Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yazo gidan sai ya zane su. Da suka gane shi suna ganinshi suke shiga taitayinsu yara ne yan shekaru biyar zuwa shidda. Sai da suka Shige Inna Meri ta fara faɗa masa cewa Bintu ce ta kira waya ta ce Walida tazo ta na son ganinta ashe wai faɗa tayi da miji da kishiya shi ne ya sa ta ce Walida ta tattaro yaran ta kawo mata su yi kwana biyu a hannunta Cikin takaici ya xe"To Inna makarantar su fa? Inna ta ce"Walida ta ce ko an basu hutu, sai ranar litini za su koma, Bintu finitinanniyar yarinya ce Baban Inna ba ta jin mgana tunda Basiru ya aureta wlh bai huta ba, ta addabeshi ta addabi matarsa, kuma shi yana jin kunyar Babanku ne shi ya sa yake raga mata  amma al'amarinta sai kara gaba gaba kawai yake yi, Walida ta gaya min ta ce sanda ta shiga gidan Bintu na tsakar gida tana na bala'i uwargidanta na cikin ɗaki ba ta fito ba amma haka Bintu ke zage zage kamar ɗiyar maguzawa." Mansoor ya yi shuru na wani lokacin yana jin Inna na faɗin "Ku shiga mganar kai da Mu'azzam Babanku bazai iya da fitinarta ba." Sai kawai ya jinjina kai kafin ya ce"Ko Bintu ta fara hauka ne ba mu sani ba Inna? Inna meri kamar tayi kuka ta ce"To ga dai shi, abubuwan da take aikatawa ba na masu hankali ba ne." Kai tsaye ya ce"Inna laifin ku ne, kunsan cewa Bintu bata san ilimin zaman aure ba me ya sa kuka aurar da ita? kuma shima Bashir ɗin wawa ne kamar shi yana namiji ashe ban sani ba sakarai ne? ta ya ya yana namiji zai zauna mace ƙarama kamar Bintu na juyasa? Ita ke auransa ko shi ke auranta? Ya karishe faɗa cikin ɓacin rai, yana jin takaicin yanzu nan in ransa ya ɓaci sai ya ta ka ya je har gidan ya ci mata mutumci tunda ya fahimci ta fara zama mahaukaciya. Ganin ya fara harzuka ya sa Inna Meri ta sausauta tana faɗin"Ka bari zuwa gobe ka kira shi Bashir ɗin da ita kanta Bintu ka ji abunda ya faru, nima ban ce ka raga mata ba, ka ci min mutumcinta tunda sakara take mara wayau." Karamin tsaki ya ja kafin ya ƙwalama Walida kira ta fito da sauri tana faɗin gani yayammu. Idanuwansa har sun fara sauya launi ya kalleta yana faɗin"Me kika je kika iske Bintu nayi a gidanta? Walida ta ce"Sai faɗaa ta ke yi tana zage zage wai duk wanda yaci amanarta ba ta yafe ba tac e na tafi da su Hassan sai Yaya bashir ya gane bashi da wayau." Inna Meri tace"Kai Jama'a me Bintu take son zama ne ni Meri? Shuru ya yi yana wani tunani, bai ɗauka haukan Bintu ya kai haka ba. Yana ji Inna na faɗin "Fitinar Bintu ya yi yawa, fitannannu biyu Allah ya bani cikin ya'yana da kai da Bintu kai na samu saukin naka Fitinar itace yanzu take son kasheni da bakincikinta." Da sauri ya ce"Ki daina haɗaani da ita Inna ni halina ba irin na Bintu ba ne, wannan fa mahaukaciya ce." Inna Meri tace"Hmm ka ma fita, yanzu ne ka daina jawo fitinar da ta fi karfinka Baban Inna." Ya na jin ta ɗauko wannan mganar ya yi saurin mikewa ya fice yana ce mata an kira sallar Isha'i zai je ya yi sallah ya dawo. Daman tasan bazai zauna ba, shi da bayason mganar kwata kwata. To kuma gaskiya ne shi ai fitinarsa ba mai iya kwantar da ita sai Allah. Ga bakar Zuciya kamar Kuturi ga kafiyan tsiya ita fa tana ganin Bintu ko kama kafar Baban Inna ba ta yi ba wajen fitina da taurin kai. Shi zata iya cewa ta wajen dangin Ubansa ya ɗauko wannan hallayar, ita Bintu fa? Ta rasa gidan uban da ta ɗauko hallayan fitina da rashin son zaman lafiya. Tana jin Walida na faɗa mata ɗakin Bintu duk an fasa kwalaben turaren wuta tana tunanin kila ma dambe tayi da yaya bashir ɗin kafin ya fita. Inna Meri ta mike tana faɗin"To Allah shi ya ye ma Bintu wannan bala'in bani iyawa da halinta ni kam in ya gaji shi basirun ya sakota ta dawo gida ta zauna." Daga haka ta mike ta shige ciki domin ta da sallah. Su Hassan sun yi barci ba mugun wasa. A can masallaci Mansoor ya haɗu da Baba da abokinsa makocinsu Mallam Hashimu, albarkacin Baba yasa suka dawo masallaci tare da su Baba Sani, a kofar gida suka tsaya wannan yace bashi da abinci Baba sani ke faɗin ko ƙwayan hatsi babu a bangaransa Mansoor ya taimaka masa. Baba Danjuma na gefe kamar ya saka kuka gabaɗaya ƴan uwansa sun zubar da kimarsu da Allah ya basu, sun koma maula wajen wanda ya ke matsayin ɗa a wajensu. Bai ce bazai ba su ba, kudin da ke Jikinsa duka ya kwashe ya ba su 20k ammh ya ce musu in ya dawo zai ƙara musu, suka karɓa ko Godiya domin sun raina abunda ya ba su. Ko kunya suka wuce bangarensu Baba Ɗanjuma ya sauke Numfashi kafin ya ce"Ka yi hakuri Mansoor kaji ko? Kansa na kasa ya ce"Haba ba komai Baba suma iyayena ne yadda zan yi maka abu suma suna da haƙƙin na yi musu." Jinjina kai kawai Baba Ɗanjuma ya yi yana ta saka albarka. A kofar gidan suka tsaya Mansoor ɗin ya kawo masa mganar Bintu. Baba Danjuma ya ce"To ni sha'anin Bintu ya fara isata yarinyar nan ba ta jin mgana." Mansoor yace"Baba ba ita ta haifi kanta ba. Ubanta zata ci wlh tunda na lura ba ta da hankali." Baba Ɗanjuma ya ce"To kila kai in ka yi mata magana ta gyara, ammh ni da Meri har mun gaji da yi mata nasiha mun ƙyaleta, yaro nan kunyata yake ji shi ya sa bai ɗauki wani mataki akanta ba, ammh sha'anin Bintu ya wuce hankali, kwata kwata ba ta daraja mijinta ta zame ma sa fitina a gidansa." Mansoor jinjina kai kawai yake yi yana tunanin gobe daga studion gidan Bintu zai wuce yana so ya ga Iskancin da aka ce tana aikatawa ne. Ga shi shegiya bata san komai ba sai hauka, ya'yanta ma ba ta iya kula da su sai dai ta kawo ma Inna ta dinga wahala da su, to a gobe zai saka Walida ta maida mata ya'yanta in bazata zauna da ya'yanta ba to ta aika su wajen kakarsu ta bangaren uba, Amma ba gidan su ba. Tare suka shiga gida da Baba Ɗanjuma, ranar Magajiya ke da Miji tana ganinsu tare ta fara masifa tana manganganu ganin haka yasa Mansoor bai tsaya ɗakin Baba Danjuma dake tsakanin Korodon Inna Meri ba, sai ya shiga falon Inna Meri ya zauna Walida ta zuba masa tuwon masara da miyar kuka yana ci suna hira da Inna har ya kamallah yace kuma a ijiye masa ɗumame da safe in ya dawo training zai shigo ya ci. Karfe goma ya bar gidan ko ɗakin Baba Danjuma bai leka ba tunda Magajiya na ciki yana shiga sai kuma ya jawo tijara, tunda ita kam tun yana ƙarami yasan ta tijararriya ce ba ta raina abun mgana musamman ma shi da ta ke ganin ba ɗan gida ba. Ya isa gida goma da rabi, da ne ya kan zauna majalisar su matasa a anguwansu amma yanzu majalisar ba kowa, dukkansu sun kama kansu wasu sun yi aure wasu kuma ba ma a garin suke sana'ar su ba ya na jin daga shi sai Nasir sai makama suke garin Gombe. Nasir kuma ya yi aure sannan anguwar da ya ke zaune da matarsa akwai nisa a tsakaninsu sai su jima basu haɗu ba. Makama ne kaɗai da shi suka rage ba su yi aure ba, ko kuma ya ce shi kaɗai ya rage tun da Makama an kusa bikinsa  ma'aikacin bankin First bank ne, shi ya sa in ya shiga anguwan sai dai ya zauna a gida ya yi hira da Inna ko Baba ya ci tuwo ya fito ya koma gida ya kwanta. Shi kanshi yasan rayuwarsa ta sauya, abubuwa masu dama sun sauya daga rayuwarsa. Mafarkinsa, burinsa da komai nashi ya sauya, shi ya sa yake jin kansa kamar bashi ba. Tabbas  Mansoor Ajin yanzu ba shine Mansoor Aji a shekaru goma da suka ga ba ta ba. Wannan wani sabon Mansoor ne, wanda ya rasa mafarkinsa da burinsa wanda rayuwarsa ta juya daga farinciki zuwa baƙinciki. ****** Washegari. *Karamchi Tv* 11:30am. Yau ba ita zata karanta labaran dare fa Salim Bunza ne, shi ya sa bayan ta gama karanta labaran safe ta tattara sauran takardun hannunta zuwa Office ɗin manajansu bangaren labarai da al'amuran yau da kullum na gidan talabijin na karamci. Mai alhakin editer ɗin su ba musulmi ba ne Peter tare da shi suka je wajen manaja tunda ranar lahadi da safe za su gabatar da shirin sharhin labaran karshen mako ita da Salim. Ta ji ma a wajen Manaja suna magana har peter ya fito ya barta sai daga baya itama ta baro bangaren zuwa rest room ma'ana ɗakin hutawarsu. Babban ɗaki ne mai cike da kayan alatu kamar falon wata mace, ga A.c ta ko'ina ga tuma tuman kujeru da suka zagaye wajen ga firiza domin sanyaya makoshin ma'aikata. Sanye ta ke da Abaya mai ruwan ash colur sai ta saka mayafin Abayan ta yi roling ɗin shi a saman kanta. Kafarta sanye cikin takalmi sahu ciki kafin kaga Mimi da takalmi na sahu waje sai ka ganta da sau ciki sau goma. Tana son takalma masu rufi sosai, jakarta karama kalan takalminta ash mai duhuwa, a can ta samu debora mai kula da shashen bangaren kula da masu shirye shirye ita da Na Misau suna hira. Zuwan ta ya sa aka cigaba da hiran da ita, duk da jefi jefi hankalinta na kan wayanta Mimi bayan aikinta sai wayarta ta fi ba ma muhimmanci. Chart suke yi da Dr. Sulaiman ya na shaida mata a satin mai shiga shi da iyalansa za su je Abuja saboda duba jikin Abi. Itama sai take faɗa amasa da safen nan sun yi mgana da Mommy tana faɗa mata Abi na a kiran sunanta ya kamata tazo ta ganshi. Sai ya ce mata to ta bari a satin da zai shiga sai ta shigo su haɗu a gida. Tana can ta na chart ɗinta Debora ta musu sallama ta fita Na Misau ma daya ga yana mgana hankalinta baya kansa sai ya kwashi takardunsa ya fice, suna da shiri shi da abokiyar shirinsan nan da Karfe ɗaya na rana. Sai da ta ji ɗakin ya dauki shuru sannan ta juya ta ga ba kowa sai ita kaɗai sai kawai ta jawo jakarta ta ɗauko Blutooth  ɗinta ta maƙala a kunnenta ta kuma yi connacting da wayarta ta sanya wakar da kamar ita kaɗai gareta acikin wayarta. Tana fara sauraran wakar sai ta koma ta jinginar da kanta jikin Kushin ɗin kujeran da take zaune, Kafarta kuma sai ta ɗora ta saman ɗaya wayarta na saman cikinta ta saka ɗayan hannunta ta dafe jakarta dake gefenta. Cikin zaƙin muryanta kamar ita ta raira wakar ta fara bin karin wakar mai taken lafazina na khairat Abdullahi. _Jarabta da soyayya zafinta na ɗanɗana matuka_ _Hakika da ƙuna gun kaifi fa ta sha gaban suka_ _Nayi wutar ciki nayi bakinciki na share kuka na. Ta shiga can ciki takai  farmaki ta kama hanjina._ _Dakyar na ke fidda numfashi SO ya tushe Kirjina_ _Wata rana kamar in yi ihu ko wani  za ya gano takaicina_ _Mashi ya soke ni wa za ya dubeni. Raɗadin zafin azaban ya zarce tunanina._ Ta daɗe tsaye tun shigowarta tana kallonta bata ma sani ba, ta yi nisa cikin sauraran waƙan nata da kuma salon yadda ta saba bin karin wakar a koda yaushe, mirmishin gefe baki ta sa ki kafin ta fara takawa zuwa gaban Mimi duk ko da yadda Takalminta mai tsini ke fitar da karamin sauti acikin tayless din dake falon. Sanda ta kariso gabanta dai dai Lokacin da ta ji ta na faɗin _In SO ya doke ka! ƴa'yanka har Jika, ba za ka manta ba ya shiga tarihinka kenan..!_ Ba ta bari ta ƙara ɗaukan wani karin ba ta saka hannu ta dauke wayar dake cikinta lokaci ɗaya kuma ta tsaida wakar, cikin kasala Mimi ta buɗe idanuwanta da har sun fara sauya launi ta sauke su fes kan Rukayya Bala(Baby) Ma'aikaciya ce itama a shashin tallace tallace na gidan Talabijin na karamchi. Kuma kawar Mimi ce tare suka yi master ɗin su a Bayero kano sun zama kawaye tun a lokacin da jin sun fito daga jiha ɗaya. Mimi ta fara aiki da gidan Talabijin na Karamchi ita kuma ta kawo Rukayya da suke kira Baby aka ɗauketa wattani kaɗan da suka gabata. Tana ganin ita ce sai ta yamutsa fuska kafin ta ce"Baby ya za ki kashe min wakata? Wacce aka kira da Bby gajera mace fara mai dan kaurin jiki, itama wani material ne ajikinta na yadi baki ta yi dinkin Bubu, amma sai ta saka wani karamin hijabi fari daga saman kanta zuwa wuyanta, ta kuma sakalo I.D card ɗinta na wajen aiki ɗauke da sunanta na Rukayya Bala da shashin da ta ke aiki. Kusa da Mimi ta zauna lokaci ɗaya tana Faɗin "Mimi kamar wannan wakar kaɗai gareki acikin wayarki? Ko da yaushe ita kike saurara kuma ni nasan ba soyayya kike yi ba, ballantana nace wani mara rabon ne ya yi breaking heart dinki, wayarki  cike suke da irin waɗaanan wakokin Mimi." Ta faɗa ta na mai kureta da ido da kokarinta ta fahimci wani abu, kamar Mimi ta sani sai tayi sauri tashi ta gyara zamanta dakyau lokaci ɗaya tana warce wayarta hannun Rukky ta haɗa Blutooth ɗin da ke kunnenta ta tusa cikin jaka sannan ta kara Juyowa ta na faɗn"Ina jin ki me ma kika ce? Hararanta Rukky ta yi kafin ta ce"Ke dai kika sani." Mirmishinta mai kara mata kyau ta yi kafin ta ce"Hajiya Baby mai sunan yan gayu in ji Hajiyar shagamu" Rukayya ta saka dariya ta na faɗin"Allah Sarki Hajiyarmu na jima ban je ko na dubata ba ko na biki na je yau ne.? Mimi tace"Oho miki, ko ɗazu sai da ta ce wai ni Binta ina ƙawar nan taki mai sunan yan gayu nace ki nan nan abun ki." Rukky tace"Tab yan adawa sun shiga ciki dole yau naje na duba Hajiya, ya ya kin tashi aiki yau ne? Nima na tashi sai na mu tafi tare" Mimi tace"Na tashi tun dazu Manaja ne ma ya tsaida ni, amma ba gida zan sauka ba daga nan sai na biya gidan Yaddiko na gaisheta ko da zan fito da safe sai da Hajiya ta rokeni da Allah da Annabi na biya na gaisheta." Rukky tace"Ba matsala sai mu fara biyawa ta can, ammh fa da yammah zaki kai ni gida in na gama miki yini." Mimi ta mike ta na faɗin"A'a ba wajena kika zo ba, sai dai ki samu adaidaita ba na tuki in yamma ta yi" Rukky ta mike ta rumgumota ta na mata magiya da fadanci tana faɗin"Haba Hajiyata Mimi, mimi mai kyau da ado." Take faɗa da sigar waka, Mimi sai mirmishi ta ke yi, a haka suka fita har main falon na ma'aikatan nasu ga sauran ma'aikata nan a zazzaune suna ganinsu ahaka aka sakar musu dariya. Na misau da zuwan shi kenan ya kallesu kafin ya ce"Yanzu haka Rukkaya maula ta ke yi tunda naga ta na rage murya" Hararansa ta yi kafin ta ce"Shisshigi ba kwarjini ina ruwanka da shiga tsakanin ƙawa da ƙawa." Sai ya ɗaga hannu yana faɗin"Ba ko ruwana kun fi kusa." Mimi na dariya ta ce"Fadanci ta ke yi min Na misau wai dole sai na yi mata lift a motata." Dariya ya kwashe dashi lokaci ɗaya yana faɗin"Rukky gaskiya ki rage son kudi ki siya mota ga kudin albashin ki, sannan ga ki lashe money ni kaina kin cuceni kudaɗe sun fi dubu ɗari biyar." Jin abin da ya ce ne ya sa Rukkaya ta saki Mimi ta waigo tana kallon Na Misau da ya ɗaga kafaɗa yana fadin"Karya nayi? Ke kika ja har a na fallasa maganar nan, tunda kika ce ba za ki aureni ba." Ido ta ke wurga ta na neman abun duka shi kuma Na Misau ya ɓata fuska ya juya yana faɗin "Justice for Na Misau." Rukky ta kasa mgana sai kawai ta rarumo laptop din da ke gaban Nura ta bi Na Misau da shi shi kuma ya saka gudu yana fadin to ba gaskiya na faɗa ba. Suka bar su Mimi da dariya Rukky da Na Misau sun saba rigimansu na fama sai sun saka cikin ka ya kulle. Manaja ne kaɗai ke iya raba wannan faɗan shima irin su ne shi ya sa yake biye musu. Sai ɗaya saura na rana suka bar Ma'aikansu Mimi ta ɗauki Rukky a motar ta wata fara ta kamfanin Toyata mai kyau da yarari motar har ɗaukan ido take yi, suna tafe suna hiran bikin kanwar Rukky da za'ayi nan da wattani huɗu. Mimi ta kalli Rukky, hankalinta na wajen tuki ta ce"Baby wai waye Bibi zata aura ne? Rukky ta ce"Wani Usman ne ɗan gidan makama yana aiki a bankin First Bank." Mimi ta maimaita sunan Usman da Makama acikin ranta sai dai ya bayyana a saman bakinta. Cikin mamaki Baby ta ce"Ko kin san shi ne? Da sauri Mimi ta girgiza mata kai alamun a'a acikin ranta tana tunanin ko dai Usman ɗin da ta sani ne shekaru masu yawa a baya. Kai ba shi ba ne, shi wannan da makama ta san shi ba Usman ba. Saurin kauda wannan tunanin tayi ganin sun shigo yankin fantami in da gidan Yaddiko yake, a kofar gidan Mimi ta faka motar ta saboda gidan na masu karamin karfi ne, tunda Mijin Yaddikk ɗan kasuwa ne mai karamin jari ya'ya ne ma suka taso suka kara gyara gidan ya yi kyau ya koma na zamani. A kofar gidan sun ga dandalin matasa tunda gidan yana da dakali kuma tun a zamanin baya Mimi tasan kofar gidan Yaddiko baya rabo da matasa. Suna ganinta sanda suka fito daga motar zuwa kofar da zata sada su da cikin gida. Suka fara kiran sunanta tunda duk wanda ke garin Gombe ya san fuskar Mimi , tunda gidan Talabijin na Karamci na gaba gaba cikin sahun manyan gidajen talabijin a garin. Fuskarta ba ɓoyayyiya bace a garin. Hannu ta rika ɗaga musu tana mirmishi Rukky na gefe tana faɗin"Hajiya Mimi kin fa samu ɗaukaka ina ga ko Manaja baya fita ayi masa wannan kiran." Ture ta Kaɗan Mimi ta yi ta na hararanta har suka shiga gidan nan wasu ba su daina kiran sunanta ba. Gidan Yadikko cike yake da jikokinta duka ya'yanta ta aurar da su amma tarin Jikokin da suke gidan sun isa gayya duk da Yaddiko na da faɗa jikoki na son zama a gidanta saboda Allah ya dora mata son yara. Suna shiga aka fara musu oyoyo Anty Mimi, itama ta na son zuwa gidan saboda yaran ammh saboda Yaddiko ya sa ba ta son zuwa duk lokacin da ta zo sai ta yi mata maganar da zai ɓata mata rai. Rai rai tare da yaran har falon Yaddiko wacce ke zaune a saman cafet tana sakan huluna daman sana'arta kenan tun tana matashiyarta har kuma ta manyanta bata daina ba. An yi an yi ta bari ta ce ba za ta bari ba yana deɓe mata kewan zama ita kaɗai. Har kasa suka zube ita da Baby suna gaishe da yaddiko. Aneesa daya daga cikin jikokin Yaddiko ta lafe a jikin Mimi saboda yadda take kaunarta sai faman yi mata cancare take yi da Anty mimi na ganki a Tv jiya. Yadikko ta ijiye julan hannunta tana amsa gaisuwarsu kallon Rukayya ta yi alamun rashin sani da sauri Mimi ta ce"ƙawata ce Rukkaya tare muke aiki da ita." Sai ta gyaɗa kai kafin ta ce"Fatima kenan sai yau na ke ganin kafarki , kina garin nan ammh bakya zuwa gaisheni sanda zan je duba Hajiya kuma kina wajen aiki." Kan Mimi na kasa ta ce"Ki yi hakuri yaddiko zan gyara in sha Allahu." Sai ta taɓe baki, da ka ganta kasan ta haɗaa jini mai karfi tsakaninta da Mimi Saboda suna ɗibar kama. Mimi Allah Allah ta ke yi su tafi sai ta ji Yaddiko ta ƙwalama ɗaya daga cikin Jikokinta kira tace su kawo ma su Mimi abinci da ruwa. Mimi bakinta na rawa ta ce"Yaddiko gida za mu wuce, Rukky za ta je ta gaida Hajiya." Kai tsaye yaddiko ta ce"Eh na sani ku ci abinci ku yi sallah sai ku tafi, ba daga wajen aiki kuke ba? Rukkaya ce ta amsa mata, ba su da mafita dole Yaddiko ta saka aka shigar musu da abinci wani daki da ke cikin falon nan suka shiga suka cakuli abincin kaɗan Jalop din shinkafa mai Kifi sai zobo mai sanyi. Bayan sun gama suka shiga tiolet suka yi alwala. A ɗakin akwai dogon hijabi suka yi salla sannan suka gyara fuskarsu suka fito. Har kasa suka duka suna yi ma Yaddiko sallama Ta ce. "Har zaku tafi? Mimi ta gyaɗa kanta sai kawai Yaddiko ta gyara zama tana faɗin"Fatima mganar nan ce da ba ki so wato maganar aure!" Gaban Mimi ya amsa sai ta sadda kanta kasa bata yi mgana ba. Yaddiko ta cigaba da faɗin"Ya kamata ki manta abin da ya faru a baya ki ba ma manemanki dama ki fito da wani ki yi auranki Fatima shekaru suna ta gudu kuma kinsan dai ba niran ki lokaci zai yi ba." Idanuwan Mimi suka tara kwallah ammh ba ta yi mgana ba. Yaddiko ta cigaba da faɗin" Wannan yaron da kike yi ma wannan kulafacin ba ki da tabbacin yana nan bai yi aure ba, tunda mahaifinki ya yi muku tsakani kika yi alkwarin kin rabu dashi to kuma zaman jiran duk na menene? "Yaddiko shima bai yi aure ba fa " Ba ta san lokacin da bakinta ya kuɓce ba sai ji kawai ta yi ta faɗa. Daga Yaddiko har Rukky suka bi ta da kallon mamaki, ita yaddiko ba ta yi mamaki ba daman ta faɗa maHajiyar shagamu yarinyar nan yaron nan data kwallafarai a kansa ta ke zaman jira shi ya sa ta zaɓi ta zauna ba aure ita kuma Rukky ta na mamakin waye wannan a cikin rayuwar Mimi da ba ta taɓa sani ba? Sai dai Yaddiko ta katse mata tunani da cewa"Au ko shi kike jira ya zo ya aure ki? Da sauri Mimi bakinta na rawa ta ce"A'a wlh yaddiko ba shi na ke jira ba, tunda nayi ma Abi alkwari na rabu da shi to da gaske nake yi wlh." Yaddiko ta kura mata ido cikin nazarinta kafin ta sauke numfashi tana faɗin"Tashi ku je jibi ina nan shigowa na duba Hajiyar ki gaishe ta." Daman kamar akan ƙaya Mimi take ,ta mike da sauri Baby ta mara mata baya  duk da haka sai da ta tsaida suka karɓi sakon  Hajiya dafaffiyar zogale a leda  da kuli ta ce a kai mata, Mimi ta karɓa suka yi ma Yaddiko sallama suka fita bayan ta ba ma yaran 2k ta ce su raba. Mimi bata sauke numfashi ba sai da suka bar layin, sai dai yadda ta ke tukin za ka fahimci Mimi ta rasa natsuwarta sai gudu ta ke yi abin da ba halinta ba ne. Rukky ta kalleta kafin ta ce"Mimi wannan halin da kika shiga yana da alaqa da mganar Yaddiko ne? Wane ne na ji tana mgana akan shi? Da sauri Mimi ta ce"Plz Rukayya ki yi min alfarman toshe kunnuwanki kamar ba ki ji mganar yaddiko ba, wannan mganar ta shuɗe daga tunanina da duniyata ba na son tunawa kwata kwata a rayuwata." Tana maganar idanuwanta sun tara kwallah lokacin da ta dire mganarta sai hawaye sharr suka zubo mata kuma ta kasa share su. Yaushe ne zata daina tunanin shi? Sai yaushe ne za ta manta da shi? *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU INA MASU

Chapter 3 of 26