suka ci.
Alhaji Ɗan Ijje ne ya miƙe yana goge bakin sa dan ko abincin kirki bai ci ba, daman yanzu baya wani iya cin abinci kirki saboda ba kwanciyar hankali a tattare da shi, rabon shi da cin abinci arziƙi tun ranar da aka rasa Bilal.
Yana miƙewa wayar sa tayi shiga yin ruri da sauri ya zaro wayar yana karawa a kunne, da ƙarfi yace "Me! Ba....n..ji wayar ce ta suɓuce daga hannun sa, ku kunna min tashar labarai Allah yasa dai ba gaskiya bane abun da naji kuyi sauri dan Allah!
Dukan su cikin tashin hankali suka miƙe tsaye jin abun da yace da sauri Hafsa ta kunna tana kaiwa tashar labarai, nan suka ga wani guri na ci da wuta ana ta fito da gawawwakin mutane ga me sanarwa na aikin shi.
_"Yaude Allah yayi an samu wasu masu ƙarfin zuciya sun farmaki gidan ƴan kidnapping a wani daji wai shi Ghamburj da ba'asan da shi ba, wanda sun daɗe suna aikata wannan ta'asar kuma ana kyautata zaton duk wani wanda ya rasa ɗan uwansa da aka ɗauke da sunan kidnapping to fa nan gurin ake kawo sa saidai kuma anyi asarar rayuka da yawa yawancin su ma kowa ya mutu dan har yanzu ba'a samu mai rai ba, daga ciki kam harda masu gidan domin hukuma tasa an bincike gidan amma ba'ayi nasarar kama ko mutum ɗaya ba, wasu an harbe su wasu kuma boom ya tashi dasu, babu abun da zamu ce saidai mu kuma yiwa wannan gwamnatin jinjina bisa ga jajircewae ta wajen kawo ƙarshen su, adoran duniya waɗanda suka rasa yaran su kuma Allah ya basu haƙurin rashi, saidai kuma komai yazo ƙarshe hakan bazata kuma faruwa domin gwamnati zata tsaya tsayin daka da kuma ci gaba da bincike akan waɗannan azzaluman, nan na kawo ƙarshen shiri bisalam_
Faɗuwar abu da suka ji ne duk yaja hankalin su kan komawa gurin, Alhaji Ɗan Ijje ne ya yanke jiki ya faɗi duk kansa su ka yi, kowa hankalin sa a tashe, suka shiga girgiza sa suna kiran sunan sa amma bai motsa ba, Khattume ce tace su ɗauko sa a tafi asibiti ,mazan ne suka shiga ƙoƙarin ɗagasa, matan kuma suka fita dan ɗauko mota cikin ƴan mintina suka saka shi a mota sukayi asbiti dashi....
Maryam hankalin ta a tashe ta nufi ɗakin su, dan ta gama kallon komai, tana zuwa ta ɗauki wayar ta, ta kira Hajiya Dannar, tana ɗagawa tace "Hajiya kinji labarin da naji yanzu, wai gidan Ghamburj ya kama da wuta! Yanzu haka maganar da nake miki Ɗan Ijje ya faɗi an tafi da shi asibiti.
Anmu na zaune aka kujera Maryam takira ta daga can itama hankalin a tashe ta miƙe tsaye tare da cewa "a'a wallahi banji labari ba, amma bari in kira Hajja Mama inji meye gaskiyar maganar.
Maryam tace to yauwa dan Allah yi sauri, hankalina ya tashi wallahi dan naji ance ba'a samu kowa da rai ba, abun ya tsorata ni yarannan duk sun mutu kenan innalillahi wa inna ilaihi raji'un.
"Ki kwantar da hankalin ki bana jin harda ita, tana faɗara haka ta kashe wayar tare da kiran layin Hajja Mama saidai a kashe layin baya shiga, wani layin ta kuma kira ana ɗagawa tun kan tayi magana daga can ɓangaren na jiyo wata murya tana cewa "sai haƙuri kinga abun da nagani kenan? Da sauri Ammu tace dagaske ne daman Hakka Mama fa da yarannan?
Daga can aka ce "wallahi saidai mu ƙara yin bincike dan ina tunanin a garin da taje wajen Musbahu, jiya munyi waya da ita tace komai ya kusan zuwa ƙarshe, da daddare kuma tayi min message wai ansamu matsala yasan komai, dan haka mu tayata da addu'a, tun a loƙacin na kira layin ta amma yaƙi shiga, nima tun loƙacin hankalina yake a tashe, ban gama tsorata da lamarin ba kuma saida naga labarain nan.
"Yanzu meye mafita taya zamu gano gaskiya, yanzu gashi yarannan sun mutu kenan tunda bata gidan aka farmaki su.
Daga other side aka ce mata "to abun dai yana buƙatar nazari saidai mu tashi tsaye sosai sannan kuma sai kunyi taka tsantsan dan yanzu duk inda kuke zai fara nema.
Ammu tace "Tom shikenan Allah ya shige mana gaba Allah yasa Hajja Mama tana lafiya, dan akwai abubuwa da yawa da ita tasan kansu.
"Hmm muna da aiki a gaban mu, duk da nasan ko me zasu yi mata bazata faɗi abun da suke son ji ba, saidai zasu iya wahalar da ita sosai duk da bana tunanin zai kasheta.
Ammu ta numfasa tare da cewa "Allah ya shige mana gaba, sai anjima Maamy, nan sukayi sallama ta sauke wayar jikin ta a mugun mace, dan kasa ci gaba da tsayiwar, dan ji tayi kanta na neman juyawa, da ƙyar ta lalibi guri ta zauna, tana kuma kiran Maryam ta ce "Maryam akwai matsala fa... Nan ta sanar da ita duk yanda su kayi...
*Wlh readers laifin kune duk yanzu sakin ƙauna kuke min bakwa comment shiyasa typing ɗin duk ba wani armashi, kuyi riƙon ƙauna mana ko komai ya tafi daidai, da na fara sai inji nagaji😤*
_Zanyi muku riƙon ƙauna idan kukayi min inkwa kuka sake ni sako sako to nima ai ga alama nan kuma ganin kalar riƙon da nake muku😎🥺😉_
Wai ƴan face book danna like ma wuya yake muku ne, a ƙala sama da mutum 200 suna karantawa amma sai kaga likes wai 50, liking bawai comment ba, to zamu sa ƙafar wando ɗaya da ku.
Ku kuma ƴan Whatsapp na dawo gare ku kuma masu yin ƙalilanne yanzu sai baifi mutum uku huɗu bane zasu fito ayi comment da su ko, shima sai mutuniyar ta fara yi zasu taya ta.
FATOU GOLD ce kawai tafi yi min riƙon ƙauna wallahi, bata gajiya kullum ita ce kan gaba, wasu kuma idan sukayi yau bazasu yi gobe ba, kuma suna group ɗin saidai su karanta suja ƙofar bakin su, kwanaki da bata hau online ba babu wanda yayi min comment gidan sai yayi shiru ma.
FATOU GOLD ina godiya da irin gudunmawar da kike ban hakan na ƙaran ƙarfin gwiwa wallahi ina jin daɗi sosai Allah ya bar ƙauna❤️🥰🔐
Wasu da yawa sunayi wallahi kuma ina godiya sosai, Allah yabar ƙauna tsakanin mu wallahi duk ina yin ku over over ❤️kar kuga banyi tagging ɗin sunan ku ba, ku kanku kunsan tanayi sosai fiye da kowa, akwai mutanen da yawa da zanyi tagging ɗinku yanzu dai kawai na fara da ita ne.
*Duk meson na saka shi a group ɗin Su waye su yayi min magana, ta wannan number 08124226526 iya littafin su waye su, dan Allah kar wanda ya min magana akan meman wani littafin, ko yace min in saka sa a group ɗin littattafai, to wallahi duk wanda yayi min magana bazanyi reply ba, sbd an saba yi min irin haka Ni ga abun da nace amma sai wasu si ta tambayata in tura musu littattafai dan Allah ku daina bana so ba littattafai nake turawa ba nawa kawai nake turawa*
_Ƴan facebook kuma kuyi searching ɗin su waye su hausa novel group kuyi join akwai a ciki tundaga farko har inda aka tsaya, dan ba kullum zanna posting a kowane group ba_
[4/25, 12:52 PM] Yaya Azeema: *💦SU WAYE SU...!?💦*
*_(Who are they...!?)_*
_💦Story and writing💦_
💎
*🌬️Yaya Azeema😎*
(THE WRITER OF 💅SARI SAMEER💅)
________* 08124226526*_______
*_episode 49💧_*
💧💦محمد لرسول الله...!💦💧
*Duk me son littafin su waye sudaga farko zuwa inda aka tsaya da kuma 💅sarki sameer💅 complete, yayi min magana👉08124226526*
_Bismillah..✍️_
$$$$$$$$$$$$$
___Su Salama na gama cin abincin bayan kowa ya dawo hayyacin sa, sai loƙacin Salama ta basu labarin abun da ya faru sukai tayiwa Bilal dariya, har saida suka ƙullar dashi.
Zaid ne ya kalli matar yace "to daga ina kike da kika zo kika kwanta a cikin kango?
Ɗan murmushi tayi tace "nima bansan daga ina nake ba, kuma bansan inda zani ba, kawai dai yawo nake ina so in samu aikin ne, har yanzu bansa mu ba shiyasa nazo nan na kwanta idan safiya tayi sai in sake komawa cikin garin ko zan samu.
Duk da rashin fahimta suka bita da ido jin abun da tace, babba da ita amma tace batasan daga ina take ba, Salama ce tace "amma taya akai baki san daga inda kike ba da girman ki.
Shiru tayi kamar bazatayi magana ba tana tunanin me zata ce musu, can dai ta ɗan numfasa tare da cewa "kidnapping ɗina akayi shine na samu dama na gudo na daɗe a hannun su shiyasa yanzu bansan inda duka ƴan uwana suke ba, saboda haka na fara neman inda zan samu aiki.
Faheema tace "kin zama mu kenan muma hakance ta kasance da mu muka fito daga wani daji, saidai mu gaskiya munsan garin mu, da inda ƴan uwan mu suke.
Zaid ya ɗora da cewa Allah sarki kinban tausayi yanzu haka zaki ta rayuwa ke kaɗai kenan bakisan kowa naki ba.
Kai kawai ta ɗaga musu dan kallon yara take musu bazata iya zama ta gaya musu ko wacece ita ba.
Zaid ya kuma cewa, "to ko kaɗan bakisan sunan garin da kike ba kafin ayi kidnapping ɗin naki da sai mu baki kuɗi ki koma.
Jinjina kai kawai tayi jin yanda ya tsare ta sai tambayoyi yake mata, a hankali tace "na manta komai kuma koda na koma ma bazan samu kowa ba saboda nafi shekara goma sha biyar a hannun su.
Duk zaro ido sukayi jin adadin shekarun da ta ambata.
Da sauri Salama tace "fin sha biyar fa!?
"Ɗaga musu kai tayi tana ƙara tabbatar musu da hakan.
Faheema tace "Tabb wannan ai inajin ma ƴan uwanki sun manta da ke, to amma dai kina da ƴaƴa ko?
Ɗaga musu kai tayi kawai, cike da fara gajiya da tambayoyin su.
Salama tace "Allah sarki, amma shine zakice zasu manta dake ai baza su manta da ke ba nidai againina gwanda ki yi tunanin sosai ki tuna sunan garin sai mu raka ki.
Murmushi tayi tace "a'a na hutar daku, ni yanzu zan shiga cikin garin ma inci gaba da neman aikin dan bazan iya tuna komai ba, dan daman iyayena sun daɗe da mutuwa, mijina ma haka ya mutu, dangin iyayena kuma bansan inda suke ba, ƴaƴan da na haifa suma nasan an sace su bansan ta inda zan fara neman su ba, shiyasa nace muku bansan inda zani ba, Ni kaɗai na rage a duniya banda kowa banda komai, ta ƙarasa maganar cikin sanyin jiki.
Tausayin ta ne ya kamasu ganin idon ta har ta ciko da ƙwalla sai su kaji suma gaba ɗayan su jikin yayi sanyi.
Bilal da tun ɗazu bai tsoma bakin sa ba sai yanzu yayi magana ya ce "To mu tafi tare mana gaba ɗaya da ita, duk kunbi sai tambayoyi kuke mata, ni na yarda zan tafi da ita gidan mu, idan mukaje nasan Abbana zai ɗauke ta sai tayi aikin acan.
Salama ce tace "a'a wallahi ni zan tafi da ita daman mu kaɗaine, nasan ma Umma na ba aiki zata ɗauke ta ba, idan taji labarin ta zata tausaya mata, zata taimaka mata ta zauna, bama sai tayi aikin komai ba,
Jinjina kai matar tayi hawaye na ƙarasa sauko mata tasa hannu ta share tana jin daɗin haɗuwa da yaran gashi daga zuwan ta acikin garin babu wanda ya kulata ya taimaka mata amma su gashi daga jin wace ita har sun yarda da ita, hawayenne yaƙi tsayawa, tana goge fuska tace nagode nagode kunji, amma ina ganin kamar in ku kunyarda dani su kuma naku iyayen fa, duk da bansan yanda suke ba, amma ina tsoron masu kuɗi, daga ganin ku kuma nasan badaga gidan talakawa kuka fito ba.
Faheema ce ta matsa kusa da ita tana, cike da tausayawa ganin tana kuka duk sai taji itama kamar tayi kukan, tace "dan Allah kiyi haƙuri ki daina zubar da hawayen ki, na miki alƙawarin kin samu ƴan uwa Ammi tana da son mutane tana da tausayi, kuma tana son duk abun da nake so zata so shi, zamuje gidan mu zakiyi rayuwa kamar acikin danginki dan Dady ma baida matsala, ƴan uwana ma haka, duk zasu karɓeki hannun bibbiyu, zan ɗauke ki kamar uwa wallahi.
"Bilal yace "Mu ma ai duk haka, kuma ni nafara cewa zamu tafi ai.
Salama ma "Saida tayi magana tace "kinga kima daina wahalar da kanki aikin ladan nan fa kowa yanaso kuma ai ni na ɗauko ta tundaga can muka zo nan har kuka san wace ita dan haka ni zan tafi garin mu da ita,
Zaid ne yace "yanzu dai duk ba wannan ba ku tashi mushiga cikin garin mu fara samun gidan da zamu zauna mu ajieye jakunkunan nan, zuwa gobe da safe sai mu wuce gaba ɗayan mu, idan munje koma inane sai ta tafi, gashinan ai ko wannen mu suna gida kuma babu wanda basu da kuɗi dan haka sai ta zaɓi duk inda yayi mata ta zauna, sai ta zauna, shikam yasan halin baban sa ba lalle bane ya barta ta zauna shiyasa ma, baice shi zai tafi da ita ba, duk da shima zai so ya tafi da ita ɗin amma yasan halin babansa da masifa.
Fateema jin ta tayi kamar ta tashi sama saboda jin daɗi, wannan maganar tasu, tasa ta nishaɗi sosai dan hakannan taji yaran duk sun shiga ranta, zata so zama da kowa ma, saidai zasu sata cikin kiɗima dan batasan wanda zata bi ba.
Faheema banza tayi dasu saima gefen mayafin ta da tasa tana goge mata fuska, aranta tana ayyana basu isaba ita zata tafi da ita, (Faheema akwai jin tausyi da son mutane)
Zaid ne ya miƙe tsaye tare da cewa "ku tashi mu tafi yanzu bamu da wani isasshen lokaci, yanzu duk ba lokacin zama kace nace bane ya kamata mu shiga cikin garin mu game ke faruwa danna fuskanci yanayin garin nan kamar kauye ne, basu da wata wayewa sosai, ta shi yasa an san samu nema da mubar garin a yau, amma sai dai ba ko'ina muka sani ba kuma abin da wannan mutumin yace mana dole mu fara cika mishi burin sa kafin mu kara gaba tunda shima ya taimake mu, kunga kuma wannan jakar in muka ce zamu tafi da ita to me zamuyi da su sunyi mana yawa zamu iya shiga wani gurin da za'a iya zargin mu akan su, ina ganin kamar yadda ya gaya mana tunda idan mukai duba yanayin fuskarsa kamar akwai matsala akwai damuwa musamman itama dai duk da ina zargin kidnapper ce, amma dai ko ma mecece ta taimake mu kuma bata cutar damu ba don haka nake tunanin kawai muyi musu abinda suka ce in yaso sai muyi tafiyar mu su suka sani in sun zo sun dauka to in basu zo sun dauka ba shikenan wannan ba damuwar mu bace, damuwarmu daya ita ce kudin da zasu ishe mu muje har gida toh yanzu kuma kunga ga kudade da yawa in yaso sai mu debi kudin da muke so mi tafiyar mu su kuma sauran tarkacen da suke bukata sai mu barshi a gida amma dai ya kuke gani ni dai anawa shawarar fa kenan.
Duk shiru sukayi kowa na tunanin maganar da yayi.
Salama ce ta ce "wallahi kar mu ajiye komai, kawai mu bude yanzu mu dauki abinda zamu dauka sauran mu watsar dashi mu kara gaba dan ni wallahi bama na kaunar in kwana a garin nan in dai da yuwuwar za mu iya zuwa gida a yau kawai mu tambaya mu shiga mota ko da ace zamu kai dare ne kawai mu bar garin nan mu tafi gida, saboda namatse in tafi gida a yau, ka ji ka da wani zance wai ma'ajiye kabiye musu mutanen da suka sace mu suka kai mu suka rufe kuma yanzu har su gaya maka wata bukata ka biya musu ita ni dai ina ganin hakan bayuwa bane kan ma mu biye musu can ta matse musu matsalar su ce kawai mu abunda muka sani kudi kuma gashi sun ba mu don haka miyi tafiyarmu gida.
Bilal ma kallon sa yayi ya ce "waye zai kwana a garin nan haba haba gaskiya nima bazan kwana a garin nan ba kana ganin yanayin garin kallon shi fa duk da ban shiga ciki bama wannan ai kauye ne ta ina zamu iya kwana a garin nan,
Fatima ce katse musu zancensu da cewa "duk da bangama fahimtar ku ba amma dai na fahimci wani abun, amma don Allah ko zaku iya gaya mun da abun da yake faruwa amma fa in ba damuwa.
Zaid ne ya koma ya zauna tare da fuskantar ta tiryen tiryen ya zauna ya zayyana mata duk abinda ke faruwa da kuma abin da mutumin ya gaya musu lokacin da zai fito dasu daga wurin bai boye mata komai ba tun daga A har Z sai da ya bata labarin komai.
Kallonshi ta itama tare da girgiza masa kai ta ce gaskiya maganar kubai kamata ba tunda dai har basu cutar daku ba to baku san me yake faruwa dasu ba kuma baku san dalilin da yasa sukai hakan ba nima dai ina goyon bayan ka wannan bai kamata ba gaskiya ace an watsar musu da komai, koma meye tunda har suka bukata toh zunubi yana kansu in ma wata mugun abun suke shiryawa Allah ya fisu Allah yana kallon su tunda dai ku sun gama muku komai sun fito da ku ba tare da sun cutar da kowa ba to kawai kuyi musu haka, yanzu abinda zamu yi shine tunda wuri kar yamma tayi muje kawai a nemi inda yiwuwar siyan gidan to in ma ba zai siyu ba ina ganin kawai mu tafi da su insha Allahu babu abinda zai faru har lokacin da zasu nema ko da daya daga cikin ku ne sai wani ya tafi dasu gida, ko kuma a nemi wani wajen a can a adana musu.
Jin abun tace ya sa su Salama yin shiru suna tunanin maganganun su,
Cike da gamsuwa zai da girgiza kai shima hakan yake so ganin ta goya mishi baya yace gaskiya wannan maganar gaskiya ce dan nima gaskiya matar da ta dauke mu bata nuna alamar cutar damu ko kidnapping din mu ta yi ba kawai dai ban ma dai san wani irin tunani zanyi a kanta bane shi yasa amma idan muka je da su duk daren dadewa koma menene zai fito daga baya, ni na ma yadda zan tafi da abubuwan gidan mu.
Tunda Zaid yace haka suka yi shiru, tunda ba gidansu za'a kai ba shiyasa babu wanda ya kara magana a cikinsu,
faheema ca ta fara mikewa ta ce toh hakan ma yayi yanzu kunga gashi nan karfe biyu na rana har ta kusa ya kamata mu hanzarta muyi abin da zamuyi ko, kar lokaci ya qurai mana tunda dai nan bamu san ma wani gari bane ba ne.
Zaid ma miƙewa yayi tare da cewa "nima dai abinda na gani kenan kawai mun kwana a garin ma fa kawai dai muje mu tambaya, sai a dora mi a hanya, Allah ya sa ma dai babu nisa da nan da inda zamu je,
Duk miƙewa suka shiga yi shi dai zan bai ci musu kara ba don bashi da wani magana a kan su, da a basu da azubar shi babu abinda ya dame shi da su, shi dai kawai ya ganshi a gida shine burin shi.
Fateema ce tayi saurin dakata da su da cewa "amma wani hanzari ba gudu ba, kamata yayi yanzu mu fara buɗewa a san kudin da za a diba sannan a san abu mai mahimmancin da ya kamata a dauka, idain jakunkunan ma za su cinye a rage wasu a barsu saboda tsaro ba don tsoro ba, saboda da in aka ga kowa da jaka irin wannan gashin ku ba in makaranta ba dole wani zai iya zargin wani abun a ganmu da jaka niki niki kowa da jaka a baya,
Nan suka yi na'am da shawarar da ta kawo musu budewa suka hawwi sai dai kudaden daban sai kuma wasu da an ku kulle su sai takaddu haka dai abubuwa tarkace su dai ba komai suka fahimta ba hakan yasa suka san yanda zasuyi suka rage jaka guda daya suka ajiye ta agun ɗata suka saka kuɗaɗen da zasuyi amfani da dasu dan kuɗine bana wasa ba har basu san ma me zasuyi da su ba, uku kuma suka bar ta da kayayyakin a ciki.
Nan suka dauki hanya zuwa cikin kauyen suna zuwa suka fara tambayar nan dan Allah wa ne gari ne nan ake gaya musu suna cikin katsina ne sai suka kuma tambaya dan Allah ina zasu samu motar da za ta kai su kano, wani babban mutum ne yace musu sai dai su hau mashina daga nan sai a kaisu can tasha in yaso a nan zasu samu motar da zata kai su har cikin garin kano,
Ba tare da bata lokaci ba suka hau mashinan da zai kai su tasha, kowa mashin ɗaya ya hau sannan aka dau hanyar tashar dasu, sai da aka yi tafiya sosai sannan suka karaso bakin titin dake kusa da tashar garin, sai dai kuma suna isa bakin tashar aka ce motar da zata tafi kano ta cika sai dai sujira ta karfe hudu, nan suka zauna suna cigaba da tattaunawa, anan gurin ma dai sai da suka yi musu wanda zai tafi da fateema kowa na shi zai zafe da ita kowa na shi zai tafi da ita suna tambayar ta wa za ta bi ita dai kawai dariya take musu har yanzu bata dauki ko daya daga cikinsu ba saboda wallahi ta kasa bata san ya zatayi ba sai dai su sasanta a tsakanin su wani ya hakura dan ita ko'ina ma zata iya zama....
$$$$$$$$$$$$$$
*BARACK*
Saida Beenish tayi sati guda a part ɗin Moohad, sosai ta warware hannunta ya warke babu inda yake mata ciwo don karayar ma, ta warke, kamar ma ba ta kareye ba babu abinda bata iya yi da kanta sai dai har yanzu Moohad ya hana ta fita ya tsare ta a cikin gidan kullum kuma part dinshi a garkame, sannan duk wani horo da za'a basu yasan tsarin sai yazo ya koya mata itama, daidai yanda zata gane, kafinma wani loƙacin a koyawa ƴan wajen shi ya koya mata, saboda a abun da ake koyawa duk a tsare yake daga wannan sai wannan haka abun yake a rubucen tsarin gurin, wani abun mamaki kuma RK bai ƙara shigowa ba, tun lokacin da yazo yayi mishi magana har kawo kwanakin nan bai kuma waiwayan shi ba, saboda haushin shi yake ji dan ganin yake ma da haɗin bakin sa tabar cikin Barack ɗin.
Ɓangarn
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 43 Chapter of 44