Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
haka ta barsu hawaye sai zubowa suke daga idanun ta kamar famfo fuskar ta tayi jaa saboda tsabar kuka. A haka Barazana tazo ta tarar da ita, buɗe motar tayi ta shiga tare da rungumo ta, tana bubbuga bayan ta, batace mata komai ba suka ci gaba da zama a haka har saida taji tayi shiru dan kanta sannan, ta rabu da ita tare da cewa ta fito daga wajen ta jasu su tafi gida, haka sukayi exchanging gurin Barazana ta jasu, tunda suka hau hanya kuwa babu wanda yayi magana har suka je gida, Ko da suka shiga gidan kuwa, Su Beenish sun dawo gida suna falo suna ta jiran zuwan su, suna shigowa kuwa suka bisu da kallo. Cikin fushi Beenish tace; Ina Ammun? "Ta tafi" Barazana ta bata amsa. Ameela kam bata kula kowa ba kuma bata kalli inda suke ba duk da tasan su ɗin kallon ta suke amma sai kawai ta wuce ɗaki ta bar su awaje. Da sauri Babyn baby ta yunƙura zata bita Beenish ta dakatar da ita, ta hanyar ruƙo hannun ta, Guri Barazana ta samu ta zauna tana sauke ajiyar zuciya tare da cewa; "ku barta ta fara samun nutsuwa ni bansan me suka tattauna ba dan fita nayi na basu guri, naga itama Ammun idon ta fal da ƙwalla ta wuce mota dan ko haɗa ido dani barayi ba. "Hmmm Ameela bansan wace irin zuciya gare ta ba, duk da itama Ammun na da laifi amma yakamata zuwa yanzu su san me sukeyi gaba ɗaya, wallahi bana son wannan abun da sukeyi duk da kowa na da laifi, "Ai kam dai amma koma meye ina tunanin wannan zuwan ba kamar sauran zuwan da take yi ba, kamar ta canza, tunda kikaga daga ita sai drivern ta take yawo, kuma naga kuɗi a hannun Ameela tunda ta karɓa wataƙil da kwai wani abun a ƙasa, saidai mu jira idan ta sauko ta gaya mana yanda sukayi da ita. "Hmm to ai shikenan, mu bar maganar yanzu, ki zubo abincin dan mu har munci, Baby ke kuma ki zuba ki kaiwa Ameela ki tabbatar taci. "To ta amsa dashi tana miƙewa ta nufi hanyar kitchen ɗin har taje daf da shiga, Barazana tace, "Baby! Ni ma ki zubo min. Itama da to ta amsa sannan ta ƙarasa shiga kitchen ɗin nasu......, *$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$* *GHAMBURJ* ___Wata ƴar tsohuwa ce take ta sambaɗa gudu a tsakiyar wani ƙaton fili da baka ganin gida a guraren sai bishiyu kawai suma tsalli tsalli, Kai baka ce ta tsufa ba, ganin yanda take gudu, dan a ƙalla zata kai wajen shekara sittin da wani abun, jinkin ta ɗan tsamurmiri amma a dake take, kuma tana da ɗan tsawo, jikin ta sanye take da riga da zani sai wani yalolon mayafi da ta yafa akai, ga wata jaka ƙatuwa dake saƙale a jikin ta, yayin da wasu ƙartin maza guda uku suke rufa mata baya suna binta. Gudu take felfalawa kamar ba gobe, suma kuma basu fasa bin ta ba, ganin tayi musu nisa kuma tazo inda zata zo yasa ta tsaya kafin su ƙaraso daf da ita tayi sauri ta cire mayafin ta tare da wurga musu shi, cire jakar tayi tare da wurga ta wani ƙaton ruwa dake ɗan nesa da ita kaɗan tana dai iya hango sa, sannan ta cire rigar jikin ta ta tsige zanin dake jikin ta, sai gata daga ita sai riga da wando wandon ma iya gwaiwar ta, ɗan kwalin kanta ta zare tare da ƙara gyara parking ɗin gashin ta da furfura ta gama cinye sa, ɗan kwalin da baida girma ta ɗauka ta rufe rabin fuskar ta dashi sannan ta ɗaga rigar ta saiga wasu ƙananun wuƙaƙe guda biyu, zaro su tayi ta riƙe su a hannuwan ta dama da hagu sai kawai ta tsugunna agun ta sunkuyar da kanta zuwan su kawai take jira, Gudu suke suma ɗaya daga cikin su yana gudun yana waya, suna zuwa daf da ita sakawai suka ka burki a gun suka kasa ƙarasowa ganin yanda ta ɗago tana kallon su idanun ta kawai suke gani gata da manyan idon yanayin yanda take kallon su yasa suka ga kamar ba mutum ba, "Ku taho! Ku taho!! Ku taho mana...! ta faɗa tana daka musu tsawa tare da miƙewa tsaye, "Ki sauke wannan wuƙar kar ki kuma tunanin guduwa ki tsaya anan gurin, ɗaya daga cikin su yake gaya mata haka. Dariya tayi da ƴar murayar ta da bata fita sosai tace "gani kuzo ku kama ni mana tana faɗar haka kuma tayi cilli da wuƙaƙen tana dunƙille hannun ta alamun su taho ta shirya da hannun ta. Matsawa suka fara yi kusa da ita, tare da rarrabewa zasuyi mata tara tara, nan kwa ta fara wahalar da su tana zille musu, suna cikin haka kawai sai taga yuyar ƴan sanda suna tunkaro su, Da baya da baya ta fara ja tana tunkarar wajen makeken ruwan nan, da ta wurga jakar, Da sauri ƴan sandan duk suka ƙaraso wajen suma suka shiga bin ta, wasu daga cikin sune suka zaro bindugu. Juyawa tayi zata gudu, ɗaya yace kina ɗaga ƙafar ki daga nan gurin zan harbe ki, ki tsaya anan wajen. Tsayawa tayi tana ɗaga hannunwan ta sama, takowa suka ci gaba dayi suna tunkarar ta ganin sun kusa yasa ta kuma yin taku uku ta matsa daga kusa dasu, "Kar ki kuma motsawa daga nan gurin ki tsaya anan, amma bataji ba da wayo da wayo suna mata barazan tana kuma matsayawa har saida taji ta a inda take son jin ta, Suna daf da ita tazarar su bata fi taku huɗu ba, kawai sai ta ɗaga hannunwan ta sama tana juya musu baya, duk basu san me ta tsara ba dan basu san da ruwa ba agun dan ya ɗanyi zurfi idan baka san da shi ba bazakace da ruwa ba agun. Tana kallon su ta gefen ido tsiran su baifi taku ɗaya ba, kawai ta daka uban tsalle ta faɗa cikin ruwan nan jikake fumm... Har ta ɓace, dan duk a tsorace sukayo gurin ruwan suna ta faman leƙe amma basu ga ko motsin ta ba. Turus duk suka tsaya kowa mamaki ya gama kashe su, Ɗaya daga cikin su ne yace; "To ku ya kai kuka bari har ta ɗauki jakar ta gudu baku kamata ba ku da angama tsara komai daku akan kar ku bari kowa yagan ku sannan duk wanda yazo ɗauka kuyi sauri ku kamasa kar ku bari ya gudu, kuma ina bindigar hannun ku meye amfanin baku ita da baku harbe ta ba ko a ƙafane haka akai daku? Sai faman magana yake musu me tafe da faɗa dan ransa ya ɓaci rashin kamata. "Sorry Sir wallahi bamuyi tunanin ita ce me ɗaukar kuɗin ba, bayan munyi waya munce munzo sai aka ce mu ajiye ta agun sannan mu ajiye bundugun da muka zo dasu in ba haka ba kuma to mu koma hakan yasa muka a jiye a ƙasa tunanin mu idan sunzo ɗauka sai muyi saurin ɗauka mu harbesu, amma sai kawai mukaji ihun wannan matar muka juya da sauri muka ga ta tsugunna tana ruƙe ƙafar ta hakan yasa muka bar bundugun a wajen muka tafi wajen ta, muna daf da zamuje gurin kawai ta miƙe cikin sauri da bamu ankara ba tazo ta ɗauke bundugun sannan ta saita mu tace duk wanda ya kuma motsawa daga inda yake sai ta harbe mu, dole muka tsaya, ta saita mu da ɗaya sauran kuma duk zare musu bullet ɗin ta zubar tare da jefar da bundugun saida take saitin jakar sannan ta ɗauka ta fara gudu sai loƙacin muka bi bayan ta muma, bamu san na loƙacin da ta jefar da ɗayar bindigar ba kawai gani mukayi bata hannun ta, muna gudun har muka zo nan kaji yanda mukayi.. Iska ya shaƙa tare da furzar da me zafi daga bakin sa, yana dafe kansa yana yarfa hannu tare da cije baki, ji yake kamar ya harharbe su.... "Amma baku da hankali ku zaku je gurin ta, yanzu gashi nan kun jawo mana asara, yanzu me kuke so muyi idan mun koma, Inna lillahi wa Inna lillahi raji'un kuna so mu koma gida yanzu babu yaran babu kuɗin kuma babu wanda muka kama sunyi ci riba biyu kenan wannan uban maƙudan kuɗi da aka basu, sun ƙwace kuɗin kuma basu bada yaran ba wannan wane irin abu ne.... Su tsuru-tsuru sukayi gaba ɗayan su kowa na tunanin mafita, ɗaya ne ya kuma cewa; "Ogah kuma daman kasan yace shi kuɗi ba damuwar sa bace dan haka kar ayi wani yuƙurin kaiwa waɗancan farmakin kama su kawai mu basu kuɗin su bada yaran kar ayi wani abun da zaisa su hana yaron gashi kuma abun da yake gudu ya farun ya faru.. "Ai ba laifin mu bane danni wannan abun nafi ganin laifin commissionana tunda duk shi ya tsara mana hakan gashi kuma ba'ayi nasarar komai ba...... Nan dai sukai ta kace nace ɗin su su kaɗai sun kasa samun mafita dole suka kaɗa bujen su suka koma gurin motocin su suka tafi gida kowa da zulumin abun da zai faru idan sun koma...... Iyo kawai take acikin ruwan nan saboda tsabar ƙwarewar ta ko motsin ruwa ta sama baka gani, kamar kifin ruwa haka take yawo cikin ruwan, ba ƙaramar tafiya tayi ba a cikin ruwan, sannan ta kawo bakin gaɓa, tana fitowa ta tarar da su a tsatstsaye suna jiran ƙarasowar ta.... Ɗaya daga cikin su ne ya ɗanyi murmushi yace; "Hajja Mama ai mun ɗauka sunyi gaba dake ne da mukaji shiru yayi yawa, Hannu tasa ta share ruwan fuskar tana girgiza kanta tana girgizar da ruwan dake kanta. "Me yin hakan kuwa ba ƙaramin shiri zai yi ba, "bani kaya tana miƙa wa na gefen sa hannu. Bata yayi sannan suka juya baya. Suɓalle wandon tayi sannan tasaka wani sket ɗan ƙarmin shima baikai mata har ƙasa ba, sannan ta cire rigar ta sauya wata, tana gama sakawa ta ɗanyi musu gyaran murya sai loƙacin su juyo. Wata ƙatuwar jacket ya kuma rufa mata ta zura a jikin ta, sannan ya bata wata hula me hat (hula me faɗi, irin ta ƴan chaina kun gane ta) sannan ta karɓi glass ta ƙwama a idon ta, sannan ta karɓe jakar da ta cillo musu ɗazu tayi gaba, binta suka yi a baya. Tafiya kaɗan sukayi suka kuma zuwa wajen wani ƙaton ruwan, jirgin ruwa suka shiga me shegen kyau, sannan matuƙin sa yaja sukayi gaba. Nan ma saida sukayi tafiya me ɗan tsayi sannan suka kuma zuwa bakin gaɓar, sauka tayi daga cikin jirgin ita kaɗai, ta kuma nufar wata hanyar, su kuma daga nan suka juya basu bita ba. Daidai wani waje ta tsaya tare da tsugunnawa ta kwashe ƙasar dake gurin saiga ƴar ƙaramar ƙofar ƙasa, ɗaga ta tayi ta buɗe matattakalar ta farawa takawa tai tashiga har saida ta sauka ƙasa sannan ta kuma yin gaba can kuma sai ga wani gida daga nesa, haka ta taka taje har bakin gidan sannan ta buɗe ƙofar tana buɗewa tayi karo da wata kyakkyawar mage me shegen tana ganin ta ta tsugunna tana murmushi ta shafa kanta sannan ya ɗauke ta ta rungume ta, tana jikin ta ta miƙe ta nufi wani ɗaki tana shiga ta sauke ta, ɗaki ne madaidaici babu komai a cikin sa sai kujera guda ɗaya da ɗan table a gaban kujerar, sai jikin bangon da yake taf da hotunan mutane wani bangon hotuna ne an saka musu jar maka wasu kuma an kansile su, wani bangon kuma an saka musu good da green, wasu kuma anja layi akan fuskokin su. Bayan ta ajiye jakar ta ƙarasa jikin wani bango ta ɗau kama tayiwa wani good amma me lanƙwasa, sannan ta kuma matsawa jikin wani kallon hoton take tare da saka hannu ta shafa fuskokin su tana sakin wani ƙayataccen murmushi wanda kana ganin sa kasan daga ƙasan zuciyar ta yake fitowa, hannun ta ne ya tsaya akan wani hoto tama murmushi tace; "sarkin rigima, gaba ta ƙarayi da hannun ta wannan karon kwa sosai tayi murmushi har haƙoran ta na fitowa tace; "To basawa Sarkin ƙarfi, ga kuma masoyiyya....hakannan taitabin su tana murmushi tana shafa hotunan.....✍️✍️✍️ [3/5, 11:53 AM] Yaya Azeema: *SU WAYE SU...!?💦* *_(Who are they...!?)_* _💦Story and writing💦_ 💎 *🌬️Yaya Azeema😎* (THE WRITER OF 💅SARKI SAMEER 💅) ______________________________ *_episode 20💧_* 💧💦محمد لرسول الله...!💦💧 Bissmillah.....✍️ ____Ta daɗe a gaban hotunan kafin ta matsa daga gurin, jakar ta kuma ɗauka sai ta nufi wani waje kai kace gurin bango ne kaɗai amma tana yaye wani abu a gun sai ga wata ƙofar ƴar ƙarama da bata fi wucewar mutum ɗaya ba, kuɗaɗe taf a cikin ɗakin jakar hannun ta ta buɗe sannan ta shiga irga kuɗin tana jere su akan wata kanta ɗakin babu komai a ciki kawai zagaye yake da glass anyi sa hawa hawa kuma ko wane hawa da kuɗi akai, jere su ta kumayi tsaf sannan ta maida ƙofar yanda take ta rufe, Ɗaukar magen ta kumayi ta ɗorata a kafaɗa, sannan ta fita daga ɗakin, a falon ta tsaya tare da samun kujera ɗaya ta zauna, tana faman shafa bayan magen da hannun ta, Sake miƙewa tayi ta nufi wani ɗan siririn corridor wanda jikin bangon duk glass batayi wata tafiya ba ta yaye wani maroon ɗin labule tare da zuge wani glass ɗaki ne tamƙameman gaske, sai gadaje a cikin sa hawa hawa kamar irin na ƴan boarding school saidai sun banban ta da irin su domin waɗannan masu kyau ne na katako kuma da girman su ba ƙananu bane duk guda ɗaya hawa biyu ne a saman sa, a ƙalla dai zasu kai wajen guda goma kowanne da hawan sa. A hankali ta ƙarasa bakin wani gado dake can jikin bango, tsugunnawa tayi tana kallon sa tare da shafa kansa, tana ɗan murmushi, a hankali tace "sleeping boy, har yanzu ba'a tashi ba. Kamar yasan me take cewa ya wani haɗe fuska alamar shagwaɓa tabi jiki, yana ɗan turo baki gaba, cikin baccin ya jawo hannun ta ya haɗa da filon dake hannun sa a riƙe ya haɗa su ya kuma ɗora kansa akai yana gyara kwanciya, tare da warwara ƙafafun sa sukayi ɗaiɗai duk girman gadon amma duk ya kusa cinye sa, Kallon sa kawai take fuskar ta cike da murmushi, da dayan hannun ta ta shafa kwantaccen gashin sa da ya sha gyara sai sheƙi yake, Ta daɗe agun bata tashi ba kafin ta samu ta lallaɓa sa cikin dabara ta zare hannun ta sannan ta miƙe daga gurin, gadon saman tabi da kallo sai suka haɗa ido da wanda ke kwance agun, gira ɗaya ya ɗaga mata yana mata murmushin gefen baki, daƙuwa ta jefa masa tace yaron nan ka rainani nace ka dena yi min irin wannan kallon kaƙi ka daina ko? Girar ya kuma ɗaga mata yana miƙewa zaune tare da zuro ƙafafun sa, yana bin nakan gadon da kallo yana ya tsina fuska a hankali cikin taɓe baki ya ce; Hajja Maaa jifa yanda wannan yaron yake bacci gatan da kike masa ko a gidan su baya samu gatan yayi yawa ni kuma ko rabin sa bakya min to wallahi gida zan bar muku kun rabani da iyaye na kun kawo mu kuna azabtar dani to Allah sai kun maida ni gida kuma yau yau ɗinnan, tallaƙe masa ƙeya tayi tana cewa ai ƙofa a buɗe take sai ka dawo, Haɗe rai yayi yana tutturo baki, ya duro kan gadon ƙasan, akan na kwancen ya faɗa yana danne sa da mugunta, Bawan Allahn ka me makon ya tashi saboda nayin gardi da yaji sai kawai ya sa hannu bibbiyu ya rungumo sa, Haushi ne ya kamasa ganin ya wani rungume sa sai kace mace, ya fara ƙoƙarin ɗaga sa, amma sai kawai ya kuma riƙo sa, yana magana ƙasa ƙasa.... Shiru sukayi danjin me yake cewa sai kawai sukaji yana cewa; "Please one more please don't leave me again, kiss me kiss me yana faɗa yana jawo fuskar ƙato zaiyi masa kiss. Shi kuma cikin zaro ido da mamaki duk yama fara kiɗimewa yana ƙoƙarin ƙwacewa amma ya kasa, Hajja Maa kuwa babu abun da take musu sai dariya da take ƙunshewa. Bai ankara ba kawai yaga yayi juyi dashi ya koma ƙasan gadon shi kuma yana ƙoƙarin hayewa kansa, har ya hau kansa idon sa a rufe kuma baidai sambatun da yake ba, "Beab Please don't go don't go, yana faɗa ana sake kai bakin sa kan fuskar sa, Ganin dai da gaske yake bashi da hankali in ya zauna a banza gardi zai sumbace sa, daddagewa yayi da iya ƙarfin sa ya buga masa duka a damtsen hannun sa yana tura sa baya, ya faɗi kan gadon, sai loƙacin ya ware idon sa akansu yana sakin ƴar ƙaramar ƙara yana ɓata fuska kamar zai fashe da kuka... "Banza ɗan iska wallahi da ka sumbace ni sai na kashe ka kama rasa wanda zaka danne sai ni ban girme ka ba, yana maganar yana kai masa duka, Hannu yasa yana karewa dan ba ɓata loƙaci ƙwaƙwalwar sa ta zayyano masa duk abun da yayi shi kansa saida yaji kunya ta kama sa, ga Hajja Mama dake kansu tana musu dariya, "Wallahi Bilal bazan yafe maka ba Allah ya isa dan ka cuce ni banza me kama da mata, ɗan daudu kawai, Dafe kansa kawai yayi cike da taƙaicin kansa bai iya cewa komai ba sai kawai saukowa daga kan gadon da yayi yana ya mutsa gashin kansa, yana sakin tsaki, "Wallahi Hajja Mama kin lalata yaron nan taɓarar sa ta fara wuce gona da iri aure yake so tunda har ya fara mafarkin ƴan mata, Sosai take dariya ta ce; "Allah ya shirye ka Zaid baka da kirki ai kane da tsokana ni yamin daidai da yayi maka haka, gobe ma sai ka kuma danne sa, sai kaje wataran ka karya masa ƙafa ma da wannan shegen jikin naka irin na ƴan can garin.... Haushi ne ya ishe shi ya tashi fuuuu ya nufi hanyar banɗakin da Bilal ya shiga, takun sa biyu ta sa hannu tajawo sa ta baya ta mayar da shi kan gadon tace; "Allah ka taɓa sa ni da kai ne sai naga me ƙwacen ka a cikin gidan nan.... Tunda ta fara maganar kawai hannun ta yake kallo da ta jawo sa da hannu ɗaya duk girman nan nasa ya ɗanyi mamaki amma sai ya basar ya danne mamakin a ransa. "Kana mamaki ko to kaɗan ma ka gani inka shigo hannu na dakan sakwara sanyi maka... "Lalle kin so ki ziyar ci lahira loƙacin baiyi ba, faɗa da ni ai ba duk kai ba, "Hmmm kawai tace masa tana girgiza kai aranta tana cewa yaro yaro ne, a fili kuma sai ta ce; "ka tashi muje ka ɗauko muku abincin ku, kuma kar ka sake ka taɓa min Boy ɗina, komai ya wuce. Ƙura mata ido yayi ko ƙiftawa bayayi har ta gama bayanin bai ɗauke idon sa akan ta ba, saida ta kai ƙarshen zancen nata sannan ta lura da kallon da yake mata, sai ta haɗe rai tana watsa masa hararar tace "Zaid.! Zaid.!! Zaid.!!! Sau nawa na kira sunan ka? Bai amsa mata ba kuma bai daina abun da yake matan ba, "Wallahi ka fita a ido na in rufe wai yaushe kamin sannin da har ka rainani haka, "Tun ranar da kika sato ni. Duka takai masa ya goce yana dariya ya miƙe tsaye yana jan hannun ta suka fita daga ɗakin..... Bilal daman fitar su yake jira, suna fita kuwa ya fito ɗaure da towel a ƙugunsa, koda ya shigo dakin kan gadon ya koma ya zauna, har yanzu jikin sa bai dawo normal ba, dafe kansa yayi tare da ce wa; "Why you want to come my dream ba dama inyi bacci sai kin addabe ni, mtsww ya ɗanyi tsaki, yana furzar da iska daga bakin sa, "Bea ya kuma furtawa a hankali, tare da lumshe idanun sa yana sake buɗe su, can kuma sai ya saki murmushi tare da kuma faɗawa kan gadon ya kwanta yana sake rufe idanun sa, a haka yana ta tunani bacci ya kuma yin gaba dashi daman ya lafiyar kura bare ta ƴayan ta... (Kunsan yana tare da cutar bacci ga kuma shauƙin Bea da bamu san a inda ya samo ta ba) Zaid ne ya shigo ɗakin cikin sauri yana shigowa yayi turus yaja ya tsaya yana kallon sa, cikin sakin baki ya ƙaraso gurin yana cewa Allah yaye maka Bilal daga fitowa sai komawa bacci ko abinci ma bazaka tsaya kaci ba, duka ya ɗala masa a cinya zumbur kuwa ya miƙe zaune yana sosa gurin, idon sa har ya ɗan cicciko da ƙwalla cikin murayar kuka yace "Zaid wai meye matsalar ka dani ne ka takurawa rayuwa ta, to Allah ya isa kaje kai da Allah yana faɗa ya mike tsaya yana cika yana batsewa, dan sosai yaji zafin dukan da yayi masa, "Banza me sumbatar namiji jarabar taka har baka tantance wanda ka riƙe macece ko namiji, sai ka faɗa kace kai aure kake so ayi maka aure tunda har kakai munzalin ka fara mafarkin ƴan mata... Banza yayi masa har yagama kwakwazon sa da surutan sa bai tanka masa ba, daga ƙarshe ma yana saka gajeren wando wandon da ƴar singlet ya fice yabar sa a ɗakin....., Yana fita shima yabi bayan sa yana bambamin yaƙi kula sa, har saida Hajja Mama ta dakatar dashi sannan ya rabu dashi, Zama yayi akan center capet ɗin dake tsakiyar falon, Hajja Mama ce ta zuba masa abinci sannan ta ɗauki cokali da kanta ta ringa basa abaki, saida taga Zaid ya zuba musu ido sannan tayi murmushi tace kaiɗinne ka girma shiyasa bana baka zo ka karɓa. Watsa mata harara yayi yace; "sai yanzu kika tuna dani bana ci... Tashi yayi daga gurin yana kiran KITI..! KITI..! da gudu wannan kyakkyawar magen ta taho gurin sa tsugunnawa yayi ya ɗauke yana mata wasa ya nufi wani ɗaki da ita dake cikin falon..... Saida ta gama basa yaci ya ƙoshi sannan ta rabu dashi ya kora da ruwa, zama sukayi suna ta hira agun tana janye shi da zance saboda kar ya koma bacci, daga baya ma shima Zaid dawowa yayi suka ci gaba da hirar tare kamar ma wani abu bai faru ba, saida sukayi sallar magriba da isha'i sannan ta sa duk suka koma ɗakin su ta tura musu magen, tace su kwanta amma gobe da safe baza su ganta ba, sai wajen yamma zata shigo duk abun da suke buƙata zata sa a kawo musu... Badan sun so ba haka suna gani ta fita daga ɗakin kuma ta ƙullo su ta waje daman haka take basa fitowa sai tana nan, Tana rufe su ta fita daga falon gaba ɗaya, wata hanyar ta sake nufa, wani ɗaki ta tura shima kamar yanda wancen yake haka yake saidai shi gadajen su na ƙarfe ne kuma basu da girma, ga mutane ne da yawa a ciki duk sun kwanta sakamakon dare da yayi, ƙofar ɗakin tasu ta ƙarfe ta samu wata guduma dake gefen gurin wajen ajiye ta, buga musu tayi da ƙarfi sai wajen huɗu ai ba shiri duk suka farfarka wasu na durowa daga gadon, daman

Chapter 14 of 44