tun baya gane kalmar agola har ya fara sanin ma'anarta.
Yasan kan tsiyatu kala kala sannan komai na shi na daban ne, gaisawarsa ma ba irin ta kowa ba ce a cewarsa Ina yini ba gaisuwa ba ce sai dai barka da yamma ko barka da safiya in ya gaisheka a haka ruwanka ne ka amsa ko kar ka amsa shi dai ba zai ce ina yini ko ina kwana ba, shi ya sa ake ganinsa wani mara kunya kuma mara tarbiya.
Da gaske ya ci sunan shi na Aji saboda mai Ajin ne ya na da kamewa a kan karan kansa yana yin komai cikin Aji ne da isa, gaye ne da ba ya son reni ko ƙankani. Shi y ssa koda yaushe maganarsa da su Nasir su zama masu aji su rika abun masu Aji duk da yana da son shiga mutane amnan kuma ya iya miskilanci za su yi ta abubuwan su ba ya saka musu baki sai ya ce su na abu kamar marasa aji, sannan shi mai ra'ayin ya yi aure da wuri ne saboda matarsa ta rika taimaka ma Inna sannan yana so ya ga ya taso da ya'yansa kamar matsayin abokan juna sabanin Mu'azzam da yake so sai ya mallaki wani abu da zai rike kansa da iyayensa tukunnah.
Ko magana ake yi sai Mansoor ya ce shi fa yana da gadon gonaki a garin su, su zai saida in ya tashi aure, sai ake ganin kamar abun nashi wasa shirme shirme shi kuma bilhaqqi a kan gaskiyarsa yake yi.
Dukkansu wata makaranatar Gwammati ta cikin gari su ke zuwa rayuwa ta yi wahala tunda Baba Ɗanjuma girma kuma yazo, sai a hankali ba domin Inna Mari macece mai tsayawa ga kanta ba da ai tuni rayuwarsu Mu'azzam ta jima da sauyawa sannan kuma tana samun taimako daga bangarori da dama ko daga can garin su Argugun ana yi mata sako itama ta kan je in wani abu mai bukatar zuwanta ya ta so.
Ko bayan haihuwan Walida ta je gaisuwan Kawu Surajo kuma ta jima acan sai dai ta dawo ta ga Magajiya ta sauka an samu Mariya daman ta bar ta da ciki.
Da ta dawo ne tafara sana'ar cikin gida na saide saide ta na samun rufin asiri to abubuwan sai a hankali da an tarfa jari sai ya darkane, kuma ga shi acikin gida ba zaman lafiya kullum fitinar Magajiya na yau daban na gobe dabam kuma har kwanan gobe ba'a taɓa jin Inna Meri na tanka in tanka da ita ba shi ya sa ba a wajen Baba Danjuma har a makota kowa ya shaida hakuri tsabar shi wajen Inna Meri mace mai kauda kai da yakana babu ruwanta mai rama Alheri ko da mutum ya yi mata sharri.
Bintu ce ta ɗauko irin fitinar Baban Inna itama an sha fama da ita acikin gidan ita da baban Inna ba'a daga musu yatsa su bar shi haka sai sun karya shi, ga su Amina da suke manya amman sai Bintu dake da karancin shekaru ta tare musu mgana acikin gida Inna Meri in abun ya isheta sai ta yi tagumi tana faɗin"Ni wannan fitina na yaran nan na rasa in da suka gado shi, ni dai Allah ya shaida ba ni da fitina amman Allah mai ganin dama ya bani fitinannun ƴaƴa guda biyu Allah dai ya ƙara shiryamin su."
A koda yaushe kalamanta kenan, to yau da gobe bata bar komai ba dole rayuwar ta yi wahala da ya sa Inna Mari ta nemi shawaran Baba Ɗanjuma ya barta ta nemi aikin da za ta rika yi a cikin gidajen masu kuɗi suna samun abun rufin asiri saboda Aminci da yardan dake tsakaninsu ya sa ya amince mata, Harira ta yi mata hanyar samun aiki gidan wata mata ma'aikaciya ce mijinta ma ma'aikaci ne sai dai aikin kula da yara ne acikin gari gidan su yake, nan Inna Meri ta fara aiki kuma albashin mai tsoka ne sai dai dalilin mazan dake gidan sun yi yawa ya sa ta ijiye aikin gidan tana ganin ita uwa ce bai dace ta zama mai aikin mace ita kaɗai acikin maza ma'aikata sama da biyar ba sai ta ga aikin bai bata sha'awa ba ta ijiye.
Da kamar ma ta hakura tunda tana ta nema ba ta dace ba nan makotan su matar mallam Hashimu Dije ita ta yi mata hanyar aikin da ta ke yi yanzu a gidan Hajiyar shagamu. Tunda a baya kanwar Dijen ke yi sai kuma ta zo ta yi aure sai Hajiya ta ce a samo ma ta wata yar babba haka sai Dije ta yi ma Inna Meri mgana jin Hajiyar ce kaɗai a gidan zata riƙa zuwa da safe ta yi girki da gyaran gida sai kuma zaman kadaicin zata ɗebe ma Hajiyar ai da gudu ta amince
Kuma sai Allah ya haɗa jininta da na Hajiya za ta je da karfe 9 na safe ta yi share share sannan ta dafa ma Hajiya abinci sai kuma su zauna su yi ta hiran duniya da Hajiya.
Inna Meri na jin daɗin zama da Hajiya ba domin alherran da ta ke yi mata ba, a'a sai saboda ita ɗin mai kirki ce da sanin ya kamata, karfe 4:30 da rabi na yi za ta ce Inna Meri ta koma gida ta yi ma yaranta girki sannan kuma in za ta tafi sai ta ce sai ta ɗaukan ma yaranta abinci kuma wani kayan sawa na jikokinta za ta ce su Yadddiko su haɗo mata duk Inna Meri take ba ma wa, ta amince da ita sosai domin ta sha mata jarabawa kuma ta ga ba ta sameta da ko sata ko gulma ko dai wani mugun hali ba, shi ya sa Hajiyar kan zaunar da ita tana gayamata wasu abubuwa da suka danganceta itama Hajiyar tasan labarin Inna Meri da abunda ya barota da garin tsohon mijinta zuwa auranta da Danjuma da kuma ya'yan da take riko.
Tunda wani lokacin kamar asabar da Lahadi su Bintu na biyota in ta kore su sai Hajiya ta ce ta kyalesu mana ai tana son zuwan su saboda suna ɗebe mata kewa sannan ta na jin su sunan Baban Inna da Ɗan Inna Mu'azzam kenan shi ya kan rako Inna Meri kuma ya shigo ya gaida Hajiyar, amman Baban Inna sai dai ya tsaya daga waje, shi ne ma Hajiya ba ta taɓa gani ba.
Kuma Hajiya har gidan wanzamai ta taɓa zuwa Lokacin da Inna Meri ta zame ta faɗi a banɗaki ta samu targaɗe ta saka direba ya kawota har ɗakin Inna Meri ta gaisheta tana da kirki da hakuri ga kyauta fara aikin Inna Meri ba za ta iya kirga alherin Hajiyar Shagamu a gareta ba. Ta san ƴaƴan Hajiya guda uku ne kuma duka masu abun hannunsu Yaddiko dai ta yi aure kuma a babban family ta yi aure sai Alhaji Hamza da ɗan siyasa ne a lokacin ma ya ci sanata, sai wanda Hajiya ke yawan korafi a kan shi kabiru soja da ke garin Abuja.
Hajiya na yawan faɗin halinsa na taurin kai da rashin jin mgana Kakin Sojan dake jikinsa ya sauya masa hallaya ko Hajiya ba ta isa ta ce ya yi abu ko ya bar abu ba yana zuwa amman ba sosai ba sai dai Alhaji Hamza da ya kan zo duk daddare in bai zo yau ba, zai zo gobe Yaddiko ma ko da yaushe ta na tafe kuma suna kula da Hajiya tana da megadi da kuma direba ko da mjinta ya rasu ya'yanta sun ji ƙa rayuwarta da ababen more rayuwa.
Tana kaunar Jikarta Fatima da take kira Binta da sun samu hutu Hajiya na tafe kiran a taho mata da ita ta yi hutu a wajenta. Itama yarinyar na ƙaunar Hajiya shi ya sa ta ke yawan yin hutun ta a gombe tare da Hajiya.
*BOOK 1 FREE NE, 2,3 PAID NE REGULAR N500, VIP 1K NE, KU BIYA KUƊIN KARATUN KU TA WANNAN ASUSUN BANKIN 0552179550 JAMILA UMAR GT BANK, SANNAN SAI KU TURA SHAIDAR BIYA TA WAƊANNAN LAMBOBIN.*
*09069067488*
*80032773332*
*Ƴan kasuwa masu bukatar a tallata musu hajojinsu cikin farashi mai sauƙi, ku yi min magana ta wannan lambar*
*09069067488*
*NA GODE.*
*Janafty*
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FAtGNQc8Y8pB008TuxFJVo
*IDAN AN CIZA..!*
*Wattpad:Jamilaumar315*
*Arewabooks:Jamilaumarjanafty*
*Mallakar:Janafty*
*SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA*
MMN MUJAHID KAYAN MATA AND SUPPLEMENT
SHIN KINA DA LABARIN MACCE MAI GYARA DABAN TAKE GA ZUCIYA MIJIN TA, MUNA DA KAYAN MATA MASU ZAFI NA BUGAWA GA JARIDA
HAJIYA TA KUDI DA KUDI AKE NEMAN SU
INA MASU FAMA DA MATSALA RAMA BA GABA BA BAYA KINA ZAUNE ANA KWATANCI DAKE KINA CI BAKI KOSHI MUNA DA MAGUNGUNA DA ZUMA 3 IN 1 KIBA BRST HIPS TA CIKO MIKI KU INA KIYI FRESH MUNA DA KWAYOYI MUNA DA GARI DUK MASU CIKO JIKI NE KIYI DUM
INA MASU FAMA DA MATSALA BRST KU TSUHU YAFI SON YAGA NONO A TSAYE DUK MAI MAGANIN DA TACCE MIKI ZATA BAKI MAGANIN NONO KAI TSAYE YAYI MIKI KARYA CE MAGANIN BRST SAI KIN SHA ADADIN WANDA ZAI MIKI SBD DUK CIKIN GYARAN JIKI NA BRST YAFI WAHALA YI
INA MASU FAMA DA MATSALA SANYI MUNA DA MAGANIN SANYI ORIGINAL
INA MASU ZAMAN BANZA BABU SANA'A KINA KONE DATA KI GA BANZA WURIN TSEGUMIN KALLON STATUS DIN WASU GA DAMA TAZU MUNA HAR GIDA GA WAYAR HANNUN KI KI MALLAKE MOTA MILLION 8 HAR FIYE GA ALBASHI GA RIBA GA KYAUTA KAYAYA KI
08066726866
*Page 12*
_28 December, 2008_
Da in ya zo a ƙofar gidan ya kan tsaya sai daga baya megadin gida wani Dattijo duk da mgana ba taɓa haɗasu bayan gaisuwa ba. Ranar shi ya leka yana ce ma Mansoor
" Ɗan Samari ai da ka rika shigowa daga ciki, kana jiran babarka taka zai fi da ka yi ta tsayuwa daga waje"
Bai yi masa gaddama ba duk da bai taɓa marmarin shiga gidan ba sai dai ganin yadda dattijon ya yi masa mgana cikin kyautatawa shi ya sa ya kasa ƙin karɓan tayinsa.
Dalilin da ya sa yake shiga daga bakin get wajen zaman megadin nan ya kan zauna ya jira har sai Inna Meri ta fito domin su koma gida tare, Islamiya tunda suka yi wannan tsiyar da Shamsu bai ƙara zuwa ba saboda wani shashi acikin zuciyarsa na gaya masa in har ya koma suka haɗu da Shamsu to ba zai kyalesa ba mafi zaman lafiya shi ne ya yi zaman sa har sai lokacin da ya ji zai iya ganin Shamsu ya wuce ba tare da ya kai masa naushi ba.
Boko ce kaɗai ya ke zuwa itama sabooda sun kusa fara Jarabawar fita ne, in ya dawo da yamman filin ƙwallo suke tafiya daga can nan yake yankowa ta nan. Su Nasir ma ba kullum su ke zuwa islamiyan ba can ya ke ganinsu a filin ƙwallo Mu'azzam kuma tsoron faɗan yayansa ya sa ba ya zuwa sai ranakun da babu makaranta da yamma.
Ko kwanakin karshen mako da suke zuwa da safe.
Yau ma zaune yake a saman bencin katakon da megadi kan zauna a kai ya sha iska yana sanye da wani yadi mai saukakkan kuɗi sai dai a goge suke tas, ya sha karin guga Kallo ɗaya zaka yi ma Aji za ka shaida da gaske ne shi ɗin Aji ne da kansa ba saƙo ba, kuma Ajin na shi ya kama kasa ba, hankalinsa na kan wayarsa ne ƙarama mai tocila ya na faman latsawa, yi yake yi kamar hankalinsa na kan abin da yake yi ne amman kuma ba akan wayar yake ba, yana can gefe in da yake hango yar matashiyar yarinyar nan da Inna Meri ta ce jikar gidan ce. Ta kofar falon da zai sadaka da falon gidan yake ganinta tana lekowa ta na kallonsa sai ta koma in ta ga kamar zai ɗago, ba yau ta fara haka ba tun daa ya fara shiga haraban gidan ya jira fitowar Inna Meri tana yawan leƙosa amman ba ta taɓa fitowa ba. Shima sai ya yi kamar bai ganta ba, alhalin duk lokacin da za ta yi wannan leken shima sai ya tattara hankalinsa a kanta. Yau ɗin ma nunawa ya yi kamar hankalinsa na kan latsa wayarsa sai da ya ji megadi na faɗin.
"Bintar Hajiya ki fito mana, kina leke tun ɗazu."
Ba ta da yadda za ta yi tunda an ganta kuma har an kira sunanta, sai ta fito tana nokewa tana sanye da doguwar riga na abaya ta yafa mayafin rigar a saman kanta sai faman mirmishi take yi lokaci ɗaya kumatunta na loɓawa. Ta wutsiyar ido yake kallonta a ransa ya ce yarinyar nan akwai arhar fara'a da dariya, Ko ba'a yi mata mgana ba ita kaɗai ma sai ka ga tana mirmishi. Yana jin ta tsaye a kansa tunda ta Ƙariso shi kuma daman Megadi ya shige ɗan ƙaramin ɗakinsa ya barsu, shi kuma sai ya yi kamar bai san da wanzuwar mutum ma a wajen ba. Kamar daga sama ya ji maganarta cikin zaƙin muryanta da ya shaida ta tun a karon farko.
"Ya sunan ka?
Ɗagowa ya yi yana kallonta kamar yadda shima ta ke kallonsa hannayenta na bayanta tana juya jikinta yamma da kudu, lokaci ɗaya kuma ta na jifansa da mirmishinta da har gobe suke da tasiri a rayuwarsa.
"Ni? to ke ya sunan ki?
Cikin karaɗinta ta ce"Ni sunana Mimin Mimin Abi"
"Ni kuma Sunana Mansoor Aji.."
"Aji..?
Ta faɗa da sigan tambaya har ta na saka a yatsa a gefen bakinta, irin sunan ya ba ta mamaki sai da ta saka shi ya yi murmishi ta na da surutu da karaɗin magana kafin ma ya kara magana ta yi zaraf ta kara cewa.
"Wajen wa ka zo? wajen Hajiya?
Sai da ya girgiza mata kai kafin yace" A'a ni wajen Innata na zo."
Cikin mamaki ta kallesa har da waro ido kafin ta riƙe haɓa ta ce" Inna Meri mai girkin Hajiya.? Sai ya gyaɗa mata kai, kamar wata babba sai ta kama baki tana dariya kafin ta ce"Laa wai daman itace maman ka? Kallonta kawai ya ke yi ba tare da ya yi mgana ba a ransa ya na faɗin yarinyar nan akwai bakin surutu.
faɗi ba'a tambayeka ba kenan shi fa bai tsareta da tambayoyi ba, amman har ta fara fesa masa ita Abuja take suna da Mommy kuma Abi ɗin su soja ne.
Sannan ta gama Jss3 yanzu za ta shiga Ss1 ne, labarai kala kala haka ta na tsaye take gaya masa shi dai ya yi kasaƙe kawai ya na jin ta kuma yana kallon bakinta.
"Kai ina ne gidan ku?
Kansa ya nuna kafin ya ce"Ni? Sai ta gyaɗa masa kai, cikin gajiya da maganar ta ya ce"Gidanmu ya na can da nisa" Ya faɗa lokaci ɗaya yana mikewa sai kawai ta ce"To ina ne ina so na sani ne"
Cikin ƙosawa ya ce"Ke can da nisa ne ba ki san hanyar ba."
Sai ta rage fara'a sai da ya kalleta sai ya ji bai ji daɗi ba sai ya samu kansa da faɗin" Ba ki san gidan ba yana da nisa daganan"
Sai ta yi zaraf ta ce"Za ka kai ni wata rana na ga gidan ku? Saboda ta kyalesa ya saka ya gyaɗa mata Kai kafin ya ce"How old are u Mimi? Cikin zaƙin muryanta ta ce"I am 16 years old."
Jinjina kai ya yi aransa ya na faɗin ba Shakka domin ya ga aikin yarinta.
Shima kawai sai ta sauya harshe tana tambayansa "How old are u?
Mamakinta ya kama shi har nuna kansa ya yi ta gyaɗa kanta sai lamarinta ya bashi dariya har sai da ya murmusa kafin ya ce"I am 20 years old."
Sai ta washe baki kafin ta ce"Ka girme ni ashe." mamakinta yake yi jin turanci mai kyau a bakinta, bai ɗauka haka Mimi take ba sai da ta dame shi da tambayoyi, har sai da ya gaji ya kalleta yana faɗin " Kin cika tambaya Mimi, kamata ya yi in kika girma ki karanta aikin jarida." Bai cika sakewa da wanda bai sani ba sai gashi ya biyema yarinya tana tambayarsa yana amsa mata. A haka har Baba Megadi ya fito ya gansu har sai da ya yi dariya kafin ya ce"Ka haɗu da gidan jarida da kanta, Bintar Hajiya akwai tamboyoyi ita komai so take sai ta sani."
A ran Mansoor ya ce y gga alama amman bai yi mgana ba. A bakinta ya ke jin izifinta goma sha Bbyar cikin mamaki ya kalleta kafin ya ce"ki na zuwa islamiya ne?
Sai ta washe baki kafin ta ce"Uncle ɗinmu ke zuwa gida ya na koya mana, sannan Mommy tana yi mana karatu da safe kafin mu tafi school."
Jinjina kai ya yi, shi ya ɗauka yadda take yar gata nan karatun addinin ba zai dameta ba, har fa sunan makarantar bokon da ta yi sai da ta gaya masa da sunan Yayyenta gidansu ya ji dai sunan khadija(Khadi) a bakinta har ya gaji, da labarin Abi ya siya mata kaza ya siya mata kaza kallonta kawai yake yi yana so ya ji ko a cikin ƙasan ran shi ta dame shi amman cikin ikon Allah bai ji ya gundira da jin maganar ta ba.
Har fa turkeshi ta yi wai shi ya sunan makarantar su? Ya faɗa mata bai yi ma ta ba har sai ya gayamata ya iya karatun Qur'ani?
Sai da tambayar ta saka shi dariya dai dai
Lokacin da Inna Meri ta fito cikin shirin tafiya ganin Binta tare da Baban Inna ya sa ta ce" Binta Kina nan ashe? Hajiya na can tana cigiyarki." Tana ganinta da sauri ta nufeta ta riketa tana faɗin"Inna Meri wai wannan ɗanki ne?
Ta faɗa ta na nuna shi sai da tambayan ya saka Inna Meri dariya. Rike mata hannu ta yi kafin ta ce"Eh mana kuma bashi kaɗai ba ne ina da wasu ƴaƴan a gida.".
Da sauri ta ce"To ina za ki je yanzu?
Ta ce gida zani Binta, kai tsaye ta ce"To nima zan bi ki ina so na je na ga gidanku ne" Ta faɗa tana kallon Aji da ya yi gim da rai kamar ba yanzu ya gama dariya ba.
Inna Meri ranar ta ga ta kanta, dakyar ta lallashi Mimi ta hakura amman sai da ta ce gobe za ta tafi da ita in dan ta zo, sannan ta yarda Inna Meri ta rakata har bakin kofar falom Hajiya sannan ta juya shi ko Mansoor har ya yi gaba a ranshi yana cewa yarinya nan akwai sai surutu da rigiman tsiya.
A hanya ya ce ma Inna yarinyar akwai surutu Inna Meri ta yi mirmishi kafin ta ce " In da surutun ta yake burgeni ta bakin Hajiya akwai mgana mai amfani a bakin Binta duk abin da ka ji ta yi tambaya akansa mai amfani ne.
Sai shima ya yarda da maganar Inna Meri ta na tambaya ne a kan gaskiyan duk abin da ba ta sani ba, kuma take son sani har suka isa gida Inna Meri sai labarin jikar Hajiya ta ke bashi. Abun da ya bashi mamaki Inna na gaya masa Hajiya na son a bar mata jikarta amman tana tsoron ta yi magana uban yarinyar ba zai bata ba.
Cikin mamaki ya ce" Saboda mene Inna? Ba ita ta haife shi ba?
Inna Meri tace"Kai ma dai kayi maagana, shine babba ma amman kuma kamar ba shi da sauƙi ko kaɗan na taɓa ganinsa sau ɗaya fusakarsa ba fara'a sannan ya yi ta magana a sama sama ina gidan ya zo Ina cikin madafi ina jin Hajiya na yi masa faɗan kan dai wani abu amman harshensa a saman nata kuma naji ma da kunnena yana mata rantsuwan bazai yi abin da ta saka shi ba."
Cikin Al'ajabi Mansoor ya girgiza kai bai sami zarafin mgana ba tun kafin ya gansa kawai yaji ya tsane shi me ya sa yana babba kamar sa bai san darajan mahaifiyarsa ba?
Inna Meri sai gaya masa take yi Hajiyar da kanta ta ke mata ƙorafin a cikin ya'yanta yafi ba ta matsala. Shi dai yana jinta amman bai yi magana ba sai dai acikin ransa sai da ya ce kuma ga shi Allah ya basa ƴa mai kyau da kaifin basira.
Tun Mimi na matashiyar yarinya kyanta ya ke a bayyane.
Bai taba tunanin in ta kara ganinsa za ta kama sunan shi ba sai da washegari ma ya koma gidan yana tsaye a haraban gidan ya ji ta ƙwala masa kira.
"Aji.."
Abun ya ɗaure mishi kai, ta kiran sunan shi cikin muryanta mai zaƙi fiye da yadda sauran abokansa ke kiransa.
Shima sai ya samu kansa da amsa mata har kuma itama ya kira sunanta.
"Na'am Mimin Abi ko?
Ta na yar dariya ta Ƙariso gabansa kafin ta ce"A'a MIMIN AJI dai?
Ido ya sakar mata ta na dariya Kumatunta na loɓawa take faɗin "Sunanka ya yi min daɗi ka bar min Please.".
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa har tana buga Ƙafafunta a kasa, a lokacin sai yaji kamar wani abu ya daki zuciyarsa da ya saka sai da ya saka hannunaa ya dafe jikin get ɗin gidan da yake tsaye har bai san bakinsa ya subuce wajen faɗin "Na bar miki daga yau kin zama Mimin Aji."
Cikin jin daɗi ta ce" Thank you kai ma daga yau ka zama Ajin Mimi."
Yadda take dariya sai ya ga fuskarta cikin fara'a da annushuwa mai kyau ne sannan ta fi kyau in tana mirmishi ko dariya.
Al'amarin alaƙar Mimi da Aji wani al'amari ne na Ubangiji shi dai kawai ya samu kansa da jin yarinyar a cikin ƙrjinsa sannan saboda ita baya fashin zuwa ya taho da Inna Meri alhalin a baya ba ko da yaushe ya ke zuwa su koma gida tare ba, saboda haka ya ya ye zuwa islamiya ko da yaushe yana hanyar GRA in an yi mgana sai ya ce ya je tahowa da Inna Meri ne. ita kanta Mimi za ta iya cewa Allah ne ya haɗa zukatan su waje ɗaya tunda ga ranar Hajiya har gajiya take yi da labarin Ajin Mimi. Tun Hajiya na ɗaukan abun shirme har dai ranar ta ce"Wai waye ne wannan Ajin ni Binta?
Mimi ta ce"Laa wai hajiya ba ki san shi ba? ɗan Inna Meri ne fa ? me dafa miki abinci."
Hajiya ta ce"Au shi ne wani Aji? To ai bari Merin ta zo na ji waye wani Aji acikin ƴa'yanta ya na nemen ya ƙwacemin gwamnatina wajen Binta ba ta da magana sai ta shi."
Haka ko akayi inna Meri na zuwa bayan sun gaisa Hajiya ta ce"Meri wai ni cikin Ƴaƴanki waye wani Aji da Binta ke yawan mganan shi, na ce ina ta san shi ta ce ni bansan shi ba ai yana zuwa gidan nan."
Inna Meri na dariya ta ce" Mansoor ne Hajiya Baban Inna, bai taba shigowa ya gaishe ki ba ne shi ya sa ba ki san shi ba."
Hajiya na yar dariya ta ce"To ni dai na ce waye kuma wani Aji? Sai ace masa ya shigo mu gaisa ya daina taremin yar jikata a waje bai zo ciki ya fara ganina ba."
A lokacin ita Hajiya a wasa take yin maganarta Inna Meri na taya ta da dariya ta ce" Zan gaya masa Hajiya, ai sunan Aji abokansa ne ke kiran shi da shi.".
Hajiya tace"Sunan banza ba, ga sunan shi mai daɗi." Mimi na zaune a gefe ta cee"Hajiya Ajin ya fi daɗi wallahi."
Hajiya tac e"To daman ke me kika sani? Har yanzu yarinya ce ke Binta.".
Inna Meri na ta dariya Mimi ta tura baki tana faɗin"Ni ba yarinya ba ce."
Hajiya ta kalleta tana dariya yarinyar da ko nono ba ta da shi sai kirgan dangi da ta fara har kuma yau ba ta fara Jinin al'ada ba, Murja har damuwa ta fara yi Hajiya ta ce ta kwantar da hankalinta wasu matan ba sa farawa sai sun kai sha bakwai kila Binta ta na daga cikin su ne.
A ranar Mansoor bai zo ba, ya je filin ball sun je buga wasa da yan anguwan Tudun wada, Mimi ta riƙa leƙe ba ta ganshi ba Inna Meri na mata dariya ta ce"Baban Inna ba zai zo ba tunda kika ga har yanzu bai zo ba."
Mimi ta fara fushi har ta na cewa in
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 26