Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Muhammad” Baba dake kalle kalle yace “Yaya naga tundaga kan Mustapha har Hassan nagani amman banga Hussaini ba, ina Hamadi”? Kawu yace “ai wannan ka sanshi” girgixakai kawai Abba yayi yace “yana mota” anatse Baba yawuce wajen motan kai tsaye yabude kofan gaba yace “Hussaini har yanzu dai halin nan na nan to sauko, fito” kowa na compound din juyowa yayi jin maganan da Baba yayi, ahankali Asmeey dake tsaye kusada Mamie gaban motan da Baba yabude tajuyo daidai Hamad na fitowa daga motan kanshi akasa cike da bala’in natsuwa sai kawai gently akuma natse yaduka ahankali gaban Baba yace “ina yini Baba!” Dawani irin sauri Baba yataroshi yace “tashi tashi Son ya gajiyan hanya yakuma karfin jiki? Aikin ya warke ko”? Gyadama Baba kai yayi still kanshi na ahaka yace “Kawu ina wuni” Kawu na murmushi yace “Hamadi lpy lau ya karfin jiki Allah dai ya karamana lafiya gabaki daya” dan shafa kanshi yayi kadan saikuma yatako kadan zuwa dan nesa da Mom dake tsaye tareda Ammi da Mama sai kawai ya duka yace “Mommy ina yininku” bayabo ba fallasa Mom tace “barka da zuwa Hamad” Ammi tace “tashi tashi kaida bakada lpy mike” mikewa tsaye yayi sai yadan waiga, Gwaggo dake kallonshi tace “yanzu zai nemi Maman shi” aiko aka kwashe da dariya harda Mamie sai kawai ya sauke kanshi akunyace, Baba yace “kumuje kumuje bismillah” Yaran suka shiga gaida yayyinsu, Asmeey takalli Hameed tace “ina yini Yaya?” “Wat happen to your face?”Juyowa Mom tayi ta kalli Hameed sannan ta kadakai tai wucewarta Asmeey tace “faduwa nayi” dan hararanta yayi tasauke kai dasauri tajuya zata gaida Ya Hamad yawuce abinshi ko kallon inda take baiyiba instead of yaje flat dinsu Baba sai kawai yawuce flat din dinsu m Ya Mustapa ya kalleshi saikuma ya kyaleshi, dan satan kallonshi Asmeey tayi Ramla taja hannunta tace “muje ciki” suka wuce flat nasu. Duk zama akayi Baba yakalli kowa na falon ganin babu Hamad yasa yace “ina Hamad”? Ya Faisal yace “yawuce chan side din” hada ido Asmeey tayi da Mom data ℳ𝒶𝓉𝒶𝓇 wani mugun kallo mikewa tayi da sauri zata fice Baba yace “ina zaki?” Ahankali tace “zanje akarasamin kitso ne” Baba yace “je flat din Abban ku ki kiramin Yayanki Hamad kafin kije wajen kitson” gyadama Baba kai tayi tajuya tawuce hakanan taji gabanta ya fadi, duk babban salla anan Bauchi sukeyi every year tana ganinshi sau daya tun tana yarinya amman shi kadai ne cikin yayyinta magana bai taba hadata dashi ba, shine ma wanda ba’a ganinshi, shi kowa ne bayama magana, kullum yana daki saidai ranan da za’a kauye, hartakai gaban flat dinsu gabanta faduwa yake hannu tasa tabude kofan falon babu kowa ciki banda akwati nan su dake nan falon da masu gadi suka kawo. Gently tace “Assalamu Alaykum” but shiru sai eco na muryanta da flat din yadauka staircase tafara hawa tana wucewa sama daidai nan falon sama ta tsaya ahankali tace “Ya Hamad!” Shiruu kaman babu kowa a side din, dan tafiya tayi zuwa gaban first room dakenan falon saman ahankali tace “Ya Hamad!” Jin shiru yasa ta wuce second door din saitadan taba tareda knocking tace “Ya Hamad!” Shiru babu amsa hakan yasa tace kodai ba nan ya shigo ba wani flat yaje ko boys quarters, maybe tafita taje boy quarters taduba tana tunanin ta juyo Ya Hamad tagani tsaye abayanta awajen mummunan faduwa gabanta yayi sosai har tana neman kurma ihu tahana kanta da kyar ta daura hannuwanta duka biyun akan kirjinta ta saman gyale tana wani kalan mummunan numfashi sabida tsorata datayi ta jingina da bangon wajen da sauri tana numfashi sosai kaman kirjinta zai fita tana kallonshi fuskanshi da ruwa gashin giranshi yawani kwanta sabida lema, dogayen gashin idanunsa sun tattare sabida ruwa pink lips dinshi sunyi wani pink sosai jikinsu duk lema hakama sajenshi a jike ga hannayenshi daya nannade hannun rigan dake jikinsa zuwa sama tafukan hannayensa ajike da alamu dai he was in the bathroom yana wani irin kallonta, hakanan kasa jure kallonshi tayi sabida yanda taga yanada wani irin kyau barinma yanda kwallin idanunsa yamai kyau, tunda take bata taba tsayawa this close to Ya Hamad ba, idanunshi namata wani iri dasauri ta dauke kanta, kawai bakinta yahau rawa, cikin wata yar kamkanuwan murya da bamatasan tanada kalanta ba dayake so scattered sabida tsoro tace “ahhhmmm…..uhmmm dama daman…..” saikuma ta dafa bango kaman zata suma sabida yanda taji yacika mata gaba and he smells damn good raspberry dawani oud da lavender da sandal wood da vanilla takeji yake mata, softly murya ciki ciki yar karama mai wani irin taushi yace “who slapped you?” Dawani irin sauri tadago idanuwanta ta kalleshi today is the first ever time tunda dai tai girma tayi kuma hankali da Ya Hamad ke mata magana, cus he doesn’t talk to them, yaune rana na farko datakejin muryansa agabanta, kallonsa take kaman yanda yake tsaye shima yana kallonta bazaka iya tantance ya yanayinsa yake ba his eyes looks warm calm serious harsh sexy kai komiba, bala’in kwarjini taji yamata idanu lips dinta rawa suka shigayi sai ta shiga wasa da yatsunta tana kallon yatsun murya chan kasa tace “faduwa nayi akasa” to her biggest suprise saitaga Ya Hamad ya matso gabanta dab da ita da sauri tadago idanunta ta kalleshi bai kalli kwayar idanunta ba duko da kanshi yayi daidai tsayinta yashiga sauko da fuskanshi wajajen fuskanta da mahaukacin sauri Asmeey ta kulle idanunta daidai saitin fuskanta Hamad ya sauke fuskanshi yana kallon wajen dayayi sauka idanunshi sukayi kan kwantaccen gashin sajenta mai kyau zare idanunshi yayi daga wajen ya maida idanunshi kan fuskanta yana kallon yanda ta kulle idanunta lips dinta na rawa tana fidgeting fingers nata sosai hakan yasa yadan koma baya ya tsaya getly yace “who slapped you?” “Mom” ta amsa kai tsaye dawani kalan sauri tabude idanunta cikeda mahaukacin mamaki jin yanda tafadi gaskiya what did he do to her? Dago idanunta tayi suka hada idanu again yai mata wani kallo sai kawai yajuya zai koma first room na wajen data fara zuwa dataga kofan abude dasauri tace “Baba yace nakiraka!” Kaman bada shi tai magana ba dakin ya shiga ya maida kofan yarufe batare daya juyoba tabi kofan da kallo tasake kai hannayenta tadaura kan kirjinta dake bugawa none stop saikuma tasake kallon kofan dakin daya shiga sai kawai tawuce harda dan gudu gudunta tashiga sauka daga staircase din har lokacin kirjinta bai dawo daidai ba tayi kofa daidai zata bude aka rigata budewa Ya Hameed ne chak ta tsaya tadan sauke kanta kasa yace “kin gayamai Baba na kiransa?” Gyadamai kai tayi, Hameed yace “meyace?” Kallonshi tayi tace “baice komiba” sama ya kalla saikuma ya kalleta yace “did u put anything a face dinki?” Girgizamai kai tayi alamun a’a, cikeda kulawa yace “put ice okay” gyadamai kai tayi tace “toh” wucewa abinshi yayi yawuce stairs itakuma takama kofan tafice da sauri tayi wajen mai kitso tazauna aka cigaba da mata kitso har lokacin takasa dawowa daidai she’s just feeling somehow sai taba kirjinta take tana feeling heartbeat nata da har lokacin bai dawo daidai ba tanajin muryanshi a kunnuwanta da bata tabaji ba, for as long as tasan kanta Mom bata taba wani abu ta gayama kowa ba hatta Baba, but wat happened data gayamai Mom ce ta mareta yanzu idan ya sanar da wani akasan Mom ce ta mareta yazatayi? Mom ai saita kusan kasheta, baya magana so ba lallai yafada ba but idan yafada fa? Sai lissafi daban daban take aranta ana mata kitson, kusan 10mins da zamanta awajen hakanan kawai ta dago kai ta kallo gaban flat nasu karaf suka hada idanu yabude kofa yafito daga flat dinsu Ya Hameed biyedashi dasauri ta dauke kanta kasa shima haka baimasan mesa ya kallo wajen bishiyan da baida wani nisa da gaban flat dinsu ba yawuce abinshi, hakanan Asmeey taji takasa daurewa samin kanta tayi da sake juyowa tabishi da kallo tundaga yanda yake tafiya anatse kanshi akasa Ya Hameed kuma na danna waya yana magana dashi, “he’s o quiet” tafadi aranta, saida ya shige flat dinsu sannan tadauke kanta tayi shiruu bamatasan mesa taki dawowa daidai ba in something daya faru within just 1min a flat dinsu, hancinta takai wajen kafadanta sai taji kaman tana kamshin dataji a jikinshi, dasauri tace “Mairo dan Allah kunji ina wani kamshi?” Mai kitson tace “kamshin mene Asmeey?” Tsare mai kitson tayi da idanu dan sun dakatar da kitson saitai shiru wondering why is she even asking this kind of question sai kawai ta dauke kai dasauri tace “uhm ni banmasan mesa nai tambayan ba barshi kinji” dan dariya mai kitson tayi tace “ai ke koda yaushe kina kamshi bantaba zama namiki kitso naji kina wari ha Asmeey kin tuna nataba rokonki turare har kika bani” dan murmushi kadan tayi hakanan sai ta manta she’s sad ma sai tunane tunane kawai take. YA HAMAD YASAN MARINTA AKAYI??🤩 💫UWA KO UKUBA?💫 ✍🏻M SHAKUR MADAM DA ANTY ABAR GULMA AZO A KOYI YANDA AKE BUGA ODAFARE DA YANDA AKE WAWATSULA AGADO🥳🥳 WACCE TA IYA BALAJA’U A GADO ITACE MAMMALLAKIYAN ZUCIYAN MIJI 🎊🎊🎊 AZO ASHIGA INTIMACY CLASS DA 5k RAK AKOYI HARKA OGA YA ZUZUCE🔥 CHAT ME UP NOW AND JOIN wa.me/+2347012181461 EPISODE 🔟 Wuraren biyar saura aka gama mata kitson dayayi yayi bala’in kyau, yan kanana aka yaryada mata su, sai fuskanta da goshinta suka fito sosai, ga gashin yayi tsayi, su Nana daman an gama musu lallin nasu da komi itane daman tarage kuma Mom tace bazatai lallen ba, mai lallen tace “Ammi tace idan an gama kizo ki karbo mana abinci” gyadamusu kai tayi ta tashi tareda sa dan gyalen nata ta yafa tarike na sa a hannunta tawuce backyard inda Ammi take tareda Mama dasu Anty Nafisa da Anty Mims da Anty Meena matan su Ya Mustapa Ya Abdullahi da Ya Faisal dakuma matan dake asalin aikatau din da aka dauko, Anty Nafisa tace “an gama kitson Asmeey?” Gyadamata kai tayi tace “eh an gama Anty” Mamie ta kalleta tareda murmushi idanunta suka sauka kan hannayenta da kafafunta dasuke nan farare kal tace “lalle fa? Kowa harmu tsofaffi munsha lalle balle ke yar yarinya” hannunta ta kalla saikuma ta kakalo murmushi batai magana ba, da zuciya daya Anty Mims matan Faisal tace “ko masu lallen basu iyaba ne? But naga wanda akama Nana yayi kyau ko Mama”? Dasauri Mama tace “yayi kyau sosai kam daga jan har bakin ai saisa duk babban salla basu yarda suyi lalli a Gombe saisun iso nan Bauchi” dan dago kanta Asmeey tayi ganin duk kallonta suke yasa cikin innocent voice tace “bayan salla zanje law school saisa banyiba is not allowed a law school” tana maganan saiga hawaye nataruwa a idanunta da sauri tajuya ta goge hawaye saikawai tawuce dasauri muryanta nadan rawa tace “Ammi wai akai musu abinci masu lallen” tabar backyard din all of them knew she was crying so no one bothered to call her back wucewa tayi tafito daga backyard din ganin hawayen yake tsayawa yasa tayi chan parking space nasu dan gidan ko’ina da mutane dukawa tayi gaban daya daga cikin motocin wajen bawai kuka take wiwi ba but hawaye ke fitowa daga idanunta sosai sai sharesu takeyi da bakin gyalenta, she’s feeling sad again wlh, she’s not happy, tasan wani yaganta tana kuka can be a problem especially idan Mom tasani, bude kofar mota akayi hakan yasa tadago rinannun idanunta da sauri dakuma tsoro, Munir tagani yafito daga motan Abban Bauchi, maida kanta tayi ta sauke kasa ganin shine tana goge fuskanta, karasowa wajen yayi cikeda damuwa saiya duka gabanta yace “wat happened Ya Asmeey? Mesa kikazo nan kika boye kina kuka? Mom ta dakeki ne”? Kallonshi tayi yanda yake kallonta cikeda damuwa dakuma so sai kawai yanzu kukan yataso mata tafashe da kuka sosai tana kallon Munir, ja idanunshi yayi cikeda bakin ciki yace “Mom ne ko?” Gyadamai kai tayi cikin kuka tanunamai hannuwanta tace “kowa yayi lalli agidan nan banda ni Munir” har wani daci zuciyan Munir yakeyi, kowa is happy agidan nan banda sister shi, kowace yarinya in this house da mata tayi lalle banda sister shi cikeda bakin ciki yace “hala sabida shegen law school din nan ne, komi law, law, law, wlh I hate abinda Mom keyi” tashi yayi yace “bari naje na gayama Baba yaza’ayi kowa yayi lalli har ita Mom din an mata banda ke sai kace gobe ne law school din look at you salla ake but you’re the only one that is sad today with red kumatunki and it’s all her doing” dawani irin sauri Asmeey tarike hannunshi tace “Munir karkaje” a zuciye yace “sainaje ki banni naje kafin masu lallin su tafi ba’a miki ba” hawaye gangarowa daga idanunta sukayi cikeda tsoro da tashin hankali tace “Mom will be angry Munir, I don’t wanna be the reason for her anger dan Allah kada kaje please please kaji kaga ni nama dena kukan I’m not sad wlh, dan Allah karufamin asiri” tashiga share fuskanta da gyalen tana kallon Munir da red eyes nata na kuka, Munir yamata wani kallo kaman ya maketa yana hararanta sai kawai tafashe da dariyan dole dan kawai ya yarda dan tasan halinshi tace “haba Nana boyfriend” zaro idanu Munir yayi yahaderai tareda fizge hannunshi yace “kika kara hadani da wata Nana that small girl ranki zai baci” hararanshi Asmeey tayi ganin yanda Allah yama Munir shegen son girma tace “kaganta wani jin kanka kake eh Dr Munir kana wani iyayi da kankamba I know u love her” yowa kanta Munir yayi dasauri tawani kurma ihu na tsoro. “Babaa!” Ta kwala kara, chak Munir ya tsaya ta kwashe da dariyan tsokana taredamai gwalo tace “Nana’s boyfriend” tawuce flat nasu da sauri tana tafiya tana waigowa dan karya biyota kadakai kawai yayi yakoma cikin motan ya zauna yace “Yaya yafara aiki?” Gently Hamad dake screwing headphone da Munir yabashi yatayashi dubawa cus ya daina aiki ya kalleshi saikuma ya maida kanshi kasa baice komiba, dan fuzar da iska Munir yayi kadan yace “Ya Hamadi Gwaggo never tells you no dan Allah zaka iya gayamata tasa masu lallen nan suma Ya Asmeey?” Dan dago kai Hamad yayi yamai wani kallo dayasa Munir ya sassauta murya yace “pleseeeee Ya Hamadi Mom ce tahanata yin lalle wai sabida law school dazata bayan salla and is not really immediately bayan salla fa sometimes it takes weeks karfin list din yafito but tahanata yi, kowa yayi lalle is only my sister that is looking different” yasake dan shiru yana kallon Ya Hamad dake abinda yakeyi cikeda damuwa yace “kaga Ya Asmeey always got my back, always protecting me I feel like a bad brother nakasa doing anything for her” yayi maganan yana kallon Hamadi dayayi kaman badashi yake magana ba daidai yagama komi yadauki wayanshi ya kunna yayi connecting yasa Qur’ani ganin yayi yasa yamikamai anatse yace “take” karba Munir yayi yana murmushi sosai yace “wow thank you so much Ya Hamadi harzan wurgar fa nace tunda zakuzo salla bari na barshi tukunna i know yanda kasan this stuff” bude kofa Hamadi yayi yafita daga motan yawuce flat nasu Munir yabishi da kallo yanda yake tafiya ahankali you can never understand Ya Hamadi, he hardly talk, baya wasa da yara, but then he’s the most intelligent person daya taba sani arayuwanshi, Ya Hamad yasan computer kaman maye, and he knows anything wayan wuta, anything technology wlh yasani ya iya he can fix anything, silent genius ne. Flat dinsu ya shiga zuwa dakinsu da babu kowa, ko ina Hameed yayi oho?Bayi yafada yayi wanka yafito daure da towel yawuce yasa key a kofan sannan yabude akwatinshi kayanshi yaciro komi yasa a wardrobe Hameed yasamai duk abinda yake bukata ya shirya tsaf sannan yaciro laptop dinshi daga bagpack ya kunna yana zama kan gado saikuma yayi jim kafin yakalli wayanshi dake gefenshi sai kawai yadaga wayan……. Gwaggo na zaune anan falo tana surutu duk wani abinda yafaru a Kano yaran nan take bama labarinshi ko gajiya batayi ba, yaran suma sun zagayeta anajin dadin labari harda na takwaran da aka mata wayanta yahau ringing da sauri ta taba wayar dake cikin lalita akasan zanin tace “yooo wa yake kirana ko su Munarin Kauye ne”? Warware zaninta tashiga yi tasa hannu taciro wayan daga lalita takalli screen din kaman ta iya karatu tace “tohh wannan lamba ce batada suna” ta danna dauka takai wayan kunnenta murya ciki ciki akufule Hamad yace “kuma karki kira sunana! Yarinyar chan batai lalleba” yana maganan ya katse wayan Gwaggo tace “wace yarinyar? Ham….” Saikuma tai shiru da sauri tuna yace karta kira sunansa, tashiga bin yaran da kallo daya bayan daya tana sauke wayan daga kunnenta kawai tazare idanun ta mike tace “duk kutashi kuzo ku nunamin kunshin sallan ku daya bayan daya”faduwa gaban Asmeey yayi dake zaune kusa da Ramla cus tasan Gwaggo taga batai lalle ba she will cause trouble tai maza ta mike zata wuce Gwaggo tace “zonan kafin na cimiki mutunci Asama” tsayawa Asmeey tayi tana boye hannunta abaya, Gwaggo tace “mehaka naga kafafunki farare tasss kaman na zabiya! Jibi yara anan ku takwas gasu Hajar hudu ku shabiyu, maza sunsha aski mata sunsha lalli banda ke sai kace yar riko” har lokacin Asmeey taki nuna hannunta ahankali tace “Gwaggo makaranta zani bayan salla saisa an hana lalli a makarantar” dakuwa Gwaggo tamata ta daga murya tace “kinci mai garinku da makaranta yo ko kirista suna zuwa hutun salla balle ke musulma ke baki gajiya da boko sai kace uwarki iyyee? Kinada tabbacin zakiga sallan badi? Babban salla guda hannayenki da kafafu fari sol kaman aljana ina masu lallen wuce ki kiramin su Amina idan basu tafi ba, ke ko sun tafi sai an kirasu” wucewa Amina tayi da gudu ta tafi, Asmeey gabanta na faduwa dumdumdum tace “Gwaggo dan Allah ni bazanyiba ni ki barni” tai stairs da gudu Gwaggo tace “kiramin ubanku Munir” dan shima Munir na falon, tsayawa Asmeey tayi tajuyo da sauri ta kalli Munir daidai yawuce abinshi da sauri Hamda ta sauko tazo wajen zatai magana Baba ya shigo ga Amina da masu lalle da kitso sun shigo falon suma, Gwaggo na daga murya sosai tace “Muhammadu Sani tun kana dan kankani kataba ganin salla tazo da bansa kunshi ba?” Dasauri Baba yace “a’a Gwaggo” cikin fada Gwaggo tace “toh wani dalili zaisa kaf cikin yaran gidan nan Asama ce mara kunshi sai kace wata bare wannan mukai baki ai sai ace mun tsaneta ne ba yar gidan bace” kallon Asmeey Baba yayi da sauri ta sauke kanta kasa zaiyi magana sukaji muryan Mom cikin harshen turenci tace “you know she’s going to Law school bayan salla Alhaji that’s why”kafin Baba yayi magana Gwaggo tace “to yar boko ke duk inda kike saikin nuna mutanen dake wajen basusan komiba kene kikasan komi, ke ba abin kunya bane yarki ta fita daban cikin sauran yara? Komi boki komi boko da boko za’a lahira dazaki hana yarinya yin adon salla? Yin ado da salla sunna ce danko Annabi tsira cewa yayi ranan salla musa kaya mafi kyawu muyi ado mai kyau amman ina zakisan haka sai ilimin yahadu kika sani bana arabi” Mom zatai magana strictly Baba yadaga mata hannu hakan yasa tai shiru, cikeda girmamawa Baba yakalli Gwaggo dake huci yace “Gwaggo kiyikuri yanzu za’a mata” cikeda rigima Gwaggo tace “ai gamasu lallin nan na aika Amina taje ta kirasu anan gabana za’a mata kafin yar boko ta zaga tahanata yi kekuma zauna da shegun idanunta masu kama dana jemage” tanuna Asmeey da atsorace tadan dago kanta ta kallo Mom data mata wani mugun kallo, da sauri ta sauke kanta kasa Mom tajuya daga sama zata koma daki Gwaggo tace “saukowa zakiyi kije kema kisa hannu abayan gida ayi aiki ba daraja kikafi sauran dake wajen ba bakina kima kika fisu ba dan sunfimini ke so dubu” wani kallo Mom tama Gwaggo saikuma ta kalli Baba daya mata kallon baison rigima tayi abinda tace yajuya yafita itama Mom din badan taso ba ta sauko tawuce tafita, Gwaggo tabita da harara, ran Munir fess kaman ya rungume Gwaggo dan dadi aka shiga yima Asmeey lallen dake cikin tsananin tashin hankali duktai zuru zuru sauran yan uwanta harda Munir suka zagayeta suna kallon yanda ake lallen Munir harda matsar da kanninsa baya karsu gwaljema yayarsa lalle, kana ganin Asmeey kasan hankalinta baya jikinta Gwaggo ta buga tsaki tace “Allah yahadaku da jarababbiyan uwa ga yara har yara Allah yabata inba haukan bama yarinya haka kaman Asama wani yahanata yin lalle ba abun tai fada dashi bane amman ita ke hanawa da kanta yarinya kyakkyawa haka son kowa kin wanda yarasa” itadai Asmeey ta saukar da kanta kasa. After magrib aka gama lallen gabaki daya both baki da ja, ta kwanta anan kan doguwan kujera dan ba halin salla suna kallon film tareda sauran yaran, Gwaggo kuma ta fita tsakar gida wajen su Baba tana magana dasu ganin an gama lallen, bude kofa akayi aka shigo Ya Mustapa ne da sauri yaran sukai wajenshi suna gaidashi Ramla ya kalla yace “come here Ramla” dasauri Ramla ta taso taje wajen kofa dayake, jakunkunan ice cream din hannunshi yabata yace “gashi ki raba muku” gyadamai kai tayi dukansu sukai godiya yawuce yafita Ramla tashiga rabon ice cream din na supreme manyan robobi tanaba kowa nasa, tazo gaban Asmeey hakan yasa Asmeey tace “kibani strawberry” Ramla tarike last strawberry tace “nawane shi vanilla zan baki” dasauri Asmeey tace “ai kafin ki dauki strawberry nace miki ni shinakeso” Ramla tace “to baza’a bayar ba” kallon Ramla Asmeey tayi cikin ido sai kawai ta dauke kai tace “ki hada duka ki shanye banso” ran Ramla baci yayi jin abinda Asmeey tace, cikeda masifa tace “ohh kullum akaina ne kikeda bakin rashin kunya ko”? Dasauri Nana tace “Ya Ramla kiyakuri” tashi zaune Asmeey tayi daga kwancen ta harari Nana tace “wayace kisa baki? Da ke akayi?” Akufule Ramla tace “wai ba Baba yace kidenamin rashin kunya ba? Dani kike magana kaman kinyi da sa’an ki? You’re a rude stubborn girl wawiya kawai” ran Asmeey yabaci jin zagin da Ramla tamata tace “ni dai ba wawiya bace” hannu Ramla tasa ta dungure mata kai saida Asmeey takoma baya tsabagen yanda Ramla ta dunguruta tace “okay nine wawiyan kenan? Ki kara magana kiga wlh sai kinsha mari akan kumatun nan naki daya saba shan mari”dasauri Yusra tai wajen kofa tabude tafice ganin Ya Ramla da Ya Asmeey na chachan baki akan ice cream…. Ganin bataga su Baba ba yasa tai wajen motoci inda taga Ya Mustapa tsaye tareda Ya Hamad tai wajensu tana haki tace “Yaya ga Ya Ramla chan da Ya Asmeey suna fada a falo sabida ice cream” “because of ice cream”? Ya Mustapa ya maimaita, gyadamai kai tayi tana zaro idanun gulma tace “she prefers strawberry itakuma Ramla tace vanilla zata bata tace bataso shine Ya Ramla tashiga dungure mata kai tace mata wawiya wai zata mareta akan kumatunta da suka saba shan mari” Ya Mustapa yace “wuce muje” binta yayi zai wuce daidai nan sai ga Mom data zagayo daga backyard tashiga flat din hakan yasa Ya Mustapa yace “ga Mom chan tafi kawai bari basai naje ba” wucewa yayi yakoma inda Hamad yake tsaye dan shi baiyi motsi ba daman. Mom na shiga dakin tagansu suna chachan baki hade giran sama da kasa tayi yaran kowa yayi tsit kaman anga dodanniya gaban kowa na faduwa harda ita Ramlan ganin Mom, maida kofan Mom tayi tarufe takaraso falon yaran kowa na komawa baya, Ramla ta kalla strictly tace “what is going on here”? Ice cream na hannunta Ramla ta nuna mata tace “Mom Ya Mustapah ne yazo yabani ice cream yace narabamana, kingani nabama koya shine nazo naba Asmeey this Vanillah agaban kowa agaban yaran nan tahaumin rashin kunya harda cemin wawiya wai kawai dan ban bata strawberry b……” Kafin takarasa maganan Asmesy ta tari numfashinta muryanta na rawa tace “wlh Mom karya takemin itane tafara cemin wawiy……..” tassssssss! Mom ta dauke Asmeey da lafiyayyen mari da saida ta ijiye kafafunta na lallen kunshi akasa saman tiles hands nata suka kwalbe ajikin chair, ita

Chapter 8 of 56