Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ita tare da kamo hannun ta guda ɗaya ta damƙe tana kwanciya akan cinyar ta, tare da saƙalo ɗayan hannun ta ta bayan Beenish tana rungume da hannun ta ɗaya ta haɗa yatsun ta da nata, sai kawai ta fashe da kuka. Lumshe idon ta tayi tana me jin kukan nata har can cikin ranta, ita ma ruƙo natan tayi ƙam hawaye na sauko mata bata son tagan ta tana kuka dan tasan dalilin kukan nata. Hannun ta na ɗan karkarwa tayi sauri ta goge hawayen ta tayanda kar Babyn baby ta ganta tana yi amma baya sani ba tun zubowar hawayen ta na farko ya sauka akan hannun Babyn baby ta zuwa gurin ido hakanne ma yasa ta ƙara volume a kukan nata.. Cikin muryar rarrashi ta ce; "me kuma ya faru meye na kukan tashi kije ki kwanta bana son shirme, ta faɗa tana ƙoƙarin ɗagota daga jikin ta, amma sai taji ta kuma ƙanƙame ta tana ƙara shigewa jikin ta, babu yanda ta iya dole ta rabu da ita tana ɗan bubbuga bayan ta tare da cewa "ya isa haka Baby ki daina kukan nan kin san bana so koh ko kina so ne ki sani kukan nima? A yanda take a jikin ta ta shiga girgiza kanta, tana cewa "taya zan so kiyi kuka nima bada son raina yake zubowa ba kawai jinsa nake yana tahowa, kiyi haƙuri yaya zan daina, nama daina wallahi na daina, ta faɗa tana sakin ta da sauri sannan ta sake ta tana ɗagowa, fuskar sa ta shiga kalla cikin kalar tausayi tace "Yaya kar kiyi nafa daina kin gani, tayi maganar ta daka hannu tana goge kuma goge fuskar ta duk dande ta yarda. Murmushi dole Beenshi ta ƙaƙalo ta aza a fuskar ta, tace "eh na gani tashi muje mu kwanta kinga gobe da akwai school. Shiru tayi bata bata amsa ba kuma bata motsa ba, a hankali ta kuma cewa; "Wai yanzu mu a haka zamu ƙare rayuwar mu babu kowa namu babu wanda muka sani gashi rayuwar taƙi yi mana daɗi daga wannan sai wancen kullum bamu da kwanciyar hankali anƙi barin mu mu zauna lafiya kullum bala'i da zai faru daban, Yaya wallahi na gaji da rayuwar nan ji nake wallahi dama na mut..... Da sauri Beenish ta rufe mata baki cikin rashin jin daɗin maganar ta ta, ta ce "Wai meye ne hakan duk me ya kawo wannan maganganun kar na kuma jin kinyi wannan zancen kinji ni ta shi ki tafi ki kwanta! Tayi maganar cikin ɗan ɗaga mata murya sama kamar faɗa faɗa. Kuka ta kuma fashewa da shi zata kuma ruƙota Beenish tayi saurin tashi tsaye tana haɗe rai ta ce; "ki tashi nace ki daina yi min kukan nan nace miki bana so ya kike so inyi da rayuwa ta ne, damuwar ki ko damuwar abun dake damuna haba Baby har yanzu baki san kin girma ba, haba dan Allah, ki tashi nace kije ki kwanta! Sosai Babyn baby ta tsorata da faɗan da Beenish tayi mata dan ina jin tunda suke da ita tsawon shekaru bata taɓa yi mata irin wannan faɗan ba ko ɗaga mata murya batayi duk kuwa irin girman kukan da zatayi mata tun bata kai haka bama, saidai ta zauna taita rarrashin ta amma bata san me ya hassala ta haka ba take mata irin wannan faɗan, ruɗewa tayi takama wani kukan kuma bata motsa ba daga inda take dan tana jin tsoro kar ta riƙe ta ta dake ta tunda de har tayi mata irin faɗan yau. Dafe kanta Beenish tayi cike da taƙaicin kanta dan ita kanta tayi mamakin yanda ta fara yi mata faɗa haka kurum, komawa tayi ta zauna kusa da ita tare da jawota ta rungume itama hawayen taji yana shirin taho mata, tayi sauri mayar da shi cikin sigar rarrashi ta ce; "I'm so sorry dear, ki gafarce ni bazan sake ba, ya isa haka kiyi shiru dan Allah kinji? Ƙin yin shirun tayi, ta ci gaba da kukan ta saida ƙyar ta samu ta rarrashe ta sannan tayi shiru. Ɗagota tayi daga jikinta ta shiga goge mata hawayen, saida ta tabbatar da tayi shiru sannan ta gyara zaman ta tare da cewa "Hanifah" Batare da ta amsa ba ta juwa ta kalle ta cike da nutsuwa tunda taji ta kira asalin sunan ta tasan da magana me mahimmanci shiyasa tayi saurin nutsuwa tana maida hankalin ta gare ta. A hankali Beenish ta ce; "Me kike so? Me kika rasa? Wace wahalar kike ji? Meye kike so meye bakya so? Meye bakyajin daɗin sa? Me kika rasa dangane da lafiyar ki? Kina da wata tawaya a jikin ki? Meye Allah ya hanaki? Me yasa kike zaɓar wa kanki mutuwa? Shiru Babyn baby tayi da jin waɗannan tarun tambayoyin da Beenish tayi mata da bata san ma ta inda zata fara bata amsa ba, "Yaya to waɗannan tambayoyi wacce kike so na amsa miki? "Gaba ɗaya, Beenish ta bata amsa tana kallon cikin idon ta. Sake shirun tayi kamar bazata yi magana ba kafin dai da ƙyar tace "Iyaye na, Farin ciki, wahalar duniya, banajin daɗin irin rayuwar da muke, babu abun da na rasa daga lafiyar jikina saidai zuciya ta wataran banajin daɗi, na zaɓarwa kaina saboda duk indaina fuskantar waɗannan abubuwan dan ina ganin sai hakan yafiye min.... Ɗan jim tayi tana kallon Beenish da taga ta tsare ta da ido ko ƙiftawa batayi, kawar da kanta tayi tare da cewa shikenan duk na baki amso shin tambayoyin ki... Har yanzu Beenish bata janye idon ta akan ta ba, ta zuba mata ido a haka ƙwalla ta shiga taruwa a cikin idon ta har ta cika mata ido ta fara gangarowa amma duk da haka bata daina kallon ta ba idon ta yana tsaye ƙam akan ta ko motsi batayi... Fara tsorata Babyn baby tayi da yanayin ta ganin yanda tayi taƙi motsi sosai ta sha jinin jikin ta, dan har jikin ta ya fara ɓari, a hankali ta ce; "Yaya ta kira sunan ta tana shirin saka hannu ta goge mata hawayen da taga yana zubo mata, sai kawai taga ta janye fuskar ta ta ture hannun ta, Cikin wata iriyar murya da kuka ne kaf cikin ta, a haka ta buɗe bakin ta da har yake ɗan harharɗewa, ta ce; "Hanifa da gaske bakya jin daɗi rayuwar ki, bakyajin farin ciki ko da yaushe bakyajin daɗin rayuwar da mu, Hanifa me yasa baki taɓa gaya min ba me yasa baki taɓa sanar da ni ba, shin a tunanin ki sai Allah ya barki da iyayen ki ne kaɗai shine ya baki farin ciki, iyaye ne kaɗai farin ciki, shin wace irin wahalar rayuwa kike, tunda muke dake kin taɓa tambaya ta abu kin rasa, me kika rasa a rayuwar ki sutura, makaranta, ci, sha, makwanci me kyau, abun hawa, me kika rasa daga cikin waɗannan abubuwan... "Kin san me ake kira da ƙaddara kuwa to wannan itace ƙaddarar ki, ya kamata kisan wannan iyaye basu kaɗai ne farin ciki ba, ki godewa Allah aduk halin da kika tsinci kanki, tunda ya baki iyayen da suka kawo ki duniya, kinzo cikin ta babu abun da ya haneki dashi, yabaki lafiya, ya baki ji, ya baki gani, ya baki hannunwan ki biyu, yabaki ƙafafu biyu, kina tafiya kina zama kina tashi kina kwanciya kina gudu, babu abun da bakya iyayi da kanki, amma baki gode masa ba har kike zaɓarwa kanki mutuwa, shin duk waɗannan abubuwan da ya baki ke ki zaɓa da ya baki su? "Ƴaƴa na wane suke tasowa da iyayen nasu amma wasu farin ciki rana ɗaya ya gagare su, wasu ga iyayen babu kuɗi, wasu ga iyayen babu tarbiya, wasu ga iyayen ba su da hankali, wasu ga iyayen babu lafiya, shin kin san mutane nawa ne suke lalacewa a ƙarƙashin iyayen nasu, wasu sun zama karuwai, wasu sace sace, wasu ƴan shaye-shaye, wasu ƴan maɗigo, wasu ƴan luwaɗi, duk fa suna da iyaye suke aika ta hakan hawai dan sun kasan ce marayu ba, baki san Allah yayi ki amaraimiya ba nan ma wata ni'imar ce kuma yafiki sanin abun da zai faru shiyasa ya barki a hakan, wasu kuma ƙarewa iyayen nasu ne lalatattu, sai Allah yayi ki ke da hankalin ki da tarbiyyar ki, amma iyayen kiga babu nagari, sai kiga halin iyayen ya hana su farin ciki, wasu iyayen ne zasu jawowa ƴayan abun kunya kiga in anfita ana nuna su, su kuma sai suce me? "Wasu kuma zasu taso da iyayen amma Allah ya jarabce su da jarrabawa kala kala, kofa gasu a haɗe ɗin amma indai farin ciki ne basu san shi, zasu ta fuskantar ƙalubale kala kala, wasu na talauci wasu na rashin lafiya, wasu kuma kiga ga kuɗin amma babu lafiya kuma kuɗin da suke dashi bai isa ya siya musu lafiyar ba, Allahn da yayi su haka yake son ganin su, saboda shi yabasu kuɗin kuma shi yaba su rashin lafiyar dan haka shi zai basu lafiyar ba kuɗin da ya basu ba shine me komai da komai sai yanda yaso zaiyi, idan ba tsara faruwar abuba babu wanda ya isa ya sa ya faru. "Da kike cewa bakya son irin rayuwar da muke, shin muna yawan bin maza ko muna wasa da ibada, ko bamu da kamun kai, ko muna aika ta wani lafin na daɓon Allah, wace irin rayuwa muke mun rasa ci ko mun rasa sha, ko mun rasa kayan sakawa, ko muna cin mutuncin wani ko cin zarafin wani, ki gaya min, me muke aikatawa da har kika ƙyamace kalar rayuwar da muke? "Hanifa baki san ni wacece ba, shin kinsan ni wane irin iyaye Allah ya haɗa ni dasu, in baki sani ba ki sani kina ta kirarin mahaifi ko kice da mahaifinki na raye da wani abun bai dame ki, to ki sauya tunani, Allah baya barin wani dan kaji da daɗi kuma baya ɗauke wani dan kaji akasin haka, ko yana nan ko baya nan abun da yake rabon ki yake cikin ƙaddarar ki to fa dole ya same ki shi kansa bai isa hana faruwan hakan! Dan Allah ya bar maka iyaye ko ya ƙwace su bawai shi yake nuna ya maka gata ba ko kuma akasin haka, ko da su ko basu sai yaso kayi farin ciki kuma sai yaga damar yanda rayuwar ka zata kasance, dan bakai kayi kanka ba, shi yayi ka dan haka shi zaiyi yanda yake so yayi dakai ba wani ba. Goge hawayen da taji ya taho mata tayi sannan ta miƙe tsaye muryar ta kamar zata fashe da kuka ta dawo gaban Babyn baby tana kallon ta tace "Kin san nawa mahaifin yana raye amma bashi da amfani aguri na, ni kuma farin cikin da zanyi shine ace baya duniyar da ace ya kasance uba agare ni, sosai hawaye ke zubo mata ta kuma gogewa taci gaba... "Mahaifina shi ya kashe mahaifiya ta da kansa da hannun sa, wanda yayi ƙoƙarin kashe ni nima dande bai samu damar hakan ba, ki duba fa uba fa da kansa ya ke son kashe ƴar cikin sa, zaman sa araye shi zaisa min farin ciki ko kuma baƙin ciki? Wahalar da nasha ko rabin ta baki sha ba, na tsaya tsayin daka duk dan in baki farin ciki, amma ban sani ke kuma a kullum shi kike rasawa, tun kina ƴar jaririya nake fama dake tun banda hankali nake kula dake har na samu na fara hankali, daidai da kwana ɗaya bana barin ki da yunwa koda kuwa zan yi sati banci ba duk dan ke insaka ki farin ciki saboda ke na bar abubuwa da yawa kuma nayi abubuwa da yawa har kika girma kika fara sanin rayuwa amma yanzu ni kike cewa bakya farin ciki kingaji da rayuwa bakya son rayuwar da muke, Ni..!? Ni..!? Ni Hanifa ki gaya min wacce irin rayuwa muke...✍️✍️✍️✍️✍️ *Wannan page ɗin sadaukarwa ne ga marayu masu ganin kamar dan mahaifan su basa raye ne yasa suka kasance wani abu a rayuwa, ko kuma suka rasa wani abu a rayuwar su, ko kuma da suna nan zasu samu komai wannan kuskuren tunanine da shiga lamarin Ubangiji* Wallahi akwai mutane da dama da nasani ko sabga aka tashi musamman ta kuɗi ko taro ko wani abu sai su saka kuka wai da iyayen su na raye da sun sha gata da anyi musu kaza da baza ayi musu kaza, For real abun wallahi haushi yake ban, Allah na tuba kai da kake da iyayen abubuwa nawa akeyi basa yi maka, wasu ma ba'a damu dasu ba, amma mutane da yawa basa gane hakan, saikaga kamar dan sun mutu shikenan andatse maka duk wani farin ciki da gata, ba haka bane wallahi, shi Allah ya fika sanin manufar hakan. _Dan Allah ina kira ga masu irin wannan tunanin da su gyara su ringa godewa Allah suna yiwa iyayen su addu'a, su dena irin wannan tunanin hakan ba daidai bane!_ [3/5, 12:35 PM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅) ______________________________ *_episode 35💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bismillah..✍️ ____Wani irin kuka Babyn baby ta fashe dashi jikin ta har yana karkarwa ta shiga karkaɗa kai tana zubewa a ƙasa.. Wata tsawar Beenish ta kuma daka mata, tana cewa "tambayar ki nake!? Cikin kukan ta fara ƙoƙarin riƙo ƙafar ta, Beenish ta janye ƙafar ta tana ja da baya, ɗagowa Babyn baby tayi tana ci gaba da girgiza mata kai gaba ɗaya jikin ta yagama mutuwa, jinta take kamar ba ita ba, gashi bata da amsar da za ta bata ba, daga inda take ta shiga rarrafawa tana nufar ta amma sai ta kuma matsawa, Hakan yasa tayi saurin miƙewa tsaye tana haɗa hannunwan ta guri ɗaya, cikin wani irin kuka na fitar hankali ta ce; "dan Allah dan Annabi kiyi haƙuri wallahi ni duk ba haka nake nufi ba, wallahi ba abun da kike tunanin nake nufi ba, wallahi da gaske nake tana maganar tana nufar jikin ta na ɓari hawaye kam kamar an kunna famfo haka suke zubowa. Ita ma Beenish ɗin kukan take amma duk da haka bata bari Babyn baby ta raɓe ta ba daga tazo kusa da ita zata matsa, hakan kuwa ba ƙaramin ƙara tayar mata da hankali take ba dan gaba ɗaya ta rikice bata san ma loƙacin da ta zube a wajen ba, kukan da tayi na ƙarshe ne yasa ta shiɗewa numfashin ta ma ya ɗauke. Saidai Beenish taga haka sai kuma ta rikice dan tama fita rikicewa a sukwani tayi kanta tana kiran ta, "Baby! Baby! Please kar ki min haka da wasa nake miki gani ajikin ki ki tashi ki rungume ni kar ma ki sake ni idan kika riƙe ni wallahi na haƙura ki tashi, sai jijjiga ta take tana surutai.... Da gudu su Ameela ma dake ƙofar ɗakin su suna kallon komai sukayo kansu, suna cikin tashin hankalin suka shiga kiran Babyn baby amma ko motsi batayi ba, duk sun rikice Beenish kam kamar zautacciya haka ta koma sai surutai take musu.. Maryam ce dake tsaye komai yake faruwa ta ƙaraso gurin hannu ta ɗauke da gorar ruwa, tana ƙarasowa ta tsugunna batayiwa kowa magana ba kawai ta yayyafawa Babyn baby a fuska bata bata motsa ba, nan ta ɗaga duka robar ruwan ta juye mata a fuska, nan take ta kawo wani dogon numfashi, tana sauke numfashin kuma ta ɗora daga inda ta tsaya, da sauri Beenish ta ɗagota ta rungume ta ƙam kamar zata mayar da ita jikin ta, tana rungume ta kuma ita ma ta fashe da kukan me sauti dan duk abunnan da kayi hawaye kawai take babu sauti amma yanzu me sauti ta saki tana kuma ƙanƙame ta ajikin ta..... *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *GHAMBURJ* *Hajja Mama* Tana sanye cikin shigar ta da tafi yi ko da yaushe, baƙar riga doguwa buɗaɗɗiya sai wanda da riga ta ciki, kanta ta naɗe sa da wani farin abu ɗan siriri tazubo da gashin ta da furfura duk ta cinye sa yayi fari, tana tsaye gaban wani hoto da tayi rubuce rubuce a ƙasan shi tana ɗan zagaya gurin, dai fuskar mutumin ta zana wata jar maker a daidai saitin girar sa, sai ta kuma samun gefen kuma tun sa ta zana su da yawa sai yayi kamar gemu, daidai bakin sa kuma sai ta saka masa baƙar makar, jinjina kai tayi a hankali ta ce; "kamar shi, kamar kuma bashi ba,wayar ta ta zaro a aljihun ta tare da danna wasu nombobin sannan ta kara wayar a kunnen ta, "Hello, Gee har yanzu fa na kasa ganewa kode zaka zo ka gani wallahi na kasa gane ainahin fuskar, shiru tayi tana sauraron abun da ake ce mata, tana gama sauraro, tace "okay tom sai ka ƙaraso, bari in sanar dasu in zuwan dare zakayi ko? Shiru tayi sannan ta kuma cewa "tom sai ka ƙaraso sai anjima. Nan ta sauke wayar ta mayar da ita ma'ajiyar ta, sannan ta kuma zuwa gaban wani hoton tayi rubuce-rubuce kafin daga bisani ta fita daga ɗakin tare da rufe sa ta saka muƙulli ajiki, tana juya suka haɗa ido da Faheema, cike da ɗan sakin fuska tace "a'a ƴan mata an tashi? Wani kallo Faheema ta watsa mata tana kawar da ido kana ganin idon ta kasan taci kuka ta ƙoshi, ko uffan bata ce mata sai ta kuma juyawa ta koma ɗakin da tafito, bin bayan ta da kallo Hajja Mama tayi tana sakin murmushin gefen baki, tare da jinjina kai, tana cewa "kin haɗa kanki da aiki yarinya indai nice, bari muga iya gudun ruwan ki.. Wani ɗakin ta nufa tana zuwa ta ta tura ƙofar dake daman a buɗe ɗakin yake, tana shiga Bilal na fitowa daga wanka, kallo ɗaya yayi mata ya ɗauke kai yana haɗe rai. Murmushi ta saki tare da cewa tuba nake autan su, bansan zaka fito daga wankan ba ai, bari in fita idan ka shirya na shigo, banza yayi mata bai tanka mata ba. Zaid dake kan gado ya diro yana watsa masa harara yace "banza me kama da mata to uban me zata gani dan ta shigo ko tsirara kake ai ba wani abun kalla da har zaka haɗe rai dan ta ganka da towel, ita ma abun haushi harda wani baka haƙuri. Shima Bilal ɗin harara kawai ya watsa masa ya wuce abun sa bai tanka masa ba, yasan idan ya biye masa haka zai ta saka sa a gaba da takura, shi kuma baya son takura a rayuwar sa, shiyasa tasu bata zo ɗaya ba kullum cikin faɗa suke, shi bayason takura shikuma Zaid yana son ya takurawa mutum da kuma shiga abun da babu ruwan sa, ko baka saka da shi ba a zance sai ya shiga. Ƙananun kaya ya ɗauka ya saka, yana feshe jikin sa da turare, har yanzu bai kula Zaid ba da yake ta cigaba da yi masa magana, ƙarewa ma da yaga ma sai ya fice abun da ya barsa a ɗakin, yana fita yaga Hajja Mama nakan dinning tana zuzzuba abinci, tsayawa yayi yana kallon ta. Jin kamar ana kallon ta yasa ta ɗagowa, suna haɗa ido da shi ta saki murmushi tare da cewa "ƙaraso mana babana, zo ka zauna kaci abinci gashi na zuba maka.., A hankali kamar baya so ya fara takawa tare da ƙarasa wajen da take, tun kan ya ƙaraso ma, ta tako zuwa gaban sa sannan ta kamasa ta ƙarasar dashi kan kujerar ta zaunar dashi, saida ya zauna ta matso masa da plate ɗin gaban sa, sannan tace bari inje in dawo kaci da yawa yanzu zan dawo. "Wai ni dan Allah me kika mayar dani a cikin gidan nan, tunda bakya so na, ki mayar dani inda ake so na mana, kinzo kin kawo ni nan, shi kaɗai ne mutum kenan? Ni yunwar ta kashe ni babu ruwan ki da cikina? Jinjina kai tayi tare da cewa; "Zaid kai de baka gajiya da jan magana ji nake yanzu na baka abincin kaima kuma bansan zaka ƙara bane shiyasa ban taso ka ba, nayi zaton ma bacci kake.. Ƙarasowa yayi yana maƙe kafaɗa tare da tallewa Bilal kai yana zama a kujerar gefen sa, sai loƙacin yace; "Bacci yanzu sai kace malalaci irin o'o ni ai namiji ne ba mace ba, Cokalin dake hannun Bilal ya ƙwala masa shi akai tare da watsa masa lemon dake gefen sa, sannan yace; "Zaid ka ishe ni na rantse da Allah zan maka abun da baka tunani dan kaga ina ɗaga maka ƙafa ko to kaci gaba, Allah wataran na riƙe ka sai an rasa me ƙwatar ka anan gurin idan kana ganin kuma ƙarya ne ka cigaba I will show you my another colour. Dariya Zaida ya sanya harda tafawa, yana dariya yace; "Gaskiya ne maza, yau maza na magana, to in baka fasa ba, daman kai har wata kala ce dakai, gaya min wace iri ce fara ko ja ko baƙa? Tsaki Bilal ya daka masa yana ƙoƙarin tashi ya bar masa gurin dan ji yake kamar ya shaƙe shi dan wallahi ya ishe shi ya takurawa rayuwar sa, shikaɗai ne matsalar sa da zaman gidan kuma dole ya bar gidan ko araba musu ɗaki, Da sauri Hajja Mama ta ce "Auta babu ruwanka da shi zauna kaci abinci ka ka rabu da shi zanyi maka maganin sa, Kamar zaiyi kuka cikin langwaɓar da kai yace; "kina fa ganin abun da yake min wallahi nagaji da zama dashi, ki mayar dani gurin Dadyna kince min zaizo amma har yanzu baizo ba wai kode kidnaping ɗinmu kikayi ne? Wani dammm Hajja Mama taji gaban ta ya faɗi, bata son ya ringa tambayar saboda duk loƙacin da yayi mata tambaya makaman cin haka da ƙyar take iya haɗa ƙaryar da zata kwantar masa da hankali yabar zance, to amma tambayar yau tafi bata mamaki na cewa kode kidnaping ɗinmu ki ka yi ne? Bata san kuma ta inda zata kuma ƙaƙalo wata ƙaryar ba. "Eh kidnapping ɗinku tayi muma ɗauko mu tayi, ƴar kidnapping ce duk abun da zata gaya muku ƙarya take muku! Duk juyawa sukayi suna kallon ƴan mata biyun dake tsaye hannun su riƙe da na juna, da mamakin ganin su da kuma mamakin abun da suke cewa yasa su Bilal mutuwar tsaye. Ran Hajja Mama ba ƙaramin ɓaci yayi ba da wannan maganar tasu, tuni fuskar ta ta koma yanda take babu ɗigon annuri a tattare da ita, su kansu basu taɓa ganin ta a irin haka ba. Jikin Bilal ne yayi wani irin sanyi a hankali ya juya ya kalli Hajja Mama, ya ce; "da gaske ne ke ƴar kidnapping ce daman? Kallon sa tayi fuskar ta babu annuri tace; "duk yanda tunanin ka yabaka, idan ka yarda da maganar su hakane sai ka ɗauki mataki idan kuma baka yarda ba nan zaku iya ɗaukar matakin da kuka ya dace gaba ɗayan, duk wanda ya shirya fita ƙofa a buɗe take, daga su har ku ɗin, tana faɗa ta juya zata bar wajen. Cikin

Chapter 28 of 44