Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
wuya ba, yau sunyi babbar ganawa da Sojan Beenish, Da sauri Beenish ta haɗe rai tare da jifanta da kofin dake hannun ta, tace "wai ke har abun burgewa ne a wannan labarin da kike shirin bada shi, to wallahi baki isaba ke bakyama jin haushin abun zaki iya zama ki bada labarin abun da ya faru, to wallahi baki isa ba, saidai idan bama gurin. Dariya Ameela tayi ganin bilhaƙƙi da gaske Beenish take yanda ta haɗe rai take masifa, sai kace ita aka jibga. "Allah me hanani labarin nan ban gansaba, mutum ɗayane zai hanani, uwar gayyar ta buɗi baki taban haƙuri tace dan Allah kar na faɗa to naji bazan bayar ba amma muddin ba'ayi haka ba to fa sai na faɗa, Babyn baby kina so kiji ko? Da sauri Babyn baby ta ɗaga kai tana murmushi. "Ameela zamu sami matsala dake wallahi kar ki sake ki kuma magana anan gurin, cewar Beenish. "Allah sai na yi kuwa, Zee Barazana Zee Fashion ko ba kuɗi akwai iya taku me baƙin, waini ji nake jiya kince baza kiyi shiru da bakin ki ba, Allah yabaki baki a hanaki magana, yanzu kuma da muke son kiyi shine bazaki yi ba, rabona da jin muryar ki fa tunjiya da kina ihu, Baby ɗan ɗauko min waccen wayar wutar in baki labarin abun da ya faru da ita. Allah sarki Barazana duk yanda taso ta tanka ma Ameela kasawa tayi saboda tana magana zata iya yin kuka, dan haka sai kawai ta miƙe zata bar wajen sukaji anbuga musu ƙofa, dakatawa tayi da tafiyar. Maryam ce taje ta buɗe dan daman tun ɗazu take zuba idon ganin ta. "Sannu da zuwa. "Yauw" Hajiya Dannar tace tare da ƙarasa shigowa cikin falon, tana ta faman sakin murmushi abun ta, Ameela na ganin ta ta haɗe rai kamar bata taɓa yin dariya ba, tashi taso niyar yi Beenish tayi saurin riƙe hannun ta, hakan yasa ta zauna tana kawar da kai gefe. Gaisawa suka shiga yi, kowannen su na gaishe da ita amma banda Ameela da ta kawar da kai gefe, Zee ma dai da ƙyar ta iya gaida ta. Bayan sun gama gaisawar ne, Hajiya Dannar ta ce "to sauri nake wallahi yanzu zan sanar daku abun da ya kawo ni ina fatan zaku ban haɗin kai domin akwai abun da na hango muku wanda ku baza ku gane hakan ba, sai nan gaba, to yanzu dai batare da ɓata loƙaci ba, ina son neman wata alfarma agunku ba daɗewa zakuyi acan ɗin ba, kawaidai zakuyi na zuwa wani loƙacin, komai ma daidai ta in sha Allah zaku bar aikin, shiru tayi tana nazarin su da kallon kowanne su, su kuma sun matsu suji me zata ce mu su. "Ba komai bane daman jiya naji labarin za'afara training a Lagos za'a ɗauki mutum ɗari kawai zasuyi gasa acikin su kuma za'a ware mutum hamsin suma hamsin ɗin mutum ashirin ake buƙata abunde mataki mataki ne idan kunje zakuji ƙarashen labarin, duk wannan abun bata gaya musu meye ba, "Wane irin training Ammu, Beenish ta tambaya, Murmushi Hajiya Dannar tayi cike da fargabar yanda zasu ɗauki maganar tace "aiki soja. Duk zaro ido sukayi cike da mamaki suke kallon ta, wannan karon hatta Ameela saida ta juyo ta kalle ta batare da tasan tayi ba, Abu kuwa bata san loƙacin da ta miƙe zaune ba, "Soja fa kika ce Ammu? Cewar Beenish dan itace me bakin bada amsa. Girgiza mata kai tayi, tace dan Allah kar ku tambaye ni dalili amma dai muddin kuna so wasu burukan naku su cika to sai kunbi ta wannan hanyar, Tana cewa buruka Beenish ta tafi tunanin, take wani tunani ya faɗo mata, tabbas Ammu tayi gaskiya dole sai sunbi ta hanayar zasu samu cikar wasu burukan nasu, itama kuwa tana da wannan burin dole ta hanyar ce zata iya samun damar yin ramuwarta, daman tun jiya take ta tunanin ta yanda zata cika wannan burin mata to ga dama ta samu ai zama ta amince ko su sauran baza su Amimce ba...✍️✍️ *Da banyi niyar gaya muku abun da ya faru ba, amma dai kwada kuji, yau nayi abun da na daɗe banyi ba, saida na gama typing kaɗan ya rage na kammala na yau, kawai ya goge gaba ɗaya 😭 shiyasa kukaga nayi dare sai bayan sallar magriba nayi muku wannan da ƙyar dan wallahi da cewa nayi ma na fasa sai gobe kuma banaso inyi muku fashi wallahi 😭😭* *Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa* _Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_ [4/19, 10:28 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) _______*08124226526*_______ *_episode 41💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 *Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526* Bismillah..✍️ ____Tana cewa buruka Beenish ta tafi tunanin, take wani tunani ya faɗo mata, tabbas Ammu tayi gaskiya dole sai sunbi ta hanayar zasu samu cikar wasu burukan nasu, itama kuwa tana da wannan burin dole ta hanyar ce zata iya samun damar yin ramuwarta, daman tun jiya take ta tunanin ta yanda zata cika wannan burin mata to ga dama ta samu ai zama ta amince ko su sauran baza su amince ba... "Amma ya kuka gani idan bakwa so bazanyi muku dole ba. Da sauri Beenish tace "mun amince Ammu, ai duk abun da kika ce daidai ne, zamuyi. Daɗi Hajiya Dannar taji marar misaltuwa bata taɓa tunanin batare da ta gaya musu dalili zasu amince ba, ba ita kaɗai ba, Maryam taji daɗin jin hakan. Ameela kuwa bata san loƙacin da ta miƙe tsaye ba, cike da masifa tace "me kika ce, kinsan kwa me kike faɗa Beenish, akan wane dalili zamu amince mu da ko makaranta ma bamu gama ba, to kima canza tunani ko kuma kije ke kaɗai dannidai babu inda zani, Barazana ma ta samu damar magana yanzu cikin muryar ta da bata fita sosai tace "nima gaskiya Ammu kiyi haƙuri amma bazan iya zuwa ba, ko kayan ma banason ganin sa bare masu sakashi bare kuma ace ni zan saka gaskiya bazan iya, kuma kema da kike cewa kin amince to babu ni babu ke daga ranar da kika fara saka kayan mun raba gari dake dan Allah duk sanda ma kika san zan iya kasancewa agu to kar kizo nima kuma bazan zo inda kike ba dan Allah kar ki amince, in kuma kema so kike ki koma muguwa marar imani da tausayi to nidai ba ni ba ke. Harara wasa Beenish ta jefa mata tana cewa "Ammu kar rabu dasu duk zasu je kar kibi takan su, su yara ne har yanzu basu san rayuwa ba ne. "To sannu masaniya ke ai sai kije amma ni kinga tafiya ta ma, Ameela na faɗar haka ta nufi ɗakin su fuuuu kamar zata tashi sama, dan ita maganar ma haushi take bata. Sosai Hajiya Dannar ta nuna jin daɗin ta a fili sannan tace "to shikenan nagode nagode my daughter, amma fa sai ku fara shiru tun yau dan gobe da safe zaku tafi inaso kubi jirgin ƙarfe goma dan naji da wuri zasu fara taron kafin a ɗibe ku. "Adai ɗebe ta dan wallahi babu inda zani saidai ko idan su tafi da Babyn baby daman tare muka gansu amma wallahi inason lafiyata bazanje a sauya min siffar jiki ba, a koya min baƙin hali da mugunta, da rashin tausayi. Tunda suka fara maganar Babyn baby ta saki baki tana kallon su, sai yanzu da Barazana ta yi wannan maganar yasa tayi saurin cewa "gaskiya nima bazan iya zuwa ba kuma bazan iya zama babu yaya ba a kusa dani ba, Ammu dan Allah kubar wannan maganar kowa fa da burin abun da yake son zama idan mun kammala karatun mu amma kuma akawo wannan zancen da ko daɗin ji babu. Ammu zatayi magana kenan Beenish ta rigata da cewa "daman ai ba dake zamu ba ke zaki zauna anan tare da wannan matar kici gaba da karatunki ki zama babbar likita, kuma fa nima ba wani daɗewa zanyi ba, bakiji me tace ba, na zuwa wani loƙaci domin cikar wasu burukan namu da zarar ya cika fa zamu dawo muci gaba da yanda muke, Ai duk wannan bayanin nata Babyn baby bataji sa ba take idanun ta har sunciko da ƙwalla dan itafa bazata yarda da wannan maganar ba, taya zata zauna babu ita taya ma gidan zai yi mata daɗi, Cike da shagwaɓa saura kaɗan hawayen ya gangaro kana jin muryar ta kasan kuka take shirin yi tace "Dan Allah yaya kar ki min haka kisan bazan iya zama a ko ina ba idan bakyanan, kuma ni wallahi bazan iya zuwa ba, saidai ke ki haƙura mu zauna tare. Barazana da taji zancen bana kwance bane yasa ta tashi zaune tana cewa "Ke dalla wai kike wani saka jam'u mu ba gamu ba, ko ance miki zuwa zamuyi, nida Ameela muna nan babu inda zamu kibari taje idan jikin ta ya gaya mata zata dawo ƙafarta. Kuka kawai Babyn baby ta saki sai kace yanzu yanzu za'ayi tafiyar. Haƙuri suka shiga bata gaba ɗayan banda Barazana, Ammu, Maryam, Beenish. Amma kamar an ƙara mata ma volume ta koma jikin Beenish ɗin taci gaba da kuka banza Beenish tayi da ita daga baya dan tasan idan taci gaba da rarrashin ta zata sa taji ko ta fasa tafiya, amma batajin zata haƙura zata yakice kowa dan cikar burinta. Daga haka Dannar tayi musu sallama tare da kuma jadda musu su shirya, saidai tana faɗa Barazana na kuma cewa bata ba, bata kulata ba tunda Beenish tace ta rabu dasu shiyasa ta rabu da su ɗin, bayan fitar ta, Beenish ta miƙe tsaye Babyn baby ma ta sharar hawaye amma taƙi kulata, saima maida dubanta da tayi ga Barazana tace "ku fara shiri fa dan zuwa babu fashi, "Kidai shirya, Malama ki daina lissafi da ni fa, daman ai duk ke kika ja min wannan abun da baki buɗe ƙofar ba tun farko ai da duk hakan bata faru ba, amma yanzu ga abun da kika ja min nan, ke wallahi ma Allah ya isa ke yakamata ma in tayiwa Allah ya isa kafin shi, dan gaba ɗayan ku ne kuka cuce ni, kuma wuta bal-bal daga ke har shi ɗin bazan yafe muku ba, "Kada ki yafe ɗin ko kinji na roƙi yafiyar ki, zuwa dole yarinya ta shirya, idan so kike ya dawo ya tarar dake a cikin gidan yayi miki maimaici to ki zauna ke kaɗai, nasan next time da katako zai miki, dan haka ya faɗa bayan fitowar ki, mantawa mukayi bamu gaya miki ba, dan shi yace ya fi so yaga ya sauya miki kamannin ki gaba ɗaya sannan zai rabu dake, dan baiyi miki komai ba. Da sauri Barazana tace "dan Allah da gaske kike haka yace? "Hmmm ki tambayi Ameel kiji, ko zan miki ƙarya ne, tana gama faɗa mata haka ta ƙara gaba, tabar Barazana da wasi wasin da gaske ne ko ƙarya Beenish tayi mata. Beenish na shiga ɗaki ta tarar da Ameela ta kifa kai a katifa tana kuka ƙasa ƙasa, da sauri ta ƙarasa kusa da ita tana tambayar ta me ya faru duk akan tafiyar ne, amma sai ta girgiza mata kai alamun a'a. Haƙuri ta shiga bata kawai dan tasan bazai wuce zuwan Ammu bane ya sata kuka. "Beenish wai me Ammu take nufi dani ne, na gaji da wannan rayuwar ta faɗa min ko ni wacece amma taƙi, me yasa take min taurin kai akan rayuwa ta, saidai ta juya Ni yanda take so, amma ni bazatayi min abun da nake so ba, me yasa Beenish, tayi maganar tana kuma ci gaba da goge hawayen da yaƙi ya tsaya. "Ameela ki nutsu ki ban hankalin ki nan, ina so daga yau ki cire wannan tunanin a ranki dan Allah kibi komai a hankali tunda kikaga haka kinsan dole da dalili ni bana tunanin Ammu da wani abun, ya kamata kiyi mata uzuri, ki kuma bata loƙaci kamar yanda ta gaya miki ɗin nan gaba da kanta batare da kin tambaye ta ba, zata gaya miki komai, yanzu kiyi mata wannan buƙatar taki, in sha Allah ita ce ta ƙarshe na miki alƙawari daga mun dawo zan tsaya tsayin daka har sai ta gaya miki, ko bata faɗa miki ni zan binciko komeye gaskiyar lamarin, daman kinga ke aikin kike so to tunda yanzu yazo cikin sauƙi ba shikenan ba dama ta samu, dan Allah ki daina bujire mata, uwa uwa ce koma ta wacce hanyar ta haife ki ai ta riga ta kawo ki duniya, kinji dan Allah kiyi haƙuri komai ga wuce ki fara shiri mu tafi kawai. Da ƙyar dai ta samu ta shawo kan Ameela ta amince zata je ɗin, taji daɗi da taga ta shawo kanta yanzu matsalar ta kawai Babyn baby bata san wane hali zata shiga ba, tasan dole bazataji daɗi ba amma ya zatayi dole ce ta saka ta hakan, ta hanyar ne kawai zata samu damar ɗaukar fansa biyu akan su, shi da kuma mahaifinsa. Daga wajenta ta kuma fitowa falon ganin Babyn baby zaune agun da ta barta sai taji ta kuma bata mugun tausayi, zuwa tayi gabanta tare da kamo hannun ta, bata ce mata komai ba, ta kamata ta fita waje da ita, can bayan gidan su tayi da ita wajen wata bishiya da wataran suke fitowa su zauna awajen, akwai kujeru agun, zaunar da ita tayi akan kujera ɗaya, ita ma ta zauna akan ɗaya, shiru tayi tana ƙare mata kallo, ɗagowa tayi itama ta kalle ta, yanayin kallon da tayi mata yasa taji wani yumm kawai sai taga loƙaci guda ta koma mata Umman su, da sauri ta girgiza kai tana damƙe ido, tare da jan dogon numfashi, sannan a hankali tace "Allah ya bayyana mana ke Umma idan kuma kin mutu Allah ya jiƙanki, Allah yasaki a aljannar fiddausi, mu kuma Allah ya bamu ikon rama muku abun da sukayi mana, A hankali Babyn baby tace "Ameen" Kallon ta tayi tana ƙara gyara zama, sannan tace "Haneefa kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki inje indawo wannan zuwan zanyi shine badan kowa saidan farin cikin ki, da banyi niyar gaya miki amma yanzu zan gaya miki, ta wannan hanyar ce kawai zata sa mu samu abun da muke so shekaru da shekaru, idan na zama soja ta hakane zan iya samun damar da zamu kamasa da hujja sosai, ta sanadin wannan sojan zamu samu damar ɗaukar fansanmu akan mahaifin sa, idan bata haka ba banga ta inda zamu samu power ɗin da zamu iya ɗaukar mataki akansa a matsayin sa na tsohon gwamna kinsan bamu isa kai tsaye muce gashi gashi ba, babu wanda zai yarda damu, wataƙil ma saidai musa kanmu a matsala amma idan ya zamana muna da kusanci da shi zamu samu babbar hujjar da kowa ma zai ganewa idon sa bawai yaji daga bakin mu ba, kin gane abun da nake nufi, to dan Allah ki kwantar da hankalin ki masan matar nan zata baki kulawa duk da bansan ta ba, amma ma yarda da ita, kuma itama Ammu nasan bazata cutar damu ba, akwai shirin da suke duk dan ganin komai ya tafi daidai. "Ajiyar zuciya Babyn baby ta sauke tana jinjina kai "tace haka ne kuma, shikenan ba damuwa kije ɗin zan zauna, amma dai bazaku daɗe ba ko? "Eh in sha Allah, kuma indai naga da dama ana iya yin hakan, to duk sati zamu ringa zuwa muna ganin ki. Ɗan murmushin yaƙe Babyn baby tayi kawai dan a cikin ranta duk da haka bata so, amma kawai zata barta ne, tunda taga tanaso, kuma dan akanta zatayi hakan, bata da zaɓi da ya wuce ta haƙura ɗin koda ita hakan bazai mata daɗi ba. Haka Beenish ta ɗan ringa janta da hira harta saki jikin ta sannan suka tashi suka koma cikin gidan... Suna daf da zasu shiga cikin falon sukaji anayin horn tsayawa sukayi, Beenish tace "to suwa kuma muka samu, mtsw mantawa ma nake wallahi ya kamata mu samo me gadi, shiga ciki bari in duba ko waye. Shiga ciki Babyn baby tayi, ita kuma ta nufi wajen gate ɗin nata batare da ta kawo tunanin komai ba a ranta. Karamar ƙofar ta fara buɗewa zata leƙa, kawai taji an banko ƙofar da ƙarfi, har saida aka buge mata hannu, tsayawa tayi tana kallon mutumin shima kallon ta yake tare da ƙarasa shigowa ciki, yana shigowa wasu ma mutum biyu suka shigo, harɗe hannun ta tayi a ƙirji tana kuma ƙare musu kallo. Ɗaya ne yace "Oga ita ce? Karkaɗa musu kai Bulama yayi yana ƙoƙarin shiga cikin gidan, Beenish tayi saurin tare gabansa, tace "Malam lafiya, wa kake nema. "Matata! Ya faɗa ransa a haɗe yana shirin tureta ya wuce, tayi saurin matsawa, baki sake tana tunanin wannan kuwa kansa ƙalau, tana ta tunanin kamar tasan fuskar amma ta manta a inda ta sansa, tunani ta shigayi, bata ja loƙaci ba, da ta kuma kallon bayansa take ta gane waye. Kafin tayi yunƙurin dakatar da shi tuni yayi gaba, mutanen sa na mara masa baya, da sauri tabi su, dataga dai zasu rigata shiga kawai tasaka gudu, ta wuce su tana shiga, saidai bata rufe ƙofar ba ya saka ƙafar sa tare da turo ta ya ƙarasa shigowa, Juyawar da zatayi taga duk ba kowa a falon, sai TV dake ta faman aiki ita kaɗai tsayawa tayi taga iya gudun ruwansa kuma taji me ya kawo sa gidan kuma bayan ya ɗauki wacce yazo ya ke nema, Zainab! Zajnab! Zainab!! Matata kina ina ki fito mu tafi yau zaki zama amarya, sai zagaye falon yake yana maganar ƙatuwar muryar sa duk ta cika gidan, Beenish har saida ta saka hannu ta toshe kunnen ta. Murɗa wani ɗaki yayi ya buɗe sai yaga ba kowa a ciki. Yana wannan dube duben yana ƙwala mata kira. Beenish ce ta nufi ɗakin su kafin ta shiga ma duk suka fito cikin sauri suka ƙarasa shigowa falon, Bulama kamar zarrare haka yayi kanta da sauri yana washe baki, yana zuwa kawai bata ankaraba saijin hannun ta tayi anasa. Ai bata jira wata wata ba, ko tambayar keke faruwa, kawai ƙwace hannun ta tare da ɗauke sa da mari tana matsawa gefe dan tana ganin sa ta gane sa, kuma angaya mata waye shi, tun laƙacin da Babyn baby ta shigo ta sanar dasu, sai Maryam ta leƙa ta window tana ganin shine kuwa tace duk su wuce ɗaki dan ba mutumin arziƙi bane, su shirya ba alkhairi ne ya kawo sa ba, saidai bata basu labarin komai akan sa ba. Memakon Bulama yaji zafin marin da tayi masa saima shafa gurin da yayi da hannu sannan ya sumbaci hannun nasa yana sakin murmushi dan tunda yasakata a idon sa yaji ya manta da duk wani ɓacin ran da ya taho dashi. Da sauri sauran biyun sukayi kanta zasu kamata, su Ameela suka yi saurin shiga gaban su ita da Beenish, Ɗaya ne ya ɗaga hannunsa zai make Ameela tayi saurin damƙe hannun sa, ɗayan hannun ta kuma ta ɗaga rigar ta tare da zaro kwalbar spray ɗin su da suka saba amfani da ita, tana zarowa ta fesa mishi saitin idonsa take yayi baya yana saka hannun sa ya shiga murza idon. Barazana ma zaro nata tayi ta fesawa ɗayan, Bulama da glass a idon sa shiyasa basuyi gaggawar fesa masa, Cikin murmushin sa da ya saba, yace "da kyau amaryar kada kiyi min taurin kai kizo mutafi zan baki farin cikin da baki taɓa samu ba, wallahi muguwar ƙaunar ki nake, ƙauna ce danƙararriya a cikin raina da na ɗau tsawon loƙaci ina dakonta, nagama jinyar ta mamanki sai kuma ke kika kuma maye gurbin ta, fatan dai ta taɓa baki labarin tsohon saurayin ta, wanda zai iya yin komai akanta, koma ince wanda yayi abubuwa da dama akan ta, yanzu kuma ya dawo kan ƴar itama kuma zai iyayin komai akanta, dan haka matata ki taho mutafi na baki farin ciki, kece matata kece rayuwa ta komai mana naki ne duk wani abu da na mallaka mallakin kine matata. Fashion ce ta kalle sa tana nuna sa da yatsa tace "uwar ka ce matar ka, ubanka ne ya haifa maka ni a matsayin mata, kaji mahaukaci taɓaɓɓe to saidai kaje a ɗaura maka auren da uwarka dan Abu tafi ƙarfin banzan tsoho kucaki irin ka, kai nayi maka kama da sa'arka, na rantse da Allah in baka ja waɗannan ƴan wahalar ba kun bar gidan nan ba, wallahi sai nayi maka sabuwar kaciya agidannan kaga sai kafi jin daɗin cin amarcin da uwarka, banza kwarto tsohon banza tsohon wofi ko kunya baka ji ba zaka zauna kana wannan maganar da ƴar cikin ka shashasha kawai kare bunsuru shine kawai me bin ƴaƴan cikin sa mtssww, taja tsaki tana shirin barin wajen, cikin fushi ya cafko hannun ta, Beenish da Ameela suka saka hannun biyu suka tura sa gefe, zasu ƙwace hannun Zee amma suka kasa dan ƙam ya riƙeta, yana haɗe rai, wayar sa ce ta shiga yin ringing da hannun ɗaya yasaka a aljinhu ya zaro ta ganin kirane daga waje me mahimmanci yasa shi ɗagawa yana saka wayar a speaker. "Hello! Oga kayi sauri kazo babu lafiya an samu matsala wasu mutane sun shigo sun ƙwace kayan, sun fito da duk wanda yake cikin gurin sun kunna masa wuta yanzu haka gashi ci yake da wuta, kuma kayan shekaran jiya ma duk suna ciki, Baisan loƙacin da ya saki hannun Zee ba, a mugun haukace ya juya ya fita daga falon ya manta ma yazo da wasu, dan gaba ɗaya hankalinsa baya kansa, yana tafiya yana lalubo number saidai idan ya kira sai a tagama ringing ba a ɗauka ba, har ya fita daga gidan ya shiga mota muƙulli daman na jiki hakan yasa kawai yaja motar ya fara gudu yana tafiya yana kuma kiran number daga ƙarshe ma sai yaji ankashe ta jefar da wayar yayi da ƙarfi yace "RABIII...! me yasa me yasa ni zakiyiwa haka me yasa sai ta wannan hanyar zaki rama, yana zuwa wani gurin goslow duk da saurin da yake dole ya tsaya, wayar sa ce tayi ƙara yayi saurin ɗaukowa dan a tunanin sa ita ce ta kira sa, yana dubawa yaga saƙon video ne ta Whatsapp da wata baƙuwar number, da sauri ya shiga, asibitin sa yaga yana ci da wuta, a ƙasa

Chapter 35 of 44