Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
datake fadi ba, she’s just crying and saying abubuwan da batama sani ba, agogo Ya Mustapa ya kalla is 12:55, daidai ana announcing jirginsu zai fara boarding in gate 5, Baba yayi namijin kokarin zuwa wajen ahankali yakama Asmeey yace “Asmeey! Barsa yatafi kinji” cikin wani irin kuka tace “Baba banso mijina yatafi, zan mutu Baba, Ya Hamadiiiii” da kyar Baba yakamata yakalli Hamad yace “tafi Hamadi” Hamad yakasa tafiya shima Ya Mustapa yazo yace “common Hamad! Ya isa! Go” yakamasa yajasa Hamad na tafiya yana kallon Asmeey dake kuka sosai jikin Baba tana miko mai hannu tana kuka, saida Ya Mustapa yakaisa security check post yadawo Hamadi yawuce suma sukai waje da Asmeey data basu tausayi wayyooo Allah na. SAINA TUNA DA WATA WAKA… Ashe sabo yana da dadi (ban kawana) Amma in za'ayi rabo da zafi (sai wata rana) Gashi zamuyo rabo dajuna (ban kawana) Amma na sani ni banda laifi (sai wata rana) Ka tausaya in nayi ma laifi (ban kawana) Kace ka yafe in kama gaba na Nida ke ayau muyi bankwana Sai wata rana rabuwa ba mutuwa ba Yar uwa rabin raina ban so muyo rabuwa. MY HEART BROKE FOR ASMEEY AND HAMAD💔💔💔😭😭😭 EPISODE 6️⃣6️⃣ Idanun Hamad sukai jazur, hawaye suka ciko hango yanda Baba ke fita da Asmeey dake jikinsa tana kuka not minding the people in the airport, black shades dinsa yasaka yawuce gate din dasuke boarding zuciyansa namasa radadi sosai ya shiga jirginsu. Rannan dayaje embassy rannan representative na Microsoft sun kirasa sunyi magana kan transportation nasa, so sune sukamai booking business class ticket, nuna masa seat dinsa air hostess tayi ya shiga ya zauna yaja kofa yarufe yacire glasses din yakai hannayensa biyu sai share hawaye yakeyi da sun kasa tsayawa he’s just in between farin ciki da bakin ciki, seeing Asmeey in that state broke him completely, ganin basu riga sun tashi ba har yanzu, wayansa yaciro daga aljihu dasauri, Ya Mustapa yakira ringing daya ya daga lokacin suna kokarin shiga mota, yace “kun shiga jirgi”? Gyadamai kai Hamad yayi kaman yana gabansa sai yayi shiru, shima Ya Mustapa haka cus yasan dalilinsa na kira, ahankali yace “tana motan su Mamie” saikuma anatse yace “bana gayamaka u should be strong ba? If you are like this how will Asmeey be okay? When u suppose to be her strength Hamadi, I know this path is not going to be easy for either of you but kaman gobe ne! Remember you are doing this for her! For future yaranku! Without this how will you take care of her? Idan Allah ya albarkace ku da yara fa yazakayi? Yazaka ciyar dasu? So koma menene think of the future Hamadi and do the right thing for future family naka, good things don’t come easy sacrifice must be made, highest wata nawa ne tazo ko kai kazo? Yanzu kaje ayi lunching app din dai tukunna on 1st November, daganan sai musan ya ake ciki kaji afara process dinta na zuwa, be strong Hamadi inba hakaba Asmeey will be completely shattered, she’s a child she will be fine kaji, remember u are doing this for her too, to be able to take care of her, ya isa haka, stuff like this happens but zata hakura, she will learn and she will adjust okay” gyadamai kai Hamad yayi maganganun Ya Musty calm him down a bit, cikeda rashin kuzari yace “toh” Ya Mustapa yace “idan kun tashi say your prayers, we will talk later, Allah ya tsare hanya” ahankali Hamad yace “Ameen” ya katse wayan yayi shiruuuuu daidai jirgin yafara tafiya a runway suna shirin tashi, yayi shiru he’s just thinking about Asmeey, he’s calmer than dazu after magana da Ya Mustapa but he’s still very much worried tunanin ta ya addabi zuciyansa, jirginsu yadaga sama sai hawaye kawai yazubomai, dagaske yadaga daga kasar Kano and matarsa na nan, why will he see her again?..…. ** Har sukakai gida Asmeey kuka take ba kakkautawa Gwaggo na tayata ta tausayama Asmeey da Mamie da duk sukai wani iri dan tasan yanda Mamie ke son yaron nan, suna parking Asmeey tafito da gudu daga motansu tai cikin gida kowa yabita da kallo sama tayi tashige dakinsu tafada gado taja bargo ta dukunkune tana wani irin kuka da ta dade batayi kalansa ba, Munir zai bita Ya Mustapa yace “let her be for now anjima sai adubata” jikin kowa yayi sanyi har Baba, but he’s greatful ganin yanda diyarsa ke son mijinta, mijinma na kaunarta. Shigowa sukayi duk aka zauna a falo, Baba flight nasa to Bauchi is by 5 na yamma so ba yanzu zai tafi ba, duk akai shiru, sai chan Faisal yace “wait ooo why are we all sad? I know harda kukan Asmeey ke samu this sadness but in reality we should be happy ko Baba?” Baba ya gyadamai kai alamun kwarai, Faisal yace “Hamadi is winning Mamie cheer up, yaronki na seat a business class a jirgi going to Washington, yana sauka akwai mutane available with security da za’a daukesa akaisa suite, Mamie kinsan yanda yaronki zai dinga samin VIP treatment kuwa? Hamadi is a hot cake da yanzu plenty brand zasu dinga neman yanda zasu sacema Microsoft shi, please let’s cheer up and be happy, Hameed kawo drinks daga fridge, cus idan bama farin ciki how can we make Asmeey happy koba hakaba Munir”? Dasauri Munir yace “hakane Yaya” zuwa wajen Mamie Faisal yayi saiya bata side hug yace “Mamie na kina kewan autanki ko”? Dan murmushi kadan Mamie tayi ahankali tace “uhm” Faisal yace “just pray for him Mamie our lives is about to change sabida Hamadi” duk sukai murmushi Ya Abdullahi yace “nakosa on 1st tayi, a TV zamuga Hamadi fa a news yana nunama duniya how software din works Mamie, yan anguwan nan sunkusan cika gidan nan adinga muku Allah sanya alheri dan har su Channels saisun dauki news din, Baba Ya Aysha saita kiraka sune yan TVC tace yaushe Hamadi yaci Microsoft talent hunt, har shugaban kasa will celebrate Hamadi, someone from Nigeria won Hamadi yazama national treasure fa” akai dariya, Mamie tai murmushi hankalinta na natsuwa, Abba yace “awa nawane tafiyan?” Ya Mustapa yace “direct flight sukamai booking is a 14hrs 40min flight” ajiyan zuciya aka sauke akace. “Alllah ya kaisa lpy”. EPISODE 6️⃣7️⃣ Asmeey saida taci kuka ta godema Allah bacci yayi awon gaba da ita, wuraren 2 Mamie tabude kofan dakin tashigo ciki ahankali, Munir daya damu biyeda ita, ganin tana bacci sai Mamie tamai alamu da hannu su tafi karsu tadata, wucewa sukayi suka fita daga dakin. Wuraren 4 Baba yayi sallama dasu yatafi yabar Munir dazaiyi one week yadawo dan hutun sati aka basa a school har lokacin Asmeey bacci take yahana kar atadata. Around 6 Asmeey taji ana shafa mata goshi, gently tashiga bude idanunta kadan kadan tana hoping idan ta bude idanu Ya Hamad zata gani, Mamie tagani saitai shiru tana kallon Mamie idanunta sunyi ja sun kumbura, murmushi Mamie tamata cikin sanyin murya tace “tashi kiyi salla, bakiyi azahar ba gashi yanzu magrib tayi?” Hawaye ne suka ciko idanunta cikin wani irin sanyin murya tace “Mamie yakai?” Girgizamata kai Mamie tayi tace “14hours flight ne, sai around 3 na asuba ko 4 zasukai In Sha Allahu” zubomata hawaye sukayi sai kawai ta maida idanunta ta kulle ta sauke wani irin ijiyan zuciya, Mamie taji tabata tausayi matuka, ahankali takai hannunta ta kama kafadanta ta dagota zaune, ba karfi ajikinta ko kadan, tasowa tayi ta zauna hawaye na fito mata sosai, sai gogewa take da bayan hannu, ahankali Mamie tace “kaman gobe ne Asma’u kinji, kema zakije, he’s going there for a good reason, ki daure kinji and be a strong girl kima mijinki addu’a, if you’re like this bazai iya abinda ya kaisa ba kinji” gyadama Mamie kai tayi Mamie tace “tashi kije kiyi salla toh” sauka tayi daga gadon da kyar gabanta yakara kumbura tawuce tana tafiya ahankali zata bayi jikinta babu karfi, cikeda tausayi Mamie tace “ki shiga ruwan zafi Asmeey” sauke kanta kasa tayi tabude bayin ta shiga Mamie ta tashi tafice. Kaya Asmeey tacire ta tara ruwan zafi da kyar ta daure ta zauna aciki tana kuka, tana tuna yanda shiya mata wanka jiya da yau da safe, she don’t think za’a taba samun someone that can take care of her better than Ya Hamadi, duk yanda zatai bayanin yanda takeji babu wanda zai gane, is as if a piece of her heart and life is gone, she feels so empty, she feels lost, kawai taji rayuwan baya mata dadi at all, komi yamata duhu, batajin dadin komi just like yanda takeji a Bauchi, she’s feeling exactly dsame yanzu, takai kusan 10min ta mike tayi wanka tai alwala tafito simple gown tasaka tasaka hijab tahau kan daduma tafara salloli tana idarwa Munir na knocking da sallama yadan bude kofan kadan ganinta kan dadduma yashigo yana murmushi yace “Ya Asmeey Mamie tabani abinci nakawo miki” kallon abincin Asmeey tayi kafin ahankali tace “anjima zanci banjin yunwa” Munir looked as her he knows exactly what is going on a head nata yasan it’s not easy sai kawai ya ijiye abincin a gefe daya yakama hannunta yarike, kallonsa Asmeey tayi sai kawai yatuna mata da Ya Hamad yanda yake rike mata hannu, sai kawai tafashe da kuka mara kara tana goge idanunta da bayan hannu ahankali, knocking akayi da sallama Munir yace “shigo” Ya Hameed ne rike da roban ice cream yana murmushi yana kallon yanda idanunta suka kumbura she’s still cleaning tears yace “kinga mijinki yace kullum nadinga siyamiki ice cream just to cheer u up amman har yanzu kuka kike” kallon ice cream din Asmeey tayi jin Ya Hamad yace asayamata sai ahankali tamikama Ya Hameed hannu yabata amsa tayi tana goge fuskanta da bayan hannu kaman wata marainiya tabude ahankali tasaka spoon ta shiga sha, tanasha tana goge hawaye, tabasu tausayi sosai, dan murmushi Hameed yayi deep down yana addu’a Allah yasa Zee tasoshi morethan this cus he loves yanda Asmeey loves his brother wlh dearly, Hamad is so lucky to have a wife like this that’s seriously crying for him, feeling empty, lonely, incomplete without him cus Asmeey is looking damn miserable sabida Hamadi yayi tafiya. Da fita zaiyi amman sai shima ya zauna sukahau hira da Munir dudda bata cewa anything but she’s sipping ice cream din, sallan isha’i aka kira suka fice itama tayi sannan ta zauna tai shiru tana kallon desk dinshi da chair da desktop dinsa daya bari a gida, tai shiru abu na tsayamata a wuya, dakin ba dadi, harwani gizo idanunta kemata kaman gashinan yazauna kan kujeran yana kallonta, ko yana aiki, koya tashi yaje bayi, koya shigo dakin, murya Chan kasa tace “Allah ya kaika lpy, Allah ya tsareka Ya kareka, Allah ya daukaka ka Ya Hamadi, wlh ina sonka” tafashe dawani kukan maraici, just to make her not feel lonely Mamie ta kwalamata kira daga kasa amsawa tayi da muryanta da baya fita ta mike tafito sanye da hijabin bayan ta goge fuskanta duka yayyin suna falo harda Abba duk sai kallonta suke idanunta sun kumbura sunyi ja fuskanta gabaki daya look puffy ga bacci ga kuka, Abba yace “kinci abinci?” Girgizamai kai yayi yace “oya zomuci tare” batai musu ba akunyace taje saita zauna hannu tasa Gwaggo tace “ohhh ke wanna yarinya Rijalu kikema wannan bakar soyayyan haka? Jiba idanu kashe kanki zakiyi shi yaje chan neman kudi” wani mugun kallo su Faisal suka mata taja bakinta tai shiru, Asmeey tadanci abinci ta dakata Abba ya barta, daya gama ta kwashe komi tawuce kitchen, Abba bai bari ta tafi ba tazauna afalo sukai hira duk yayyin na gidan kuma sabida Asmeey ne sai around 10 duk suka tafi Abba yace “tashi kije ki kwanta” Mamie tace “zaki kwana a dakina?” Girgizama Mamie kai tayi alamun a’a Mamie zatai magana Abba yahanata Asmeey tawuce tareda Munir yamata saida safe yatafi dakinsu ita ta shiga nata tamaida kofan tarufe hannunta tadaura akan bakinta tafashe da kuka sosai she’s seriously missing Ya Hamad, yazatayi? Mezatayi dazata dan ji sanyi aranta? Tadade ahaka tawuce gado ta kwanta ta kankame pillow tana kallon desk dinshi bini bini tana share hawaye sai juyi take takasa bacci ahaka bacci yayi awon gaba da ita chan tabude idanu but still it’s just 1:00 nadare tashi tayi ahankali tawuce bayi tayi alwala tazo tahau salloli har 4:00 tana zaune kan dadduma taji karan an bude kofa chan taji anyi knocking kofarta taji muryan Hameed anatse yace “Asmeey” dasauri tamike tace “na’am” tayi wajen kofan dasauri sabida zuciyanta na bata Hamad ne yakira da sauri tabude kofan, wayansa yabata yace “gashi it’s Hamad” dawani sauri tasa hannu ta karbi wayan yace “I will collect it in the morning” gyadamai kai tayi ta maida kofan tarufe tawuce gado ta zauna taredasa wayan a kunnenta zatai magana saitai shiru takasa hawaye ya sauko daga idanunta takai bayan hannu ta share tana shesheka ahankali dake taba zuciya, cikin weak cool voice Hamad yace “mesa baki bacci ba?” Tone nata na she’s crying tace “nayi natashi ne, kun sauka Yaya?” Gyadamata kai yayi yace “eh, Nigeria is 6hours ahead of nan, it’s 11 na dare da yan kai anan yanzu Nigeria is 4AM ko”? Gyadamai kai tayi kaman yar yarinya zuciyanta namata wani iri kaman zata mutu, cikin sassanyar murya Hamad yace “Husnahhhhh!?” EPISODE 6️⃣8️⃣ Wani abu taji muryansa yamata uwa ya kwance makullin datasaka na dauriya a zuciyanta, kawai saita fashe mai dawani irin kuka mai sanyi yet piercing heart, Hamad ya lumshe idanu yana jingina kansa jikin kujera ya sauke ijiyan zuciya ahankali, cikin muryan lallashi da tsantsan so yace “I am sorry Baby, kiyafemin….” Cikin murya mai bala’in rauni Asmeey tace “ka…k….ka….tafi…k…a…barni“ kukan is not even making her talk properly, murya chan ciki yace “kinaso nakasa yin abinda nazo yi anan?” Cikin muryan kuka tace “ah’ahh” ahankali cikin murya mara kwari yace “kukan nan yana dagamin hankali sama da komi, I will come back soon and get u kinji”? Gyadamai kai tayi kaman yana gani yace “stop crying now and wipe those tears” bayan hannunta takai kam fuskan ta goge hawayen tass, murya chan kasa Hamad yace “I love you alot!” Wasu fresh hawaye ne suka zubomata kaman zata kurma ihu ita kawai mijinta yadawo she don’t think she can do this rayuwa babu shi, ahankali yasake cewa “Asmeey” ganin he’s seriously disturbed yasa ta gyara muryanta tace “kakai gida?” Murya chan kasa yace “no ina mota ne”? Ahankali cikin tsananin son Hamad tace “kaci abinci toh?” Sanyi sosai Hamad yaji da tambayan yace “no but zanci nakai gida, kinci abinci?” Gyadamai kai tayi tace “eh tareda Abba” shiru yayi saikuma ahankali for the second time yace “I miss u” dan kukan datake rike taji yasake dawo mata muryanta na rawa tace “yaushe zaka dawo?” Allah sarki tabasa tausayi, from the way she talks kasan she couldn’t hold it in any longer Asmeey is missing him kaman zatace wayyo Allah, dan dakewa yayi yace “soon! But kidena kuka kinji, idan wani abu yasameki I will not be able to cope, u mean alot to me Asmeey, when u are not crying i get strength nayi all work sabida nadawo dawuri, but when I am worried sabida ke I will not be productive” gyadamai kai Asmeey tayi, ta share fuskanta ta saita muryanta da kyau tace “wazai kaika gida?” Ahankali yace “dreba dawani security personnel haka kaman escort ne” gyadamai kai tayi, Hamad yace “Ya Hameed yakawo miki Ice cream”? Gyadamai kai tayi tace “eh, nagode” murmushi yayi yace “okay, me kikeso nasa akawo miki gobe”?Ahankali tace “bakomi” gyadamata kai yayi yace “idan gari yawaye gobe i will be busy, zasu kaini police station for wasu formalities da documentation sai kuma bank, jibi shine zanje office nasu and meet with the CEO tareda lawyer na daganan aiki zai fara” gyadamai kai tayi tace “Allah bada sa’a Yaya” “Ameen matar Yaya” dan murmushi tayi, ahankali tace “garin nada kyau?” Gyadamata kai yayi yace “yes yafi Nigeria kyau, u will love it here but akwai sanyi” murya chan kasa tace “yaushe zakamin ho….ton…..k..ka?” Shiru Hamad yayi saikuma yasaki dan murmushi jin matarsa is asking for abinda yayi hating d most wato pictures amman saiyace “zan miki pictures gobe in sha Allah, download Snapchat a wayanki zansa Munir yamiki adding dina” gyadamainkai tayi tace “okay” yasake yayi shiru kafin anatse yace “I have to go now, zan basu wayansu gobe I will call u with my new number” gyadamai kai tayi zuciyanta yasake mata badadi kaman karya tafi saitaji kaman batada lpy, ahankali Hamadi yace “Baby” murya chan kasa tace “uhmm” anatse yace “be eating and stop getting worried everything is going to be okay, we will see soon kinji” gyadamai kai tayi hawaye na cika idanunta murya chan kasa yace “I love you Asmeey” kasa amsawa tayi ta katse wayan dasauri takifa kanta a filo tana kuka saida aka tada salla ta tashi tai asuba tahau gado bacci yayi gaba da ita Mamie ita tashigo dakin tadauki wayan Hameed dazai tafi aiki tabasa. Wuraren 10 Asmeey ta tashi da mugun zazzabi, wasa wasa Asmeey tafara ciwo rashin lafiya saida Mamie takira Musty yazo magunguna yabata da allura bayan ya duba jikinta, akace kar wanda ya gayama Hamad, rannan all through Hamadi bai iya yakira ba ko bai iya yayi sim din bane oho hakan yakara damunta kuka kawai shine aikinta. Tunda ya shiga garin they welcome him with flowers masu kyau aka daukesa awata latest tesla mobile car, wani skyscraper apartment aka kaisa lafiyayye 34th floor ne suite dinshi security yace “this is ur suite Sir you can change the password anytime u want” yabude mai kofan kunga gidan Hamad Ya Allah wani lafiyayen apartment ne an gyara komi harda decorating is a one bedroom glass apartment falon nada girma gawasu fararen chair ga mahaukacin fine kitchen ta gefe dayan yanunamai bedroom wani hamsakin gado an ijiye abubuwa da yawa agadon ansa welcome Mr Hamad, saikuma computer room nasa kunga computers da desktop da aka ijiyema Hamad all courtesy of Microsoft ga abinci da dama security yace “make yourself at home Sir, your appointment tommorow is 10AM” Gyadamai kai Hamadi yayi yawuce yatafi Hamad ya tsaya yayi shiru a katon dakin yana kallon duniya gabaki daya ta glasses din yana tunanin inama shi da Asmeey natare. Wanka yayi yabude akwatinsa ya jera komi a drawer abubuwan Mamie yaciro he’s hungry cake yaci sai yazo yadan ci fruits daya gani awajen all other things bai taba ba shima kasa bacci yayi saidai barawo ya daukesa sabida tunanin Asmeey. Washe garin nan sai yamma suka dawo dan saida aka budemai komi yadawo gida ya kara gyara suit dazaisa dan gobe ne zaije aslin Microsoft office by 11 na safe. EPISODE 6️⃣9️⃣ Da asubahi yatashi he’s missing zuwa masallaci, jin kiran salla, one of this days zai zagaya area yaga idan zaiga wani mosque around, daddumansa ya shimfida yayi salla ya idar yayi shiru yana tunanin Asmeey, wlh abukace yake, he needs matarsa, he needs her beside him, ga sanyi yanaji, takalmin data sayamai ya kalla, sai kawai yadaura hannu saman maransa yayi addu’a, Allah ya dubesa sai kawai gaban nasa ya kwanta, Al’Qur’aninsa yakaranta har saida gari yasoma haske sannan yatashi yashiga bayi yayi wanka yafito yahada coffee yasha da dan dambun naman Mamie ya maida komi fridge yadawo daki yafara shiryawa. Shiryawa yayi cikin wani black suit daidai jikinsa dayamai bala’in kyau, ya daura necktie yasa covershoe, kagansa bazaka dauka Hamad bane he’s fair so he look American sef, kallon madubi yayi saiyaga kaman bashiba gabansa faduwa yayi, he’s feeling nervous, wat if yakasa introducing software nasa da kyau? What if he got shy? What if he stutter? Agogo ya kalla is 9:58 hakan yasa ya zauna yadauki wayarsa Mamie yakira dake zaune kusada Asmeey data gama kwara amai takoma bacci, Gwaggo tace zazzabin kawazucin Hamad Asmeey keyi, tashi Mami tayi tabar dakin sannan ta dauki wayan ganin number kasan waje da gudu ta dauka tace “Hamadi” murya chan kasa yace “Mamie” kaman yana gabanta anatse Mamie tace “ya kake? Ya wajen? Kana lafiya? Menene yarona?” Dan shiru yayi sai chan yace “Mamie gabana nata faduwa!” Ahankali Mamie tace “mesa?” Dan ijiyan zuciya ya sauke yace “yau zan fara zuwa kamfanin by 11, yanzu goma na shirya but nakasa fita” ahankali yace “i am scared Mamie”dan murmushi Mamie tayi koda yana yaro he’s very brilliant but idan an kirasa za’a basa kyauta baya yarda yaje wani zubin saidai takama hannunsa yana boye fuskansa ajikinta suje, murmushi tayi tace “kayi azkar yau?” Gyadamata kai yayi yace “eh!” Anatse Mamie tace “being scared, feeling nervous is a normal thing and it’s okay dan kanajin hakan!” Mamie tadanyi shiru tace “kahadiye fears dinka! Face it! Kaikaci gasan nan so nothing can pull you down, kaje wajen nan kanuna musu kai jarumina ne kaji Hamadi?” Gyadamai Mamie kai yayi ahankali, Mamie tayi dan murmushi tace “they will love you cus nobody comes in contact da Hamadi na dabazai so shi ba, a ina zaka hadu da lawyer ka da Ya Mustapa yabada ku?” Anatse yace “a gaban building din” Mamie ta gyadamai kai tace “wuce kutafi kafin kashiga wajen ka karanta Allahumma Lasahala…..” gyadamata kai yayi yace “okay” saikuma ahankali yace “ina Asmeey?” Dan murmushi Mamie tayi taboyemai tace “suna tareda Munir a parlor yasata kallon cartoon, ta warware so don’t u worry” dan ijiyan zuciya yasauke yace “tom Alhamdulillah, bye Mamie” “bye Allah yabada sa’a” karfi yaji ya shigesa yamike yadauki jakansa da laptop dinsa ke ciki yafito yawuce kofa yana budewa security na tsaye yace “good morning Sir” Gyadamai kai Hamad yayi, yasa hannu ya karbi jakan Hamad suka wuce kasa yau wata arniya benz aka daukesa da ita yashiga baya har champagne an ijiye masa but baitaba ba bayashan alcaholic drink, he’s feeling nervous wayansa ne yay kara, lawyer yamasa message ya iso suna kaiwa suka daukesa yace “Hamadi kaine ka girma haka?” Adan kunyace Hamad yayi murmushi tunda yazo sai yau yaga wanda ya iya hausa shima bawani sosai ba dan anan aka haifesa, hutu kawai yake kaisu Nigeria, ciki suka shiga kai Hamad baitaba ganin kampani haka ba mai kyau, parking sukayi suka fito Lawyer mai suna Kamal ya gyarama Hamadi necktie da suit nasa yace “Masha Allah kayi kyau muje” security yayi gaba suka shiga elavator sai sama 15th floor sukaje kofan na budewa Hamad yaga mutane ma’aikata maza da mata sunkai 100 ana tafi sosai ganinsa. “Welcome Mr Hussain!” Sai chan gawani mutum dayaci mahaukacin hadadden suit yazo wajen rikeda flowers yakalli Hamad dan sunada hotonsa da komi na passport yamikamai flowers yace “welcome champion, Mr Hussain Hamad Abubakar! We are honored to have you here” kan Hamad na kasa ya karba yace “thank you Sir” CEO ya tsaya yana kallonsa sai yayi murmushi love at first sight sunada wani believe na yaro mai kaman disorder disorder haka are damn genius, a resume na Hamad he made mention he’s a shy person bayason too much crowd, and pictures and seeing him in reality sai yaji damn he love the guy, hannu yamikama Hamadi alamun gaisuwa dan kallonsa Hamad yayi looking somehow wired kafin ahankali yamika masa hannunsa yayi murmushi yace “let’s go” wucewa sukayi tareda Hamad lawyer da some team na biyeda su abaya, Hamad baitaba ganin conference room this fine ba zama akayi ga bottle water agaban kowa sannan aka fara main event din, aka bama Hamad main floor yamusu introducing software din kafin asalin rannan lunch. Tashi yayi daga kujera dauke da system dinsa ahankali yatafi gaban smart board ya kunna system nasa kowa na kallonsa gabansa nadan faduwa saiya tuna da Mamie then Asmeey then Ya Mustapa, addu’a yadan karanto aransa, babu wanda yama gayamai ga yanda zaiyi connecting system dinsa to smart board din kawai yayi yadauki remote sannan ya kalli kowa na dakin da full confidence cikin harshen turencin sa mai dadi da zaki just simple layman accent yace “good morning ladies and gentlemen, I’m Hussain Hamad Abubakar from Nigeria and I designed this software name it SOFT AI, so what makes this SOFT AI different from all other

Chapter 35 of 56