din, wucewa yayi wajen ya shiga falon baida wani girma, Abba ne aciki sai Mami, sai Kawu, dakuma yayyinsa, wajen Ya Mustapa yaje ya zauna duk suna kallonshi yasauke kai kasa yace “ina Kwanan ku” Abba yace “lpy lau yaya katashi yau”? Ahankali yace “fine” yayi shiru sannan yadan gyara murya yadubi duka yaran nasa yace “akwai very important magana dayasa nataraku, Baba bayaso ya zauna anan sabida baiso wani yaji kunyarsa yakasa magana or yafadi ra’ayinsa” Abba yayi shiru sannan yace “Muhammad Sani na so ya aurar da Asama’u!” Abba Yayi maganan yana kallon yaransa dayaga babu wani wanda yayi motsi cikinsu, Abba yace “Asama’u batada wani manemi ko daya balle ace yafito” yayi shiru na kusan 3min kowa na kallonsa, ahankali Abba yace “inaso ka aureta Hassan!” Dasauri Hameed yadago kansa yakalli Baba cus baitaba kawo kansa maganan zatayo ba, Kawu yace “ka aureta Hameed!” Kallon Hamad Ya Mustapa yayi dake kusada shi asace batare da kowa ya lura ba, kansa na kasa but fingers dinshi yaga sunyi motsi more like rawa sai calmly yaga yaharde hannun nasa biyu yarike ya ijiye kan cinyarsa, Ya Mustapa yadauke kai kaman bai kallesa ba, Abba yakalli Hameed yace “bakace komi ba Hameed bawai tursasa ka nakeba saisa ma Baba yaki zama anan sabida kar kunyansa yasa kuyi abinda zaku cutar da kanku” Hameed is an upright person, he’s outspoken saisa ake cemai baida kunya shi a inda Hamad yake, kai tsaye yace “Abba ni inada budurwa wacce nakeso sunanta Zainab, Yaya Mustapa yamayi magana da ita awaya” Abba na kallonsa yace “and so? This is kanwarka ake magana dan kanada wata budurwa, nan da yan shekaru masu zuwa idan Allah ya budamaka kaga zaka iya rike mata biyu sai kayi” mikewa tsaye Hameed yayi da sauri Abba ya kallesa kowa ma haka banda Hamad da kansa ke kasa har lokacin, Hameed yace “Abba I am sorry gaskiya the same reason dayasa tundaga kan Ya Mustapa, Ya Abdullahi and Yaya Faisal basu taba marmarin auren yaran matan nan ba nima I am no exception” duka yayyinsa kallon Hameed suke, Abba dake kallonsa cikin natsuwa da magana irinta manya yace “and wat is that reason Hameed danni ban sani ba” rai adan bace Hameed yace “Abba have you seen yanda yaran matan nan ke tsoron mahaifiyar su? Tundaga kan Aya down to Munir? Abba kana ganin na auri yaran matan nan will I ever be husband to her? No no no Abba wlh Mom dinsu ce mijin, Mom dinsu ce komi tasu, they fear mahaifiyarsu kaman me, she’s in total control of lives nasu” Hameed yace “Abba idan Mom takira Asmeey tace Asmeey karkima Hameed girki bazatayiba” Hameed yayi magana da muryan Mom da saida Yaya Abdallah yayi murmushi cus he’s saying the truth wlh, Hameed yace “idan tace shigo mota kizo bauchi yanzun nan wlh they no born those children ko Asmeey takejin maganan! Kafin nadawo daga bank Abba Asmeey ta tafi” Hameed yadan lumshe idanu yace “Abba ni bazan taba iya auren wacce uwarta ta maida robot ba, she’s always ready to obey command, this is abinda yayyina suka gani basu taba kwadayin ko marmarin hada zumuncin nan ba cus it will never end well, banda haka that woman hates Mamie na alot! She hates us, she also hates y……” hannu Abba yadagamai hakan yasa Hameed yayi shiru, Abba yace “I don’t care idan she hates us or like us, Muhammad Sani kanina ne and I will always be yayanshi, zumunci is the most important thing to me” Kawu yace “kwarai Yaya” Baba yace “koba kanina araye ni mai daukan Asmeey na aurar da ita ga miji nagari ne, so idan wayannan ne dalilanka ban karba ba inaso ka auri Asmeey Hameed!”.
💫UWA KO UKUBA💫
✍🏻M SHAKUR
EPISODE 1️⃣8️⃣
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈
CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461
Baki Hameed yabude ganin da gaske Abba yake fa dan haka shima dole yayi da gasken, hakan yasa yahade rai yace “Abba nifa bazan auri wacce wani yarigani ganin jikinta ba!”Dasauri kowa ya kalleshi adakin da fuskan bacin rai sosai banda Hamad da har lokacin kansa akasa, Abba ya dakamai tsawa yace “what are you saying Hassan”? Cikin kunkuni Hameed yace “karya nayi Abba sabida baici nasara ba doesn’t mean bai mata wasu abubuw……” enough! Abba yafada rai abace, yanunamai kofa yace “fita! Get out” wucewa Hamee yayi fuuuu yafita daga dakin, Abba yadanyi shiru saiya kalli Hamad dakansa ke kasa anatse yace “Hussain zaka auri Asma’u”? Tashi Hamad yayi akufule yace “no!” Kawai yawuce yayi kofa yafice daga dakin Abba yabisa da kallo haka kowama na dakin Abba ya sauke kai tareda dafa kai yayi shiru chan Abba yadago kansa yace “wai nakalli Hameed shine mai dan hankali dazai iya zama da mace compare to Hamadi dakeda kunya bayama son mata na kallonsa, kuma naga Hameed shine yadan kama aiki a hannu zai iya rike mace da albashinsa, shi Hamad har yanzu bai sami aiki ba, amman jibi rashin mutuncin da Hameed yamin” ahankali Kawu yace “yanzu yaya zamuyi Yaya? Bazamu iya samo wani mu basa auren Asmeey ba gaskiya daga waje wanda bamusan yanayin halinsa ba, gwara yaranmu da suna gabanmu kuma mu muka tarbiyantar dasu” ahankali Ya Abdallah yamike yace “Abba reasons na Hameed are valid, I’m not talking about the last statement dinshi wannan hauka ne kawai yake but statement din mahaifiyarsu yaran dayayi is true, very very true, Abba auren yaran matan nan ba zaman lpy bane and idan kun shirya yi ku shirya ganin drama da damuwan uwarta daban daban cus kunsan gaskiya bawai mahaifiyarsu na sonku bane ko tana shiri daku ba she hardly talks to Mamie, Abba think about it please” ahankali Abba yace “to ya kukeso mu ceci Asma’u eh? Abdullahi idan ni mahaifinta Yayan kuma mahaifinta banyi ba who will? Do you have a better solution mu barmata yar ta kashe? Mubar innocent Asma’u ta mutu sabida halin mahaifiyarta sai muzo mukaita kabari nan gaba?”Shiru Ya Abdallah yayi sai kawai yawuce yafita shima, Faisal yamike yabisa abaya cus the truth is they don’t hate Asma’u infact babu wata kanwarsu da suka tsana tundaga kan Aya kawai they don’t want problem na mahaifiyarsu saisa dukansu bama su taba gigin neman yaranta ba duk sukaje suka auro matayensu awaje.
Dakin yarage daga su Abba sai Ya Mustapa, tasowa Ya Mustapa yayi yazo kusada Mamie yazauna dukansu suka kalleshi ganin magana yakeso yayi, Abba yace “me kakeso kafada Doctor? Kaima bayan kanninka zaka bi”? Girgiza kai Ya Mustapa yayi yace “Abba ku aurama Hamadi Asmeey!” Dukansu kallonsa sukayi jin maganan dayayi, Abba yace “Doctor Hamad! Da kanka kake fadin abama Hamad Asmeey? Ta ina kake ganin Hamad zai fara zaman aure da wata eh? Baka gansa bakaga kalansa ba”? Anatse Ya Mustapa yace “Abba sabida yanayin Hamadi sai muyita kallonsa bazaiyi aure ba? Hameed nada budurwa Zainab yariga yabama wata zuciyansa, koya auri Asmeey bazata sami zuciyarsa ba, so I support kar Hameed ya aureta but for Hamad baitaba soyaya ba just like Asmeey bata taba ba, Hamad is shy and calm, Asmeey is calm too and sad and lonely girl with zero friends, so I think a unionship nasu they will find solace and comfort in one another, they will learn to love ajunansu and unite, they will build not just love har friendship da companionship, Hamad zai chanza within a blink on an eye and be free da matarsa” Abba yayi shiru duk suna kallon Ya Mustapa dake magana hakama Mamie, ahankali Mamie tace “rike mata, rike gida, ciyarwa da sauransu fa doctor? Hamad bai kama sana’a ba kwakkwara yaya zai lura da ita?”Murmushi Ya Mustapa yayi yace “Mamie Hamadi is not that jobless da bazai iya rike mata ba yaron nan yanada sana’an sa, Hamad is genius, gifted, he works and he earns money, ana gobe salla they paid him 250k for a job dayayi that’s albashin Hameed na one month ya samesa in a day, Mamie kudenama Hamad kallon baida aiki trust me cikin duka yaranku Hamad shine ma yafimu aiki ga potential, akwai wani gasa daya shiga na Microsoft idan yagama yaci Mamie wlh kudin da yaron nan zaiyi sai kunyi mamaki and they will invite him to kasan waje ranan kaddamarwa zaku gansa a TV saisa na siyamai desktop rannan cus dashi yake aikin nashi ya lalace, Hamad is not lazy kuma ba lallai ma yajira mu mumai wani abuba, kumai addu’a kusamai albarka Mamie and wish him well, aure na bude kofofin arziki Allah bazai taba hanasa abinda zai ciyar da Asma’u ba banda haka I’m still here, gasu Abdallah ga Faisal ga Hameed we will all support our brother, Mamie Asmeey bazata taba wuni without a meal ba I promise you that” Duk shiru sukayi suna kallonsa Abba yace “na yarda toh doctor, inada wata miliyan daya muka koma kano sai atada gini a musu flat yasata agidan, bazan turasa gidan hayaba karya zaman mai wani burden akai biyan kudin gida duk shekara, kuma ayanda Hamad yake gwara suna gabanmu muna kwabamai, muna nunamai ga yanda akeyi dan yaron sai ahankali” Baba da Kawu duk sukai na’am Ya Mustapa yace “Baba karka damu zan dauki nauyin ginin in sha Allah” ahankali Mamie tace “Idan mahaifiyar ta tafara bura’uba fa? Hamad baida bakin fada ko fitina da tashin hankali? Nasan maganganun Hameed yayi shirme amman kuma yafadi gaskiya dayawa, idan Asmeey Hameed zata aura bazan waniji tsoro ba Hameed nada jan wuya dazai tsorata Asmeey ta natsu tasha ruwan jikinta idan mahaifiyarta na abubuwan data saba, but Hamad fa? Ta ina zai iya da jaraban matan nan?” Murmushi Ya Musty yayi yace “one problem at a time Mamie, and Mamie kinsan mene kinga yaran nan biyu Asma’u da Hamad idan sukazo suka kulla soyayya ba mahaifiyar Asmeey da idan duka danginta ne Asmeey zata yakesu sabida mijinta, babu abinda so baya sawa Mamie kawai mubisu da addu’a” Abba yace “wannan gaskiya AlMustapa, idan muka tafi da ita kano saitai haukanta aurenma sirri ne, so maganan nan ta tsaya tsakanin mu, bari na kira Muhammadu Sani” Baba yadaga wayansa ba’a wani jimaba saiga Baba yashigo ya zauna Abba ya sanar dashi komi sun dauka bazaiso hadinta da Hamad ba cus baida aiki amman Baba yace “wlh wlh nafison Hamad! Nafison Asama’u da Hamad Yaya, nasansa da kunya da jin nauyi yasa naki zuwa nan amman shinake mata kwadayi dama, arziki kuma Allah ke badashi ga wanda yaso, ni da inada arxiki? Rana daya Allah yasama kasuwata albarka, zan sayamai gida a kanon sai su zauna ciki” Abba yace “kadakata tukunna su zauna agabanmu muna kallonsu kasan yanayin Hamad we have to groom him and teach him zaman aure” Ya Mustapa yace “Hamad bazai taba yarda ma ya zauna agidan da zaka basa ba Baba yanada zuciya da kwazo fa bayason irin abubuwan nan, ko ginin da zamumai yanzu zakuga yanda za’ayi dashi sai munyi daga” Waya Baba yadaga yakira Yayan Mom, Yakira wasu abokansa guda biyu, dawani babban Malami daya sani karfe biyu a masallacinsu na nan cikin gida.
Shigowa dakinsu Hameed yayi dan tuntuni yana waje yayi wani bako dan shi yanada friends anan Bauchi yana shigowa daidai Hamad na fitowa daga wanka yasaka wani ash yadi but idanunsa sunyi ja da sauri Hameed yace “meya sami idanunka haka kuka kayi?” Da sauri Hamad ya dauke kai yace “soap” gabansa Hameed yasha yana kallon idanun yace “soap? Yaushe kafara sa soap a idanu wajen wanka? Did you cry Hamadi?” Kokarin matswa gefe Hamad yayi Hameed yabisa yace “why did you cry”? Dan lumshe idanu yayi saikuma ahankali ya nunamai shoulder shi, dasauri Hameed yazo yadan daga rigansa yaga ciwon yace “you got hurt wurin nan jiya ko?” Gyadamai kai yayi Hameed yace “sannu kasha magani”? Maganin ya nunamai dake gefen gado kawai yawuce yahau gadon yadauki laptop dinsa ya kunna Hameed yabisa da kallo zuciyanshi na kokonton abinda yasashi kuka, Hamad is very soft tun yana yaro he cries for ciwo especially idan da zafi, but could this small ciwo be abinda yasasa kuka abayi? But wani abin ne? But mene toh? Wani abu yabatamai rai ne? Wat happened? Yayi shiru cus yakasa kawo wani abu
Sai yazo bakin gadon ahankali ya zauna ahankali yace “Hamad” juyowa Hamad yayi yakallesa, murya chan kasa Hameed yace “I love you!” Wani irin dauke kansa Hamad yayi da gudu yadauki filo yana kare fuskanshi adikile yace “wat is this”? Kaman mace Hameed yawani shake murya yace “Wallahi I love you Habiby na Hamadi fine boy” dawani irin sauri Hamad ya yunkura zai tashi Hameed yarike shi yana hayowa gadon yace “wlh bazakaje ko’ina ba, wai kai bazaka koyi irin abubuwan nan ba, hakafa kai aure matanka zata dinga gayamaka, I love you Hamad” yawani make murya yana kanne idanu uwa mace, juyawa Hamad yayi yakifa fuskanshi akatifa sosai kaman zai shige ciki da kyar yace “please stop this Hameed” Hamad is really really shy, Innalillahi wannan wani irin namiji ne, how will Hamad bring kanshi yayi making love to matarsa? Wlh he’s not sure idan Hamad can look at nakedness din mace ma, sai kawai yasakesa ganin karyaje yahana kansa numfashi sabida yanda yake manna fuska akatifa kaman zai yaga yashiga ciki, yace “matarka ta shiga uku Hamadi” yawuce bayi abinsa shima dan yayi wanka”.
💫UWA KO UKUBA?💫
✍🏻M SHAKUR
KINSAN YANDA AKE JIYAR DA MIJI DADI? KINSAN YANDA AKE SA ME GIDA KUKA AGADO? KINSAN SIRRIN SARRAFA TANTAKWASHIN DADI? KIN IYA HATSABIBIN KUKA? MAKIRIN KUKA? SHEDANIN KUKA DA AKEMA MIJI? KIN IYA STYLES? KIN IYA KISSA???
JOIN INTIMACY CLASS DINA WITH JUST 5K KI KOYA🔥
GROUP DIN TSAWON SHEKARA DAYA NE KIKA BIYA 5K BAKI KARA BIYAN WANI KUDI SAI BAYAN 1YEAR JUST TODAY AND BE A BADDIE FOR OGA🙈
CHAT ME UP DON SHIGA
wa.me/+2347012181461
EPISODE 1️⃣9️⃣
Flat dinsu Baba yashiga yara duka an musu wanka sunsa kayan salla an basu breakfast tea da bread sunasha harda yaran su Su Ya Mustapa, dasu Ya Abdallah duka, suna ganin Baba falon kaman makaranta. “Good morning Baba” murmushi Baba yamusu yace “anashan shayi to asha ina zuwa nima abani nawa nasha” wucewa yayi sama ya kalli agogon bango ganin 9 something ya kalli dakin Mom saiyaji ransa na baci yawuce wajen kofa yabude kai tsaye ya shiga ciki, Mom yagani zaune tayi wanka taci gayu tasa wata shadda dayasha aiki ga Mama gefenta dake kada musu shayi, Mama na ganinsa tace “ahh Baban Aya kaine, mun tashi lpy ina kwana” haushi rufe Baba yayi baima amsata ba yace “bamu wuri Maman Nana” tashi Mama tayi takalli Mom tace “bari naje Maman Aya kuka gama kirani awaya” gyadamata kai Mom tayi cikeda isa tana gyara farin glasses na idanunta, Mama tazo tabi ta gefen Baba tawuce tafita ta maida musu da kofan tarufe, Mom ta kallesa ba yabo ba fallasa tace “ina kwana” Baba bai amsata ba rai abace yace “wat are you still doing agidana? I thought I made it clear cewa ki barmin gida this morning”? Tea da Mama tahada mata tasa hannu tadauka takai baki ta kurba, Baba na kallonta wondering tayaya ma ya auri mace mai girman kai haka harya iya zama da ita na all this years suka hayayyafa, kurban tea tayi ta ijiye cup din sannan tasa hannu tadauki wani file dake nan kan table ta mikamai da hannu tana kallonshi ido cikin ido tace “ka sakeni yes naji ka sakeni, but korana daga gidan nan Baban Aya baka isa ba saidai ni na koraka idan naso” kallonta Baba yakeyi sosai ba rahama kan fuskansa yace “gidan mahaifina daya baro kauye yashigo nan birni yagina mana all i did was nakara kudi nasai land nayi renovating gidan nan na maidasa haka na zamani shine zakice ni zaki kora”? “Kwarai! Kajini da kyau Baban Aya, gidan nan is mine ka duba takardun nan kagani da signature ka akai, gida nawa ne!” Abba na tsaye wajen kawai yasa hannu a aljihu zuciyansa na tafarfasa yashiga kiran Faisal yana dagawa yace “Son kazo ina sama” ya katse wayan Mom ta ijiye file din kan table tacigaba da shan tea tana kallon TV abinta, juyawa Baba yayi yabude kofa daidai Faisal na hayowa saman zai wuce side din Baba, Baba yace “gani nan Son” tahowa Faisal yayi suka shigo dakin tare yakarasa wajen table yadauki file yamikama Faisal daya tsaya yana jiran Baba batare daya kalli inda Mom take ballema ya gaida matan ba dan wlh he hates her sosai, Baba yace “takardun gidan nan ne wai gida ta ne tayaya akayi suka dawo nata Faisal”? Faisal is lawyer he knows all this hakan yasa yashiga reviewing komi sannan yakalli Baba yace “Baba ya akayi kayi signing takardun nan?” Baba yayi shiru saiya kalli Mom datamai wani murmushin keta ya dauke kai yakalli Faisal yace “tana bani takardu da dama ina signing na makarantun yaran gidan, kasan kap yaran gidan nan ita ke handling school nasu, sune kawai abinda nake signing saidai tahaka ne tabani na signing ban sani ba” dan ijiyan zuciya Faisal ya sauke yace “gidan nata ne yanzu Baba kayi signing” kurban tea Mom tayi tasauke kasa tadanyi murmushi tace “ilimi nada dadi yau kaga rananta ko Baban Aya? Nasan with this kind of people dakakedasu as yan uwa watarana za’a saka ka sakeni, ka koreni, nasan ba cikakken ilimi gareka ba haka naje dakinka na dauko takardun nayi komi na hada ciki takardun makaranta su Yusra kayi signing yanzu inga ubanda ya isa ya koreni daga gidan nan wlh saidai ni na koreka da yaranka da matarka da mutanen nan daga gidan” Faisal jiyayi kirjinshi na tafarfasa ya cigaba da tsayuwa anan he can insult this bitch of a woman hakan yasa yace “Baba can I go?” Gyadamai kai Baba yayi Faisal yajuya zai wuce Mom tace “kaikuma uwarka kagani ka watsar ba ni Salima ba” juyowa Faisal yayi yamata wani kallo sannan kawai yabude kofa yafice.
Baba yakalli Mom yanuna mata files na hannunshi yace “Salima ni zaki kwacema gida? Gidan mahaifina? Shi zaki maida naki sabida kinga banda sani kan harkan makaranta kaman ke? Salima tunda na aureki nataba cutar da ke? Makarantan nan da abinda kika zama yau is all thanks to me nina saki kikai karatun da kudina? Gidan nan banawa bane eh nasan ninasai filaye kusan uku na hada na karama gidan girma nayi renovation saisa yan uwana suka bar gidan yadauki sunana a paper da komi ba nasu sunayen amman hakan baya nufin nine mai gidan nan gabaki dayansa Yaya na ciki, Kawu na ciki, mahifiyarmu Gwaggo na ciki, this house is gidan gado da mahaifinmu yabari, Salima kin maida gidan da babu zufanki ko daya ciki naki sabida makarantan da karatun da kikayi na ilimin mallakan abinda babu zufanka aciki ko shi karatun lawyer?” Baki Mom ta tabe tace “kanka akeji Baban Aya! Shekarun mu talatin da aure munada diyar 27yrs shine zaka sakeni yanzu? Ni zaka saka? Maisa baka sakeni tun ina yar yarinyataba sai yanzu zakamın sakin rashin mutunci kace na tattara na barmaka gidanka, is something wrong with u?Akwai wani level da ake kaiwa a aure da wlh miji bai isa yasaki matarsa ba, Baban Aya baka isa kasakeni ba wlh! Zama daram babu inda zanje! Gidanku bawai na kwace to sell it kowani abu bane no it’s just lave-rage, idan kanason gidan ku na gadon nan u want to protect it at all cost to ka zauna dani zama daram inba hakaba get ready kahakura kaima da gidan gadonku” Ijiyan zuciya Baba yasauke yana girgiza kai yace “fine gidan nan ba kirike, Alhamdulilah ni da yan uwana ba dukiya ko wani abun duniya ne agabanmu ba kirike gidan bazan taba kaiki kotu kona tsaya yakanki sabida gidan nan ba, but just know this dagayau ke ba matata bace! Me and you are complete strangers! Babu any hakki naki akaina u are on your own, I don’t know you dagayau Salima, gidankuma gashi duk yanda kikeso kiyi dashi gado ne kici, kin nunamin kalanki ba yarmu kadai kika tsana ba yau kin nunamin nima you’ve always hated me, baki sona ko daya Salima inhar kin iya kin amfani da ilimi da wayau kika yaudareni nayi signing takardun gidan nan only shows me baki taba sona ba, kaman yanda bakison mahaifiyata da yan uwana kije bakomi, take” ya ijiye mata files din akan table yawuce yafita Mom tabishi da kallo kirjinta na bugawa feeling very bad a zuciya, she thought Baba would beg her yace ya maidata just to save gidan, itafa she cares so much about that name tag na marraige Mrs Salima Muhammad S Turaki, her name, her status is her identity! Marraige is power! But karfin hali da taurin kai yasa taki magana tasan laslas he will come back to her ta cigaba da shan shayin zuciyanta na tafarfasa kasa daurewa tayi ta tashi tabude kofa tafito dakinsu Asmeey tawuce tabude kofan babu kowa ciki kirjinta ya shiga tafartafasa yana suya kaman an zuba kwalbati.
Sauka tayi kasa yaran harsun gama breakfast sun fice waje Gambo kawai ke falon tana gyarawa tace “barka da saukowa Hajiya” ko kallon Gambo batayiba tawuce hanyar dakin Munir kai tsaye tabude kofan bai dade da tashi ba yayi wanka shiryawa yake yana kokarin saka rigansa na shaddan dayasa Mom tabude kofa tashigo dakin fuskanta a murtuke tana kallonsa, daukekai yayi daga kallonta dan bala’in haushinta yakeji rai abace Mom tace “baka iya gaisuwa bane ko bakinka ciwo yake”? Rigansa yakarasa sawa da kyar murya ciki ciki yace “good morning Mom” tsaresa Mom tayi da idanu yanda yajuya abinsa yana daukan agogonsa yana kokarin sawa tace “Aya na gidan nan har yanzu?” Da kyar yace “eh” kallonsa Mom take tace “okay yayi mata kyau, jeka kiramin Asmeey” batare daya kalleta ba yace “bazata iya zuwa ba” Mom jitayi kaman Munir ya watsamata garwashi ajiki amsan daya bata wat the hell! Ita Munir ke amsawa haka? Karasawa wajensa tayi tawani juyodashi tana kallon kwayar idanunsa da kyau tace “mekace yanzun nan Munir”? Sosai gabansa ke faduwa amman ya dake ya danne tsoron yakuma daure yaturo mata baki sosai cikin tsananin jin haushinta yace “nace miki bazata iya zuwa ba Mom” tassss! Mom ta yanka masa mari mai rai da lafiya tace “such insolence! Are you sick upstairs? Ni kakema magana gatse haka without respect? Are you talking to your Mom like this Munir?” Azuciye Munir yace “yes Mom namiki cus you are not the type of mothers da aka suffanta dake shiga aljanna” Munir yahau huci idanunsa na tara hawaye yanama Mom wani kallon tsana da rashin tsoro irin na yara, eyes nashi na looking kaman yana hararan Mom, Mom tace “ohh kayi girma ko Munir ni kake harara with those eyes kaman na aliens? Zakaci ubanka yau” tayi maganan tajuya tana neme neme abinda zata dakesa dashi taga charger laptop dinshi kawai tadauka ta cire ta taso tana linkewa tayo kan Munir dake kallonta har lokacin kawai tadaga wayan zata chaulamai rike wayan yayi azuciye yafizgo saida Mom tabiyosa kaman zata fado kansa dan kafafunta yau suna ciwo tadake tana kallonsa tace “dambe zakai dani Munir”? Yanama Mom wani kallo yana turo baki yaki magana, Mom takalli wayan tace “sake wayan nan, ka sake wayan nan nace” Munir yaki saki sai huci yake kaman zai rufe Mom da duka wlh, kana ganinsa kasan kawai dan Mom mahaifiyarsa ce da wlh saiya kaita kasa yau sabida yanda yakejin haushinta kuma ya zuciya, Mom ta bala’in girgiza ganin Munir is becoming fearless yanzu, tadake tace “is because of salla sannan kasa kayan salla da kaga other side of me” tai maganan tana yarda wayan kasa ta matsa gefe tanunamai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 56