Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
rainanku ana haihoka na karbeka na rike, saida tasake nakuda nakusan awa guda cur sannan ta haihosa shima na amshesa, baka gansa ba lokacin gabaki dayansa yayi kalan ruwan kwai wai jondus (jaundice) aka haifesa da ita, ga uwarsa ba lafiya haka nina dinga lura daku har taji sauki, kai kasha madara amman akai juyin duniya shi yasha yaki hakafa uwarku na cuta da bamata hayyacinta aka kamasa aka daurasa kan mama yasha, halama saisa yake cuta kullum sabida ya zuge na jikin uwarku alokacin, saida aka cire mata mahaifa gabaki daya kuma shine yakusan kasheta dan yaki fitowa daga ciki, kuma shine tundaga asibiti har yau yake damunta da cuta daban daban ai ban manta dakomi ba, nida nai wahalar sa wai nine yanzu zai taso ya tsana bayaso” dariya kawai Hameed kerike wa yace “toh kiyakuri Gwaggo” Mamie tadade tsaye gaban dakin sannan tabude kofa tashigo Gwaggo ta watsamata harara Mamie ta kalli Hameed tace “ina yake?” “He left the room Mamie” Mamie tadan kalli Gwaggo tace “Gwaggo kiyakuri tashi muje” kaman jira Gwaggo take tace “ohh Allah kana gwadamin ni kike cema nazo nafita daga dakin jikokina eh Batola kin rabani da Hamadi yanzu da Hassan zaki rabani shima” dan lumshe idanu Mamie tayi tabude tace “bahaka bane Gwaggo kiyakuri daman na dauka zaki sauka kasa ne bari naje” ihu Gwaggo tahau yi tace “eh kitafi wlh duk abinda akemin agidan nan zan sanar da Abubakar duk anbi an rabani da jikokina” ijiyan zuciya Mamie ta sauke tawuce tafita direct dakinta tawuce tabude tashiga Hamad na kwance kan gadonta jin an bude kofa ya kallo kofan daure fuska Mamie tayi tareda folding hands a kirji tace “wat are you doing here? Ba cewa nayi zan kawo muku abinci kaida Hameed ba”? Dan sauke kanshi kasa yayi yace “I’m not hungry” karasowa dakin Mamie tayi zuwa gaban gado tadan sassauta murya tace “mesa kabar dakin sabida Gwaggo? Cinyeka zatayi? Why do you always make her cry eh Hamadi? Can’t you see how she deeply loves you eh? She was worried sick sabida kai, the least you could do is kadan zauna ko bazaka kulata ba seeing you makes her happy, Hamadi why are you like this eh? When will you stop giving me headache? Yaushe zaka chanza halin nan eh? We are your family idan kayi haka awaje it’s okay but us fa, banda mu wa kake da shi? Mesa kake gudun Gwaggo not just she kowa ma why why why Hamad? Kullum ina daga kafa ina cewa ka girma zaka dena idan yanzu your 33 baka chanza ba sai kakai 50yrs zaka chanza eh?” Kanshi na kasa yana sauraron Mamie murya ciki ciki asanyaye yace “sorry Mamie” cikin fushi tace “I don’t want your sorry katashi kaje kuci abinci and tell her sorry” gyadamata kai yayi yatashi zaune ahankali sannan ya sauka daga gadon gently sabida ciwo yawuce ta gefen Mamie yafice tabishi da kallo tai shiru tana nazarin sa, Hameed na zaune yafaracin wainan Gwaggo namai zuba Hamad yabude kofan da sallama chan kasa ya shigo daga Gwaggo har Hameed suka bishi da kallo, Ya tsaya awajen yakasa tahowa ciki Hameed yadauke kai yacigaba da cin abinci abunsa Gwaggo tace “taho zokaci abincin ka kona maka fura zaka sha?” Girgiza mata kai yayi yana tsaye bai kalleta ba, wani washe baki Gwaggo tayi tace “yauwa toh dan Albarka zoka zauna kaci ko guda daya ne kaji” ahankali ya shiga tahowa Gwaggo ta matsamai da sauri gently yazo ahankali yashiga zama yadan kama gefen cikinsa Hameed yabishi da kallo Gwaggo tace “Wajen aikin ka kema ciwo?” Girgiza mata kai yayi yajuyo yasa hannu yadauki spoon ya gutsiri masan kadan yasa a miya yakai baki dan yatsine fuska kadan yayi Hameed yace “is it too spicy for you?” Girgizamai kai yayi yana taunawa kaman wanda akasa dole yaci, Gwaggo dake kallonshi batako kyafta idanu tace “miyan yayi yaji ne”? Girgiza mata kai yayi daidai ana bude kofan wani magidanci dake kama da Ya Mustapha yashigo rikeda yaro a hannunsa yana kallon Hamadi yace “Hamad ya jikin?” Dan kallonshi yayi daidai yaron yasauka daga jikin Babanshi yataho wajen Hamadi da gudu daukanshi Hamad yayi for the first time yasaki murmushi sosai dimples dinshi suka fito da white fararen hakoransa yaron ma ya k washe baki, Gwaggo tace “Areef narasa meya gani a jikin Hamadi dayake sonshi haka” karasowa cikin dakin Ya Abdallah yayi yace “ai ba Areef ba harsu Akram da Abdool dukansu haka sukeson Hamad, Areef oya come Uncle Hamadi is sick today” makema Babansa kafada yaron yayi, Hameed ya ballama Areef harara aiko ya tsala ihu yana shiga jikin Hamad garin haka ya takemai ciwo wani kalan runtse idanu da karfin gaske Hamad yayi dayasa Hameed da sauri yadaga Areef yana karbansa, Abdallah yace “Subhanallahi Hamadi, sannu, Hamadi” Gwaggo tace “shikenan Areef yatakemai wajen aiki duba kagani ko wajen na jini Abdullahi” jin haka asauri Hamadi ya daura hannunshi awajen murya chan kasa dake fita da kyar yace “I’m fine” bottle water Abdallah yadauka yabashi amsa yayi yakai bakinshi yasha kadan duk sukai shiru suna kallonshi barinma Gwaggo, akufule da karaman murya yace “kudena kallona” “mundena” Gwaggo tace amsa da sauri, Hameed yatashi yana sauke Areef yawuce bayi, yace “it’s time for magrib” Gwaggo tace “Abdullahi kaga nima kamani ka kaini kasa” kamata yayi suka fice, Hameed daya fito yajira Hamad shima yadauro alwala suka fito suka wuce masallaci. Suna magrib suka dawo gida da sallama suka shigo falon, Abba suka gani zaune a falo dayake kokarin cin tuwonsa na dare, duk yayyinsu na falon, Hameed yawuce dinning yazauna tareda Faisal suna danna waya, sai Ya Mustapa zaune wajen Abba tareda Abdallah sai Mamie dake zaune a gefensu, karasowa ciki yayi dukansu suka kalleshi harda Abba daya dakatar da abincin dayake ci ya tsareshi da idanu irin kallon da uba kema dansa na nazarin yanayinsa din nan da kula, sauke kansa kasa Hamad yayi yakaraso har wajen yadan duka cikin muryanshi mai cikeda natsuwa yace “sannu da zuwa Abba” anatse Abba na lurada shi yace “jikin yahanaka zama karatun dakukeyi a masallaci bayan magrib ne?” Gently ya gyadama Abba kai batare dayayi magana ba, Abba yadan jinjina kai yace “Maman Doctor yaci abinci kuwa?” Anatse Mamie tace “kowa yaci abinci banda shi” kallonshi Abba yayi babu wasa kan fuskanshi yace “zonan kaci abinci, Doctor bani maganin dazaisha na dare” ba musu yataho yazauna gaban Abba kanshi akasa Faisal da Hameed suka kalleshi, Hamad yadan dago kanshi yakalli Ya Mustapa daya kawo maganinshi Ya Mustapa yamai wani kallo yace “eat my friend” maida kanshi kasa yayi Abba yabashi spoon dayakecin tuwon dashi ya karba ahankali shi Abba yasa hannu yace “oya bismillah ci zakasha magani” ahankali yafara ci Mamie na kallonshi yaci kusan 5spoons ya ijiye spoon din ahankali, Abba yace “ka koshi?” Gyadamai kai yayi Abba ya wanke nashi hannun tsaf yadauki ruwa yasha ya ijiye cup hakan yasa ahankali Hamad ya mika hannu zai dauki plates din da Abba yagama cin abinci dasu yakai kitchen Abba yace “barshi bakada lafiya” sai kawai Abdallah yatashi ya dauka dan yaran sunada tarbiya da kyau, yana dauka Hameed yazo da sauri ya karba yawuce kitchen, Abba ya tsare Hamad din da idanu da kansa ke kasa anatse yace “meke maka ciwo yanzu eh Hussain?” Kanshi na sunne akasa yace “bakomi Abba naji sauki” Abba yakalli Ya Mustapa bawasa kan muryansa yace “meke damunsa likita ance kaduba sa dazu? Tell me menene matsalan?” Ahankali Ya Mustapa yace “Abba he got infection, rashes sun fito wajen stitches dinsa, I think maybe from ruwan wanka or sabulu or it could be anything, nayi dressing wajen dazu I will still do it yanzu sai yasha maganin” Abba ya maida dubanshi ga Hamad da kansa ke kasa, cikin murya mai tsauri yace “bakaga kuraje a wajen ba da bazaka fada ba eh Hamadi? Bazaka iya kiran Yayanka ka gayamai ba ko Mamie ko ni? Kana kallon ciwo jikinka kaki magana kai yaro ne wai? Inda wajen ya rube fa? Halaka kanka kakeso kayi? Bazaka dena abubuwan nan ba ko mutuwa kakeso kayi kahuta mesa kake haka ne”? Murya chan kasa kanshi akasa yace “kayakuri Abba” dan ijiyan zuciya Abba ya sauke yace “tashi muje Doctor yamaka dressing din aka gama saikasha maganin, tashi” ahankali yatashi ba musu bai kalli kowa na dakin ba yawuce stairs Mustapa yawuce yadauki jakar dake kan kujera daya ijiye yawuce sama Abba yabisu bayan ya dauki ledan magungunan. Yana shiga dakinsu kwanciya yayi akan gadonshi ahankali daidai Doctor na shigowa dakin yazo wajen gadon yana kallonshi yace “how are you?” Ahankali yace “Yaya key the door pls” wani kallo Dr yamai sannan yabude jakan yashiga ciro hand gloves nashi daidai Abba na shigowa dakin da sallama. “Assalamu Alaykum” Hamad ya sauke kanshi kasa kaman yayi disappearing yakeji, ahankali Abba yazo wajen gadon ya tsaya yana kallon Hamad din dayaki kallonsa yayi folding hannuwansa a kirji, Mustapa na hada komi sannan yazo gadon yakai hannunshi zai dage riganshi Hamad yadan rikemai hannu sabida Abba, Abba dake kallonsu yace “wai mehaka Hamad” sakin hannun Ya Mustapa yayi ya runtse idanu kawai, Dr yadan dage t-shirt nashi sama zaija wandonsa kasa kadan Hamad yarike hannunshi yadan kalli Abba daya haderai yace “sakenmai hannu yayi aikinshi kadade bakaji kunya ba shirmen banza da wofi, kunyan ai shi yasaka a wannan condition, da tunda kaga abin kabi Yayan naka asibiti yabaka magana da tuni anyi an wuce wajen, cikamai hannu nace” sakin hannunshi yayi ahankali, Ya Mustapa yaja wandonshi kasa maranshi yafito har zuwa wajen walls nashi ga hair kadan akwance ana gani ya runtse idanunshi sosai kunya kaman zaiyi ihu, Abba dayaga ciwon cikin bacin rai yace “look at wat he did to kanshi bakasan kunya na halaka mutum ba, kuraje na fitowa haka ajikinka ka kasa fadama kowa alhalin kanada Yaya likita, ga sauran yan uwanka, ga mahaifiyar ka, gani duka, wannan wani irin abune wandonka za’a cire gabaki daya dakake irin halin nan kaniyanka da abinda kake boyewa” daidai Ya Mustapa yafara goge ciwo mugun ijiyan zuciya ya sauke dayasa Abba yayi shiru da fadan dayakeyi ganin abin namai ciwo sosai yadena fadan yahakura, Doctor ahankali yace “sorry” daidai lokacin aka bude dakin duk yanda yakejin zafi saida yakai hannu yaja wandonshi zai rufe Abba yace “wai mehaka Hussaini eh”? Abdallah ne yashigo dakin sai Faisal biyedashi tareda Hameed suka maida kofan suka rufe, cikeda masifa Abba yace “cigaba da aikinka kaji sun ganshi din ba yan uwansa bane” da kyar cikin karfin hali yace “sufita! I want my privacy” dan murmushi Ya Mustapa yayi kana ganin Hamadi haka kaman ka samai y’ata baisan yanda ake taunawa ba silent rigimamme ne wlh, Abba da ranshi yagama baci yaci “kaci me garinku da privacy, babu inda zasu hukuncin ka kenan, next time wani abu yakara samunka kaki fadi haka duk zamu taru akanka idan kuma bakason haka kabi yayanka asibiti kuyi abunku ku biyu” sai kawai Abba ya zauna abakin gadon yana karbe hannunshi daga wandon yarike yace “bude ka cigaba Mustapa” ahankali Ya Mustapa yaja wandonshi da boxer nashi kasa but this time sai baija kasa sosai ba ganin yanada kunya and yan uwan shi are there, dudda Abba ya lura da abinda Mustapa yayi sai baice komiba hasalima hakan yamai dadi tunda haka Allah yayo Hamad da shegen kunya, cigaba Mustapa yayi kowa tsaye daga yanda Hamad keyi da kafa kasan da zafi Hameed yayi wani iri da fuska idanunshi sukai jaaa, yana kan gyara stitches din sai kawai ga hawaye sun fito daga idanunshi na azaba dasauri Hameed yajuya yafita daga dakin idanunshi sunyi ja, hannu Abba yasa yakai yasharemai fuskanshi, saikuma ya sassauta murya cikeda so yace “ya isa kadaure Mustapa ka kusa gamawa ko”? Gyadama Abba kai yayi yana karasa dressing din su Abdallah na kallo, Faisal ma yakasa daurewa yajuya kawai yafice, Abba yakara sharemai hawaye sannan aka gama idanunshi sunyi jaaa, Mustapa yamai allura aka bashi magani yasha Abba na zaune dashi ahaka yace “sannu kadena rufe wajen da wando dan Allah Hamad ciwon ya warke, dagakai sai yan uwanka agidan nan kumama duk aiki suke zuwa kai kadai ke wuni so kafinga bari yanashan iska” gyadama Abba kai yayi Abdallah yace “sannu Hamadi” gyadamai kai yayi duk suna tareda shi ahaka bacci yayi awon gaba da shi sabida alluran Abba yace “yatashi yayi isha’i” Mustapha yace “kada kadamu Abba nan da 3 days ya warke” gyadamai kai Abba yayi yace “kuwuce kuma kutafi gida” bargo Ya Mustapa yasa ya rufamai sannan suka kashe wuta suka fice. 💫MOTHER OR CURSE? 💫 ✍🏻M SHAKUR OYA JOIN GROUP DINA INDA NAKE POSTING UWA KO UKUBA IDAN KINA CIKIN 1-8 DONT JOIN 9 PLEASE https://chat.whatsapp.com/HOfjHAh3gw5502DZ5uJTWn EPISODE 3️⃣ Around 10 nadare Hameed yashigo dakin wuta ya kunna yana kallon Hammad dake bacci mai nauyin gaske yawuce bayi ya watso ruwa yafito daure da towel yaje yasa boxer kadai yazo zai kwanta ya tsaya yana kallon Hamad, saiya tashi yakai hannu yasake gyaramai bargon dayake lullube dashi sannan ya kashe wuta yahau gadonshi, ya kwanta daidai wayanshi na ringing ya daga yakai kunne murya chan kasa yace “Zeezee” daga tachan bangaren tace “Ya Hameed baka kirani ba why is your voice so down haka kaman you are not happy wat is it”? Dudda akwai duhu juyowa yayi yakalli gadon Hamad ahankali yace “my brother is sick Zee” dasauri tace “subhanallah your twin? Wanda akama operation last week?”Gyadamata kai yayi yace “yes!” Murya chan kasa tace “ayyahhh so sorry Allah yabashi lpy, Ya Hameed kanason twin brother ka sosai” murmushi kadan yayi kaman bazaiyi magana ba yace “I don’t even love him as much as he loves me! Hamadi na sona sosai fa, he’s not much of a talker but actions nashi speaks love, anytime I’m sick baya bacci he stays all night yana kula dani, before nace kaza or nafurta i want kaza Hamad yamin is as if he reads my mind, kokuma my mind na jikinshi ne I don’t know but kaman magic, saisa anytime he’s sick jinake rayuwana ba dadi, sai narasa ina zansa kaina naji dadi, most times he knows we all get worked up idan baida lafiya saisa baya fada mana, he’s always sick ne yau mura, gobe kai gata kaza, he feels bad yana unnecessary damunmu shi ba sikla ba, even today bansan he was sick ba cus bayaso mu damu, and bansan why I didn’t noticed ba cus I’m always the first to know whenever he’s sick, I’m feeling very bad Zee I don’t give dan uwana dsame kind of love and care he gives to me” Zee tace “don’t say that, kanason brother ka sosai saisa ma har kakejin guilt din nan, anyways shi kadaine ban sani ba agidanku, bantaba ganin twins da ba’a san daya ba sai akanku” dariya Hameed yayi for the first time yace “Hamadi baya hoto, he hates pictures, he hates cameras, bayason mutane, Grandama dinmu tace mutum daya kadai Hamadi keso aduniya” Dasauri Zee tace “waye?” Ahankali yace “Mamie! Idan kinga yadanyi few magana ko hira to da Mamie ne, gashi you will never hear meyake cemata kaman munafuki, Gwaggo always call him makiri takadirin yaro” dukansu sukahau dariya yadan tsagaita yace “don’t worry bari yaji sauki zan jawoshi muzo zance gidanku tare” murmushi tayi tace “okay” ahankali yace “bari ki kwanta we will talk tomorrow agaida Mama bye” bye. ** Bauchi! “Wai bazaki tashi ba Asmeey?” Wata doguwar matashiya fara dake tsaye gaban wani gado haka mai kyau 6/7 tahau dukan wacce ke nannade cikin bargo da ba’a ganinta tace “kowa yatashi anyi salla an tafi aji banda ke, bazaki tashi ba sai Baba yashigo gida daga masallaci wai Husna” ko motsi batayiba, baccin ta takeyi lafiyayye, bude kofan dakin akayi hakan yasa wacce ke tsaye gaban gadon ta juyo da sauri, wata hamshakiyan mace ce tsaye gaban dakin mai jiki yar gajera haka dan batada tsayi ga farin glasses a kan idanunta tana sanye da dogon hijabi har kasa mai kyau ga charbi a hannunta, tanada jiki, fuskanta babu alamun wasa, kana ganinta kawai kasan no nonsense mutane ne hakan yasa yarinyar dake tsaye gaban gadon cikin whispering tana kallon wacce ke cikin bargon ta side na idanu tace “ai ga Mom nan” awani mahaukacin zabure yarinyar dake nannade cikin bargon tawani yaye bargo ta taso da mugun gudu akuma firgice tana dirkowa daga gadon har tana neman fadi sabida baccin dake idanunta jikinta ba karfi amman ta dafa gado ta tsaya da kyau tana goge idanunta da gefen bakinta da duk miyan bacci, daga ita sai yar rigan bacci daya tsaya mata a knee fari fari, kanta babu dankwlali gashinta dayake a tsefe baki sidik yayi biji biji ya sauko har gadon bayanta, fara ce sosai like asalin fara dan tafi wacce ke tashinta haske ma, ba siririya bace tanada dan kiba unlike dayan da siririya ce sosai saidai tafi wacce ta tashi daga baccin tsayi da matured face alamun kaman ta girmeta, sannan wacce ta tashi na bala’in kama da matar dake kofa kaman tayi kaki ta tofar, har yanayin rashin tsayin saidai yarinyar da dan tsayinta ba laifi but bawani sosai ba dan akafadan wacce ke tashinta daga bacci tsawonta ya tsaya, strictly matan dake kofan babu wasa kan fuskanta cikin wani thick powerful voice tace “okay ita Ramla bata isa ta tasheki ba kinaji ana tashinki kinyi shiru right”? Baki tabude zatai magana babu wasa kan muryan matan tace “idan kince uppan sainazo wajen nan na daura miki mari stupid girl!” Shiru taja bakinta tayi gabanta na faduwa dum dum dum, matan tace “nabaki 3min do whatever you want to do kifito kiwuce aji kona saba miki” dawani irin sauri tajuya tayi bayin dakinsu matan ta kalli dayan budurwan da kanta ke kasa tace “kekuma me kike jira? Oya bacemin daga sight kiwuce kitafi aji kema” dasauri yarinyar tace “toh Mom” hijab nata dake kan gadon ta dauka tasaka da sauri tawuce gaban dressing mirror su tadauki Al Qur’anin ta tazo wajen sai kuma takasa wucewa, babu wani yaro in this house da baya shakkan Mom kawai ajininta abin yake, she’s so scary cus bata da wasa and batason nonsense even a bit, ganin haka yasa Mom tajuya tawuce tabar wajen itakuma Ramla tafito, Babban gidane sosai tashiga sauka kasa ta sauko falo tabude kofa tafita gidansu is a very biggggg house, ga flats daban daban chan tawajen masallacinsu akwai wani katon class tawuce direct tabude kofa tashiga yaran gidan su ne ciki, 6boys ne awajen akwai dan 20yrs sai sauran duka kanninshi ne sai kuma mata yan 8yrs, da 9yrs sai ita datashigo ta zauna tana sauke ijiyan zuciya ganin Malamin su bai shigo ba yar 9yrs din tace “Ya Ramla ina Ya Asma’u?” Yar 8yrs tace “hmmm Ya Asmeey ai bata tashi ba, Allah yasa Malam yamata dukan latti jiya daman ta dakeni” ballamata harara Ramla tayi tace “zan fasa miki baki fa, wayace ki taba mata hoda ba saisa ta dake ki ba” turo baki tayi tajuya ta cigaba da karatunta daidai nan Malaminsu ya shigo wani Ustaz ne da dingilallen wandonshi yasa hula akai ga dorina akan kafadarshi ko kadan baya ragama anyone cikinsu wanda hakan umarnin Baba ne saisa suke tsoronshi ba wasa duk wacce tai latti ko takasa bada hadda akwai duka although hadda Saturdays and Sundays suke bayarwa, baice komiba yawuce gaban aji ya zauna zauna. Tana shiga bayi ko brush batayiba tafito tasa hijabi tai salla ko azkar batayi ba ta mike tsaye tadauki daddumanta ta ijiye kan gadonsu tadauki Qur’anin ta tazo kofa tafito gabanta na faduwa sosai ta shiga sauka kasa tafito tawuce class ta window ta leka ganin Malam yana aji haba saita kasa shiga idanunta take sukai ja, masallacinsu ta kalla tasan Baba na ciki but dazaran tawuce zata shiga masallacin Malam zai hangota hakan yasa tajuya takoma flat nasu tabude tawuce kitchen nasu tana bude kofa taga wata mata but bata dazu ba wannan looks exactly like Ramla tareda wasu mata da kana ganinsu kasan yan aiki ne binta da kallo matan tayi hakan yasa arude idanunta sunyi raurau tai wajen matar kaman zatai kuka tace “Ammi” wani kallo matan tamata tace “yauma kin sake latti ko Husna” saiga hawaye kaman jira take tace “Ammi dan Allah kisani kowani aiki zanyi I will even cook abincin lunch din su Yusra saikicema Malam kene kika sani aiki yau su Gambo basajin dadi basu tayamu aiki ba kinji Ammi wlh dukana zaiyi” Ammi na kallonta tace “inaji ana tashinki fa kikai shiru Asma’u? Mesa bakiji kullum kece ke latti eh kinsan idan Baban ki yazo yaganki a kitchen din nan ranki harda nawa saiya baci da safen nan dan haka wuce kitafi kibama Malam hakuri kinji” girgizama Ammi kai tayi kawai tasaki kuka zatai magana cikin kakkausan murya akace “Asma’u” juyowa tayi arude ganin Mom ce saida kirjinta yayi mugun faduwa kawai tafashe da kuka sosai taboye bayan Ammi tace “na shiga uku wayyooo Allah Ammi Mommy zata dakeni mari na zatayi Ammi” dan murmushi Ammi tayi tace “Mommy dan Allah kimata hakuri kada ki tabata yanzu zata tafi kinsan Asmeey akwai tsoron duka” Mom zatai magana duk sukaji muryan Baba. “Meke faruwa awajen nan?” Duk juyawa sukayi daidai Baba na karasowa wajen ya tsaya dab da Mom yana kallo kitchen din yana jiyo kukan Asmeey, yan aiki duka suka gaidashi but baima iya amsawa ba yace “meke faruwa? Meya faru Asma’u ke kuka? Mesa bataje makaranta ba”? Cikin kuka Asmeey tace “Baba Mommy” dan kallon Mom yayi dake kallonta rai abace saikuma yakalli Asmeey dake lekowa daga bayan Ammi yace “zonan” ba musu ta taho ahankali tana goge fuskanta da tasan Baba bazai taba dukanta ba baya dukansu, agabasa ta tsaya kanta akasa yace “mena gayamiki kan zuwa aji latti da asuba” ahankali tace “kace nadena?” Baba yace “so danazo na tadaku kika tashi kika kalleni ina wucewa natafi daman bacci kika koma?” Fuskanta tashiga gogewa takasa magana, Baba dake kallonta yace “kinaso ki gamu da fushina ko”? Girgiza kai tayi tace “Baba bazan karaba kayakuri” shiru yayi yana kallonta saikuma yace “zoki wuce kitafi” bakinta na rawa tace “Baba Malam zai dokeni” saikuma ta rushe da kuka Mom tamata wani kallo dayasa tayi kan Baba zata shige jikinshi Baba ya kalli Mom hakan yasa ta dauke kanta tawuce tashiga kitchen din shikuma yace “wuce muje” ba musu tabishi suka fice tana murmushi, har ajin nasu yayi sallama Malam ya amsa yana tasowa Baba yace “basai ka tasoba Malam kaga Asma’u sai kuka take sabida tasan tayi latti amata afuwa adaga mata kafa nayau gobe tayi latti amata hukunci” murmushi Malam yayi yace “shikenan Alhaji ta shigo” Baba yakalli Asmeey dake gefenshi data share fuskanta da sauri tanamai murmushi mai bala’in kyau yace “da idanunta awajen kaman na mutanen da wuce kishiga” murmushi tayi ta shiga tana ballama kannenta harara dake kallonta barinma su Yusra. Dan saurayin dake 20yrs yana kama da ita sosai yajuyo yakallota yamata gwalo kirne fuska tayi Malam yadawo ya zauna kowa ya natsu suka cigaba da karatu. 7:00 daidai na safe aka tasosu duk suka fito dayake almost dukansu yaran suna zuwa school Asmeey ne kawai da Ramla basa zuwa su sun gama university Ramla NYSC zata yanzu ita kuma Asmeey law school duk suka wuce cikin gidan, zama all the children sukayi anan babban falo su Gambo da Ammi na bama kowa breakfast, Asmeey tawuce sama da sauri dakinsu tawuce taje tai wanka tai brush tafito tai shafe shafen ta sannan ta dauko wani white shirt mai boturi tasaka sannan tadauki black skirt daidai ita tasaka tadauki black veil tai rolling daya mata kyau ta dauki wani LV bag mai kyau ta hada yan abubuwa da wasu books da jotter ciki ta feffesa turare sannan tafito daga dakinsu, gidansu is big flat da akwai 2more flat ciki, flat din dake left and right sai dakin Baban su at the center sai dakinsu na mata agefe na maza ana dayan gefen babansu, right flat din tawuce da saurinta da dan kunne

Chapter 2 of 56