Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taduka ta haifo, saita daura hannunta saman cikinta sannan takalli Ya Mustapa tace “taci abinci Doctor?” Girgixama Mamie kai Ya Mustapa yayi ahankali yace “tube za’a samata kokuma asamata nutritional drip cus the way she’s now she can’t eat da kanta or take any magana da kanta saidai ta IV or tube” Shiru Mamie tayi tajuyo takalli Asmeey ahankali tace “azo asamata yarinyana najin yunwa Mustapa, ba abinci a cikin nan nata” tajuyo ta shafa fuskan Asmeey cikeda so tace “kikaji sauki only abincin dakikeso za’a dinga dafawa kinji? Just get well soon Ma’u na kinji? N….na….na…..yi……” muryan Mamie yafara rawa itama takasa daurewa Ya Mustapa ya girgiza mata kai alamun no, da kyar Mamie ta saita kanta tace “nayi alkawari bazanyi kuka ba, amman idan bakiji sauki ba zantayi, get well soon Asmeey natafi dake na kula dake dakaina kinji”? Tayi shiru tana kallonta Abba yadan dafa kafadan Baba dake kallon Asmeey jikinsa babu kwari yakasa komi, motsi hannayen Asmeey sukayi dasauri Hamad ya matso kusa da Mamie yace “Husnahhh Yaya her hand just move” wani irin mikewa hannayen Asmeey sukayi saikuma tashiga dunkule yatsunta kaman wacce zata dawo gurguwa tafara wani irin motsi tana jiniya irin na mahaukata marasa magana yawu na fitowa bakinta tana wani irin nishi tana fotoda harshe tana runtse idanunta tana wani kalan complex ihu. “Uhnnnnnnn……unnnnnnnn…..”Mamie ta tashi daga gadon da sauri tarude, Mustapa ya danna alerm na kiran doctors Hamad yarude yace “Asmeey! Asmeey! Husnah menene!” Kai Asmeey batasan ma metakeyi ba Baba yayi baya zai fadi Abba yarikesa daidai doctors guda biyu na zuwa, daya psychiatrist dayan gynecologist dinta tsoho, da nurses biyu sukace afita afita har Hamad suka kora aka taru akan Asmeey kai Mamie tayi kuka ta gode Allah sukai charko charko agaban dakin. Saida suka bata 30min dakin sannan suka fito suka wuce while Ya Mustapa yazo wajen jikinsa ba kwari yakallesu, Hamad yace “Yaya what happened to matana?” Dan ijiyan zuciya yasauke yamikama Hamad wata paper yace “her doctor yayi referring nata to psychiatric hospital, wat happened to her now is experiencing na pains datayi she’s feeling kaman yanzu ake mata komi, and she will be having the episodes every here and there, she needs to be transferred to psychiatric hospital” Baba daya rude yace “menene shi psychiatric hospital? Shi asibitin nan fa”? Anatse Munir yace “asibitin mahaukata ne psychiatric hospital, Baba Yaya baiso yafadi mukune but ciwon hauka yadan kama Asmeey! Naga file nata an rubuta type 2 depression dakuma wani abu da bangani da kyau ba! This hospital basu da capacity kula da patient dakeda matsalan kwakwalwa saisa akaece akaita asibitin mahaukata inda zataga physician da nurses dasuka kware akan abinda ke damunta!” Kowa kallon Munir yake har Ya Mustapa cus he just explained abinda he couldn’t bring kansa to explain to his family, wani abu Hamad ya hadiye awuya anatse yace “matana bata haukace ba! She’s just sick!” Kowa ya kallesa gwanin ban tausayi, Baba duk karfin halinsa ya fashe da kuka yana shafa kirji yace “Asma’u hauka? Innalillahi! y’ata bata haukace ba wlh! Za’a mata sauka zataji sauki, wlh bata haukace ba, Munir kada ka kara kirama yar uwarka hauka!” Ijiyan zuciya Hamad ya sauke idanunsa sunyi jajir yakalli Ya Mustapa yace “how many days will it take me nasamanwa Mamie visa?” Kallonsa Mustapa yayi baice komiba, dasauri Ya Aya tace “I have Ya Hamad na garinku!” Shiru Hamad yayi ya fuzar da iska yace “Ya Mustapa I will fly my wife to Washington DC, Aya talk to your husband idan zai yarda kibimu, Hameed contact those your people muji yanda Mamie zata sami express visa na raka mara lafiya, I have medical insurance for me and my family a DC, ko babu ma I will put my last kobo na samawa matana lafiya, I won’t stay still and do nothing! I am her husband and I will call the shot! Asmeey bazataje asibitin mahaukatan Nigeria ba! We are going to DC!” Yakalli Hameed yace “go home bring my system to me we are traveling this week at max!” Baba kallon Hamad kawai yake yanajin wani natsuwa aransa, Asmeey tasami miji dayake tsaye akanta wlh! Alhamdulillah he made the right choice for Asmeey, wato kap rayuwan yarinyar nan d only Allah datasamu mai kyau cikinsa is Hamadi!. EPISODE 1️⃣1️⃣0️⃣ Cikin 5days aka samawa Mamie Visa kudi ke magana alaji! And Hamad spend it, Aya mijinta ya yarda cus Mamie tadan tsufa ita kadai the work will be too much for her, Ya Aysha tadauki yar Aya ta wuce da ita Abuja. Business class Hamad yamusu booking da special care na patient shiyakema Asmeey komi ambulance yakaisu airport, special care services daya biya handle check in nasu da kaisu jirgi aka kwantar da Asmeey agado, aka mata fixing duk wani medical abu datake bukata onboard, Hamad na kusada ita while Mamie da Aya na seat nasu jirginsu ya daga, for those 14hrs runtse idanu Hamad baiyiba yanakan Asmeey pampers ake samata, ya chanza mata pampers yana share mata yawu yakama hannunta yarike yana kallonta, wlh yanzu ne ma yakeson Asmeey dan soyayyan dayake mata yanzu yafi nada yawa, like wani irin mugun kaunarta Allah ke dauramai this days kaman zai cinyeta. Daga baya ya kwantar da kansa jikin gadonta yana rikeda hannunta bacci yakamasa koda Mamie tazo dubasu taga yayi bacci yabata tausayi tadauki bargo tarufa masa cus Asmeey arufe take ta tsaya tana kallon Asmeey she’s sleeping tana addu’a kar Allah yabar yarinyar nan ahaka Allah ya warkar ita Da asuba jirginsu ya sauka akwai sanyi sosai sweater yasama Asmeey kafin kowa yafita special services dinsu akazo aka fitarda su aka sakasu a ambulance direct sai asibitin da Hamad yayi komi dasu a online sunada progress report da medical history na Asmeey da komi sharp sharp akasa Asmeey on admission akai komi da komi suna bari a kwana but just one person dakin Asmeey ita kadai, komi akwai, hospital ne babban gaske they have psychiatric care and support unit a ward din kuma Asmeey take, nan da nan akai plugging nata to so many things, ga name tag nata a hannu an samata uniform farare masu bala’in yau, Aya tace “yaje gida da Mamie tahuta” baiyi musu ba yariga yakira driver sa yana hospital din sukaje suka shiga mota shida Mamie suka tafi gida, hannun Mamie yarike suka shiga elevator har zuwa floor nasa suka wuce gaban dakinsa yabude ko’ina a gyare Mamie tabi gidan da kallo tace “nanne gidanka?” Gyadama Mamie kai yayi Mamie tai murmushi tace “Alhamdulillah” wucewa sukayi two bedroom ne yakaita duka dakunan kafin cikeda girmamawa da bawa mahaifiya daraja yace “wani daki kikeso Mamie”? Dan murmushi Mamie tayi tanuna laptop room nasa tace “nan nakeso kai ka zauna anaku Asmeey zataji sauki soon tare zakuyi zamanku” sunnar dakai yayi yashiga dakin dudda agyare yake tsaf but saiya shiga kakkabe kakkabe Mamie tace “laaaaa me kakeyi Hamadi common jeka huta ruwa zan watsa namana girki shigo da akwatunan mu” Gyadama Mamie kai yayi yafice itakuma tashiga bayi ta tsaya tana kallon komi dantane yasami daukaka haka saida ya shigo taleko tace “zoka nunamin Hamadi” shigowa bayin yayi yanuna mata komi yafice ya kwantar da akwayinta yabude mata komi yaciro kayanta ta jeramata wardrobe kayan abincin ya ijiye akasa yadaga akatin yasa a Sam sannan yafice yaje dakin yayi salla a jirgi saiya zauna yayi shiru, yabar Ya Aya da wayansa dakeda line dinsa na garin nan hakan yasa yakira wayan da landline na dakinsa da sauri tadaga tace “Ya Hamadi!” Murya chan kasa yace “how is she?” Murmushi kadan tayi she just loves yanda Ya Hamadi ke son kanwarsu he’s not even hiding it anymore yanzu oo baya iya boyewa, tace “she’s fine asibitin nada kyau doctors daban daban keta zuwa dubata yanzu bakinta ake dubawa, in sha Allah sauki yakusan samuwa” ijiyan zuciya yasauke kadan yace “I will be back soon please don’t leave her site, there’s Qur’an awayana ki kunna mata, it makes her sleep easily” ahankali Ya Aya tace “tom zan kunna yanzu” ya katse wayan. Nan da nan Mamie tahada simple porridge na dankalin turawa ta debo a plate tazo dakin knocking tayi shiru hakan yasa tadan bude dakin kadan yana zaune gaban gado but bacci ya kwashesa Hamad is exhausted baya bacci kullum yana cikin browsing condition na Asmeey online, koda yaushe yanakan kula da ita he’s not letting kowa do something for her wucewa gaban gadon tayi ta zauna ahankali firgigit yabude idanu, kallonta yayi saiyadan saukar da kansa kasa yace “sannu da aiki Mamie” abincin Mamie ta debo a spoon anatse tace “yaushe ne zaka koma aiki?” Ahankali yace “next week Monday” spoon din takai bakinsa ahankali yabude baki ya karba yasauke kansa kasa anatse Mamie tace “while Asmeey is recovering kaima u need to take care of yourself kaga yanda karame, kwata kwata bakacin abinci, baka bacci, Hamadi Asmeey zataji sauki trust me! Kallan addu’o’i da rokon Allah da sauka da akasa anayi kan yarinyar nan gakuma namu addu’an she will get better soon kawai ta azabtu ne, but zata warke and she will be stronger than ever trust me, but you have to be strong, haihuwa kuma Allah ke bayarwa daman, zai kara baku, put yourself together kafara shirin komawa aiki kaji”? Gyadama Mamie kai yayi idanunsa na taruwa da hawaye kafin yakai bayan hannu da sauri ya goge yacigaba da basa tass ya cinye sukai waya da yan gida sannan tawuce tai parking abincin dazata kaima Aya tadawo dakin saitaga wani wahalallen bacci ya kwashesa a zaune yake baccin wlh, ahankali tazo tadan gyara masa kwanciya gently ya kwanta taja bargo ta rufamasa tazauna bakin gadon tana kallonsa saita daga hannu sama tace “Ya Allah ka tausayama this children Asma’u da Hamadi don rahamar ka kabasu ikon cin jarabawan nan! Ya Allah lafiya na hannunka, kabawa yarinyar nan dabama asan meke mata ciwo ba lafiya Asmeey ba uhm ba uhm’um, Ya Allah help this girl please!” . EPISODE 1️⃣1️⃣1️⃣ *** BAUCHI Har karfe hudun rana Mom na zaune agidan ita kadai ko kukan kaza bataji balle motsin mutum in that big huge house, ga yunwa ya isheta, ga zazzabi tanaji, wayanta ta dauka tai dialing number Gambo yar aiki amman baya shiga takira yafi sau goma sai chan ga Gambo na kiranta cikin muryanta na yan kauye tace “Hello Hajiya kina jina kauyenmu ba network naga kinmin fulashi, nazo kauyen mu mahaifiyata ba lafiya saita warke zan dawo, ina saman dutse yanzu hak……” katse wayan Mom tayi taja dogon tsaki batasan zata sanar da ita kafin tai tafiya ba kodan taga bata gari, tashi tayi saikuma tai dialing number Fawaz but busy yake nuna mata kaman yayi blocking nata da wayan na shiga daukane bayayi but this time he blocked her, tashi tayi ahankali tafada bayi wanka tayi tafito taciro abaya tasaka tadauki handbag da key motarta tafito compound wani irin ba dadi gidan ke mata yanda babu kowa ciki, tawuce wajen motarta tayi tayi tayi ta kunna yaki kaman battery yamutu makaniken ta takira yace “gashinan zuwa” takoma ta zauna anan compound within 20min sai gasa yazo ya duba motan yace “Hajiya sai taje office mun mata gyara fa dole saina tafi dashi” ijiyan zuciya Mom ta sauke taso tai amfani dashi tace “to zan maka transfer” bonnet yabude yayi tabe tabe motar ta tashi yabude gate yafice yasauko yarufe gate, Mom na zaune a compound din zuciyanta baya mata dadi ko kadan kusan 20min wayanta yahau ringing dasauri takalli screen din makaniken ne dauka tayi tace “Idris yaya”? Hayaniya taji wani yace “gani nayi an rubuta Hajiya motar ta kama da wuta fa anan junction na layin zuma!” Faduwa gaban Mom yayi junction na anguwansu kenan fa dasauri tamike tayi gate tace “me mene?” Bude gate tayi tafito yace “gashinan an cirosa kafansa ya kone amman yana lafiya motar ce dai naci da wuta kan titi” daganan kofar gida Mom ta hango motarta na kamawa da wuta akan titinsu ga jama’a faduwa wayan yayi daga hannunta kirjinta na bugawa bamatasan mezatayiba, da kyar ta duka tadauki wayan tashiga tafiya har zuwa junction kawai ta tsaya turus tana kallon ikon Allah, sosai motanta keci da wuta gabanta sai bugawa yake ita kadai Fawaz yarabu da ita, kare ya cijeta, an barmata gidan ita kadai, yanzu motarta yakama da wuta fushi Allah yake da ita? Amman ai ba ita ta kashe Asmeey ba kuma Allah yasani, tasan yes tai wishing yarinyar ta rasu but da ranta sukabar dakin ai, natural death tayi ai, alhaki ne yafara kamata? Kurmus tana tsaye tana kallo motanta ya cinye ana kashewa baya kasuwa saida ya rage langalangan mota kadai sannan ta mutu Mom kawai ta juya tana tafiya da kyar takoma gida ta shiga ta zauna she needs a car but tanadama kudin siya account nata tabude tanada 2.5 a current bank nata, tanada 1m a savings account nata, sai pension nata na stanbic ibtc bank tanada about 9M. Ta kashe kudi zuwa kanon nan hotel da car rent da sauransu, she needs a car ga promotion za’a mata yanzu how is she going to get to work tommorow batajin bolt ko uber na aiki a Bauchi ba tashi tayi takoma daki tadebi ruwan zafi a water dispenser ta jefa Lipton tasha tashi tayi takoma watsa maganinta a baki tai salla ta zauna ahaka har 10 nadare, daga baya ta daure taje baya ta watso ruwa ta sa kayan bacci tazo ta kwanta akan gado for the first time in her life takasa kashe wuta tai shiru, mesa yaranta babu wanda yakirata and she know by now kowa yasan meya faru metayi? Aya bata kirata ba, Aysha haka, Munir haka, Yayanta Alhaji Mahmoud haka, koda su yaran suna tsoro da shakkan confronting nata Yaya fa? Mesa bai mata magana ba ai baya tsoronta shi duk ta damu yanda babu wanda ya kulata. Ahaka bacci yayi awon gaba da ita…… Inyaaaaaaa! Inyaaaaa! Inyaaaaaa! Taji kukan jariri da muryansa da keda bala’in zaki kaman zai yaga mata kunne akanta, gently tashiga bude idanu, duhu tagani ko’ina yayi baki kirin chan saiga wata yar jaririya cikin farin kyalle asama hanging jaririyan tadago kanta idanunta jajir kaman jini takalleta tace “Inyaaaaaa……inyaaaaaaaa” tana kallonta sai taga jaririyan tabude baki harshenta yakoma kaman maciji yayi tsawo daga saman yazo wajenta zai kama wuyanta wani wawan ihu Mom tayi ta tashi zaune daga bacci ahaukace. “Innalillahi wayyo Allah na! Na shiga uku” tashiga tari sosai tana shafa wuyanta da fuskanta tana kallon dakin da ko’ina amman bakomi taji kafanta na zugi, dasauri takalli kafan saitaga bandage din ya futa wajen yazama ciwo sosai ga jini kaman an sosa hannunta ta kalla saitaga jini alamun ita ta sosa maybe cikin bacci dasauri tashiga sauka daga gado tawuce bayi ta kunna tap gaban wash hand basin ta wanke hannunta tadago kanta takalli madubi kawai saitaga Asmeey tsaye abayanta da fararen kaya tana kallonta ihuuuu Mom tayi ta runtse idanu. “Wayyoooo Allah na nashiga uku Innalillahi! Auzubillahi! Bismillahi Rahmani Raheem” tabude idanun ahankali a tsorace ta kalli madubin babu kowa dasauri tajuyo takalli bayanta babu kowa jikinta wani irin rawa yake mata tsoro har cikin zuciyanta, bude kofan tayi tafito tawuce saman kujera tadauki charbinta na wajen tadawo gado ta zauna tana jan charbin tana. “Astagfurullahi lazi! Astagfurullah wa’atubuilaika!” Sai juye juye take tana kallon dakin, baccin dabai kara daukanta kenan ba ahaka gari yawaye bayinma tsoron shiga taji abude tabar kofan tayi wanka tafito ta shirya tabude drawer tacire duka gold nata tanaso ta sayar ta hada kudi tasai mota. EPISODE 1️⃣1️⃣2️⃣ Batason karamin mota akwai raini batasan yazatayi without a car ba cus is a necessity! Zuba gwalagwalan da akalla ta saida zasu iyakai 50M ajaka ta shirya tsaf tafito ga anguwansu ba’a samu keke ko machine tashiga takawa akasa sai kallonta ake she looks so posh to be walking akafanta kunya kaman zata nutse kasa Tawuce junction bamata ga body motarta ba kawai ta tare keke tashiga tace kotu. Court taje yau take especting official appointment letter na komawanta chief judge hartaga yan cases nata around 2 shiru babu wani letter karshe dai takasa daurewa tawuce office na wani superior haka datake mutunci dashi yace “Hajiya Mrs Turaki” murmushi tayi ta zauna tace “yanaji shiru har yanzu banga letter ba” kofansa ya kalla saikuma yatashi yawuce Mom yadan fita sannan yadawo yazo dab da ita yaduko wajen kunnenta cikin whispering yace “maybe because u are out of town saisa bakiji news ba Muntari Surbajo yabi ta karkshi fa” dasauri Mom ta kallesa ranta na mugun baci, ya gyadamata kai yace “the guy get people on top he work am shi za’a bawa I heard it from a trusted source zakiga email yau, tun rannan namiki kiran duniya sabida kema u should come do your thing but wayanki baya shiga na village u go wat happen to your line ne?” Kasa magana Mom tayi sabida bacinrai tace “ta ina yayi passing requirement na zama chief judge wannan ai yaudara ne da karya” mutumin yace “ahhh u know our work well forget that thing see an riga an basa saidai kiyakuri kawai check ur email sef”dasauri Mom tabude wayanta tashiga email aiko ga message an mata waita yakuri akwai wani basic requirement da sukeso da batada shi so sabida haka an bama a more befitting candidate than her the position of chief judge, Mom saida ta jefar da wayanta akasa tana wani huci kaman macijiya mutumin yace “ahhh calm down Mrs Saraki! Calm down I know it’s painful sunga mace ne ke” yadauki wayan yabata karba tayi kawai tamike tace “sai anjima” tafita bata tabaji ranta yabaci kaman haka ba kuma da an sameta waya datayi yan dabarunta da kyar ta tare keke ta shiga tafada inda zai kaita kasuwa zuwa tayi ta saida zinaren tafito tasake shiga wani keke ga ledan kudi a hannunta sai taka tsantsan take dashi, suna ahaka a keken wasu maza suka tare keken Mai keken na kokarin tsayawa Mom tace “drop na daukeka f……” tsayawa taga yayi batasan meya faruba tadaiga daya daga cikin passenger dasuka tare keken ya hura mata hoda a fuska taji daya yana cewa Oga yace “tasaka jan leshi da abaya wlh itac…..” daganan bata sake jin komiba. Bude idanu tashigayi kwance taganta akaman police station bayan counter akasa da sauri ta zabura ta tashi macen dake wajen tace “ahh Mrs Saraki kin tashi” dasauri Mom tace “Meya sameni Matter?” Kallonta Matter tayi dan sunsan Mom tace “wasu yan Fulani suka kawoki wai an ganki wasu yan keke napep sun wurgoki a sume”? Arude Mom tace “ina wani bakin leda haka da handbag dina?” Dasauri matter tace “ke kadai ce har agogon da dankunne sun cire miki ke harda takalmi ma just ke kadai aka kawo but we are investigating it” faduwa gaban Mom yashiga yi tace “Innalillahi my gold money! Wayyyooo I need to go to the bank nai blocking account dina please matter bani takalmi da aron 1k” Mom nabasu cin hanci so matter batai musu ba tabata wani slippers da 1k Mom ta karba tafito aguje mata na binta da kallon tausayi Mom tawuce tahau machine ta tafi gt kafin tai blocking account tace aduba mata wlh an cire duka kudin account dinta tass da atm card nata balance dinta 0 kuma tanada 2m, suma Mom takusan yi aka taru akanta da kyar ta ita bayani akace ta POs suka cire kudin menene menene da kyar Mom na layi ta tafi UBA shima an kwashe yar 1m dinta biyar bata magani yanzu, ba waya bakomi yan zobunan hannunta da agogo da takalmjnta mai tsada an kwashe ina zata fara samun wani kudi da zamatasai waya? “Innalillahi wa innailaihi raji’un!” Daga jiya zuwa yau Allah is just stripper her off all her privileges one after another! Jama’a muji tsoron Allah! Billahillazi kome kikeda shi bazai hana Allah ya karbe komiba in a second dan shine yabaki! Leave life carefully and avoid cutar dawani, Allah na yafe laifin dakamai but baya yafe laifin dakama wani har sai wanin ya yafemaka. Wait did u all see how Mom lost everything in matter of hours??? Muje zuwa! EPISODE 1️⃣1️⃣3️⃣ Hamad yayi baccin daya dade baiyi kalansa ba bini bini Mamie na shigowa ta dubasa tasan harda jetlag, sai wajajen 2 na rana yatashi afirgice agogo ya kalla sannan ya mike da gudu yafada bayi yafito ya shirya cikin kananun kaya yasaka jacket da p-cap yafesa turare yafito zaune yaga Mamie afalo tahada komi dazasukai hospital tana kallon tv data kunna itama ta sanya katon jacket tayi kyau, sauke kansa kasa yayi da sauri tace “muje toh tunda ka shirya” gyadamata kai yayi yataho yadauki abubuwan suka wuce kofa suka fito driver yajasu sai hospital. Ya Aya na zaune da ita adakin tayi wanka ta chanza kaya taci abinci dan she request for food an kawo mata ga Asmeey na ayanda suka kawota ba change ga Al Qur’ani na playing Mamie tace “kinci abinci?” Gyadama Mamie kai tayi tace “eh nace chicken soup” ijiye komi Hamad yayi yadan juyo ya kallesu ganin suna hiransu saiya zauna bakin gadon yasa hannunsa ta karkashin bargon da aka rufa mata yakama hannunta yarike yana kallon fuskanta yakai dayan hannun yana share mata lips yayi shiru yana kallonta bayako kyafta idanu daga Mamie har Ya Aya na kallonsa. Yana ahaka aka bude kofa wata baturiyan Dr yace “Dr wanna see you Mr Hamad Hussain” gyadamata kai yayi yasaki hannun Asmeey yatashi daga gadon yaduko yasake share mata baki yadan tsaya yana kallonta kaman karya barta sannan yajuya yafice Ya Aya takalli Mamie, kasa daurewa tayi tace “Mamie wlh Ya Hamad yana son Asmeey, in all of this abubuwan dake faruwa soyayyan dayakema Asmeey kawai ke kwantar min da hankali” murmushin manya Mamie tayi tanuna Asmeey tace “kinga mara kunyan yarinyar nan nawa itama haka takeson mijinta” murmushi Ya Aya tayi saikuma hawaye suka cicciko idanunta Mamie tace “kin manta abinda aka fadi ko?” Dan huci Ya Aya tayi takai bayan hannunta ta goge fuskanta tass sannan ta rage murya tace “Mamie har abada wlh banjin zan iya yafewa Mom ba! Mamie na tsani Mom sosai! I hate her with passion, she did all of this to this girl sabida wani mahaukacin dakikin dan iskan yaro!” Tai shiru zuciyanta na tafarfasa cus Munir yagaya musu komi saikuma Aya tafashe da kuka tace “Mamie me Mom zatayi da mutumin dayaso batamin rayuwa? Dayaya nai escaping Allah ya kubutar dani? Mamie Fawaz nada bad history tundaga kan yimi yan aikinsu ciki, shi kawai iskanci yasa agaba kowa yasani, how could she have something with him and still tanason hadasa da Asmeey, kishi take da Asmeey yarta? Dahar tanason kashe yarinyar? Such type of woman is not worthy of being my mother!” Aya tai maganan ahankali murya chan kasa tace “growing up matar is always harsh batason yara na mata gum body, she’s strict tanaso muyi karatu, but during Asmeey tsanan was too much! Is just too much ashe is all because of that evil man! Ai gata gashi bazata kara ganina ba arayuwanta, saidai Aysha which itama nasan ta yafe Mom, Munir kam kawai tsoron Allah ne da yaron nan zai iya harbeta yasami dama” Aya tai huci zata kara magana kawai Mamie saita rungumeta tana patting bayanta cikeda so tace “ya isa Aya! Just forget everything! Let’s focus on Asmeey kinji”. EPISODE 1️⃣1️⃣4️⃣ Office na Doctor Hamad ya shiga Dr ya nunamai kujera ya zauna, cikeda girmamawa Dr yatashi ya kunna wata yar TV na office din yatashi wasu hotuna haka kaman na xray ko scan suka bayyana a screen din Dr yace “this is your wife’s cervix, this are ovaries, this is her fallopian tube, and this is her vagina” yakalli Hamad dake kallon screen din sosai, anatse Dr yace “everything seems okay, all the organs are fine no any damage” ahankali Hamad yace “can she get pregnant again Dr?” Murmushi Doctor yama Hamad yace “absolutely yes! I must say whoever did the evacuation must be an experienced Doctor, and he was careful cus that’s the only explanation for not having any damage organs” dan ijiyan zuciya Hamad ya sauke ahankali yace “Alhamdulillah” saikuma

Chapter 47 of 56