Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taga yafito kam machine tabisa taga gidansu. Komawa cikin gida yayi Mamie yagani a dinning ta ijiye abinci da kula a tray tana ganinsa tace “zoka daukan muku abinci” karasowa yayi tace “this pepper soup na Asmeey ne zai rage mata ciwon cikin” gyadamata kai yayi yadauka yawuce sama kofa yabude yashiga Asmeey is still sleeping ijiye abincin yayi he’s hungry jiya baici wani abincn kirki ba white rice da stew yadeba kadan yakoma desk dinsa yafara ci yana taba system wayansa yakalla saiyasa hannu ya dauka watsapp yashiga yaduba block yaga number yafito wajen calls yaduba shima yaga block saiya juyo ya kalli Asmeey saiyayi shiruuuu sai kawai yayi murmushi yamaida wayan ya ijiye yacigaba da cin abincinsa. Wuraren 2:30 ta farka baccin yamata bala’in dadi yau dan motsi tayi hakan yasa Hamad yajuyo da kujeran ya kalleta saikuma yatashi yazo wajen gadon yadan kalleta suna hada idanu tasauke idanunta, mugun kunyanshi takeji tun jiya bata iya hada ido dashi dagota yayi tamike tsaye murya chan kasa yace “are you feeling better now”? Gyadamai kai tayi murya chan kasa na bacci tace “zansha coke Ya Hamad” dan dariya kadan yayi yace “I guess this is the period carvings dana karanta dazu” yayi maganan ahankali yana wucewa da ita bathroom nasu kayanta taga ya wanke akunyace ta sunnar da kanta ruwan zafi yatara mata a bucket sannan yafito drawer yaja yadauki ledan pad da pant yawuce nayin yasake knocking yabude ya ijiye mata komi yawuce yafita Asmeey tabisa da kallo he’s so damn caring, he just knows everything. Kusan 10min tabata abayin tafito tray tagani na abinci ya ijiyemata agado ga coke mai sanyi dasauri ta dauka coke din tana kokarin zamaya shigo hararanta yayi akunyace ta sauke kai magungunan ta ya dauka yabude su yazo gabanta ya tsaya ya mika mata karba tayi tasha da coke Ya Hamad kawai ya girgiza kai ganin she’s in coke era yawuce ya zauna, pepper soup tasha taci rice itama kadan rannan haka suka wuni he was just taking care of her kaman kwai ko fita palor batayi ba all through rannan, Mamie ma saidai tazo ta gaidata daga kofa batare data shigo ba. ****** Bayan 4days Yau day5 na MP! Kwata kwata batasan tanada son bacci hakaba sai agidan nan ashe ta iya bacci, babu abinda takeyi wlh tsinke bata dagawa, Ya Hamad yajuyo gyara daki ya wanke mata kaya yamata guga yakaita bayi yahada mata ruwan wanka yafito mata da kayan sawa yakawo mata abinci yabata magani iyakanta, tai wanka tashafa mai tasaka kaya sai kyau take kara yi Ya Hamad yasayo mata wani cream mai kyau na Olay da shower cream dinsa, fuskanta ya warke tsaf kaman ba’a taba marinta ba jikinta ma haka sai yan tabon da baza’a rasaba, kullum tana daki especially this days kuma Ya Hamad bai kara mata komiba dudda baida magana baida yawan surutu but idan yana kula da ita is as if he’s communicating with her. Yau Saturday around 11:30AM ta farka Ya Hamad tagani gaban desk dinsa yakifa kai yana bacci murmushi tayi tashi tayi tabude wardrobe ahankali tadauki wani lace baby pink taciro yau kawai tanaso tayi gayu bayi tawuce dasu tai wanka ta shirya tsaf abayin tafito, cream ta shafa ta feffesa turare saita saka kwalli bata iya tasaka dan kunne da daura dankwali ba man baki tashafa taciro baby pink veil dinta tajuyo takalli abincin dake wajen bataso taci, indomie kawai takeso taci slippers ta zura tana gyara gyalen kanta tabude kofa tafice, ahankali take tafiya muryan su Abba taji a falo da yayinsu harda Gwaggo wani kunya taji kaman ta koma daki but tasan sun ganta hakan yasa tashiga saukowa kanta akasa, shi karan kansa Abba daya ganta saida yace “Masha Allah Asma’u, kin fito”? Gwaggo tace “yau kwanan ta nawa gidan nan jibi yanda yarinya tai kyau jama’a daman Asama nada kyau haka”? Hameed yace “ta ina zamu sani kullum muna ganinta da kumburaren kumatu da lips da jan idanu” Mamie ta hararesa yayi shiru, karasowa falon tayi akunyace tana lullube bakinta da gyale tana murmushi tace “Abba ina kwana” Gwaggo tace “toh mayafin zakisa abaki” murmushi Abba yayi yace “lafiya lau yarinyana ya karfin jiki ya hannu”? Ahankali tace “fine” Mamie tace “kinyi kari?” Girgixamai Mamie kai tayi ahankali tace “indomie zanje na dafa” Mamie tace “zaki iya dafa indomie da hannu daya konasa Lami ta tayaki dafawa ai tana kitchen”? Akunyace sabida yayinta tace “zan iya Mamie” takalli su Ya Mustapa tana rufe fuska tace “Yaya ina kwanan ku” duk murmushi sukayi Ya Mustapa yace “rannan Monday zakuzo asibiti za’a bude hannun ayi xray agani” gyadamai kai tayi, Ya Abdullah yace “Amarya anyi fresh” dariya Faisal da Hameed sukayi tawani lullube fuskanta cikeda iskanci Faisal yace “mijin naki fa?”Bata gane sarcasm dinsu ba hakan yasa da zuciya daya tace “bacci yake Yaya” Hameed yace “wayyoo Allah na aure, Abba ai gobe ne zuwan ku gidansu Zee ko”? Dakuwa Abba yamai yace “kaci mai garinku Hameed” Gwaggo tace “ahap na gayamaka idan baka aurar da takadirin nan ba saiya hanamu zaman lpy agidan nan” Mamie takalli Asmeey tace “jeki dafa indomie ki” gyadama Mamie kai tayi tamike tawuce kitchen har Gwaggo kallonta suke, Asmeey tayi kyau, tayi fresh sai sheki take, tawani kara kumari tayi haske ga fara’a a fuskanta. Gwaggo tace “wlh banyi nadaman wannan aure ba, aiko jiya Muhammadu Sani yakirani nake gayamai idan yaga yanda yarsa ta chanza zai rantse ba Asmeey bane toh babu mai dukanta kullum saidai naga Hamadi ya goyo wannan jakan katuwa ya sayawa matarsa kayan dadi yawuce sama baya sammin” duka yayyin saida suka wani harari Gwaggo, Faisal yace “kaga Gwaggo da magana ke matarsa ce dazai sammiki”? Gwaggo tace “yoh to ubanwa ya haifi ubansa? Baniba tunda dai shine mukeda shi agidan nan mai mata ai kamata yayi yakawo kayan dadin sai nima asammini nasa albarka” tashi Abba yayi yace “bari nadan kwanta yau natashi da ciwon kai” duka yaran harda Gwaggo sukace “Allah sawake Abba” wucewa yayi Mamie tabisa abaya yayyin suka cigaba da zama, ka’ida rannan asabar tareda iyayensu suke zuwa suyi breakfast idan ba sunada wani abinyi ba basa barın gidan sai wuraren azahar. Kusan 15min Asmeey tayi a kitchen tagama dafa indomie guda daya da boiled eggs guda biyu tarike Fanta mai sanyi a hannunta tafito daga kitchen ta ijiye a dinning Gwaggo tajuyo tace “bazaki kawo muci tareba” aiko su Yaya suka mata chaaaa. Ya Abdullahi yace “wai bazaki bar kanwar mu tayi kiba ba?” Faisal yace “kaga uban abincin dataci taci dumamen Abba, tasha shayi da bredi da kwai, ina kallo saida taci soyayyan dankalin Ya Doctor, takora da yoghurt” Gwaggo tace “nifa inzomin ko menene takirashi bantaba ci ba shine nakeso na gwada ci naji, mijinta yanda sayo mata shi kwali guda ni bai siyamin ba sabida bakin hali sonake na dandana wlh idan da dadi Hamadi saiya sayo tawa” daidai lokacin akai knocking kofa Asmeey na kokarin zama a dinning da sauri ta kalli kofan, itane karama bai kamata tana falon yayyinta su tashi bude kofa ba besides ma tunda har akai knocking baki ne dan duk dan gida kai tsaye suke shigowa daki, fitowa tayi daga dinning zatai kofa Ya Faisal yatashi yace “koma kici abincinki I will get the door” Kai tsaye yawuce kofan suna swalle Gwaggo yana kallo falon direct ya hangame kofan. “Ina yini” duk suka jiyo muryan mace dayasa kowa yajuyo har ita Asmeey dake kokarin komawa dinning tajuyo, wata matashiya ce zata girmi Asmeey zatayi age mate da Ya Aysha akalla she’s 25 ko 26 sanye dawani abaya black mai kyau hannunta rike da iPhone da handbag tadan kallo cikin falon idanunta suka sauka kan wata kyakkywan yarinya fara kaman baturiya sanye da lace tayafa mayafi ga gaban gashinta na showing anmata kitso kanana masu kyau, yanda ta tsare Asmeey da kallo yasa Faisal yace “helloooo lafiya wakike nema?” Dan murmushi tayi kadan tana kallon Ya Faisal tace “sunana Aneesah! Hamad nake nema!” Wani wawan bahaggon bugawa gaban Asmeey yayi taji zuciyanta kaman anyi spraying pepper spray, kowa na dakin hatta Ya Mustapa saida yajuyo for the first time jin Hamad ake nema yana kallon yarinyar yagane ta that parking space girl, Gwaggo takara gwalo idanu tana kallon yarinyar mai neman Hamadi, murmushi Aneesah tasakeyi tace “sorry nazo muku gida Hamad nake nema, you all nasan baku sanni ba but shi yasanni the other day we were together ni da shi a kofar gidan nan we spoke for a while, shinazo nema please yana ina?” Yanda zuciyan Asmeey ke zafi da daci batasan sanda tace “baya nan!” Kallo komawa kan Asmeey yayi harshi Faisal saida yajuyo yakalli Asmeey data hada fuska tamau kaman bata taba dariya ba, Aneesah ta tsare Asmeey da idanu kaman yanda Asmeey ke kallonta ana kallon kallo daidai Hamadi yahayo staircase yashiga saukowa kwata kwata koda wasabaima kalli kofa ba so baimasan meke faruwa ba yakarasa saukowa daidai idanunsa na sauka kan Aneesah dake door entrance nasu ga Ya Faisal agefe ga Asmeey tawajajen dinning tana kallon Aneesah yanda zuciyanta ke kuna bamata lura ko tajuyo kamshin ya Hamad ba, cikeda wani salo na rainin wayau Aneesah tace “wani Hamad ne baya nan? Cus ga nawa Hamad din danazo nema nan yafito” tanuna Hamad da Asmeey tajuyo da kanta da sauri ta kalla suka hada ido today is the first time yake ganin fire spark a idanun Asmeey sai kawai ya tsaya daga wajen da Asmeey take batare daya kalli kofan ba, murya kasa yace “I don’t know her!” Awani irin hankali da voice din that can pass to others as shagwaba Aneesah tace “dan Allah kazo muyi magana just give me a minute banda lafiya ne I am very sick kaga drip aka samin” tanuna hannunta da kanula ke jiki, takawa Hamad yafara yi yawuce Asmeey dake kallonsa zaiyi kofa wani irin zuciya daya kwashe Asmeey batasan sanda tajuya kaman mahaukaciya tayi dakin Gwaggo dake wajen ta shiga jikake gammmmm! Tabugo kofan sosai da saida kowa na falon yayi motsi Hamad yajuyo yakallo kofan dakin Gwaggo yayi jinmmm sannan yadake yakaraso wajen kofan yasa hannu yakarbi kofan daga hannun Ya Faisal yama Aneesah wani kallo yace “the next time zaki kara zuwa nemana I will report you to the police as stalker, I’m a married man! Get out of my house” yana maganan yamaida kofan yarufe yasa key, kowa kallonsa yake cikin whispering da anaji karara Faisal yace “you’re doomed today!” Yanuna dakin Gwaggo da Asmeey ta shiga irin yau kashiga uku Hamad , Hameed dake murmushin keta yace “you are done for Hamadi!” Ya Abdallah yace “you’ve been cooked yau zakaga bala’in mata yaro!” Gwaggo tace “wace tijararra ce wannan datazo nemanka ta dagulama jikata zuciya? Yanzu jibi inzomin nata tabarsa bata ciba kuma babu abinci acikinta” dan kallon Ya Mustapa Hamad yayi asanyaye, Ya Mustapa yace “baruwana this is wat we married men face daily! Hakanan zaka nemo yanda zakai lallashi da bada hakuri da explanation, welcome to the club bro” zokaga dariya ganin yau Ya Mustapa bai shiganmai ba, tsayawa Hamad yayi wajen yamaida kansa kasa gwanin ban tausayi, shi yakasa zama, shiya kasa zuwa wajenta, shiya kasa magana, yakai kusan minti goma awajen saiya wuce duk suka bisa da kallo munafukai suna jiran suga yawuce dakin Gwaggo sai kawai sukaga yayi staircase, Gwaggo tace “yau anyi mara mutunci anan iyye ai shikenan! Kayi laifi katafi sama abinka.” EPISODE 3️⃣9️⃣ Tashi Gwaggo tayi tawuce dinning tadauki indomie ta tawuce dakin dashi tabude kofa tashiga ciki tana kallon Asmeey datahau gadon takifa kanta agadon tana kuka, Gwaggo tace “kiyakuri mana haka lamarin rijalu suke, amman karkija laifinsa haka mata ke binsa kaman zasu cinye, shi ba ruwansa dasu, tashi kici abincin” cikeda masifa Asmeey da Gwaggo takara kılar da ita tace “bazanci ba” Gwaggo takama baki tace “tohhh babban magana ai shikenan daga nazo lallashinki zakihau mini masifa shikenan nayi nan ku karata ke da shi” ta tashi tabude kofan tayi fitowanta tadawo wajensu Faisal ta zauna tana masifa. Faisal yace “dan Allah kona tafi Hameed call me kabani update yanda za’a shirya daga fadan nan” suka wani kashe shida Hameed, Ya Mustapa yamai wani kallo yace “tashi kabar gidan nan lokacin tafiya yayi infact kutashi all of us mutafi hardakai Hameed tashi kabini gidana I need you to do something, Gwaggo kema tashi muje” dasauri Gwaggo ta tashi tana warware mayafi dake kugunta, Hameed na kumburo baki yace “kai Yaya dan Allah nidai ka barni nan, to wazaiga reconciliation din wannan da harda Gwaggo zaka dauka” kunnensa Ya Mustapa yaja yace “kumuje” dukansu ya tattarasu badan sunso ba suka fice, Hamad na tsaye wajen window he’s so nervous yaga Ya Mustapa yadauki Gwaggo da Hameed a motarsa, sukuma su Ya Faisal kowa ya shiga tasa motar sunbar gidan dasauri yawuce kofa yashiga saukowa kasa direct dakin Gwaggo yayi kai tsaye yabude kofa Asmeey na zaune kan gado takifa kanta a kafa tana kuka jin an bude kofa yasa tadago kanta ganin Ya Hamad ne dauke kanta tayi ta tashi azuciye tasauka daga gadon zata wuce bayi taku daya yarike mata hannu wani irin fashewa tayi da kuka zata kwace hannunta tace “ka saken mini hannu ka koma wajen bakuwar ka” tashiga kokawa dashi yaki barinta, Asmeey tace “nace kasaken ka koma wajen bakuwarka data saba zuwa wajenka a kofar gida kuna hira, I don’t want to talk to you ,leave me alone” kin sakin hannunta Hamad yayi yana kallon idanunta yana shafamata hannu kirjinsa na bugawa sosai, yana kallon yanda take kuka idanunta sunyi jazur she’s seems very very hurt, ahankali yace “are you jealous?” Dakatar da kukan datakeyi Asmeey tayi dasauri takallesa da jajayen rinannun idanunta lips nata na rawa tace “jealous?” Itama ta tambayesa cus she’s genuinely confuse, batasan mesa she’s really hurt kirjinta namata zafi sosai ba, to mesa takejin haka? Kasa magana tayi sai kawai ta sauke kanta kasa tashiga kokarin fizge hannunta tace “ni kasaken ka koma, yau baku dade a hiran bane” dayan hannun yakama yarike yana murzawa, ahankali calmly yace “I don’t know her!” Sake fashemai da kuka Asmeey tayi tanason ta kwace hannunta zuciyanta na tafarfasa tace “amman ai tana zuwa maka hira ko”? “the other day nadawo daga masallaci naganta a kofar gidanmu” Hamad yafada trying ya wanke kansa, Asmeey da kishi ya rufe mata idanu tace “metace maka?” Asmeey ta tambayesa cikeda karfin hali dajin zafi, murya chan kasa mai taushi kuma Hamad yace “I can’t remember but I told her I’m married karta kara zuwa” kaman fa wacce she owns him Asmeey tace “toh metazo maka yau”? Lumshe idanu yayi awani irin hankali yace “wallahi ban saniba!” Yanda yamata rantsuwa saitaji zuciyanta yawani yi melting ya karaya it’s shows bayason tai fushi and he cares about her anger, he’s not saying sorry but he seems scared da yanda take fushi, dan rage tone din kukan tayi tace “to mesa kawuce ni kabita bayan nine matarka?” Dan wannan ne yafi cimata zuciya akomi, sosai Hamad ke kallonta, she’s really angry fa, she’s questioning him sosai, no wonder yayinsa sukace he’s done for, is she jealous of him? Ya tambayi kansa, ahankali cikeda muryan lallashi yace “ban bita ba, naje narufe door ne sainaga kin shigo nan” kallonshi takeyi tana making crying face saikuma cikin masifa sosai tace “duk randa wata yarinya tazo gidan nan wajenka duk abinda namata ita taja wlh, saina jijjima mutum ciwo, kuma takara zuwa tagani zata gayamin idan mijina nata ne mayya kawai mai biyo maza gida, classless girl kawai Husband snatcher!” Baitaba ganin Asmeey na masifa ba sai yau, and she looks damn cute, funny as well and lovely ganin akansa take fada haka, dan murmushi yayi karaf akan idanunta fashewa da kuka Asmeey tayi kaman yarinyar dake borin masifa, ashe Asmeey ta iya daru tace “okay I am funny ko? I look funny, murmushi kakeyi” dasauri Hamad ya girgiza kai yace “no nothing is funny My Baby” masifa da kishi yasa bamataji my baby ba, cikin kuka tace “toh why are you smiling? Kadauka da dadi wato tazo gidanmu tana neman mijina? Why are you smiling”? Ahankali yana kallonta sosai yace “you look cute when you’re jealous ne” yayi maganan yakai hannu yadan sosa goshinsa, Asmeey tawani kara kulewa cikin fushi ta fizge hannunta tace “to go and meet that girl tunda I am funny and I am jealous ne” tawani juya fuuuu zatayi kofa da sauri kawai Hamad yarungumota tabaya ya kulle hannuwansa acikinta kaman dan baby murya chan kasa yace “Hussyn Hamad! Don’t punish meeeee!”Shima yayi magana kaman dan baby so sweet, makemai kafada Asmeey tayi zatai magana kawai yawani juyoda ita yafizgota zuwa jikinsa kawai yahada bakinsu, kankarewa taji tayi da gudu ta runtse idanunta, tafiya Hamad yashigayi da ita, kawai suka fada gadon Gwaggo he’s kissing her totally lost kaman wanda wani abu ya shigesa just now, Asmeey na kokarin kwace kanta ahaukace Hamad yakai hannunsa kirjinta zai taba boobs nata dawani iron sauri takulle hannayenta akirjinta ta fizge bakinta tana tashi zaune tajuyamai baya da sauri ta daure hannayenta akirji tana wani irin nishi kaman zuciyanta zai fito, yakai kusan one minute ahaka sannan yataso zaune yazo ta bayanta gently yadaura fuskanta abayanta yana maida ijiyan zuciya just like her yana shakan kamshinta, ahankali yace “wash your face I will bring dankwalinki and shoe let’s go out zaki fita?” Dasauri ta gyadamai kai kirjinta na bugawa, mikewa yayi yasauka daga gadon yawuce kofan Gwaggo saikuma ya kifa kansa jikin kofan yana dan huci so yake gabansa ya kwanta he’s wanting Asmeey sosai! Kusan 2mins yayi sannan yabude kofan yafice ahaka yana addu’a Allah karya fito dako Abba ko Mamie, daki ya shiga yafada bayi sai chan yafito wallet dinsa yadauka da key yawuce yadauki dankwalin kayan data saka dawani black flat shoe da handbag yadauki wayanta yasa aciki ya kashe wutan dakin yasauko kasa yadawo dakin Gwaggo, ta wanke fuskanta tana zaune yana shigowa tasauke kanta kasa, zuwa wajen yayi ya warware dankwalinta yashiga dauramata yau yadanyi kokari simple daura saiya dauki veil dake gadon ya rufa mata yabata handbag karba tayi yamika mata hannu, kin karba tayi ta tashi tana zura takalmin ya kalleta tayi kyau wlh shima haka yana sanye da native farin yard, hannunta yakama suka fito taki yarda su hada idanu, fitowa waje zuwa wajen machine dinsa yana gogewa yana kallonta bata taba hawa machine ba, wayansa yaciro yama Mamie text sun fita sannan yahau kan bike din ya karkato matashi sosai yace “hau” dan kallonsa tayi kafin ahankali takai hannu ta dafasa tahau machine din, kunna machine din yayi yay horn mai gadi yabude musu yaja machine din ahankali yafice mai gadi yabisu da kallo sunyi bala’in kyau! Wani irin murmushi Asmeey tayi feeling very safe tana bayansa babu wasu mutane anguwansu dayake na masu kudi ne, suka fito suka shiga titi baya wani gudu sosai da ita, wani restaurant mai bala’in kyau yakaita cosmo parking yayi ta sauka ahankali tana dafasa yasauko ga few men awajen kawai saiya rike mata hannu yace let’s go. Shiga sukayi dakansa yaja mata table tazauna aka kawo musu menu ya karba yabata yace “order” kasa kallonsa tayi ta karba ahankali tana kallo tai jimm kafin ahankali tashiga fadin abinda takeso, tasan baya aiki baida kudin kaman su Ya Hameed, duka abinda tai order was 11,500 Hamad ya karba sai kawai taga yashiga bada order da yawa, jiya he design website for wani an biyasa 150k just last night, even though his plan is yabama Mamie 100k afara sayama Asmeey kayan akwati but he don’t mind spending everything on her now he will work hard again yasami kudin yamata akwati saiti like every other girl. Wucewa waiter yayi bayan yagama musu placing order, ahankali yasa hannu ya dauki hannunta dasauri ta kallesa saikuma tadan kauda kai murya chan kasa yace “stop being Angry nadinga saka nikaf”? Gyadamai kai tayi yayi murmushi kadan kaman irin masoyan nan sunzo outing, daidai nan aka kawo musu order su, mamaki tayi ganin abubuwan daya musu order harda drinks masu hayaki zuciyanta yayi wani iri dan tasan baida kudi and taga Menu su da tsada abinda tai order was the cheapest one, wucewa waiter yayi, ganin abubuwan daya musu order sai taji zuciyanta yayi wani iri dan tasan baida kudi, he doesn’t have, taji wani tausayi da ya taso ya tsayamata azuciya saitaji kuka yazo mata cus tasan sabida fushin datayi yasa zai kashe kudi haka yakawota nan just to make her happy haka, hawaye ne yasauka daga idanunta dasauri takai bayan hannunta ta share, kallonta Hamad yayi saikuma yataso dasauri yazo dab da ita looking seriously worried ganin she’s still not happy, awani irin hankali yace “Asmeeey” dago idanunta tayi takallesa hawaye sun ciko sosai ga mamakinsa kawai rungumeshi tayi tafashe da kuka ajikinshi mara kara sosai sai jikinta dake rawa wlh ya mugun bata tausayi, murya chan kasa tace “I’m sorry Ya Hamad!! I am making you spend plenty money! Bazan kara fushi ba kayakuri wlh it’s not your fault nasani, I’m sorry” dawani irin sauri yadagota sai kawai yashiga patting back dinta batare daya damu da mutanen wajen ba, issue yadauka nakan table din yakai fuskanta yashiga sharemata yayi murmushi murya kasa kasa yace “waya cemiki u are making me spend? You are my wife I am not even doing enough! You deserve much more than this sabida you are My Queen okay” ahankali yace “I want to be a husband to you just like Annabi Muhammad SAW is to matayensa! Loving! Kind! Helpful! Romantic! Playful and sweet! Don’t think of tommorow! Kudi da arziki na Allah ne! Allah daya bani yau nakawoki nan shizai bani gobe! Have faith in Allah Husnah, I am sure he will give me enough to give matana duk abinda takeso, it’s okay!” Gyadamai kai tayi feeling calm, kalaman shi were so soothing ma zuciyanta, bata tabaji yayi dogon magana hakaba sai yau, sake kallonta Hamad yayi still looking worried yace “don’t cry again, everything here is for u! Idan bai isheki ba akaro, now eat” gyadamai kai tayi tadauki spoon tafaraci just sabida to make him, sai kallonta yake, dan kallonsa tayi tai murmushi kadan ahankali tace “kaima kaci” ijiyan zuciya ya sauke ganin she finally smile, gyadamata kai yayi yadauki spoon yafara ci sunayi suna kallon junansu bini bini just like lovers da basu riga sunyi aure ba. AWWN GRADUALLY GRADUALLY HAMAD DA ASMEEY ARE DEVELOPING DEEP LOVE BOND! LOVE STARTS FROM TAUSAYI DAKUMA DAMUWA DA JUNA❤️ ASMEEY GENUINELY LOVE HAMADI WLH!❤️ HAMAD LOVES MATARSA LIKE A FOOL! YACE MY QUEEN!❤️ YA FOLA GABAKI DAYA INA GAYAMUKU❤️ SU HAMADI MAI KOYI DA FIYAYYEN HALITTA SAW! EPISODE 4️⃣0️⃣ Sosai taci abincin takoshi yakira aka mata takeaway komi sannan yabiya da card dinshi, ya kwasan mata komi yarike yana kallonta suka fito sukahau machine, cold stone ice cream ya wuce da ita sai murmushi take the joy in her face means everything to him, hannunta yakama suka shiga ciki yace “choose flavors dakikeso” gyadamai kai tayi sai murmushi take tashiga nuna musu, 3 cups yasa aka mata sauran tasa a fridge, sai murmushi take tace “thank you Yaya” she looks very happy suka fito, hawa machine sukayi ahanya suka sayama Mamie fruits sannan suka taho gida wajajen 4 sai murna Asmeey take taji dadin fitan sosai, Mom na kaita eatery a Bauchi iron idan sun tashi daga office but Mom ke order komi, bata taba samin privilege na tayi order abu da kanta ba sai yau, eatry ma bawai ita Mom ke kaiwa ba dan kanta take zuwa. Baitaba sanin zai iya tsayawa and get hug a public ba sai yau and baidamu ba, karasawa gida sukayi aka bude musu gate daidai Abba da Mamie na fitowa compound din Mamie na raka Abba zuwa wajen mota, wani kunya Hamad yaji itako Asmeey is so happy, duk manyantakan Abba saida ya kallesu saiyaji he’s really proud of Hamad maganan Ya Mustapa na kara dawomai fresh a mind, gashinan gradually Hamad is changing kaman ba shi ba baijin Hamad ya taba daukan wata a machine dinnan nasa ba sai yau, saukowa Asmeey tayi

Chapter 25 of 56