Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
taje daf da gurin taja burki ta tsaya, da sauri Aunty Babba ta buɗe motar ta fita tare da zuge musu gate ɗin suka fita sannan ta rufe ta buɗe ƙaramar ƙofar ta fita, tana zuwa ta buɗe motar ta shiga, Beenish taja su suka ɗauki hanya babu wanda ya kuma magana acikin ɗif kamar babu kowa aciki, duk sunyi shiru kowa da abun da yake saƙawa a cikin ransa...... *$$$$$$$$$$$$$$$$$* "Dan Allah...! Dan Allah,Dan Annabi ku taimaka kuyi haƙuri kar ku kashe shi na roƙeku, kada kuyi haka, ku rabu damu namuku alƙawari zan sashi yabaku duk abun da kuke nema amma dan Allah ku rabu dashi ko inhelar ce ku taimaka ku bari ya sha idan numfashin nashi ya daidai ta sai kuyi magana, sai roƙonsu take ga tsohon ciki ajikin ta amma duk ta fita a hayyacin ta ganin me gidan nata yana shirin barin duniyar. Da haka ta kuma rarrafawa taje gaban su tare da dafa ƙarfar mutum da taga yana shirin kunna sigari, kallon ta yayi ta ƙasan ido tare da ɗaga ƙafar sa saida ya saita daidai cikin ta sannan ya turata ta faɗi ta bayan tare da sakin wata mahaukaciyar ƙara saboda azabar da taji ta a ƙasan marar ta, Hankalin sa ya mayar kan mutumin dake ɗaure ajikin kujera yana ta fusge fusgen yanda zai kwace daga ɗauren musamman da yaga yanda yayiwa matar sa, hawaye ne kawai yake gangaro masa daga cikin idanun sa, idan ya yunƙura yaga ya kasa sai ga koma tare da ci gaba da kuka me ciwo, ga numfashi sa da ya dawo ƙirji yana shirin ɗaukewa idanun sa sun kaɗa sunyi ja shi kaɗai yasan halin da yake ciki, Gashin kansa yakamo ya ɗago dashi, sigarin da ya kunna ga zuƙa tare da hura masa hayaƙin a daidai saitin hancin sa, nan da nan kwa yayi wata ɗauke gaba ɗaya sannan ya kuma kawowa cikin mawuyacin hali, Da sauri matar ta kuma yunƙurawa zata tashi tana sakin kuka me ƙarfi amma bata kai ga ƙarasawa ba ya kuma turata baya ta faɗi tare da bugewa da jikin kujera nan itama ta ɗauke bata kuma motsawa ba, ko kallon inda take beyi ba, ya ci gaba da abun da yake yana zuƙu sigarin sa yana busawa bawan Allah nan duk dauriyar sa dole yakasa yanaji yana gani babu ƙarfin ƙwatar kansa, tun yana gani bibbiyu ya dawo ganin dishi dishi kansa yana lanƙwashewa sai ya kuma yin ƙarfin hali ya buɗe su amma sai su ƙara rufewa saboda sunyi masa nauyi ga numfashin sa saura ƙiris ya ɗauke.... "A'ah...! A'ah..! Baba..!!Baba...!! Muryar ta ce ta karaɗe duka Hole ɗin dake ciki da mutane almost 200 suna ɗaukar lecture, gaba ɗaya mutane hankalin su ya koma kanta, kowa ya zuba mata ido, da gudu Babyn baby ta ƙarasa kusa da ita tana zuwa ta faɗa kanta ta rungume ta sai kawai ta fashe da kuka tana ƙara ƙanƙame ta, cikin sanyi jiki Aunty Babba ta ƙaraso kusa dasu itama idon ta ya canza kala dan har ƙwalla ta tarar mata ta cika idon, tayi saurin gogewa bata bari ya sauko mata, Kowa na gurin duk da basu san ne ya faru ba amma saida suka tausaya musu yanda suka riƙe juna suna kuka dole su baka tausayi. A hankali DR. JAVEED ya shiga takawa zuwa gaban su yana zuwa ya naɗe hannuwan sa a kan chest ɗin shi yana me binsu da kallo gaba ɗayan su, 'Aunty Babba ce ta shiga rarrashin su tana ɗan bubbuga bayan su amma basu bar kukan ba saida sukayi me isar su, sannan Babyn baby ta ɗago daga jikin ta cikin sanyi jiki, sai ta ɗora hannun ta a kan fuskar ta tana girgiza mata kai, Muryar ta har ta fara fashewa ta ce; Yaya me yasa? Me yasa zakiyi haka? Ke da kike share min hawaye na ke kike kwantar min da hankali a koda yaushe kina yawon gaya min indaina tunanin komai inba abun dake gabana ba kina yawon gaya min kar inbari tunani yasani kuka, kina yawon gayan kar nasake na ringa bari hawaye na yaringa zuba a kan tunani amma ke me yasa kikayi kina tunanin zan iya daurewa zan iya hakan bayan nasa kema kina cikin damuwa yaya nasan da ciwo amma kar ki bari raunin ki ya ringa bayyana idan ina gurin, a duk loƙacin da naga haka ina iya kaiwa sati ban dawo daidai ba ko so kike nim..... Da saura ta ɗora hannun ta a kan bakin ta ta rufe mata baki tare da girgiza mata kai tana ƙaƙaro mmurmushin dole tanayi, fuskar ta cike da murmushin dole da ta aro sa itama ta shiga goge mata nata hawayen tana ce wa; Babyna babu fa komai ni ba a bun dake damuna bakiga ma mmurmushi nake miki ba kawai wani a abu na ɗan tuna kuma kukan da nayi ai dannaga kina yi ne amma ni babu abun dake damuna ki kwantar da hankalin ki duk abun da nake gaya miki gaskiya kar kiyi tunanin komai kinji... 'Duk wannan maganar da take tanayi tana mmurmushi saidai kuma bata sani hawaye har rige rigen fitowa suke daga idon ta tana ta ƙoƙarin ta ɓoye damuwar ta amma ba hali, duk wanda ya kalle ta sai yaji tausayin gashi magana take tana mmurmushi yayin da kuma idanun ta suke ta faman tsiyayar da ruwa, zubar hawaye da kuma mmurmushi duk a loƙaci ɗaya. Babyn baby da ta fahimci halin da take ciki sai taji ta ƙara bata tausayi dan haka cikin sanyi murya tace; Yaya...... Bata kai ga ƙarasa faɗar abun da zata faɗa ba, Dr.Aveed yayi gyaran murya dukkan su ɗagowa sukayi suna kallon sa dan su sun ma manta a inda suke, suna kallon sa kuma, Bineesh tayi saurin sunkuyar da kanta murya ƙasa ƙasa tace sorry Sir dan tasan halin sa baida mutunci ga wani kuka da take jin yana taso mata, amma tana dannewa, gudun kar ta ƙara rikita ƙanwar ta ta, Ƙara taku ɗaya yayi zuwa inda suke yayi gaf da su, Bineesh da kanta ke ƙasa sai kawai taji anriƙo mata hannu da sauri ta ɗago ta kalle sa a ɗan tsira ce sai kuma ta ƙara maida kallon ta ga kan hannun su da nata ke cikin nasa. Jikin ta ne yafara kyarma cikin harhaɗa magana ta ce; S.ss.ir.. yana jin ta kira sunan sa, a hankali yace; Shiiiiit, yana faɗin haka kuma yajuya baya tare da jan hannun ta yanda yayi ɗin bata da zaɓi dole ta shiga binsa a baya fuskar ta kuma har yanzu bata bar zubar da hawayen da take yi ba, fita yayi da ita daga cikin gurin... Suna fita daga gurin Babyn baby ta kuma fashewa da wani kukan tana toshe bakin saboda bata so sautin kukan ga fito, Aunty Babba ce tayi saurin riƙota ta rungume ta tana bubbuga bayan ta. Tafiya suke amma kawai jefa ƙafarta take dan hankalin ta yafara barin jikin ta, a hanya mutane sai kallon su suke masu gulma nayi saboda mamakin ganin hakan ansan dai Dr.Aveed bashi da mutunci kuma duk a bun da zaiyi maka a gaban mutane zaiyi maka, to me yake faruwa da har ya riƙo hannun ta kuma bisa ga dukkan alamu office ɗin sa yake shirin shiga da ita, saɓanin ko da yaushe shi bai yarda da kowa ya shigar masa office ba, hakannan kuma har maza bare kuma mata da in banda tsana babu a bun da yake nunawa matan makarantar. Tunanin su kuwa daidai office ɗin sa ya buɗe ya shiga da ita amma sai yabar ƙofar a buɗe saboda duk yana ankare da masu kallon su da suna tahowa kuma yasan babu a bun da mutane bazasu faɗa ba a kan hakan dan wannan a bun sabon a bune a gun sa Zaunar da ita yayi a kan kujera sannan ya wuce ya je wajen fridge ya ɗauko gorar ruwa ya dawo inda take zaune da take ta faman share hawaye da hannun ta amma hawayen yaƙi tsayawa, jin hannu a kusa da ita yasaka ta ɗagowa a hankali ta sauke rinannun idanunta da suka sauya kala, ganin yana miƙa mata yasa ta miƙa hannun ta a hankali ta karɓa tare da kafa robar a bakin ta bata sauke ba saida ta shanye ta tass sannan ta sauke tana maida ajiyar zuciya tare da lumshe idanun ta na ɗan sakanni sannan ta kuma ware su, yanda tasha ruwan sanyin nan haka taji zuciyar ta ta ɗan yi mata sanyi, daga nan kuma sai ta shiga sauke ajiyar zuciya akai-akai. Duk abun da take a kan idon sa amma daga nesa kuma dan zaka iya cewa ma ba ita yake kallo ba, sun kai wajen 5 minutes babu wanda yayi magana a cikin su, zaman gurinne ya gundureta, zumbur ta miƙe tsaye kamar wacce aka tsikara haka ta tashi, tana tashi ta nufi hanyar waje, bata kalli inda yake ba bare kuma tayi masa godiya, "Su waye ku.!? Tambayar da taji ya jefo mata kenan a loƙacin da take ƙoƙarin fita daga cikin office ɗin, cak taja ta tsaya amma sai ta kasa juyowa saboda koda ta juyo bata amsar tambayar sa bare ta basa dan haka juyowar ta a yanzu bazata amfane sa da komai ba, dan haka bata wani tsaya dogon tunani ba kawai tasa kai ta ƙarasa fita daga ciki. Bayan ta yabi da kallo tare da jinjina kai, watakon ko godiya baza tai masa ba kuma ya tambaye ta tabawa iska ajiyar sa, jinjina kai ya kuma yi a karo na biyu kafin a hankali ya furta "SU WAYE SU? Me ya sa shiga irin wannan halin me take tunani, can wata zuciyar tace masa to kai ina ruwan ka me yasa kake son sanin SU WAYE SU, kafadun sa ya ɗaga tare da ɗan taɓe baki ya kuma cewa kuma fa hakane ko ma me yasa na jawo ta gashi yanzu ta watsa min ƙasa a ido, shiru yayi yana sakin tsaki sannan ya kuma cewa amma kuma ina san sanin ko "Ko SU WAYE SU. ko ba komai cikin makarantar nan suke dole ingano ko SU WAYE SU a yau ɗin nan, 'To a kan me wata zuciyar ta kuma tambayar sa shiru ya kuma yi loƙaci guda kuma tunanin a bun da ya faru loƙacin da suke kuka su duka da loƙaci da take hawaye tana mmurmushi sai yaji a bun ya kuma dukan zuciyar sa. *Hmmmmm ya sauke nauyayyen numfashi tare da furzar da iska daga bakin sa, a hankali ya sake ce wa; tausayi, kuka me hakan ke nufi? shi kaɗai sai kunta da warwara yake yakasa tsaida a bun da ya kamata yayi, kira ne ya shigo wayar sa hakan yasa ya katse tunanin da yake yayi saurin ɗaukar wayar duba screen ɗin yayi take annurun dake fuskar sa ya ɗauke cikin tsananin damuwa da ɓacin rai ya ɗaga wayar yana cika yana batsewa.., "HAMMAD dan Allah kar ka kuma kirana na gaya maka, indai akan wannan harkar ce bazan taɓa amince maka ba, kuma wallahi idan bakayi wasa ba Allah sai nasa an ɗaure ka wallahi wallahi wallahi, wai yaushe ne zaka barni inyi rayuwata cikin salama, daga ɗan abu ƙanƙane kullum sai ka ɗaga min hankali, kasani idan kasa martabar mahaifina ta zube ko wani abun ya taɓa masa jam'iyya to kasni bamu kaɗai zata shafa ba har da ku, matsaya ci kawai wallahi nagaji da kai kuma idan ka kaini ƙarshe wallahi sai na haɗaka da RK idan ina tsoron wani yaji to shi bana tsoron sa nasan zai fahimce ni, dan haka yana kan hanyar sa ta dawowa inbaka rabu dani ba case ɗin zai koma hannun sa wallahi mtsww banza me zuciyar mata sha shasha, marar kishin ɗan uwansa mtsawww. Yana gama faɗar haka ya kashe wayar gaba ɗaya ma tare da yin jifa da ita yana dukan table ɗin dake gaban sa daga inda yake ya zame ya yayi zaman dirshen ɗago kan da zaiyi yaga ƙofar sa a buɗe hakan yasa shi yayi saurin miƙewa daga gurin gudun kar wani yagan sa kan kujera ya koma ya zauna tare da rafka uban tagumi yana tunanin me kuma zai biyo baya daga ɓangaren Hammad......, *(Duk me son in saka shi a group yayi min magana ta number ta a WhatsApp, dan Allah idan kasan ba karantawa zakayi ko zaka tambaye ni wani littafin to kar kayi min magana Please 🙏)* *(ƴan facebook kuma da basa WhatsApp kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL GROUP kuyi join anan zan ringa posting kullum amma idan kana wani group ɗin zaka iya ganin sa saidai baizama lalle kagani kullum ba kuma ba ajere ba.)* ___loƙacin da Beenish ta fito daga office ɗin sa direct can hole ɗin nasu ta nufa, tana ta sauri taje gurin su Babyn baby garin saurin bata kula ba tayi karo da wani wani saurayi da suke tafiya tare da abokan sa su biyu a bayan sa da sauri tayi baya tana shirin ta bashi haƙuri kawai ɗagowar da zatayi taji saukar mari a fuskar ta. yana marin ta abokan nasa suka kwashe da dariya suna nuna ta da yatsa. Cikin tsananin mamaki ta dafe kumatun ta, bata jira mamakin yagama sakin ta ba, itama ta ɗauke sa da nata marin kafin ya dawo hayyacin sa ta kuma sauke masa wani ta ɗayan ɓarin yana sake ɗagowa ta kuma wanka masa wani saida tayi masa guda huɗu zafafa, dan ranta yagama ɓaci da marin da yayi mata gani take har yanzu bata rama ba, tunda tayi masa na farko abokan sukaja baya cikin tsananin mamakin abun da tayi mishi, Hannu ta ɗaga zata ƙara masa ɗaya daga cikin su yayi saurin riƙe hannun nata, ta watsa masa wani mugun kallo da idanun ta da har yanzu basu baje daga zan da sukayi ba tare da fusge hannun ta daga nasa, da sauri yaja da baya gudun kar yaje shima ta sauke masa marin, Wanda ta mara ɗin da yaga haka shima bai daddara ba dan shima ranshi ya kai ƙololuwar ɓaci a zafafe ya ɗago hannu zai kaiwa wuyan ta shaƙa yaji an riƙe hannun, da sauri yabi hannun da kallo tare da sauke sa a kan fuskar ta, da wani irin kallo yake bin ta na uku saura kwata. "Kayi na farko kayi na ƙarshe wannan shine dana sanin da zakayi idan kabari hannun ka ya kuma sauka a kanta sai kayi sha'awar dama baka zo duniya ba... Duk da taƙaicin da yake ji hakan bai hanasa kwashewa da dariyar sheƙiyanci ba, yana dariyar ya matsar da fuskar sa daf da ita yana kallon ƙwayar idon ta, cikin karkatar da baki gefe ya ce; oh really idan kuma naƙi fa? Su waye ku waye uban ku a cikin garin dan da alamar ku baƙi ne ko bakusan ko ni waye ba. Cike da jin haushin maganar sa ta tattaro yawun bakin ta ta tofa masa a fuska, hannun ta dake riƙe da nasa ta murɗe cikin ɗaga murya ta ce; Uban ka ne uban kuma da kake ikirarin bamu san kai waye sai me bamu sani ba kuma bama so mu sani kuma bazamu taɓa sani ba banza kawai ajawo, ka wuce banzan namiji lusari asararre kaje ka tambayi uwarka waye kai tunda ita ta haifeka, ita yafi dacewa da tasan kowa ta haifa, amma mu bama buƙatar sani, tana wannan maganar saiji tayi ƙas hannun sa da ta murɗe yabada sauti, amma duk da haka saida ta ƙara murɗawa sannan ta tura sa baya ya kuma faɗawa akan hunnun, ba shiri ya saki ƙara, kan kace me guri yagama taruwa da mutane daman wasu dasu aka fara faɗan wasu kuma sai yanzu hankalin su yayo wajen. Da sauri Barazana ta ƙaraso wajen ita da Ameela, gurin Aunty Babba suka ƙarasa tunda suka ganta haka bama su tsaya tambayar ba'asi ba, sai ma jinjina mata da sukayi, sannan suka juya gurin Beenish da Babyn baby da suke tsaye hannun su riƙe da na juna, hankalin su ne ya tashi ganin fuskar Beenish kamar tayi kuka, da sauri Ameela ta ce; Me ya faru badai shi kika zubarwa da hawaye ba. Mmurmushi Beenish tayi tare da dafa kafaɗar ta ta ce; kar ku wani damu bashi bane abune ya faɗan a ido dalilin haɗuwar mu dashi kenan ban lura da shi ba, bai jira na bashi haƙuri ba kawai ya....., Barazana ce ta dakatar da ita da cewa shikenan kawai ai mun gane maimaita saɓo saɓo ne, dan wallahi zuciya ta a kusa take hmmm. Kan kace me magana ta karaɗe makaranta duk wanda yaji labari sai yazo ya ganewa idon sa, da sauri abokan sa suka ɗauke sa suka saka shi a mota suka fita dashi daga cikin makarantar. Wata ƙawar Ameela ce da suke ɗan gaisawa amma sama sama ta matsa kusa da ita tace; Ameela wai me ke faruwa? Da kamar bazata kula taba, sai dai ta ce; "Nasan tunkan kizo kinji labarin komai bansan kuma me kike son ji daga gurina ba, tana faɗar haka ta kawar da kanta ta juya gurin Aunty Babba da tayi tsaye kamar soja taƙi ko motsawa jira take kawai wani ya kawo musu wurgi ta ƙarasa sauke abun da take ji a kansa, Haushi ne ya kama ta jin yanda ta bata amsa, yanzu isakan cin nasu yafara wuce gona da iri, a wannan karan sun taɓota dole ta ɗau mataki a kai tunda suka taɓa mata abun son ta.... "Wai su waye su? Naga kamar zaƙewar su tayi yawa, Wata ce take tambayar wannan wacce tayiwa Ameela magana, ɗan juyawa tayi ta kalle ta, sannan ta ce; "To nidai bazan ce nasan su ba kuma bazan ce ban san su ba, wannan abun da kika gani ma kaɗanne sa basu tarar masa su duka ba, amma dai abun mamaki bisa ga dukkan alamu basu san waye ba, nasan da baza suyi masa haka ba duk jiji da kansu, daman ance rana dubu ta barawo rana ɗaya ta mai kaya, yau zasu kwashi kashin su a hannu kenan sun jawo ruwan dafa kansu. "Nima dai nayi mamaki da naji ance wai wata ta karya ɗan gidan Commisiona of police, shiyasa nazo inga su waye masu wannan aika aika to amma a ina suke danni yau nafara ganin su.... "Bahiyya! Ameela ta kira sunan ƙawar tata da take wannan maganganun ashe duk tana jinta... A wani wulaƙance ta ɗago ta kalle ta, zaro ido Ameela tayi ganin kallon da tayi mata na raini da wulaƙanci tundaga nan ta fahimci inda maganganun ta suka dosa, ta kowa tayi tazo har gaban ta, itama a wulaƙancen ta kalle ta tace; "Wannan ya zamana first and last da zaki min irin kallon nan in bahaka ba wallahi sai na tsiyayar miki da ido inga ubun da ya tsaya miki...shiru tayi na ɗan wani loƙaci sannan ta cigaba.. "Ke kiji da abun dake damun ki, ki rufawa kanki asiri kamar yanda tsohuwar ki take son rufa miki, ke yanzu ina ke ina shi hanyar jirgi daban ta mota da ban, abun ba haɗi, shawara zan baki son maso wani baida amfani ki bari ya gani ya yaba, har kike kirari akan sa to be san kinayi ba abun kunya, kin dage kina hauka akan wanda bai san kinayi ba ƴar gidan malam Shehu wallahi in ban tona miki asiri a gurin nan ba kice a shegiya nazo duniya wacce bata san inda yake mata ciwo ba... Maganar kuma bamu san ko waye shi ba, koma waye ba damuwar mu bace sanin hakan baida amfani a gare mu, wannan ke ta shafa indai ke kin sanshi ai shikenan mtsawww ta doka tsaki tabar wajen. Iya shaƙa ta shaƙa ga mutane wasu na mata dariya, saboda irin masu rawar kannanne da son nuna su masu shine alhalin na mota ma da ƙyar take samu amma sai ƙaryar arziƙi, ji tayi kamar ta shaƙota amma tana tsoron kar taci gaba da yi mata ɓarota shiyasa zata ɗaga mata ƙafa amma tayi alwashin sai tasa tayi danasanin abun da tayi mata a gaban mutane. 'Wiwiwiwiwiwiiiii nan kallo yafara komawa inda ake jiyo jiniyar ƴan sanda, motar ƴan sanda ce ta shigo cikin gurin da gudu har inda dandazon mutanen suke. Wacce aka kira da Bahiyya ta saki wani irin murmushin farin ciki harda tafawa sa hannu, tana kallon su Ameela, ta fara takawa zuwa wajen su cikin jin daɗi tace; To yanzu zaku san ko shi waye koh, angaya muku kowa ake taɓawa a kwana lafiya, in wani yayi rawa an basa kuɗi to a wani wajen idan kayi duka zaka sh......., Bata kai ƙarshe ba Barazana ta kwashe da mari tare da caƙumar wuyan ta ta shaƙeta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana kifa mata mari dashi.... Ganin hakan yasa ƴan sanda sukayi saurin yowa kansu........✍️✍️ Please comment and share and likes hakanne zaisa kuna ganin update da yawa. *(Duk me son in saka shi a group yayi min magana ta number ta a WhatsApp, dan Allah idan kasan ba karantawa zakayi ko zaka tambaye ni wani littafin to kar kayi min magana Please 🙏)* *(ƴan facebook kuma da basa WhatsApp kuyi searching ɗin SU WAYE SU HAUSA NOVEL GROUP kuyi join anan zan ringa posting kullum amma idan kana wani group ɗin zaka iya ganin sa saidai baizama lalle kagani kullum ba kuma ba ajere ba.)* [3/5, 11:43 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* ______________________________ *_episode 7💧_* 💧💦محمدالرسوالله...!💦💧 Bissmillah.....✍️ _____Bata kai ƙarshe ba Barazana ta kwashe da mari tare da caƙumar wuyan ta ta shaƙeta da hannu ɗaya hannu ɗaya kuma tana kifa mata mari dashi.... Ganin hakan yasa ƴan sanda sukayi saurin yowa kansu........✍️ Maven ƴar sanda ce take ta fara jan Barazana amma ko gezau ba tayi ba kuma bata fasa abun da take ba, nan aka shiga ƙoƙarin rabasu amma aka kasa saida ƙyar aka iya ɓanɓare Bahiyya daga hannun Barazana, Barazana sai ciki take tana batsewa tana watsa mata kallo ji take kamar ta kuma shaƙota, Ƴan sandanne suka jata zuwa motar su babu musu ko wata garda ma ta shige tana shiga suma su Beenish suka bi bayan ta ƴan sanda sunyi mamaki dan su a tunanin su wacce suka tarar tana ƙoƙarin kashe wata ita ce me laifin da ta daki ɗan gidan Commisiona of police, shiyasa kawai basu wani tsaya jin ba'asi ba tunda idon su ya gane musu no need su tsaya tambayar wacece, Da sauri wani ɗan sanda ya tari gaban su su duka huɗun, tun kan yayi magana, Ameela tace; mu duka muka aikata dan ni na karyawa tsinanne hannu dan haka dukan mu zaku kama, ba ita kaɗai ba, tana gama faɗar haka tabi gefen sa ta haye kan motar da kan ta, yana gurin kamar gunki duk suka raɓa ta gefen sa suka haye kan motar, shidai tunda yake yau ce rana ta farko da ya haɗu da irin waɗannan shi sa ko maza sukaje kamawa sai kaga suna tsoron a kamasu amma su suna mata ba tsoro a tattare da su, da kansu ma zasu shiga motar, aikwa dole ya nuna musu ko su

Chapter 5 of 44