kam ita ko ajikin ta dan ita ba ruwanta da ƙyamar talaka ko rashin yarda da mutum ita kowa ma nata ne, babu ruwanta, tare suka jero da ita tana ta faman zubar tana bata labarin yanda Bilal yake da tsoro kamar mace, shiyasa taga yana yi mata wannan abun amma da ya fahimta zai daina, yanzu ma dan ya riga da ya tsorata ne, matar sai dariya take itama tana gaya mata yanda ya nuna tsoron sa loƙacin da yaganta, Allah ya sama baiyi mata fitsarin a kanta ba, a gefen ta yayi.
Suna tayiwa Bilal dariya har suka ƙaraso inda yake, yana zaune yana ganin ta ya kuma haɗe jikin sa yana ɗora kansa akan gwiwar sa, yana damƙe hannun sa.
Salama ce ta zauna a gaban sa tana cewa "dalla rago kawai, wai kama gama fitsarinne ko in rakaka ka ƙarasa, tana maganar tana masa dariya.
Banza yayi mata bai kulata ba bai kuma ɗago ba yanzu dai ya yarda ba aljana bace, abun da ya hanasa ɗagowa kuma kunya ce dan tunanin sa ko ta gansa ba wando yana fitsari, shiyasa yaƙi ɗagowa, gashi kuma Salama ma zata kuma raina sa tunda har ta fara tsokanar sa, duk yanda taso ta kulata ƙin kulata yayi, gashi bayaso ya tashi yaje wani gurin ya kuma gamo da wani abun da bar mata gurin zai yi gaba ɗaya.
Suna zaune agun Salama tana tsokanar sa su Zaid suka dawo gurin tundaga nesa suke zancen macen da suka hango agurin, ko da suka ƙaraso da ido Faheema ta tambayi Salama tana nuna matar.
"Gulma ajali in ba'ayi ba a mutu, ki zauna mana amma daga zuwa har kin fara min signer da wace, bakyau dai zuɓɓe.
Kunya Faheema taji ta kamata jin tonon siririn da Salama tayi mata, sai kawai ta maze tace "to ai gaskiya ne kinsan duniya ba abun yarda bace, mu barku ku kaɗai muzo mutarar da ku da wata kinsan ai dole mu tambaya.
Zaid ma yace "nima daman yanzu nake shirin tambaya tundaga can muke tambayar kanmu da wace ce?
"Uhm da gaskiyar ku to wannan dai da kuke ganin ta, aljanar big boy ce, yanzu ya samo ta yake fitsari, shine ta biyosa har nan.
"Kumar ya aljana? Ban fahimce ki ba, Faheema ta tambaya tana ɗan zaro ido.
Salama ce tace "malame kunga ku bamu abinci muci bansan gulma, idan mun gama kwaji komai, duk yanda suka so ta basu labari ƙin basu tayi, matar ma zata yi magana ta hanata, tace ta rabu da su wallah sai taci abinci zasuji komai, kamar suyi mata dukan tsiya haka su ka ji, amma dole suka rabu da ita suka zauna suna buɗe abubuwan da suka siyo.
Anyi anyi Bilal ya ɗago kansa yaci abinci yace wallahi indai matar nan tana gurin bazai ɗago ba, cikin sanyin jiki matar ta miƙe tsaye tace "yaro kayi haƙuri bari in tafi, amma ni bazan taɓa zutar da ku ba, kuma ba aljana bace wallahi.
Shi kansa Bilal bai san loƙacin da bakin sa ya suɓuce ba yace "cuta nawa kuma tunda kin riga da kin ganeni, me yasa tun kan na tsugunna baki motsaba, saida na kusan gama fitsarin bayan kin gama kalle ni zaki motsa, yanzu kuma zaki wani ce bazaki cutar damu ba, ai ni kingama cuta ta wallahi.
Ita kanta matar saida da dariya ta kamata, suma su Zaid da basu san labarin ba saida suka shiga yi masa dariya, matar ta danne dariyar ta ce "dan Allah kayi haƙuri wallahi wallahi banganka ba, kaji dai na rantse, da gaske nake nima bacci nake kuma a lulluɓe nake saida naji motsin ka, sannan na shiga cire mayafin da ma rufa, ina ƙoƙarin buɗewa naji kana ihu shiyasa na yi saurin miƙewa amma dan Allah kayi haƙuri ka yarda da abun da nace maka.
Yana daga kwancen ya kuma cewa "ki ƙara rantsewa bakiga komai ba.
"Wallahi banga komai ba.
Zaid ne yace kaji min ɗan iskan yaro to in ta ganka ma meye aciki, wannan bata haife ka ba, ba uwarka bace, ke ma kuma kika tsaya biye masa, to babu inda zata saidai ka dawwama anan kuma muna gama ci zamu bar gurin sai muga yanda zakayi.
Ɗagowa Bilal yayi yana aika masa da harara yana tutturo baki, kuma duk da haka bai ɗago ya kalli matar ba,
Salama ce ta ce "kinga Mama ki yi zaman ki muci abinci ki rabu da wannan yaron.
Dawowa tayi ta zauna idon ta nakan Bilal yanda taga yana ta wani ɗauɗɗauke kai gefe, ita sai ys bata dariya ma, shi nan ashe kunya ce ta hana sa ɗagow, nan dai su Zaid suka ɓuɓɓuɗe abubuwan da suka siyo, kowa ɗaukan abun da yake so yayi suka hau ci abubuwa suka siyo da yawa ga ruwana sanyi da lemuka, nan dai kowa yaci ya ƙoshi dan Bilal ma baisan loƙacin da ya saki jiki ya ringa tura abincin ba...
$$$$$$$$$$$$$$$$
*MARYAM*
_____Drivern na mayar dasu gida, Babyn baby ta kwanta zazzaɓi ya rufe ta, saboda kukan da tasha, har dare zazzaɓin ba sake taba, saida Maryam ta lallaɓa ta fita a daren taje ta samo mata magani sannan ta dawo, ta ɗan soya mata ƙwai amma ta kasa ci, ta tambaye me zataci kafin ta sha maganin tace babu komai, da ƙyar dai ta lallaɓata tasha lemo, sannan ta bata maganin tasha ta kuma kwanciya, saida Maryam taga ta kwanta sannan hankalin ta ya ɗan kwanta a gefen ta ta zauna tana kallon ta, nan take ta shiga tunanin mahaifiyar ta dan har yanzu bata mance fuskar taba, saboda suna yanayi da Babyn baby.
Anan falon ta rabu da ita kan kujerar dan bata so ta tashe ta, itama sai ta ɗauko bargo a ɗaki ta shimfiɗa a ƙasa, ƴar ƙaramar wayar ta ta ɗauko ta kunna radio nan take jin sanarwar abun da ya faru da Bulama asibiti ya ƙone da wani gidan sa gobara ta kamasu, da sauri ta tashi zaune tana mamakin ya akai hakan ta faru ko shiyasa jiya ya fita ba tare da ya ɗauki Zee ba,indai kwa hakane ya zama dole gobe su bar gidan nan, dan dama bazata iya zama ba ita kaɗai saboda Bulama ya san tana gidan ko badan kanta bama, idan yazo zai iya cutar da Babyn baby idan ya rasa sauran,kusan kwana tayi tana tunanin mafita, saida safe ta kira Hajiya Dannar ta sanar da ita abun dake faruwa, nan Amma tace mata ta bari zata zo gidan anjima sai su tattauna.
Babyn baby ta tashi jikin da sauƙi saidai bazata iya zuwa makaranta ba, hakan yasa dole ta zauna a gida dan ta ƙarasa warwarewa, tunda ta tashi take kiran layi kan su Beenish amma babu wanda ya ɗauka daga cikin su, ta kira ko wannen su yafi sau ashirin, bata da aikin yi daga takira layin wannan idan ba a ɗaga ba, sai ta kuma kiran na wannan haka tai tayi, rashin ɗaga wayar tasu shi ya kuma ɗaga mata hankali, tayi jigum ta zanbga uban tagumi idon ta duk ya cika da ƙwalla kana ganin ta zata baka tausayi.
Maryam na ganin ta haka ta zauna ta riga janta da hira tana kwantar mata da hankali, amma duk da haka ta kasa sakin jikin ta.
Suna cikin wannan halin Ammu ta ƙaraso gidan, saida ta kira Maryam tazo ta buɗe mata ƙofa, tashi tayi taje ta buɗe mata, tare suka shigo cikin gidan.
Ammu na ganin ta saida taji tausayin ta da sauri ta ƙarasa ta zauna a gefen ta tana rungume ta tace "haba my little baby me yasa zaki saka kanki cikin damuwa, jifa kwana ɗaya yanda kika koma, dan Allah ki kwantar da hankalin ki, bafa daɗewa zakyi ba, ko bakya so agano inda mahaifiyar ki take, duk fa anayin wannan abunne duk domin ke, yanzu da kema fa nake shirin turaki wani gidan yau kiyi min naki aikin yanda mamanki idan ta dawo zataji daɗin abun da ƴarta tayi akanta.
Da sauri Babyn baby ta goge hawayen ta tace ina so!
"Yauwa mu daughter ko kefa, idan kina shiga wannan damuwar kuma ai bazaki iya komai ba, ke da ya kamata ki zage ki zama jaruma, amma sai kina kuka saboda wasu sun tafi, sai kace baza su dawo ba.
Cikin muryar kuka "Babyn baby tace da gaske Mamana tana raye bata mutu ba?
Duk da Ammu bata da tabbass amma dan ta kwantar mata da hankali tace "eh tana raye mana, ai shiyasa duk muke wannan abubuwan dan mu gano inda take, amma sai kin zama jaruma kunji?
Cikin jin daɗi tace "zanyi ko ma meye indai zata dawo, inganta, banta taɓa ganin taba fa.
Ammu tace "ai nan bada jimawa ba zaki santa, harma kuyi rayuwa tare, kedai ki ta addu'a Allah yasa agano ta da wuri, duk wani shiri da muke ya tafi daidai.
"Ina yin addu'a kullum sai nayi mata addu'a, in sha Allah zanganta.
"Yauwa haka ake so, a koda yaushe mutum ya shiga wani hali yai ta gayawa Allah buƙatar sa, Allah zai biya masa, sosai Ammu taita janta da hira har tace da ita ta tashi taje ta shirya zasuyi magana da Maryam, sai su tafi anjima da yamma, ba musu Babyn baby ta tashi ta tafi batare ma da tunanin ina za'a kaita ba.
Saida ta shige ɗaki sannan Ammu ta sauke ajiyar zuciya tana maida dubanta ga Maryam da ta zuba musu ido kawai take kallon su, tana sauraron su.
Maryam ce ta rigata cewa da "har kin samu inda zamu zauna ne naji kince ta shirya da yamma zamu tafi.
"Eh mana, bana taɓa gaya miki daman inaso aje gidan Ɗan ijje ba, ina so ku gano waɗanda yake mu'amala dasu, da inda yake ajiyar kuɗaɗen sa, da shige da ficen sa, zaki je gidan ne a matsayin ƴar aiki Babyn baby kuma amatsayin ƴarki, nayi magana da wata ƙawata da take da alaƙa da matar gidan, tace zaku iya zuwa, daman suna neman masu aiki, saboda ɓatan ɗansa yasa duk ya zama kamar mahaukaci duk ya kori wasu daga gidan harda matar sa, ma'aikatan ma abu kaɗan zakayi masa ya kore ka, shiyasa yanzu gaba ɗaya suka rasa ma'aikata, kuma sai kunyi taka tsantsan dashi, zan tura miki dukan halayyar sa yanda zaku zauna lafiya dashi, sannan sai Babyn baby ta zama me biyayya sosai a gaban sa, sannan ku ringa jan ƴaƴan sa har ku saba dasu indai kuka saba dasu to shima zai saba daku, saidai bashi da yarda sai kunbi sa a hankali, ba kowa zai iya zama dashi ba har sai inka fahimci waye shi sannan zaku zauna lafiya, abun dai da muke buƙatar sani kin ringa da kin sani tun ba yanzu ba nayi miki bayani, loƙaci yayi da zamu gano gaskiyar lamari akan sa, shin da hannun sa ko babu hannun sa aciki.
"Jinjina kai Maryam tayi tace gaskiya ne wannan daman abun da ya kamata mu fara yi ma tun farko kenan, yanzu indai ansan da zuwan namu ai shikenan ba wata matsala ko yanzu zamu iya tafiya, danni wallahi Allah ina tsoron Allah ina tsoron Bulama dan mutumin nan ba a haifa sa da ɗigon imani ba, nasan yanzu duk wani shirin sa nice kan gaba, amma yanzu idan muka koma can nadan babu ta yanda zai taɓa kawowa ina can.
Dariya Ammu tayi tace "kai mutumin nan bashi kirki, kice har yanzu da tsoronsa bai sakeki ba.
Itama dariyar tayi tace "hmm ai baza ki gane waye shi ba, ba mutuwar ce abun tsoron ba, ta hanyar da zaibi ne abun tsoro kuma shi baya abu ɗaya yanzu dai ba ya ganni da yaran nan ba, to wallahi idan yazo har su zai haɗa dan shi bai ɗauki ran mutane a bakin komai ba, ko ita rabin sa'ar su ɗaya da abu ajinkin su, yana shakkar su da tsafe tsafen su amma badan haka ba da tuni ya daɗe da ganin bayan su, kuma da son da yakewa ƴar ta har takai ga ya maida shi kan jikarta kinsan kwa wannan ai ba ƙaramin so bane kuma babu abun da bazai iyayi ba tunda har ya ɗau wannan tsawon loƙacin akan ƙudirin abu ɗaya.
"Gaskiya ne babu abun da bazai iya ba, saidai mu roƙi Allah yayi mana tsari da shi sannan Allah ya kawo ƙarshen sa.
Maryam tace "Ameen dai"
Nan suka ci gaba da tattaunawa har Babyn baby ta shirya ta fito da ƴar akwatin ta,
Kallon ta Amma tayi tace "ina zaki da uban kaya haka so kike a zargi da wani abu da wuri kenan ai ai bakko zaki nema ki saka kamar kalar biyar ko ki bawa Maryama ta haɗa da baki ta ƙulle muku a ɗan kwali ku da zaku a matsayin ƴan aiki, ina ke ina shiga irin haka.
Waro ido tayi jin me akace mata, da sauri ta ce "Ammu to makaranta ta fa?
"Kar ki damu zakici gaba da yi amma sainan da kamar wata ɗaya sai a roƙi matar gidan akan karatun naki, sai ace mata saboda haka kuma fara neman aikin ana biyun ku tana biya miki kuɗin makarantar kingane?
Jagwab Babyn baby ta zauna kan kujera cike da tunanin taya hakan zata faru, ba ƙaramin bayani su Ammu suka shaba kafin su fahimtar da ita ta gane, har ta yarda.
Sai wajen ƙarfe huɗu sannan suka fito daga gidan tare da motar Amma suka shiga, Saida ta kaisu bakin unguwar, sannan ta sauke su tana ta kuma yi musu bayani sosai da ƙara bawa Babyn baby haƙuri sannan ta juya su kuma suka nufi cikin unguwar saida suka sha tafiya sosai sannan suka ƙarasa cikin layin tundaga bakin layin gidan sa ya fara, haka sukai ta tafiya har suka isa bakin gate ɗin, Babyn baby sai cika take kamar zata fashe haka take jinta ansata ta saka riga da zanin ga wani uban mayafi da aka bata ta yafa shima na Maryam ne, sannan suka siya mata silifas a hanya, jinta take gaba ɗaya kamar zata nitsi dan ta ƙaici.
Saida me gadi yayi musu sallama da cikin gidan suka faɗi gurin wanda suka zo sannan aka barsu suka shiga.
Tunda ga waje suke ta bin gidan da kallo har suka ƙarasa shiga har cikin falon, Maryam ce ta iya yin sallama mutum biyu ne a falon samari guda biyu, amma yanda tayi sallama sai kawai suka ɗago suka kalle su suka juya suka ci gaba da game ɗin su ko amsawa basuyi ba.
Jinjina kai Maryam tayi sai ta kuma ɗaga murya ta kuma yin wata sallamar duk da tasan sunji, da sauri Hajiya Khatume ta fito tana amsawa tace "ku kuna ji ana ta yin sallama babu wanda zai amsa ko baza ku daina wannan halin naku ba ko, to kuci gaba duniya ba uwa bace da zata ɗaga muku ƙafa, zata koya muku hankali wataran.
Saida ta gama da su sannan ta juyo tace "kuyi haƙuri dan Allah basu da kirki wallahi yaron zamani sai haƙuri, ku shigo ciki dan Allah.
Murmushi Maryam tayi tace ah babu komai wallahi, fatan kin gane mu dai ko mune aka turo da zamuyi aiki.
Da sauri tace "nasani ai Hajiya ta sanar sani tunda kuka taho, nan suka ƙarasa shiga cikin falon, Babyn ce tayi ɗaraf zata zauna akan kujera, wani daga cikin samarin yace "ke baki da hankali kin taɓa ganin ɗan aiki ya zauna akan kujerar masu gida?
Mamaki ne ya kusan kashe Babyn baby, sai kawai ta ƙame ita bata zauna ba ita bata miƙe ba, gudun kar tayi musu katoɓara yasa Maryam tayi saurin riƙo hannun ta tace kuyi haƙuri yarinya ce dake wannan ne farkon fara aikin ta bata sani ba, ke kuma ba haka ake ba, ki zauna a ƙasa ki gaishe su.
Shiru kawai tayi tana zama a ƙasa amma aranta ta rantse bazata gaida su ba, har gwanda matar taga tana da kirki, amma sude babu wanda zata gaisar...
Matar gidan kawai ta kalla ta ce "ina wuni.
Da fara'ar ta tace "lafiya lau ƴan mata, sai kinyi haƙuri da yaran namu kinji.
Ɗaga mata kai kawai Babyn baby tayi hakannan taji duk haushin su ya cika mata ciki, shiru tayi ta shiga kalle kalle a falon, su kuma su Maryam suka ci gaba da gaisawa, Khatumme tana yi mata bayanin tsare tsaren gidan.
Babyn baby na kalle kallen ta idon td ya sauka kan hoton Bilal, ɗan waro ido tayi dan bata mance sa ba, mamaki ne ya kamata daman gidan su sukazo, yin aikin yanzu idan ya ganta fa ya tona musu asiri fa ya zasuyi shikenan burin su bazai cika ba, wata zuciyar ce tace mata ai ba lalle ya gane ki ba, wata ƙilma ya manta fuskar ki, da sauri ta shiga girgiza kai a fili ta ce "kai a'a wallahi zai gane ni.
Da sauri Maryam ta kalle ta tare da cewa "me kika ce Baby?
Sai yanzu abun da tayi ya faɗo mata sai tayi saurin cewa "uhmm daman kawai kawai bamma san me na faɗa ba zancen zuci ne kawai.
"Bata kuma ce mata komai ba ta juya suka ci gaba zancen su da Khattume...✍️
*Ina me sanar daku Free ya kusan ƙarewa in sha Allah ina tunanin indai nakai inda nake son kaiwa a page 50 zan dakata Free pages zasu ƙare sai ku fara shirin payment 500*
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
________* 08124226526*_______
*_episode 47💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
_Bismillah..✍️_
*SOKOTO*
_____*BULAMA*
Tun yana kan hanya ya fara kiraye kirayen mutanen sa yana sanar dasu abun dake faruwa tsakanin sa da Rabi, nan yasaka yaran sa dake cikin garin Sokoton, yace su isa gidan nata kafin ya ƙaraso, shi kaɗai yake tuƙin sa babu ɗan rakiya yana tafiya kuma yana shirya abubuwan da zaiyi.
Yana shiga garin Sokoto ya dira a gidan Rabi, a waje ya tsaya sannan ya zaro wayarsa ya kira yaran nasa yace suna ina, duk fitowa suka shiga yi daman suna kusa da gidan sun rarraba kansu gudun kar a zargi wani abun a kansu.
Gaba ɗayan su ko wane da makami a hannun sa wajen su goma take suka doshi cikin gidan tare da yiwa gate ɗin wani irin mugun bugu, da sauri me gadi ya baɗe ƙofar yana sako kansa dan ganin su waye masu bugun hauka haka, yan leƙowa ɗaya daga cikin yaran ya mareshi ta gaba tare da tura fuskar sa gaba ya tura sa sannan suka danna kai ciki su duka.
Saidai suna shiga sukaji an saki harbin bindiga da sauri suka fara shirin juyawa amma Bulama ya hana su, tunda basuga me harbin ba kawai ƙarar bindigar suka ji, nan su kaga ƴan sanda na fitowa daga cikin falon gidan su huɗu ne, ga bindugu a hannun su.
Yaran Bulama tsorata su yi dan sun san kafin suyi wani yunƙuri zasu iya harbin su daga inda suke hakan yasa suka fara juyawa da gudu wasu ma basu san sun ture Bulama ba wajen guduwa su fita daga cikin gidan, shikam Bulama ƙyam yayi ya tsaya batare da ko motsi ba.
Me gadin ma tashi yayi yabi bayan yaran Bulama dan yama rasa inda zaiyi, saboda baiga shigar ƴan sandan ba, sai fitowar su kuma yasan matar gidan bata nan hakanne yasa shi binsu shima.
Gaba ɗaya kansa sukayo suka zagaye sa, suna saita shi da bindiga, tare da cewa "you are under arrest kada ka motsa zamu harbe ka.
Wani shu'umin murmushi Balama ya saki tare da cewa "naga alamar baku san ko ni waye ba, to ku hanzarta sauke bindugun ku kafin kusan da wa kuke tare, wa ya baku lasisin yin harbi acikin gida, kuma aikin ta kuke ko aikin hukuma, me yasa bakuyi bincike ba kafin ku fara yanke hukunci yana da kyau ku fara binciken ita kanta matar gidan kuga wace ce ita indai baku kamata ba da ko wane irin laifi ba to na yarda kuzo kuyi arresting ɗina da babu inda zani, yana da kyau ku muje ciki gaba ɗayan mu.
Ɗaya ne daga cikin ku yace babu ruwan mu sa wace ita abun da idon mu ya gane mana da shi zamu yi aiki mun kamaka ka shigo da ƴan daba gidan matar aure wanda hakan kaɗai ya ishe mu shaida kana mata barazana, gashi kuma mun gani da idon da haka ka wuce kawai duk wani sauran bayanai kayi su a police, we are under our permission, saka mu akai dan haka dole ka juya nutafi, "Sani arrest him!
Da sauri wanda aka kira da Sani yayi kansa zaisaka masa ankwa tura sa gefe tare da zaro tasa bindigar dake ƙugun sa, yaja wuyan wani ɗan sanda yana saitawa akan sa, yace duk wanda bai ajiye ba shima sai ya harbe shi.
Duk ajiye bindugun sukayi suna faman rarraba ido.
"Yanzu ku zan sa a ƙulle sakamakon shigar da kukayi kuna shirin kama mutane batare da anbaku izini ba, ku gaya min daga wane station aka aiko ku, yanzu in kira insanar dasu.
Babu wanda ya tanka masa dan basu san me zasu ce masa ba kar suje yajawo musu ruwa dan ba wanda ya sa su yin hakan inba Rabi ba komai na bogi ne daidai da bindigar ba ta gaskiya bace, babu ko bullet ɗaya a ciki.
Ganin duk sun ajiye bindugun yasa Bulama ya saki wanda ya riƙe yace "nawa ta biya ku zan ninka muku su sai huɗu, ku dawo yi min aiki, amma kada ku taɓa nuna kuna bayana ku kasance tare da ita ɗin ni kuma zan gaya muku me zakuyi mata, kun yarda.
Ai da sauri suka shiga ɗaga kai, jin yace zai ninka musu sau huɗu, murya ƙasa ƙasa wani yace "oga ai angama ko mai kake so zamuyi maka saidai gaskiya yanzu bata gidan tace daman in kazo mu kamaka musaka amota sai mu shaƙa maka abu ka suma, daga nan sai mu kira ta mu sanar da ita.
Murmushi kawai Bulama yayi yace "da muatane a cikin gidan?
Girgiza masa kai sukayi, sai ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 41 Chapter of 44