ba kwa gurin...
Kowannen su komawa yayi gurin sa ya zauna suna maida hankalin su gare ta batare da ta kalli inda suke ta ci gaba da cewa.....
"Hmmm ko watan da yawa wuce ansa mu wani da ya fahimci wani yayi ƙoƙarin fitar da maganar amma koda ya faɗa sai aka ƙaryata sa koda hukumar tazo bincike sai aka tanadi komai da zai hanasu samun hujja shima kuma bashi da hujja tunda da ido yagani shiaysa babu wanda ya ɗauki mataki ko kuma yaci gaba da bincike, daga baya ma kuma aka kashe shi, shiyasa duk wanda yake son rayuwar sa baya faɗa nima da na faɗa muku bawai bana son ta bane, saidan kawai nima ankamani da wani abun yanzu haka wani bincike ake akai na ana gano gaskiya za su kashe ni, na faɗa muku dan wataran koda zaku iya dakatar da wannan rashin a dalcin da sukeyi, daman neman wanda zan faɗawa nake sai kuma Allah ya haɗa ni daku tunda naji taimakon da kuke son shiyasa naji na yarda daku kuma inaji ajikina zakuyi wani abun saidai kuma maganar gaskiya koda kunyi nasara akai ankama ku to rayuwar ku tana cikin wani hali ba lalle su barku kuci gaba da rayuwa ba...
Maganar gaskiya nima ba halina bane kuma ban taɓa kashe wani ba, inadai gani anayi ko nawa aka bawa mutum suna kashe shi ba sabon abu bane a wajen yawancin likitocin, fahimtar bana kashe kowa yasa suka fara zargin ko nakai munafurcin su, shine suke zargin hakan, dan indai kai farkon zuwa ne bazaka taɓa fahimtar me ake aikatawa ba, sai ka kula sosai, nima fahimtar danayi sunyi wani meeting ne isu isu banda ƙananun maiakata, anan najiyo duk wani sirrin su na fara bincike akai na gano har tarihin su, shiyasa suke ta kuma bincike akan nagano wani abun nasu ko bangano ba da zarar sun gano gaskiya bazasu taɓa bari na ba, dan haka wannan asibitin gaba ɗayan sa babu gaskiya a cikin sa...
Kabeer yace "waye me asibitin?
Ɗan numfasawa tayi kaɗan kafin tace "wani mugun mutum ne ya buɗe gurin akan wani banzan ƙudurin sa kwata-kwwta babu Allah a ransa mugunta kawai yasa gaba bashi da tausayi bashi da imani, tun kan ya fito daga gidan yari yake aikata kisan kai, daga baya ma saida ya san yanda yayi ya gudu a gidan yarin, tunda ya fito kuma bai tsaya ba yaci gaba da cin zalincin mutane daba fashi haka yaringayi yana tara kuɗaɗe daga haka har ta samu ya gina asibitin ko karatun arziƙi baiyi ba kuma baida masani akan harkar likitancin ko sunayen magunguna bai sani ba, amma ya gina shi, sannan yasa mutane a ciki irin sa, daga farko ma yanda yake yi idan aka kawo marar indai a buge yake sai ya ƙulle ɗakin ya biya buƙatar sa, sai ya gama sannan yasa a duba ta, saboda akwai likitoci waɗanda suka iya aikin saidai kawai rashin aiki da abun da suka iya ɗin sai su biyewa son zuciyar su, amma abun da na fahimta daga baya shine duk wannan abun da yake bashi kaɗai bane akwai sa hannun hukuma ko kuma masu manyan muƙami da suke faɗa aji hakan yasa suke duk abun da suka ga dama ba tare da anyi bincike akan su ba an hukunta su an barsu a haka suna ta tsulla abun da suke so, ni nasan tawa ta ƙare domin dole su gano gaskiya yanzu haka ma saurin da ku kaga inayi shi yake kirana kuma idon sa yana kaina duk inda ma naje zai nemo ni, kuma hukuncin da zai min ma sai yafi haka, dan haka ina so daku da ku tsaya tsayin daka ku kawo ƙarshen abun nan, amma ta bayan gida zaku ɓullo musu, kar ku bari su fahimci kunsan wani abu kuma fara tabbatar da cewa wanda zaku gaya shima zai iya taimaka muku kar ku samu wanda baida tausayi, idan aka bashi kuɗi zai iya juya muku baya, sai kunyi shiri sosai kafin ma ku tadar da maganar sannan ku cigaba da samun wasu shedun daga cikin asibitin ta yanda zaku samu ƙwaƙƙwarar hujja da babu dama su kare kansu, zan baku address ɗina kuje gidan mu, dake unguwar Narewa ku tambayi inane babban gida za'a nuna muku, idan kun shiga sai ku tambayi wace Khabirat za'a nuna muku ita, sai kuce ta baku ajiyar da na bata, zata baku wata jaka, a kwai system ɗina duk wani abu yana cikin flash ɗina shi kaɗai zaku ɗauka duk sauran bayanai da abun da nayi bincike da hotuna da muryoyin su da na ɗauka duk zaku samu a cikin sa shi kaɗai ma hujja ce amma dai ku kuma samo wasu hujjojin saboda gudun matsala, daso samu ne ma da yanzu ma nake so kuje ku karɓa saboda indai naje muka haɗu dasu zasu lalubo gidan mu kuma zasu binciko wani abun gwanda kuje ku karɓa ta yanda ko sunje baza su samu abun da suke so ba.
"Yanzu to kina da tabbacin basu ganmu ba loƙacin da muka taho kar su biyo sawun mu su san munyi magana dake,
Girgizar kai tayi tace "saida na tabbatar da wanda yayi masa hakan ya fita daga asibitin tare da waɗancen mutanen, shi kuma me asibitin baya nan, sauran kuma ba wanda hankalin sa zai kawo wani abun, dan haka babu wata matsala kuje kawai sannan ku kula sosai, ni yanzu zan tafi wajen sa idan na dawo da rai zan nemeku idan kuma sun kashe ni shikenan Allah ya baku sa'a ku kuyi nasara babban burina nidai koda na rasa raina, a samu a dakatar da su sudena ɗaukar rayukan ƴan uwa musulmai, da ai tayin asarar rayuka da yawa gwanda ayi asarar rai guda ɗaya, sannan bayan shi nasan wata mata da yake yawan zuwa wajen sa alamu kuma sun nuna mun itama tana da hannu aciki amma ita bangama gane inda take ba...
Cike da ɗanjin tsoro matar tace "a'a kibar wannan maganar kema zaki rayu baza ki mutu ba, in sha Allah tare duk zamuyi aikin In Allah ya yarda babu wanda zai rasa ransa, yanzu ke idan kika gudu bakije gurin sa ba me zai faru?
"Zai binciko inda iyaye na suke, akan su zai sauke abun da zai min sai ya kashe su ga ƙannena ga yayye na babu wanda zai bari duk sai ya kashe su akan laifin da be shafe su ba, to da yayi musu hakan gwanda ni inkai kaina har inda yake, nasan idan kwanana bai ƙare zan dawo na same ku idan kuma kwanana ya ƙare saidai ku bini da addu'a.....
Wayar ta ce tayi ƙara alamar kira ya shigo hakan yasa ta dakatawa tayi saurin ɗauka saida gaban ta ya faɗi da taga private number tasan shine hannun ta na karkarwa tayi saurin ɗagawa, tana ɗagawa tace a gafarce ni in hanya na kusa ƙarasowa, shiru tayi tana sauraron masifar da yake mata kafin daga baya ya kashe wayar sauke ta tayi cikin sanyin jiki, ta ce musu ni zan tafi ku shiga ciki...
Suma duk jikin su ne yayi sanyi ji suke kamar su hanata tafiya, cikin sanyi jiki dan har ƙwalla ta fara cikowar matar tace "baki gaya mana sunan ki ba da kuma shi me asibitin..
Murmushi yaƙe ta ƙaƙaro tayi sa da ƙyar dan ganin matar na ƙwalla yasa ta kuma jin jikin ya mata sanyi, amma sai ta daure tayi murmushin dole, tace "mama kar fa ki damu kanki zan dawo da rai, sannan sunana Maryama shi kuma mutumin cikakken sunan sa, ALƘASIM KHAMIS(JAMBO) amma yanzu yana amfani da BULAMA shine sunan da ya canza bayan fitowar sa daga gidan yari...
Tana gama faɗar haka yana jirana kar yabiyo diddigina, kamar suyi mata kuka haka suka fita daga cikin motar shi kam Kabeer ai kasa magana ma yayi, sai kuma mataimakiyar sa Rabi tana aiki a wani gida saidai har yanzu bangano inda take aikin ba kuma suma a kwai plane ɗin su a gidan nayi ƙoƙarin gano hakan ban gano ba har loƙaci ya ƙure ban gano ba ta kamani, itace ma ta ankarar dashi abun da nakeyi shekaran jiya akai hakan shiyasa ya nemi ni yau, nasan kuma zasu ƙara bincike sai ku hanzarta kuyi wani abun kafin su fargar da wani abun....
"Ba matsala in sha Allah zamu dage gurin ganin komai ya zo hannun mu, daga nan su ka kuma yi mata sallama jiki a sanyaye.
Suna shirin fita tace na manta bari in faɗo muku number ta in case koda baku samu gidan ba sai ku kirata tayi muku kwatan ce, katse recording ɗin da yake yayi sannan yace ta faɗo masa, karan to masa number tayi yana sakawa a tasa wayar har ta gama faɗo masa sannan suka fita daga motar.
Suna fita ta bisu da kallo bata san loƙacin da wani irin hawaye me ɗumi ya shiga gangarowa daga idon ta zuwa kan kumatun ta ba, sosai taji jikin ta ya kuma sanyi yana mata karkarwa ta cikin jiki iyayen ta kawai take tunawa da ƴan gidan su idan ta mutu ya zasuji, wani irin kuka taji ya tahoma ta, tayi saurin saka hannun ta ta toshe bakin ta da hannu, girgiza kanta ta shiga yi tanawa kanta da kanta magana "No! No!! Maryam karkiyi kuka kar ki karaya kar wani abun ya ɗaga miki hankali don't cry ki daure tunda gashi kin sauke nauyin dake kanki, kije kawai idan kinje ma ko sun kashe ki aljanna fa zaki makoma me kyau me yakai wannan farin ciki me kike nema a duniya, murmushi ta saki kamar wata zararriya haka tai tayiwa kanta zance ita kaɗai, saidai kuma duk son taga ta kwantar wa da kanta hankali amma hawaye sai zubowa kawai suke tana maganar amma ruwan hawayen ya gama wanke mata fuska, sauri tayi tasa ƙasan mayafin ta ta shiga share hawayen saidai kuma tana sharewa wani na zubowa.
A haka ta ɗauki wayar ta ta lalubo wata number sannan ta kira wayar ana ɗagawa bata tsaya yin sallama ba kawai ta ce; Aunty Khabeerat "wasu zasu zo karɓar jakar nan ki basu saƙon ciki, daga haka ta kashe wayar a hankali ta tayar motar tayi rivers ta fara tafiya a hankali tana tunanin wasu abubuwan yanzu ko iyayen ta basu san halin da take ciki ba, amma ta wani fanni sakayau take jin ta da ta faɗa musu sai take ganin kamar da wani nauyi ne akan ta da ta faɗa kuwa sai taji sanyi sanyi amma da abun kullum yana ranta ta rasa wanda zata gayawa....
Haka take ta tuƙin a hankali cikin mutuwar jiki har tabar unguwar gaba ɗaya....
Su kuma bayan shigar su cikin asibitin sai suka rasa inda aka kwantar dashi suna gurin suna dubi dubi tun ta inda zasu fara neman wanda zasu tambaya, sai ga wata nurse nan tazo tace kune masu patient ɗin da muka ɗauko a waje, da sauri suka shiga cewa eh gaban su na faɗuwa tsoron su kar ace ya mutu, amma sai sukaji tace mun samu ya farfaɗo saidai yanzu yana bacci kuma kansa ya bugu sosai dan in bayi sa'a ba zai iya farkawa da loosing memory amma ba lalle ba zadai a ƙara duba sa sosai sannan jijjiyar hannun sa ta daina aiki duk yanda zamuyi muga ta dawo daidai hakan baiyiyu ba, zaku iya shiga ku gansa saidai ba yanzu zai tashi ba, sai nan da yamma ko dare,
Ba ƙaramin tausayi ya basu haka suka amsa mata da to sukayi mata godiya sannan ta nuna musu ɗakin suka shiga, kwance suka gansa an ɗaure masa hannu da ƙafar sa da aka karya masa saida suka ɗora sa...
Sun daɗe akan sa kafin daga bisani tace Kabeer baka ganin tunda bacci yake muje gidan nasu mu karɓo tun wuri kar loƙaci ya ƙure wani abun ya faru...
"Eh gaskiya nima tunanin da nayi kenan tunda unguwar da nisa, sai ma ankusa fita daga garin, gashi kuma bamu sani ba saidai muje da kwatance,
"Amma kasan me kira Ruƙayya ba subar asibitin tun kan wani ya ankare dasu..
"Zaro wayar yayi yace cikin sauri ya danna kira yace ni ai na manta ma dasu ai ko bata farka ba kawai ta tashe ta su koma can gidan, bugu biyu ta ɗaga kiran, tana ɗagawa yace; "Fateema! Ruƙayya ta farka, tace "eh ta tashi tun ɗazu nama bata labarin Babyn nace mata kuma kun tafi kai baban yarinyar wani asibitin gata nan tana zaune ma.
"Yauwa to alhamdulillah kin san me nake so da ke kiyi sauri ki goya jaririyar ku bar asibitin yanzu yanzu kuma ku kula dake kar ku bari aga fitar ku, sai fa kunyi sauri kubar komai ku tafi kawai..
"Tom shikenan yaya yanzu zamu tafi, daga nan ya kashe wayar..
cikin sauri ta tashi ta goya babyn ta sanar da yayar tata abun da akace musu, duk da bata jin ƙwarin jikin ta dole ta daure tayi jarumta ta sauko daga kan gadon ta saka hijabi ko minti uku basuyi ba suka fito daga ɗakin har suka fito basu haɗu da kowa ba agurin fita daga gate ɗinne na me gadin ya gansu har yake musu sannu yana ansauka lafiya kenan, shima saboda loƙacin da suka zo shi ya taya su da ɗaukar kaya suka shiga cikin asibitin shiyasa da yagan su ya gane su har tayi musu magana, sama sama suka amsa masa sannan suka fice daga gurin suna fita kuwa sukayi sa'a wani me napep ya sauke wata mata, sai kawai suka shiga suka gaya masa inda zasu ya nufi gurin, adaidaitar su na shan kwana wasu motoci guda uku suka shawo kai da gudu kuma harda motar mutanen da suka zo ɗazu suka daki me gadi da su da likitan,
Suna parking suka fito daga motocin ɗaya sune dai waɗanda suka shigo ɗaya kuma matasan samari ne a ciki su biyu da wata budurwa, ɗayar kuma mace ɗaya ce a ciki sai Rabi da wata tsohuwa.
Haka suka ɗunguma cikin asibitin gaba ɗayan su, duk fuskokin su cike da damuwa dan tsohuwar ma kuka take, sauran kuma kana ganin fuskar su zaka san sun sha kuka, cikin ɗakin suka je inda suka barta kwance haka suka je suka tarar da ita, sai Babyn da ta mutu itama a gefen ta, sai loƙacin duk wasu suka kuma fashewa da kuka, haka suka gama koke koken su daga nan aka sa aka fitar da gawar tasu aka je akasa su a motar asibiti ambulance, ana sakata suma duk suka shiga nasu motocin sannan suka bar asibitin gaba ɗayan su...
Su Fateema sun sauka lafiya babu wata matsala da suka haɗu da ita har sukaje gida, suna zuwa suka kuma haɗawa yarinyar madarar jarirai, dan da farko Ruƙayya tayi ƙoƙarin ta shayar da ita amma abun mamaki gaba ɗaya ruwan nonon ya ɗauke tun a asibitin ta gwada bata amma yaƙi zuwa, haka da suka dawo gida ma ta kuma ƙoƙarin bata amma still babu, haka suka haƙura suna bata madarar.
A ɓangaren maryama kuwa tana nufar dajin ta ringajin gaban na ƙara faɗuwa, amma haka ta daure taci gaba da tafiya tana bin kwatancen da akayi mata, tana cikin tafiya kawai taji tushhh an harbi tayar motar ta tsorata tayi da sauri ta taka burki, dube dube ta fara yi ko zata ga daga inda akayi amma bata ga kowa ba, tasan kuma batazo inda akace tazo ba ci gaba da tafiya tayi, tana gaba kuwa aka kuma harbin taya ɗaya haka akai ta kawowa motar harbi saida aka harbi duka tayoyin, sannan aka fara harbo cikin motar gaba ɗaya ta gama rikicewa tsoro da furgici duk suka haɗar mata, tsayar da motar kawai tayi tana ambaton sunan Allah duk addu'ar da tazo bakin ta yi take, hawaye kuwa ya gama wanke mata fuska gaba ɗaya zubowa kawai yake jikin ta ya ɗau ɓari sai faman karkarwa take buɗe motar tayi da ƙyar tana so taga ta inda zata fara neman tseratar da kanta, ganin bata ga kowa yasa ta fara ƙoƙarin guduwa takun ta biyu aka bata tusshhh take ta zube agun bata sake motsawa ba....
Fitowa suka fara yi daga saman bishiyoyin da suke, su su biyar ne, ko wannen su da bindiga a hannun sa, motar suka buɗe suka shiga duddubawa, gefen giya daga can ƙasa suka ɗaga saiga wani abu ɗan ƙarami, yana ta irga nombobi stopping ɗin sa sukayi ya dakata da recording ɗin da yake da aka saita sa, sannan suka fita daga motar suna fita kuma suka bar wajen batare da sun bi ta kanta ba, bare kuma motar.....
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
A ɓangaren su Khabeer kuwa daga asibitin da basu fita ba sai wajen la'asar suka bar asibitin sannan suka nufi hanyar tasha da zata kai su garin narewa wajen ƙarfe biyar suka tashi, daf da magriba suka isa garin basu sha wata wahala ba suka samu aka kaisu gidan, suna shiga kuwa suka faɗi kamar yanda tace musu suka nemi Khabeerat dake tasan da zuwan su itama direct ta nufi part ɗin ta dasu, gidan babban gida ne sosai family house kowa da ɓangaren sa,suna shiga saka zazzauna nan suka sake gaisawa, sannan tace suci abincin da ta jere musu a tsakiyar falon, haka su kace baza suci ba saida ƙyar tayi musu dole suka ɗan ci kaɗan daga suka ce sun ƙoshi,
Daman ta basu guri suna zaune agun ta fito daga ɗakin tace to gashi gashi kuma naga za'a kira sallah sai kunyi dai zaku tafi ko?
Duba a gogon hannun sa yayi yaga baifi minti biyu bama a kira sallah hakan yasa yace eh bari suyi idan sukayi sai su tafi.
Ana idanr da sallah kuwa suka karɓi jakar Kabeer ne ya karɓa sai ya buɗe ta ya ɗauki flash ɗin kawai dake jikin system ɗin, daga haka sukayi mata sallama har waje ta rako su tana Allah kiyaye hanya, zata juya kenan saiga wasu motoci nan sun shigo layi da gudu dagaka tawa tayi daga niyar komawar da take niya, cike da mamaki tace to waɗannan kuma daga ina haka naga ma kamar nan gidan suke nufowa,
Kabeer najin maganar da tayi tunanin sa ya kawo masa mutanen ne, dan haka da sauri yace; "Mama mu koma ciki sune, da sauri duk suka koma cikin gidan tare da rufewa, matar tana ta tambayar su lafiya SU WAYE SU da ƙyar suka ce mata abunnan zasu marɓa, kuna da wata hanyar fita daga cikin gidan nan...
"A'a wallahi babu wannan ce kawai" ta basu amsa.
Matar duk ta rikice tace "Kabeer yanzu meye mafita kaji su fa har sun shigo gidan, juyawa yayi dake da ɗan tazara daga bakin gate ɗin zuwa can part ɗin juyawa yayi ya hango su yaga har sun shigo gidan mutum biyu da bindugu a hannun su, sai sauran da suke mara musu baya, suna zuwa tsakiyar gidan ɗaya ya harba bindiga sama nan da nan kuwa cikin gida ya rikice wasu suka fara fitowa zasu gudu sai suka ga a shema a cikin gidan su ne, kowa hankalin sa ne ya tashi wannan ya tambayi wannan meke faruwa wannan ya tambayi wannan an rasa me bada amsa kowa sai yace baisani ba,
Ɗaya ne yace gasu can, ya nuna inda su Kabeer suke da suna daf da shiga part ɗin, binsu sukayi da sauri, suma sai suka ƙarasa shiga part ɗin cikin sauri, saidai kafin suyi yunƙurin rufe ƙofa har sun cimma su sun tura ƙofar da ƙarfi, gaba ɗayan su karkarwa suke, mussaman matar da bata san meke faruwa ba, suna shiga kawai suka jawo su waje suka turo su tsakiyar gidan, sannan suka shiga caje cikin gidan, basu tambayi komai daga gare su ba saida suka gama bincike part ɗin sannan suka zo wajen, bayan sun buɗe jakar da ta barta a falo ganin babu flash ɗin a ciki yasa suka suka barta sannan suka dawo wajen, inda aka tsare sauran mutanen.
Ɗaya daga cikin sune yace "kun ɗauko flash ɗin?
"A'a baya ciki sun ɗauka yana gurin su, su fito mana dashi kafin mu harbe su, da sauri Kabeerat tace "eh eh yana gurin su nidai bansan komai ba wallahi dan Allah kar ku kashe ni, haka kawai aka ce na basu kuma na basu bansan menene aciki bama,
Dafe kai sukayi jin abun da tayi musu dan su yanda suka tsara zasu ce basu san inda yake ba, amma yanzu tace ta basu..
"Ku kawo wannan abun idan kuna son ku tsira da ranku da lafiyar ku.
Mutane sun cika gun fal yaran ciki ma sun fara kuka, duk suna so su tambayi ba'asi amma an hana kowa magana dole suka zuba musu na mujiya.
"Kabeer kar ka basu ko zasu kashe mu kar ka bayar saboda ko ka bayar ba barin mu zasuyi ba,
"A'a mama gwanda mu basu mu cire kanmu a wannan case ɗin, mu basu mu huta muna, kar su kashe mu, shi kaɗai suke so nasan kuma idan nabasu baza suyi mana komai ba..
"Ko ma menene Kabeer kar a basu baza su bar mu ba ko mun basu..
Wani ne ya kwashe ta da mari tare da doka mata kan bindiga faɗuwa tayi a wajen, jikin sa na karkarwa ya fara taɓa ta yana girgiza ta "Mama Mama ki, dan Allah kuyi haƙuri kar ku kashe ta wallahi zan baku bari in ɗauko muku wallahi zan baku., Yana maganar bakin sa na karkarwa ya miƙe tsaye ya zura hannun sa cikin aljihun wandon sa na ciki ya ɗauko musu, hannu na karkarwa ya miƙa musu.
Ɗaya ne ya karɓa yana musu dariyar mugun ta yana basu shima suka buga masa ƙasan bindigar a akansa, take shima ya zube a wajen bai ƙara motsi ba, saida suka tattaɓasu suka tabbatar da sun mutu saboda koda sun ƙwace wannan ɗin idan basu kashe su ba zasu iya tona musu asiri shiyasa dole a kashe su...
Matar sukaji kamar da numfashi ajikin ta hakan yasa ɗaya ya samu mayafin jikin ta ya ɗaure mata wuya da shi har saida yaga ta daina numfashi sannan ya saki mayafin, mutanen gurin duk wanda yayi ƙoƙarin yin ihu ko kiran waya sai sun daka masa tsawa haka suka gama mulkin su agun babu wanda ya tanka musu, har suka bar wajen kuma abun haushin daman duk mazan gidan basa nan wasu bama sa garin wasu kuma duk sai dare zasu shigo, shiyasa sukayi abun da suke so ba tare da anyi ƙoƙarin taimaka musu ba, Saida akaga sun bar gidan sannan wasu sukayi kan mutanen da sauri.
"Ke Kabeerat ina kika samu waɗannan mutanen yaushe suka zo, kuma me sukayi wa waɗannan mutanen, kowa da kalar tambayar da yake mata amma amsar ɗaya ce bata san me yasa akayi musu haka ba, sude wata ƙawar tace kawai ta bata ajiya sannan tace zasu zo su karɓa, kuma sunzo ta basu gashi kuma abun da ya faru duk a gaban su...
Duk da basu san Su waye su ba amma sun basu taimako dole suka fara tunani a kwashe su a shiga dasu ciki idan manyan suka dawo sai aji abun da ya kamata ayi za'ayi musu jana'iza ne anan ko kuma za'a nemi ƴan uwansu suzo su ɗauke su, Khabeerat kuma ta kira ta kira number Maryam bata ɗaga ba, ta kirata yafi sau a ƙirga amma ba'a dagawa, gashi kuma ita kaɗai tasani, bata san daga wane gari suka zo ba..
Nan dai suka yanke shawara duk aka kwashe su aka kaisu part ɗin Kabeerat ɗin....,
*$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$$*
Yana zaune kan kujera yana da jiki sosai ga kuma tsawo, yana ta faman zuƙar sigarin shi waya ce a hannun sa yana yi yana ƙyalƙyala dariya da wata ƙatuwar murayar sa dake tafe da ta masu zuƙe zuƙen, mutane biyu ne a gaban sa sun durƙusar da kai suna jiran ya gama wayar,
"To me yasa baku kashe har ita ba, idan kuma ƙarya take tasan komai, shiru yayi, sannan yaci gaba da cewa tom ku tabbatar kun ƙaraso akan loƙaci ana yin sallar asuba ku taho, na matsu inji sa a hannuna, daga
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 44