Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tsohuwar budurwansa ne bayan wasu shekaru yau suka haɗu shike nan  kike son ji?   Ya faɗa ya na mai kureta da ido, ta kasa mgana saboda mamaki dai dai lokacin da Mimi ta kariso wajen jikinta kamkame da rigar da Aji ya ba ta kamar wani zai ƙwace mata. Tana zuwa wajen ta saki baki tana kallonsu cikin mamaki ta ce"Su waye na ke gani haka? Ai baza taɓa mantawa da su ba  sai ta tuna islamiyan Mallam Dahiru cikin buɗe baki tare da murnan ganinsu ta fara nuna su ɗaya bayan ɗaya. "Makama.." Ya amsa mata da" Na'am Mimi" Sai ta nuna Ahmad tana fadin"Ahmad.." Shima ya amsa mata da cewa"Na'am Mimi shekarun da yawa" Sai ta koma ta nuna na kusa da shi "Nasir" Nasir na dariya ya ce"Na san ai ko ba ki gane Nasir don komai ba kya iya gane ni da kullum sai Aji ya yi faɗa da ni akan ki. Hajiya Mimi ai ni mun taɓa haduwa shekarun baya." "Kin gane wannan?.   Ya faɗa ya na dafa kafaɗan Mu'azzam sai ta kura masa ido kafin ta ce"Laa wai Mu'azzam ne? Ɗan Inna ne ya koma haka? Ɗan Innan da ta faɗa ya sa suka fashe da dariya shima Mirmishi ya yi kafin ya ce"Anty Mami ashe baki manta da ni ba." Saboda tun a baya baya kiranta da Mimi Sai dai ya ce mata Anty Mami. Farinciiki ya kara cika kirjin Mimi cikin fara'a da tuni ta manta da kukan da take yi ta ce" Mu'azzam ina Inna? fatan tana nan cikin koshin lafiya" Kai tsaye ya ce"Inna na nan lafiya kalau, ina su Hajiya?sai ga shi mun sake haɗuwa bayan wasu shekaru a bikin Makama" Sai ta nuna Makama kafin ta yi mgana ya yi saurin cewa"Usman ba wanda ya auri ƙanwar Anty Baby."   Mamaki ya hana Mimi mgana sai faman mirmushi take yi, Rukky ta gaji da ganin abun mamaki ta kalli Mimi tana faɗin "  Duk a ina kikka san su ne wai? Mimi ta ce"Na san su shekaru da daɗewa Rukky."Sai ta saki baki tana kallonta ba ta kara mgana ba Dinner ai ta gama rushewa wasu har sun fara tafiya gida tun dare ya yi sha biyu ta wuce. Ita kuma Mimi su Nasir kawai take kallo ta na mamakin yadda duk su ka zama magidanta, tambayansu bayan rabuwa ta fara yi Nasir ke gaya mata dukkansu sun yi aure har Mu'azzam. ta rike baki tana faɗin"Muzamman ikon Allah" Sai ta bashi kunya Nasir na dariya yace"Ajin ki ne kawai ya rage gauro har mun gaji da biyan yara suna masa kiɗan gauran ci." Mirmishi kawai ta yi, amman ta kasa mgana sai ta saki mganar ta kama wata in da take gaya ma Nasir a baya da suka haɗu ta karɓi lambarsa ta yar da wayarta ne shi ya sa ta rasa lambarsa.   Shi kuma Usman na wajen Amaryasa tana kunkuni a zo a kai su gida ita kuma Rukky ta koma gefe tana mgana a waya, Dole dai su Nasir ɗin ne za su maida mutane gida ga shi motoci uku ne a hannunsu tunda Aji ya tafi da ta wajen nashi Mimi ta samu keɓewa da Mu'azzam da Sauri ta ce"Mu'azzam ka bani lambar wayar yayanka mana.". Mu'azzam ya yi shuru ya na kallonta ya kasa mgana ita kuma sai ta yi mirmishin karfin hali kafin ta ce"Ba ka son ba ni ne? Kar ka damu ba zan ce a wajen ka na samu ba." Ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce"Ina tsoro ne kinsan halinsa fa, ba ya sauya ba ne in ya ji ni na baki lambarsa tamu da shi za ta yi muni." Da sauri ta ce masa in sha Allahu bazai sani ba.   Jakarta ta karɓo wajen Rukky ta ɗauki wayarta ta kwafe lambar suma dukkansu ta karɓi lambobinsu wannan karon ba za ta kara bari Aji ya suɓuce mata ba. Ganin dare ya yi ga sauran mutane ya sa Mimi ta ce Rukky ta tuka su da sauran ƙawayen Bibi sai su je ta sauke  su, ita sai ta wuce gida domin ba ta gayama Hajiya zata kwana ba.   Tare suka bar wajen ɗaya saura na dare suka maida Amarya da tawaganta zuwa gidanta dag nnan Mimi ta ce za ta tafi gida Rukky ta ce ba za ta bar ta ta tafi ita kaɗai ba. Za ta rakata sai ita ta kwana a wajen Mimi ɗin. Ƙawayen Bibi ma duk nan za su kwana Ango ya yi musu lamuni tunda dare ya yi ga kuma yadda abubuwa suka kasance. Anan suka yi sallama su Mu'azzam ya ɗauke su sauran abokan masu mota kowa ya kama gabanshi, suna tafe a tare motar Mimi na gaba ta su na baya sai da suka zo shatalelen da kowa zai ɗauki anguwar da zai je sannan suka yi ma juna hon su suka ɗauki hanyar anguwan Tunfere su Mimi kuma su dauki hanyar da za ta sada su da GRA.   Lokacin suka isa har Hajiya ta jima da yin barci Baaba Uwani ta ji bugun kofar falo ta zo ta buɗe musu daman Hajiyan ta ce kada ta yi saurin barci Binta ba ta ce za ta kwana acan ba. Sai ko ga su sun dawo, Rukky ta ga abun mamaki Mimi da wannan rigar kamkame ajikinta ta kwaana. Kamar ta rike Mutum haka ta rika ji sai kuma mirmishi ta ke yi kuma ta yi tambayan duniyan nan waye Aji Mimi ba ta ba ta amsa ba. Sai da safe da Hajiya ta shigo ɗakin Mimi ta mike da gudu ta isa gareta tana rike da rigar ta Rumgume Hajiya lokaci daya t na fadin"Hajiya albishirin ki" Hajiya na mirmishi ta ce"Gori fari tas Binta." Mimi na Dariya ta ce"Hajiya jiya na ga mansoor wlh na ganshi, kalli wannan rigar ma ta shi ce fa.   Hajiya ta yi shuru cikin mamaki tace"Mansoor dai da na sani na wajen Meri.? Mansoor na Binta" Mimi ta gyaɗa kai farinciki ya cika zciyarta Hajiya ta ce"Ikon Allah ya na nan daman? Ubangiji mai yarda ya so. Masha Allah." Hajiya ta na faɗa lokaci ɗaaya ta na zama gefen gadon Mimi sai a lokacin suka samu gaisawa da Rukkaya. Rukky tace"Hajiya wai waye wannan Mansoor da tun jiya da Mimi ta ganshi ta ke farinciki duk da wulakancin da ya yi mata? Hajiya ta yi tsai kafin ta ce"Wulakanci ya yi mata kuma mai sunan yangayu? Nan Rukky ta zauna ta kwashe komai da ya faru jiya ta gaya ma Hajiya ta karishe da fadlɗin"Masifaffe ne Hajiya wlh bashi mutumci waye shi har da zai saka Mimi kuka? Hajiya ta yi dariyasu na manya kafin ta ce" Ina wanda Yaddiko ta taɓa  yi ma Binta zencensa lokacin da kika rakata wajenta?. Da sauri Rukkaya ta gyaɗa  kanta ta kosa taji kan zencen.   Hajiya ta gyara zama kafin ta ve" Shi ne kike mganar shi yanzu. Saurayin Binta ne tun tana da kuruciya  shima ai yaro ne lokacin shi ne kuma har gobe ta kasa mantawa da shi acikin tunaninta kuma ina da tabbacin saboda shi ta kasa aminta da kowani namiji har yau." Mimi ta yi saurin cewa"Ba saboda shi ba ne Hajiya." Hajiya ta katse da cewa",Saboda shi ne mana Binta, kinsan na san ki sarai ko mahaifiyar ki murja ba zata gayamin wacece ke ba." Sai Mimi ta yi shuru sai ta dukar da kanta tana wasa da Botirin dake jikin rigar Aji da ke hannunta.   Rukkaya ta gyara zama tana faɗin"Hajiya me ya faru ne? Ina so naji labarin wannan Soyayyar? Hajiya ta gyara zama tana faɗin "Yau zan faxamiki komai mai sunan yan gayu" Daga nan Hajiya ta fara bata labarin yaddaa Alaqan ta fara ta dalilin Inna Meri da yadda haɗuwar Mansoor ta kasance da Mimi, da duk soyayyarsu da yadda abubuwa suka faru da kuma yadda alaaqan ta lalace daga karshe. Hajiya ta karishe da faɗin"Tun daga wannan abun da ya faru iyayensa suka yanke alaaqa damu, tun daga lokacin  Meri  bata kara zuwa wajena ba  nima kunya da nauyi sun hanani na taka  shima yaron ban kara jin labarinsa ba, Binta saboda haka ta ta fi can wani gari karatu ko an yi hitu ba ta cika zuwa Gombe ba , itama tun da Mahaifinta ya ce ko bayan ransa bai yarda ta auri wannan yaron ba ta nuna dakiya duk iya tsawon waɗanan shekarun tana nuna bata damu ba ne amman ni nasan ta damu kuma ya na cikin ranta ba ta manta da shi ba, kamar yadda shima bai manta da ita ba, saboda ya ƙaunaci Binta kuma duk da soyayyar dukkansu  suna da yarinta ne alokacin sun dauketa da zafi, saboda shi Binta ta zauna a wajena har ta gama babbar Sakandiri,  mahaifinta bai so ba, saboda ni na matsa ya sa ya barta  Saboda mahaifiyarsa ko da yaushe yana gidanan sun shaku da juna sosai har ta kai su ga aminta da auran juna ni kuma ban hana ba saboda yaron ya fito da gidan mutumci mahaifiyarsa ta zauna da ni har muka rabu ina kewar kyakyawan hallayan ta har gobe in na tuna abinda Kabiru ya yi ma iyayen yaron nan da shi kanshi sai naji ciwo a raina Rukkaya ba ni da yadda zan yi ne kawai.".   Hajiya ta ƙarishe kamar za ta yi kuka Rukky ta cire tagumin da ta yi ta na kallon Mimi da ke kuka hawaye wasu na koran wasu Ajiyar rai ta sauke kafin ta ce"Ikon Allah, Hajiya ai ba laifin Mimi ba ne bai kamata ya yi mata abin da ya yi mata ba jiya." Hajiya tace" Zai iya yi mata ma wanda ya fi shi, tun a lokacin mahaifiyarsa na kuka da shi wajen bakar zuciya da riko, ai daman tun a wajen ya furta ko ita kaɗai ta rage a duniya sai dai ta mutu ya mutu amman ba zai taɓa auranta ba, kila ya kasa manta abin da ya faru ne shi ya sa ya nuna mata haka kuma Kabiru daman ya yi masa tsakani da Binta haka suka yi yarjejeniya da iyayensa."   Rukkaya ta ji hawaye sun cika mata ido cikin tusayin kawarta ta ce"Hajiya Mimi na son wannan mutumin har gobe kuma nima ma yadda saboda shi ta hana kowa wata damar, me zai hana shi Abi a rokesa ya janye kalamansa saboda farincikin Mimi? Hajiya ta yi shuru kafin ta ce" Duk da Kabiru  ya yi sanyi saboda rayuwa ta sauya masa amman dai bai taba furta haka ba sai dai ya nuna kar a takura mata, Ai an gama lalata alaqar tunda farko yanzu da wuya kalaman baki su iya gyara ta." Rukkaya ta ce"Da kuma haka Hajiya, ai shima na ji abokansa na faɗin yanzu ya samu duniya ƙwallo yake yi fa yana babban kungiya a nan garin Gombe ne." Hajiya tace"Ba shakka ai yana da zuciya ni dai a sanina burinsa ya zama sojane to ina ga bayan faruwan lamarin komai ya sauya." Hajiya ta kalli Mimi dake kuka kafin ta dafa kafaɗaanta tana faɗin" ki kwantar da hankalin ki Binta na sha kuka a gaban Allah ina rokon ya kawo miki abokin rayuwa nagari tunda kika haɗu da Mansoor yau ina ji a jikina kaddaran ku ba ta kare ba, ki yi addu'a sai ki ga komai ya tafi da sauki." Sai kawai Mimi ta saki kukanta ta kwantar da kanta saman Cinyar Hajiya tana fadin"Hajiya ta nan anan nake jin wani irin zafi acikin ƙirjina, Ina son Mansoor soyayyarsa ita ce ta cigaba da rike rayuwata Hajiya. Tun da Abi ya raba ni da shi farinciki na ya zama rabi da rabi, ganinsa kuma da na yi yau ya fama min wannan cutar dake cikin zuciyata Hajiya Mansoor na sona har yanzu sai dai ya kasa mantawa da abinda ya faru ne, har yanzu ya na ganin bai cike wannan bambamcin da Abi ya nuna akwai a tsakanina da shi ba shiyasa ya nuna ya manta da ni, in har baya sona me ya sa ya damu saboda rigata ta yage? Hajiya shi ya sakamin wannan da kanshi a jikina."   Take faɗa ta na gunjin kuka Hajiya na ta faman lallashinta a ɓoye sai da Rukky ta share kwalla. Daman akwai irin wannan soyayyar ta a mutu har yanzu?. Ƙarshenta dai tafiya ta yi gida saboda Mimi ta yi kuka har ta gaji kanta ya fara ciwo Hajiya ta saka Baaba Uwani ta hada mata Tea ta sha sai ta sha magani ta kwanta. Tana kwanciya sai barci ta fara barcin kenan Mommy ta kira wayar Mimi sai Hajiya ta kira Baaba Uwani ta ɗaukar mata wayar suka yi mgana   Hajiya ba ta ɓoye mavta komai ba na game da Haɗuwar Mimi da Mansoor ba, da kuma halin da take ciki Hajiya ta ce"Murja ku yi mgana da Kabiru ya janye kudurinsa a kan Binta da yaron nan matukar yana son cigaba da ganin farincikin ƴarsa, in kuma ya na son baƙincikin da ta danne acikin zuciyarta ya yi sanadiyar mutuwarta ai shike nan, amman ki faɗa masa ya sani ya tursasa ma Binta ta yi masa biyayya akan tafarkin sunnar ma'aiki ai aure ta ce za ta yi ba karuwanci ba, sannan da talaka da mai kuɗi duk na Ubangiji ne, yanzu yaron da ya ce ba shi da makoma mai kyau Allah ya ɗaukakasa an ce ƙwallon kafa yake bugawa sannan shi dai wanda ya wulakantan shi ƴar sa ke so har kwanan gobe, ki sanar dashi ni ma uwace a gare shi kuma ya yi ta saɓa umarnina tun a baya kuma na yafe mishi to shima ya yi hakuri ya duba Isharan da Allah ya nuna masa tun a duniya ya Janye kalamansa a kan Binta ya saka baki a nemo wannan yaron da ahalinsa ya roƙesa su gafara ya kuma amince Binta ta aure shi shine kawai masalahan da zamu samu sannan shine farincikin Binta a yanzu." Duka mangaganun Hajiya a kunnen Abi tunda a speaker Mommy ta saka wayar ya na kwance ne amman kuka yake yi, ita ma Mommy sai sharan hawaye take yi tana kauda kai ba ta so ya gani. Ita ya kallo ya na tuna a zamanin baya bai taɓa ba ta damar magana ba, duk abin da ya yanke ko ta na so ko ba ta so haka za ta bi, kuma gaskiya Hajiya ta faɗa shi ya san ya rika take maganar Hajiya a matsayinta na uwa ba ta isa ta ce ya bar abu ya bari ba ya na ganin ya na da kaki sannan ga yadda ya gina rayuwarsa ba wanda ya isa ya rushesa masa. Ya daɗe da yin nadaman abin da ya aikata ma wannan yaron sai dai kunya da tunanin inda ma zai fara ya kasa mgana.   Ya sha kiran Mimi sai ta zo ya kasa magana sai dai ya yi ta lallashinta yana bata Hakuri, ya na so ya samu damar neman gafaran kowa kafin Ajali ya riske shi bakinsa ya yi nauyi amman kalaman Hajiya sun zaburar da shi lokaci ya yi da ya kamata ya gyara abunda ya ɓata shekaru goma da suka gabata. Tabbas Mimi zata samu farinciki ba zai zama uba mai hana ƴarsa nata farincikin  a saman na shi ba, kafin ya bar duniya zai yi ma Mimi abinda zata dauwama tana tunawa da shi ko bayan ransa.   Mommy na sharan jawaye a fakaice ta zari tissue ta na goge masa hawayensa cikin karfin Hali ya rike mata jannu da hannunsa na hagu da ya ke motsawa  ta kasa kallonsa shi kuma so ya ke ta kallesa amman ta kasa saboda kukan da ke cin ranta. Kowacce uwa tana son ganin duka rayuwan ƴa'yanta ya inganta, amman ita a cikin Ƴaƴanta akwai wacce ta ke cikin rayuwar rabi farinciki rabi damuwa. Ta san Mimi ba za ta manta da yaron nan cikin sauki haka ba, ta kuma san shi saboda shi ne ta ke zaune har yau ba ta yi aure ba tunda ba ta rasa manema ba ne. Tun a lokacin ta san ba'a kyauta ba, amman ba ta da wannan ikon na faɗin haka mutumin da bai ji mganar mahaifiyarsa ba ita din banza ya ji nata.   Cikin ƙaryewan murya ya ce"Murjanatu ki ɗago ki kalleni don Allah." Dakyar ta dago ta kallesa sai sharr hawaye  shima hawayen ya ke yi da karfi ya kamkame hannunta kafin ya ce"Ki yafe min nasan ke ma na cutar dake, amman ki sani na yi nadama tuntuni nauyi da kunya da rashin sanin ta inda zan fara suka hanani mgana amman tun da Hajiya ta nuna min hanya in sha Allahu zan gyara kuskurena Murja." Mommy ta kalleshi cikin mamaki kafin ta ce"Da gaske Habibi? Sai ya jinjina mata kai kafin ya ce"Ki kira Dr  ki faɗa masa ya zo ina son ganinshi, zan saka ya san yadda zai yi a tafi dani Gombe zan roki gafaran Hajiya da Mimi sannan zan saka a nemo wannan yaron na rokesa gafara na kuma roke shi ya auri Mimi saboda farincikinta,  na kuma yi alkwarin yin azumi uku na kaffaran rantsuwan da na yi." Da sauri Mommy ta Rumgumeshi tana Fadin"Thank You Habibi Allah ya baka lafiya, yanzu kuwa zan kira Sulaiman Mimi za ta samu farinciki itama." Yadda ta ke murna ne yasa ya san ya jima ya na danne mata Hakkinta a matsayinta na uwa.   Ashe abun na damunta acikin ranta ba taa taɓa nuna masa ba. A gabansa ta kira Dr Sulaiman suka yi mgana ta kuma haɗasu shima ya gayamasa ya yi musu bucking din jirgi zuwa Gombe. Cikin mamaki ya ce"Me ya faru Abi? Kai da ba ka da lafiya in Hajiya ce sai a kirata ta zo ta ganka." Cikin muryan ciwo yace"A a ni zan je da kaina gafaranta zan nema Dr.  kuma ina son na gyara kurakuraina na baya." Ba shi da abun cewa illah ya amsa da zai yi musu bucking din jirgin Mommy ta ce kar ya damu ba sai yazo ba,  ita za ta iya raka Abin har Gonbe kuma ta bashi duk kulawan da ya dace. Ba ta kuma yi maaganar da kowa ba har su Hajiya ba ta kira ta ce ga yadda suka yi da Abi ɗin ba.   Sun dai yi waya da Mimi da ta tashi barci ta ji muryanta duk ya dishe alamun kuka sai ba ta neme ta da mgana ba, ballantana ta nuna mata sun yi mgana da Hajiya Abi ta tambaya Mommy ta ce mata ya samu barci saboda ba ta so ta haɗasu ya yi mata wata mgana. Farinciki ta ke ji acikin ranta yau ko da ba wani abu a kallah ya sauke nauyin cin zarafin mutanenan da ya yi abu sam bai yi daɗi ba. *****. *Washegari.* 8:45pm. Mu'azzam bai samu tafiya ranar lahadi saboda sanda suka koma gidan Aji a daran jiya baya gidan Allah ya sa Mu'azzan akwai key ɗin gidan ajikinsa da shi suka yi amfani suka buɗe gidan suka shiga suka kwanta.. Har safe suna ta kiran wayarsa bai ɗauka ba sai da rana Mu'azzam ya je Studio ɗin su ya same shi. A camp ɗin su ya kwana sannan ya ki ba ma kowa damar da zai tattauna abin da ya faru jiya da daddare. Hakanan suka je suka raka Makama ango gidansa Nasir ya wuce gidansa Ahmad ma ya wuce gidansu gobe da Asuba zasu kama hanyar Mu'azzam zai rage masa hanya zuwa Kano daga nan ya samu motar kaduna.   Mu'azzam ya zo ya na ba ma Inna labarin abin da ya faru ta riƙe haɓa tana fadin"Allah Sarki Bintar Hajiya ashe ba ta manta da ni ba" Mu'azzam yace"Wallahi Inna sai da ta tambaye ki." Inna ta yi mirmishi itama tausayin Mansoor da Binta na cika ranta. Kafin ta ce"Bakomai  Ɗan Inna, komai ya yi zafi maganinsa Allah zai huce ka ga ya dawo da kanshi." Mu'azzam ya ce"Inna har yau Yaya Mansoor na son Anty Mami ni nake  faɗa miki haka." Inna ta ce" Har gobe ma Mu'azzamu, yana nuna cewa ba ya ta ita ne yanzu amman ƙarya yake yi duk wannan abubuwan da ka yana yi saboda ita ce kuma ina mai rantse maka in ba ita ya aura ba da wahala Baban Inna ya yi aure saboda ba zai iya zama da kowacce mace ba sai ta." Mu'azzam yace"To inna ba za a iya  yin wani abu ba? Haka za'a barshi ya karar da rayuwarsa cikin kunci? Inna Meri ta  yarfa hannu kafin Ta ce"Me zan iya yi a kai Mu'azzamu ban da addu'a? A gaban ka mahaifin yarinyar nan ya ce mu yi masa tsakanina da iarsa, shima kuma kana ji ya rantse sai dai ya mutu bai yi aure da ya aureta , ni na rasa wannan bakar zuciya irin ta Baban Inna da kafiya da riko, rikon da yake ma abun a ranshi ne yasa ka ga duk ya koma haka" Mu'azzam kamar ya yi y kuka ya ce"Inna ni dai in har ɗan'uwana zai yi rayuwar farinciki zan nemi Anty Mami mu yi magana , zan koma gidansu a Abuja na roki mahaifinta ya bari Yayana ya auri ƴarsa ko da zan mallaka masa duk abin da na mallaka ne."   Da sauri Inna Meri ta ce"Kul kar ma ka fara, ka san ai kun gwaada haka a baya komai ya lalace. Ko ka je ya amince ya janye maganarsa ya za ka yi da Baban Inna? kana tunanin shi taurin kansa da wannan bakar zuciyar zata barshi ya yafe ne ya amshe ta ko da ya na sonta? Ai ya gwammace ya mutu da wannan bakinciki akan dai ya yafe abunda ya faru ya nuna ya na son yarinyar nan har yanzu, ai gani zai yi kamar ya ragu bakar zuciyarsa ba ta kitsa masa abu mai kyau a kan rayuwarsa addu'ata kullum Allah ya saussauta masa wannan baƙar zuciyar." Inna Meri ta karishe tana fashewa da kuka Mu'azzam sai ya koma yana ta lallashinta amman shi kanshi kamar ya yi kuka. Allah yasa Walida ba ta nan tana Gidan Bintu can za ta kwana. Asuban ci zai yi na tafiya shi ya sa ma a gida ya kwana ɗakin Saddiqu, saboda Mansoor dai ya yi ma gidansa ya ji ba zai ji daɗin kwana shi kaɗai ba. Amman ya kwana tunanin mafita a daran kuma ya kira wayar Anty Mami ba ta ɗauka shi dai zai kara kutsa kansa cikin wata kasadar a karo na biyu mai kamceceniya da kasadar da ɗan'uwansa ya kutsa kanshi a karon farko a shekarun baya. Ko kaɗan ba su Bari Baba Danjuma ya fahimci akwai matsala ba Saboda kada su ɗaga masa hankali. Amman fa ya fahimci daga Inna har Mu'azzamu yanayin su ba daɗi sai ya dauka saboda tafiyar Mu'azzamun gobe ne Tunda Ɗan inna ne in ya zo uwar tasa ba ta son ya tafi.   Mu'azzam ya yi ta tufka ya na warwara, sai dai abu ɗaya ya kashe masa gwiwa da ya tuna Nasir ya gayamasa an taba hira da ita acikin labarinta ta ce mahaifinta ya yi hatsari ba shi da lafiya? Abin da bai sani ba shin ya na nan a raye ko ya rasu? Amsar da ya kasa samu har suka bar garin a mota ma ya ke tambayan Ahmad yace shi ba'a garin ya ke ba wlh bai sani ba sai dai ya Kira Nasir din ya ji ta bakinsa tunda yana garin zai iya sanin wani abu. ***** 30 April 2022 Yasan Mu'azzam ya bar garin duk ba su yi waya ba, saboda yasan yanayin aikinsa ba zai jima ba. Sai da a daran ranar litini ya koma gidansa daman baya son lokacin da zai samu kaɗaicewa wani na gefensa. Tun haɗuwarsa da Mimi bai ƙara barci cikin salama ba. Ya ji ya tsani kanshi ta yadda har gobe zuciyarsa ba ta daina son wannan yarinyar da yake ganin bakinta fiye da kowa a duniya ba.   In da ya san yadda zai iya ciro zuciyarsa ya ciro son ta ya jefar ya maida zuciyarsa da ya yi haka domin ya cigaba da rayuwa cikin salama.. Tun da alaqan ta yanke bai taɓa kwana ya tashi bai tuna da ita ba, Soyayarta da kishin ta suke kara wahalar da shi. saboda ita ya kasa kallon ko wa ta ƴa mace da sunan so, saboda ita ya kashe maganar aure acikin zuciyarsa gabaɗaya rayuwarsa ta zama kamar mattaciya saboda cutar da zuciyarsa take ciki.   Kwance ya

Chapter 13 of 26