Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mutane cikin guarding ɗin gida dan cikin fako yayi musu kaɗan, manyan baƙi da ƴan gida ne kawai aka shigar da su falo. A nan su Beenish suka rabu tabi bayan Faheema dada gudu inda take jiyo muryar ta tana ta kurma ihun a sake ta, Yaude kowa yaga tashin hankalin da bai taɓa gani ba, duk da yawanci kowa mamakin abun da ya faru yake, duk da basa wajen gurin amma hankalin su a tashe yake. RK kam duk da haka bai tashi daga inda yake ba, sai dai sojojin gurin da duk sukayi masa runfa suna kare sa, sai daga baya de da yaga abun yaƙi ƙarewa sannan yace su matsa masa miƙewa yayi daga inda yake ya tunkari tsakiyar gurin, zasu bishi duk ya dakatar da su, duk da ba haske sosai amma ana iya ganin na kusa dakai. Shima gurin da yake jiyo muryar ƙanwar sa ya nufa dake sauri yake yi ma sai ya riga Beenish ƙarasawa yana zuwa kuwa shi kuma Magana ɗaya yana shinrin sakata a motar ƴan sandan, wata uwar damƙa yakaiwa damtsen hannun sa da a take ƙashin sa yayi ƙara wulli yayi dashi gefe guda baiyi duba sa kayan ƴan sandan dake jikin sa ba, kamota yayi ya fito da ita, duk da baya gani sosai amma yasan itace, wani waje ya kuma nufa da ita, Suna juyawa ita kuma Beenish na ƙaraso ganin dishi dashin juyawar su yasa tayi tunanin ko duk wanda yake son ɗauke ta ne, sai ta kuma bin su, da gudu har tana karo da muta ne ta faɗi ƙasa ɗagowar da zatayi taga babu su, tashi tayi ta ci gaba da tafiya zata wuce wani guri kenan taga kamar wasu mutane suna jan wani mutumi sun saka masa ƙyalle a fuskar sa, A kalar ta ta juya zuwa gurin, da sauri wani ya sha gaban ta, har tana karo dashi, hannun ta ya riƙe ita kuwa ta kai masa duka gefen fuskar sa, tana ƙoƙarin ƙwace hannun ta, shi kuma yana janta, ji tayi an ƙara riƙe ɗayan hannun, nan hankalin ta ya fara tashi saboda duk babu komai da zata iya ceton kanta, gashi ita kaɗai ce hannun ta kuma da zata dake su dashi sun rirriƙe mata shi, janta kawai suke amma duk da haka tana ƙoƙarin turjewa da ƙafar ta a haka har takalman ta suka cire, "Ku sake ni nace, ku sake ni kafin na kashe ku, wallahi zanyi muku illa, basu fasa ba sukaci gaba da tafiya da ita, bakin wata mota suka kawo ta, tana zuwa tajiyo sautin muryar Babyn baby tana cewa "dan Allah ku sake mu wai me mukayi muku, Aunty Babba kiyi wani abu mana. "Babyn baby kiyi shiru haka surutun ya isa haka" cewar Ameela. Da ƙarfi Beenish tace "ya akai haka kuna nufin kun tsaya an kamaku ina Barazana? "Gani" kinji ki da wani Abu zasuyi mana abun da Allah baiyi mana bane muga gudun ruwan su, in sun sha yanzu ai bazasu sha gobe, na rantse da Allah sai mun gutsun uwar commissioner dan durun uwar sa mu zaisa ayiwa wannna izayar.... Bata gama faɗa ba wani ya make mata baki tare da wanka mata mari, amma duk da haka bakin ta bai mutu ba, tace "kaima bana gane kaba zaka ci kutumar uban ka shegu guntun sigari.... Marin ta ya kuma yi, ku saka su acikin mota mu yafi dasu, basai muga a inda zaku ramaba idan kun rayu kenan ai yauce ranar mutuwar ku..... Aunty Babba sai ƙwace ƙwace take dan ita maza biyar ne suka riƙe ta, sauran kuma maza bibbiyu ne suka riƙe ko wancen su riƙon da bazasu iya ƙwace wa ba, duk wannan abun da ake fa acikin duhu ne dan hasken gurin kaɗanne. Buɗe ƙatuwar motar akai zasu fara saka su a cikin motar kawai na gaba yaji an yankar masa hannu da sauri ya sake ta yana riƙe hannun, ba zato ba tsammani saiji sukayi ana ta yankar su da wuƙa wani a wuya wani a hannu wani a ciki, kuma sun rasa wanda yake musu daga sun juya sai suga babu kowa, masu taurin kai duk da haka sunƙi sakin Beenish da Aunty Babba, duk da haka ƙoƙari suke su saka su a cikin motar, Fitt kakeji an cirewa wani hannu ba shiri kuwa ya faɗi yana sakin ƙara, haske ne ya ɗan kawo wal ya ɗauke nan sukaga kamar macece take musu wannan ta'asar, Mutum biyu aka yanke wa hannu fit ya faɗi ƙasa, waɗanda aka yanka kaɗanne suka fara kai duka suma suna zaro nasu wuƙaƙen ashe mutanen ɗan caucau ne suka hallara(magana ɗaya kenan) Fitilar motar aka kunna gurin ya ɗanyi haske, nan suka fara kai nasu wuƙaƙen kan su Beenish, da ta zaro tata kuwa sai da taci uwar tasu a tsawo da kaifi, duk kawowar da zasuyi sai ta kare sannan takaiwa mutum ta yanke sa a hannu, Guri ɗaya su Beenish suka haɗe suna kallon ikon Allah tare da mamaki da al'ajabi da yagama kashe su dan ko ƙwaƙƙwaran motsi basayi saboda mamakin yagama kashe su, dan har suna tunanin waye wannan dan a tunanin su ma namiji ne.. Ita kuwa baza baƙar rigar ta kawai take tana kare su, wani ne ya zagayo ta bayan su, cikin hanzari ya ɗaga tasa wuƙar zai sauke ta akan Beenish dake gefe, saidai baikai ga sauke ta ba tayi wani juyi ta kifa kansa suka faɗi ƙasa, itace akan sa shi kuma a ƙasa, wuƙar ya ƙara ɗagawa zai luma mata tayi sauri ta jirkice gefe ya daki ƙasa, sai loƙacin hankalin me baƙar riga ya dawo kansu, Da sauri ta ƙaraso gurin ta taka hannun sa wuƙar ta faɗi ƙasa ganin Beenish a kwance yasa tayi tunanin ko ya yanke ta, da sauri ta durƙusa ta kamo hannun ta anan glass ɗin idon ta ya faɗi ƙasa nan sukayi ido huɗu da Beenish zaro ido tayi cike da ɗumbin mamaki da ya kusa kashe ta da ranta, Bakin tane ya shiga yin karkawa tana nuna ta da ɗayan hannu zatayi magana kenan ta girgiza mata kai alamu kar tace komai miƙar da ita tayi tsaye tana ɗan bubbuga kafaɗar ta, tana ɗaga mata gira, tana yin haka, ta juya da sauri ta kuma yankar wani da tagani a kusa da su, tana baza rigar ta ta tsugunna agun tana miƙewa kuwa ta zaro wasu ƙananun wuƙaƙe guda biyar ta zube su a gaban su, cikin sauri tayi gaba tare da ɗan ɗaga muraya tace "take carefully" cikin gudu ta ɓacewa ganin su..... Mutanen magana ɗaya tuni tsoro yasa suka fara shiga mota waɗanda suke da damar iya shiga ɗin sauran kuwa suna kwance jini na fita ko motsawa sun kasa. Cikin rawar baki da har haɗa magana kamar masu koyon magana a kusan tare suka haɗa baki su huɗe wajen cewa "Haj...jjj....jjjjja..!!!! kasa ƙarasawa sukayi saboda tsabar mamaki da yagama kashe su.... "Maaamaaa.!!!" Beenish ta ƙarasa musu.... Tsugunnawa Ameela tayi ta ɗauki wuƙaƙen da ta ajiye musu kallon su ta shiga yi tana miƙewa tsaye tace tabbas itace wannan wuƙaƙen ba inda ake samun irin su sai a gun ta... Beenish ce ta matso kusa da ita tana karɓa itama ta shiga gani ta ƙura musu kamar ance zatagan ta ajikin wuƙaƙen. "Wai daman tana raye har yanzu wallahi nazaci ta mutu" cewar Babyn baby. Hannu Aunty Babba ta ɗora akai tana cewa "Oh my God ya Allah he he Hajja Mama na nan a raye? Beenish ce tayi shiru kafin daga bisani yace "Hmm ni daman nasan bata mutu ba, kuma tana sane damu bazata taɓa cire idon ta akan mu ba, duk wani motsin mu zata iya sani mune de bazata taɓa bari mu san inda take ba, kuma maganar gaskiya dole mu nemota ganin ta na da matuƙar muhimmanci a rayuwar mu, "Gaskiya ne maganar ki, ni abun mamakin ma me ya kawo ta nan dan nayi mamakin ganin ta wallahi, inji Ameela. Barazana tace "Kema ai kin san halin ta bai kamata ma kiyi mamaki ba, hmmm Hajja Mama ikon Allah tana nan da halin ta ashe.. "Wayyo Mamana Hajja Mama tawa nikwa ta Allah ni wallahi dama ta ɗan saka ni a gefen rigata ta tafi dani, ji nake kamar na bita" cewar Babyn baby "Ɗan murmushi sukayi gaba ɗayan su, suna cewa "yanzu ma ai da kin bita zaki same ta tana waje inajin.... Gurin ne ya fara washe wa alamun an daina sakin hayaƙin tiya gas ɗin amma fa ba irin namu bane nan kar wasu suji inacewa tiya gas kuma anzauna lafiya ana shaƙar numfashi, irin na ƙasar waje ne kawai hayaƙi ne da shi. Tushh Tushhh Tushhh kawai kake ji ana harbi a waje sosai ƙarar bindugu suke fita, kanaji kasan musayar alburusai kawai ake. Ganin hakan yasa Ameela cewa ya kamata mu bar gurin gidan nan kafin a tado da waccen maganar ta koken bamu da hujjar kare kanmu indai aka gani acikin jakar mu, idan aka gani waɗancen masu zubin jaɓoɓin da kayan su kore kamar gansa kuka, zasu iya jiƙa mana aiki, Beenish tace "To a haka zamu fita kinajin harbin da akeyi ai sai a haɗa damu, ga kuma wuƙaƙen nan a hannu kowa ta karɓi tata, Ameela ta miƙawa Ameela na shirin karɓa kawai idon ta ya sauka akan sunan da aka rubuta ajikin wuƙar, wai Boss, da sauri tace muga sauran ga mamakin su sai su [3/5, 11:57 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅) ______________________________ *_episode 23💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bissmillah.....✍️ ___Jinjina kai yayi sai ya kuma cewa "Ina Sir SMA? (sergeant major of the Army), shugaban sojojin gaba ɗayaiwanda shine ƙarshen muƙami sama da kowa da kowa yake. Kuma shine wanda RK ya fara gaisarwa a airport... Sai loƙacin kowa hankalin sa ya dawo kansa, nan aka shiga neman a amma babu shi babu me kama da shi, a garin laluben sa ne ma akaci karo da wayar sa da ta faɗi, sunji taƙaicin ganin ta saboda da ace tana jikin sa dole zasu iya bibbiyar sa ta hanyar wayar amma yanzu ba su san ma ta inda zasu fara ba, "Sir mun fa duba ko ina babu shi amma de ga wayar sa, suka miƙa masa. suna miƙa masa loƙacin yayi daidai da shigowar sauran tawagar sojojin da suka bi motar basu samo ta ba, hakan yasa suka dawo, dan sanar da RK (General of the Army) Suna ƙarasowa tun kan suce komai ya zare glass ɗin idon sa ya watsa musu wani kallo take duk sukayi ƙasa da kansu dan babu me iya bari ya haɗa ido dashi musamman da suka san abun da sukayi. Cikin ɗaga murya me tare da amo irin ta zaratan maza kuma a matsayin sa na babban soja da ranshi ya ɓaci yana zazzaro musu ido yace "Prepare to move out and hold the line..!! Kan kace me kowa ya shiga hankalin sa, waɗanda ma basa gurin da sukaji maganar sa da gudu su ƙaraso gurin suka shiga yin layi, a ɗan ƙanƙanin loƙaci da baifi minti ɗaya ba da ƴan sakanni suka gama saita kan su, a tare suka buga ƙafafun su na dama tare da sara masa kowa hannun sa a saitin kansa yanda de akeyi idan za'ayi salute ɗin wani ne muƙamin, a tare suka sake sauke wa tare da ƙamewa ƙam baki suka sake haɗawa su ka ce; "Sorry Sir!!! Wani irin kallo yake binsu dashi, hullar kansa dake ɗauke da tambarin sunan sa sai ƙasan tambarin da akayi star biyar ta ban girma, hannu yasa ya janye ta gefe ta dawo saitin kunne sa, facemask ɗin sa ya cire ya jefar dashi gefe, ainahin fuskar sa ta bayyana hmmm abun zan fara cewa shine Masha Allah domin Allah yayi halitta anan gurin fa, kana kallon sa zakace balarabe ne domin yanayin hasken sa da kuma gashin dake kwance a gefen fuskar sa hatta girar sa sun kusa haɗewa saboda yawan gashin gata baƙa ta wani lanƙwasa, yana da manyan ido ga gashin idon sa zara-zara da alama yana da baiwar gashi ga gemun sa da yasha gyara sai ya ƙarawa fuskar kyau sosai sannan hasken sa ya ƙara fitowa tubarkallah masha Allah de kawai zamu ce, amma yanayin halin da yake ciki na rashin annuri akan fuskar yanda ya haɗe ta tamau kamar baisan wani abu sakin fuska ba bare akai ga murmushi uwa uba kuma dariya, Cikin ƙara ɗaure fuska idon sa har ya fara sauya launi dan tsatstsan baƙin cikin da yake ji, murya a dake ya ce" every body get ready to go and find out the solution, If not I will shoot you one by one, "Okay Sir! Suka sake haɗa baki. "kuma ku tabbatar kun dawo min da motar nan, akwai kaya da yawa a ciki, don't let missing the car and all about abun da duk yake cikin ta, duk wata boarder asaka matakan tsaro, da titina da gaɓar ruwa, duk inda akasan mota zatabi ku kira ku sanar da masu gurin su saka ido sosai idan akayi sake aka fita da Sir SMA daga cikin garin nan, ko ƙasar nan you are in trouble gaba ɗayan ku, sannan abi unguwa unguwa a fara checking duk inda ba yarda dashi ba ashiga ayi bincike sannan a rufe duk wasu kasunni da ma'aikatu daga yau zuwa gobe duk wanda ya fito a harbesa did you understanding what I'm saying right? "Yes Sir" "Good dividing your self in to four and go to work. Nan suka fara raba kansu kamar yanda ya faɗa, "Sergeant! Moohad! Daghfal! Gahyoor! Ya kira sunayen su da sauri. Suma cikin sauri suka amsa da "Yes sir!! "Sergeant, ka ɗau mutanen ka kubi duk wata madakatar ruwa. "Moohad duk wajen da iyakar manyan tituna. "Dhagfal, cikin unguwanni da bincika tashar jiragen ƙasa. And you Ghayoor a shiga duk wani dajika dake zagaye da nan., Sauran tawaga kuma ku kula da kasuwanni kada abari kowa ya buɗe shago duk wanda kuma ya fito a harbesa.... Ƙara sara masa sukayi suna na'am da duk umarnin da yayi, a take me kiran waya ya ɗauko wayar sa ya fara sanar da duk wata sanarwa da ta dace ayi, suma sauran duk wanda tawagar sa basu cika ba haka suka ringa kira suna sanar da duk wanda baya nan, Fita suka farayi daga cikin gidan, anan akayi karo da su Beenish suna gurin da aka barsu su kaɗai basu kwa motsa ba suna gurin. Wanine ya daka musu tsawa tare da cewa ku tashi muje..., Miƙewa sukayi duk da babu walwala a tattare da su amma baza kace kuma a tsorace suke ba, duk tsayawa sukayi daga bayan su suna tura su da bundugun hannun su har sun kusa fita suna daf da fita dasu wani sojan ya ƙaraso da gudu ya ce; "Sir GA yana son ganin su. Juya ƙyar su akayi aka juyo dasu sannan wanda ya sanar da saƙon ya saka su a gaba suka nufi inda yake, su kuma suka ƙarasa fita cikin sauri. A cikin minti talatin sukayi duk wani shiri da zasuyi, tuni gari ya fara cika da sojoji ta ko ina, wasu motacin duk sunzo inda suka fita wasu suka fara barin gidan, haka can bakunan titi ma tuni an fara rufe hanyoyi masu gaɓar ruwa ma ansanar da su sun fara aiwatar da nasu aikin, duk yaji labarin wanda aka ɗauke sai ya jijjiga da mamaki, Cikin farfajiyar gurin duk ta doɗe babu kowa duk sun fita yawan cin mutanen gidan kuma tuni ansaka sun koma cikin gidan gurin ya rage daga shi sai wasu mutum huɗu dake take masa baya sai kuma ƴan tsirarun sojoji suma kuma daman masu tsaron gidanne, sai kuma su frBeenish da akasa suka zube a ƙasa suka tsugunna a gaban RK. Tunda ya sallame su ya samu kujera ya zauna tare da ɗora ƙafafun sa akan wata kujerar yana dudduba wayar da ya karɓa ta SMA. Da hannu yayi wa mutanen da suke bayan sa alamar da su basa guri, matsawa sukayi na gefen sa kuma ya kalle sa ya kuma kallon wani guri sannan ya nuna masa cikin gidan, nan ya fahimci me yake nufi, cikin gidan ya shiga, suna zaune agun babu wanda yace uffan, ba jimawa ya kuma fitowa hannun sa ɗauke da leda me ɗan girma, a gaban sa ya ajiye jakar, batare da ya kalle su ba, yace; "Basu" Buɗe ledar yayi, ya zaro wani yadi sai ya miƙawa Aunty Babba dake gaban sa haka yaringa zaro wa yana miƙa musu, duk karɓa sukayi saidai babu wanda yayi yunƙurin ware sa, Miƙewa yayi daga kujerar ba tare da ya kalli inda suke ba, "ka kai su inda suke.. yana kaiwa nan yayi gaba. Yana tafiya, yace ku saka mana, ku tashi mu tafi. Sai loƙacin suka ware duk da sun san meye amma suka ƙi buɗewa sai yanzu, hijabai ne kala kala kowa da kalar tasa, miƙewa sukayi suka saka a jikin su duk kuwa yayi musu kyau sai suka canza kamanni kamar basu ba, Har yanzu babu wanda ya ce komai a cikin su, saida suka miƙe ma sannan Ameela tace Babyn baby ɗauko mana jakunkunan mu, gurin da suka hango mayafen nasu ta nufa taje ta kwaso musu duk wani abun su amma bata ɗauko mayafen ba jakunkunan kawai ta ɗauko sai spray ɗin ta da hango ƙasan kujerar, har ta ɗauko zata miƙe ta hangi wani ɗan kunnen gold ware ɗaya ɗauko sa tayi dan kallo ɗaya tayi masa ta gane ta gansa a kunnen Faheema riƙewa tayi a hannun ta sannan ta juya tabi bayan su dan har sun ɗanyi gaba ma, A cikin wata mota aka ɗauke su tasu kuma akasa wani yabi su da ita abaya, Saida suka hau titi sannan sojan yace musu wacce unguwar ne? "Sambas road, Barazana ta faɗa masa. Da kwatan ce suka ƙarasa gidan ya sauke su, a bakin gate ɗin, duk a gajiye suka fito daga motar, zuge gate ɗin sukayi, wanda ke binsu da motar su ya shigar musu da ita compound ɗin gidan baida girma dan haka yana shiga yayi musu parking ɗin ta, sannan ya fito, loƙacin da ya fito kuma suma duk sun shigo suna shirin shigewa ma, bayan su yabi da kallo yana kallon bombom ɗin su duk da a hijabai suke amma hakan bai hanasa ƙura musu ido ba, Barazana ce ta juyo jin kamar bataji fitar sa ba, tursu tayi ta tsaya ganin yanda ya zubawa sauran ido ko ƙiftawa ma bayayi. "Wait..! Duk tsayawa sukayi suna kallon ta, tare da kallon inda sukaga tana kallo, suna kallon sa yayi saurin janye idon sa cike da kwaɗaituwa da su ji yake kamar yaje ya rungume su. "Me ya faru? Beenish ta tambayi Zee. Batare da ta basu amsa ba tayi gaba Saida tayi taku kamar uku sannan tace"ɗan iska ne kunga kallon da yake faman binmu dashi.. "Aunty Babba kuji da shi wallahi nagaji da yawa bari in shiga daga ciki, inji Beenish.. Aunty Babba ce tace ba matsala kuma kuje bari inje ni, ta faɗa tana kallon su Ameela da Babyn baby, bayan Beenish suka bi, ita kuma tabi bayan barazana da har taje gurin sa. "Kai me kake kallo? Wani kallo ya watsawa Barazana, yana kawar da kai yace; kaya mana. Bai ankara ba kawai yaji ta wanke sa da mari, Aunty Babba ma na ƙarasowa ta sauke masa nata, dafe fuska yayi ransa a ɓace ya ɗago zai rama Aunty Babba ta damƙi hannun sa, tace kar ka kuskura malam tun da kyan ganin ka ka kama hanya ka bar wajen nan kafin mu canza maka kamanni wawa kawai... Tana fadar haka saki hannun sa, Barazana tace "ko ba kaya ba zakaci kutumar uban ka ne waɗannan kayayyakin sunfi ƙarfin uban ka ma baranta na kai, daman iskan ci aka ce kazo kayi mana, wallahi kaci sa'a amma da saina tsiyayar maka da idanu anan gurin wawa kawai a jawo, na mamajo kwarton banza kwarton wofi.... Kawai kallon su yake amma ya kasa taɓuka komai saboda tunawa da yanda yaga suna faɗa ɗazu yasan yanzu shi kaɗaine kuma bashi da komai da zai tsorata su shi kar yaje su illata sa, shiyasa ya yafawa kansa ruwan sanyi cikin salama ba tare da yace musu komai ba, sum sum yabi gefen su yana girgiza kai, abun da ya iyayi kenan ya wuce ya fita daga gidan. Saida suka ga fitar sa sannan suka juya suka shiga ciki, suna tafiya suna ci gaba da surfa masa masifa sai kace yana gurin har yanzu. *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *Hajja Mama* Gudu kawai take shararawa akan hanyar ta sai motoci uku da suke bin bayan ta, motar da aka kawo RK ita take tuƙawa, gudu suke sosai kai kace zasu kife saboda tsabar gudu, Basu tsaya ko ina ba, saida suka zo inda zasu zo loƙacin da suka zo gari ya ɗan fara washewa dan sallar asuba ma a hanya sukayi ta, duk fitowa sukayi daga motocin buɗe, bayan motar taje ta buɗe, saiga wani babban mutum a ciki sai kuma budurwa duk a kwance alamun de kamar a sume suke, macen ta fara ɗagowa sai loƙacin naga ashe Faheema ce, ɗayan kuma de SMA ne. Kamasu sukayi duk suka sakasu a cikin jirgin ruwan, sannan ta buɗe booth ɗin motar saga wasu manyan jakunkuna guda uku da ƙyar ma suka iya ɗagosu suka saka a cikin jirgin ruwan, saida suka tabbatar da sun ɗauki duk wani abun da suka san zasu ɗauka, sannan Hajja mama tace suyi gaba zata biyo su su tsaya a bakin ruwan furjaj haka kuwa sukayi suka tuƙa sukayi gaba saida da taga sunyi nisa ma sannan ta kuma shiga motar ita sa sauran ta wagar suka kuma juyawa hanyar da suka biyo ta cikin dajika suka ringa bi, saida sukayi nisa su masu motocin sukayi wata hanyar daban ita kuma taci gada da tafiya, saida tayi nisa sosai ta saita wata hanya sannan ta tsayar da motar cikin sauri ta fito daga ciki wata igiya me ƙwari ta ɗauko a ciki, sai taje ta ɗauro bayan motar dashi sannan taje jikin wata bishiya ta ɗaure ajiki, dawowa tayi ta shiga motar ta tayar da ita sannan ta kuma fitowa ta samu wani ƙaton dutse me nauyi ta ɗora sa akan total ɗin motar sai ta kunna giya motar na ta ƙara, da sauri ta fita ta rufe motar sannan taje wajen bishiyar ta kunce ɗaurin da tayi nan kwa mota ta tafi da gudu kamar da mutum a ciki daman hanaya ce street dan haka tafiya kawai take. Tana ganin tafiyar ta juya da gudun gaske tabi wata hanya, wani rami ta shiga shima saida ta ɗanyi tafiya sannan tazo wajen wani ruwa kamar ɗan ƙaramin kogo haka gurin yake sai kawai tayi tsalle ta faɗa ciki, ashe ruwan me yawa ne, saida tayi kwana saiga shi ya bayyana me yawa, iyo kawai take kamar kifi, ko ɗagowa ma batayi saboda tsabar ƙwarewa, saida tayi tafiya me ɗan nisa sannan ta kawo bakin ruwan da tace musu su haɗu, tana fitowa ko kaya bata sauya ba, ta shiga jirgin suka ci gaba da tafiya.

Chapter 17 of 44