tayi wani mahaukacin haske, fatanta yayi kyau amman bata iyacin abinci sosai, so kwata kwata batai kibaba sai uban nono dake kara tasowa sunyi shar kaman zasuce tass, Mamie is trying for her, the way take selecting abinci da ita akema haka datagaji but Mamie bata gajiya gashi batason kamshin abinci abinda yasa ma yanzu idan ta sauka kasa taje fita suje driving me which yanzu ta iya ana mata process na license ma kawai Ya Hamad baya taba yarda ta fita anguwa ne tun gidan Zee dataje rannan sai saloon Hameed ke kaita yajirata adawo da ita tarasa mesa baya bari tafita at all at least kodan layinsu ne tafita da motanta but baya bari.
Yau tun safe datai breakfast take bacci sai yanzu around 12 taji cikinta nawani irin juyawa tashi tayi zaune tana kama cikinta doguwan rigane na atampa ajikinta babu hula akanta kitson kanta yayi kyau tadade batai ciwon ciki ba hakan saiyasa ta tuna ai tama dade batai MP ba, tun Ya Hamadi na nan fa tayi har yau, shine zaizo yau yafara mata haka dafa gadon tayi ta yunkura zata tashi taje bayi tana mikewa taji jiri na dibanta hakan yasa ba shiri takama gadonsu tarike ahankali tace “Mamie!” But shiru kulle idanunta tayi tashiga tafiya tana dafa bango tana layi at dsame time cikinta nawani irin ciwo tace “Ma….” Daidai ta buge da kofa dan juya mata dakin yake, kofan tashiga bugawa tana Ma….mi….. tana sulalewa kasa daidai Ya Hameed yaci gayu cikin wata shadda yafito fita zaiyi, jin ana buga kofa kadan kadan yasa yabi kofofin wajen da kallo ganin dakinsu Hamad yasa yayi wajen dasauri daidai Asmeey na Maaa…..tana haki dasauri yataba kofan anatse yace “Asmeey” saikuma yaji shiru dasauri yabude kofan kofanma sai bai budu duka ba sabida tana wajen akwance tarike cikinta idanunta na juyawa dasauri Hameed yace “Mamie! Mamie!”Yatura dakin yashiga da sauri yana dukawa gabanta yana kallon kofa yana kiran Mamie kadan kadan Asmeey ke bude idanunta dake juyawa she could see yanda Hameed ke kallon kofa yana maganan da bataji all she’s seeing is Ya Hamad, duk uban azaban ciwo hannunta tamika ahankali takama hannunsa bakinta na motsin. “Yaayaa” juyowa Hameed yayi dasauri yace “Asmeey” yanda idanunta ke juyawa tarike hannunsa gam yasa sai kawai ya ciccibeta ya dauka daidai Mamie na zuwa tace “meya sameta?” Dasauri yace “Mamie let’s go to the hospital since Yaya baya kasan dauko hijabi” yana maganan yashiga tafiya da Asmeey yana sauka Asmeey na kallonsa sosai da juyayyun idanu tana motsi da baki tana magana da ba’aji har motansa yakaita ya ijiyeta abaya zai taso tarikesa da muryan da baya fita tace “yaushe kadawo Yaya” tsayawa Hameed yayi yana kallonta her lips are still shaking tana kallonsa idanunta ajuye hakanan kawai yaji gabansa yafadi dasauri yazare hannunta daga hannunta daidai Mamie na zuwa yafito Mamie tashiga tazauna tana rikota tace “Asmeey meya sameki” murya kasa kasa tace “Yaya kadawo! Yaya kadawo” jin sambatun datake yasa Mamie ta taba kanta tace “Subhanallahi mugun zazzabine ajikinta, kara gudu Hameed bari nakira Abban ku” kara gudu yayi bini bini yana kallon Asmeey ta madubi har sukakai asibitin su Ya Mustapa ansan Mamie da Hameed aka karbi Asmeey sharp sharp akai admitting Hameed yace “nagayama Hamadi Mamie?” Dasauri Mamie tace “kasansa zai rude yahau kuka awajen bari muji tukunna kira Yayanku” daidai Abba na zuwa ya zauna kusa da Mamie suna jiran Dr, chan saiga Dr yafito yakira su Mama duka suka bisa yayi murmushi yace “to Mama da Abba congratulations za’a sami jika!” Murmushi Abba da Mamie sukayi hakama Hameed aransa yace “dan iska Hamadi ai wlh saina gayama su Ya Faisal” Dr yace “tana dauke da juna biyu na kimanin sati takwas wato wata biyu” Hamad yace “just few days to Hamadi yayi tafiya yamata ciki kai wannan yaro”Dr yace “but tanada malaria sosai and malaria baida kyau ajikin mai ciki zamu riketa anan zuwa gobe haka, dan Allah aka koma gida let her be on bed rest kartai aiki sannan ya zamto tana cikin kwanciyan hankali always saikuma ba hayaniya ko damuwa sannan next week inda hali ku kawota tafara Antinatal” Mamie da Abba suka gyadamai kai sai murmushi suke Dr yace “anjima kadan zaku iya ganinta” tashi Abba sukayi suka godema Dr suka fito Abba na fito daidai number Baba dan kiransa Baba na dauka Abba yace “to barka barka Allah fa ya albarkaci zuri’a Muhammadu Sani, wannan karan Jikan namu ne namu namu”
Maganan Abba yasa Baba yagane Asmeey na dauke da juna biyu yace “ahhh Alhamdulillah Alhamdulilah ubangiji Allah ya dayyaba yasa albarka, Allah ya raya tana ina”? Abba yace “muna asibiti ba lafiya wai tanada malaria za’a rikemu dai zuwa gobe” Baba yace “Toh Allah yakara mata lafiya Allah ya sauketa lpy” Abba yace “Ameen Ameen” sauki sallama Baba was very very happy
Wajajen 9 Asmeey ke bude idanunta ahankali Hameed kadai tagani zaune kan kujera da waya a kunnensa Mamie kuma na salla, alamun motsin mutum yasa yakalli gadon dasauri ganin Asmeey na kokarin tashi zaune yasa yace “I will call u later” ya katse wayan yazo wajen gadon yace “careful Asmeey bari na tada gadon” taba botun yayi katifan yataso tashiga bin dakin da kallo cikin rashin karfi saikuma ta kalli Ya Hameed dake kallonta tace “ina Yaya?” Hameed na kallonta yace “wani Yayan?” Cikin raunin murya tace “Ya Hamad” dan murmushi yayi yace “aiko kinata sumbatu da sunansa dazu to yana chan kasan nan” fashewa da kuka tayi ahankali tace “wlh na gansa” tasowa Mamie data sallame salla tayi tace “kindaiga Hameed dai ko Asmeey” ahankali Asmeey tace “Mamie wlh na gansa shiya daukeni” zama Mamie tayi kusada ita tace “Hameed yajiyoki yazo ya daukeki” dasauri ta kalli Hameed, mugun kallo ya watsamata yawuce abinsa yafita daga dakin, Mamie tace “mezakici?” Fuskanta ta share tace “tea” tea Mami tamata ta karba tana kallon tea brain dinta na kokarin recalling taga Ya Hamad har tana rike hannunsa, ai tasan Ya Hameed baida idanu kaman na Ya Hamad dazu har idanun Ya Hamadi tagani, da kyar tasha tea akazo aka mata wasu allura nan da nan tayi wani bacci koda Hameed yadawo tayi bacci ko kallonta baiyiba yama Mamie sallama yatafi.
Ba’a sanar da Hamad ba anaso sai an koma gida, washe gari aka sallamesu aka bata magunguna.
**
Mom na zaune cikin gidan Fawaz dan yanzu kusan kullum saitazo dudda rabonta dashi tun a kano but coming there is now her new therapy, wayanta ne yahau ringing da sauri ta daga wayan Mama ce wayan takai kunnenta Mom tace “Ya akayi?” Cikeda kwarema a munafinci tace “ya gajiya hala kina kotu ko nakira ne na tambaya ko ke an aiko miki da taki ankon? Gashinan na karbi nawa na iyaye ganasu Nana kyauta ina gayamiki Maman su Aya ko sisin mu babu ciki” Anatse Mom tace “ankon wa?” Dan shiru Mama tayi chan tace “wlh abin nan namin ciwo yanda mutanen nan suke nuna u are nobody, ke gaki mara daraja akan yarki, keya kamata ki turo mana anko fa ke mai y’a amman sai masu danda ke aiko mana” Mom jitayi zuciyanta yafara radadi gane kan zancen, Mama tace “kinsan ance dashi da Asmeey zasu dawo daga kasan waje January, ga anko nan za’a hada bikinsu dana Hameed on 20th ayi, ga anko nan na manya lashe iya leshi da atampa embellish, ina mai tabbata miki Ammi Maman su Ramla itama ta amsa nata dana yaranta kecedai wacce batakaiba, gaki banza kin haifa musu bakisan da auren yarki ba yanzu biki yazo shima baki sani ba” Mom bata tabajin abu ya tsaya mata arai ba irin na yau, Mama cikeda watsa fetur a wuta tace “hmmm na manta fa yanzu Hamadi yasha karfin mu indai kudine, wai kinsan Umara da mijinki yaje da nawa duk Hamad din yabiya kuwa? Rannan Baban su Nana Allah ya matsi bakinsa yake gayamin ke kinga zafafan motocin daya siya musu agidan nan, kinga yanda aka gyara gidan, kinga estate din dasuka gina su yaran, to yanzu haka Mustapa na China kampani zasu gina anan Nigeria kampani iya kampani kaman dangote fa, ai wlh Hamad yasha karfinki Maman Aya! Baki isa kirabasa da matarsa yanzu ba! Yanada kudi da capacity daureki if u try nonsense” Mama tai maganan da gayya dan itama Mom batada mutunci, wani abu Mom taji ya soki kirjinta ta daure tace “hmmm in yasan wata baisan wata ba, ko duka kudin duniya ya mallaka kafin Hamad yasan dukiya ni nake cikinta nakuma dandana nayi wanka ciki!”Mom tai maganan cikeda girman kai tace “Allah dawo dasu zan gwada muku cewa saidai ayi koni ko shi! Dolene dayanmu baya duniya shine za’ayi bikin nan! Sannan y’ata zata cigaba da zama dasu! Barikiji y’ata saina karbeta wallahi! Biki dai saidai ayi na Hameed namiki alkawarin nan inhar nice Salima Mrs Muhammadu Sani Turaki!” Ta buga kirji tana kashe wayan.
SEE YHUU SATURDAY 💃
EPISODE 7️⃣7️⃣
KANO!
She doesn’t really know abinda ke damunta but somehow she understood kaman ciki gareta, Mamie kaman kunya takeji takasa mata maganan cikin, su Ya Hameed ma haka to ai su maza ne, but matan Yayyin dasuka zo gaisheta sai mata Allah sauketa lpy suke, Matar Ya Faisal Anty Nana harda dan kuka dan har yanzu ita batada ciki.
Itakuma duk kunyansu takeji balle ta tambayesu, dakinta taje dan sallan la’asar tai shiru tadauki wayanta ta duba batada any miss call ko chats from Ya Hamad she knows ba’a gayamai tana rashin lafiya ba even last time sabida ansan zai damu same with now ko itama bazata so ya damu ba but kuma she wants him to call her ijiye wayan tayi tashiga bayi tayi salla tana zaune kan dadduma Anty Asiya Matar Ya Musty tabude kofan tace “oya muje an gama girki” juyawa tayi zata wuce dasauri Asmeey tace “Anty”
Dan dakatawa Anty Asiya tayi ganin Asmeey na kokarin mikewa tsaye saita shigo tareda maida kofan tarufe tace “na’am menene Asmeey?” Dan kallonta Asmeey tayi saita rasa yanda zatai maganan saita shiga wasa da yatsunta tarasa mezatace Anty Asiya tace “menene Asmeey wani abu na damun kine?” Gyadamata kai tayi sai kuma ahankali tace “mesa Mamie kaman tanajin kunyana?” Tadanyi shiru Asiya tai wani murmushi Asmeey tace “rashin lafiyan menayi a hospital?” Dariya saida ya kufcema Anty Asiya tace “laaaaaa aini nasan Mamie bazata taba bude baki ta sanar dake ciki gareki ba akwai wannan kunyan bafulatanan tareda Mamie saidai likita ya gayamiki but zata kula dake, nima nan Dr yagayamin nakira su Nana na gayamusu, ciki ne dake Asmeey har wata biyu, su Ya Hamadi an raya sunna” wani irin kunya yakama Asmeey batasan sanda tajuya tarufe fuskanta da hijabi ba Asiya tadinga dariya tace “ahhh kajita aikin gama yagama munsan komi ustazan munafukai keda mijin naki” dukawa Asmeey tayi tana rufe fuska sosai Asiya tace “nidai sauko natafi” tafice abinta kai Asmeey saitaji tanajin kunyan kowa yanzu ciki gareta? She’s going to be a Mom? Ita da Ya Hamadi are going to be parents? Hannunta takai ta taba cikin sai kawai taji wani dadi da sanyi ya lullubeta no wonder Mamie ke nan nan da ita hawa gado tayi ta kwanta tayi shiru tadaga yatsunta tana kallo dama haka ake ciki da wuri sau uku sukayi fa ko? Rannan farko da kaman baiyiba sai da safe ya karasayi, yayi da daddare na biyu daganan aka karbeta takoma wajen Mamie, bai karayiba sai rannan dazaiyi tafiya da daddare sau uku but hartayi ciki? Tai shiru saita sake murmushi tawani rufe fuska yanzu shikenan kowa yasan abinda sukayi the only person dataji tanason gayamawa is Munir dasauri tabude waya taciro numbersa zata kirasa tagaya masa amman sai kunya duk ya kamata, tayaya zata wani gayama Munir tanada ciki she’s very shy, sai kuma ta shafa cikin tadan dage riganta takalli flat tummy tace “Abee will be very happy if he finds out about u” saikuma tasake murmushi takulle fuskanta duk kunya ya isheta wasa wasa haka bacci yayi awon gaba da ita, bacci take yawan yi gaskiya bata taba amai ba sai dai rashin son warin abinci, Mamie ta shigo dakin da magrib ta tadata tace “jeki salla bari nakawo miki abinci” tashi tayi ahankali duk sai taji tanajin kunyan Mamie tawuce bayi tai salla taci abinci bada wani yawa ba tana zaune awajen akai knocking.
Mikewa tayi taje kofa Ya Hameed ne kallo daya yamata yace “ya jikin akwai abinda ke damunki?” Girgizamai kai tayi tace “babu” ice cream dinta yanata yace “gashi” murmushi tayi tace “thank you” ywuace ta maida kofan tarufe takoma tazauna tadauki wayanta tana dubawa shiru tana calculating yanzu karfe nawa wajensu tunda Nigeria nagaba dasu da awanni shida and this is 7:30 probably wajensu karfe daya ko sha biyu na rana ne yana wajen aiki, ahankali ta ijiye wayan tashiga shan ice cream din tass ta shanye tawuce tayo alwala tai sallan isha’i sai kawai ta tashi tazauna kan desk dinshi ta kunna MacBook nata tacigaba da rubuta wani write up datake rubutawa datamai suna THE JOURNEY…..
EPISODE 7️⃣8️⃣
Wajejen 11 tafara hamma takoma gado ta kwanta ahankali ta rungume pillow tai shiru saiga hawaye ya gangaro daga idanunta takai bayan hannu ta share, is not like she’s complaining she’s happy here Mamie da Abba da Gwaggo dasu Ya Faisal suna kula da ita wlh sosai but deep down she’s lonely, fita waje ma fa wani Rahama ne, bata zuwa ko’ina ko saloon baya bari taje da kanta saidai yasa akaita, bata fita compound sabida aiki and shi baya kiranta, she miss him, she misses him alot daurewa kawai take nothing is funny. Takai kusan 12 nadare kuka take kafin bacci ya dauketa.
Wuraren 5 ta tashi da tashin zuciya sosai da sauri tai bayi amai tafara yi ba kakkautawa tadaure tayi brush tayo alwala tafito Mamie tashigo takalleta yanda ta kwanta kan dadduma awahale tace “meya sameki”? Tasowa zaune tayi ahankali takalli Mamie abu yamata yawa kawai saita fashe dawani irin kuka bana wasaba, cikeda damuwa Mamie tace “menene Asmeey”? Rasa yanda zatayi Asmeey tayi kai kirjinta zafi yake mata sai kawai tarike hannun Mamie gam tana kuka ba magana, Mamie tai shiru tana kallonta kafin ahankali tace “Hamad yakiraki yau?” Tana kuka ta girgiza mata kai, Mamie tace “jiya fa?” Sake girgiza mata kai Asmeey tayi, Mamie tace “shekaran jiya fa?” Sake girgiza mata kai Asmeey tayi, Mamie don’t even need to ask further from the way she’s crying mijinta baya kiranta yanda yakamata sai Mamie kawai ta rungumeta tana shafa bayanta tace “ya isa komi zai daidaita kiyakuri, rayuwa baka tare da mijinka waje daya ba dadi, Alhamdulillah an fara miki papers naki yana dawowa zaku tafi tare sannu kinji” gyadamata kai tayi Mamie tace dagota tareda sharemata fuska tace “kidena sa damuwa aranki haka Asma’u is not good for you and for your baby kinajina” sauke kanta kasa Asmeey tayi akunyace, Mamie tace “bari na kawo miki shayi” ahankali tace “anjima zanci Mamie amai zanyi yanzu” dasauri Mamie tace “kinyi amai ne?” Gyadamata kai tayi tace “eh shiya tasheni” gyadamata kai Mamie tayi tace “kinyi salla?” Gyadama Mamie kai tayi Mamie tai shiruuu tana kallonta sai kawai yakamata tace “muje gado” gado suka wuce Mamie ta kwantar da ita ta daura kanta a cinyanta tana shafa mata kai da hannu daya Asmeey ta kankame hannun Mamie guda daya tana sauke ijiyan zuciya feeling calm and happy sai kawai Mom tafado mata arai, lumshe idanu dasauri tayi tajason mahaifiyarta she wish ko hannun Mom zata iya rikewa haka amman bakomi she promise she will love kome zata haifa genuinely saida bacci ya kwasheta Mamie ta gyara ta ta lullubeta tai shiruuu tareda jan bargo tarufe ta tafice takoma dakinta su Abba basu dawo daga mosque ba dakinta ta shiga tai dialing number Hamad but baya zuwa sai kawai ta kira Doctor dake China katse wayan yayi shi yakirata back yace “Mamie na ina kwana ya kuke ya Asmeey dajiki” dan ijiyan zuciya ta sauke tace “fine Alhamdulillah ya wajen ya kk” ahankali yace “fine menene Mamie?”Anatse Mamie tace “Dr damuwa nake da Asmeey, yarinyar sai ramewa take wlh, rama sosai fa, babu abinda yarage sai haske bauuu ko Gwaggo saida tace dibanki ake kullum ne cus raman yay yawa kuma damuwa ce zalla aranta sosai” anatse Ya Mustapa yace “meke damunta Mamie”? Dan shiru Mamie tayi kafin ahankali tace “from wat i observe they’re having communication issues!” Mamie tai shiruuu hakama Ya Mustapa, Mamie tace “Doctor ni mace ce I know how we are, duk yanda mukakai ga son Asmeey da nuna mata kulawa can never equal to kulawa da soyayyyan mijinta, banda haka I think Asmeey loves Hamad way tooo much, maybe sama da yanda shi Hamad dinma ke sonta” anatse Ya Mustapa yace “Mamie don’t say that wallahi cus Hamad na son Asma’u beyond yanda duk muke tunani, and this communication issue daman dole saisun fuskanci hakan cus Mamie Hamad baya magana, muna gida daya da Hamad Mamie have u ever seen that boy make call? Yakira wani ko akira sa ko muji yana waya? Saidai mu, muma once in a while mu din ma bata wuce few minutes call” anatse Mamie tace “amman yayi aure Mustapa the same way yacire kunya yayi abinda yakamata ga yarinya nada juna biyu yanzu haka zaiyi abinda yakamata yadinga waya da ita kafin abu ya sameta cike gareta kasan haka sama dani kune likitoci” Ya Mustapa yace “hakane Mamie”yadanyi shiru chan yace “Mamie bawai ina taking side na dan uwana ba but duk wanda ya auri Hamadi should get ready na fighting da dabi’unsa, for once Mamie karkima Asmeey kallon yarinya ita mace ce, mata have plenty ways na chanza maza, tadena zama wani dum dum Mamie u know tadinga kiransa mana ita, tadamesa, tamasa hira, it’s a gradual process it shouldn’t always be Hamadi that is putting on efforts itama ta koyi abubuwa cus both of them sai ahankali, Asmeey lacks exposure gaskiya, akwai wani class danaga Asiya na ciki na wata wai M Shakur Intimacy class zansa Asiya tabiya mata asaka Asmeey, tadan waye cus this shiru shiru can’t work for them before shima yaje yahadu da wata achan this our gender bamu da tabbas especially yanzu da Hamadi yazama hot cake” Mamie tace “nidai kama kaninka magana, zan kira Asiyan asata a class din, Asmeey hakkinsa ce dole yakirata kowani rana yaji yatake, da munce sai yadawo agayaa masa zancen juna biyun amman gaskiya na fasa ka gayamasa koni zan gayamasa dudda inajin nauyi, but tell him sabida he should take his wife seriously! Haba yarinya na nan yasan bata da kowa fa”.
EPISODE 7️⃣9️⃣
Mamie tace “ yan uwanta duk an dauka tana chan dashi babu mai kiranta batada wata kawa, gata ba yar kano ba, ba inda tasani, yarinya ba inda take zuwa ya za’ayi bazata damu ba, Fisabillillahi fa Doctor, the only abinda takeda shi is Hamadi, gaskiya he needs to do better inba hakaba raina zai baci” Ya Mustapa yayi dan murmushi jin Mamie na fada sosai yace “Mamie kiyakuri I will talk to him” ahankali Mamie tace “kaikuma yaushe zaka dawo?” Murmushi yayi yace “kewana kike ne Mamie na” dan shiru tayi idanunta na tattaro hawaye ahankali tace “ina kewanka sosai Mustapa baka ba Hamadi, sai marasa jin nan kuka barmini Oga Hameed da Faisal, dama dama ma Abdullahi” dan dariya yayi yace “awwwn nima ina missing Mamie na sosai, this week zan dawo kinji so don’t cry again, clean those tears” hannu tasa ta goge fuskanta tass tasauke ijiyan zuciya Ya Mustapa yacigaba da hira da ita har tadan warware kafin suyi sallama yana murmushi Mamie na son dukansu Matar akwai big heart
Haka rannan all through Asmeey ta wuni ko abincin kirki bataci rannan ba sabida ciwo bawai zazzabi takeba kawai batajin dadin jikinta zuciyanta kawai tashi yake kome takai baki saita amayar wuraren 10 daga Abba har Mamie sukabar dakin bayan sun dubata sunyi kusan awa daya tareda ita, Suna barın dakin saitaji kaman duk wani ni’ima na dakin sun tafi dashi duniyan yamata zafi wayanta ta dauka ahankali jikinta yayi wani sanyi tai dialing number Hamad yashiga wayan unlike other day yanata nuna mata ringing amman harya gama ringing bai dauka ba sai kawai zuciya taji yakawo mata wuya she can’t hold it any longer kawai ta shiga typing message.
Zaka iya kirga yau kwana na nawa baka kirani ba? Talking to me is a waste of time ko? I’m no longer in your agenda, you have a busy schedule which your wife don’t happens to be among Mr Hamad! Shikenan dagayau bazan kara kiranka ba bazan kara daukan wayanka ba kuma Allah ma yaciremin tunaninka nima nahutama rayuwana dan banga amfanin tunanin wanda shi baya tunani na ba he can go days weeks without talking to me idanma wata kagani kanaso achan kuyi aurenku nina hakura.
Asmeey ta tura message din tana vibrating sosai zuciyanta namata zafi saitaji dakin ma is hot for her all she wants is inda za’a mata surutu sai kawai ta taso ta dauki hijab ta sanya tareda bude kofan ta ahankali tafito tasauko kasa dakin Gwaggo tawuce tabude kofa ahankali Gwaggo na kampatsa uban hamma tana magagin bacci taga mutu dasauri tace “wayyoo” akufule Asmeey tace “nice kekuma” tashi Gwaggo tayi tana chanza wutan dakin zuwa mai haske Asmeey tawuce tazauna bakin gado Gwaggo tace “lafiya? Ubanme kikazo yimini a daki” kallon Gwaggo tayi cikeda masifa tace “kice nafita nafita mana” ganin masifa Asmeey keji yasa Gwaggo ta taso tareda rike baki tace “ke diyar yar boko waya gabaki gayamin gaskiya” banza tama Gwaggo tahau gadon tashige ciki tai kwanciyanta, murmushi Gwaggo tayi saita taso takama hannunta tanamata tausa tace “kece kibini muje unguwa baki zuwa kullum kina gidan nan ai sai cuta ta kasheki bakiga ko ciwon kai banyi ba, ina zan zauna gida babu kananun yara sai randa marasa mutuncin nan suka ga daman kawo mana Areef zasu kawo shima Abdallah haka gashi sai gayu suke sun tsufa basuson su hayayyafa, bari kiji Asmaa kina haiho wannan kafin shekara ta zagayo ki haiho na biyu ba’a bata lokacin yanzu kiyi kigama saikiga kin tsufa da kyanki bakiga Mamie ba yanzu kaman ba ita ta haifi gardawan nan ba” Gwaggo tace “yanzu dai gobe zaki bini muje makota daman za’ayi bikin diyar Hajiyayye sunanta Firdausi kinga yarinyar akwai rashin kunya da tsiwa kaman ke ki shirya muje gobe kinji zakije?” Gyadamata kai Asmeey tayi tace “eh zanje Gwaggo” Gwaggo tawani kwashe da dariya tace “ko kefa inada fura nabaki kisha” tasowa zaune Asmeey tayi tace “bazai sani amai ba? Inata amai yau Gwaggo” Gwaggo tace “gwada sha mugani” yar fridge nata na dakin tabude tacirowa Asmeey guran aiko Asmeey tasha sosai yayi sanyi tabalain jin dadinsa tanasha ta lapke sai bacci Gwaggo ta gyara mata kwanciya tana rufa mata bargo tace “ke bakisan nafi kowa dadin zama ba da kin lapke chan baki zuwa wajena yanzu zaki gane nine nafi kowa dadin zama Allah dai ya saukeki lpy, Allah yamuku albarka keda Hamadi”
Rabon da Asmeey datayi baccin daya mata dadi harta manta sai yau ko harda huran data sha ne haka ta lapke Gwaggo tai juyin duniya Asmeey ta tashi da asuba tai salla takasa wuraren 5:30 arude Mamie tazo dakin Gwaggo ijiyan zuciya ta sauke ganin Asmeey na bacci a dakin Gwaggo ta sallame salla tace “kaman yarnan irin laulayinki ta dauko mai fitina jiya datazo ta tasani agaba harna fara bacci fa saida natashi nabata hura” dan murmushi Gwaggo tayi tace “tafi abinki zan tada ita anjima kadan tai salla, masu ciki nada uzuri dan Allah” juyawa Mamie tayi tafitoo around 6 Asmeey ta tashi mikewa tayi tashiga bayin Gwaggo tayo alwala tazo tasaka hijabi tai salla tana idarwa tai azkar tasake komawa gado sai wajajen goma Gwaggo ta daka mata duka tace “wai bazaki tashi mutafi biki diyar Hajiyayye ba” tashi Asmeey tayi ahankali tana shafa inda Gwaggo ta daketa tace “bari naje nai wanka” tawuce tafito saita wuce kitchen Mamie na magana da mai aiki she woke up good yau kawai saita rungume Mamie tace “Mamie ina kwana, Mamie zanbi Gwaggo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 38 Chapter of 56