Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Mimi dai kuka ta yi kamar zata ba ma uku lada domin ta so ta bi Hajiya su koma gombe Hajiya ta girgiza kai kafin ta ve"A'a ki zauna ki yi ma mahaifinki biyayya shi ya haife ki ya fini iko da ke, ina miki fatan Allah ya sanya hakan ya zama alheri a rayuwar ki Binta ki yi Hakuri kin ji ko? Mimi tana ji tana gani Hajiya ta tafi ta barta daga nan ta fahimci ta rasa wani hop, domin Mommy ba ta isa da ja da hukuncin Abi abunda ya faɗa tabbas haka din ne zai kasance. Tun daga wannan daran Mimi ta ke kukan Rashin Aji a rayuwarta kukan da har tsawon shekaru goma ba ta taɓa dainawa ba. Kuma wannan zafin da kirjinta ya soma tun daga ranar ne, to shi ya haifar mata da ciwon da har gobe bai warke ba. ****** Labarin abin da ya faru da Mansoor ya za ga gari ba wanda bai sani ba. Wani tarihi ne da shi kanshi ba zai taɓa mantawa da shi a rayuwarsa ba, sannan tarihin dafin soyayyar da ba shi da magani. A ranar kwanan hanya suka yi zuwa Gombe tunda Mota ce ga Mansoor ba lafiya kafin su isa duk jikinss ya kara tsami, Allah ya sa Baba Ɗanjuma ya riko kuɗi a Hannunsa Inna Meri na cikin tashin hankali ba ta tuna da wannan ba.   Motar da su hayo ma daga tasha Sai da Baba sani ya biya, suna ta faɗa da masifan yaro ya jawo musu bala'i, sai dai suna ganin halittar da Mansoor ya  koma sai suka yi shuru domin su kansu sun san yaron ya kai kanshi in da ya kusa mutuwa. Jinya ce sosai Mansoor  ya yi domin ya samu targade da gocewar kashi sama da huɗu a jikinsa ga raunika a saman kansa ga tsamin jiki ga raunin dake cikin zuciya wanda ido ba ya iya gani. Shi kaɗai yasan irin ƙunar da zuciyarsa take ciki, ciwo dai idanuwana ba sa iya gani sai shi kaɗai da zuciyarsa ke cikin kirjinsa ya san halin da ya ke ciki. Makota haka suka yi ta tururuwan zuwa ganinsa wasu duk saboda gulma ne, wasu kuma domin ganin abunda ya faru mata kuma suna ta zuwa yi ma Inna Meri barka da arziki.   Su Baba Sani ke kara ma lamarin magi da gishiri suna ƙara abunda bai faru, har suna cewa shi kanshi Yaya Ɗanjuma da Merin dakyar suka sha domin yaron ya je ya jawo Yar soja an kusa kashe shi fitinarsa ya sa yau ya kusa janyo abin da zai saka har su a kashe su a banza. Nasir da makama kullum suna gidan wajen Mansoor dake kwance ya na jinya, Ahmad kuma sai da ya dawo garin ya zo ya ga yadda Mansoor ya koma shuru shuru ba ya mgana kamar an sauya shi. Baya cin abinci baya mgana ba ya fara'a ko da yaushe ya na kwance yana fama da kuncin zuciya. Kullim mganar Inna Meri shi ne" Baban Inna ka mike ga kanka wannan kwanciyar  ba zai yi maka kyau ba" Sai kuma ta saka masa kuka, Baba Ɗanjuma shima ko da yaushe cikin yi masa nasiha yake yi. Su Nasir ma koda wani lokacin cikin faɗin " Aji ba fa karshen rayuwarka ba ne ya zo, Mimi ba ita kaɗai bace mace a duniya ka mike ka gina rayuwarka zaka samu wacce ta fita a gaba."   Mu'azzam kuma kamar yafi kowa damuwa maganar kenan" Ka manta da abin da ya faru ka tashi ka kula dani kamar yadda ka saba, ba na jin daɗin ganinka a haka" Haka su Yaya Amina suna tafe zuwa duba shi kowa na bashi mgana Har can mallam Sidi inna ta aika Yalwa da ya'yanta sun zo har Baban shi Karimu sai da ya zo duba shi. Inna Meri ba ta ɓoye musu abunda ya faru ba ta gayamusu komai. Yalwa na kuka ta ce"Allah ya isar masa ba mu yafe ba."   Karimu kuma cikin fusata ya ce"Ke sakarai miƙe  ga kanka, ubanka har ya bar duniya ba lusarin namiji ba ne ka tashi ka zauna da kafafunka domin gina ma kanka kyakkyawan rayuwa anan gaba." Ya san duk abin da su ke faɗa gaskiya ne, amman shi a cikin Kirjinsa wutar ƙiyayya ke bayyana, daddare haka zai kwana bai yi barci ba yana kukan zucci, Auwalu bai taba tausaya masa ba sai dai ya riƙa dariya yana faɗin"Maganin ma su janye janye kenan in ban da karfin hali ina kai ina wannan yarinyar? Tabbas gaskiya ya fada soyayya ta rufe mishi ido da ya sa ya kai kansa inda bai dace ba.   Yana so shima ya manta amman ya kasa ji yayi ya tsani duk abunda ya danganci wani aiki mai kaki burinsa na zama Soja tuni ya za ma mattace acikin zuciyarsa. So yake yi ya zauna ya yi kuka amman kuma ya kasa sai ranar da Mu'azzam ke masa mgana ya samu ya riko hannunsa ya danna a kirjinsa yana faɗin "Ta nan ne,a nan na ke jin ciwo da zafin abun. Ina so na manta amman na kasa." Kawai sai ya fashe da kuka ya dunƙule a jikin Mu'azzam ya na kuka kamar ransa zai fita Mu'azzam bai hana shi ba domin yana so ya samu sukuni. Tun daga wannan kukan da ya samu sararin yi ya samu sauki acikin zuciyarsa, wannan abin da ya faru Shine silar sauya rayuwar Mansoor ya  koma rayuwa shi kaɗai ya koma Shuru Shuru sannan mai riko sannan bakar zuciyarsa ta kara ninkuwa sama da sau goma.   Daga lokacin Inna Meri ba ta kara takawa gidan Hajiya ba, Hajiya ma ba ta kara nemanta ba alaqar ta ƙare. Ana ta masa mganar ya koma makaranta shima sai ya yi tunanin gwara hakan zaman ya ishesa. Da taimakon gonakinsa na gado aka saida ya samu ya fara karatu a gurbin Jami'ar Gombe state University. Sun ba shi Agric kuma bai sauya ba saboda shi ya riga ya gama sarewa da duk wani burin shi.  Da farko tare da Mu'azzam za su shiga sai kuma Alhaji Mustapha ya kawo maganar zuwa Police Acadmy Wudil a matsayin Mansoor ya je tunda shi ke son aikin Kaki, amman ina ya ce har Abada da ya zama ɗan sanda gwara ya mutu. Sai ko Mu'azzam ya ce zai je tunda Aminin Alhaji Mustpaha ke shugabantar makaranta Kuma shi ya bashi Upper ta mutum ɗaya. A lokacin tuni shima Mu'azzam ya watsar da mafarkinsa yace shi zai tafi Wudil Mansoor kuma ya ce ƙaninsa ba zai yi aikin kaki ba. Inna Meri tace bai isa ba sai Mu'azzam ya tafi, Mu'azzam ɗin ma ya nuna ya na son ya je. Kawai sai Mansoor ya ce"Ka je ka je, ka za ma duk abin da kake son zama Mu'azzam amman ka sani har Abada bazan taɓa kaunar wani aikin kaki ba."   Mu'azzam ya ɗauka zuwa gaba Yayan nashi zai rage wannan kiyayyar sai dai kash kiyayyar ta shi mai girma ce har Mu'azzam ya tafi Wudil bai kaunaci wannan karatun na shi ba, Tafiyar Mu'azzam ta kara saka ya zama ya na son kaɗaici, Saboda zaman shuru in ba shi da karatu sai yake zuwa ya na tsaren wani shago a kasuwa yana samun kudin abun hawa zuwa makaranta, ya daina neman kowa hatta su Nasir ya Guje su. Ko sun neme shi ba ya zama in da za su gan shi, su ma sun gaji da nemansa sun kyale shi a tunaninsu nan gaba zai dawo dai dai. Yana Aji biyu a jami'a Coach na Team ɗinsu na Nasara tare da na Tudun wada Team suka zo nemansa akan suna bukatar wani yaro matashi wanda ya iya buga kwallo za'a bashi horo na shekara biyu wata kungiya zata ɗauke shi. Mansoor suka nema tunda daman tare da shi suka rika bin shugabannin manyan Team ɗin su na yan ƙwallo daga na manyan anguwanni har na ƙananu.   A lokacin sai ya ga ya mu su Mu'azzam ne kuma ya tafi Police Acadmy baya nan, Coach ɗin su na Nasara Team yasan Aji ya iya taka kwallo shi ya matsa akan cewa shi Ajin ya zo a matsayin Mu'azzam ɗin mana. Da farko yaƙi amincewa sai daga baya ya ga to miye aciki? daman shi tuni mafarkinsa ya daɗe da sauyawa amman bai amince ba sai da ya yi mgana da Inna Meri da Baba Danjuma suka sanya ma lamarin albarka. Sannan ya amince ba zai taɓa mantawa da Coach din su na nasara Team ba wato Shehu Master Allah ya jikan sa ya rasu shi ya ɗauke shi ya kai shi wajen Coach ɗin su na Gombe United  a lokaci suka yi mgana sosai ya jaraba shi ya gani sai ya ce za'a bashi horo na shekara biyu, shi kuma sai ya ga ya masa yana karatu sai ya nuna masa hakan bazai shafi karatunsa ba.   Kwatsam ne fuskar Aji da sunan shi ya bayyana acikin yan kwallon kafa, Ya yi horan shekara biyu sannan aka gabatar da shi a Kungiyar kwallon kafa ta Gombe United lokacin kontiragin  Captain ɗin kungiyar saura shekara ɗaya ya kare, tare suka ƙarisa wannan shekaran ɗayan da Aji bayan kuma ya bar Club ɗin ƙokarin Aji ya saka ya samu matsayin Captain saboda daman dalilin da ya sa a ka kawo shi kenan. Shi ne sanadin da ya sa ya zama duk abin da ya zama a ƙwallon kafa, kuma tunda ya riga ya hakura da mafarkinsa sai ya maida kansa ga karatunsa sannan ga wasan kwallon kafa.   Shima ya yi singing kontiragin  na shekara goma ne da Gombe United sun kuma fara biyan shi albashi bayan alawun da yake samu in suka fita wasa, da haka ya gama karatun shi ya yi service ɗin sa anan garin Gombe zuwa Lokacin rayuwa ta mika abubuwa da dama sun sauya ciki har da gama makarantar Mu'azzam ya fito da matsayin  Assistant superintendent of police ASP, ya kuma samu an ijiyesa a garin kano sai dai ya riƙa zuwa ganin gida. Kuma har a lokacin Mansoor bai kaunar aikin kaki duk ko da matsayin Mu'azzam na Asp. Ya samu shahara da suna a duniya saboda ƙwallon kafa, sunan Aji ya tashi kan mutane ko da daman ya shiga wasan ƙwallon kafa da sunan shi na Aji sai sunan ya kara ɗaukaka su kansu su Nasir suna mamakin shigar Aji kungiyar kwallon kafa sanin shi ba ya ra'ayin haka sai dai kuma in suka yi duba da rayuwarsa ta sauya sai su daina mamaki.   Acikin Shekaru goma ya taka matsayin da ya taka ya mallaki kwalin Degree sannan ya na shekaru na biyar a kungiyar Gombe United a matsayin Captain mai buga lamba huɗu dan ƙwallon mai sa'a wanda kuma kungiyar ke alfahari da shi saboda yadda ya iya taka leda. Ya yi kudi ko na ce ya samu arzikin da ya gyara gidan su sannan ya fitar ma da Iyayen shi bangaren su, har su Baba Sani suma ya gyara musu bangaren su,  ɗawainiyar  gidan ya dawo a kansa gabaɗaya sai dai abin da ba'a rasa ba Mu'azzam ya saka Hannu.   Gidan ya rage mutane tunda matan duk sun yi aure mazan kuma sun yi aure wasu kuma suna can wajen sana'arsu da matansu Auwalu ma ya yi aure wahalan rayuwa ya sa Aji ke taimakonsa da Mu'azzam yanzu. Sannan tun daga kan Mimi Aji bai kara neman wata mace ba in aka yi masa mganar aure sai ya sauya fuska gashi ya siya fili ya yi gida ya siya mota ya siya mashin sannan ya siya ma Baba Danjuma ma. Har aka aka ƙarama Mu'azzam matsayi bayan shekaru uku zuwa superetendant of police SP kuma ya yi aure da yar'uwansa Hibbatu cikin shekara ɗaya ta haiihu aka samu mai sunan Baba Danjuma Gaddafi. Da ɗaya da ɗaya kuma su Nasir su ma suka samu aiki suka yi auran su, Nasir ya na aiki da Nepa makama kuma aikin banki yake yi , Ahmad kuma yana kaduna yana ɗinki shima ya yi auransa Aji kaɗai ya rage shidin ma yanzu ya sauya ya daina nemansu sai dai in dan su suka nemeshi.   Ya riƙe wannan abun acikin zuciyarsa da ya kasa barinsa ya yi rayuwa irin ta kowa Mimi ita ce sanadin da ya sa rayuwarsa ta sauya zuwa juyin waina daga sama zuwa kasa tun kuma daga rabuwar sa da Mimi a falon Mahaifinta bai kara ganinta ido na ganin ido ba sai a wajen bikin Makama sai dai can bayan wasu shekaru da suka gabata ya fara ganinta a talabijin a matsayin ma'aikaciya. Ko rashin lafiyar mahaifinta sai a hirar da aka yi da ita ya sani, domin tun bayan abin da ya faru alaqar gabaɗaya ta lalace ita kanta Inna Meri ba ta da labarin gidan Hajiyar Shagamu a yanzu. Mafarin Labarin Mimi da Aji. *Janafty* *IDAN AN CIZA..!* *Wattpad:Jamilaumar315* *Arewabooks:Jamilaumarjanafty* *Mallakar:Janafty* *SADAUKARWA GA HAJIYA AISHA AHMAD IYA* Ina kuke mata yan kwalisa.. *KHADYS EMPIRE* Ta Kawo muku kayan mata masu kyau da saukin kudi💃🏻 kamar haka. *Zumar Matsi Guarantee 3500* *Maganin sanyi komai nacinsa 4k* *Zumar kacha kacha 2500* *Zumar kiba 4k* *Setinn kayan mata na yar gata 8500 Me abubuwa har kala Takwas a ciki* *Dahuwar kaza ta manyan mata 8k* Zaku sameta a Kan Lambar waya 08147832783 tana garin kano tana aikawa da kayanta ko ina da yardar Allah. Dadin dadawa kuma tana bada sarin komai cikin farashi me rahusa yadda zaki sami Alheri. Wani ƙarin jin daɗin ma free delivery withn kano take yi, koh ba yanzu zaku siya ba kuyi saving numbern ta dan nan na gaba Na gode. https://wa.link/pd4ie0 *Page 16* *4rd May, 2022.* _Abuja, Thursday_ *03:40Am* Tun ranar mandoy ɗin da ta gabata Mommy ta so su je Gombe kamar yadda Abi ya bukata amman kuma tana jagorantar wani case a kotu sai ta ga gwara ta tsaya ta gama kafin su tafi. Dole ya sanya ta kira Sulaiman tace ya dakata da Bucking ɗin su ya bari sai ranar jumma'a tunda ranar Alhamis ne karshen shari'an nasu.Sun gama tsara na su amman shi Abin da Ubangiji ya tsara ya sha bambam da tunaninsu.   A daran Alhamis duk wani shirin tafiya Brr.Murjantu ta gama yin sa saboda Sulaiman ya kirata ya faɗa ma ta jirgin ƙarfe goman safe za su bi zuwa Gombe in Allah ya yarda shi ya sa tunda ta dawo daga wajen aiki ta kasa zama sai faman shiri take yi musu tunda wannan ne karo na farko tun bayan abin da ya faru da shi da zai kara takawa zuwa jiharsa.   Alhaji Hamza kawai ta kira suka yi mgana Saboda shi zai tura musu motar da za ta ɗauke su daga filin jirgi zuwa gidan Hajiya, Lafiya lau ta gama duka shirinta a daren Abi yace mata ba ya jin daɗin  jikinsa yana so ya yi wanka ita ta rarrafa ta ɗora shi saman keke ta kai shi tiolet ta taimaka masa ya yi wanka sannan ta gunguroshi zuwa ɗaki ta shirya shi, sannan ta zo ta yi masa shirin kwanciya a daren sun kwana a jikin juna a baya bata ɗora masa nauyinta saboda yanayin laluransa sai ranar kuma da kansa ya bata umarnin ta matso kusa da shi bayan ta matso sai ya saka hannunsa mai motsi ya jawota gefensa har kanta na matsuwa da ƙirjinsa.   Manganganun da ya yi ta gaya mata sun bata mamaki da tsoro sai dai ba ta taɓa tunanin tafiya Habibi zai yi barta ba. Ya jadaddamata in har bai samu zuwa Gombe da kansa ba ta taya shi neman yafiyar Hajiya sannan ta yi masa alƙwarin neman yaro nan ta bashi hakuri sannan ta yi masa alkwarin samar ma Mimi farinciki da kuma ba ta abin da take so, a  lokacin kallonsa ta yi cikin mamaki kafin Ta ce.   "Ka daina faɗin haka Habibi in sha Allahu gobe za mu je Gombe, kuma da kanka za ka samu damar neman gafaran Hajiya, sannan kai da kanka za ka yi magana da Mansoor ka nemi yafiyar sa." Mirmishi ya yi mata ba tare da ya yi mgana ba sai dai ta ga ya yi mata wani  iri duk ya sauya mata. Ta san ya yi shekaru yana jinya ƴan'uwanta ba duka ba ne su ka bata goyon zaman jinyar Major Kabir ɗin ba, gani suke zata yi wahala da shi tunda ba ranar warkewa. Ita kuma me ya rage mata a duniya ban da ta zauna ta kula da Mijinta uban Ƴaƴanta domin ta samu rabauta ranar gobe kiyama,  Shi ya sa ba taɓa nuna masa gajiyawarta ba tana Ƙoƙari a kansa da amanar gidansa da ƴaƴansu   Sun jima kafin su kwanta yana ga ya mata wasu irin mganganu ma su kama da kamar mutum yana barin wasiyya sai hankalinta ya tashi ganin haka ya sa sai ya bar mganar ta rumgumshi ta ce su kwana su yi barci gobe suna da tafiya a gaban su. Barci ne mai nauyi ya kwasheta acan cikin barcin ta yi mafarkin ta ga an taru gida ya cika ana ta kuka kuma taga wai an saka Habibi a makara za'a fita da shi ita kuma ta rike tana ta kuka.    Kamar an wancakalar da ita haka taji ta a gefe ta bar jikin Kabir, sai da ta tashi a firgice dai dai Lokacin da ta ji ya na tari ba kakkautawa. A firgice ta miƙe ta laluba hannunta ta kunna hasken ɗakin sai ta ganshi kwance in da ta kwantar da shi sai dai kuma tari ya sarƙe shi yana yi kamar numfashinsa zai ɗauke hankalinta ya ta shi sai ta tuna mafarkin da ta yi, ai da gudu ta diro daga kan gado ta isa gare shi tana riƙe shi ƙokarin tarairayosa take yi ta ji yana faɗin"ruwa! ruwa! Ba tare da tunanin komai ba ta sake shi sai ta kwashi gudu kamar za ta faɗi zuwa falo fridge ta buɗe ta ɗauko masa ruwa mara sanyi tunda Saboda shi ba ta kunna fridge ɗin falo sai dai na Kitchen. Abin da ya sake ba ta tsoro ko da ta koma har ya faɗo daga kan gado ta ruɗe ga ta ita kaɗai ta nufe shi da sauri tana kiran sunan shi.   " Habibi, Subhanallah!"   Haka ta ke faɗi dakyar ta iya ɗago kansa domin sai taji ya kara yi mata nauyi ta kafa masa goran a baki ta na bashi ruwan abin da ya sa ka ta fashewa da kuka shi ne ganin ruwan gefe da gefe sai zubewa yake yi kaɗan ne ma ya ke shiga bakin sa. Cikin muryan kuka ta ce"Na shiga uku ni Murja me ya same ka haka Habibi? Shi kuma sai ya kauda kansa ruwan ya suɓuce daga hannunta ya ganganra ƙasa inda su ke zaune gabaɗaya ya jiƙa su ita a koƙarinta ta mikar da shi ta maida shi saman gado kamar yadda ta saba dubarunta. Amman yau sai ya gagareta shi kuma tarin na neman ƙara sarƙe shi cikin muryan da ta fara karyewa ba ta ma wani jin sa sossi ta ji ya kira sunan ta. "Murjanatu.." "Murjanatu.."   Da sauri ta amsa da "Na'am Habibi me kake so? Ko na je na kira Megadi ya zo ya taya ni mu ɗora ka saman keken ka? Sai ta ga ya girgiza mata kai lokaci ɗaya yana riko hannunta cikin sarkewan numfashin da ba ta lura ya fara sama da ƙasa ba ya fara mgana"Murja ki yafe min kin ji? Sannan ki tayani neman gafara Hajiya da kuma afuwar Mimi domin na zalunceta sannan ki yi min alkwarin za ki nemi yaron nan ki ba shi hakuri kuma ki yimin alkwarin yi ma Mimi duk abin da take so saboda farincikinta." Yana mgana cikin In ina saboda mumfashinsa na sarƙewa Mommy ta fashe da kuka kafin tavce"Ka daina faɗin irin haka sai na ga kamar mutuwa za ka yi ka barni Habibi?   Cikin ƙarfin  hali ya ce" Naso na samu damar neman yafiyar su da kaina sai dai lokaci ya kuremin Murja, na amimta dake nasan za ki kula da ƴaƴana ki yi min alkwari guda uku na farko ki tayani neman gafaran Hajiya na biyu ki nemi yaro nan ki tayani neman yafiyarsa, na uku ki yi min alƙwarin yi ma Mimi abin da take so Murja" Mommy na kuka ta ke ɗaga masa kai lokaci ɗaya tana faɗin"Na ɗauka amman dai in sha Allahu tare za mu je duk ka nemi gafaran su." Hawaye ke fita ta gefe da gefen idanuwansa ya ce"Ko bayan raina ban amince ki bar gidan nan ba Murja, ko da aure za ki sake yi ki zauna nan ne gidanki domin ki kula da yaran mu."   Mommy kuka ta ke yi har da majina ta kasa mgana sai da taji ya kara riƙo ta da karfi lokacin tarin ya kara sarƙeshi faɗi yake yi " Na yafe miki duka laifin da kika taɓa yi min Murja wanda kika sani da wanda ba ki sani ba , nima ki yafe min duk zaman kuncin da na yi da ke a baya ki yafe min Murj...' Sai ya kasa karisawa domin tarin ya sarkeshi kuma yana tafiya da numfashinsa yadda Mommy ta ruɗe ne yasa ba ta fahimci lokaci ya kure ba. Domin a lokacin ana kokarin zare ran Abi ne, ita a tunaninta ba ta makara ba ya sa ta sake shi ta mike a guje ta fita haraban gidan tana kururwan kiran ma'aikatan gidan.   Allahu akbar ko da suka taso da gudu suna tambayan ta ko lafiya ta rika nuna musu cikin gida tana faɗin sunan Habibi tana wani irin kuka yasa su ka kwashi gudu zuwa cikin gidan har vikin bedroom ɗin su suka iske Abi kwance a kasa idanuwa sun kafe ba ya motsi. Megadin gidan dattijo ne na yanzu tun bayan yin ritayansa shi ya duba Abi ya tabbatar da rai ya yi halinsa itama kuma a koƙarin Mommy a kama mata shi su je asibiti har ta saka mayafi tana faman kiran can asibitin in da Dr Ashiru ke aiki. Megadi ya kalleta duk ta fita hayyacinta sauran ma'aikatan ma maza tuni sun fara salati matan kuma kuka suke ganin yanayin Hajiya duk ta fita hayyacinta ta ruɗe.   Tsawa ta daka musu lokaci ɗaya tana faɗin"Ku kama min shi mu fita waje,asibiti za mu je a duba shi." Kai Baba Megadi ya girgiza kafin ya ce"Hajiya sai dai mu yi hakuri Allah ya yi ma Alhaji rasuwa." "Rasuwa? Habibi ne ya rasu?   Ai ba ta san lokacin da ta yi kansa tana kiran sunan shi ba, lokacin har megadin ya saka hannu ya shafe masa idanuwansa, Allahu Akbar Kullu Nafsin Za'ikatul maut kowani rai sai ya ɗanɗani zafin mutuwa Allah ya sa mu dace. Mommy kamar ta zare ko na ce ta yi hauka haka ta ke rike gawan Abi tana wani irin kuka ta surutai faɗi take  yi"Habibi me ya sa ka yi min haka? Ka tafi ka barni Wayyo Allah na shiga uku na lalace." Ma'aikatanta mata ne ke tare da ita mazan daman guda uku ne megadi sai direba da mai kula da haraban gidan. Matan kuma mai girki wata bakatafiya ce saira sai mai gyaran gida wata yar matashiyace mai suna Aina'u daga can gidan su kano aka aiko mata da ita saboda su taya ta taimakon gidanta da mijinta. Har gwara Saira da shekarunta ita ke ba ma Hajiya hakuri su kansu ma kukan su ke yi Aina'u kuma sai mutuwar iyayenta suka dawo mata sabuwa itama gefe ta samu ta zauna ta na faman rusa kuka jikinta sai rawa yake tunda take a duniya ba ta taɓa ganin gawa ido na ganin ido ba sai yau.   Abi ya cika misalin 3: 50am na daren ranar Jumma'a ne kuma Mommy ba ta iya kiran kowa ba saboda tashin hankali har aka kira sallar asuba gwan Abi na jikinta ta rumgume ta yi kuka har muryanta ta daina fita tunaninta gabaɗaya ya toshe, da ita da su Sara tare su ka yi wannan zaman acikin ɗaki tana kuka suma suna tayata. Sai wajen shida saura na safe sannan Megadi da su Habu suka sake shigowa ganin halin da Hajiya ke ciki ya sa Megadi ya durkusa a gabanta yana faɗin" Hajiya ki yi hakuri ki daina kuka don Allah, ya kamata ki kira waya ki sanar da su abin da ya faru ya kamata a suturta Alhaji domin a yi masa gata a kaisa

Chapter 20 of 26