Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ƙyar na samu ina nuna hoton ki duk inda naje sannan wani yace min ai school ɗin ku ɗaya amma baisan gidan ku ba, da ƙyar dai na samu wanda yasani shine aka rako yanzu ma wanda ya rakoni ya tafi da kun gaisa wataƙil ma kun san shi.. Wani farin ciki taji ya kuma zo mata jin yanda ya sha wahalar neman ta, cike da farin cikin ta kuma rungume sa tana cewa, "Allah sarki ashe haka kasha wahalar nema na kaima, sakin sa tayi sai faman murmushi take, ta juya ɓangaren su tana kallon tace "kunga Uncle ishaƙ da nake baku labari, Duk murmushin yaƙe sukayi mata suna ɗan russinawa suka gaida shi, dan babu wanda yayi farin ciki kawai dai sun nuna mata kara ne, dan yanda suka ganshi dai suka ga duk ba yanda take basu labari, mussaman ma Zee da taga kallon da yake mata duk ta tsargu hakan yasa tayi wani sak dan ji tayi kawai bai mata ba. Bakin Aunty Babba kamar gonar auduga, bakin ta yaƙi rufuwa cikin murna ta ce Uncle mu shiga daga ciki, Ameela ku muje mana, kawai ɗan jinjina mata kai sukayi suna kuma kallon ko ina na gurin, aransu suna ayyana to dan zuwan sa ne kawai kuma sai ya lodo mutane haka, dan su a tunanin su duk mutanen sa ne.. Aunty Babba ce taja hannun sa suka fara yin gaba, sai Beenish da Barazana da suka bi bayan ta Ameela kuma hannun Babyn baby ta kama suka koma motar dai ta tayar da ita, suka bi bayan su da motar a hankali suke tafiyar har suka ƙarasa bakin gate ɗin. Ganin suna shirin yin gaba taja hannun sa, yasa Rabi saurin ƙarasowa, kusa da su magana ɗaya, basu san da ita agurin ba sai maganar ta kawai da sukaji... "Naseeru! Da sauri Magana ɗaya ya juya jin ankira sa da sunan sa na asali, Saida yayi mamakin ganin ta, Cikin sauri tace "kuyi sauri wancen da suke shirin shiga dashi mugune kuyi sauri ku dakatar da shi, zan baku ko nawa kuke so, kar ka bari ya shiga gidan kaji Naseeru? "Yaushe kika zo daman kina cikin garin loƙacin da mukayi waya shine kuma baki gaya min ba. "Dalla kabar wannan maganar kaga shiga fa zasuyi, duk wata magana mayi daga baya. Waye wancen ɗin to naga ai sun san juna da waccen me yasa kika ce a dakatar dashi kada ya shiga? Cike da gajiyawa da maganganun da yake mata dan bata so su shiga kuma bata son su haɗu da Bulama agaban yaran dan zai nuna yasan ta kuma batason yaran su san sun san juna, shiyasa ta kasa ƙarasawa tun ɗazu, "Cikin ƙosawa tace "magana ɗaya kaide kayi abun da nace maka, Kallon ta yayi sai ta kuma juyawa ya kalli can inda yaga Aunty Babba ta ƙwafe tana fam zuge gate ɗin, Fito yayi tare da cewa "kice dai kawai akwai wani dill ɗin tsakanin ku, to kawai kije kiyi gaba da gaba da shi mana mu zamu take miki baya. Cikin ɗan zaro ido Rabi tace "kai amma baka da tunani sai kace wata ƴar daba zanyi gaba kuna bina a baya, haba Allah ya kiyaye, agaban su so kake sunamin kallon ƴar daba, jika ta fa yazo ɗauka mugu ne kuma cutar min da ita zaiyi, kuma akan abun da bai shafe ta ba, wata matsala ce a tsakanin mu, bana son kuma saka su a ciki dan haka kawai koda sun shiga ku rufarwa yaran sa, daga nan sai ku shiga, shi kuma sai ku fito dashi daga cikin gidan, kuyi masa talala bashi da wani ƙarfi inya so anan zaku samu damar ɗauko min yarinyar da na nuna maka hoton ta, ka gane? "Ƙwarai kuwa kuma anan ne nima zan rama abun da sukayi min, kai muyi jafa ya faɗa yana kallon sauran mutanen nasa, tuni sukayi gaba kowa na faman jan ƙafa yana nuna yafi kowa shegantakar sa tafi ta kowa kowa ƙwaran kansa ne, duk bakunan su kamar guntun baƙin man mashin.... Da sauri Rabi tace "kai! Kai! Kar ku taɓa ƴan matan dan Allah ko nawa kake so zan biyaka ka rabu da su akan wannan ramuwar taka, nasan hakannan baza suyi maka haka ba, duk yanda akai kaine la shiga hurumin su, yanzun ma wallahi in kun shiga Allah sa ku fito ƙalau amma duk da haka kar ku taɓa kowaccen su ɗauko min ita kawai zakayi sannan ku fito da mutumin da suka shiga dashi, shikenan abun da zakuyi min ina jiran ku a cikin mota, "To ai kin gama magana indai zaki biya ni lahanin da sukayi min to angama magana. Nan sukayi gaba ita kuma ta koma cikin motar ta, Maryam jikin ta sai ɓari yake gashi bata son duk su ganta itama musamman Bulama bata so su haɗu itama a fannin ta a cewar ta idan ta fita duk suka ganta batasan wane mataki zasu ɗauka ba, gashi kuma yaran baza su yarda da ita ba, indai har suka ga sun juna a tsakanin su, gashi daman basu san taba, babu me yarda da ita, shiyasa ta kasa ƙarasawa gurin da suke, da ta kwa sun shiga cikin gidan ji tayi kamar tayi tsuntsu taje ta dakatar dasu, gashi sai kiran Hajiya Dannar take amma bata ɗaga ba, gaba ɗaya hankalin ta ya tashi, tana lungu kuma gurin duhu ne dashi babu haske agurin, daga inda take duk tana hango komai da suke, abun da yafi ɗaga mata hankali ma da kuma mamaki ganin yana magana da ɗaya daga cikin su alamun ma sun san juna tunda har da su runguma da kuma sumbatar goshi abun ya matuƙar ɗaure mata, kai tunda take bata taɓa sanin suna da alaƙa ba kuma Hajiya Dannar ma bata taɓa bata labari ba... Ga shi kuma ganin Rabi na magana da ƴan daba shima ya kuma ɗaga mata hankali dan a tunanin ta duk tare suke da Bulama duk shirin sune bakin su ɗaya.... Su Magana ɗaya na zuwa wajen mutanen nan suka shiga kai musu duka nan suma suka shiga mayar musu, dan basu san hawa ba basu san sauka ba kawai sukaji suna dukan su dan haka suma ba shiri suka shiga ramawa, suna cikin wannan damben sai ga jiniya nan ta karaɗe wajen, su Magana ɗaya kallo ɗaya sukayi gurin suka gane su waye nan kwa suka fara sakin waɗancen suna neman hanyar guduwa, sauran da basu sani ba suka tsaya agun, har sojojin suka shiga dirowa daga motar suka nufo su da bindigun su a hannu, sai loƙacin duka fara ƙoƙarin guduwa amma babu inda sukaje duk akayi ram dasu, Hajiya Rabi kam da suka wuce ta gaban su ai tuni tasa drivern ta ya yanka juyi da ita suka bar gurin tun kafin a ankare dasu suka bar unguwar ma gabaki ɗaya. "Magana ɗaya ma da yaransa duk sunyi nasarar tserewa saidai kuma duk sunbatu abun hawan su agun da saiyadojin su suka gudu" Nan suka kwashi yaran Bulama suka saka su a cikin motar su, su kansu basu san me ya faru ba suke faɗan, sude sun biyo sahun ƴan matanne da RK ya turo su, ashe loƙacin da suka tafi ɗauko Beenish gidan sukaje sai aka hana su shiga, har suna shirin komawa saiga mahaifiyar Faheema nan zasu fita kallo ɗaya ta gane su dan haka bata kawo komai a ranta ba tace a bar su su shiga yanzu zata dawo su jirata.. Shine fa da suka shiga sukayi karo da Beenshi a falon gidan hannun ta ɗaure da aunka a bayan wata kujera, falon ba kowa sai wata ne aiki itama jikin ta da kayan sojoji, suna zama kuwa saiga RK ya fito duk tsurewa sukayi dan basuyi tunanin ganin sa ba, cikin wata riga yake fara me ɗan gajeren hannu sai wandon sojoji gajere da ya saka, sai wani takalmi baƙi da gaban sa ya ɗan kwanto ya rufe masa yatsun ƙarfa yayi, kansa babu hula sai gashin sa da ya sha gyara yayi baya dashi sai gefe da yake a ɗan lanƙwashe lanƙwashe na gaba kuma duk yama kusa rufe goshin sa amma shima anan naɗe yake a jere kuma, daga gani ma daga wanka ya fito saboda yanda fuskar sa tayi wani fayau da ita gwanin burgewa kyan sa ya ƙara bayyana saidai muce masha Allah domin Allah yayi halitta akan bawan Allahn nan,(tunda na ɗora idona akan sa har yanzu duk wanda na kalla a kusa dani sai inga kamar a gidan zoo nake ina kallon wasu halittun hhhh) Suma ai duk saranda sukayi suna kallon sa saboda duk haɗuwar da sukayi dashi basu taɓa kallon sa irin na yanzu ba ko a ɗazu da facemask a fuskar kuma da hula ko ganin kalar gashin sa basu yi ba, yanzu kam sosai suka saki ido da hanci suna kallon sa, sunga halittar da basu saba ganin irin taba, saida na rufewa su Abulele ido gudun kar ta bari ya kamata tana kallon sa ta bamu kunya... Haɗe rai yayi yana ƙarasa shigowa cikin falon wayar sa ya zaro ya ɗora ƙafa ɗaya kan ɗaya yayi kamar ma baisan da su a falon ba, duk da yana sane dasu da duk irin kallon da suke masa. Saida ya daɗe yana aikin dannan waya su kuma tsoro da yanda yayi da fuska yasa duk suka rasa me zasu ce masa gaba ɗaya. "Stop looking at me witch. Ba shiri duk sukayi ƙasa da kansu cike da mamakin abun da yace ko wacce sai ta shiga tsarguwa kode ita kaɗai take kallon sa shiyasa yace mata mayya, saboda da su duka suke kallon sa zai ce musu mayu, dan haka ko wacce sai ta fara tunanin ai da ita yake. Tunda yayi maganar kuma bai kuma ce musu komai ba. Beenish da taƙaici ya gama isar ta ta miƙe tsaye, ta matso kusa dasu tace dan Allah ku roƙe sa ko zai saurare sa nagaji da zaman nan tunda ya ɗauko ni ya barni a mota fa kamar wata akuya kuma yasa anfito dani ya kuma bari na anan duk magiyar da nake mishi yaƙi ya saurare ni kamar ba musulmi ba ko inda nake ma bai kalla ba, Duk shiru sukayi suna sauraron ta amma suna tunanin abun da zaije ya dawo, dan sai yanzu da suka gansa suka ƙara jin shakkar sa saboda kwarjinin da yayi musu, sai yanzu ma suka ga gaskiya abun da tayi masa bata kyauta ba ita tajawa kanta a yanda yake da matsayi ga ƙarfi gashi soja sojoji kam ba imanine da su ba, tsaf zai iya yi mata abun da yafi ma abun da yayi mata ɗin, duk sai suka nemi wani ƙarfin su da suke ji dashi suka rasa dan dama su kaɗai ne basu zo da wani shiri ba da zasu iya yin faɗa da kowa ma bare kuma dashi.. Babyn baby ce ta ta rungume ta kamar zatayi kuka tace "Zai haƙura Yaya ki kuma basa haƙuri muma daman haƙurin muka zo mu bashi, in sha Allah zai haƙura da abun da kikayi masa ki kwantar da hankalin ki babu me raba mu dake muna tare mutuwa ce kawai zata iya rabamu, "Ok fine" Duk juyawa sukayi suna kallon sa da yayi maganar amma duk da haka bai ɗago ba idon sa nakan wayar sa, saima gani da sukayi ya miƙe tsaye, bai kuma kalli inda suke ba kawai yayi hanyar fita, nan suka shiga basa haƙuri amma ko tsayawa baiyi ba bare ya juyo saima ficewa da yayi daga falon duk bin bayan sa sukayi da kallo baki sake. Kuka Beenish ta saka "cikin kuka tace wai me yake nufi da mune kunga irin rashin mutuncin nasa duk maganar da zakuyi masa bazai saurare ku ba bare yabaku amsa ni wallahi tafiya ta zanyi inyaso ya kashe ni wannan ai wulaƙanci ne daga yin ɗan ƙaramin abun da bai taka kara ya yakar ya ba, sai ka hau mutum da duka kuma ka ɗauko sa ka rabasa da ƴan uwansa ambaka haƙuri ambasa haƙuri amma yaƙi kula mutane ma bari ya faɗi wani abun... Ameela ce ta shiga bata haƙuri, tana cewa zai haƙura ne, agun sukai ta zama har wajen ƙarfe biyar babu kuma wanda ya shigo falon tun suna surutun su har suka gaji, sai da sukaji ankira sallar magriba sannan, Beenish tace suzo su fita loƙacin babu masu tsaro da yawa duk sunje sallah nan suka samu dama suka fito suka shiga motar su, tuni Beenish ta ɓalle abun da aka ɗaure ta dashi ashe daman ba'a ƙulle yake, ta kwa cire ta jefar dashi a wajen, sannan tace musu ita zata tuƙa sa, cikin ɓacin rai ta tayar da motar suka ja tunda kwa har suka shiga ai babu wanda zai hana su fita saboda su masu gadi basu san meke faruwa ba, suna zuwa kuwa aka buɗe musu suka fice daga gidan tunda ta hau titi kuwa take kwarara gudun hauka dan duk da haka a tsorace take ji take kamar zai biyo su ya kuma sawa a kamasu, saboda gudu saida ta kusan bugawa wata mota, ganin hakan yasa, suka dakatar da ita da tuƙin, Barazana dake gefen ta sukayi exchanging ɗin guri ta karɓi tuƙin ita kuma ta koma gurin ta shima saida ƙyar ta yarda ta bata, Ita ma dai kuma ba gudun hankali take ba da kaɗan nata ya ɗanfi na Beenish ɗin hankali, suna wannan gudunne na tsoro har suka ƙaraso unguwar tasu, sai kuma suka tarar da wannan abun. Dalilin da yasa ƴan sanda suka kuma biyo su kenan bisa ga umarnin RK da ya basu umarnin su ɗauko su gaba ɗayan su, kuma idan sun ɗauko su, su wace masa da su barack ɗin sojoji ba gida zasu kai masa su ba, sai gashi kuma da suka zo suka kuma tarar da wata rigimar a ƙofar gidan, dan haka bayan sun gama saka yaran Bulama a mota, sai suka fara ƙoƙarin tura gate ɗin sukayi, saikwa ya buɗe nan suka fara tura kai ciki wasu suka shiga wasu kuma suka tsaya tare da yaran Bulama.....✍️✍️ *Kunga typing ɗin ku yafara ƙasa koh, to comment ɗin ku ne yayi ƙasa shima, kullum ragewa kuke yi, masu yi kullum ƙalilanne waɗanda de nasani ne, kuma daman nace yawan comment yawan typing 🤗* [3/5, 12:25 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) ______________________________ *_episode 32💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bismillah..✍️ *PAID BOOK💸* Loƙacin da suka shiga cikin gidan, a falo su Aunty Babba suka tsaya, nan suka ƙara gaisawa, Aunty Babba ce ta shiga tambayar sa me yake son ci ta dafa masa, yace mata babu komai ba abun da zaici, ya hutar da ita.. Idon sa nakan Abulele yace "ya sunan ki, baku gaya min sunayen kuba sai ya wayance da tambayar su gaba ɗayan su, saboda Aunty Babba kawai suka basa amasa, ganin yanda Aunty Babba take ta kumma mannewa a jikin sa yasa Ameela miƙewa tace "mu basu waje mana, kuzo mu koma ɗaki, kamar jira suke tana faɗa duk suka miƙe, a kusan tare suka fara tafiya zuwa ɗakin su. Suna Shiga Barazana ta fashe da dariya ƙasa ƙasa, tace kan Bala ba gashi wai wannan tsofe tsofen tsofen mutumin Auny Babba take so, kunga yanda take ta faman hauka akansa ko kunyar mu ma bataji. Suma duk dariya sukayi ƙasa ƙasa yanda bazata jiyo su ba, Babyn baby ma tace "wallahi nima abun sai yaban mamaki tabb lalle so hana ganin laifi bare kuma muni ita a haka tagani take son abun ta, "Nifa nama lura da mutum kamar ɗan duniya ne naga yanda yake kallon Zee kode ya sanki Zee? Cewar Ameela "Wata uwar harara ta wurga mata tare da cewa "uwar sanina yayi ni a dangina babu masu zubin wannan halittar a gidan uban wa zai sani, nima naga kallon da yake min ɗan iska ne kawai, yaci darajar Aunty Babba da na tsige masa wannan matsiyacin gemun da hannu shege ni wallahi ma ji nayi kwata kwata banyarda dashi ba bai kwanta ba... Beenish tace "wallahi nima haka ni abun mamakin ma yanda ya haɗo uban mutane ya taho dasu sai kace marar gaskiya ko kuma uban daba ya wani lodo mutane kamar yazo dambe ko gurin maza zaizo ai sai haka bare kuma yasan gidan mata ne. Ke kwa kika sani ko anbasa labari yanda muke shiyasa ya taho da shirin sa, cewar Zee, A can falo kuwa sai ƙara shigewa jikin sa take tana shafo gemun sa, neman haɗe bakin su ma take amma sai kakkaucewa yake yaƙi bata haɗin kai dan shi ji yake kamar ya ture ta ta faɗi dan ya gaji da abun da take masa, daman zaman da yake da ita dan saboda Abulelen sa na gun, dan haka hankalin sa na kanta, amma yanzu tunda ta tashi sai yaji kamar akan ƙaya yake abun Aunty Babba take masa duk sai ya kuma jin haushin ta da tsanar ta sun kama sa. Ɗan hannu ya saka aljihun sa ya zaro wayar sa, sai yayi danne dannen sa ya kara a kunne yana wayar ƙarya, a loƙacin tasamu ya ɗan janye ta daga jikin sa, ya miƙe tsaye a hankali yace "sweetheart Bari in ɗan amsa waya ina zuwa. Wani daɗi ta kumaji ya mamaye ta da ya kirata da sweetheart sai kawai tayi kwance akan kujerar tana ɗaga masa ka. Ta gefen ido ya wurga mata uwar harara sannan ya nufi hanyar fita, yana buɗe ƙofar yaga sojoji sun nufo wajen da sauri ya koma sai ya juya ya kalli inda Aunty Babba take sai yaga ta rufe ido hankalin ta ba akan sa yake ba, lalbulen dake jikin ƙofar ya shiga ya ɓuya daga ƙarshe ta yanda idan aka buɗe ƙofar ba za'a gansa ba, yana gurin aka turo ƙofar yanda kwa ya lissafa hakance ta faru, yana bayan ƙofar basu gansa ba da suka buɗe, Da sauri Aunty Babba ta tashi tana cewa Uncle ka ga...... Ɗif tayi ta kasa ƙarasawa ganin sojoji ne suka shigo, batasan loƙacin da ta miƙe ta kwasa a guje ta nufi ɗakin su, kafin suyi yunƙurin kamata har ta rufe ɗakin tasaka muƙulli. Sauran dake suke zaune akan gadon suna gulmar ta, ta shigo musu a haka, hakan yasa duk suka miƙe suka shiga tambayar ta lafiya me ya faru? Cikin sauke numfashi da ƙyar tace "wallahi sun ƙara biyo mu fa, wannan mugun sojan shida wasu, kawai sai ganin su nayi a falo, yanzu haka sun taho nan ɗakin... Duk tsuru-tsuru su kayi da ido kowa na tunanin meye mafita musamman Beenish da tasan ita ta aikata laifin, daman tasan za'a rina, to yanzu kuma idan ya kamata wace irin mugun ta zai mata kuma, tayi laifi kan laifi, sai yanzu take da nasanin tahowar da tayi. Bam Bam Bamm sukaji ana ta bugun ƙofar da ƙarfi duk rasa abunyi sukai, Beenish ce ta kalli Aunty Babba tace "dan Allah harda shi kingan shi da idon ki. "Eh mana nagansa da ido na, kema kin san dole yazo ai tunda shi mu ka yiwa laifin. "Na shiga uku to yanzu me zamuyi nifa gaskiya bazan yarda in koma ba wallahi nasan abun da zaimin sai yaci uwar na farko, dan haka nidai bazan fita ba, tana faɗar haka ta nufi wajen wardrobe ɗin su tace Babyn baby zo ki rufe ni idan na shiga, ki ɗora min wannan bargon. Dariya suka saka mata duk da halin da suke ciki bana dariya bane amma saida sukayi ganin abun da take shirin yi, Haɗe rai tayi ta tsaya tana kallon su kamar zatayi kuka, tace "au dariya kuke min kunma maida ni mahaukaciya kenan ko dan kunga baku za'a kama ba, shikenan tunda haka abun yake na fasa shiga bari inje inma kashe ni yayi sai kufi jin daɗin dariyar, tayi magana cike da dakewa tana haɗe rai dan har cikin ranta take wannan maganar dan sun bata haushi.. Duk da haka maimakon ta basu tausayi amma dariya ta kuma basu saidai yanzu basu bari ta fito ba kowa ya ƙunshe abar sa sai dai ƴar kallon kallon da suke suna ƙara riƙe dariyar su, gudun ƙara tunzurata dan sun lura ta canza gaba ɗaya a tunzure take abu kaɗan sai ta sauke fushin ta akan su, Da sauri duk suka tari gaban ta suka shiga bata haƙuri, Aunty Babba tace haba masoyiyya ai baza'ayi haka ba ba haka muke nufiba, muje in ɓoye ki kawai, kinga ma fah ƙofar da muƙulli ba iya shigowa zasuyi ba ki kwantar da hankalin ki, duk kinbi kin sauya bansanki da tsoro bafa jaruma Beenish, ma yayi miki da har kika fara tsorata da shi wallahi dakewa zakiyi ke ko shi, shima zaiji shakkar ki amma idan kina nuna tsoro haka ai sai yayi galaba akanki kuma ya rainaki, gwanda kema ki nuna masa jaruma ce ke, duk ina jarumtar taki kin mata da maza nawa muke faɗa sai yanzu guda ɗaya ne zai gagare mu har ta ɗaga mana hankalin ƴar uwa ai dole muyi shiri na musamman akan sa koh ya kuka ce? Ta juya tana kallon su, Duk jinjina mata kai sukayi alamun haka ne. Buɗar bakin Beenish kam sai cewa tayi baku da hankali gaba ɗayan ku wallahi nutumin da yake faɗa da mutane sama da ɗari shi kaɗai shine zaku haɗa kanku da shi ku da kuke faɗa da spray ne barkono in kun isa kuje gurin sa a haka kar ku tanadi komai kuga yanda zaiyi da kasusuwan ku, dan bai dake ku bane shiyasa kuke wannan maganar da ƙafa fa kawai ya ɗan taɓa ni saida na bar inda nake na koma ƙasan gado, hmmm idan na faɗa muku yanda naji bazaku gane ba wallahi har yanzu jin dukan sa nake ajikina gaba ɗaya jikina ciwo yake min, ai ƙarfin mu ba ɗaya ba, mu ƙarfinmu dabara ce kawai, amma idan kunga zaku iya dashi bismillah bada ni gaɗa a lahira, dan wallahi bazan yarda mu sake haɗa hanya da shi ba, tana maganar ta nufi hanyar banɗaki ta kuma ƙulle kanta dan har ga Allah ta gama tsorata da shi duk abun da take faɗa da gaske take. Su fa ko a jikin su dan wallahi tana shiga banɗaki suka kuma kwashewa da dariya, suna mamaki wai yau su ake cewa basu da hankali Beenish tayi nisa... Ameela ce ta koma kan gadon tace "tsoro ne kawai da ta bari ya shiga zuciyar ta har take irin waɗannan maganganun, kalli ƙofar ma fa a rufe take amma duk tabi ta tayar da hankalin ta harda ƙara shiga banɗaki ko wa yace mata shigowa zasuyi... Daga waje kam tun sojojin nan na budu har suka gaji sai kawai suka fita daga gidan ma gaba ɗaya kuma suna fita suka tafi da waɗancen mutanen batare da sun kira RK sun sanar dashi abun da ya faru ba kuma basu gaya masa babu ƴan matan ba sukayi tafiyar su a haka. Bulama saida ya tabbatar da sun tafi sannan ya iya fitowa daga inda yake yana sauke ajiyar zuciya harda dafe ƙirji ganin basu gansa ba duk da baisan me ya

Chapter 26 of 44