Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ina neman koto da taban dama domin wanke me laifi da yake shirin ɗora kansa laifin da bashi ya aika ta ba. Kowa da mamaki yake kallon ta, Da sauri lauyan Jambo ya miƙe tsaye yace; "ya me girma me Shari'a ina da jaa wann.... Ɗaga masa hannu yayi ya dakatar dashi tare da cewa koto bata baka dama ba, Cike da taƙaici ya jinjina kai yana komawa ya zauna, Alƙali yace mata muna sauraron ki, "Labaran bashi ya kashe su ba, Jambo ne, ni yabawa abu na zubawa malam Rabo yaci ya mutu da yaga haka kuma......nan ta kwashe duk yanda suka tsara ta bada labarin komai, Jambo da borin kunya ya fara hauka yana ƙaryata ta yana faɗin sai ya kashe ta, babu wanda ya isa ya kamasa, da ƙyar jami'an gurin suka kama sa, direct aka fita dashi waje sannan aka yanke masa life in prison, Kowa yayi farin ciki da haka, Khadija kuwa sa taji haka saida tayi da nasanin duk abun da tayi masa, kuma tayi tayi ya maida ita amma fir yaƙi shima, dan ji yayi gaba ɗaya garin ya fitar masa a rai, ko wata baiyi ba, ya ɗauki mahaifiyar da ƙanwar sa, suka koma, can wani gari dake kusa da Zamfara me suna Lautai, haka rayuwa taita tafiya, duk da yarinyar sa tana ransa amma bai taɓa zuwa ganin ta ba, ko sau ɗaya, Itama kam ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba ba uwa ba uba, mahaifiyar ta na gidan yari, mahaifinta kuma na inda ba'a dawowa, a hannun ƙanin baban ta take, shikuma matar sa bata da mutunci, zaman haƙuri kawai take gashi ta nemi inda labaran yake a faɗin garin ta rasa inda ya shiga, Bayan wasu shekaru, aka samu da ƙyar tayi aure, inda mutumin kuma akayi sa'a ɗan garin Lautai ne, kuma layin su ɗaya, dan haka basu wani daɗe ba suka haɗu da juna, sai ta basa ƴarsa mahaifiyar sa taci gaba da kula Abu, (Bari dai inyi muku a gurguje naga zai ɗauke ni loƙaci) A taƙaicce dai,bayan wajen shekara goma, Jambo bai canza hali daga gidan yarin yake ƙula duk wani abu da yake so, tare da taimakon mahaifin sa sa ya goyi bayan ɗansa suka ci gaba da neman inda suke a haka har sukayi nasarar gano inda suke, saboda mugunta me garin ya koma can garin da zama gaba ɗaya tare da iyalen sa duk dan ɗaukar fansa. A haka suka kadawa garin gaba ɗaya garin da mugunta dake ƙaramin gari ne kuma ƙauye yasa basu da ilimi na boko da na zamani, hakan yasa me gari mulke ƴan garin, ake ta zuba mugunta duk dan ayi nasara akan su Labaran. Kamar yanda suka tsara saida suka kashe mahaifiyar da ƙanwar sa, da Abu taga haka sai ta ɗauke ƴarta taci gaba dayi musu magani ita sa ƴar dan mahaifinta da zai mutu a rubutun takardar ya sanar da ita duk yanda zatayi wasu magungunan sannan ya bata wasu acikin jakar da ya cilla, ta tsinceta loƙacin da ta rataye zanin wanka ya faɗa baya, bayan ta gama shiryawa da wasu kayan sai ya zagaya ɗauko sa anan taci karo da jakar. Daga nan suka kafawa Labaran da abubuwa da dama amma sunƙi yin nasarar kashe shi, dan haka sai kawai suka ɓillo masa ta wata hanya, suka jinginar dashi bashi da wani amfani kallo kawai yake amma baya magana, kuma baya tafiya, yana kwance ko da yaushe, Babu yanda Abu ta iya dole ta taimaka masa da magunguna da kuma kula dashi, mijin da yaga haka sai ya dakatar da ita da cewa idan bata daina ba, sai ya sake ya, haka ta haƙura saidai ta saci idon sa ko kuma ta aiki Abu ta kai masa wani abun ko ta taimaka masa, loƙacin shekarar ta sha uku, sosai take tausayin mahaifin nata kuma a haka take taimaka masa, shi kaɗai me a gidan shiyasa wataran take kwanciyar ta kusa dashi, Suna shan wahalar rayuwa dan duk abun da ta samu a kansu yake ƙarewa, amma duk da haka batayi ƙasa a gwiwa ba, ga karatu da tasaka yarinyar dake can cikin garin su Islama da boko. Loƙacin da Abu ta cika shekara ta ashiri, ta gama secondry school sun kusa sauka a karatun Qur'ani, loƙacin ne su kaji wani mummunan labari cewar Jambo ya fito daga gidan yari, Hankalin su ya tashi dan har aiko musu yayi tunda bai auri uwar ba sai ya auri ƴar ta ko tana so ko bata so, Ita dai tasan bai isa yayi mata komai ba, saidai kuma tana tsoron abun da zai yiwa ƴar da kuma labaran dan haka ta roƙi mijin ta da yabar ta ta dawo dashi cikin gidan sa, a wani ɗan ƙaramin fili, sake cikin gidan amma yaƙi yace saidai ta siya haka ya saka masa kuɗi me yawa ta siya ta biya aka gina, mata sannan ta maidashi ɗakin, Abu taci gaba da kula dashi, Tashin hankali dai da yayi yawa taga indai yarinyar ta tana cikin garinnan bazai taɓa ƙyale ta ba sai ya cika ƙudirin sa akan ta kamar yanda yayi alƙawari, Da kanta ta ɗauke ta tare da kayan ta ta baro garin da ita suka shiga garin Kano batasan ko ina ba, amma a haka ta ringa yawo tana nemawa ƴarta gidan aiki, a haka suka samu, bata bar garin ba saida ta samu ta siya mata ƙaramar waya itama ta siya tare da layika, aka saita musu komai da nuna musu inda basu sani ba, kwanan ta biyu a garin ta dawo ƙauyen su, Tundaga nan ta samu salama domin kuwa duk bala'in Jambo har gidan yazo amma ba yanda zai yi da ita dan tafi ƙarfin sa, ya nemi Abu ya rasa, kuma shi duk da be taɓa ganin yarinyar yarinyar ba yaji yana sonta kuma da aure, amma gashi ya rasata, daga ƙarshe ma haka aka ce masa ta mutu dan har gawar ƙarya aka haɗa da taron mutane duk dan ya yarda, wasu sun yarda amma duk da haka loƙaci zuwa loƙaci yana zuwa ya tayar da hankalin ƴan garin, saidai yayi ya gama ba wanda yake kula sa, duk da yaji labarin Labaran bai mutuba shima nemansa yake ido rufe. Tun yana zuwa har ya daina zuwa, tajishi ɗif gaba ɗaya ma baya garin, kullum sai tayi magana da Abu duk halin da suke ciki sai sun sanar da junan su, duk wata tana turo mata kuɗin ta na wata idan an bata, duk sanda zasu haɗu saidai su haɗu a ɓoye... Bari mu dakata anan, sauran labarin ma ƙarasa sa acikin labarin, nasan dai yanzu kowa ya fahimci asalin Zee Barazanar, Zee Fashion, zamuji inda ta samo wannan sunan ya akai da ga Abu ta koma barazana. *Ci gaban labarin* Wash nagaji hannuna ya ƙage sai gobe😟😅🤣 [3/5, 11:50 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* ______________________________ *_episode 16💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bissmillah.....✍️ *Ci-gaban labari* ____Sun daɗe suna binciken yanda zasu gano tracking information na inda number take amma network ya hana su saboda ƙaranci network dake garin, sunyi sunyi amma da ya fara sai ya katse sun kasa har wajen ƙarfe biyu suna yin abu ɗaya amma ya gagara dole suka haƙura suka barwa gobe, Washe gari a subar fari suka bar garin, basu tsaya ko ina ba, sai a garin kano loƙacin da suka wajen sha ɗaya, dan haka makaranta kawai suka wuce basu tsaya ko ina ba, Shigar su ke da wuya sukaga pastocin hotu nan su, gaba ɗayan su, ganin hakan saida gaban su ya faɗi, kasa fitowa sukayi daga cikin motar, Da ƙyar sukayi ƙarfin hali suka fito suna bin duk inda suka ga hoton su da kallo, suna gurin daman kamar su ake jira sai gashi ɗan aike yazo musu wai Dr.Aveed yana neman su, Ko kallon ɗan aiken basu yi ba suka nufi office ɗinsa har zasu shiga aka ce musu baya nan yana can wajen da suke meeting a can a ke neman su, direct suka nufi can ɗin, Suna shiga bakin su da sallama duk amsawa sukayi suna duban ƴan matan da akace sun daki lectura guda, saboda tsaurin ido irin nasu basa tsoron abun da zai biyo baya, Sunkuyawa sukayi suna gaida ƴan wajen kawunan su duk a sunkuye, Sir Suraj kuwa sai washe baki yake yana binsu da kallon mugunta, Dr. Aveed ne yace; "kun aikata wani babban laifi sosai kuwa domin faɗa da lectura ba abu ne me sauƙi ba, duk da a kan gaskiyar ku kuke bai kamata kuyi masa haka a gaban mutane ba, kamata yayi kuyi masa a gefe ko kukai ƙarar sa gaba tunda akwai manya a gaba ko ba haka ba? Nan mutanen wajen kowa ya shiga jinjina kai cike da gamsuwar maganar da, Sukam shiru sukayi kansu a ƙasa suna sauraron duk abun da yake cewa. Sir Suraj kam tunda yaji yace akan gaskiyar su suke, gaban sa ya faɗi, sai faman zuba ido yake akan ko wannen su, "Saƙo daga me wannan makaranta yace kar ku kuma yin haka kuma ya yabawa ƙoƙarin ku nason kare wa mata incen su bisa ga ɓaya garin malamai kuma yace ku cigaba da saka ido akan duk wanda baiyi daidai ba ko ya taka mana doka, ko soyayya bamu yarda lectura yayi da wata yarinyar ba a cikin makarantar nan koda kuwa soyayyar gaskiya suke su bari in sun fita waje sa yi, me wannan makaranta yace in miƙa godiyar sa gare ku, sannan saboda yazama izna ga sauran wanda yaga zai daina ya daina wanda yaga kuma bazai daina ba, bismillah muna nan idon mu akan sa. "Wata takada ya ɗauko a envelope yazaro wata takardar yayi ƴan rubuce-rubuce, sannan ya miƙawa Sir Suraj yana cewa "ga wannan kayi singing. Sir Suraj karɓa yayi hannun sa na karkarwa yayin da zuciyar sa take dukan uku-uku, baisan takaddar mece ba, amma a haka yayi singing ya miƙa masa, sai ya ajiye ta ya ɗauki wata shima yayi singing ajiki ya miƙa masa yace; "takardar korar ka daga aiki ne, daga yau ka gama aiki muddin ƙarƙashin wani ne, domin yace duk makarantar da kaje sai yasa ankoreka, saidai kaje kayi kasuwanci... Miƙewa yayi cikin sauri, ransa yagama ɓaci, cikin jin haushin maganar sa, yace; "wannan wane irin shirme ne yaza ayi yara suyi min ƙazafi su dake ni kuma ku goyi bayan su dan rashin adalci, ni zaku kora a aiki wallahi baku isa ba, sai nasa duk an ɗaure ku sai kunyi da nasanin wannan abun da kukayi, kuma baku isa kun hanani ba zanci gaba da koyarwa kuma anan makarantar ko kuma in sa a ƙulle ta, gaba ɗaya, sai na jefe rayuwar ku cikin ƙunci, Dr. Aveed ne ya miƙe tsaye shima cikin ɓacin rai yace; "it's enough for you kar ka kuma wata maganar banza anan If not sainasa an ɓalɓallaka anan gurin, ka fice mana daga nan gurin duk abun da kake son yi kaje kayi bamason hauka anan gurin, Da sauri Sir Suraj ya ƙarasa gaban sa yana jifan sa da wani irin banzan kallo yace; "Ni nake hauka, zakaga hauka kuwa ganin idon sa, yana faɗar haka ya caƙumi kwalar rigar sa, yana ƙoƙarin fara dukan sa, sauran sukayi saurin rirriƙeshi suna son su janye sa baya amma yaƙi sakin sa, gurin ne ya kaure da hayaniya sosai, Sir Suraj sai zage zage yake kamar ɗan maguzawa, kana jin yanda yake zagin kasan ba tarbiyya a cikin ta, Beenish ce ta miƙe da sauri, sai ta miƙawa Aunty Babba hannu, Aunty Babba tasan me take nufi itama miƙewa tayi sannan suka taka zuwa inda suke babu wanda yasan da zuwan su, kawai tsugunnawa sukayi a ƙasa kamar zasu ɗau wani abu, a tare suka cafko ƙafafun sa kowa ya riƙe ɗaya, sannan suka ja su da ƙarfin su gaba ɗaya, yanda sukajawo sa babu wani musu dole ya bi inda ƙafafun sa sukayi, cikin tsoro baisan loƙacin da ya saki Dr. Aveed ba, jin ƙato kake timmmmm ya faɗi a ƙasa kansa ya bugu da sauri ya dafe kan dan yama kasa tantace a ina yake me ya faru dashi shidai kawai yajishi kansa kamar wani yummm kamar ba a duniyar yake ba. Duk sauran matsawa sukayi suna mamakin su, Aunty Babba ce tasa hannu ta ɗagosa tsaye tare da kaiwa fuskar sa wani lafiyayyen naushi a kuncin sa, take ta fasa masa, baki, duk da haka bata haƙura ba saida ta kuma naushin sa a ciki sannan tasaka ƙafa ta harbasa ya kuma faɗuwa ta kuma binsa da hannu ɗaha, ta kamo ƙafar sa, tafara jansa, babu wanda yayi yunƙurin dakatar da ita tunda kisan kai yake shirin yi, gwanda ayi masa haka, Fita tayi dashi daga gurin bata dena jan sa ba saida ta kaisa tsakiyar makarantar mutane da dama suka taru a wajen wasu na ɗaukan hoto, gaba ɗaya baya cikin hayyacin sa, ita kam ko ajikin ta, barin sa tayi a wajen ta juya zata bar wajen muryar da taji ne ya sa ta saurin da katawa tare da juyo da kanta cikin sauri, ai ita kanta bata san loƙacin da ta ƙarasa gurin ba, Yarinyar naganin ta nufota ta juya zata gudu saidai zafin naman Aunty Babba yafi nata, ba inda taje Aunty Babba ta cafko ta, ta baya, ta janyo ta tare da yin cilli da ita ta yardar da ita agefe, sannan tahau kan ruwan cikin ta, kawai fuskar ta kama ta ringa zuba mata maruka idan yarinyar ta buɗi baki zatayi ihu sai Aunty Babba ta zuba mata yawu a baki, haka taitayi mata tana ɗura mata yawu a baki, saida taga yarinyar ta daku iya dakuwa, sannan ta ɗagata ta kuma jefata kan Sir Suraj, tana watsa musu harara...... Dr. Aveed zama yayi akan kujera yana maida numfarfashi, Beenshi ce ta ɗau ruwan dake gabansa ta tsiyaya masa sanann, ta basa karɓa yayi shima ya hau sha, yana fara sha tunanin loƙacin da yabata shima ya faɗo masa, Bayan ya gama sha ya ɗan samu peace of mind sannan ya kalli ragowar tare da sallamar sauron aka tashi daga taron, Suma matan haɗa kai sukayi zasu fita suna daf da fita, sukajiyo muryar sa yana cewa; Thank you for save me, God bless you. Tsayawa sukayi batare da sunjuyo ba, su kace "Ameen sannan suka sa kai suka fita daga gurin zuciyoyin su cike da farin ciki da jin daɗin wannan maganar sosai sukaji daɗi gashi an ƙara musu ƙwarin gwiwa, "Wai Su waye su? Tambayar da ya kuma maimaitawa kansa kenan, saidai bashi da wanda zai basa amsa, haka ya ƙari zaman sa yana ta tunani, kafin ya tashi shima ya fita daga wajen. Suna fitowa sukaga abun da yake faruwa loƙacin Aunty Babba ta gama jibgar yarinyar da ta munafurce su badan Allah ya taimaka musu ba, da tuni yanzu ya jawo musu matsala, suna zuwa suka kamo hannun ya suka nufi motar su, suka shiga a ranar dai basu sami shiga lecture ba, Har suka fice muatane basu dena binsu da kallo ba. Rasa wanda zai taɓa su Sir Suraj akayi, sai security ne suka zo suka fita dasu, amma asibiti suka nufa dasu domin sai anyi treatment ɗin su, A falo duk suka zube suna sauke gajiyar da suka kwaso, gaba ɗayan su a matuƙar gajiya su ke, ga yunwa da suke ji. "Beenish ce tace; Baby ki ɗan dafa mana wani abun mana, kowa yunwa yake ji, Ɗan turo baki tayi cike da shagwaɓa tace; "yaya muyi order mana wallahi ko miƙewa tsaye bana sonyi, Allah nagaji. "Daman nasan bayi zakiyi ba, a haka kike so in kaiki gidan babyn to shi baya son mace malalaciya, wallahi idan baki zage ba yana dawowa duk zan gaya masa abun da kike zance ya canza wata wannan bata dace dashi ba sam..... Neman ta sukayi suka rasa a gun har ta shige kitchen ɗin saida ta shiga sannan tace; "kema fa kin san da wasa nake ni ba gajiyar danayi yanzu zanyi muku me daɗi ma kuma bani 30 minutes yanzu zan gama. Dariya suka ɗanyi, Ameela na cewa; wai yaushe zai dawo ne, naji shi shiru ko a online bana ganin sa, makaranta ta ɓoye sa. Beenish tace; "Ai jarrabawa suke idan suna jarrabawa baya hawa online munyi waya dashi shekaran jiya yace min nan da 2 weeks ko 3 zai dawo, "To Allah ya kaimu da rai da lafiya, kice mun kusa yin babban baƙo, cewar Aunty baba, tana miƙewa daga gurin tana cewa; "Auta bari in zo in taya ki kar aikin yayi miki yawa koh, Cikin jin daɗi tace "yauwa Babbar yaya wallahi kin fisu daman nasan bazaki barni ni kaɗai ba, loƙacin da take maganar loƙacin Aunty Babba ta ƙarasa shiga tana dariya, sannan suka hau aikin tare. Su kuma Barazance ta jawo system ɗin ta ta buɗe, aikin da sukeyi suka ɗora dayi ita da Beenish, Ameela kam baccin gajiya ne ya ɗauke ta a gun. *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *MEDUGURI....* 'Wata mata ce ƙatotuwa fara tas ƴar lukuta tana zaune a kan kujera kana ganin ta kasan kuɗi ne ke magana muguwar me kuɗi ce domin sirikar dake jikin ta da kuma da kuma ɗankunnen da danƙwaleliyar sarƙa da awarwaro duk na gold masu tsada sai kuma ƴar barimar hanci dake kan hancin ta itama ta gold ce, babu miyafi a jikin kawai ta kashe ɗauri tana hakimce kan kujera da jarida a hannun ta, sai kayan marmari dake gaban ta a yayyan ke tana duba news paper ɗin tana ɗaukar kayan marmarin tana sawa a baki. Wata budurwa ce ta shigo cikin tamfatsetsen falon tana sunkuyar da kai saida ta ƙarasa gaban ta ta zube a ƙasa tana gaishe ta amma yanda kasan ta gaida kujerar wajen haka tayi mata, saida ta ɗauki loƙaci metsawo bata ko kalli inda take ba, shiru matashiyar budurwar tayi tana jiran ta har tsawon loƙacin da zata ɗauka kafin tayi mata magana, "Are you a verging? Tambayar da ta watsawa budurwar kenan, da batayi tsammanin taba, Ita abun ma kunya ya bata cikin sunnar dakai murya ƙasa ƙasa tace "Eh" "Why kike son maida kanki haka, baki san me akeyi a gidannan ba kika kawo kanki? Cikin sanyin murya tace "Nasani. A jiye jaridar tayi tana kallon yariyar she is so calming. "Zaki iya tafiya bana harka da irin ku, ki bari indan kinyi aure kin fito zan iya karɓar ki, amma bana harka da irin ku, ki sani duk abun da kikayi sai anyiwa wanin ki, dan haka kiyi abun da in kinsan kinyi akayi miki bazai cutar dake da yawa ba, ina fatan kin fahimta, "Hajiya dan Allah kiyi haƙuri ki karɓe ni ni wallahi banda kowa nasan baza'a taɓa aura ta ba, nagaji da rayuwar shiyasa na zaɓawa kaina wannan kar kice haka wallahi daga guri me nisa aka kwatanta min gurin ki, Shiru matar tayi tana ci gaba da ƙarewa yarinyar kallo hakannan taji batason saka yarinyar a harkar, Ɗan numfasawa tayi, sannan tace zakiyi aiki a ƙarƙashina, sannan ki kula min da gidana, duk wanda zai zauna dani duk abun da yaga nayi kar yasake yasaka min baki indai bani nasaka da shi ba, sannan bana son sa'ido,gulma, munafurci, shiga abun da ba ruwanki, ko baƙo nayi ban yarda ko gaisuwa ta haɗa ku ba, idan muna tare duk wanda ya shigo inda nake ki tashi daga gurin batare da kin gaida shi ba, idan kikayi haka zamu zauna lafiya, duk wata zan ringa baki dubu ɗari biyar akwai wata tsohuwa a gidan tare zakuna aiki, ga ɗakin da take ciki can kije zata ƙarasa miki sauran bayani, tana gamawa ta miƙe cikin takun isa take takawa ta nufi hanyar fita daga falon. Tana fita daga gurin ta kuma faɗawa wani ɗaki dake kusa da falon, tana shiga ɗakin ta hango sa yayi ɗaiɗai a akan makeken gadon dake ɗakin, kallo ɗaya tayi masa ta ɗauke kai, bathroom ta shige bata daɗe ba ta fita, ta ƙarasa gaban madubi ta shiga gyara fuskar ta duk da kasan cewar babu abun da tayi amma saida ta kuma gyara ta ɗau turaruka ta kuma shafe jikin ta dashi ƙanshi ya cika ɗakin, gurin wardrobe ta nufa ta ɗauko mayafi da cover shoe ta maƙala a ƙafar ta ɗauki jakar ta, kyau iya kyau tayi sa kuɗi sun zauna, Hanyar waje ta nufa zata fita, da gudu ya sauko daga kan gadon ya tari gaban ta yana ta faman lullumshe ido yana kuma shaƙar ƙanshin turaren da tasaka, Wani mugun kallo ta watsa masa, tana cewa; "meye haka maye ka koma bana son irin wannan kasani, Please DANNAR ki taimaka min wallahi ina cikin wani hali, Allah ji nake kamar in mutu kidai cutar dani haka Please Dannar yafaɗa yana ƙoƙarin kamo hannun ta tayi saurin janyewa, tana nuna sa da yatsa tace; "RIMA, ka kiyaye ni ka fita daga ido na ko angaya maka na aure ka ne dan nabaka wani abu najiki na, ka manta contract ɗin da muka ƙulla kaci ka sha kai bacci babu ruwanka dani kuma zan fita zanyi sati guda kar kasa ke ka fita ko ƙofar gida, zaka iya kiran matar ka tazo nan ta sameka, Tana faɗar haka ta sa hannu ta janye sa gefe ta fice daga ɗakin, tana tafiya tana juyi tana taku ɗaiɗai, manyan mata na tafiya. Tana fitowa harabar gidan da gudu wani yazo ya buɗe mata mota amma sai ta tsaya, tana ya tsina fuska, tace; "Kai bakayi wanka ba bance maka zan fita ba, a haka kake son in fita dakai kana faman bugawa, dalla malam bani waje, kaje ka kirawo min Safwan, ko meyake yazo ya kaini airport. Da gudu ya nufi wani part ɗin dake cikin gidan, tana tsaye agun, kamar wajen 5 minutes sai gasu nan, shi a gaba yaron a baya, Cikin haɗe rai ya ƙaraso wajen yana kawar dakai gefe, ya haɗi girar sama da ƙasa, ko inda take bai kalla ba, ya shige gaban motar ya tayar da ita, yana jiran ta shiga, Ni kake so inbuɗe motar da kaina, batare da ya kalle ta ba, yace; "baga sani nan ba, "Kai nake so ka buɗe min in kuma ban isa ba sai ka gaya min, Gunguni yayi a ransa ya fito ya zagaya ya buɗe mata gaban motar, sannan ya koma ya shiga shima, sai loƙacin ta motsa daga inda take ta taka a hankali taje ta shiga saida ta shiga taja ƙofar ta rufe, Jan motar yayi me gadi ya buɗe musu suka fita daga gidan, Shiru babu wanda yacewa kowa wani abun, tsawon loƙacin kafin tace; Kayi waya da yayar ka yau? "Eh, "Me ta ce maka? "Meye naki a ciki? "Hmm kawai tace tare da sakin ɗan ƙaramin murmushi sannan ta kuma cewa, zanyi tafiya zanje London ɗauko wasu kaya zanyi kwana biyar a can daga can kuma zan wuce gurin yayar ka ka sanar da ita idan kunyi waya anjima, sannan ka kula da kyau banda yawon dare, nasamu sabuwar me aiki zatazo part ɗinka zata kula da kai kafin nadawo, nasaka maka 1 million a account ɗinka,

Chapter 11 of 44