imani haka ya ringa yi min ihun kare akai saboda jahilci na rantse da Allah bai daki banza ba, wallahi sai na nuna masa ƴar halak ce ni, tana kaiwa nan kuma ta fashe da kukan baƙin ciki dan tana maganar tana kuma jin yanda zuciyar ta take mata zafi, ji take idan ta samu dama sai ta iya raba ransa da duniya...
Rungume ta Ameela tayi tana cewa "kiyi haƙuri dan Allah kibar wannan maganar tundade yanzu ance mu tafi kinga ai anyi mana iyaka da shi, In sha Allah ko hanya bazamu ƙara haɗawa dashi ba, mun rabu kenan, ki taso mutafi.
Shiru tayi tana share hawayen ta amma bawai dan taji haƙurin da take bata ba, dan ƙudurinta na nan bai sauya ba kuma bazai sauya ba bazata taɓa jin sanyi aranta ba in bataga ta ƙuntata masa ba kamar yanda take ji.
Miƙewa tayi tsaye, Ameela ta kamo hannun ta suka fito har yanzu jikin ta a sanyaye yake batajin ƙwari sosai,
Jin zasu fito yasa Moohad saurin juyawa ya bar bakin ƙofar, dan duk yaji me suke cewa.
Suna fitowa daga ɗakin a kan kujera suka ga, su RK shida Ammin sa, tunda suka fito Beenish ta ƙura masa ido tana kallon sa, shima itan yake kallo yanda take aika masa da kallon tsana shima haka yake aika mata dashi har bazan iya tantance waya fi tsanar wani ba acikin kallon da sukewa juna,
Kawai saka ƙafarta take Ameela nayi mata jagora tana janta, shi kuma hannun sa na cikin na Ammi yanda taji yana damƙe hannun ta tasan lalle ranshi a ɓace yake, kuma idan ta bashi dama komai ma zai iya aikatawa, ƴar kallo kawai ta zama ta kalli idon sa ta kalli Beenish abun ya mugun tsaya mata a rai yaushe suka haɗu da har sukayiwa kansu irin wannan tsanar haka kana kallon idon su zaka gane hakan.
Beenish bata janye idonta akan sa ba har saida suka fita daga falon, shi kasa janye nasa ma yayi saboda yanda yake jin sa har yanzu kalamanta basu daina yi masa yawo akai ba, ji yake kamar yaje ya shaƙeta ko ta daina numfashi bazai barta ba, baisan loƙacin da ya shiga ƙoƙarin miƙewa tsaye ba, Ammi tayi saurin dakatar dashi, ita tama rasa me zata ce masa dan abun ya gama sha mata, kai loƙacin da Moohad ya faɗa mata bata yarda ba amma yanzu sai taga abun ma yafi wanda aka gaya mata.
Da ƙyar ta samu damar cewa "calm down please kar ka bar hakan ya dameka wannan ba komai bane ka manta da ita yarinta ce ke damunta.
"Ammi" bata da kunya bakiji irin maganganun da take gaya min am not her mate, amma zata tsaya gaya min magana how u can imagine ta ɗaga hannu ta mareni amma duk da haka Ammi kike cewa ba komai bane in rabu da ita why Ammi? Taya zan iya yin hakan, how Ammi? How how? I swear I will never leave her Ammi without punishment..!!!
"Ya Allah, Allah na gode maka da kaban ɗa me jin magana da haƙuri irin wannan, yanzu ɗan albarka a gabana kake irin wannan furucin yaushe wai ka canza hali ko daɗewar da mukayi bama tare wasu suka gurɓata min tarbiyyar ka, yau ni nake faɗa kake faɗa, nace ka rabu da ita kana gaya bazaka taɓa barinta ba, Tom shikenan ai yanzu ka isa da kanka sai kayi abun da kake so, bazan kuma saka ba ko in hanaka ba, kayi duk abun da kake so, tana faɗar haka ta cire hannun ta daga nasa tana shirin tashi tsaye, da sauri ya riƙota yace "Ammi no ki daina faɗin haka, ya kamata ki fahimce ni, ki gane tunda kikaji na faɗi haka abun is too touch me it's painful, I'm very shocke da ta min wannan abun babu wanda ya taɓa yi min irin a duniyar nan Ammi yarinya ce fa ko sa'ar Faheema bata kai ba, amma kike cewa in rabu da ita, Ammi Please try to understand me.
Haɗe rai tayi tace "kayi abun da nace kada kasake kabari naji ance ka kuma shiga harkar su in ba haka ba kuwa zamu ɓata da kai kuma saima sanar da mahaifin ka, tana gama faɗin haka ta ɗau jakar ta ta fice daga falon, be kuma yin magana ba bare ya hanata fita harta fita gaba ɗaya.....
Yadai jita amma baya jin wannan karan zai yi abun da take so dan yanda yake ji bazai iya barin yaran nan su ci gaba da walwala ba batare da ya koya musu hankali ba musanman wannan yarinyar da ta mare sa...
$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*GHAMBURJ*
___Sosai Bilal yake kuka da jin wannan mummunan labarin, Zaid ne shima kamar yayi kukan ya zauna yake basa haƙuri amma ina yaƙi yayi shiru su kam ƴan matan ma mamaki ne ya kamasu ganin ƙato da shi namiji ya zauna yana kuka, alhalin ko su da suke mata basuyi ba, sai shi shafaffe da mai.
Da ƙyar dai suka samu yayi shiru, nan dai suka kuma tattaunawa a tsakanin su, suna zage hajja mama tass, saboda da suna da yawa yasa kowa ya saki jiki har suka ɗan ci abinci duk da ba daɗinsa suke ji ba, yanzu duk hankalin su yayi gida musamman Bilal da Zaid,
Bayan sun gama ne Salma ta tashi tare da zuwa wajen wani window tana leƙen waje sai taga ai kamar ma dajine wajen, tana shirin barin wajen ta hango Hajja Mama tana ta sauri daga nan kuma taga tayi wata kwana tanayin kwanar kuma ta daina ganin ta, da sauri tace "kuzo ku gani kunga matar nan har tayi kwana.
Da sauri duk suka tashi suna rige rigen zuwa, saidai ko da suka leƙa ɗin daji kawai suka gani.
Faheema ce tace "ai daji ne ma, yanzu bazamu iya fita ta windown nan ba, duk window suka shiga bi da kallo Salma tace "ke yanzu taya zaki iya fita daga fara gwada sai muma muyi.
"Bilal yace "wai bata ce ƙofa a buɗe take ba saidai karnuka ta gashi wajen kuma babu karnukan kawai dai daman tsoratar da mu take.
Zaid ne yace "daɗi na dakai baka da tunani kawai sai ta kama barin ƙofa a buɗe ashema ba sato mu tayi ba.
Ɓata rai Bilal yayi jin yace masa marar tunani a gaban ƴan matan salon su raina sa.
Faheema ce me irin tunanin Bilal ɗin tace "kuma fa hakane, bari muga, tana zuwa ta murɗa ƙofar ga mamakinsu kuwa sai suka ga ƙofa ta buɗu, farinki ciki ne ya kamasu gaba ɗayan su, suka nufi ƙofar basuyi tunanin komai ba kawai duk suka saka kai suka fita suna fita ƙofa ta rufe, tafiya suka fara yi sai suka gansu kawai a ƙaton waje ga kuma ƙofofi sude inda suke saka ran itace hanya suka bi dan basu tsaya bi takan kofofin ba, sude burin su kawai su gansu a wajen dajinnan, murna kawai suke yau zasu fita, musamman su da suka daɗe a cikin gidan,
Tafiya sukai sosai amma har yanzu sun kasa gano inda zasu bi su fita daga gurin, daga sunyi inda suke tunanin hanya ce, sai suga ba haka bane, ga gurin shiru kamar babu kowa a ciki, sun sha wahala sosai kafin suka zo wajen wani window me glass da har zasu wuce, Bilal yace musu, tundade muna hango wajen kawai mu fasa glass ɗin tunda babu ƙofar fita.
Nan sukabi shawarar Bilal saidai kuma abun da zasu fasa ɗin suke tunani laluben makami suka shigayi amma basu samu ba, nan Faheema ta cire takalmin ƙafar ta da yake da ɗan tudu, ta bawa Zaid tunda shine babba acikin su kuma zai fisu ƙarfi, a hankali ya shiga dukan gurin bugu ɗaya kuwa ya tsage, yana kuma bugawa da ƙarfi ya tarwatse ya saura kaɗan ya shiga masa ido su kuma duk tsugunnawa sukayi.
A hankali suka shiga fita cikin da bara kar su yanke har suka gama fita gaba ɗayan su, nan ɗinma de da suka fita sai suka ga zagaye yake da katanga, tafiya sukaci gaba dayi, suna tafiya suna hira hankalin su kwance, sun kusa tsakiyar wajen sukaji haushin karnuka da suka rasa ta inda suke, nan fa ido ya raina fata musamman da suka tuna da maganar Hajja Mama, tsayawa sukayi wannan ya kalli wannan ya kalli wannan sun kasa motsawa, basu ankara ba saida sukaji haushin ya kusantosu.
Ihu suka saka gaba ɗayan su suna juyawa da gudu kowa takansa yake babu wanda yasan yana da gudu sai yau, amma fa gudun kare da mutum ba ɗaya ba, tuni mahaukatan karnukan suka kusan kamasu, suna zuwa daidai wani waje kawai sukaji ansaƙalo ƙafafun su duk zubewa sukayi suka faɗa da gaba, babu wanda baiji zafi ba haka suka kuma miƙewa zasu gudu duk sukaji ƙafafun su a saƙale ga karnukan sun kusan cinmasu gashi basuga kowa agurin ba, daga su sai filin Allah sai igiyar da ta riƙe su, sai kuma karnukan da suka zo dab dasu kowanne su ma zaro harshe...✍️
*Comment ɗinku shi zaisa inji ƙwarin gwiwa in ringayi musamman yanzu da na daɗe banyi typing ba, inbakwa ƙarfafamin gwiwa, taya zan iya, jiya na fara amma masu comments kaɗanne, to gashinan kunga alama tun anan dan wannan baifi rabin najiya ba, shima da ƙyara nayi, gsky ba kamar da ba duk kunyi shiru hmmm*
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
[4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
_______*08124226526*_______
*_episode 38💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
Bismillah..✍️
_____Gaba ɗaya karnukan sukayi kansu saura kaɗan su cije su, da sauri me tsaron su ya ƙaraso wajen tare da yiwa karnukan magana, suka dakata daga abun da suke shirin yi.
Duk korasu yayi gefe ya tsaya yana kallon yaran da duk sun gama ficewa daga ahayyacin su, ihun wannan na wuce na wannan ba ga mazan ba baga matan ba kowa ihun yake, ashe duk matsorsta aka tara, su malam Bilal kam harda kuka shida su Faheema Zaid ne dai ihun kawai yake amma babu ƙwalla.
"Abun da zaifi muku sauƙi shine ku koma inda kuka fito in bahaka ba kuma bazan ƙara taimaka muku, dan wahala zaku ci baza ku taɓa iya fita daga gidan nan, zaifi muku kyau da ku koma ɗin, amma in kunji shawarata in ba haka ba kuma jiki magayi.
Yana kaiwa nan yaja karnukan sa suka tafi.
Babu wanda ya samu damar tashi akan loƙaci saima ƙara bajewa da sukayi suka kwanta agun, Salma ce ta kalli Bilal dake gefen ta, taga yanda yake ta faman sharar hawaye, yana gogewa da hannun kamar wani ƙaramin yaro bata san loƙacin da ta kwashe da dariya ba tana nuna sa da yatsa tare da tashi zaune,
Suma tashi sukayi zaune suna taya ta dariyar duk da basu san me takeyiwa dariyar, Bilal kam da yasan dashi take sai yayi saurin haɗe rai cike da jin haushin ta.
"Dan Allah ku kalli wannan ragon ko ni banyi kukan da yake ba, sai kace mace amma kaidai rangwanta tayi maka yawa abun kuka baya maka wahala.
Zaid yace kaɗan ma kika gani indai wannan yaronne babu abun da ya iya in banda bacci.
Bilal najin su bai tanka musu ba saima miƙewa da yayi ya tashi ya zare igiyar dake ƙafarsa aikwa gurin har yayi ja, yana ganin yanda gurin yayi yaji kamar ya kuma sakin wani kukan amma ganin yanda suke masa yasa ya juya kawai ya fara tafiya yana wani haɗe rai.
Da sauri Salma ta tashi itama cikin sauri tabi bayan sa tana cewa haba ɗan Boy sorry na dena tsaya mu tafi tare, tana tafiyar kuma still tana yi masa dariya bai kulata ba yaci gaba da tafiya,
Su Zaida ma tashi sukayi suka bi bayan su da sauri harda ɗan gudu- gudun su, dan har sun ɗanyi musu nisa.
Salma tana zuwa ta riƙo hannun sa tace; "sorry fa nace maza, kaiɗinne kake abun mata, yanzu daka haɗe rai har ka koma namiji wallai.
Ƙwace hannun sa yayi ƙoƙarin yi saita ta riƙesa sosai tace "Allah bazan sake ka ba salon kaje ka ɓata Hajja Mama ta huce akanmu tunda ance tafi ji dakai, ni lallaɓaka zanyi wallahi ko ta soni nima.
Bai kuma yunƙurin ƙwacewa ba ya rabu da ita tana ta zuba shidai tafiyar sa kawai yake.
Su Zaida ci gaba sukayi da kunna sa suna tsokanar sa, musamman Zaida ya saba daman, saida suka gama yi masa sannan suka dawo kan maganar fitowar tasu sunayi suna dariya suna maida yanda akai, Bilal ma a loƙacin ya saka baki saidai shi baiyi dariyar ba, shi daman baifiye yi ba, indai ba a wajen mahaifinsa yake ba, anan zakaga dariyar sa sosai, duk tafiyar da suke Salma na riƙe da hannun sa.
Tun suna tafiyar cikin daɗi har suka fara gajiya gashi basu kusa zuwa ba.
Suna cikin tafiya Bilal ya tsaya da tafiyar tare da marairaice fuska yace nifa wallahi bazan iya tafiya ba, na gaji bantaɓa irin wannan tafiyar ba.
Duk tsayawa sukayi shima Zaida yace to da waye ya taɓa yin irintar muma duk babu wanda ya taɓa yi ɗin, da haka zaka daure yaro duk bama kai kaja mana ba, muna zaman mu lafiya ga abun da ka jawo mana, da baka buɗe ƙofar ba ai da tuni hakan bata faru ba.
Faheema tace "eh da laifin sa amma muma da namu laifin me yasa bamuyi tunani ba muka biye masa yanzu ai gashi abun da ya faru, ni wallahi ma bansan ta inda zamu koma inda muka fito ba.
Dariya Salma tayi tace "ta inda muka fito tanan zamu koma ko zamu kwana a hanya.
Duk surutan su bai damu Bilal ba saima tsugunnawa da tayi agun da yaji hakan bai masaba sai ya zauna kawai yana miƙe ƙafa yana kallon ƙafar tashi da yaga duk ta kumbura.
"Ɗan Boy wai meye hakan ka tashi mutafi dan Allah.
Yatsina fuska yayi kamar zai fashe yace "wallahi da gaske nake bazan iyaba kinga fa yanda ƙafata tayi gashi sai zafi take.
"Faheema tace "to pha wata sabuwa yanzu ya kake so ayi kenan anan zamu barka ka taho daga baya ko kuwa.
Zaid yace "eh hakan za'ayi mana, da tafiya a gabanmu amma mu zauna ai wannan hutun jaki da kaya zamuyi gwanda kawai mu ƙarasa, idan munje ma samu mu huta gaba ɗaya.
Salma ce ta tsugunna a gaban sa tace "kayi haƙuri muje kaga bazasu jira mu ba, indai ta nice zan jiraka ka huta, kuma kaga yamma nayi kar dare yayi mana a hanya mu kasa gane inda zamu koma, gashi karnukan nan kar su kuma dawowa.
"Wai baku da ido ne bakuga me ƙafata tayi ba nace muku bazan iya ba bazan iya ba amma kunƙi yarda, ku bari idan na huta wataƙil in iya takawa.
Tsaye sukai kowa baki sake suna kallon sa, basu san ma ya zasuyi da shi ba,
Zaida ne yayi gaba yace "nidai kunga tafiyata idan zaku jirasa sai ku zauna, dan bazan bari yamma tayi ba ina wajennan kun mantama tafiyar dake cikin gidan kafin mu fito saida muka daɗe.
Faheema da Salma duk yanda suka so da Bilal ya tashi amma ya ƙi sai haƙuara sukayi suma suka bi bayan Zaid, a tunanin su idan yaga sunyi gaba ai dole ya tashi ya biyo su, amma har suka ɗanyi nisa baida niyar tashi saima kuka da yafarayi dan dagasken yake bazai iya tashi ba.
Salma ce "gaskiya bai kamata mu tafi mubar sa ba tunda kukaga haka dole kasawar yayi, idan muka koma babu shi mu kanmu bazamu ji daɗi ba, kuma komai ya faru dashi ɗayar matar zata iya ɗaukar mataki akanmu, duk da gaba ɗayanmu babu wanda yayi kalar wahala ko saba irin tafiyar amma shiɗin yafi mu rangwanta mu zamu iya finsa dauriya bamu san waye shi ba bamu san wacce irin rayuwa ya taso ba, dan Allah mu tsaya mu samu mafita akan hakan kunji dan Allah.
Suma daman duk tausayin nashi sukaji musamman da suka fara jiyo kukan sa, Zaid ma kuma yasan halin shi da rashin juriya babu abun da ya iya na ƙarfi ko wahala, hakan yasa suka sauya tunani, sukayi na'am da shawarar Salma suka juyo, amma duk da haka suna tafiya suna mita.
Yanda suka barsa haka suka same ya miƙe ƙafafu yana ta dirzar kuka sai yau yake ta tuna abubuwa da dama, yaji kewar mahaifinsa na taso masa sosai, kukan sa yake bilhaƙi ko tunanin mafita ma bayayi.
Suna zuwa sai ya kuma daɗawa kukan nasa volume, yana kawar da kai gefe shi a dole sun bashi haushi da suka tafi suka barsa.
Duk sunji tasauyinsa amma abun da yayi saida ya basu dariya, Salma ce ta cire ɗan kwallin kanta ta tsugunna tana bashi haƙuri sannan ta kamo fuskarsa ta shiga goge masa hawayen da duk ya ɓata fuskar tasa har tayi ja idon sa ya kumbura.
"Yaya Bilal yanzu ya kake so ayi duk so kake mu zauna sai sanda ka gama ko kuwa ɗaukar ka zamuyi.
Da sauri ya ɗago ya kalle sa jin wai ko ɗaukar sa zasuyi da girman da taya zasu iya ɗaukar sa, a fili kuma sai yace "ba tafiyar ku kukayi ba, to ku tafi mana ni nace ku dawo.
Sun san kawai faɗe yake amma ƙarya yake yace so yake su tafi,
Faheema ce ta zauna kusa da ƙafafunsa hannu ta ɗora ta danna ƙafar da ƙarfi, take ya saki ƴar ƙaramar ƙara, yana riƙe hannun ta.
"Ka tsaya mana idan aka ɗan matsa maka zakaji sauƙin ta sai ka lallaɓa mu ƙarasa.
Salma tace "eh Boy ka bari a matsa maka bari inyi maka ɗayar zakaji sauƙi sosai Sa'a mu tafi.
Shiru yayi baice musu komai ba suka shiga mammatsa masa ƙafar, tun yana jin zafi kuma har ya fara jin ba zafin.
Zaid kam gefe ya koma ya zauna ya zuba musu ido.
Sunkai wajen minti ashirin suna yi masa sannan suka barshi haka, suka ce ya gwada miƙewa, sosai yaji raɗaɗin ya tafi yana miƙewa ma yaji ya iya tsayawa.
A hankali ya furta musu "thanks.
Ɗan murmushi kawai sukayi masa sannan Salma ta kuma riƙo hannun sa suka shiga tafiya.
Zaid kam taɓe baki yayi yana cewa; "rago kawai.
Harara Bilal ya jefa masa batare da yace dashi komai ba suka ci gaba da tafiya....
$$$$$$$$$$$$$$$$$$$
*BULAMA*
Suna ƙarasawa cikin falon yacewa Commissioner ya shiga ɗayan falon bari yaje ya kaita ɗaki ya dawo.
Shidai bin duk abun da yace yayi yake, haka ya shiga falon yayi zaune yana tunani abun duniya duk ya isheshi yauɗinna, ya daɗe zaune cikin falon kafin Bulama ya shigo ciki, guri ya samu ya zauna yana facingvɗin shi fuskar sa ɗauke da murmushi da kamar ɗabi'ar sace yawan yin murumishi dan ko mugunta zaiyi sai yayi wannan murmushin a jikin sa yake.
"Commissioner da kansa meke tafe dakai Allah ya taimake ka ina cikin garin dan jiya jiya na shigo.
Saida Commissioner ya ɗan numfasa kafin yace "wai sun kore ni daga aiki yau suke aiko min da takarda harda gargaɗin in banmu su gida sun ban 24 hours.
Murmushin dai Bulama ya kuma saki me ƙayatarwa dan har haƙoransa na bayyana, yana jinjina kai yace to kuma shine me? Shine zaka ɗaga hankalin ka, ni daman tun farko nakyi maka sha'awar aikin nan ba dande ka nace yasa na shiga ciki aka baka, ga ayyuka nan kala kala da zaka samu kuɗi fiye da wannan da zasu biya ka, ƙarewa ma a gidan su kake zaune, yanzu kuma idan ta kasance suka kore ka saika koma ina, wannan gangancin ne Malam Khamis nifa da zaka bi ta shawarata kar ka kuma ɗaga murya akan maganar ka banmusu ka shigo sana'ar mu a dama dakai zaka samu alkhairi kaine kaƙi don kayi kuɗi tuntuni amma da yanzu kafin haka, amma ka tsaya kana fama da aiki a ƙarƙashin wani haba Khamis, amma zan baka loƙaci kayi tunani akai idan kuma kaga can ɗin kafi so kayi min magana zansa a mayar dakai.
Nauyayyiyar ajiyar zuciya commissioner ya sauke cike da nazarin maganar da Bulama yace masa, shi bawai kuɗinne baya so ba, yana so amma tasu harkar ce kamar bazai iyaba, baya so ya fiya wasa da rayukan mutane su kuma abun su kenan yana jin tsoron ranar da asirin su zai tonu azo a haɗa dashi, su basu da iyalai shikam ƴaƴan sane abun ji, ya tabba sace ɗansa da akayi yana da alaƙa da zargin sa yana cikin su shi yasan hakan ce zata faru shiyasa ma yabar lamarin da tunanin sa masu zaman kansu ne amma yasan bamuyi haka ba, loƙaci guda zasuyi maka abun da kayi musu ba wani jan loƙaci dan basu da tsoro, shiyasa ya daina zargin su, amma rashin sanin su waye suka yi hakan na matuƙar ɗaga masa hankali...
Taɓasan da Bulama yayi ne yasa shi dawowa cikin hayyacin sa, yana mai maida sunansa gare sa.
"Khamis 1tunanin me kake yi ne haka ina magana ko kina bakayi.
Murmushi ya ƙaƙalo ya aza a fuskar sa, tare da girgiza, yace "ina tunanin da kace nayi ne amma dai kaban loƙaci to amma inda matsalar take da akace nan da 24 hours in tashi idan na tashi bansan inda zanyi ba kasan ba wani planing ne da ni ba, ban ajje komai ba, a samu kawai a biyawa kai buƙata.
"Kar ka damu da wannan indai gida ne ka zaɓi duk wanda yayi maka a cikin nawa ka ɗauka na baka kyauta.
Cikin jin daɗi yace "gaskiya naji daɗi Alhaji nagode kuma sosai, sai yanzu naji hankalina ya ɗan kwanta, saidai akwai wani abu da zanyi akwai wasu ƴan mata da muka samu saɓani to sune suke yawan dagulan lissafi ina raba ɗayan biyu ma yanzu haka da haɗin kansu wajen korar nan tawa, dan dama sunce sai sun sa an koreni da aikin da na dogara dashi, saboda ɗan wani saɓani da muka samu da su tunda daɗewa.
"Ban fahimce ka ba, bansan inda maganar ka ta dosa ba, fahimtar dani, nan ya kuma yi masa bayanin su, yanda wasu abubuwan suka faru a tsakanin su saidai bai gaya masa asalin haɗuwar tasu
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 32 Chapter of 44