*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 12💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
____Da sauri suka fito daga gurin suka nufi wajen da sukayi parking ɗin motar su, duk wanda yagan su yasan babu kwanciyar hankali a tattare da su, dan gaba ɗaya fuskar su ɗauke take da damuwa,
Har zasu shiga, Beenish tace su ɗan jirata tana zuwa, babu wanda ya tambaye ta me zatayi ko ina zata, haka ta juya tabar wajen, su kuma suka bubbuɗe murfin motar Ameela ce ta shiga driver seat sai Babyn baby ta shiga gefen ta, su kuma ragowar suka shiga baya, bata dawo da wuri dan har saida suka kira wayar ta suna tunanin ina ta shiga?
Can dai bayan wani ɗan loƙaci, sai gata ta dawo gurin da sauri, sai faman zufa take kamar tana sharewa da hannun ta, babu wanda ya tambaye ta inda taje, kawai Ameela ta tayar da motar.
A guje taja motar suka fice daga cikin makarantar, basu tsaya a ko ina ba saida suka zo gida, nan ma da suka shiga gidan babu wani ɓata loƙaci kowa jakar sa ya ɗauka ya zuba kayan da zai buƙata, sannan suka je suka zubasu amota suka kuma ɗaukar hanyar garin su Barazana.., gudu kawai Ameela take shararawa a hanya, yanayin halin da suke ciki yasa basu wata hira me tsayi sai ɗan jefi jefi, Barazana kam ko ƙala batace musu ba, duk da janta da suke sa hira amma takasa sakin jiki, hakan yasa suma jikin su duk ba walwala.
Sunci rabin tafiya, dan sun ma kusan ƙarasawa ga yamma tayi sosai ana daf da kiran sallar magriba, Beenish ta ɗauki wayarta ta dannawa wata number kira ba a jima ba, aka ɗauka, "Ya ake ciki ne, kun gama komai? Shiru tayi tana sauraron abun da akece mata.
"What....!!!" Haydar me kake so kace min ban fahimci maganar kaba, okay turo min maza turo min, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un, ya Allah! Kashhh...! Ta ƙarasa maganar tana dafe goshin ta tare da dafe kanta cikin matsananciyar damuwa.
Dukan su zuba mata ido sukayi suna jiran ƙarin bayani amma tayi shiru, wayar ta kawai ta zubawa ido hawaye na shirin zubowa daga idon ta, tayi saurin mayar dashi,
Barazana dake gefen ta ta karɓi wayar hannun ta, itama mutuwar gaske ce kawai batayi ba ta de yi suman zaune, sai taji damuwar da take ciki kamar ma wannan so take ta fita,
Ameela dake gaba tana tuƙi kawai ta samu gefen hanya tayi parking ɗin motar, tana juyowa cikin tsananin damuwa tace; "Wai Kun barmu a duhu ku gaya mana me yake faru mana,
"A hankali Beenish ta buɗi bakin ta da yayi mata nauyi, dan dan bakin tane ma kawai yake magana amma kamar bata hayyacin ta take maganar,
"She is laying to us gaba ɗaya shiri ne, she is his wife, matar sa ce, Why? Why? Me yasa zasuyi mana haka? Me yasa? meye haɗin su damu waye ya turo su SU WAYE SU..!!!!?? Gaba ɗaya ta rikice har dukan goshin ta take,
Suma cikin tashin hankali da basu taɓa yi ba ganin Beenish cikin wannan halin yasa suma nasu hankalin ba ƙaramin tashi yayi, duk da basu gama fahimtar zancen nata ba gaba ɗaya,
Babyn baby dake baya tuni ta fashe da kuka, tana tambayar ta, "Yaya wai suwa kike magana me yake shirin faruwa kin saka mu a ruɗu ki fahimtar da mu,
Ɗago jajayen idon ta da suka sauya kala tayi tana sauke su akan Babyn baby, da take kuka, karkaɗa kai tayi kawai tana kuma lumshe kyawawan eyes ɗinta tana jingina kanta jikin motar tana sauke ajiyar zuciya da ƙyar, cikin wata iriyar murya tace "tayar da mota muje...
"Cike da ɗan shouting Ameela tace "Beenish wai me yake faruwa yaza'ayi kice muje, baki gaya mana real abun da ya faru ba, meye hakanne??
Duk da haka Beenish batace komai ba, Saida ta ɗan ja loƙaci sannnan ta buɗe idon ta tare da tashi zaune tana kallon Ameela na ƴan sakanni sannan "tace duk bayanin nan da nayi muku baku fahimta ba me yafaru yau?
Duk da haka da kallon rashin fahimta suke binta,
Barazana ce tace; "Batun yarinyar da muka taimaka yau tayi mana ƙarya ne ita ɗin matar sa ce, ku kalli nan, ta miƙa musu wayar nan suka shiga kallon hotunan da aka turowa Beenish, wani sunyi tare tana kansa wani kuma suna kitchen suka ɗauka, harda na bikin su ne event da akayi,
"Ya Allah Ameela tafaɗa jikin ta nayi mata sanyi ji tayi kamar an kunce mata notikan gwaiwar ta,
"Na shiga uku mutane me suka zama meye ƙudurin su, akan mu taya suka iya haɗa wannan abun kamar gaske da kuka da yanda suke tsoron junan su gaba ɗaya, taya hakan zata zama ƙarya shiri, shiri akan mu SU WAYE SU to waye ya basu wannan aikin? Babyn baby ta faɗa itama tana dafe kanta dan gaba ɗayan su abun ya mugun ɗaure musu kai har sun rasa wane kalar tunani zasuyi akai.
"You see, koma me ya faru mu muka jawa kaina saida na gaya muku gaskiya amma kuka ƙi fahimta yanzu gashi zata jefa mu cikin matsala, daga taimakon ta, wallahi mutane yanzu basa tsoron Allah kowa abun gudu ne, ɗan haƙƙin da ka raina shi yake tsokane maka ido, yanzu da wacce hujjar zamu kare kanmu akan wanann lamarin?
Duk shiru sukayi mata babu wanda yabata amsa duk da maganar a kwai ƙanshin gaskiya a ciki amma hakan bai hanasu jin rashin daɗi ba akan maganar,
"Ameela tayar da motar nan mu ƙarasa idan mun samu nutsuwa ma tattauna, anyi mana hakane dan a dakatar mana da karatun mu, hakan kuma bazai taɓa yiyuwa ba, ko kun mata waccen makarantar da a ka kore mu itama ai da adakatar damu ne akayi mana sharri, dan haka duk makarantar da zamu shiga haka zasuyi ƙoƙarin yi, amma ni da akwai wanda nake zargi muje dai kawai, zamu sake shiri,
Ameela zata yi magana ta dakatar da ita da cewa wallahi kaina ciwo yake kuyi shiru mubar maganar haka, kar musa abun a ranmu makasa yin komai idan muje, gwamda mu fara gamawa da wannan sai muji da wancen, ko ba karatu zamu rayu kuma burin mu zai cika in sha Allah zamuyi nasara, duk da sun ƙwace duk wata sahida da muke da ita sun siye duk wata ɗauka da mukayi da kuma mutanen da zasu bamu haɗin kai, bamu da me kare mu sai Allah da yake ji yaje gani, ku kwantar da hankalin babu abun da zai faru, muje.....
Babu wanda ya kuma yi mata magana kamar yanda ta buƙata haka sukayi Ameela taja motar suka ci gaba da tafiya saidai ba karsashi a jikin ta, da ƙyar take tuƙin cikin da dauriya dan ita de bata so tarasa burin ta kuma bazai taɓa cika ba, indai batayi karatun ba.
Sumadai kowa da kar tunanin da yake akan maganar ta (ko ba karatu zamu rayu kuma burin mu zai cika) dan suna ganin dole sai sunyi karatun babu me ɗaukar su wani aiki inbada shi ba basu san dalilin ta na faɗin hakan ba.
Allah sarki ita kuma anata ɓangaren tunani take tayi ta yanda zata ɓullowa lamarin tayi musu hakane a tunanin ta ko zasu kwantar da hankalin su, amma babu wani abu da tasani akan hakan hasali ma ƙwaƙwalwar ta bata aiki a halin yanzu takasa tuna komai, ita kaɗai tasan halin da take ciki a yau ɗinnan dan ita ba kanta take ji ba, sauran idan suka kuma samun matsalar karatun su, a karo na biyu bazata yafewa kanta ba dan ganin take kamar ita ce ta jawo musu duk abun da zai faru dasu silar tane.....
Abun sai damunta yake gashi kowa yayi shiru sai taji ma kamar haushin ta suke ji, cikin sanyin murya tace; Dan Allah kar ku damu kanku akan wannan ɗan ƙaramin abun mun fuskanci fiye dashi bai kamata wannan ya ɗaga muku hankali ba, koda mun rasa wannan makarantar akwai damar maki da yawa da zamu bi mu zama wasu abun a rayuwa har al'umma suyi alfahari damu ko iya nan muka tsaya mu godewa Allah, muyi aiki da ƙarfin mu ilimin mu wajen wayar da mutane ko su su waye, mu tsaya akan gaskiyar mu baza mu taɓa taɓewa ba, bazamu taɓa ƙin yin nasara ba, alamun nasara tana tare da ƙalubale ba ko wanne buri ne ke cika ba, ba tare da an fuskanci matsaloli daban daban, indai zakai nasara akan abu sai ka fara shan wuya, kafin in haɗu daku babu kalar rayuwar da ban fuskan taba, amma hakan baisa na mutuba ko naji wata tawaya ko nayi ƙasa a gwiwa har yanzu ina kan baka ya ko da ku ko baku wannan alƙawari nayiwa kaina, sai inda ƙarfina ya ƙare koda kuwa zan rasa raina, sai na taimaki duk wanda yake buƙatar sa, garin neman cikar wani burin basan bari in shiga haƙƙin wasu ba, idan kunga zama dani kamar na shiga haƙin ku dan Allah ku fito ku gaya min, domin da ban fahimci hakan amma yanzu na fahimta nasan da magana a bakin kowannen ku sann.....
"Beenish..!!! wai me yake damun ki ne saboda wannan ɗan abun har kike yi mana wata maganar da bata dace ba, ko wanne irin hali muka shiga bai kamata kinayin irin wannan furucin ba ga ko wannen mu, dan Allah kija bakin ki kiyi shiru dan naga alamar ba a daidai kike ba, kin ɗauko maganar gaskiya kin hau hanya tiryen tiryen amma kin shirin faɗawa rami yakamata duk halin da kike ciki ki ringa tunanin me kike cewa, Ameela ta faɗa tana jan tsaki dan maganar Beenish ba ƙaramin ɓata mata rai tayi ba wallahi, shekara da shekaru suna tare babu wanda ya taɓa nuna mata komai amma shine yanzu take son ta canza musu zama suna zaman lafiyar su,
Beenish tasan halin Ameela da zuciya da saurin hasala, dan yanzu bataƙi su kama faɗa ba duk da halin da suke cike, daman sun kwan biyu basuyi ba, amma Ameela bata barin magana a ranta kana mata zata maka idan kagaya mata fara ƙal yanzu sai tagaya maka baƙaƙirin masifarfiyace a cikin su, ta wani wajen kuma tana da sauƙin kai idan baka taɓo ta ba, dan itama kuma tasan abun da ta faɗa bai dace ba ta faɗa,
A hankali tace; "kuyi haƙuri wallahi gaba ɗaya na rasa wane kalar tunani zanyi, naji duk kunyi shiru kuma fuskokin ku duk ba annuri shiyasa nake jin kamar haushi na kuke ji....
"Saboda kece kika ƙaddaro mana, ko kuma ke kaɗai kika aikata batare da mu ba, zakizo kina faɗawa mutane baƙar magana, wallahi kin ban haushi danji nake kamar na jawo ki na kikkifa miki maruka da zaki dawo cikin nutsuwar ki, ke kuma dalla malama rufe mana baki kin cika mana guri da ƙara, ko wani abun akayi miki, Ameela ta faɗa tana kallon Babyn baby dake ta faman zubar da hawaye ita abu kaɗan sai kuka taɓara tayi mata yawa,
"Aunty Babba ce tace; "Yauwa Ameela gaya musu dai ko zasu dawo cikin nutsuwar su dan naga basa tare damu, kece daidai da su, ni wallahi maganar tata mamaki taban sai naga kamar ba ita take yi ba, wallahi Beenish kina da ƴar matsala idan kina irin wannan rikicewar nan gaba kuma me zai faru, kamar yau kika fara fuskantar matsala irin wannan sai me idan mun rasa karatun da munsan da shi, ko a yanzu akace bazamu ƙara shiga ba, mun samu abun da muka samu, babu inda zamuje ayi mana kallon jahilai ko wacce da ilimin ta daidai gwargwado arabi da boko, idan kuɗi ne kuma ga kasuwanci ne kala kala dole sai munyi aiki ƙarƙashin wani.
"Barazana da tayi shiru tun ɗazu bata tanka musu ba sai yanzu tace; "Mutanannan baku da dama yanzu ai duk gashi kun dawo kan hanya da tayi muku haka, amma da to be censoring speaking maganar ta gaskiya ce babu wanda beyi tunanin wani abun ba, amma da tayi muku haka duk gashi kun gane gaskiya banzaye kawai,
Aunty Babba ce tayi "saurin cewa kai Barazana har dani kike cewa banzaye?
"To da mece?
Hannu ta kawo zata buge ta, tayi saurin cafke hannu tace rufamin asiri in mutu a ɗakin uwata maza su kaini ba mata ba, idan kika buga min wannan gudumar hannun naki irin na samudawan da da akeyi tun abaya, ai saidai a ɗauki gawa ta, Amma dai kun haɗa dangi da samudawa dan wallahi a bincika ba daga tsatstson mutane irin mu kika fito ba,
Babu wanda bai murmusa ba a cikin su, dan inda sabo sun saba Barazana akwai ta da yankowa mutum magana duk girmansa, dan ita ko nata da lafiya bakin ta baya mutuwa da surutu, duk da sun yi mamaki basuyi tuananin zatayi magana ba, halin da take ciki ganin tun tahowar su batace komai ba gashi kuma wani abun ya sake faruwa,
Beenish duk binsu da ido takeyi hawaye na cika mata ido dan ita abun da suke yi ma tausayi suka bata tasan duk suna yin wannan abunne saboda ita bawai dan ransu ba, gashi suna nishaɗi kamar sun manta da abun da yafaru, kamar babu wata damuwa a zuƙatan su, haka sukai ta tafiya suna hirar su gwanin ban sha'awa gwanin ban tausayi,
Basu suka ƙarasa garin ba sai da aka fara kiran sallar isha'i,
A bakin wani gida sukayi parking ɗin motar, duk firfitowa sukayi daga cikin motar, suna kallon yanayi garin layin da suke babu hayaniya sosai gurin shiru.
Barazana ce ƙarshen fitowa tunda ta fito take ta ƙara kallewa ƙofar gidan su kallo tana tuananin yaushe rabon ta da gidan mahaifin ta amma ya gagare ta zuwa, batasan loƙacin da ƙwalla ta fara zubo mata ba, abun da yafi komai tsaya mata a rai shine ganin yanayin garin kamar ba'ayi wani tashin hankali ba, makamancin yanda aka gaya mata,
"Ameela ce tace; "kin tsaya mu shiga mana, duk da naga ma kamar babu wata matsala, naji unguwar taku shiru,
Ji tayi jikin ta duk ya mutu sai taji bata son shiga gidan ji take kamar tace musu su koma, amma babu dama dole ta ɗaga ƙafarta da tayi mata nauyi tayi gaba suna binta a baya babu abun da suka ɗauka suka ɗai suka fara yin gaba,
Sallama sukayi a bakin ƙafar gidan duk da babu ƙofa a bakin gidan amma duk da haka saida sukayi sallama, jin shiru yasa ta ƙarasa shiga cikin gidan gaban ta na dukan uku uku musamman da taga cikin gidan ma kamar babu wani abu da yasame sa, gashi nan yanda tasan shi a da, sai wata mata dake can nesa dasu durƙushe gaban wuta, da alamu kamar bataji sallamar da suke ba,
Ameela ce ta kuma rafka uwar sallama, daga wani ɗaki wata mata ta fito tana amsawa dake cikin gidan akwai hasken nefa haske ko ina na jan ƙwai hakan yabata damar ganin masu yin sallamar, da ƙar fi tace "Abuuu..! Abu! Abu! Sai maita mata sunan take, wani na namijine shima ya fito da saurin yana fitowa ya ɓangare baki yana cewa BABAR ABU! ga Abu......!✍️✍️✍️
"To wa ya kira ta kenan indai babu abun da ya faru a garin nasu🤔🤔🤔 (Ah... muce gobe da cin ƙosan Babar Abu kenan, mu tashi da wuri) Ina fatan dai readers baku manta Babar Abu ba.
[3/5, 11:48 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 13💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
____Da gudu wata mata ta fito, daga ɗakin da suka fito, tana fitowa kuma taja burki ta tsaya tana bin Barazana da kallo, da gudu Barazana taje ta faɗa kanta tana fashewa da kuka,
Itama kukan tasaka tanajin kamar tayi kukan dan tausayin yarinyar tata, shiru sukayi tana ta bubbuga bayan ta alamar rarrashi, saida suka ɗauki loƙacin kafin Babar Abu ta ɗan ja ta baya, tare da ƙarewa fuskar ta kallo tasa hannu tana goge mata hawayen ta, sannan tace, me kika zo yi, "me yasa baki sanar dani ba, bana ce kar ki ƙara zuwa ba, baki sanar dani ba, yanzu idan wani abun ya faru da ku fa.
Itama cikin muryar kuka tace "Inna ina wayar ki take, da ita aka kirani ance garin nan babu lafiya sunzo sun kashe BABA, gaba ɗayan ku kuna cikin mawuyacin hali dan ana shirin bankawa gidannan ma wuta, babu wanda suka ƙyale, shiyasa gaba ɗaya hankali na ya tashi na taho, da nazo kuma naga alamar kamar babu wani abun da ya faru.
Cikin zazzaro ido da al'ajabin da ya gama cinye ta, tace; "waya ta kuma ni waya ta na ɗaki, ban kiraki ba, kuma babu abun da yasamu Labaran, mahaifin ki yana nan da ransa. muryar wa kika ji da aka kiraki.
Shiru tayi tana ɗan tunani ko zata tuna muryar amma sai taji batasan me muryar ba, girgiza kai tayi tace; "Inna ban ɗau muryar ko waye ba, kawai an kira ni cikin damuwa da ruɗewa yake min maganar yana gaya min, dan naji murayar sa na kamar kuka yake.
"Ikon Allah to waye ya aikata hakan danni ban bawa kowa waya ta ba, tun jiya ma waya na cikin jaka, sai ɗazun nan na ɗauko ta,
"Abu waɗannan kuma fa daga ina kika same su ɗan matashin saurayin ya tambaye ta yana washe baki, dan shi duk zantukan da suke ma bai dame saba, hankalin sa yana kan su Ameela,
Matar dake gaban murhu tana jiyo su amma ko kai bata ɗago ta kalle su ba bare tazo inda suke,
Ɗayar matar ce, tace; bayin Allah ku shigo sun barku a tsaye ga tabar ma ku zauna ta faɗa yana shinfiɗe musu tabarmar a ƙofar ɗakin, duk zama sukayi suna yi mata sannu,
Juyawa tayi ta kalle su tace bayin Allah kuyi haƙuri kunzo mun barku a tsaye,
Da sauri Ameela tace "laa ba komai Inna"
Jan Barazana tayi suka zauna suma, suka gaggaisa da sauran sannan tasa a kawo musu ruwa.
Barazana ce tace; to yanzu Inna meye abunyi ki ɗauko wayar ki in duba, dan akwai alamar tambaya akan wannan lamarin dole saidai ko idan ɗauka akayi baki sani ba,
Jiguma tayi tana tunani tace; "amma abun da mamaki bari dai in ɗauko miki ki duba, tashi tayi ta shige ɗakin dake kusa dasu.
"Me kuka fahimta game da lamarin nan?
Beenish ce ta gyara zama tace; "Tunanin da nake tayi kenan tun ɗazu, tabbas Barazana wannan abun yana da alaƙa da abun da ya faru ɗazu, to amma meye haɗin can da kuma nan garin, anyi mana haka ne dan mu baro garin kuma duk yanda a kayi akwai haɗin baki kuma dole na kusa ne yayi mana, in ba hakaba taya har aka iya fakar ido aka ɗauki wayar ta aka kiraki, kiyi tunanin a cikin nan gidan babu wanda kike tunanin zai iya aikata miki hakan?tunda har tace a jaka ta ajiye ta, to shiga a kayi aka ɗauki wayar aka gama abun da za'ayi aka mayar mata batare da sanin ta ba, duk dan a raba mana hankali.
"Zancen kenan kunga wayar fanko wallahi an cire sim ɗin a cikin wayar,
Da sauri Barazana ta karɓi wayar ta shiga dudu ba ta sai kace me son gano wani abun a jikin ta, can kuma ta miƙa mata wayar tana miƙewa tsaye, tace ku tashi mu tafi....
Duk kallon ta sukayi da mamaki,
Ameela tace; "Ina zamu tafi?
"Inda muka fito, dole muje muyi yanda zamuyi mu gano inda sim ɗin nan yake dan dashi za'a iya yin abubuwa da dama idan bamuyi saurin dakatar da su ba komai ma zai iya faruwa, Barazana ta bata amsa,
Da sauri itama mahaifiyar ta ta tamiƙe tana cewa; "amma dai ba yanzu ba, kinga dare yayi babu abun da zai faru in sha Allah, shima kuma malam baya gidan zaku iya kwanciyar ku anan gobe da sassafe sai ku fita,
"Eh hakan za'ayi Zee ki bari sai gobe yanzu ma idan mun tafi muna cikin haɗari dan zasu iya bibbiyar mu cikin dare yanzu in muka tafi a ƙalla sai kusan asuba zamu ƙarasa dan haka mubi ta maganar ta ai na taho da system ɗita zamu iya fara aikin mu anan,
Shiru tayi tana kuma nazarin abubuwa da dama kafin da ƙyar ta zauna dan taso tafiya a cikin daren nan.
Sallolin da ake binsu sukayi sannan aka zuba musu abinci duk da garaugarau ne haka suka cishi da yawa ba laifi, bayan sun gama kuma suka koma ɗaki suka fiffito da system ɗin su suka fara aikin da zasuyi da ita,
Bari mu ɗan yi waiwaye, ance waiwaye adon tafiya koh, kar mu ta tafiya bamusan inda muka dosa ba,
*WACECE BARAZANA*
Zainab Ɗahiru Yunusa Sarkin noma, asalin su ƴan Zamfara ne, mahaifin ta kuma manomi ne, ya haɗu da mahaifiyar ta a wata ruga dake cikin ƙauyen Zamfara, sunje shuka wajen wata gona, mahaifinta riƙaƙƙen makiyayi ne shi kuma, sun kaɗo shanun su zasu shigar musu gona sai mahaifin sa yayi saurin dakatar su, akan kar su shigar masa gona, acikin yaran wani yaso yayi masa rashin kunya, sai tayi saurin tsawatar wa yaron akan ya kore su suyi wani wajen kar su shigar wa mutane gona, shi kuma yaron yaƙi ji har suka so suyi ƴar ƙaramar rigima da ƙyar dai aka rabasu suka haƙura,
Shi kuma mahaifin Zainab tunda yaga mahaifiyar ta yaji tayi masa, dan haka bayan wannan rabuwar tasu, da kansa yaje har cikin rugar su ya lalubota sannan yaci gaba da bibbiyar ta, tun bata lura ba har ta fara lura, da yaga haka sai ya gaya mata ƙudirin sa akan sa, tace ita bata san zance ba, da ƙyar dai ya samu ya shawo kanta har ta amince suka ƙulla soyayya me ƙarfi, loƙaci da Alhaji Rabo(mahaifinta) ya gane haka sai yayi ƙoƙarin datse alaƙarsu amma hakan ya gagara dan saida yarinyar tayi ƙokarin kashe kanta sannan ya amince, mutane da yawa basa so ci kwa harda mahaifiyar ta da take cewa ƴarta bazata auri ɗan sarkin noma ba, kuma daman ita da wanda take so yarinyar ta aura, ta ɗan gidan me gari ne kuma yaron baida tarbiyya ko kaɗan dan har kisan kai yake, dake yana ɗan gidan me gari shiyasa yake duk abun da yaga dama, ba tare da anɗau matakin komai ba akai, shiyasa take tsoron abun da kanje ya dawo saboda tayi masa alƙawari bayan kuɗaɗen da take karɓewa a hannun sa, duk da sunan zata basa ƴarta, shiyasa hankalin ta yake tashi, bata ƙaunar yaron ko kaɗan, tayi iya abun da zatayi taga bata basu rabu ba, saboda yariyar akwai taurin
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 44