Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
RK kuwa zuwa loƙacin tun yana neman ta har ya daina ya watsar da lamarin ta a fili amma aransa indai zai zauna sai yayi tunanin yanda akai ya rasa ta, amma abun da ya barwa kansa shine kawai wani ne ya taimaka mata ta tafi gida, shiyasa ya daina neman ta yaci gaba da harkar gaban sa, Bangaren su Barazana kam sun kwantar da hankalin su sakamakon kwanan ta daya washegari Moohad ya same su aboye ya sanar dasu abin da ke faruwa tare da cewa sai taji sauki zata fito sun nemi ma da ya barsu suje su ganta amma ya hana su saboda tsaro yasan duk inda sukayi RK yana kallon su, idan ya gansu a part ɗin sa, zai iya gano wani abun shiyasa ya hana su zuwa, sannan kuma ya sanar da su cewa su daina nuna tsoro a kan RK babu ruwansu da shi suyi abin da ya kawo su kawai, idan kuma suka ci gaba da nuna jin tsoro akansa zai musu abin da basa tunani don haka duk wani abu da zai ce su yi to suyi kar sununa gazawar su, indai suna so su zauna lafiya dashi to su jajirce sosai akan abun da yake koya musu, dan shi mutum ne me son ganin mutum ya jajirce akan abu musamman idan shi zai koya maka, sannan kar su ringayi masa shishshigi ko yawan kallon sa, duk abubuwa ne da suke cikin abun da baya so, tun daga nan suka maida hankalin su akan abin da ya kawo su yanzu sosai suka saki jiki duk wani training da za'a koya suna yin shi sosai suke karɓar training. Kamar ko da yaushe a inda suka saba yin training ɗin, suna gurin yayin da kowannensu riƙe da bindiga 1 by 1 suke saitawa gurin da zasu harba, wani RK da sojan da suke basu horon suna bayan su, duk wanda ya harba sau ɗaya bai harbi cikin tsakiyar layi ba, gefe zai koma, haka suka dinga yi kowa na harbawa amma basa harbawa daidai tsakiyar cycle din da ake so su harba, duk yadda aka so a nuna musu yanda zasu yi amma duk sun kasa sai dai kowa ya harbi gefe, sun gama ƙular da RK dnn ya nuna musu ya nuna musu yanda za su yi amma ina sun kasa har hannun wasu ya riƙe yana saita musu amma daga ya matsa sai su harbi wani gurin daban haka suka dinga yi sun daɗe suna abu ɗaya amma har yanzu babu wanda yayi nasara ya harbi daidai tsakiyar gurin. Suna cikin yin haka kawai suka ga wani bullet ya taho shuuuuu ta gefen kunnen RK ya wuce bai sauka ko'ina ba sai daidai tsakiyar inda ake so a harba, haka aka dinga harbo bullet ba a daina harbun gurin ba sai da aka harba sau wajen biyar sannan aka daka ta, Ba RK ba kaɗai gabaki dayan su cike da mamaki, dan a kusan tare duk suka juyo suna duban daga inda bullet ɗin yake fitowa, a wani irin slow RK ya juyar da kanshi yana duban gurin, Beenish fi ya gani da bindiga a hannunta jikinta sanye da kayan sojoji tun daga kafarta ya fara bi da kallo da ke sanya cikin wani arnan takalmi na sojoji, sai wando rigar kuma ba ta sa ta zo zan ba sai ta saka fara rigar sojojin kuma ta daura ta a ƙugunta, sai hannunta cikin wata farar safar hannu,, gashin ta kuma ta daure shi ya ɗan sauko yana lilo, kanta kuma sai ta ɗaura p_cap akai ta dan tura ta gefe kadan yadda za a ga fuskarta sosai, wata irin tafiya ta shiga yi tana wulwula bindigar hannun ta har ta ƙaraso inda yake, sannan tayi wata irin juya bindigar ta totse ta a ƙugun ta, ɗagowa tayi tana kallon sa ido cikin ido ta sakar mishi da wani arnar murmushi tar da daga hannunta ta buga masa wani uban salute da yatsu biyu tana ɗaga masa gira ɗaya sai ta ɗan duƙar da kai batare da ta cire hannun ta daga saitin kanta ba tace "Sir I'm back! Tana faɗar haka ta ɗago tare da ƙamewa tana sakin murmushin gefen baki sannan ta raɓa gefen sa ta wuce gurin su Ameela..... *Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa* _Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba, sannan akwai wasu da suka buɗe group irin nawa amma bashi bane, nawa zaku gansa da dpn su waye su ɗin da kuma ɗan rubutu a gefe_ [4/25, 8:28 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) ________* 08124226526*_______ *_episode 50 💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 *Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526* _Bismillah..✍️_ Kowa baki sake yake kallon Beenish, tunda loƙacin da suka juyo idon ƙyan akan ta komai tayi a kan idon su, suna binta da kallon mamaki, dan ko motsawa ma wasu basa yi. RK kam ya kame ya daskare ya manne a tsaye yama kasa motsawa duk wani ruwa dake lungu da saƙon na jikinsa a daidai lokacin nan dai to saida yaɗan dakata, wadna shi kansa bai san dalilin hakan ba dan yama rasa wani kalar irin tunani zaiyi akai, saboda tunanin nashi ma tsayawa na wucin gadi, ya kai wajen minti 3 a tsaye ba tare da ya motsa ba, sannan hankalin shi ya dawo jikin shi a hankali ya juya yana kallon bayanta inda ta tsaya gabansu Barazana. Beenish na zuwa gabansu Ameela ta kuma faɗaɗa murmushin ta tare da watsa musu harara ganin yanda suka saki baki sun kallon ta kamar yau suka fara ganinta kowa ya kafeta da ido babu mai magana domin ta gama narkar da su agun da mamaki. Sai da tasa hannu a saitin fuskarsu tana wavin dinsu da hannunta tare da cewa "yade kuke kallo na kamar baku taba ganina ba, Ameela bata san lokacin da itama tayi saurin dawowa hayyacinta ba, ta ke ta rungume Beenish tana sakin ta sannan ta shiga kallon ta tundaga sama har ƙasa sannan washe baki kawai saita ta ɗaga hannun ta ta hau sara mata dan taji daɗi ganin ta a haka sosai, itama Barazana nan take ta ɗaga hannun tana sara mata tare da sakar mata murmushi, ganin abin da sukai sai ya burge sauran take suma dukansu suka ɗaga hannun su kayi mata salute tare da saukewa suna ƙamewa. Wani saurayi ne dake jikin su yayi saurin matsowa kusa da ita tare jinjina mata babban yatsan sa, Daɗi ne ya kama Beenish ta ƙara wage baki da murmushi, itama sai ta sara musu tana dan sunkuyar da kanta ƙasa alamun gaisuwa, gaisawa suka shiga yi tsananin ta da su Ameela da sauran ƴan matan, sai surutu suke suna tambayar ta ina ta shiga like basu san komai ba, sun ma manta a ina suke, Iya shaƙa RK ya shaƙa da ganin abun da sukayi mata, hakannan yaji ransa yayi mugun ɓaci, cikin ɓacin rai da ɗaga murya yace "Ke! Gaba ɗayan su saida suka firgita dajin yanda ya kira sunan da ƙarfe cikin tsawa, ita kanta Beenish saida hantar cikin ta ta kaɗa dan daman suna zancenne kawai amma hankalin ta yana kansa, jira take kawai taji hukuncin da zai yanke mata, amma tunawa da abun da ya kawota da kuma wasu maganganun da Moohad ya gaya mata akan halinshi, sai kawai ta maze a fuska bazaka taɓa cewa da ɗigon tsoro ba amma cikin ranta dukan uku uku yake, Mamakine ya kamasa ganin duk sauran sun nutsu sun maida hankalinsu kansa amma ita ko juyowa batayi ba bayan yasan kuma tasan da ita yake, cikin fusata yayi kanta gadan gadan yana zuwa ya juyo da ita da ƙarfi tare da ɗaga hannun sa zai mare ta saidai yaji caraf ta riƙe hannun sa tare da ɗaga idanun wanta tana sauke su acikin nasa, da bakin ta tayi wani abu yana ɗan fitar da ƙara kaɗan kaɗan kamar dai tsaki tare da rage yanayin kallon ta tana girgiza masa kai, hannun sa da ta riƙe sai ta juya nata ta zura a tafin hannun sa tana shigar da yatsun ta tsakankanin nasa yatsun ta damƙe, sannan ta wani kashe murya tana turo baki ta ce "My hus nagaji da zaman laɗaicinne ni kaɗai, naga kuma kaƙi ka dawo kasan kasabar min da kanka a tsawan satinnan ji nake kamar mun shekara dakai wallahi shiyasa na fito amma kayi haƙuri idan muka gama sai mu koma, ko kuma kazo mu tafi yanzu I need you now my husss.... Ta ƙarasa maganar tare da janta sai kuma ta zaro bindigar dake gefen ƙugun ta ta shiga yi masa yawo da ita akan ƙirjin sa, sannan ta sauya kalar kallon da take masa zuwa kallon tsana a daidai zuciyar sa ta tsayar da bindigar tana ɗage masa gira sannnan tayi ƙasa da murya wanda shi kaɗai ne zai iya jin me tace, tace "inajin yanda na ɗora ta nan badan ina tsoron Allah ba saina harbeka saboda na tsaneka na tsaneka na tsaneka ji nake kamar na kashe ka, tana maganar tana kuma goga masa bindigar a wajen zuciyar sa sannan ta watsa masa banzo kallo me cike da tsana, Ƙoƙarin cire hannun ta tayi daga nasa amma sai ta ji su gam ya mugun damƙe shi kamar zai karya mata yatsun dan da ya lanƙwasa su babu abun da zai hana su karyewa, ita kaɗai tasan azabar da take ji amma haka ta kuma daurewa ta ƙaƙalo murmushin yaƙe, tare da kuma sakin jikin ta kamar zata faɗa kansa tace "auch ash tana kuma riƙe nasa kamar irin bata jin zafi nan sai tace Husss muje ciki dan Allah nagaya maka I need u then I know u too. Kawai kafeta yayi da ido dan tagama kaishi ƙarshe har ya rasa ma wane irin ɗanyen hukunci zaiyi mata dan gani yake duk abunma da zai mata yayi kaɗan, sako sako yayi da riƙon hannun nata yana zare ya tsunsa daga tsakankanin nata, ta ɗauka sakin ta zai yi sai kawai ta ji ya ce "yes I really really need you Beb oya let's go! Yana faɗar haka yayowa hannun nata wawuyar damƙa da saida ƙashin ta ya amsa ta ciki ita kaɗai taji ƙarar juyawa yayi zai fara tafiya da ita, sai taja ta tsaya tana jan nasa, juyowa yayi yaɗan kalle ta, da ita kaɗai tasan ma'anar sa, tsaywa tunanin yanda zatayi kar ta bishi, amma tana wannan tunanin yajata da ƙarfi yana cewa "let's go let's go Beb! Bata da wani zaɓi dole ta shiga binsa abaya zuciyar ta na mata dukan uku uku, shikam tunda yafara janta bai waiwayo ba, janta kawai yake, Gaba ɗaya ƴan gurin sun zama ƴan kallo harda shi kansa ɗayan sojan lamarin ya shamai kai sosai abune da bai taɓa ganin ba, su kansu su Ameela mammakin su yaƙi ɓoyuwa sun kasa tantancewa abun da suka gani suka ji mafarki ne ko gaske. Beenish bata gama tsorata ba saida taga sun ƙaraso part ɗin sa, yana shirin shiga ciki da ita, nan ta turje, da iya ƙarfin ta take jan hannun ta zata ƙwace, saura kaɗan ta ƙwace bata ankara ba sai kawai ji tayi yayi sama da ita ya saɓa ta a kafaɗa ya damƙe ƙafafunta da hannu ɗaya, ɗayan hannun kuma ya buɗe ƙofar ya shiga ciki, cikin tashin hankali ta shiga mutsul mutsul tana wurwurga ƙafa tana dukan bayan sa, amma ba sauke ta ba sai da ya juya zai rufe ƙofa ta gasa masa cizo a gefen wuya da sauri ya jefar da ita ta gaɗi ƙasa, juyawa yayi yaci gaba da ƙulle ƙofar, tana ganin haka bata bima takan zafin da taji ba, ta miƙe cikin sauri tana kwasa aguje tayi ɗakin sa, tana shiga Allah ya taimake ta da muƙulli ajiki tayi saurin sakawa ƙofar key, sai loƙacin ta zame a wajen ta zauna tana sauke numfashi tare da dafe ƙirjin ta hannu tana zazzaro ido ita kanta tasan yau sai ta Allah tajawo ruwan dafa kanta yanzu gashi bata da mafita sa'arta ɗaya da ɗakinnan da muƙulli amma tasan yau da ina jin sai ya kashe ta a gidan nan. Saida yagama rufe ƙofar juyowar da zaiyi yaji tana saka key a ɗakin sa, mamaki ne ya kamasa yaushe har ta tashi daga wajennan ta shiga ɗakin baiji taba, anya kwa yarinyar nan ba aljana bace ko kuma da aljanu ajikin ta, abubuwan da take ba irin na mutane bane, rannan daga fitowar ta ya nemeta ya rasa kuma babu inda bai duba ba yanzu kuma gashi kafin ya juyo harta bar wajen, sannan yau baisan daga ina ta fito ba sai kawai ganin ta yayi kuma tana harbi to waye ma ya koya mata harbi irin haka, ga abun da tayi masa a gaban mutane tana wasu maganganun kamar mahaukaciya, to kode tana da taɓin hankali in ba haka ba a ina sukayi haka da ita shi da ya nemeta ya rasa amma tazo tana wasu banzan maganganu kuma agaban kowa, gaskiya dai saidai idan taɓin hankali gare ta, ya faɗi ƙarshen maganar tasa a fili, dan shifa gaba ɗaya lamarin yarinyar nan ya ɗaure masa kai. Rasa me zaiyi mata yayi sai kawai ya koma kan kujera ya zauna ya ɗors ƙafa ɗaya kan ɗaya yana tunanin mafita gashi duka spare key ɗin suna cikin ɗakin. Beenish na zaune agun saida ta gama tsanewa sannan ta miƙe tsaye ɗakin ta shiga bi da kallo babu wasu tarkace a ɗakin daga gado sai wardrobe sai kan madubi da ɗan tarkace akai, gaban madubin taje tana kallon kanta a madubi, a hankali tace wayo Allah na yanzu ya zanyi in bar ɗakin nan, ƙarar waya taji, da sauri ta juya tana kallon kan gadon can ta hango ta, da sauri ta ƙarasa gurin tana ɗaukar wayar duba screen ɗin wayar tayi nan taga hoton me kiran tare da suna an rubuta My Dad da ɗan emojin heart, gaban ta taji ya yanke ya faɗi ganin hoton mutu min, tabbass ko zata mutu ta dawo bazata taɓa manta wannan fuskar ba, take duk wani annuri da yayi ragowa na fuskar ta ya ɗauke idon ta har ya sauya kala, tana kallon wayar harta katse wani kiran ya kuma shigowa ɗagawa tayi tana saka wayar a handsfree tare da hararar wayar kamar shine a zahiri. "Hello Son, hello kana jina kuwa? Hello... Kashewa tayi dan bata so ta kuma jin muryar sa a rayuwar ta, yanda ta tsani rayuwar ta haka ta tsani mutumin nan da duk wani wanda ke tare dashi, cikin tsantsar ɓacin rai ta ɗaga wayar ta doka ta da ƙasa take ta tarwatse, bin wayar ta kuma yi tasa ƙafar ta dake cikin takalmi har yanzu ta murjeta tana tattakawa da ƙarfi kamar kamar ta samu mutum sai ciccije baki take yi, tana gama takawa kawai ta zube agun tana fashewa da wani irin kuka, cikin kukan tace "Allah ya isan mu tsakanin mu dakai mugu la'ananne in sha Allah ƙarshen ka bazai kyau ba daga kai har iyalan ka, yanda ka baƙanta mana rai kaima Allah ya baƙanta maka fiye da wanda kayi mana, Allah ya isa Allah ya isa, wani kukan ta kuma fashewa dashi tana toshe bakin ta da hannu "Baba Baba wannan mugunne ya raba mu da ku ya kashe mana Mama ya sanya rayuwar mu cikin garari ya raba mu da ku gaba ɗayan mu, hannuwanta tasa duka biyu ta riƙe kanta tare da cire hular kanta, tana kama kan da ƙarfi tana ci gaba da kuka, sosai take kuka kamar ranta zai fita , dan sosai ganin sa yasa ta tunawa da abubuwa da dama, komai na shiga dawo mata cikin kanta... tammat bi hamdulillah. Alahamdulillah Alahamdulillah duka duka anan na kawo ƙarshen su waye su na 1 sai kuma mun haɗu a Book 2 ranar Monday in sha Allah dan gobe da jibi bazan yi ba, zan ɗan huta kafin muci gaba, daman kowa dai yasan paid book ne dan haka me son ci gaba da karanta su waye su zai ci gabane kawai idan ya biya ansashi a paid group. *TAMBAYYOYIN KU DAKE CIKIN BOOK 2* 1, Shin ya zata kaya tsakanin RK da Beenish wane irin zama zasuyi kenan shin zatayi nasara akansa da kuma mahaifinsa da take son ɗaukar fansar mahaifin ta akansa, shin shima kuma idan ya gane me take son yi wane irin mataki zai ɗauka a kanta. 2, Ɓangaren su Bilal shin wa Fateema zata bi acikin su, idan tabi Salama zata koma hannun Rabi ne da ta baro, idan kuma tabi Faheema zata koma hannun baban Faheema da ya kashe mata miji agabanta wanda bata manta fuskar sa ba, ida kuma tabi Bilal zata haɗu da su Maryam da kuma ƴarta. Sannan jakunkunan hannun su babu matsala idan sukaje ko wane gida dasu baza'a samu matsala ba? 3, yaza ta kaya tsakanin Rabi da Bulama da suka fara takun saƙa a tsakanin su, waye zaiyi nasara? 4 waye Musbahu, shima kuma da alama zasuyi takun saƙa tsakanin sa da abokan harƙalar sa musamman Boss ɗin Hajja Mama, 5, SMA yana mutu ne a gidan Hajja Mama ko yana raye, Hajja Mama ta mutu ko tana raye? 6, meye tsakanin su Beenish da Dannar sannan me tayiwa ƴarta da basa jituwa me take son sani game da rayuwar ta? 7, waye Sardauna? Wace ce Dhuhar? 8 , meye da meye acikin jakar da kowa yake farautar ta da ba asan tana hannun wa ba. Duk meye ma musomin wannan abun duk akan me ake maganar Su wa da suwaye acikin wannan ƙungiya? SU WAYE SU...!? hmm kar na cika ku dan akwai tambayoyi da yawa fa na manta ma wasu guraren. Wallahi har yanzu ba'a fara littafi ba hajiyata acikin kaso ɗari baifi kaso biyar mukai ba, akwai hargitsi a gaban mu, kude ku cigaba da kasancewa da ta daban acikin littafin ta na daban wanda iya na dabanne suke karantawa....💃💃💃💃 Kude kar ku bari abaku wannan labarin domin kaji da kanka yafi abaka labari wallahi, kuyi min riƙon ƙauna ku fito ku siya dan yanzu zan gane masoyan gaskiya, banda laɓe a waje ana jiran update kawai gwanda ki garzayo ki shiga dumu dumu ayi tafiyar dake... Special thanks to all fans ɗin su waye su, ina godiya sosai da gudunmawar da kuka bani tundaga farko har zuwa yanzu da muka ƙare na 1, masu Comment jinjinar bangirma agare ku, ƙwarai da gaske ina jin daɗin yanda kuke min saaidai ince Allah ya bar ƙauna ❤️ kuci gaba da yi min riƙon ƙauna. *Zaku biya 500 ne kacal domin samun damar ci gaba da karanta littafin su waye su, dan Allah basai kunyi min mgn ba kawai ga account nan ku tura sai kuturon da shadar ta nan 08124226526. Ga account ɗin da zaku saka kuɗin ku,👉 *8124226526 Azima Aminu Dahiru opay bank,* *0003562691 Ibrahim Badamasi Babangida ja'iz bank,* Ƴan Nijar kuma zuwa ranar Litinin zan baku account ɗin da zaku saka naku. Ƴan facebook kuma da basa Whatsapp zan buɗe muku privet group a facebook ɗin duk wanda ya biya sai insaka shi a ciki. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 44 of 44