leka ka duba Magajiya ba ta ji daɗi ba kwana biyu."
Sai ya amsa mata da to, yana fita sai ya ganta nan kofar ɗakinta kamar ta fito daga makewayi ne. Mariya na cikin ɗaki ta dawo shekaranjiya ta na jin muryansa yana faɗin" Magajiya ya jiki?
Dakyar ta amsa shi kuma cikin yanayinsa ya ce"Allah ya kara lafiya"
Bai ji ta amsa ba Mariya ce ta leko tana gaishe shi ya amsa yana kallonta har ya wuce sai ya sake dawowa yan faɗin"Ke me ya sa kika tafi wani waje kika bar zuwa makaranta? Kafin ta yi mgana Magajiya ta yi zaraf ta ce"Ba wani waje ta je ba gidan ƴar'uwanta ne ko za ka hana ta ne? Ko bangaran magajiya bai kalla ba ya cigaba da faɗin "Walida ta biya Jamb ke me ya sa ba za ki yi ba?
Da sauri ta ce"Ina son na yi Yayanmu Baba ne ya ce ba
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 23 Chapter of 26