tace; "JANNAT...! "wai jiran me muke tunda bazai buɗe ba mu ai sai mu buɗe sa tunda jan ajin nasa yaƙi ƙarewa, nasan yana kallon mu yayi mana shiru, tayi maganar tana kallon glass ɗin motar da take tunanin yana gurin wataƙil ma ita yake kallo.
"Hmmm kema aikin san halin BILAL yanzu hakama wannan abun da muke duk a banza baisan muna yiba, ya nan yana baccin da yasab...
Tun kan takai ƙarshen maganar tata, yarinyar da tayi magana ɗazu tace; "Ni nasan ma UNCLE baya cikin motar nan dan jikina yabani wataƙil ma yana waccen motar. ta nuna motar bayan ta, duk bin gun sukayi da kallo, Amma babu wanda yabar wajen.
Wacce aka kira da Jannat tace "Bari kuga tana faɗar haka tasa hannu ta buɗe motar, wayam suka gani babu kowa abayan motar,
A kusan tare wasu suka ce Kashhh...!! Suna me dafe goshin su cike da rashin jin daɗin rashin ganin sa, ashe duk wannan abun da sukayi daman baya ciki,
Yarinyar ce ta kuma cewa "You see what I'm saying... Tayi maganar cike da ɗan iyaye harda taɓe baki tana yi musu nuni da hannu ta.
Ta gefen tace ta ɗan dungurar mata kai tare da cewa "MUBEENA iyayi ai ba faɗar kice tasa hakan ba,
Bata kulataba tayi ga ta nufi wajen wata motar, tunkan ta ƙarasa ma aka buɗe motar, tsayawa tayi tana jiran taga me fitowar...
Sauran ma duk maida hankalin su sukayi ga wajen motar.
Ɗaya daga cikin Bodyguard ɗin sane ya fito daga motar ciki da ƙarfin hali, dan yadade zaman bazai musu ba shiyasa suka yanke shawarar gwanda kawai sugaya musu ayita ta ƙare,
Yanzu ma de ba haka suka so ba, dan ba wanda suke son gani ba suka gani.
'Yana fitowa sauran ma duk suka shiga fiffitowa har suka gama fitowa gaba ɗayan su.
Cike da ƙaguwa Mubeena tace "UNCLE BILAL...! ta kira sunan sa tana jiran taji ta inda zai amsa.
Gaba ɗayan su suka haɗu a waje ɗaya kallo ɗaya zakayi musu ka fahimci ba ƙalau suke ba.
Wata mata ce ta ƙaraso gurin su cikin tsuke fuska take binsu da kallo kafin daga bisani tace "Where is Bilal...!? Tayi maganar tare da ƙara canza yanayin ta, dan jikin ta yabata Bilal baya cikin ko wacce mota musamman da taga yanayin fuskokin su ya sauya tasan something is wrong,
Gaba ɗayan su shiru suka yi tare da sinnar da kansu ƙasa, babu wanda ya iya furta komai saboda sunfi kowa sanin wacece ita.
Cikin ɗaga musu murya sama tana me daka musu tsawa tace; "Ku bani amsa. Nace ina Bilal? Me yasa kukayi shiru Answer me. I said where is Bilal? Why are you silent? Ina yake..!?? maganar take ko tsayawa batayi cikin fara hassala tana tsare su da manyan idanunwan ta dara dara tubarkallah.,
Babu wanda bai razana ba da yanayin yanda tayi maganar, take cikin su ya ɗuru ruwa,
Cikin rawar murya ɗaya yayi ƙarfin halin cewa "Ma'am we so sorry, Bilal is not here, the some people have gone with hi...
Hannu ta ɗaga masa tana binsa da wani irin mugun kallo, kafin ma tayi magana mutanen gurin suka shiga cewa "What...., Wasu mutanen sun tafi dashi, What does that mean, what do you want to say..!?
Matar da tayi magana ce ta kuma katse musu tambayoyin su tare da maida duban ta ga sauran tana me harɗe hannunwan ta akan chest ɗin ta, tana kallon su alamun suci gaba da maganar da suke...
Cikin rawar murya cike da tsoro wannan tsohon ya shiga labarta musu duk abun da ya faru tundaga A har Z.
Cikin zazzaro ido take kallon sa jijiyar goshin ta har sunfito, ɗaga murya tayi tace "SU WAYE SU..!? a cikin garin nan dake ku kuma lusaraye ne har kuka tsaya mata sukayi muku haka, wallahi! wallahi! wallahi! gaba ɗayan ku sai ranku ya ɓaci muddun wani abu ya samu Bilal ko na rashin jin daɗi ne sai na lahira ya fiku jin daɗi, shine har kuka iya tako ƙafar ku kuka shigo cikin gidan nan, kuma kuka iya kallon ƙwayar idona kuke gaya min kun tsaya mata sun tafi dashi...
Nan mutanen wajen ma kowa ya shiga tofa albarkacin bakinsa tsayawa faɗar na kowa ɓata loƙaci ne, amma dai sun ɗau zafi da yawa saura kaɗan su fara hayaƙi...
Hajjaju kiyi haƙuri ki kwantar da hankalin ki mubi komai a sannu yanzu bai kamata mutsaya ana maida yanda akai ba, loƙaci is going abun da yakamata muyi shine muje asan yanda za'ayi a fara bincike, tun kan ƴallaɓai yaji wannan maganar muyi mu gama in ba haka ba kuwa basu kaɗai ba kowa na gidan nan sai ya fuskanci fushin sa dan haka muyi abun da ya kama ta.
"Juyawa tayi tana kallon ta, tana me marairaicewa kamar zatayi kuka, tace "KHATUME taya kikeso in kwantar da hankalina kinsan Bilal shine rayuwata bana son duk wani abu da zai taɓa sa bare kuma ace min baya nan, sunfa tafi dashi bansan me zasuyi masa ba, zasu iya cutar dashi, ko SU WAYE SU bazan taɓa barin su ba, duk sai nasa anƙulle su domin hukuncin kidnapping sai sunyi zaman gidan yari zasu san sun shiga wasan da bana su ba,
Juyawa tayi gurin Bodyguard ɗin cikin nuna su da yatsa ta kuma cewa "Wallahi idan wani abu ya sameshi bazan ƙyaleku ba, kuje duk inda zaku nemo sa sannan ina son ganin su ku haɗo da su nabaku nan da ƙarfe biyar ɗin yamma tana kaiwa nan ta juya fuuu tabar wajen, tare da sakin wani irin shu'umin murmushin gefen baki a hankali ta furta Allah raka taki gona umma ta gaida ayssha, mugun iri kawai, tana tafiya tana wannan maganar a hankali tana jinjina kai alamun akwai maganganu da yawa a ranta.
Wacce aka kira da Khatume ta kalli sauran saboda ita tana da sauƙin kai cikin sanyin murya tace "dan Allah kuje ku tsanan ta bincike ku gano inda yake kafin ƴallaɓai ya dawo kar kubari kowa yaji labarin nan, gudun tada wata maganar yanzu bari in shiga ciki zan sanar da Abbakar sai yasa Police su bibiyi hanya suma.
Godiya sukayi mata dan sunji daɗin yanda ta karɓi abun sun ɗauka ma abun zaifi haka zafi dan haka ba ɓata loƙaci suka shiga motocin su cike da samun ƙwarin gwiwa suka fita daga gidan ita kuma ta tarkata sauran suka bar gurin suma kowa ciki da mamaki da al'ajabi........
**************************
"Zaune suke a cikin wani ɗaki me faɗi babu komai a cikin sa, yana tsakiyar su hannunwan sa a ƙulle da igiya sai ƙafafun sa suma a ƙulle ko riga babu ajikin sa daga shi sai ɗan boxer bakin sa a ƙulle da salatif, kafin nan kuma saida suka fara ɗan sassamashi da duka saboda taurin kai da yaso yayi musu suka nuna masa nasu taurin kan yafi nasa,
Fari ne sosai irin har fatar nan, baida jiki sosai amma yana da ɗan tsaho kaɗan yana da kyau sosai akwai idanu ga hanci ga gashin kansa kamar na ƴan India a kwance,
Wayar sace a hannun su ɗaya tana ɗaukan sa videon jikin sa,
Me ɗaukar hotonce tace "BABYN BABY cire masa abun bakin sa muyi masa tambayoyi idan yabamu amsa ya tafi idan kuma bai bamu ba yaci gaba da zama anan, nifa yaron ma yaɗan burgeni aradu gashidai a ido babu ruwan sa amma sai ɗan iskan jiji da kai da wulaƙan ta mutane, kinsan saida mukazo ma nagane sa ranar da muka je restaurant ɗinnan,
Ɗaya tace "To yanzu ina jiji dakan gashi tunɓur agaban mu, yayi mana wani gigin mu saki videon ɗan iska, a social media muga ta tsiya,
Bayan ta cire masa, suka sakashi a gaba suna tayi masa sheƙiyanci da tambayar rainin hankali saboda ɗaukar sa suke yi, idan yaƙi bada amsa kuma sai su zabga masa mari a haka saida suka sa fuskar sa tayi ruɗu ruɗu ta kunbura saboda yaron ajebo ne ɗan madara jikan madara...
"Kai dan ubanka waye baban ka mun manta ma bamu san ko ɗan gidan uban waye ba muke wannan abun yakamata ya gaya mana full address ɗin sa ko ya kukace,
"Hhhhhh Barazana baki da mutunci wallahi to uban me zamuyi da sunan ubansa, ba damuwar bace tunda de burin mu yaci ka kuma mun samu abun da muke so ai ɗan koli yaci riba kamata yayi ma yanzu mumaida shi inda yafi kauri,
Wacce aka kira da Barazana tace "nima haka nake tunanin kar afara neman sa dan da alama anaji dashi.
"Yo Allah na tuba munajin tsoron wani ƙaton banza ne ni bari ma kuga abun da zanyi wayar dake hannun ta ta katse videon sannan ta shiga daddanawa maida dubanta tayi ga saurayin da yake gabansu sannan tace; Nace ba munajin ka ya sunan ka full name kuma muke so...
Banza yayi dasu tare da kawar da kansa gefe shi kaɗai yasan hukuncin da zai musu saidai kuma matsalar itace duk baiga fuskokin su ba domin duk sunsaka ƙananun hijaban nan masu haɗe da rigunan su, kuma hijabin me niƙab ne iyaka idanun su kawai yake iya gani,
Saida yaga suna ƙara ƙoƙarin kaimasa wani dukan sannan yace "BILAL MAS'UD ƊAN IJJE.
"Good boy yaro yanason lafiyar sa kenan kaga yanzu duk inda muka ji sunan munsan mun taɓa haɗuwa da ɗaya daga cikin ƴan gidan.
Wani irin kallo ya watsawa wacce tace masa yaro ita kuma sai ta ɗage masa gira tare da ƙifta masa ido tace "yadai bana son kallon banza fa yanzu jikin yaro zai gaya masa, ta ƙarasa maganar tana watsa masa harara.
Tana gama faɗar haka ta miƙe tsaye tare da cewa "Beenish kinyi shiru tun ɗazu bakice komai ba,
Ɗan murmushin ta saki tare da cewa "Babyn baby babu abun da zance kawaidai nima bansan me yasa naji nayi hakan ba, jikina duk yayi sanyi ina ganin mu sake sa ya tafi kawai mungama dashi ai,
Jinjina kai tayi tace "hmmm mutanen ne suka motsa ko to yayi, "AMEELA mu fita dashi ko akwai wani abu nidai duk binciken da zanyi a wayar nan nayi idan mun zauna zakuji komai,
Ameela tace " amma fa babu wanda zai tuƙasa saidai ya tuƙa kansa danni bazan zama direbar saba, ɗazu ma Sa'a yaci,
Barazana ce ta miƙe tsaye tare da cewa "Kunsan me nayi kuwa na turawa ubansa videon nan fa yanzu dan haka muhaɗa tarkacen muyi gaba,
"FASHION...! kinsan kwa me kikayi amma dai ba da number ki ba ko,
Babayn Baby tayi tambayar cike da ɗan zaro ido...
Dariya tayi tace sai kace yarinya irinki me tunanin ƴan yara,
Harara ta watsa mata tace "wallahi tunanin yafi naki,
"Hmmm da kamar wuya kam saidai zan yarda idan kikace naki yafi nawa a fannin soyayya amma bayan nan babu ta inda zaki fini,
Yanayin ta ne ya sauya loƙaci ɗaya take kuma ƙwalla ta cicciko mata ido dan haka sai kawai ta juya ma ta fita daga gurin da kallon suka bita, suna me jinjinawa wannan halin nata, da badama kayi zancen soyayya a gaban ta shikenan zaka fama mata ciwon ta.
Ɗaya daga cikin su tace "Haba ZEE me yasa zakiyi mata wannan zancen bayan kinsan dai halin ta, yanzu in bamuyi Sa'a ba sai takai gobe tana abu ɗaya,
Dariya Barazana tasaki tace "Rabu da ita zamu shirya wallahi hakan nan nake so inga tana kukan abun dariya yake ban, matar Baby a gidan Babyn ta Allah ya shirye ta....
Beenish tace "Daman ke ai haka kika iya inbanda kisa mutun a gaba babu abun da kika iya gaskiya ki rage kinsan dai abun yana hoting ɗinta bai kamata kiringayi mata haka ba,
"Allah sarki ƙawata bari inje in rarrashi abata kunsan dai ba'a shiga tsakanin mu ko inma mutum ya shiga shi zaiji kunya bari inje ku fito dashi, nasan ko Aunty Babba zata iya sunkuto mana shi da hannun ta me albarka ko babbar mu ta faɗa tana kallon ƙatuwar cikin su, itama harara ta watsa mata kawai dan tasan idan ta biye mata nan zata sata a gaba taita yi mata iya shege da tsokana, saboda ita ƙatuwar cikin tasu beyerabiya ce gata ƙatuwa ga ƙarfin tsiya da take dashi....
Beenish ce tayi ƴar dariya tace Allah ya shirye ki Zeeee wanda baisan kiba ya shiga uku.
"Wallahi ko ɗaya mutum bazai shiga ba bare har uku, tana maganar tana wani irin tafiya kai kace wajen biki take, har ta kusa fita daga wajen Ameela tace "bakiji ba?
Cikin wani irin salo ta juyo tana fari da ido tace ko baki faɗa ba nasani kinsan inkiyar tawa tunda na rufe fuska ai bamaƙi taku me kyau ba, kunsan ko ina muke akwai iya taku,
Ƙatuwar cikin su tace "ai munsani basai kin faɗa ba,
Juyawa ta ƙarayi tace to ke ya kika ganni gaba da baya komai daidai, duk da acikin babbar rigace amma hakan ma wanka ne,
Ameela ce ta shiga tafawa tanayi mata jinjina da babbar yatsar ta......
Juyawa tayi da niyar tafiya sai kawai ta kuma tsayawa tare da juyowa tana kallon Aunty Babba tace ƙawar yimin inyi miki kyaut...
Tun kan ta rufe baki ma Ameela ta shiga cewa "ZEE BARAZANA ZEE FASHION KO BA KUƊI AKWAI IYA TUKU.....
"Bare ma akwai komai tabata amsa ta na ci gaba da takun ta ta fice daga gurin...
Aunty Babba tace "Zee..! Zee..! hmm saidai fatan shiriya.
Ameela tace kunga ta fita dan na matsu mu koma gida wallahi zanyi baƙo,
Harar ta sukayi a kusan tare su ka ce; "A'a kin mata baƙi zakiyi da yawa ba baƙo ba,
Daga nan ba ɓata loƙaci, kamar yanda kuwa Barazana tace haka kuwa sukayi Aunty Babba ce ta ɗaga sa suka fita dashi daga gurin cikin motar sa sukaje suka buɗe baya suka sakasa Aunty Babba ce ta shiga gaban motar sa sai Ameela a gefenta ita kuma Beenish taje wajen ƴan rigima da ta shiga, Barazana ce zata tuƙasu Babyn baby kam tunda ta shiga baya take ta faman kuka koda Zee ɗin tazo ƙin kulata tayi,
A guje suka bar geto area ɗin da suka shigo daɗin tama babu mutane da yawa bayan sun fita daga cikin unguwar suka sami can wajen da ba mutane a gun, sannan sukayi parking motocin nasu, su Ameela ne suka fito daga tasa motar sannan suka rufe sa aciki tare da jefa masa wayar sa kan cinyar sa, suka bar wajen motar suka koma wajen tasu motar, basu damu da hannun sa dake ƙulle ba kawai sukayi tafiyar su, suka bar sa agun,
Ji yayi kamar yayi hauka ga bakin sa da yake a ƙulle ga hannunwan sa a ƙulle kuma ko kaya babu a jikin sa, sunci masa mutuncin da tunda yake a rayuwar sa babu wanda ya taɓa yi masa makamancin sa, abun da yake ƙara kona masa rai shine idan ya tuna mata ne sukayi masa haka sai yaji ya tsani kansa ma gaba ɗaya, zaune yayi a cikin motar shi kaɗai yana ta tunanin mafita dan ko wayar sa bazai iya ɗauka ba bare ya kira gida azo a ɗauke shi.........✍️
_*Ƴan WhatsApp me son group yayi min magana in saka sa dan bazan ringa share ɗin sa tare da link ba saboda bana son mutane su ringayi join batare da karantawa zasu yi ba, gwanda duk wanda yasan karantawa zai yi sai yayi magana ta number ta 08124226526*_
*Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin Su waye su group ku shiga anan zan ringayi kullum, dan gaskiya ba kullum zan ringa posting group group ba sai lkcn da na samu free time.*
*Yawan comment yawan typing idan anaso a ringa ganin update akan loƙaci kuma me yawa to nima sai naga an fara comment in bahaka ba kuma nima sai sanda aka ganni*
Ina fa ƙara faɗa muku tafiyar ta dabance yanzu duk a makafi kuke babu wanda zai gane hanya yanzu sai nayi muku jagora zuwa guri me nisa,
Amma idan kai na dabanne kamar ni to idanunka zasu buɗe da wuri mutafi tare da kai cikin littafi nadaban,
*Zee barazana zee fashion ko ba kuɗi a kwai iya taku.....Haka naji ance nima amma dai banyarda ba ko hakane zainabobi?*
My WhatsApp number 08124226526
Please comment and share, Saboda Allah
[3/5, 11:28 AM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
______________________________
*_episode 3💧_*
💧💦محمدالرسوالله...!💦💧
Bissmillah.....✍️
"A fusace ya miƙe tsaye tare da dukan tebur ɗin dake gaban sa, da ƙarfi ya furta "BILAL..! Never......!!!
Gaba ɗaya mutanen dake gefe gefen sa suma suka muƙe tsaye suna me duban wanda yayi maganar,
"Sir what happen..?? Me yasamu Bilal ɗin bashida lafiya ne?
Ɗagowa yayi yana kallon su yama manta a inda yake, cikin ɗan kiɗemewa tare da fara fita hayyacin sa gaba ɗaya ba nutsuwa a tattare dashi,
Glass ɗin idon sa ya ɗauka yasaka tare da gyara zaman hular kansa, sannan yace "Zama ya ƙare zanneme ku gobe, So, u can go, yayi maganar yana barin wajen yayi waje, ya kusan fita kenan wani yace "Amma sir kamar.....
Juyowa yayi a fusace yace "Amma me? Eh nace zannemeku idan kuma hakan beyiba kowa sai yakama gabansa buƙatar kuce batawa ba, danma kunci Sa'a mtssww ya ja tsaki yana ƙarasa fita daga gurin,
"Oh Allah gamu gare ka wai ɓarawo a hannun mata, ƊAN IJJE baida tausayi wallahi, mutumin nan yagama raina mana hankali wallahi,
"Salisu kade iya bakinka dan maganar nan zata iya komawa kunnen sa kasan shidai kamar me aljanu haka yake wajen jin magana,
"Mtsww ai saidai wani munafukin ya faɗa masa amma babu ta yanda zaiji kuma koma yaji aidai bai isa yayi min abun da Allah beyi min ba, ni wallahi ma na kusa dena zuwa wajen sa, ku da baku da zuciya sai kuyi tazama ana wulaƙan taku mtsw yana kaiwa nan yana ƙafafun sa ya fice daga wajen shima yana ta faman huhhura hanci,
Babu wanda ya ƙara yin magana acikin su suma sukaja ƴan matan ƙafafun su suka fice daga gurin, suna me jinjina ƙarfin hali irin na Salisu ko ɗar bayajin tsoron Ɗan ijje basu san me yasaba kodan baitaɓa kamasa da irin waɗannan maganganun ba ne ya hukuntashi shiyasa yake faɗar duk abun da ya ga dama a bayan idon sa,
************************
"Mutumin da ya fito daga gurin yana fitowa ya nufi inda motar sa take buɗewa yayi ya shiga tare da jan motar da gudun tsinya yabar unguwar cikin matsanancin ɓacin rai.......
Baizarce ko ina ba sai ƊAN IJJE'S house, tunkan yaƙarasa bakin gate ya fara doka horn me ƙarfin gaske, saura kaɗan yabi takan wasu ƴan mata guda biyu dake gefe suna tafiya Allah ya kare su sukayi saurin matsawa ɗaya har faɗuwa tayi a ƙasa saboda sun tsorata,
"Wayyo sannu sister Allah yasa dai bakiji ciwo ba, miƙewa tayi tana karkaɗe jikin ta harda ɗan guntun hawayen ta tace "SIYAMA waye wannan dan Allah yake irin wannan gudun acikin unguwa baya tsoron yayi kisan kai yanzu da bamu matsa bafa takan mu yake shirin bi to wallahi Allah ya isa dan bazan yafe masa ba, wannan ai shiga haƙƙin ɗan adam ne,
"Wallahi haka yake me wannan gidanne babban mutum dashi amma yana abu kamar ƙaramin yaro daga shi har yaransa babu wanda suke ɗauka da mutunci kowa bi takan sa suke saboda suna taƙama da kuɗin da Allah yabasu, bakiga yanda sukeyiwa wata ƙawata dake aiki a gidan ba ƙaramin yaro ya iya bura'uba acikin gidan, gashi bata isa tabar gidan ba inadai suka ɗauke ka aiki ba ƙaramin abune zai fito dakai daga cikin gidan ba,
"Ke Siyama..!! kamar ya bazai bar gidan ba?
Hmm kedai bari kawai idan kinajin labarin cikin gidannan zaki sha mamaki kisha mamaki kisha al'ajabi sannan kisha dariya....
"Dan Allah mu shiga ni na yarda zanyi musu aikin indai zasu ɗauke ni da yaseen sai na nakasasu,
"SHA'IBA dan Allah mubar wannan maganar anan gurin dan bamai yiyuwa bane,
Suna tafiya suna ta surutun su har suka ƙaraso waje Jen gate ɗin dan shi kuwa tuni ya daɗe da shigewa ciki,
Sosai ta tsaya tana bin gidan da kallo, sannnan ta kalli ƙawar tata tace "Siyama shiga gidan nan kamar nayi nagamane me hanani shiga cikin gidan nan sai Allah amma sai na shiga ko za'ayi tsirena abawa kaji sai na shiga,
Taƙaici ma bai barta tabata amsa ba tayi tafiyar ta tabarta a awajen saidaga baya tayi saurin bin bayan ta suka ci gaba da tafiya tare tana me yi mata shirme da shiriritar zance, dan kawai jinta take tanayi mata kallon mahaukaciya.......,
***********************
Yana shiga cikin gidan ya nufi Part ɗin cikin gidan da motar Saida yaje bakin ƙofa sannan ya tsayar da ita tare da ɓalle murfin motar ya fito daga ciki cikin hanzari ya nufi wajen ƙofar kai tsaye, yana zuwa yasa ƙafar sa ya tura ƙofar da ƙarfi....
Duk waɗanda suke cikin falon nan Saida suka tsorata tare da maidai dubansu ga bakin ƙofar,. Gaban wasun sune yayi mummunar faɗuwa sakamako tozalin da sukayi dashi...
"Whare is BILAL!?
Dukansu shiru sukayi dan babu wanda yake da ƙarfin basa amsa,
Da sauri Mubeena tace "Ya ɓata.....,
Ko kallon inda take baiyi ba yaci gaba da takowa cikin katafaren falon da ya gaji da haɗuwa iya haɗuwa komai akwai,
Tambayar ku fa nake babu me bani amsa ne.!? Me yasa kuka barsa ya fita da izinin wa ya fita..!? Yayi maganar cikin ɗaga murya, yana daka musu tsawa. Kowa kamewa yayi awaje ɗaya cike da jin tsoron abun da zai biyo baya duk da ba laifin su bane amma bazai gane hakan ba sai ya haɗa dasu,
JANNAT da bata cikin falon jin muryar sa yasa ta saukowa daga upstairs cikin sauri tare da mayafi akan ta, cikin nuna damuwar tace "Ƴallaɓai ka gafar ce mu sannan ka fahimce mu kabari muyi maka bayani muma bamu san ya fita ba, nima da na fito neman sa zanje na kira police na sanar dasu za'afara binciken inda yake, nasan za'agansa bazai taɓa bata ba acikin garin nan kona su waye su dole su dawo dashi,
"Laifin waye me yasa baku kula da shiba har ya fita baku sani ba, wallahi idan ya mutu gaba ɗayan ku sai na ɗaureku sai nasa an rataye min ku....shin kunsan wane hali yake ciki a halin yanzu ku kalla ku kalli BILAL kunga yanda suka maidashi, ya ƙarasa maganar yana nuna musu videon da aka turo masa,
Ƙara rikicewa sukayi gaba ɗayan su sun rasa inda zasu tsoma ransu ganin halin da yake ciki wasu harda kuka saboda jin tausayin sa ganin suke ma kamar za'ace musu ya mutu, ga kuma furucin da yayi musu idan ya mutu suma duk sai sun mutu,
Da ƙyar ya tsaya ya saurari bayanin su yanda suma Bodyguard ɗin suka basu labari,
Mamaki da al'ajabi da taƙaicin jin waɗanda sukayiwa ɗan sa haka yake ji,
Da ƙarfi yace "MATA..! MATA..! MATANE SUKA KAMASA, mace dai har suka iya yin wannan abun to kuwa sunjawowa kansu bama iya sukaɗai ba gaba ɗaya familyn su sai nasa an ƙulle su, shiru yayi yana ƙara jinjina maganar da yake ganin abun kamar ba gaske ba,
Can ya kuma cewa "Tabbas ina son sanin ko SU WAYE SU? ina son sanin gidajen su
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 44