Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tashin hankali Bilal ya shiga gaban ta, hawaye har ya fara cika masa ido yace, dan Allah ki faɗa mana gaskiya me mukayi miki me yasa kika kawo mu nan, ko ba kidnapping ɗinmi kikayi ba amma meye dalilin ki na kawo mu nan, kin rabamu da kowa namu, duk da bakya musguna mana kina bamu kulawa yanda ya kamata amma meye dalili, suma kuma waɗannan su waye su da suke cewa sato su kikayi? Wani banza kallo Hajja Mama ta kuma watsa masa tana ya tsina fuska, tace; "ni ba kidnapping ɗinku nayi ba dan babu abun da zanyi da kuɗaɗen ku, kai ka taɓa ganin anyi kidnapping ɗin mutum kuma ambarsa haka, dan haka idan zaku kwantar da hankalin ku ku cigaba da zama ku kwantar idan kuma bazaku kwantar ba ku cigaba da ɗagawa kanku hankali dan babu me fita daga nan gurin, matsa min, bani hanya in wuce, sannan duk wanda yayi yunƙurin fita daga falon nan ma, sai ya ziyar ci lahira kana saka ƙafar ka awaje to ku sani kamar ka jefa kanka cikin kabarin kane, dan babu abun da zai hanani kashe mutum, kana mutuwa kuma zamu bawa karnuka gawar ka, dan haka duk wanda ya shirya mutuwa a cikin ku ya iya fitowa yanzu ma basai anjima ba. Tana kaiwa nan tayi ficewar ta..., Duk saranda sukayi babu me ƙwaƙƙwaran motsi, dan sunma rasa abun cewa, musamman Bilal da Zaida su jin sune ma ya bar gangar jikin su, dan jin abun suke kamar almara kamar ba gaske ba, basu taɓa tunanin hakan daga gare ta ba. Faheema ce ta samu damar cewa; "daman wannan matar daga ganin ta bazatayi mutunci ba kana ganin ta kasan muguwa ce, kuma wallahi kidnaper ce ita, ni da har cikin gidan mu taje ta ɗauko ni. Da sauri Zaid ya ƙarasa gaban su cike da rashin kwanciyar hankali, yace "dan Allah da gaske kike to taya ta ɗauko ku, nidai bada haka ta ɗauko ni ba, wasu ne suka biyo ni ta taimake ni tundaga nan kuma ban sake sanin inda nake ba, sai anan gidan, kuma tace min zata mayar damu ai tana tsoron mu fita ne mutanen da suka biyo ni su kashe ni, shiyasa take son na zauna anan zuwa wani loƙaci, ashe duk ƙarya take min. Ɗayar ce ta kalle sa tace "haka take yi dan nima kusan hakan tayi mun, muna tafiya ta sa aka ɗauko ni, dan Saida suka fara ƙwace min mota ma sannan ta sa aka ɗauko ni, mu biyu muke tafiya da ƙawata amma ni kaɗai suka ɗauka, dan sunga mahaifiya ta tana da kuɗi shiyasa ɗayar kuma da suka san babu abun da zasu samu idan sun sato ta ai basu ɗauko har ita ba... "Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un kawai Bilal yake maimatawa ƙafafun sane suka shiga rawa da sauri ya zauna agun danji yake yana shirin faɗuwa ƙafafun sa bazasu ɗauke sa ba, take shima ya shiga tunanin yanda ta ɗauko sa daga cewa zata taimaka masa ta fito da shi daga rufewar da ƴan matan nan sukayi masa tana fito da shi tasaka sa a mota da sunan zata kai sa gida, shima dai kuma daga haka dai farkawa yayi ya gansa a gidan koda ya tashi ya tambaye ta sai cewa tayi ai bacci yayi suna tafiya ta tashe shi yaƙi tashi da har zata sauke sa saiga wasu nan sun biyo su suna cewa ta basu yaron dake cikin motar ta ta, hakan yasa ta tayar da motar da gudu har ta ɓacewa masu binsu shiyasa kawai ta kawo sa gidan ta, amma sunyi waya da mahaifin sa yace zaizo ya ɗauke sa ta ajiye sa agun ta har sai yazo kar ta bari ya fito saboda mutanen da suke neman sa kashe sa zasuyi, shiyasa ya tsorata sosai da abun da kunnuwan sa suka jiyo masa.... *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *COMMISSIONANER* Tun ranar da abun ya faru aka ji masa ciwo a ƙafa hakan yasa ya zame da ƙyar ya sha zuwa gida,, dan harda saran wuƙa a gefen hannun sa, hakan yasa shi zaman jinya a gida, koda ya fara jin sauƙi baiyi gaggawar fitowa ba, gashi wayar sa ta faɗi a gun so yake ya nemi Magana ɗaya suyi magana da shi akan batun ƴan matan da shi har yanzu ƙidurin sa yana nan na ɗaukar fansa akan ƴan matan musamman yanzu da suka sake yi masa illa ta sanadin su, gashi kuma sun haye ba tare da komai ya same su ba, shiyasa yake so ya sake shiri na musamman akan su, dan alƙawari ya ɗaukar wa kansa sai ya tarwatsa rayuwar su gaba ɗaya... Tun safe ya tashi ya fara shirin fita aiki, yayi shirin sa tsaf, yana shirin fita daga ɗakin matar sa ta shigo ɗakin bakin ta ɗauke da sallama amma kana ganin yanayin ta kasan ba lafiya ba. Tsayawa yayi yana kallon ta tare da cewa "lafiya kuma me ya faru naga yanayin ki haka, takardar dake hannun sa ta miƙo masa, cike da damuwa tace; "sun ce na baka sannan kuma wai awa 24 da huɗu suka baka. Karɓa yayi ya shiga warware ta, a razane ya ɗago ya kalle ta yana zaro ido kamar zasu faɗi ƙasa, sakin takardar yayi a hankali yana kuma binta daɓas ya zauna a ƙasa, a hankali ya fara furta Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un, ya furta ta tafi sau biyar hular dake kansa ya zare ya ajiye ta gefe, take gumi ya shiga tsatstsafo masa ta ko ina sai muzurai yake da idanu yana rarraba ido. Matar ce ta ɗauki takardar itama karantawa tayi tana gama karantawa ta ɗora hannu akai "na shiga uku, Abban su me kayi haka wane laifin ka aika ta aka kore ka daga aiki, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un ina zamu shiga idan suka kore mu daga gidan nan ina zamu koma mun shiga uku Abban su kayi wani abun mana ka tashi kaje ka basu haƙuri kar su kore ka, basu san baka da lafiya bane baka basu san da hutun da ka ɗauka da dalili ba, me yasa zasu kore ka saboda rashin imani ma da tausayi kana zaune kana jinyar babu wansa yazo ya dubaka, sai ranar da kake shirin komawa, za'a wani aiko maka da takardar dakatar da aiki me yasa ma baza su bari kaje can gurin nasu ba, sai kawai ayims aike saboda rashin ɗaukar ka da muhimmanc..... A zafafe ya miƙe tsaye cikin daka mata tsawa yace "ke Malama kimin shiru haka, ya isa haka! Cikin sauri ya hau cire kayan aikin nasa ya sanya na gida, a cikin minti da baifi ɗaya ba zuwa biyu ya gama shiryawa ko kallon inda take bai kuma yi ba ya fita fuuuu... binsa kawai take da ido bata kuma gigin yi masa wata maganar ba....., *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *LAUTAI* Khalifa da ya fito daga gidan, can gida ya koma, Allah ya taimake sa babu kowa a gidan dan haka yana shiga shiryawa yayi ya ɗauki duk abun da zai ɗauka, ya kuma fita daga cikin gidan cikin sauri, dole ya bar motar sa a gida saboda baisan garin ba dole saidai yayi tambaya yaje tasha ya hau motar haya, saida ya sake komawa gidan da ya ajiye Fateema ya tambaye ta garin sannan ya kuma fita. Tasha yaje ya hau motar Kano a daren, basu suka sauka ba sai wajen ƙarfe, biyar na safe loƙacin anata sallah, baisan ko ina ba baisan kowa ba, haka ya zauna a masallacin da su kayi sallahr, sai da gari ya fara haske sannan ya fito da tambaya ya kuma samun inda zaije ya hau motar garin da zaije, ko karyawa bai tsaya yayi ba ya kuma tarar wata ya hau kai tsaye aka wuce garin Lautai da shi, bayan sallar azhar suka sauka, nan ma dai saida ya sha wahala kafin ya samu ma aka kula sa, da ƙyar ya samu aka kaisa wani gida, saida da ya ɗan fara bayani sai aka ce masa ba gidan bane, nan yaci gaba da tambaya amma bai samu ba, har wajen ƙarfe huɗu yana garari bai samu inda aka sanshi ba, Masallaci yaje yayi sallah la'asar, yunwa ce ta fara damun sa hakan yasa ya fara neman abun da zaici, yaga ana siyar da abincin siyar wa amma bayajin zai iya ci, wata ƴar kasuwa ya ƙarasa inda yaga ana siyar da abubuwa da yawa, nan ya samu ya siyi gurasa kawai ya samu guri yaci, ya sha ruwa, Tunani mafita ya farayi dan ya cire rai kuma baya so ya koma gida ba tare da ya samu labari ba, ganin yamma nayi masa yasa ya kuma tashi har zai koma cikin garin sai yaji ƴan acaɓa na cewa "Lautai ta biyu, kai ƴan mata ina zaku? Kuzo ku hau mu tafi. Tsayawa yayi yana kallon masu mashinan, nan dai yaji suna ta cewa Lautai ta biyu sai kawai tunanin sa ya basa ko ya gwada zuwa indai har akwai wata Lautai ɗin to ai inajin ma ita ce, kenan wannan ta ɗaya ce waceen ta biyu, tunawa kuma da maganar da tayi masa bata san garin ba kawai sunan sa ta sani zai iya yiyuwa kenan bai gaya mata ta farko ba ko ta biyu. hankalin sa ne ya kwanta da hakan da yaje kawai ya gwada zuwa can ɗin ko zai dace. Juya akalar sa yayi ga zuwa wajen ƴan mashinan, yana zuwa suka ce "Malam ina za'a kai ka? "Lautai ta biyu. Nan ya hau mashin ɗin mai mashin ɗin yaja suka tafi, saida sukayi tafiya sosai sannan ɗan acaɓan yace "malam wace unguwar zaka sauka? "Wallahi ni baƙo ne bansan ko ina ba wani gida de nake nema idan ka sani sai ka kaini, gidan Ali Bashir yana da ɗa Shu'aibu. Shiru ɗan azaɓan yayi yana tunani, sai can dai yace "gaskiya bansani ba saidai ko in tambaya zamuyi, nan suka fara tambayar mutane wasu suna cewa basu sani ba, daga ƙarshe dai da me mashin ya gaji sai yace bari inkai ka gidan me gari in yaso sai yaba da cigiyar sa ko acan cikin gari yake, ko kuma shi yasan shi, da to ya bishi kawai dan bashi da zaɓin da ya wuce hakan. Nan ya kai sa gidan me gari ya sallame sa ya juya, da ƴar jakar sa ya ƙarasa wajen mutanen dake wajen, yayi musu sallama daga haka ya faɗa musu gurin me gari yazo nan akai mishi iso har gaban sa. Bayan sun gaisa ya sanar da shi abun dake tafe dashi, take kuwa wani dake gefen me gari yace "ai ɗan nasa ya mutu ko? wanda yake aiki a Kano daga ƙarshe kuma yayi aure bayan auren nasu aka kashe shi shi da matar da ƴar su guda ɗaya koh. Cike da jin daɗi Khalifa yace "Eh...Eh. shine kuwa. Nan ƴan gurin na suka fara ɗaukar maganar kowa ma ya gane wanda ake magana, sai da suka gama kace nace ɗin su, sannan me gari ya kalle sa ya ce; "yaro saidai gaskiya wanda kake nema ya daɗe da barin garin nan kuma babu wanda yasan inda ya koma, amma yanzu dai za'a raka ka gidan ɗan sa akwai ɗan sa guda ɗaya da ya rage again nan, za'a raka ka inyaso daga nan sai su faɗa maka inda yake, ina fatan dai lafiya ko? Khalifa yaji daɗi baiji daɗi ba, da sauri yace "Ehh lafiya ƙalau. "To...To Masha Allah bari ayi sallah sai a raka ka ko? "To nagode" Bayan anyi sallar magriba aka raka sa gidan, saida suka tura yaro yayo musu sallama da Malam. Tare suka fito da yaron, nan yaron ya tafi, shima wanda ya rako sa ya juya ya tafi cike da rashin sanin juna, Khalifa ya gaida shi. Da fara'ar sa ya amsa sannan yace "yaro mu shiga daga ciki mana Bama tsaya anan ba ko. Iso yayi masa zuwa cikin gidan, suna shiga ya ɗaga murya, ya ce; "Kubra kawo mana tabar ma munyi baƙo! Daga can cikin ɗaki ita ma ta ɗaga murya tace "To ganin nan! Ba jimawa ta fito daga ɗakin hannun ta ɗauke da tabarmar, in duka ta shinfiɗa musu, suka zauna, itama zama tayi daga ɗan gefe suka gaisa da baƙon sannan ta tashi tace bari a kawo mishi ruwa, ta faɗa tana miƙewa daga gurin...., Da sauri wata ƴar budurwa tabi bayan ta inda zata ɗebo ruwan, cikin ƙasa ƙasa da murya tace "Uwar Abu wannan saurayi ga daga ina? Baƙon ki ne? Ɗan hararar ta tayi tace "ke matsala ta dake gulma kullum cinki take, to nima ban sanshi.. Ɗan ɓata rai tayi ta ce; "kai Uwar Abu daga tambaya nifa ba gulma nake ba, kawai nagansa kalar ƴan birni ne kuma gashi yazo gurin ki, na sani ko Abu ce ta aiko sa... Dungure mata kai tayi tace "Ni matsa min in wuce in son ji kike jeki tambaye sa mana nima basan shiba, kinji min ƴa daga zuwan mutum zaki wani tsare ni da tambaya, tana faɗan haka tayi wucewar ta ta bar ta agun... Turo baki tayi tana ƙara kallon baƙon tana gunguni ƙasa ƙasa, tare da komawa wani guri ta zauna tana facing ɗin sa yanda zata fi kallon sa da kyau...✍️✍️ Yauwa free pages ya kusa ya ƙare, kowa ya fara shirin payment🤗 *Banjuuuuuuuu kina ina ki fara taru ko da biyar biyar ne dan sai na karya miki record ah to siye dole Aheeee😎😎* [4/19, 10:24 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) ______________________________ *_episode 36💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bismillah..✍️ ____Turo baki tayi tana ƙara kallon baƙon tana gunguni ƙasa ƙasa, tare da komawa wani guri ta zauna tana facing ɗin sa yanda zata fi kallon sa da kyau... Uwar Abu na ƙarasawa ta tsugunna ta ajiye musu ruwan tare da basu waje ta koma ɗakin ta. Malam ne ya kuma gyara zama yana tura masa ruwan tare da cewa yaro sha mana, ya faɗa yana zuba masa idanu dan ya ƙagu yaji meke tafe da yaron. Ɗan murmushi Khalifa yayi yana ɗaukan ruwan ya ɗan kurɓi kaɗan ya ajiye tare da gyara zaman sa, yana fuskantar sa da kyau kamar yanda shima yake kallon sa, "Malam daman abun dake tafe dani abunne me mahimmancin gaske duk da bansani ba a wane matsayin zaka ɗauki maganar ba, an bani address ɗin gidan ka sakamakon wanda nazo nema ance baya garin saidai inzo wajen ka tunda mahaifin ka ne. Jin abun da ya faɗa yasa Malam saurin haɗe rai laƙaci guda yanayin fuskarsa ya sauya launi. Khalifa bai fahimci komai ba yaci gaba da cewa; "Ban sani ba ko kasan farkon zancen, nazo neman wata jaka ne dake hannun sa wacce ɗan uwanka yabawa mahaifinka ajiya, to yanzu buƙatar jakar ne ya tashi ake neman sa, dalilin da ya kawo ni garin kenan kuma akace ya tashi saidai inzo in sam... Shiru yayi bai ƙarasa ba sakamakon ganin Malam ya mike tsaye tare da ɗaga masa hannun cike da tsantstsar ɓacin rai yace "Dakata da wannan banzar maganar taka tun kafin in irga maka uku ka tashi ka fice min daga gida in ba haka ba kuma sai ranka yayi mummunan ɓaci sai kayi danasanin zuwan ka garin nan. Zunbur shima Khalifa ya miƙe mamaki al'ajabi tsoro da fargaba duk a loƙaci ɗaya suka saukarwa masa take wani irin gumi ya shiga tsatstsafo masa daga cikin kansa take jikin sa ya fara ɓari, muryar sa cike da rauni kamar me shirin fashewa da kuka yace "Malam dan Allah kar kace haka kar kamin haka duk da bansan me yasa kace haka ba bansan me yafaru ba amma dan Allah ka ka sanar dani meke faruwa? Kar ka koreni, ka taimake mu kamar yanda Allah ya taimake ka, wallahi matar nan tana cikin mawuyacin hali dole sai da taimakon ka zamu iya samun wasu abubuwan ka taimaka ka gaya min inda yak... Kafita nace maka.! Malam yakuma katsesa da tsawa me ƙarfi da saida tasa mutanen gidan leƙowa suga meke faruwa, "Wallahi wallahi ka kuma cewa tak a gunnan zakaga me zai faru bana son jin komai daga gare ka kuma nima bazan faɗa maka koman ba kafice min daga gida kada ka kuma dawomin cikin gida har abada kafice nace! Khalifa duk da haka bai daddara ba ya kuma yin yunƙuri zaiyi magana ya kifa masa mari fuskar sa cike da ɓacin rai yace "wai kai wane irin taurin kaine da kai nace ka fita ko! Ka fita nace bazan faɗa ɗin ba ka fita! Tunda Khalifa ya dafe kumatunsa bai kuma cewa komai ba kamar mutum mutumin domin gaba ɗaya ma ji yake kamar ba a duniyar yake ba, ko inda takamin sa yake bai kalla ba a haka kawai ya shiga tafiya baisan inda yake saka ƙafar sa ba. Yarinyar dake laɓe (wacce take tambayar Uwar Abu baƙon daga ina yake) da gudu ta fito tayo wajen takalman sa ganin yana shirin fita babu takalmin, saidai ta na tsugunnawa zata ɗauka Malam ya daka mata tsawa yace idan kika kuskura kika taɓa to idan kika bishi kar ki kuma dawo min cikin gida, sak tayi agun ita bata ɗauka ba kuma bata fasa ɗauka ba, hannun ta ya tsaya a tsakiya. Uwar Abu ce ta ƙaraso gurin itama cikin sauri tace "Malam wai meke farune meye hakan? Ko ma meye ai kamata yayi kabari yasa ka takalmin s... Wani banzan kallo ya watsa mata da yasata haɗeye guntun maganar ta tunda daman bataji me yake faruwa ba, Kowa na gidan saida yazo gurin cike da mamaki suka tsaya suna kallon Malam a yanayin da basu taɓa ganin sa ba, mutumin da ko magana da ƙarfi bai fiya yiwa mutane ba amma yau shine harda irin wannan tsawar ga kuma ɓacin rai dake danƙare akan fuskar sa da ta nuna sosai, mutum ne wanda bai fiya faɗa sosai ba inka ga yayi faɗa ko fushi to ba ƙaramin abu bane zaisaka shi yi, ganin hakan yasa duk suka shiga taitayin su babu wanda yayi yunƙurin ƙara tambayar sa ko yin wata magana suka zuba masa ido har ya juya cikin fushi ya shiga ɗakin sa tare da bugu ƙofar da ƙarfi. Khalifa tafiya yake kwai saidai da yaji ƙafafunsa sun kasa ɗaukar sa yasa shi zamewa jinkin wani gida yayi zaman dirshen a ƙasa tare da haɗa kai da gwiwa baisan loƙacin da hawaye ya shiga sauko masa ba ji yake kamar ance bazai taɓa cikawa matar nan alƙawarin da ya ɗaukar mata ba, yanzu da wani ido zai koma gida ya kalle ta yace ba'a dace ba ya faɗa mata irin korar wulaƙancin da yayi masa gashi dare yayi baisan ma inda zai dosa ba daga nan, abun ba ƙaramin tsaya masa arai yayi ba to meyasa Malam zaiyi masa haka me yasa bazai faɗa masa ba me yasa yanayin sa ya sauya sosai daga jin maganar me yake faruwa? Sai faman tambayoyi yake jerowa kansa da bashi da amsar su, Inuwar abu yaji akansa da sauri ya ɗago dan ganin ko waye, mace ya gani akansa a tsaye hannun ta riƙe da takalmansa sai yanzu ya tuna ba takalmi a ya fito, yarinyar ce ta biyo shi ganin baban nata ya shiga ɗaki. Kallon ta yake itama zuba masa idanu tayi tana kallon sa, saida ta gama kallon nasa sannan ta tsugunna ta ajiye masa takalman sa tare da zama a gaban sa, tana kallon sa tace; "kayi haƙuri da duk abun da mahaifina yayi maka wallahi ba halin sa bane, naji tattaunawar ku saidai bangane ba kuma bansan komai ba saidai idan baza ka damu ba idan zaka kuma yi min bayani indai nasani to ko ta wace irin hanya ce zan taimaka maka ina fatan banyi maka shishshiga b? Jinjina mata kai kawai yake sosai ya ɗanji sanyi da zuwan ta da kuma abun da tace masa, "In Sha Allah zan taimmake ka kar ka damu ka sanar dani dan Allah, "Saida yaja ɗan loƙaci kafin yace "kin san inda kakanki yake ma'ana mahaifin mahaifinki? Shiru tayi tana nazarin kafin ta ɗan numfasa tace "gaskiya bansan inda yake ba da gida ɗaya muke zaune dashi a yanda babar mu taban labari saidai tace rana tsaka kuma yabar gidan aka neme sa aka rasa a cikin garin amma dai mahaifin mu yasan inda yake saidai yaƙi gayawa kowa dan ko antashi za'a neme sa sai yace a daina yana zaune lafiya kuma zai dawo tun anayi har akadaina daga baya ma idan aka tambaye sa sai yace ya rasu amma su basu yarda ba, saidai babu yanda aka iya dole aka haƙura akabar zancen tun loƙacin... Kaji iya abun da nasani kenan saidai kayi haƙuri ni yanzu zanci gaba da bibbiyar lamarin nasa zan gano gaskiyar lamarin in Allah ya yarda amma sai kaban loƙace yanzu ka tafi in ka dawo nan da wasu watannin duk yanda ake ciki zan sanar da kai. Wani dogon numfashi yaja dan ba haka yaso ji ba, amma ya zaiyi dole ya ƙara gwadawa ta hannun ta saidai watanni da ta faɗa yayi masa nisa. "Tom nagode da hakan ma amma watanni da kika ce basuyi nisa na, in kina da waya kiban number ki sai in ringa kiranki inajin yanda ake ciki tunda kinji dai abun da mahaifin ki yace kar na kuma dawowa duk da bana jin zan iya haƙura ɗin, "Hmm gaskiya banda waya amma bari inje gida in ɗauko biro da takarda kaban taka idan nasamu waya sai in kiraka, kuma watanni da nace bawai dole sai abun yakai wata ba kawai dai bansan yanda lamarin zaizo bane zan samu abun da wuri ko bazan samu ba, amma yanzu indai da number to duk yanda muke ciki zakaji ni da wuri. "Ok thanks a lot, yanzu kije ki ɗauko ɗin in baki. Tashi tayi da sauri tace "to ka jirani dan Allah ko da zakaga na daɗe dole sai na saci hanya zan fito, ai anan zaka kwana ko. Ɗaga mata kai kawai yayi dan besan me zaice mata ba, shi da ba wanda ya sani a garin a ina zai kwana. Harda gudu gudu take haɗawa wajen tafiya tana tafiya tana waigen sa, dan tausayin sa takeji hakannan. Tana ƙarasawa gidan ta shiga ciki da saurin ta, turus tayi ta tsaya ganin duka ƴan gidan ma tayi a tsakar gida ga mahaifin ta da saida ta firgita da suka haɗa ido, da sauri ta sunkuyar da kanta ƙasa take taji zuciyar ta ta tsinke shikenan yau kashin ta ya bushe gashi kuma ta cewa saurayin ce ya jira ta yanzu ya zatayi idan aka hanata fita da ta sani ma cewa tayi ya faɗa mata ta haddace akanta amma batayi wannan tunanin ba a loƙacin. Tana wannan tunanin taki saukar bulala akan ta, ihu ta ƙwala tana shirin juyawa ta fita ya jawo hannun ta, ɗakin sa kawai yayi da ita, tana ihu amma babu wanda ya dakatar da shi

Chapter 29 of 44