Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma abun da suke yi dan samun hujja suma suna ciki sun ƙone, Ya daɗe agun yana kuka yana saƙa da warwara, da ƙyar ya iya miƙewa daga gun ya tashi gwiwayin sa duk a sake, yana tafiya hawaye na zubo masa, a haka yaje ya same su suna inda ya barsu ko kallon ta bai iyayi ba, ya kamo hannun ta kawai ya riƙe yarinyar tana ta tambayar sa amma ya kasa bata amsa, hakan yasa ta fahimci abun da yake nufi kuka kawai take yana janta bai hanata ba dan shima kukan yake haka suka ringa tafiya da su kansu basu san inda suke dosa ba... A gurguje.... Bayan shekara bakwai, acikin shekarun abubuwa sun faru da dama, saida suka samu nutsuwa daga inda suka baro take basa ƴar ƙaramar jakar tarkacen sa da yayi tunanin ta ƙone, ashe loƙacin da Kabeer ya sake ta ita kuma ta ɗauka, dake babu nutsuwa a tattare dashi yasa baiga jakar ba, saida suka sauka a wani gari yagani, a cikin shekaru bakwanan ya samu aiki a wani gari basu daɗe tare ba ya auri Fateema inda suka samu gidan su madaidai ci suke rayuwar su ga kuma cikin mutunta juna suna bawa jaririyar kulawa iya bakin ƙoƙarin su har ta girma, makaranta babu wacce batayi, duk wani nauyi da za'a saukewa yaro sunayi mata, babu abun da suka rage ta da shi, suna zaman kwanciyar hankali dan inba zama sukayi bama basa tuna rayuwar su ta da, sun tattara komai sun barwa Allah, saidai duk daɗewar nan Fateema bata haihu ba sai a wajen shekara shida ta samu ciki.... Watarana kwatsam saiga mutanen nan sun gano inda yake inda suka fara bibbiyar sa, saidai wannan karan ta ruwan sanyi suka biyo masa suna so ya basu, amma shima saboda yayi musu barazanar ko sun kashe shi abun yana hannun mutane da yawa kuma kashe shi ne zaisa asirin su ya ƙara tonuwa hakanne yasa suke binsu a hankali ba kamar shekarun baya ba, Saida daga baya dai da sukaga bashida niyar bayar da shi watarana yazo ya same shi a gida shi maɗai saida ya fara dukan sa sannan ya ɗaure sa yana tambayar tambayar sa ya basu yana zaune akan kujera a ƙulle. Fateema kuma da tsohon ciki ajikin ta, haka ta fito daga ɗaki da gudu, "Dan Allah...! Dan Allah,Dan Annabi ku taimaka kuyi haƙuri kar ku kashe shi na roƙeku, kada kuyi haka, ku rabu damu namuku alƙawari zan sashi yabaku duk abun da kuke nema amma dan Allah ku rabu dashi ko inhelar ce ku taimaka ku bari ya sha idan numfashin nashi ya daidai ta sai kuyi magana, sai roƙonsu take ga tsohon ciki ajikin ta amma duk ta fita a hayyacin ta ganin me gidan nata yana shirin barin duniyar. Da haka ta kuma rarrafawa taje gaban su tare da dafa ƙarfar mutum da taga yana shirin kunna sigari, kallon ta yayi ta ƙasan ido tare da ɗaga ƙafar sa saida ya saita daidai cikin ta sannan ya turata ta faɗi ta bayan tare da sakin wata mahaukaciyar ƙara saboda azabar da taji ta a ƙasan marar ta, Hankalin sa ya mayar kan mutumin dake ɗaure ajikin kujera yana ta fusge fusgen yanda zai kwace daga ɗauren musamman da yaga yanda yayiwa matar sa, hawaye ne kawai yake gangaro masa daga cikin idanun sa, idan ya yunƙura yaga ya kasa sai ga koma tare da ci gaba da kuka me ciwo, ga numfashi sa da ya dawo ƙirji yana shirin ɗaukewa idanun sa sun kaɗa sunyi ja shi kaɗai yasan halin da yake ciki, Gashin kansa yakamo ya ɗago dashi, sigarin da ya kunna ga zuƙa tare da hura masa hayaƙin a daidai saitin hancin sa, nan da nan kwa yayi wata ɗauke gaba ɗaya sannan ya kuma kawowa cikin mawuyacin hali, Da sauri ta kuma yunƙurawa zata tashi tana sakin kuka me ƙarfi amma bata kai ga ƙarasawa ba ya kuma turata baya ta faɗi tare da bugewa da jikin kujera nan itama ta ɗauke bata kuma motsawa ba, ko kallon inda take beyi ba, ya ci gaba da abun da yake yana zuƙu sigarin sa yana busawa Shu'aibu duk dauriyar sa dole yakasa komai yanaji yana gani babu ƙarfin ƙwatar kansa, tun yana gani bibbiyu ya dawo ganin dishi dishi kansa yana lanƙwashewa sai ya kuma yin ƙarfin hali ya buɗe su amma sai su ƙara rufewa saboda sunyi masa nauyi ga numfashin sa saura ƙiris ya ɗauke, girgiza wa ƴar su kai yake alamun kar ta fito daga inda take a ɓoye, sai kuka take a hankali dan tunda yaji sune yace ta tsaya ko me zata gani kar tayi kuka kuma kar ta fito in ba hakaba kuwa zasu kashe ta, hakan yasa taji tsoro taƙi fitowa daga gurin..... Mutumin ne ga kuma busa masa sigarin a hanci sannan yasa hannu ya toshe masa hanci bai saki ba saida yaga ya dai na numfashi, Wani ƙaton ƙarfe yarinyar ta ɗauko da Shu'aibu yake fita dashi, idan zasuyi aikin saran nama, lallabowa tayi ta dage iya ƙarfin ta ta buga masa akai nan take kuwa shima ya faɗi a ƙasa ya suma, Hannun ta na karkarwa ta saki abun ta koma kansa ta shiga girgiza sa tana kuka tana kiran sa, "BEENISH..! Da sauri ta juya gurin ta ganin ta farfaɗo yasa ta tashi da sauri ta koma kusa da ita tana kuka tace Umma Baba ya mutu kice masa ya tashi, dan Allah kar ya mutu ya barmu, yunƙurawa tayi ta tashi da ƙyar tana dafe kanta da yake mata ciwo, sai loƙacin idon ta ya sauka akan mutumin dake kwance bata san loƙacin da ta tashi ba tana kallon yarinyar tace Beenish me kikayi masa, tashi mu gudu idan ya tashi muma kashe mu zaiyi, Suna kuka gashi suna kallon sa amma babu yanda suka iya, dole ta shiga ɗaki ta ɗauko duk abun da zata ɗauka cikin sauri ta kamata suka bar gidan.. Mota ta tarar musu suka ma bar garin gaba ɗaya, suna zuwa kuma asibiti kawai ta tambaya dan tana jin cikin ta na muraɗawa kamar naƙuda, suna zuwa kuwa akace mata ai tanama daf da haihuwa, karɓar ta akayi tayi duk wani ciki ciki da zatayi aka shiga labour room da ita, Bata ɗau loƙaci ba ta haifi santaleliyar ƴarta mace, saida aka kaita ɗakin hutu sannan aka kai mata yarinyar da ta bada ajiya, kwanan su uku aka sallame su saidai basu san inda zasu dosa ba, a cikin garin suka ringa yawo da taga kuɗin gurin ta sun kusa ƙarewa sai kawai ta fara bin gida gida neman aiki, nan kwa ta samu wani gida, ta haɗa su da Allah zata zauna da ƴarta itama sai su bata wani aikin, anan suka ci gaba rayuwa tsawon shekara ɗaya, suna zaman su wani yayi musu sharrin Beenish ta ɗaukar masa kuɗi nan kwa akayi musu cin mutunci a ka kore su daga gidan, Wajen wata me saida abinci ta kuma samo musu, suka farayi, agurin tana cikin wanke wanke watarana taga wata mota ta tsaya a gaban wajen tare da sauke glass sai taga ana nunata, tashe tayi da sauri ta shiga cikin gurin yaranta da ta bari suna wasa taje, zanin goyon ta ta ɗauka sai tayi sauri tace "Beenish tashi yi sauri maza miƙewa tayi tana tambayar lafiya taga duk ta tsure haka, shiru tayi mata cikin sauri ta ɗauki Haneefa shine sunan yarinyar da ta haifa wacce kuka fi sani da Babyn baby..... Goya mata ita tayi ta ɗaure ta sosai, sannan ta jawo ta wani lungu tace ku tsaya anan duk abun da zaki gani kar ki sake kiyi magana, kuma kar ki fito nagaya miki.... Tana gama faɗa musu haka ta juya tana fitowa fili kuwa taci karo da mutane a gaban ta daman tun ɗazu suke neman ta suna ganin ta kuwa suka dannan mata farin ƙyalle sukayi gaba da ita tare da danna ta cikin mota.. Kuka me ƙarfi ta fashi dashi tana toshe bakin ta tace tundaga ranar ban kuma ganin su ba ban kuma fita ma waje ba kullum ina ƙulle, anan gurin na barsu bansan wane hali zasu kasance ba da masani bance ta tsaya anan ba, yanzu nasan suma sun kashe su yaran da basuji ba basu gani ba, sosai take kuka tunawa da abubuwa da tayi, shima taya ta yake babu me rarrashin wani..........✍️✍️✍️ Ni zanzo na rarrashe ku🤣😅 [3/5, 12:12 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) ______________________________ *_episode 28💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bismillah....✍️ *Five star ⭐* ___Suna zaune a falo sukaji anayi musu bugun hauka, kallo kallon suka shiga yiwa suna mamakin wanda keyi musu bugun dan sun san sude basu da wani wanda zai shigo musu gida, Aunty Babba ce tace "waye ne haka, ta faɗa tana miƙewa tsaye, tare da nufar wajen ƙofar, Leƙawa ta farayi ta wata jikin wata ƴar ƙofa, da saura ta juyo tana kallon su, suma kuma duk sun zuba mata ido suna jiran suji me zatace, a hankali tace "Soldiers! Duk miƙewa sukayi ko wacce da gudu ta shiga wawuro abun da zata kare kanta wasu suka shiga kitchen suka ɗauko wuƙa, wasu kuma muciya, harda ne fork spoon, a yanda suke da shigar su nan babu wanda ya sauya kaya, zuwa sukayi suka jeru a bakin ƙofar duk suka yi ready jira suke kawai Aunty Babba ta buɗe, tana buɗewa itama taja da baya baya ta dunƙulle hannun ta tana tala ƙafa, turo ƙofar akayi, ana turowa kuwa wanda ya fara sako ƙafar sa duk suka kai masa duka, da sauri akaja shi ta baya aka mayar dashi gefe, ƙafa ɗaya ya ziro da taci uban takalmin sa na sojoji me tudu, shima dukan suka so kai masa, har suna ɗaga zasu sauke masa, sukayi saurin dakatawa, suna janye hannunwan su, ɗayar ƙafar ya ziro tare da saka ƙafa ya tura Beenish dake gaban sa, nan kwa ta faɗi wuƙar hannun ta, ta faɗi gefe, Babyn baby ce ta shiga fesa masa abun hannun ta saidai ko gezau beyi ba saboda ya saka glass itama damƙo ta yayi ya jefata gefe, a tare sauran sukayi kansu, amma tun kan su matso inda yake yasa ƙafa duk ya tura su babu wacce bata faɗi ba kuma babu wacce bataji jiki ba, Shigowa yayi gaba ɗayan sa sannan ya zare glass ɗin sa ya shiga kallon su ɗaya bayan ɗaya, idon sa akan Beenish ya tsaya saidai suna haɗa ido ta galla masa harara tana shirin miƙewa yasa ƙafa ya kuma buga ta saida ta matsa daga inda take, ƙara ta saki bata san loƙacin da bakin ta ya furta Allah ya isa ba, a fusace ya kalle ta zai kuma yin kanta, sai kuma ya tsaya tare da saurin kawar da idon, sakamakon ganin rigar ta ta yaye sai santala santala cinyoyin ta da suka fito saboda daman rigar iya gwiwa ce shiyasa da ya bugata sai ta ɗaga, Sauran sojojin ne suka shiga shigowa duk suka zagaye su kowa ya tsaya akan kowacce yanda babu damar su tashi. Kallon su ya shiga yi, idon sa ya sauka akan wani soja da yaga idon sa ta kalli waje ɗaya bin idon nasa yayi yaga inda yake kalla, taku ɗaya yayi yaje gaban sa, yana zuwa kuwa ga kwashe shi da wani lafiyayyen mari, gaba ɗaya gurin saida suka tsorata, su kansu su Ameela duk saida suka dafe kumatun su dan ji sukayi kamar su aka mara, "Get out from here..! Sum Sum Sum ya fice hannun sa dafe da fuskar sa, yana cewa "Sorry Sir" a haka ya fice daga falon... Sauran kuwa gudun suma kar hakan ta faru dasu duk suka shiga hankalin su tare da sunkuyar da kawunan su babu wanda ya kuma kallon wata ma bare su kallowa kansu wani abun.... Juyawa yayi ya kalle ta ya kuma maida kallon sa kan cinyoyin nata a karo na biyu da yaga har yanzu bata rufe ba... Ganin inda ya kalla yasa ta saurin jan rigar ta batasan loƙacin da ta miƙe tsaye ba, bakin ta ne ya fara motsi alamar gunguni, tana ɗagowa taga kallon da yake binta da shi, kamar zai kamo ta, kawai sai ta saki tsaki, tana aika masa da harara, saboda duk ji tayi haushi ya kamata wayasan tunloƙacin ma da rigar ta yaye amma bazai ce ta gyara ba saboda iskan ci zai tsaya yana kallon ta, hakan yasa ta kuma sakin tsaki batare da tasan tayi ba, A fusace yayi kanta zai kamo ta ganin hakan tsoro ya kamata bata san loƙacin da ta kwasa a guje ba tayi wani ɗaki dake gefen ta, saidai kafin ta rufe yayi saurin saka ƙafar sa a bakin ƙofar, idon sa ya watsa mata da yasa ta fara jin tsoron sa, ganin yanda ya haɗe fuska yana binta da mugun kallo yasa taji jikin ta na ɓari, da baya da baya ta fara ja tana girgiza kai cikin tsoro tace nifa badakai nake ba, da wancen shegen nake wanda naga yana kallon kaga kai kuma baka kalle ni ba shiyasa nace badai nake ba Allah ka yarda dani.... Duk abun da take bai motsa daga inda yake ba sai kallon up and down da yake binta da shi, cikin ɓacin, me take nufi da shegen da yake kallon ta to waye ya kalle ta in bashi ba, shine shege kenan.... Takawa ya fara yi yana shiga cikin ɗakin, ganin ya fara shiga yasa su Aunty Babba duk suka miƙe suna shirin zuwa wajen, sojojin duk sukayi saurin tare su, suka hanasu damar motsawa ma bare su kai da zuwa can, Tana ganin ya fara takowa ta kuma tsorata jikin ta har karkarwa yake ita kanta mamaki take yanda ta tsorata haka duk irin damben da suke da mutane to ya akai shi zai gagare su kuma har take jin tsoron sa harda rawar jiki, nufar ta kawai yake ita kuma tana kuma ja da baya, tana yayyarfa hannu, haka suka shiga taku tana ɗaga ƙafar ta zai ɗora tasa akai jira yake yaga iya gudun ruwan ta, aikwa dai tana zuwa jikin bango ta tsaya, tana kuma tunanin yanda zatayi, a gaban ta ya tsaya tare da zaro wata ƴar ƙaramar bindiga, Beenish na gani jikin ta ya kuma ɗaukan ɓari, Ɗora bindigar yayi akan goshin ta, da sauri ta rufe ido abun mamaki sai kawai hawaye suka shiga gangaro mata bata san sanda suka taru ba har suka kai ga saukowa... Tsayawa yayi kallon ta ganin yanda tayi sai kawai ya kuma mayar da kan bindigar kan wuyan ta yana ɗan motsi da ita kamar irin saita ta yake zai harbe ta, da sauri ta buɗe idon ta tana buɗewa suka haɗa ido, sai ta tsaya bata janye ba, ta gefen ido take kallon sa, cikin aro jarumta da dauriya, ta faki idon sa ta gefe tayi saurin ƙwace bindigar tare da ɗaga ƙafarta ta kaiwa ƙasan wandon sa duka, tare sa tura sa da ƙarfi, nan kwa yayi baya amma ba sosai ba, da sauri tayi gefe tana nuna sa da bindigar tace idan ka kuma yin wani yunƙuri sai na harbe ka anan gurin, bil haƙi da gaske yake, sai wani zazzaro ido take, tana jujjuya bindigar tana saita ta, saki kawai ya rage tayi dan har dannawa tayi tana saki bullet zai fita. Naɗe hannun rigar sa ya shigayi dan shi kaɗai yasan irin hukuncin da zai yi mata saboda tunda yake ko namiji babu wanda ya taɓa yi masa abun da tayi masa, duk da yanajin zafin dukar masa alulu da tayi amma yayi jarumta ya dake kamar baiji dukan ba, nufar ta ya kuma yi, yaga me zatayi ɗin, Ja da baya ta kumayi duk da ga bindigar a hannun ta amma saida ta kuma tsorata saboda yanda taga yanayin sa ya kuma sauyawa, kamar ba mutum ba, Ganin da gaske dai kamata zaiyi batasan loƙacin da ta saki harbin ba, saidai kuma iska ce kawai ta fito saboda ba bullet ko ɗaya a ciki, Zaro ido tayi cikin sauri kuwa ta jefa masa bindigar zata gudu taku biyu yayi ta cafko ta, gashin kanta ya damƙo sannan ya jefata gefe ta faɗi nan kwa ta saki ƙara ƙarfin hali ta kumayi ta miƙe ya kuma mayar da ita da ƙafa, zata tashi yasa ƙasan takalmin sa ya danne mata hannu, take ta kuma sakin ihun azaba, "wayyo Allah hannuna... Daga waje su Ameela suka jiyo ihun ta ai duk yanda sojojin nan su so hana su saida suka yi yanda sukayi suka ƙwace daga gurin su duk suka nufin cikin ɗakin, suma sojojin binsu sukayi cikin sauri duk a kusan tare suka shiga ɗakin, loƙacin da suka shiga shi kuma RK ya caƙumo wuyan rigar ta ya ɗago ta tsaye, naushin ya kaima ta tayi saurin tsugunnawa ya daki iska, sai kawai yasa ƙafa ya kuma jefata gefe, a dadai wajen suka ƙarasa gaban sa, saidai basuyi yunƙurin yin komai ba sojojin suka yi ram da su duk suka kame su, suka fara jansu zasu fita dasu amma sunƙi basu haɗin kan fitar... Duk da haka bai haƙura ya kuma tunkarar ta ya kuma yin ball da ita daga inda take sai da ta kusan shigewa ƙarƙashin gado, sosai ya jigata ta, saida ta dawo tayi laushi ko motsi me kyau batayi sannan yajawo gashin kanta da haka ya ringa janta har ya fito da ita wajen falon nasu, inda sauran ma suke, sun tsaya ne kawai saboda bindigar da aka nuna musu ance duk wanda ya motsa daga gurin sai sun harbe sa, hakan yasa suka kasa komai, Karɓar bindigar hannun wani sojan yayi ya samu waje kan kujera ya zauna, duk da haka Beenish na riƙe a hannun sa, saida ya zauna sannan ya sake ta tare da nuna mata inda zata tsugunna ba musu kuwa ta tsugunna san jikin ta gaba ɗaya ciwo yake mata.. "Ku bincike mana ko ina! Nan sauran sojojin suka fara shishshiga ɗaki ɗaki suna bincike gidan, shi kuma yana zaune dasu a falon yasaka musu bindiga duk wanda yayi ƙwaƙƙwaran motsi sai ya harbe sa, hakan kwa yasa duk suka kasa motsi.... Saida suka gama caje gidan tsaf sannan suka fito suka ce basu samu komai ba, da ya danganci kayen maye, saidai kuma kuɗaden da suka gani waɗanda Dannar ta bawa Ameela, Karɓa yayi ya ajiye su a gefen sa, batare da ya kalli inda take ba yace; "Get up and put on your clothes, Ƙin motsawa tayi, hasali ma yi tayi kamar batasan da iya yake ba, "Don't let me repeat it again" Cikin rashin jin daɗin jikin ta ta miƙe da kyar take iya takawa zuwa ɗakin su, tana shiga taga yanda suka hargitsa musu ɗaki tsaki taja a ranta tana mamakin yanda sojoji suke da mugun ta gaba ɗayan su mugaye ne, guri ta samu ta zauna da niyar babu inda zata ta shigo kenan, kwanciya kawai tayi akan gadon tana ƙara tunanin yanda ya ringa ball da ita, dan haka ta barwa ranta abun da zatayi masa dan sai ta rama cin mutun cin da yayi mata, sai yayi da nasanin dukan da yayi mata dan wallahi bai daki banza ba sai ta rama.... Tana kwance agun tana ta saƙe saƙen abun da zatayi masa, sai kawai ji tayi ambanko ƙofar da ƙarfi, a tsorace ta tashi tana kallon gurin kuwa suka haɗa ido da shi batasan loƙacin da ga diro daga kan gadon ba, tsayawa yayi a bakin ƙofar yana aika mata kallo me cike da gargaɗi, Turo baki tayi tana sake yin gunguni magana ciki ciki ta nufi wajen wardrobe ɗin su, buɗe tata tayi sai ta zaro riga me haɗe da hijabi ganin yana gurin kuma bazata ta taɓa ce masa ya matsa ya bata guri ba kar taje ya kuma kammala ta, kawai sai ta ɗora ta akan rigar jikin ta ta saka hijabin, ko ɗaure sa batayi ba, tana juyowa taga baya gurin ma, wata zuciyar ce tace kiyi zaman ki wallahi kar ki fita ko ina, wata kuma tace kin manta waye shi kenan, ai da sauri ta fito daga ɗakin, ashe gwanda da Allah ya taimake ta ta fito saboda yana bakin ƙofar fita yayi daman dan gabata guri ta saka kayan, tana fitowa ya daki kanta yana turata, gadan gadan ta tafi zata faɗa kan wani glass da sauri ya jawo hannun ta ya tsayar da ita, tana tsaya kuma ya ci gaba da tura ta, tayi tunanin a falo zasu tsaya, sai taga yaci gaba da tura kanta hanyar waje, sunaji suna gani ya fita da ita daga falon, saida suka fita sannan sojojin suka sake su, suka bi bayan su, suma da sauri duk sukayi wajen... Babyn baby sai kuma take tana "cewa ina zasu kai ta, kunga fa zai tafi da ita muyi wani abun, kar mu bari ya tafi da ita kashe ta zasuyi, dan Allah kar ku kashe ta ita kaɗai ta rage min a duniyar na kar ku tafi da ita, itace uwata itace ubana, itace komai nawa, Aunty Babba kunga fa ya saka ta a mota dan Allah ku tayani roƙon sa gwanda su ajiye ta ni su kashe ni, gaba ɗaya ta fita hayyacin ta daman tunda taga yana dukan ta take kuka, amma ganin za'a tafi da ita ne yasa kukan yanzu yafi na farko.... Da gudu taje wajen motar tana ƙara roƙon sa, amma ko inda take bai kalla ba, sai ma sawa da yayi aka janye ta daga gurin motar sannan yasa drivern yaja motar suka nufi hanyar fita, Dukan su babu wanda bai zubar da ƙwalla ba da suka fita daga gurin ga kukan da Babyn baby take yafi ɗaga musu hankali, sun haɗu sai rarrashin ta suke duk da suma hawayen suke..... *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *RABI* ___Su uku ne a zaune a wani falo, ita da wasu maza guda biyu, Kallon wani mutum tayi da ƙasumba ta cika masa fuska rabin ta kuma duk fara ce, girar sa ma ta kusa haɗewa saboda yawan ta, kana ganin sa kaga kallar mugaye, ya harɗe hannu wansa akan ƙirjin sa, yana binta da kallo saida yaji tayi shiru da maganar ta sannan yace; "wannan matsalar kice tsakanin ki da ita sauran ya kamata kije ki nemo ni banda dill akan ta, loƙacin da kukayi baki sanar dani ba munafurtata ma kika yi baki sanar dani kina aiki a ƙarƙashin su ba, dan haka babu wani abu da zan iya yi miki akan ta, matsala ta guda ɗaya ce da kika ce Maryam na raye har yanzu itace dole zanyi wani abu akai amma Dannar babu matsala ta da ita, Maryam kuma indai a duniyar nan take bazata min wuyar gano inda take ba, bare ma kince zata kawo miki ziya a karo na biyu to yanda akabi aka kawar da ita wancen loƙacin to yanzu zamu sake shiri sosai ta yanda in

Chapter 23 of 44