kanta Ramla saida kirjinta yabuga bata taba kawowa Mom zata daki Asmeey over this silly ice cream issue ba, idanun Asmeey harwani baki sukayi gashi a left side Mom tamata marin inda tamata dazu da safe, Mom namata wani mugun kallo cikin kakkusan murya tace “is this tarbiyan dana baki? Are you stupid kike kiran yayarki dake gaba dake makaryaciya! Are you stupid Asmeey!” Mom ta daka mata tsawa da saida falon ya amsa idanun Asmeey sukai jaaa ga duka kannenta awajen, she felt embarrassed, baki tabude zatai magana amman kuka yasa ta kasa magana cus tana bude baki zata fashe da kuka ga kanninta awajen, Mom dake huci sosai tana kallonta tace “okay I’m talking to you kin sauke kanki kasa ni ga shashasha eh?” Dago kanta tayi ta kalli Mom sai kawai jikinta yahau rawa ganin idanun Mom tace “so….s……” saikuma sorry yakasa fitowa sabida kuka, ran Mom yayi masifar baci tawani fizgo gaban rigan Asmeey haka yarinyar ta taso fuuuu kafafuwanta sukai daba daba akasa skirt nata ya sauka kan black lallin Ramla naso tabata hakuri cus she’s regretting telling Mom amman tsoro take ahada da ita, Mom tashiga daga murya tana jijjiga Asmeey yace “don’t you know how to apologize Asmeey ko saina daddakaki zaki bada hakuri” rawa bakinta yashiga yi idanunta sunyi fiki fiki sun kankance daidai lokacin Gwaggo tabude falon ta shigo tundaga lallin da taga ya kwalbe akasa ta shiga kallo da yanda Mom tarike yarinyar tana kallon yanda hannayen Asmeey da jikinta ke kyarma kawai Gwaggo ta kurma mahaukacin ihu tana bude kofa da saida gidan kap ya amsa. “Ihuuuuuuuu zatai kisan kai jama’a ataimaka zatai kissan kai!” Tundaga su Mamie da Ammi dake backyard dasu Ya Mustapa da Hamad dasu Baba dake masallaci harda Ustaz da su Ya Hameed saida aka fito da gudu ana yowa flat din jin ihun Gwaggo, Mom ta dauke kai daga kallon Gwaggo dake ihu babu ko dar a zuciyanta ta shake wuyan rigan Asmeey dake kyarma tace “I said apologize now!” Ta daka mata tsawa ahankali cikin muryan ban tausayi jikinta na rawa sosai tace “so….so…sorry” “Sorry Wa ne”? Mom ta sake dauketa da mari a same kumatu for the second time mercilessly, Gwaggo tai ihu ta taho tana ture Mom tace “wai ke yarnan bataki bace ko yar riko ce?” Mom dako gezau batayi ba da tureta da Gwaggo keyi tana rike da Asmeey tace “speak!” Bakinta na wani kalan rawa tace “so……sorry Ya Ramla” daidai lokacin su Ya Mustapa na shigowa falon Ya Hamad biyeda shi, awani kalan zuciye Mom ta hankada Asmeey saitin center table dake tsakiyan falon da mugun karfi sai kasa tamugun buge da center table din a gefen cikinta daidai kan idon Baba dasu Mama da kowa hadda matan su Ya Mustapa, Mom tajuya fuuuu tawuce stairs Baba kawai yayi mutuwan tsaye yakasa magana ganin yanda Mom ta buga yarsa da center table mugun buguwa ma, Gwaggo ganin yanda yarta sandarewa tayi ta kankame awajen cike da mamaki kowa na falon was freeze har ita Mama yar fadan Mom,
Mamie ce ta iya motsi cikin kowa takarasa tsakiyan dakin ta duka tasa hannu ta dago Asmeey data kasa motsi idanunta har lokacin duhu duhun mari suke mata, ahankali Mamie tace “Ma’u sannu tashi, kinji ciwo”? Jikinta na wani irin kyarma totally destabilize ga lallen da aka mata ya dame duka har center table yabaci shima da lallin da sauri ta girgizama Mamie kai har lokacin bata gani da kyau ga kunya yagama kasheta ga jikinta rawa kawai yake, tajuyo tana kokarin neman Mom dabata gani a falon ba kowa na kallonta, ahankali Mamie tace “Doctor zoka dubata” dasauri Asmeey ta kalli Mamie jikinta na rawa yana kyarma amman takakalo murmushi muryanta ciki ciki yayi rauni tace “babu abinda kemin ciwo ai ban buge ba” dasauri Yusra tace “duk Ya Ramla taja Mom ta daketa and she lied cus Ya Hamad ai bata cemiki wawuya ba kene kika kirata wawiya because of ice cream” ran Ammi taji yabaci tashigo tsakar falon tace “are you the reason aka daketa haka? Ramla do you even love your sister? Kalli kumatunta, kalli lallinta, kalli yanda jikinta ke bari, bakida imani ne Ramla ke ba mai marba Asmeey ice cream bane bakene babba ba? Wace kalan muguwa ce ke”? Tadaga hannu zata daketa Abba yace “dakata! Karki daketa!Yarane ba’a raba yara da irin kananun fada haka musamman wajen rabo amata afuwa, Husna” da sauri Asmeey ta kalli Abba idanunta sunyi firfirr ba hawaye tace “uhmmm na’am Abba” magana Abba zaiyi but sai yayi shiruuu ganin yanayin yarinyar yace “kaita ta wanke hannayenta da kafafun Maman Doctor, Nana ku gyara inda yabaci da lallen” yunkurin dagata Mamie tayi tace “tashi muje” Asmeey takasa tashi bakinta zaiyi magana sai kawai ta kasa sai hawaye yataru a idanunta ta juyar da fuskanta irin na neman inda zata saka kanta dinnan Mamie ahankali tace “zo Asmeey come” Mamie zata kamata Asmeey zata fita daga jikinta takasa da sauri ta shige jikin Mamie duk yanda takeso ta daure ta danne takasa tafashe da kuka sosai jikin Mamie mara kara sai shesheka da jikinta dake motsi irin kukan nan mai taba zuciya tana huci mai bala’in zafi a jikin Mamie, Baba ya yunkura zai wuce sama Abba yarikemai hannu alamun no dan yaga yanda Baba ya zuciya kuma babu kyau hukunci acikin fushi hakan yasa ya tsaya, Munir yawuce ahankali wajen ya tsugunna kusa da Mamie da Asmeey ke jikinta yadaga hannunsa yadaura saman bayan Asmeey yayi shiruu idanunsa sunyi jazur, ahankali Hamad yajuya yafice daga falon yarufo kofa, Gwaggo da sai alokacin tadawo daidai tace “toh wlh wlh tunda dai abinda akema yarnan agidan nan kenan zan tattarata natafi da ita, kuma dagayau tabar shashin nan, idan uwarta ta isa tazo inda nake ta tabata, bantaba ganin muguwa Uwa irin mahaifiyarta ba, wlh kekuma sarai ai kinsan halin uwarta koda tamiki laifi ai sai ki rufamata asiri ba yar uwarki bace? Kuma ai kina sane ai haushi takeji ansata tayi lalli alhalin tahana ba dole ta dirketa ba, ga lallin nan tasa yabaci hankalinta ya kwanta, Mara Imani da idanunta kaman na mutan da, saisa Allah yahanata tsayi kaman in kifeta da kwando, muguwa dunkulen magi kawia ai gajeren mutum akwai bakin hali” Gwaggo na fadin haka ta karaso takama hannun Asmeey dake jikin Mamie tace “tashi muje” fitoda ita daga jikinta Mamie tayi tace “tashi kuje Asmeey” idanunta akasa taki kallon kowa ta kasa tashi, rai abace Baba yace “badake ake magana ba tashi” ahankali ta tashi da dauriya da kyar, Gwaggo tariketa tajawota aka mammatsa suka taho Ya Mustapa yabi yanda ke tafiya da kallo dakuma gefen cikinta suka fice sai kawai Mamie itama tabisu abaya haka sauran matayen, Mama kuma tawuce sama abinta wajen Mom danta bata hakuri Ya Mustapa yajuya yafito kowa ma yafito.
Flat din su Mamie Gwaggo tashiga da ita har lokacin fada take sosai dakin dake kasa tawuce dan ita duk dakunan kasa nakowani flat nata ne cus duk inda taga dama take kwana tabude tashiga tace “wuce kije ki wanke hannunki” wucewa tayi ahankali ta shiga bayin ta maida kofan tarufe takarasa wajen wash hand basin tadaga hannuwanta da akama lalle duk sun gwalje both baki da jan tai shiru sai kawai hawaye suka sauko daga idanunta tabude tap din ta wanke hannayen tasss and lallin yayi mata bala’in kyau inda ta gwalje ne yayi wani iri, lallin yayi dan ja, Kuka takeso tayi but saita hana kanta gabanta har lokacin faduwa yake, Mom sai fadomata take arai bazata taba kwana anan ba sabida kar ran Mom yabaci zata bari Gwaggo tai bacci saita tafi wanke, kafafunta tayi suma tass ta dauro alwala dan batai salla ba ta kalli kumatunta da sunyi jaa sosai abunka da fara ko yaya aka mareta kalan fatar fuskanta saiya chanza towel na bayin tasa ta tsane fuskanta sannan tabude bayin tafito Mamie tagani tsaye kusa da bayin tace “alwala kikayi?” Dasauri ta gyadama Mamie kai tana kakalo murmushi tace “eh banyi salla ba shizanyi yanzu” Mamie na kallonta tace “babu abinda ke miki ciwo?” Gyadama Mamie kai tayi Gwaggo tace “wannan ai ko zata mutu bazata fadi ba uwarsu yanda kikasan ta tsafesu ni zoki salla muje falo muci abincin dare yunwa nakeji”dan takowa Mamie tayi dab da ita gently takai hannunta ta daura saman kumatunta dayayi ja tana kallon idanunta, wlh tunda Mom ta mareta koda yanzu tai alwala tasa ruwa a fuskanta bataji sanyin dataji kaman sanyin dataji yanzu da Mamie ta daura hannunta kan kuncinta ba sai jikinta yayi sanyi sai taji jikinta ta ciki yadaina radadi cikin murya mai sanyi dakuma so Mamie tace “ya isa! Calm down zanma Mamanki magana dakaina kinji, next time koma menene karkima nagaba dake rashin kunya, kinfi kowa sanin mahaifiyarki macece mai bama yaranta tarbiya yanda yakamata bata yarda danta ko yarta ya taka na gabansa ba, next time respect Ramla kinji no matter what don’t talk back at her just like yanda Mom bazata bar su Yusra ko su Nana sumiki rashin kunya ba kema bazataso kima na gabanki ba, but ya isa okay” gyadama Mamie kai tayi idanunta na cicciko da hawaye, ahankali Mamie takai hannunta gefen cikinta tace “wajen namiki ciwo nasa Doctor yakawo miki magani?”Girgizamata kai tayi tace “a’a bayayi” Mamie tace “to yi salla abinki” Gwaggo taja tsaki tace “wlh takara taba yarnan tagani yo ita ubanwa naga tana girmamawa? Girmamani take? Mata sai girman kai jitake tafi kowa sabida tayi boko, bokon da agidan d’ana tayi kuma da kudinsa banza kai shashasha muzuba ni da ita zan nuna mata matsayinta”
Mamie dai tawuce tafita Asmeey ta dauki hijabin datagani kan gadon wajen tasaka tai salla magrib da isha’i ma da akayi Gwaggo da tunda tafara salla take kallonta tace “kiwa Allah Asama kitashi kicire hijabin nan muje muci abinci cikina sai kuka yake” tashi tayi ta cire hijabin tawarware mayafinta tasa aka yadan sauko mata shoulder Gwaggo tai gaba ta biyota abaya su Ya Mustapa duk suna falon Ball ma suke kallo a tv falon da Ya Abdallah da Ya Faisal da matarsa ke basa abinci, shi kadaine be ciba sai Ya Hameed shima.
Hameed yakalli Asmeey fuskanshi ahade yace “kawomin ruwa” hararansa Gwaggo tayi tace “bazata kawoba bakaga kalan dukan data gamaci ba” tabe baki yayi yace “inda sabo ai tasaba yanzu” wani mugun kallo yayyinsa sukamai, yadanyi murmushi, haushin Mom yakeji sosai aransa, he hates the woman wlh sabida yanda take da duka, da girman kai da fadinrai, haka su Ayah suka wahala a hannunta shi besan me Baba yagani ajikinta take zaman aure da irin matar nan ba, wucewa fridge Asmeey tayi a kitchen tana tafiya ahankali tasa ruwa a tray da cup tafito dashi tazo falon kanta akasa tazo gabanshi ta ijiye. “Gashi Yaya” zata juya Mustapa yace “zonan” faduwa gabanta yayi ta gyadamai kai tazo gabanshi babu wasa kan fuskanshi like a big brother yasa hannu a aljihunshi yaciro wayanshi ya kunna flash yanuna mata gefenshi yace “sit” zama tayi ahankali Gwaggo tace “yauwa dubamin ita” hannunshi yadaura saman kanta ya juyar da fuskanta yana haska kumatunta Mamie ma tafito ta tsaya kansu sannan yasauke wayan yace “inda kika buge namiki ciwo?” Girgizamai kai tayi tace “a’a Yaya” hannunshi yakai ahankali yataba gefen cikin ta saman riga da kyau jin wajen is not hard yadan sauke ijiyan zuciya yana kallon yanda take runtse idanu she need drugs, hannunshi yacire dan murmushi yamata tareda shafa kanta yayi cikeda kauna ta dan uwa yace “it’s okay okay don’t fight with ur sister again, i will buy another ice cream for you gobe” Abdallah yace “wani flavor kikeso nima zan siya miki” Faisal yace “akan strawberry flavor tayi fada nima zan siyamata gobe” Hameed yadan harareta yace “sweetthooth kawai i will also buy for you” murmushi kadan tayi feeling so loved, ahankali tace “nagode Yaya” Mamie tayi murmushi tana kallonta Gwaggo tace “sauko muci abincin” Ya Mustapa yace “jekici abinci zan fita nakawo miki drugs” tashi tayi zuwa kujeran da Gwaggo take ta zauna suka faraci tanadan jin nauyin yayyinta dan ba koda yaushe take ganinsu ba, but kuma tana sonsu sosai sunada kirki sosai and suna son kanninsu suma.
Parking yayi ahankali tareda kashe motan ya kalli paper bag dake gefen sa kan kujera yayi jimmmm sai kawai yatashi yakai hannu yadauka tareda bude kofan yafito yarufe yafara tafiya zuwa flat nasu ko kadan baisan yayyinshi kowa na falon ba hakan yasa kai tsaye yabude kofan yashigo tsayawa yayi ganin kowa harda Mamie duk a falon ga Gwaggo da Asmeey datai tsuri gefen Gwaggo ana kallon ball Baba ne kawai baya falon, duk juyowa akayi ana kallonsa banda Asmeey da tana ganin shine ya shigo ta maida fuskanta tv, ganin yanda kowa kallonshi yake yasa da sauri yaboye abun hannunshi abaya yajuya dasauri zai fita daga falon Mamie tace “Hamadi!” Chak ya tsaya hakanan gaban Asmeey yafadi batare data dauke kanta daga tv ba, Mamie tace “ina zaka daga shigowan ka? Ina kaje ban ganka ba tun dazu? Come” dan jimm yayi sai kawai yasa hannu ya maida kofan yarufe yahade rai kanshi akasa yafara takowa zuwa wajen Mamie Mamie tabi paper bag din da kallo tace “meka sayo?”Agefenta ya ijiye paper bag din da sauri batare dayace komiba kawai yajuya kowa na falon yabishi da kallo yawuce stairs, Gwaggo tace “mara mutunci meya kawo miki banda ni? Koni ba mutum bace” Mamie tasa hannu tabude paper bag din fari ba logo ajiki kawai saita dago kai takallo sama harya shige dakinsu sai kawai tasa hannu taciro ice cream a babban cup strawberry da akai breaking cone da chocolate da so many orishirishi ciki ga cokali takalli Asmeey da idanunta ke tv tace “Ma’u gashi yayinki yasayo miki ice cream” kowa na falon saida mamaki ya kashesa barin ma Hameed daya wani zaro idanu irin na gulman nan, Asmeey ta kalli Mamie saita kasa tashi ta amsa Gwaggo tace “tashi ki amsa Hamadi ya siyamiki yaga kinci bakar duka uwa jaka” tashi tayi zuwa wajen Mamie akunyace tasa hannu takarba ice cream din Mamie tace “kije daki kisha abinki” batai musu ba tawuce dakin Gwaggo tana kallon ice cream din daya dadada mata rai, dan satan kallon sama tayi kafin tabude dakin Gwaggo ta shige.
Gwaggo tace “Doctor kaika aikashi ya sayo abin ne?” Girgizamata kai Ya Mustapa yayi ya mike tace “bari na sayo mata magani” su Abdallah suma sukama Mamie sallama suka fice flat nasu.
Hakan yasa dasauri Hameed yatashi yazo wajen Mamie cikin whispering yace “Mamie Hamadi buying ice cream for a gurl this is unbelievable” hararanshi Mamie tayi tace “munafincinka yakesa Hamad baya shiga harkan kowa cus u give meaning to anything me dan ya sayama Asmeey ice cream? Ba agabansa taci duka ba yanada tausayi” Hameed yana wani murmushi yace “Mamie kodai kodai he he….” Tallabemai keya Mamie tayi tace “kaga saida safe” ta tashi tana murmushi tayi stairs abinta ta shige dakinta shima yatashi yace “bari naje na sami dan iskan nan” dakinsu Hameed yabude Hamad baya ciki it seems yana bayi kayan jikinshi yarage dagashi sai singlet da boxer yazo gaban bathroom din ya jingina da bango yayi folding hands nashi yana jiran yafito, kusan 5min yayi awajen Hamad ya bude kofa yayi wanka yana sanye dawani ash color joggers da white t-shirt na polo mai kyau ga kayan daya cire abayi a hannunshi, hada ido sukayi da Hameed dakemai wani kalan kallo da sauri ya dauke kai ya fuske yafito zai wuce karaf Hameed yasha gabansa yace “wat is that you did earlier?” Chak ya tsaya batare daya kalleshi ba yace “I don’t know wat u are talking about” dariya ke neman kufcema Hameed yace “karya kake munafuki why did u buy ice cream for Asmeey?” Tambayan kaman zaisa ya nutse akasa sai kawai yama juyama Hameed baya kaman zai kara komawa bayin Hameed yarikeshi ya fashe da dariya cikeda iskanci yace “so you are in love” watsar da kayan hannunshi yayi akasa yace “stop Hameed leave me alone” tsabagen son yakureshi Hameed yace “to kaida bama kasan ya ake sex ba how would you be intima……” wani kalan tura Hameed yayi da karfi kaman zaki yawuce da sauri ya sunkuci laptop dinshi zai fice daga dakin Hameed yadaga murya yace “google wat is sex and start learning tun yanzu kafin asami matsala bayan aure” da sauri Hamad yafita yana bugo kofan me Hameed zaiyi inba dariya ba dariya haryana faduwa gaban bayi is not like Hamad baisan sex ba but he can swear baisan yaya akeba wlh kuwa kunya irin na Hamad daban ne aduniya, he hates maganan banza, he hates looking at abubuwan banza ko iskanci ko tsiraici ko maganan kiss baiso ayi a inda yake yanzu sabida dan maganan nan zai iya harsu koma Kano yadena zama dakin nan kenan yadinga avoiding nashi, ba lallai yanason Asmeey ba bama ya tunanin tsokanane kawai yasan tausayi yarinyar tabashi yasayo mata ice cream kaman yanda suma sukace zasu saya mata, da kyar yagama dariyan yaduka ya kwashe kayansa yaje ya ijiye masa yafada gado abinsa sai bacci.
Babu kowa a falo hakan yasa yawuce dinning kawai yama ijiye laptop dinshi yawuce kitchen yadauko ruwa yaja kujera ya zauna yabude ruwan yasha yana sauke ijiyan zuciya sannan yafara aiki.
Almost 30min shi kadai afalon yana aiki aka bude kofan aka shigo hakan yada yadago kanshi karaf suka hada ido da Ramla wacce tana ganinshi taci burki gabanta na faduwa hakanan cikin duka yayyinsu ba ita kadaiba all of them sunfi shakkan Ya Hamadi cus babu wacce yake wasa da ita babu wacce ta taba ganin hakorinsa baitaba mata magana ba, gashi yanada kwarjini wani kallo yamata dayasa batasan sanda ta sauke kanta kasa ba tace “uhnnn dama…..daman wajen Asmeey nazo” bayabo ba fallasa yace “get out!” Har tsakiyan kanta taji muryanshi kusan tunda tasan Ya Hamad this is the first maganan dayake mata wlh kuwa gyadamai kai tayi tace “tom saida safe Yaya” tajuya tabude kofa tafice.
Wuraren 11:30 Asmeey tafarajin munsharin Gwaggo sosai ahankali ta lallaba ta sauka daga gadon batare datai making sound ba tana rike da veil nata a hannu tazo wajen kofa kaman barauniya tabude kofan ahankali tafito tana maida kofan tarufe tajuya da sauri tana tafiya ahankali ahankali sadaf sadaf tana warware gyalen tana kokarin yafawa danta rufe gashinta tai wajen kofa daidai takai kofa tasa hannu zata bude kofan taji saukan zazzakan murya that is so calming and soothing a kunnuwanta. “Where do you think you’re going”? Amahaukacin firgice tajuyo karaf suka hada idanu da Ya Hamadi dake zaune a dinning ga laptop gabanshi da bottle water a gefe ya tsareta da crazy eyes nashi kawai saitaji ta dimauce jikinta yayi wani iri, she couldn’t stand his gaze at all tama kasa magana gabanta sai faduwa yake sai kawai tajuyo ta wuce hakanan saita sake samun kanta da so ta kalleshi dago idanunta tayi kaman mara gaskiya ta kallonshi hada idanu sukayi mugun faduwa gabanta yayi tabude kofan dakin Gwaggo da sauri ta shiga daidai Ya Mustapa na shigowa da ledan magani a hannunshi dinning ya wuce ya zauna yana kwalama Asmeey kira. “Asma’u Asma’u” daga ciki Asmeey tace “na’am” fitowa tayi ganin Ya Mustapa a dinning a yasa taje wajen ta tsaya gefensa batare data yarda ta kalli inda Ya Hamadi yake ba, magunguna guda biyu yaciro yace “2 2 zakisha, duba fridge idan akwai ice kisa a kumatunki karya kumbura idan babu kisa ruwa a leda yayi kankara zuwa anjima” gyadamai kai tayi tawuce kitchen shikuma yatashi yakalli Hamad dake aiki yace “good night” gyadamai kai yayi Asmeey tafito da bottle water ganin babu Ya Mustapa duk sai taji wani iri magungunan tadauka daga dinning tawuce dakin Gwaggo da sauri.
WAYYO ASMEEY💔💔
AFADI GASKIYA MAMIE HAMADI YA SIYAMA ICE CREAM KO ASMEEY??
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
M SHAKUR TA IYA LITTAFI🤩🤩
THANK YOU ALL FOR READING🤩
GAYAMIN ME KIKEFI SO GAME DA THIS BOOK +2347012181461
EPISODE 1️⃣1️⃣
Tana shiga cikin dakin Gwaggo ta maida kofa tarufe ta jingina da kofan hannayenta biyun dake rike da bottle water da magani duka ta daura kan kirjinta dake bugawa nonstop, why is her heart racing sabida Ya Hamad? Saikace yauta fara ganinshi toh kodan bai taba mata magana bane? Anytime sukazo salla ma hardly take ganinshi dan baya shiga mutane, wani zubin daga ranan dazasu zo sai rannan salla take kara ganinshi, takai almost 2min tsaya awajen sannan tawuce ta zauna bakin gadon tabude maganin tabude ruwa tasha, at first batason magani but dukan Mom yasa ta koyama kanta shan magani da kanta, cus drawer su na daki Baba na ijiye musu basic magunguna haka irinsu paracetamol, Ibuprofen maganin ciwon mara da first aid kit she learn to take care of kanta, kallon gadon tayi yanda Gwaggo ke maka uban minshari abinta ta rakube ta kwanta gefe dudda ga uban space tai shiru gabanta sai faduwa yake she wanted to go back to side nasu hakan zaisa laifinta yaragu gashi an hanata fita anan and she knows, Mom tasan ba’a side nasu ta kwana ba, hannunta takai saman kumatunta da taji yana mata zugi takai hannunta saman cikin nata shima dake mata zugi saitai shiruuu hawaye ya gangaro mata bata taba iya bringing kanta to ask her self maisa Mom is always beating her? Mom bata tausaya mata, Mom hit her kaman she’s not her Mom, tana son Mom but Mom bata sonta, dazu data rungume Mamie she wished Mom ta rungume haka, hawaye ta kara sharewa ahaka tagama tunane tunanen ta bacci yayi awon gaba da ita.
Around 1:00 yagama abinda yake dan har Abba saida yashigo still bai gamaba kashe system dinshi yayi yadan kalli kofan dakin Gwaggo saikuma ya mike tsaye ahankali yawuce kitchen freezer yabude yadauki ruwan data saka dayaga yayi kankara yadauka yadauki bowl yasa, yasa wasu ruwan a freezer incase zatai amfani dashi gobe, yafito daga kitchen din yana tafiya ahankali yawuce gaban dakin ya tsaya yayi dan jimmm, hannu yadaga yadaura kan kofan yayi knocking kadan he could hear minsharin Gwaggo daga wajen, sake knocking yayi ahankali but still shiru yasake yin jimmm, ataushashe cikin yar kankanuwan murya dake ratsa mind yace “Asma’u!” Firgigit Asmeey tafarka tabude idanunta dan har cikin zuciyanta taji yanda aka kirata, da muryan bacci dake a hargitse tace “uhnn na’am” dan jimmm Hamad yayi, kusan 10seconds sannan calmly dan yasan bacci take karya firgitata yace “open the door” tashi tayi daga gadon dasauri ta sauko batare datama san dankwalinta baya kanta ba bata da kayan bacci anan so gown din atampan ne ke jikinta ta taho wajen kofan kai tsaye tasa hannu daya tabude kofan while dayan hannunta nakan idanunta tana murzawa sabida bacci, sauke gentle eyes dinshi Hamad yayi kan fuskanta she’s not even looking at him sosa idanu take sabida bacci, idanunshi yadaura kan lafiyayen hadadden kitson da aka mata dayayi kyau sosai da sauri yasauke kanshi ya maida kan fuskanta for the second time ahankali yace “Asma’u!” Dasauri ta dago kanta takalleshi tana janye hannunta daga kan idanunta da suka kada sabida bacci ga kumatunta daya kara ja inda aka mareta gabanta na faduwa sabida yanda yakira sunanta, tsareta da idanu yayi na kusan 10secs dukansu babu wanda yayi magana this time around shine yafara janye idanunshi daga kanta yamika mata bowl da ruwan ice ke ciki yace “put this a fuskanki” bowl din itama ta kalla saita gyadamai kai ahankali tasa hannuwanta kan bowl din zata amsa sai bai saki ba hakan yasa tadago kanta ta kalleshi ganin bai sakin mata ba, hada idanu sukayi yanda taga yana kallonta yasa ta sauke kanta kasa da sauri har lokacin hannuwanta nakan bowl din tana jira ya sakin mata, cikin yar kankanuwan murya da ita kadai zata iyajin maganan sa Hamad yace “next time if anyone tries to slap you use your hands or elbow ki kare fuskanki,” dan dago kanta tayi tadan kalleshi har tsakiyan zuciyanta takejin muryanshi dakeda bala’in dadi, ga kamshin dayake yi daya cika wajen, bawai fuskanshi ko expression nashi shows he care bane but his
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 56