Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gadin na laɓe daman beyi nisa ba yana ganin sun tafi yayi saurin fitowa daga gurin, cikin kuka yafara jijjigata yana cewa SU WAYE SU..!????✍️✍️✍️ *Sai kuma Monday idan Allah ya kaimu gobe zanyi bacci harda munshari😅😅😅* More comments more typing 🤗 Please share, likes, vote and comment 🥰 [3/5, 12:01 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* 💧💪Jajirtattu writers association 💪💧 ______________________________ *_episode 25💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bissmillah.....✍️ "Rasa inda zai saka ransa yayi gashi gurin duk ba motocin da suke wucewa, gashi tayi masa nauyi amma da haka ya daure ya arowa kan sa jarum ta, ya ɗuke ta da ƙyar, ya nufi titi da ita sauƙin ta basu da nisa da bakin titin. Yana ƙarasawa ya tari wata napep da sauri yasaka ta a ciki saida suka fara tafiya ma ya faɗa masa inda zai kaisu a bakin wani asibiti ya sauke su tare da taimakon me napep ɗin suka fito da ita a haka suka shiga cikin asibitin, suna shiga kuwa likitoci suka yi saurin tarar su aka shiga da ita ciki.... Ya kasa tsaye yakasa zaune, sai zarya yake a bakin ɗakin da aka ajiye ta addu'a yake tayi Allah yasa kar ta mutu. Sosai likitoci suka duƙufa akan ta suna bata taimakon gaggawa amma ina har yanzu babu alamun zata farfaɗo, yanke shawara sukayi kawai suyi mata operation su ciro ɗan dan sunji alamun da ransa. Babu ɓata loƙaci cikin gaggawa suka shirya komai aka fito da ita aka nufi ɗakin CS ɗin, nan aka nemi saka hannun sa ba wani ɓata loƙaci ya karɓa yayi signing yana ci gaba da addu'a sukuma aka fara gudanar da aikin. Sun ɗau loƙaci kafin suka samu suka ciro ɗan, ana ɗauko ta yarinya ta callara kuka, nan suka fahimci macece yarinyar, duk yanda suka so suka matar ta farfaɗo bata farfaɗo kuma abun da yasa basu barta ba, saboda bugun zuciyar ta na bugawa shiyasa suka san bata mutu ba, Shirya Babyn akayi tsafa aka saka mata kaya, sannan aka fito dasu daga ɗakin CS ɗin loƙacin da suka fito baya nan yaje masallacin cikin asibitin.. Sai bata kulawa ake anan har yanzu shiru, wani likitan zuciya suka kira azo a gwada yi mata aiki ko za'a gano inda matsalar take, saidai kuma yana zuwa da ya bincika ta bugun zuciyar ya tsaya har ana shirin rufeta za'a sanar dashi ta rasu sai kawai aka ga, hannun ta ya ɗan motsa, hakan yasa sukayi saurin dakatawa suka ƙara haɗuwa akanta, bugun zuciyar ya kuma dubawa sai yaji yaci gaba da bugawa, tun yanayi a hankali har yadawo yi sa sauri da sauri, duk hamdallah sukayi suna sauke ajiyar zuciya dan sunji daɗi..... Duba tasu ka ci gaba dayi kafin suka samu numfashin ya fara dawowa sosai sukayi farin ciki da haka, ganin zata farka yasa su kuma yi mata allurar bacci sannan suka daidai ta mata oxging ɗin dak kan hancin ta yanda zai ci gaba da taimaka mata wajen shaƙar numfashin. Fita sukayi sannan suka sanar da mutumin da ya kawo ta zuwa loƙacin ya dawo, sosai yayi farin ciki da jin anfito da baby lafiya itama kuma ta farfaɗo bata mutu ba, har sujjadar farin ciki yayi sannan ya shiga ciki, ɗaukar yarinyar yayi da suka ajiye ta a gefen gadon..... Bacci kawai take yarinyar tasaka hannu a baki, ƙura mata ido yayi tana ta kallon ta jin son yarinyar yayi yana ta shiga zuciyar sa, ta hannun sa ko babban motsi bayayi saboda kar ta tashi, da ƙyar ya iya ajiye ta sannan ya fita daga ɗakin zuwa yayi akayi masa lissafin duk kuɗin da zai bada miƙa musu ATM yayi suka ciri adadin kuɗin su sannan ya karɓa ya koma ɗakin yana zuwa kuma ya sake ɗauke yarinyar ya riƙe ta yaci gaba da kallon ta...... Ba ita ta farfaɗo ba sai can cikin dare wajen ƙarfe biyu sannan ta farfaɗo tana farfaɗowa kuwa idon ta ya sauka akan su shida yarinyar da suke kan kujera yana bacci a zaune, sai yarinyar a hannun sa a haka bacci ya ɗauke sa shida yarinyar.. Lumshe ido tayi sai kawai hawaye ya shiga fitowa daga cikin idon ta tunawa da abun da akayi mata da kuma wanda yayi mata, kuka ta farayi sosai duk da bata bari ya fito sosai ba, amma da haka saida yaji kukan kamar a mafarki haka yayi saurin buɗe idon sa cikin sauri ya miƙe tsaye ya ƙarasa daf da ita ya shiga bata haƙuri yana danna wannan abun da idan andanna sa likitoci suke zuwa zaiyi ƙara acan wajen su, (na manta sunan sa) A cikin mintinan da basu fi biyu ba zuwa uku sai ga wani likitan ya shigo cikin gaggawa yana zuwa ga shiga tambayar ta farfaɗo, Eh yace mata yana kuma cewa ta duba ta. Dubata likitan ya kumayi amma sai yace lafiya ƙalau babu wata matsalar amma ta rage samuwar dake ranta ta daina wanann kukan zai iya taɓata... Godiya yayi masa, ya fita daga ciki, shi kuma mutumin yaci gaba da yi mata sannu yana bata haƙuri, cikin kuka tace "Me yasa zasuyi haka me yayi musu da suke son ganin bayan sa, dan Allah kar ka bari a kashe shi kaje kayi saving ɗin life ɗin sa, sannan ka tafi da yarinyar ka riƙeta a gun ka na baka ita kasaka mata duk sunan sa kake so, sannan kar ka taɓa sanar da kowa yarinyar nan na raye daga ciki kuwa har ƴan uwa na, ka sanar dasu abun da na haifa ya rasu, idan ta girma taje gurin su ta neme su da kanta, domin zama cikin su a yanzu itama rayuwar tana cikin hatsari muddun suka san tana raye itama baza su bar ta da ranta ba da hali ma kabar ƙasar saboda kaima baza su barka ba mugaye ne basu da imani a zuƙatan su munafukai ne gaba ɗayan su... Sannan ga kuɗaɗe nan kayi duk abun da kaga ya dace da su, kaje ofishin ƴan sanda ka shigar da ƙara sannan ka basu wannan recording shi kaɗai ne zaisa a kamasu shikaɗai ne hujja, idan kayi haka kayi tafiyar ka in yaso su zasu iya ci gaba da binciken amma dai komai yabar hannun ka baza su ƙara bibiyar ka b....... Tari ya taso mata babu ƙaƙƙautawa ta dafe bakin ta ita kaɗai tasan halin da take ciki saboda zuciyar ta wani irin zafi take mata, Tana tarin tace "ka kula min da yarinya sosai na baka amanar ta, sunan kaka ta, ka bata ilimi, kamin alƙawari matuƙar kana raye zaka kula da ita kamar yanda zaka haifi ƴar cikin ka.... Da sauri yace na miki alƙawari, amma dan Allah ki gaya min su waye su in sha Allah sai na ɗaukar miki fansa akan duk wanda ke da sa hannu sai inda ƙarfina ya ƙare kuma bazan kai ofishin ƴan sanda ba domin duk munafukai ne ana basu kuɗi zasu rufe komai ko su maida laifin ma kaina, nayi aiki a wajen su naga yanda suke gudanar da aikin su cikin cin hanci basa yin adalci akan duk wani case da akazo musu dashi, idan baka da kuɗi ma wani loƙacin korar ka suke, dan haka ki faɗa min kawai ni zanyi maganin su nayi miki wannan alƙawarin.... Tarin ya ɗan lafa mata kaɗan amma tana jin ƙaikayin sa a ƙasan maƙogaron ta, cike da dauriya tace; "Nima ban san su waye su ba, idan ka cire Rabi da Haisam sauran bansan su, amma dai duk ƙungiyar su ɗaya kuma kamar akwai wasu da basu halacci gurin ba naji suna maganar su tare da komai dai yana ciki ka saurara da kyau naji suna ta ambatar RED GANGSTER bansan me hakan ke nufi ba.... Shiru tayi tana ƙara jinjina girman abun abun da bata taɓa kawowa aran ba mafi kusan ci da ita wai su suka yaudare ta suka ci amanar ta, daman duk soyayyar da suke nuna mata ta ƙarya ce..... Kuka ta kuma fashewa da shi tana cewa "me yasa? Rabi mai yasa me na tsare miki da kike son ganin bayana da na ɗan dake ciki na tunkan yazo duniya ma wane irin laifi na aikata miki, wanda na ɗauki son duniya ma na ɗorawa ya cuce ni da shi za'ahaɗa baki aga baya na, saboda son zuciya irin nasu, kuɗi kuɗi kuɗi me acikin dukiya idan banda bala'i dukiyar ma da ka haɗata da gumin ka wata masifa take zamar maka bare kuma wacce zaka gina ta da haramun kaciyar da kanka da haram ka gina ƴaƴan ka da haram bayan ka zalun ci mutum wannan wace irin rayuwa ce shin mutane basa mantawa da zasu mutu ne ko tunanin su mutuwa bazata zo kansu ba, wannan rayuwa rashin gaskiya da son kai yayi yawa acikin ta ga maci amana ace makusan cin ka dashi za'a haɗa kai a cuce ka aga bayan ka duk dan saboda son zuciya da ba Allah a zuƙatan su......kuka take sosai tana wannan furucin wani irin baƙin ciki na kuma taso mata ji take ma gwanda tabar duniyar ma ta huta gaba ɗaya dan ta tsana aci amanar ta babu abun da ta tsana fiye da munafurci akan muna furci tasha rabuwa da mutane da yawa kuma ko waye kai duk yanda kuke da ita idan kayi mata zata iya raba hanya dakai... Haƙuri kawai yake bata yana cewa tayi shiru saboda yanayin da take ciki kana ji kasan maganar take cike da ɓacin rai da ƙunar zuciya... Sun daɗe suna hira tana ƙara faɗa masa wasu abubuwan anan da duk wani abu da tasan zai buƙata, sannan kuma koda wasa tace koda ta mutu kada ya sake ya yaje gurin dangin ta bare ya basu ƴarta... Kiran sallar asuba ne ya katse musu hirar su, tashi yayi yace bari yaje yayi sallah, jinjina masa kai tayi kawai tana ƙara lumshe idon ta dan bacci bacci taji yana shirin ɗiban ta, yarinyar nakan ƙirjin ta ta rungumo ta da hannu ɗaya suna saurarar bugun zuciyoyin su, a haka bacci yayi gaba ita...... Bayan ta idar da salla ya haura upstairs ɗin dake cikin asibitin inda ake saida magunguna nan ya nufa zai siyo mata magungunan da kuma madara da akace abawa yarinyar tunda uwar bata cikin hayyacin ta kafin zuwa ta dawo daidai... Yana gama siya yabiya kuɗaɗen sannan ya juyo saidai juyawar da zaiyi ya hango wata mota daga nesa tana nufo asibitin, kallo ɗaya kuma ya fahimci wace motar ce. A mugun guje ya ya sauko daga saman dan kayan ma sakin su yayi agun,yana saukowa ya nufi hanyar ɗakin da aka kwantar da ita yana shiga yaga tana bacci ƙarasawa yayi ya zare yarinyar a hankali sannan ya kuma fita da ita daga ɗakin wani ɗakin ya shiga inda ya samu wata mata ta haihu shi da niyar ya basu ajiyar ƴar yayi amma da yayi musu bayani ma cikin ɗan ƙanƙanan loƙaci yanda dai zasu fahimci abun da yake nufi, sai kawai suka tausaya masa tare da sanar dashi cewar ai suma yarinyar da suka haida ta rasu ma, nan wata mata me karsashi ta karɓi tasa sannan ta basa waccen yarinyar da ta mutu tace kafin su shigo kayi sauri kaje ka sanar da likitan cewar ta rasu in ba haka ba suma zasu iya tona maka asiri idan aka basu kuɗi, idan kun gama komai ka dawo ka same mu anan, basu dai wani tsaya doguwar magana ba ya karɓi ƴar hankalin sa duk a tashe yaje ya sanar da likitan nan kuwa suka yarda tare da karbar yarinyar, sai suka koma ɗakin da take kwance har yanzu bacci take, Cikin sauri yayi kanta yana cewa likita zan dauke ta mubar asibitin ko kuma ku bamu wani wajen mu ɓuya koda a nan ɗakinne sosai ka ƙulle mu ta waje, wasune suke bibiyar mu nasan yanzu suna daf da shigowa koma sun shigo idan suka ganmu kashe mu zasuyi, dan Allah ka taimaka mana..... Tunda ya fara maganar likitan yake binsa da wani irin kallon sama da ƙasa ko da yagama kuwa sai yace to shikenan zanyi tunani akai, amma idan zaka biya sama da kuɗin da suka biyani, Cikin zaro ido yayi baya kamar zai faɗi tsabar razana da yayi, baisan loƙacin da caƙumi wuyan sa ba, ta shaƙe shi yana cewa me kake nufi da inbiyaka sama da kuɗin da suka baka SU WAYE SU eh su waye suka biyaka, me kake nufi.... Cikin dariyar rainin hankali yace "kamata yayi ka fara duba marar lafiyar taka sai kaga abun da nake nufi... Sakin sa yayi cikin sauri ya juya ya koma kusa da ita kara kunnen sa yayi take kwa yaji bata numfashi hannun ta ya ɗaga shima yajisa a sake.... Wata mahaukaciyar ƙara yasaki tare da yin kukan kura ya damƙo likitan yana kai masa naushi cikin ɓacin ran da shi kansa baisan yana da shi ba, me yasa ka kashe ta me yasa wane irin rashin tausayi ne me yasa ka kashe ta me yasa ka kashe ta??? Duk yabi ya fice a hayyacin sa, hawaye na zubo masa. Amma duk abun da yake masa saima wata dariya ta ƴan iska da yasakar masa yana cewa, me yasa na kashe ta saboda kuɗi kaji ko nace saboda da kuɗi itama jaririyar da bata mutu ba da kaina zan kashe ta Hhhhhh ya kuma sakar masa dariya duk da yana jin azabar riƙon da yayi masa amma hakan bai hanasa faɗar abun dake ransa ba.... Wata mahaukaciyar shaƙa yayi masa da a take yafara tari yana zaro ido da suka kaɗa suka jazur... Saida yaga numfashin shi ya kusan ɗaukewa sannan ya sake sa yana ture sa gefe, Gurin matar ya kuma komawa yana ci gaba da jijjiga ta yana kiran ta yana sumbatu dan sam baiso ta mutum ba, dan shi duk da tana maganganun ta na jiya bai taɓa kawo mata mutuwa ba, dan shi sauraron ta yake kawai azin zafin ciwo ne yasa take wasu surutan... Sosai yayi kuka kamar ransa zai fita... yana gurin suka shigo cikin wajen saidai maimakon yaga waɗanda yake tunani sai yaga sabbin wasu fuskokin, su uku ne. Yana ganin su ya miƙe yaje kusa da su yana binsu da kallo, cikin tsananin ɓacin rai yace "wallahi dukan ku sai kunyi nadama sai nasa kunyi da nasanin zuwan ku duniya kamar yanda muka rabata da farin ciki kuma sai nasa kun dawwama a cikin ƙunci wallahi sai na ɗaukar mata fansa kuma ko ban ɗauka da hannu na ba, wani na zai ɗauka sai na haifar muku da dana sani cikin rayuwar ku, Allah bazai taɓa barin ku ba, Sai Allah ya nuna muku ƙarshen ku gaba ɗayan k...... Tasss wani ga kwashe shi da mari ya ƙara taro sa ta ɗayan ɓangaren, tare da cewa kai kasan su waye mu da kake gaya mana magana son ranka, an kashe ta ɗin kuma kisa ma yanzu muka fara kaima kuma zamu kashe ka in yaso sai kafi jin daɗin ɗaukar fansar tunda har dakai idan kaje inda take sai ka faɗa mata zaka ɗaukar mata fansa, wani marin ya kuma kwashe shi dashi.. Amma duk da haka bakin sa bai mutu ba yaci gaba da cewa "an faɗaɗin ku kashe ni nima ku huta amma kusa aranku gaskiya zatayi halin ta ko ba daɗe ko bajima sai Allah ya tonu asirin ku sai kun girbi abun sa kuka shuka, da hannun, sai a loƙacin da kuke tunanin komai ya zame muku daidai a rayuwa, zaku ga sakayya kuje kuyi duk...... Bai ƙarasa ba sakamakon dukan da suka rufe sa dashi haɗuwa sukayi gaba ɗayan su suna dukan sa tun yana iya karewa har ya daina, ɗaya daga cikin sune yaje ya ɗauko wani ƙarfe ya buga masa a akai take ya zube a wajen yana sakin ƙara, ɗaya kuma ya samu ya daki ƙarfar sa da ƙarfi take kwa tayi ƙara, basu rabu dashi ba saida suka ga baya shurawa sannan suka rabu dashi... Ganin zasu fito yasa mayar dake leƙen su tayi saurin janye wayar da take ɗaukan video da ita ta juya ta ɓuya a wani lungu saida taga fitar su har likitan sannan tayi saurin fitowa ta shiga ɗakin da sauri, saida ta shiga kuma sai ta rasa ma ta ina zata fara basa taimako.. Fita tayi ta koma can ɗakin su inda yakai musu yarinyar, da gudu ta shiga ciki tana kuka ta sanar dasu abun dake faruwa, Namiji ɗaya ne sai wata mata sai kuma marar lafiyar da ta ke barci. Fitowa sukayi gaba ɗayan suka shiga ɗakin kwance suka gansa da alama kuma kamar babu rai a tattare da shi, ga matar can ma itama kwance babu rai... Namijin ne ya tsugunna a gaban sa tana sauraron ko da rai, da sauri ya miƙe yace "Mama da sauran rai a jikin sa fah, ya kamata muyi gaggawar yin wani abun.... Kallon sa tace to "Khaber yanzu meye abun yi, ya kake ganin za'ayi dasu, kar muce wani likitan yazo a duba sa ko da rai ajikin sa kuma suje su kuma yi masa lahani. To ya Mama ya zamuyi dole mu kuma neman taimakonbwani ai ba duka aka taru a ka zama ɗaya ba, bazaiyiyu ace gaba ɗaya likitocin an haɗa baki da su, idan muka samu hujja ma har shi zamu iya sawa a kamasa.. "To kuma haka ne kaje ka gwada zuwa wajen wani likitan wanda de kake ganin da sauƙi sauƙi ko kuma abun da za'ayi ma kawai ka kira mana wannan likitar da take kula da Ruƙayya, kayi mata bayani koda ba ita zata duba mana ba sai ta faɗa mana wanda zai iya taimaka mana. "Tom shikenan bari naje muga, yana faɗar ya fita daga ɗakin yabar su da jimami., Yana fita kuwa yayi sa'a itama ta fito tana ta sauri, shima da sauri ya tare ta yana cewa "Dan Allah wani taimako muke nema duk da naga kamar sauri kike... Dakatawa tayi tana kallon sa "tace eh wallahi amma faɗi inji ko zan iya saida ya ɗan kakkali gefe da gefe yaga babu kowa, sannan cikin ƙasa-ƙasa da murya ya fara yi mata bayanin duk abun da suka sani suma.. Tayi mamaki batayi ba, ɗan numfasawa tayi sannan tace; "bawai bazan taimaka muku bane saidan kawa*78635i saboda aikina, taimakon da zan iya baku kaɗai shine ku fito da su ku same ni awaje in ɗauke ku a mota ta in kai ku wani asibitin amma yanzu gaskiya bana tunanin da wanda zai taimaka maka..... Cike da mamaki yace to amma me yasa? Kaga sauri nake kaidai kayi abun da nace kawai idan kuna so, Babu yanda ya iya dole ya amsa mata da to sannan ya koma ciki ya sanar da su cikin gaggawa ya ɗauko sa, sukuma suka bi bayansa, a ɗakin suka bar waccen mayar kwance a mace.... Da ƙyar ya iya kaisa waje yasaka sa a motar da ta ajiye sa, shiga yayi sai mahaifiyar tasu ta shiga gaban motar ita kuma ƴar budurwar ta aka ce ta koma gurin yayar ta Ruƙayya ta zauna da ita su suje.. Har ta juya sai kuma tayi saurin dawowa ta raɗawa yayan nata wani abu sannan ta basa wayar hannun ta, sannan tabar wajen ta koma ciki, ita kuma likitar ta tayar da motar suka ɗauki hanya.. "Ke kwa dan Allah in tambaye ki mana, me yasa kika ce babu wanda zai taimaka mana acikin asibitin, shin idan aka sanar da kisan kan daɗaya daga cikin ma'aikafa yayi baza a hukun tasa ba ko me kike nufi wallahi abun yaban mamaki ne tun ɗazu nake tunanin abun a raina, cewar Kabeer. Shiru tayi kamar bazata yi magana ba, taci gaba da tafiya batare da ta tanka musu ba, saida ta daɗe kafin ta numfasa tace.... Yanzu haka ma angan sa loƙacin da yake kisan saidai babu wanda ya isa yayi magana, an daɗe anayin hakan domin duk wanda ke cikin asibitin nan yasan halin asibitin nan sannan ba a gina sa dan bawa ko wane marassa lafiya lafiya ba, kawai dai sirri ne amma kowa yasan me a keyi kuma ba daidai bane amma idan kafa ɗa kana cikin matsala daga kai har dangin ka ma zaka iya jefaku cikin halaka, saidai ka gani ka nuna ba kaga komai ba, sannan ba kowa suke ɗauka aiki ba, duk wanda ka gani yana aiki anan da wata manufa yake yin ta, sannan dan taimakon marassa lafiya anayin saidai ba kowa ba sai wanda a kaga dama...✍️✍️ *Kuyi malej da wannan dan gaskiya page ɗin ba'a nan naso in tsaya ba, wataƙil gobe ɗorawa zamuyi akan wannan page ɗin wallahi naje wani biki ne munci rawa mun ƙoshi🤣 nagaji da yawa, wannan ɗin ma Allah yasa nayi sa tun safe kafin in fita amma da kun lashe yaseen* [3/5, 12:03 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* 💧💪Jajirtattu writers association 💪💧 ______________________________ *_episode 26💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bismillah....✍️ __Yanzu haka ma angan sa loƙacin da yake kisan saidai babu wanda ya isa yayi magana, an daɗe anayin hakan domin duk wanda ke cikin asibitin nan yasan halin asibitin nan sannan ba a gina sa dan bawa ko wane marassa lafiya lafiya ba, kawai dai sirri ne amma kowa yasan me a keyi kuma ba daidai bane amma idan kafa ɗa kana cikin matsala daga kai har dangin ka ma zaka iya jefaku cikin halaka, saidai ka gani ka nuna ba kaga komai ba, sannan ba kowa suke ɗauka aiki ba, duk wanda ka gani yana aiki anan da wata manufa yake yin ta, sannan dan taimakon marassa lafiya anayin saidai ba kowa ba sai wanda a kaga dama..... Daidai loƙacin suka ƙaraso wani asibitin shiga ciki sukayi suna fito dashi kuwa aka tare su da gaggawa aka zo aka ɗauke sa, aka nufi emergency dashi... Suma duk fita sukayi likitar har tana shirin jan motar ta matar tayi saurin leƙawa tace "yarinya ban tari numfashin ki ba, kuyi haƙuri ki ƙarasa bamu labarin waye me wannan asibitin kuma hukuma batasan dashi bane, da aka kasa ɗaukar mataki akai.... Shiru tayi tana nazari kamar bazata ce komai ba sai kuma tace ku shigo daga ciki to, saboda tsaro nasan zasu kula da wancen koda

Chapter 20 of 44