ba shi Umarnin Shigowa.
Kamar ma ba zai shigo ba ya na ta tukubiri ya cire takalmin kafarsa ya shigo daga barci ya tashi daga shi sai jallabiya mai ruwan kasa da dogon wando. A kofar ɗakin ya durkusa yana gaida su Inna da kwana bangaren su Hajiya kuma ko kallo kamar ya ga kashi. Su kuma suna ta kallonsa da mamakin sauyawarsa ya kara girma fiye da tunaninsu Hajiya ma ta fi mamakinsa duk ko a baya ta san shi da tsawo amman bai kai haka buɗewa da kiba ba, ita kuma Mommy daman ba wani ganinsa ta yi sama da sau uku ba, ta dai san ya samu bambamci mai yawa tsakanin baya da yanzu.
Inna Meri ce ta kalle shi kafin Ta ce"Ba ka ga baƙi bane? Ko ba ka gane su ba ne?
Kai tsaye ya ce"Na gansu Inna, kuma na gane su." Ya faɗa cikin saka mamaki a cikin ganin nasu a gidansu kafin ya cigaba da faɗin"Naga kakar Mimi naga mahaifiyarta abun mamaki me ya kawo su? ko sun manta cewa babu sauran wata alaqa a tsakaninmu ne?
Ya faɗaa ya na mai kallon fuskokinsu ɗaya bayan ɗaya sai kuma a cikin su aka rasa wanda zai fara magana daga Hajiyar har Mommy ya yi musu ƙwarjini.
Sai Baba Ɗanjuma aka bari da rattaba masa bayanin da Mommy ta yi musu bai ko gama saurara ba ya kausasa murya Ya ce.
"Baba."
"Baba."
Baba Ɗanjuma ya amsa da na'am domin shi kanshi yasan akwai rigima. Cikin shan alwashi ya cigaba da faɗin" Na rantse da wanda raina ke hannunsa ba zan iya yafe masa. Shari'a da ni da shi sai a gaban Ubangiji." Ya karishe faɗa ya na jin wani irin nauyi acikin ƙirjinsa an ma raina masa wayau bayan an gama tozarta shi an lalata masa rayuwa shi ne za'a zo ana gaya masa mganar banza.
Uban kuturu to ya yi kaɗan ma yana jin Hajiya ta fara masa nasiha tana faɗin "Shi kabirun ma ya rasu ba za ka yi hakuri ba?
Kai tsaye Ya ce"Kowani mai rai ai mamaci ne, nima wata rana zan mutu za muje gaban Ubangijin da ya yi talaka da mai kuɗi a gabansa sai ya fitar min da haƙƙina"
Daga nan sai jikinsu ya yi Sanyi Mommy na jin haka sai ta fashe da kuka tana faɗin"Wlh ya yi nadama don Allah ka bar komai ya wuce." Kamar a fusace Ya ce" Ba komai ba ne ballantana na bar shi ya wuce, rayuwata gabaɗaya ne aka lalatamin kinga kuwa ba kamar a bar shi ya wuce ba ne. Akwai hisabi tsakanina da wannan mutumin kuma yadda ya sha alwshin yarsa ta fi karfina nima yanzu na fi karfinta da duk abin da ya ke takaman tana da shi."
Hajiya ta ce"Ka yi hakuri ba laifin Binta ba ne, har gobe tana sonka ka amince ka aureta sai ku manta baya ku fuskanci gaba."
"Ni ba ni da kudin auranta. Har yanzu ni talaka ne, sannan mahaifina har ya mutu a kauye ne kuma har gobe ni agola ne a gidan nan kinga kuwa har gobe ban chanchanta ba."
Ya ba ma Hajiya amsarta sai su ka kasa mgana Baba Damjuma ne ya ce" Mansoor ka yi hakuri ka ji ko! Ko Allah muna yi masa laifi ya yafe mana."
Inna Meri ta amsa da cewa"Kuma ba'a son kafiya ba a son a yi ta ba ma musulmi hakuri ya nuna kafiyarsa."
Kansa na kasa ya na jin wani iri zuciyarsa na wani irin zafi sai yaji kamar a yanzu komai ke faruwa. Taruwa suka yi da na su iyayen da na shi suna ta ba shi mgana.
Mommy na kukan ta na fadin farincikin Mimi ya na tare da shi ne ya taimaka mata don Allah. Inna Meri na ta faman fadin ya Sausaauta ma kamsa in kuma ya ciza ya hura saboda kada ya zo ya yi nadama.
"Inna na yi rantsuwa, kina so na yi azumin kaffara ne?
Ya faɗa yana kokarin saka wani tunani acikin ranshi, shi ya kasa ma sarrafa yanayin da yake ciki a lokacin Mommy kuma ta tare shi da faɗin"Shima har azumin kaffaran ya so ya yi Allah bai amince ba."
Mirmishi ya yi mirmishin da ko inna da Baba sun jima ba su gan shi cikin wannan Mirmishin ba.
"Na amince zan yi azumin kaffara a kanta, zan aure ta."
Hajiya da Mommy su ka haɗa baki wajen fadin"Alhamdulillah."
Inna Meri kuma kallonsa take yi domin a jikinta taji ba ta yarda da maganarsa ba.
Baba Damjuma kuma na ta saka albarka ya na fadi "Ko kai fa? Ai gwara ka manta komai." Mommy ta rike Hannun Hajiya tana fadin"Habibi zai yi farinciki yau ya ga Mimi ta samu abin da take so."
Munafukin mirmishi ya yi kafin ya ce"Kafin nan ina da wasu sharuɗɗa guda huɗu, biyu zan faɗe su kafin aure. Biyu kuma zan kafa su bayan auran."
Ba tare da tunanin komai ba Mommy ta ce ba komai sun amince nan take Aji y ace zai tura ma Mimi sharudɗan ta wayarta da amincewarta zai yi amfani daga nan ya tashi ya fice kuma bai nuna alamun wasa yake yi ba kuma bai nuna alamun ya yafe ba.
Inna Meri sai ta rasa gane in da ya dosa a jikinta taji kamar ya na shirya wani abu.
Hajiya da Mommy suna ta godiya,Inna Meri ta rakasu har wajen mota jikinta duk ya yi sanyi Magajiya da su Gaje kamar za su rasu saboda son jin gulma ai tunda suka ga Mansoor suka san babban abu ne ke faruwa ita kuma magajiya ta so ta gane Hajiya Shiyasa Inna Meri na dawowa daga rakasu ta tare ta da Fadin"Ikon Allah wannan kamar Hajiyar da kika yi aiki a gidanta ko?
Inna Meri ba ta iya karya ba sai tace mata Eh ita ce. Daga haka ta wuce bangarenta Magajiya ta yi wani munafukin dariya kafin ta ce"A yi dai mu gani."
Gaje kuma fadi take yi"Kwanaki yar ta zo yau kuma kakar da kanta anya lafiya kuwa?
Harira ta ce"Da fa wata mgana, duk boyen su dai ai za ta bayyana har mu sani."
Duk Inna Meri na bangaranta ta na jinsu ta ma rasa abunda ke yi mata daɗi.
Baban Inna yafi ba ta mamaki wai ya amince cikin sauki haka?.
Ko da ta san shima ya na sonta ba ta ɗauka lamarin na shi zai zo da sauki haka ba.
Baba Danjuma daganan masallaci ya tafi saboda ana ta kiran sallah itama daga wajen ta ɗauro alwala ta shiga daki ta yi nata sallar.
*****
Mimi ta dawo wajen aiki ta ga Hajiya da Mommy ba sa gidan da ta yi ma baaba uwani mgana sai ta ce sun fita har ga Allah ta ɗauka suna gidan Daddy ne yasa ba ta Damu ba. Sai kawai ta kwabe kaya zafi ya isheta ta koma ta kwanta tana duba wayarta kuma Hoton Aji ta ke kallo har barci ya ɗauketa. Sai da taji muryan Mommy na kiran sunanta sannan ta farka.
Ta ga Mommy na ta fara'a amman ba ta ɗauka wani abu ne ya faru ba.
Ce mata ta yi ta tashi ta yi sallah tana tashi ta shiga tiolet wajen Mommy ta gyara mata wayarta sai ta ga Hoton da take kallo tunda wayar nata ba tsaro.
Mirmishi ta yi kafin ta ce afili"Kin kusa samun abin da kike so ƴata."
Daga haka ta ijiye mata wayarta ta fita zuwa ɗakin da ta sauka itama kwabe kaya tayi sai da ta yi wanka sannan ta yi sallah.
Dukkansu suka hadu afalo su ka ci abinci har da Mimi sai bayan sun gama ne Mimi ta kalle su kafin ta ce"Mommy ina kuka je ne?
Mommy ta yi mirmishi kafin ta ce"Gidan surukan ki mana"
Cikin mamaki Mimi tace"Gidan surukai na kuma? Ta faɗa da sigan tambaya.
Mommy ta kalli Hajiya suka yi dariya kafin Hajiya ta maida kallonta wajen Mimi dake musu kallon tuhuma da mamaki.
Cikin tausasa murya Hajiya ta ce" Eh mana mun je neman gafara abin da ya faru ne a baya." Mimi ta yi wani iri da fuska kafin tace"Ban gane ba"
Saboda ita dai ba ta san da mganar ba.
Nan Hajiya ta zayyana mata komai sai ta tuna lokacin rasuwar Abi Mommy ta yi ta jadadda cewa kafin rasuwar Abi ya so ya zo gombe ya nemi gafaran Hajiya ashe ciki har da Ajinta a ranta sai taji wani irin sanyi da Sauri tace"To shi ya ce yafe din Hajiya?
Hajiya tace"Bai yi mgana ba amman mun fahimci yafiyar sa tunda ya karɓi tayin mu ya amince zai AURE KI.!"
Mimi ta waro ido cikin mamaki kafin tace"Aure kuma?
Cikin matukar mamaki da kaɗuwa ta yi tambayan.
Wannan karon Mommy ce ta ja ƴarta Jikinta tana lallashinta lokaci ɗaya tana warware mata yadda komai ya fara ta karishe da Flfadin"Habibi kafin ya rasu ya yi ta nanata min mi yi miki abunda kike so, ni kuma nan duniya na tabbatar da yaron nan shine farincikin ki Hajiya ma ta tabbatar min da haka, kuma silan shi ne kika sa ba ma kowani namiji dama ciki har da ɗan uwanki Jaheed kina son shi kina kaunarshi tunda kuma har ya janye kalamansa kafin rasuwar shi kina da damar ki yi rayuwar farinciki" Kafin Mommy ta gama mgana ta fashe da kuka kamar wata karamar yarinya sai ta ji kamar a mafarki.
Cikin kuka take kallon Mommy Lokaci ɗaya tana faɗin"Aure fa Mommy? Kuma Aji ya ce ya amince da bakinsa?
Mommy ta gyaɗa mata kai kafin ta ce" Eh duk da yace ya na da Sharuddansa bai faɗa mana ba ya ce zai tura miki da kan shi in kin amince shike nan zai yi azumin kaffara."
Mimi ta ji kamar numfashinta zai ɗauke cikin wata irin murya ta ce" Mommy ni fa na hakura tun lokacin nan da kin faɗa min da ban barku kun je gidan ba." Hajiya na yar dariya ta ce"Ba ki son shi ne? In ba ki so ba shike nan ba ko ba haka ba Murja"
Mommy na taya ta dariya ta ce"To tunda ba ta so miye amfani Hajiya? daman daboda farincikinta ne" Mimi na jin haka ta yi saurin cewa"Mommy...!
Sai kuma ta kasa mgana sai kawai ta tashi da gudu ta shige koradin in da ɗakinta yake ta na Rufe fuska jinta ta ke yi kamar tana yawo a saman iska. Ta shiga ɗakinta tayi tsaye zuru ta na tunanin ko dai mafarki ne har marin kanta sai da ta yi. Ashe ashe burinta zai cika? Ashe ashe za su iya zama ma'aurata ita da Aji.
Tsalle ta buga lokaci ɗaya ta haye gadonta tana birgima nauyin da ke saman Kirjinta ya na sauka a hankali farincikin da take ji ya sa ta manta ma a inda take.
Mikewa ta yi ta fara uban tsalle asaman gado ta na cilli da fillows ɗin kan gado, ji take yi kamar ta kurma ihu duniya su san yau ta na cikin farinciki.
Ita kaɗai sai dariya ga hawaye sannan ta koma ta rufe fuskarta da bakinta tana yar dariya ta yarda farinciki na saka mutum ya yi hauka bai sani ba.
A falo kuma bayan fitan Mimi Mommy ta ce"Mimi na son yaro nan Hajiya, ni kuma sai naga kamar shi ya daina sonta ko abunda Habibi ya yi masa ya shafe kaunarta a cikin zuciyarsa ne? Hajiya ta ce"Ba na jin haka, ina da kyakyawan yakinin kamar yadda ba ta manta da shi, shima bai manta da ita i ba, in har ya daina sonta me yasa ya kasa aure? Sannan me yasa ya amince da bukatar mu a karon farko? Mommy ta yi shuru kafin ta ce"Haka ne to ya zamu bullo ma Alhaji Hamza da sauran ƴan'uwanta?
Hajiya ta ce"Ki bar ni da shi Hamza su kuma yan'uwanta in mgana ta tabbatar sai ki faɗa musu iyaka dai su kawo dogon turancin su na yaran zamani kada ki sauresu tunda dai Binta na son wannan yaron da ikon Allah sai ta samu abin da take so."
Da haka su ka cigaba da tattaunawa su tunaninsu bai kai ga in da tunanin Mansoor ya kai ba, a ran Mommy sai da ta jinjina zafin kan Mansoor ba ta ɗauka haka yake ba.
Mimi ranar kasa barci ta yi sai dai barawo kila ya sace ta, washegari haka ta tashi cikin annushuwan da ta jima ba ta aciki, Mommy da Hajiya su ka fara tsokanarta da Amarya tana jin kunya Baaba Uwani na wajen ta gyara zama ta na fadin"Wai ni Hajiya kun bar ni cikin duhu, Aure Hajiya binta za ta yi ne ban sani ba? Hajiya na yar dariya ta ce"Mu na saka ran haka"
Tuni Baba Uwani ta saki guɗa sai da ta rangaɗa guda uku Mimi na jin haka tayi waje tana dariya daman a shirye take wajen aiki za ta je. Baaba Uwani har haraba ta bi ta tana yi mata kirari da Amarya hak nnan ta zazzage mata sauran kuɗin jakarta Baaba Uwani faɗi take yi" Ko waye wannan ya yi farar sa'a, ya tsinci dami acikin akala kyakyawan mace a jari ce ballantana Binta Fatima take uwar ado da kwalliya"
Mimi farinciki ya sa ta kasa rufe baki haka taja motar ta zuwa wajen aiki ranar duk wanda ya ga Mimi sai yace me ya faru da ita bakinta yaƙi rufuwa ko a wajen karanta labarai haka ta ke ta washe baki kamar gonar auduga in kuma akace me ya faru sai ta kara sakin dariya ta kasa cewa komai.
Amman yini ta yi sadaka bakin Jakarta ta ɓude, daman can ba ta da rowa amman kyauta ranar na musamman ne gabaɗaya dalibai yan Inteen sai da ta saka musu Data ma'aikatan kuma ta bi su 2k kafin kuma ta kariso daman ta tsaya a banki ta cire kudi ta yi ta ba da sadaka a hanya kafin ta karisa wajen aiki. Rukky na bangaren su taji Labarin Hajiya Mimi na ta rabon kuɗi sai ga shi ta garzayo, ita kanta yanayin da ta Mimi sai da ta rike baki tana faɗin"Faɗa min me muka samu ne? Mimi ta saki kayattaciyar dariya kafin ta ce"Za ki ji in lokaci jin ya yi."
Yadda ta faɗi mganar muryanta cikin annushuwa ya sa Rukky ta zargi wani abu.
Cikin juya ido ta ce"Ko dai ko dai, kun daidaita da Jaheed an saka rana, aure kawai mu ke jira." Mimi na yar dariya ta ce"Kin faɗo kasa warwars kinsan ai ba zan iya auran Jaheed ba."
Rukky ta ce"Ke ce dai da Iyayin ki, ina laifinsa Allah na tuba."
Mimi na jinta sai ta yi mata shuru Saboda ba ta san mganar Jaheed wanda har yanzu bai daina damunta da magiyan ta amince masa su yi aure. Dannan duk da bakinta na rawan ta yi ma Rukky zencen sai ta kasa saboda ba ta san matsayinta ba an ce ya ce sai ya ba da sharuɗɗa kuma ya ce ita zai turo mawa, to a ina zai samu lambar wayarta? Shiyasa ta yini duba wayarta amman ba wani sakon da ya shigo, Haka ta koma gida ta na wannan annushuwan ta iske ma Yaddiko a gidan ta zo, Hajiya da Mommy sun fi kowa sanin sirrin annushuwanta da walwalanta sai da Yaddiko ta tafi Hajiya ta tasa ta da tsiya kala kala tana tsokanarta Mommy kuma na gefe Flfarinciki ya cikata har kwallah Sai da ta share tana faɗin"Allah ya jikan ka Habibi, ga Mimi yau tana cikin farinciki."
Har washegari ba ta ga kira ko saƙo ba sai ma Jaheed dake damunta da kira da turo saƙo, ko da wani lokaci taji karanta wayanta jikinta na rawa take dubawa sai ta ga ba wanda ta ke tunani ba ne, ganin an kwarari sati sai jikinta ya fara yin sanyi kada ya zo murnanta ya koma ciki.
A daran ta kusa kai ɗayan dare ba ta yi barci ba, da ta gaji ta ta shi ta yi salla raka'a huɗu sannan ta koma ta kwana da asuba da ta tashi ta yi sallah sai ta jawo wayarta za ta yi karatu nan ta ga an tura mata da saƙo
gabanta sai da ya faɗi ganin sunan shi domin ta yi saving din lambar shi.
"Aji Nah"
Hannunta na rawa zuciyanta na bugawa Fat! Fat! ta buɗe saƙon tana karantawa sama da kasa ta na ma kuskure wajen karatun, abunda ya rubuta ne bai wani ba ta mamaki ba sanin halinsa a wajenta Sharuɗɗan nasa ba su yi mata tsauri ba.
Da sauri ta mike ta fita daga ɗakin zuwa ɗakin da Mommy ta sauka ta isketa ta idar da sallah ta na Lazimi. Gabanta ta karisa ta zauna tana faɗin"Gud Morning Mommy."
Mommy ta amsa mata da gyaɗa kanta Mimi sai ta mika ma ta wayar tana faɗin "Aji ya turo min saƙo" Da Sauri Mommy ta karɓi wayar a hannun Mimi ta danna wayar haske ya kawo sai ta shiga ta karanta saƙon kamar haka.
"Sharaɗi na farko bayan sadaki da ɗaurin aure aba za'a yi wata bidi'a da auran mu ba, sannan sharaɗina na biyu shi ne a cikin gidanmu za ki zauna tare da mahaifiyata domin har gobe ba ni da kuɗin da zan iya siyan gidan da ƴar Major kamar ki za ta zauna ba"
Ina jiran Amsar ki, domin da amincewarki zan yi amfani.
"Mansoor Aji."
Mommy ta ɗago tana kallon Mimi kafin ta ce"Ban gane ba shi da gidan da za ki zauna ba? Ba ƙwallon kafa kika ce yana yi ba?
Mimi ta gyaɗa mata ai kafin ma ta dire mgana Mommy ta mika mata wayarta lokaci daya tana faɗin" Ban yarda ba, ko da Habibi ya amince da auran nan kafin ya rasu bai ce ki je in da zaki wulakanta ba farincikin ji yake so Mimi, ki amsa masa da cewa ba ki amince ba, kin dai amimce da sharaɗin farko amman na biyu ya sauya tunani" Mommy na ta faɗa Mimi ta dukar da kai ta na tubutu a wayarta sai da ta gama sannan ta ɗago tana faɗin "Mommy mi ye ciki? Ai ba daji zai kai ni ba, tare da mahaifiyarsa zan zauna ba matsala Mommy." Baki sake Mommy ke kallonta kafin ta ce" A ina za ki zauna a wannan gidan? To ni dai ban ga wajen zama ba."
Cikin yar shagwaɓa Mimi ta nuna ma Mommy fuskar wayarta kafin ta ce"Ni fa na tura masa na Amince."
Mommy ta warce wayar tana gani kafin ta waro mata ido tana faɗin" Ba ki da hankali ne? Ta fada cikin Faɗa sai kawai Mimi ta kwantar da kanta a saman cinyarta tana faɗin" Mommy ba farincikina kike so ba? Mommy ta gyaɗa kanta kafin ta samu zarafin mgana Mimi ta yi saurin cewa"To ki amince, zan iya za ma a ko'ina in dai zan samu abin da nake so abin da na ke so Aji ne, ba wani abu na shi nake bukata ba shi ɗin nake so." Sai Mommy ta kasa mgana amman ta na hasko in da Mimi za ta zauna a wannan gidan ne, amman kalamanta ya sa bakinta ya mutu.
Hajiya ma da ta ji abin da Mansoor ya ce sai ta nuna ba komai duk in da yake son ya ijiyeta hakkinsa ne kuma ta da tabbacin Meri za ta yi ma Binta rikon ƴa ce ba suruka ba.
*ƙarshen littafi na ɗaya.*
*Janafty*
*Wed Aug 14 2024*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 26 Chapter of 26