Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na shirya a kanta don hka duk wanda yace xae bata min plan dina wllh......" da sauri baffa ya mike yana dan buga kafadarsa ciki lallashi yace "cool down my guy, ynxu wa yace mka baxa a aura maka ita ba, daxu baka ga baffanka ibrahim ya xo ba dasu sambo, ai duk kan maganar daurin auren ne, ka kwantar da hankalinka insha'Allahu ranar juma'ah Aneesah taka ce my son" Abdul yyi murmushi yace "gud dad," snn yayi ma Hajiyar wani irin kallo ya fice daga falon, Hajiya xuwaira ta fashe da kuka tana salati tace "shknn na banu Alhaji, ynxu wnn tsinanniyar yarinyar Abdul xae auro mana, to me suka yi ma Abdul dina hka, kuma kafa san namiji wawa ne duk irin tsanar da xae mata lkcin da xata koya masa sonta ma ba sani xae yi ba, ni dae na shiga uku ni zuwaira," baffa ya harde hannayensa yana jijjiga kafa ransa a jagule, can ya mike shima ya fice daga falon.. Haydar yyi parkin a hankali yana hararan kofar shiga falon nasu kamr yyi masa laifi, can yyi tsaki ya fito daga motar yyi hanyar balcony a xuciyarsa yana cewa forsaken home knn, ya shiga falon da sallamarsa yana kallon agogo, yau satinsa uku rabonsa da gidan, suna xaune falo gaba dayansu suna kallo, pretty ta taso da gudu taxo ta rungumesa cike da farin cikin ganinsa, ya shafa kanta yace "ykk bbyna," sumy da meenah suka tabe baki a tare suka maida hankalinsu ga kallon da suke yi, Hajiya ta taso da murnarta tana masa sannu da xuwa, ya hade rai yana amsawa ba tare da ya kalleta ba, yyi hanyar stairs pretty na biye da shi yaji wani siririyar murya na masa sannu da xuwa daga cikin falon, ya juya da sauri yana kallonta, ya juyo yana kallon pretty yace "wnn kuma fa," pretty tayi wani irin dariya can ciki tace "ohon masu," bbu yabo bbu fallasa yace "yauwa," snn ya juya xae haura sama Hajiya ta dakatar da shi, hka ake yi Haiydar baxa ka tsaya ku gaisa ba, cikin fushi yace "to saninta nayi da xan tsaya mu gaisa," Hajiyar ta tabe baki tace "to matar da na xaba maka knn ko kaki ko kaso, ko shi Alhaji usman bae maka bayani bne a can kanon, xaka shigo kana cika kana babbatse ma mutane, ga ta nn sunanta zeenah, 'yar gidan Aminiyata ce kuma sae da na nemi shawara gun Alhaji usman shi ya bani go ahead din yin komai, don hka nn da wata daya ne bikinku tunda kai baka san ciwon kanka ba, degree fa gareta nn da kke ganinta, kuma da ka san irin mutanen dake nemanta da da gudu xaka amince mata, daxun. nn ta xo gaisheni nace ta bari ta kwana kawae tunda na samu lbri gun Najeeb cewar yau xaka dawo." . Haydar ya kasa ce ma mahaifiyar tasa komai don takaici, sae kallonta da yake kawae, abun ma sae ya kusan basa dariya, ya juya ya sake maida kallonsa ga zeenah dake xaune a falon ta sa wasu shegen kayan bacci sae jujjuya masa ido take, kawae ya girgixa kai bai ce komai ba ya juya xae haura sama, Hajiyar ta dakatar da shi da mamaki, "ina xaka ina maka magana baka ban amsa ba, kai fa dan rainin hankali ne Aliyu," ya juya yana dubanta cikin fushi yace "to me kike son nace, ni dae baxa ki xaba min matar da xan aura ba tunda ni ba yaro bane, taje can da degree dinta ta auri manyan mutanen dake nemanta, ni ko da auren nake so kiyi min ma wllh wnn tafi karfina, bare ni ban aikeki ki nema min mata ba , ni fa mum kar ku takura min a gidan nn, ynxu ma ni ba xama na dawo yi ba, kayana xan dauka," yana kai wa nn ya juya ya haye sama pretty ta bi sa a baya, Hajiya ta mike tana salati kmr xata yi kuka tace "ni kam Allah ya hadani da bala'e'en yaro, ya dubi tsabagen ido na ya dinga gaya min magana, to ka xo ka fita gidan nn yau na gani, ni dama nasan bbu abinda surutan Alhaji usman xae yi a kanka, da dae ya biyo ka har nn, nai masa bayani yana kallona ina kallonsa ya gane irin tashin hankalin da nake ciki, ohh ni kam na banu" sumy ta tabe baki tace "wllh mum ki sa masa ido da kyau, ni dae ina suspectn kila ma wajen shegiyar 'yar aikin nn yake xuwa don fa akwae ranar da na gansa hanyar suleja ko ina xa sa oho, ni kuma na raka kawata zee wajen wani saurayinta da yace muje can mu same sa," Hajiya tace "ke ban san mugun fata, wace 'yar aikin, yar aikin da yace min ya ajiye a titi yace ta wuce gida kar ta sake dawowa, ko ba gaban ki ya fada hkn ba," meenah ta fashe da dariya tace "Allah yasa" Hajiya ta juya tana kallon zeenah da ta gama rudewa ganin Aliyu, ba karamin kwarjini yyi mata ba ita kam, ae ita irin wa innan take so, nn da nn taji wani mugun sonsa na mata yawo a xuciya, ta kasa daina kallon stairs din, shknn ita kam ta sami mijin aure, Hajiya ta katse mata tunaninta ta hanyar cewa "ki kwantar da hankalinki zeenah, hka Aliyu yake, amma nasan yana ganinki sae da ya rude nunawa ne kawae baxe yi ba," zeenah ta kirkiro murmushi tace "ba komai Hajiya," sumy da meenah suka kauda kai suna mata dariyar wayyo yarinya. Aliyu ya sauko rike da jakar kayansa ba tare da ya kallesu ba xae bar falon, Hajiya ta shige gabansa tana huci "kana da hankali kuwa Aliyu, ni kke mayar wa ba komai ba ko," sae ta fashe da kuka ta koma gefe tana cewa "dama hka rayuwar take, kaje Aliyu, ni nasan da mahaifinku na da rae duk hkn baxae faru dani ba," ya tsaya kallonta can ya dan yi tsaki ya juya ya koma sama, yana hayewa sama tayi murmushi ta dawo ta xauna tace "idan ba hka nayi masa ba baxae koma ba," ta ciro wayarta ta kira Alhaji usman tayi masa bayanin komai, tana kashewa ko minti biyar ba ayi ba ya kira Haydar din, ranar kasa bacci haydar yyi tunanin Aneesah kawae yake, ga shi har lkcn bae taba furta mata kalmar so ba, ya kasa yin hkn, yana tuna zeenar da Alhaji usman yace masa lallai lallai ita ce matarsa sae yaji ransa yyi mugun baci, to shi macece da xa ayi ma auren dole, yyi tsaki yace nasan maganinku. Washegari alhamis Aneesah ta kare waec dinta, suna tsaye da kawayenta bakin makarantar suna ta murnar gama waec, ita ko hankalinta yyi nisa duk a hargitse xuciyarta yake, wae yau xata wuce gombe to yayanta fa, ita baxata iya rabuwa da shi ba, mota ce tayi park dae dae bakin makarantar matan da ma mutanen dake wajen gaba daya suka maida hankalinsu ga motar har Aneesah, aka sauke glass din motar ana kallonsu, salima tace "waww wnn wajen wa ya xo," Aneesah dae ta tsura masa ido tana kallo, fateema tace "kai maxaje na inda suke, ku dubesa fa, ae Allah ya bani saurayi hka an banu," hka duk suka dinga fadin albarkacin bakinsu, ita dae Aneesah tsit ake jinta, shi ko ita yake ta kallo, suka ce ke Aneesah ke yake kallo f,a ko gurin ki ya xo ko dae yayanki ne, dama gashi kuna kama, lips dinku iri daya, hancinku iri daya, bakin ki iri daya, Aneesah ta dan yi dariya ta karasa kusa da motar tana kallonsa, mates din nata suka bi ta da kallon mamaki, ya hade rae yace "bayan kin gama walakantani gaban kawayenki kinyi kamr baki san ni ba," ta marairaice masa tace "aa nifa banyi kmr ban san ka ba yayana," yyi murmushi yace "to ya angama exams lfya," ta gyada masa kai tana masa wani shegen kallo, yace "hmm wnn kallo hka," ta kauda kai tana dariya, tace "bari ka gaisa da frnds dina," tana fadin hka ta gayyatosu suka karaso bakin motar, yace masu "hi" suka gaishesa gaba dayansu, ya amsa yana murmushi yace masu "hw 're yhu ol," "fyn thank u, nd yhu," suka mayar masa, ya gyada kai yace "same" nn ya tambayesu ya suka gama jarabawa duk suka ce lfya lau snn yace "nyc 2 meet yhu oll 4 d first tym," "nyc 2 meet yhu 2," suka mayar masa suna 'yar dariya, nn Aneesah tayi masu sallama ta shiga motar suna binta da kallo snn yyi reverse suka bar anguwar. @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 13-15 Dai-dai wani shoppin Mall Haiydar yyi parkin motarsa Aneesah ta juya tana kallonsa tace "yayana xan fa yi tafiya yau, naga kuma ba gida mu ka taho ba," ya kashe mota yana kallonta yace "ina xaki," ta dan marairaice masa tace "gombe xan tafi," ya tsaya kallonta da mamaki yace "wae me xaki je yi gombe Aneesah," ta tsura masa ido ko kiftawa bata yi, ya kamo hannunta yace "talk 2 me Aneesah," ta kauda kanta a raunane tace "Ammi ce tace tunda yau xan gama exams na wuce can kawae,"ya lumshe ido yace "sbda me Aneesah," nn da nn hawaye ya taru idonta a hankali tayi masa bayanin abinda ke faruwa da irin maganganun da Abdul ke gaya mata na cewa ta kusa xama matarsa, Haiydar yyi murmushi yana kallon mutanen dake ta shige da fice cikin mall din, can ya juya yana kallon Aneesar da ta tsura masa ido yace "wae a wani anguwar ma baffan naku yake," Aneesah tayi shiru kmr baxa ta ce komai ba can dae ta gaya masa sunan Anguwar, yace "to Address fa," tace "me xaka yi da address yayana," ya daga kafada yana kallon cikin idonta yace "just wants 2 knw," xata yi magana wayarsa yyi ring ya daga yace "srry bbyna gani nn xuwa," Aneesah ta xuba masa ido tana kallo, ya hura mata idon yace "mu je kanwata," ta dan hade rae tace "ni don Allah ka barni na wuce gida yayana, ammi xatai ta jirana," yace "i knw kanwata ynxun nn xamu fito ae, kin dae ga ina ne nn," da kyar ya lallabata ta fito daga motar fuskarta a daure snn suka shiga ciki yyi mata siyayya sosae ita dae binsa kawae take bata ce komae ba, daga bayansu taji muryar pretty, gaba daya suka juya suna kallonta ta karaso tana tura trolleyn kayan da ta siya a hankali Haiydar yace "sae ynxu kika gama," tayi murmushi tana kallon Aneesah tace "ya exams mumy," Aneesah tayi murmushi tace "Alhmdllh, ya gida," pretty tace "lfya lau, ya su Ammi" Aneesah ta kalli Haydar tayi murmushi ta ce tana nn lfya, Haydar ya hada kudin gaba daya ya biya da na prettyn don ita ma ta gama siyayyanta snn suka fita ixuwa mota... Tare suka yi gidansu Aneesah da pretty, ta shiga ta gaida Ammi da yayanta, ita dae Aneesah bin ta kawae take da kallo, tana son yarinyar ssai, Ammi ta xuba masu abinci suka ci tare da ita, haydar kuwa yace ya koshi, sun jima suna hira daga bisanni yyi ma Ammi sallama yace xasu koma gida, Aneesah ta rakosu har bakin mota, ya fito mata da kayan shoppin din da yyi mata yana kallonta yace "no more gombe kina ji na," ita dae murmushi kawae tayi ta kauda kanta a xuciyarta tana cewa gombe kam dole naje sa, pretty ta shiga mota tana daga ma Aneesar hannu, haydar yace "yauwa baki bani Address din da na tambayeki ba Aneesah," tace "wae me xaka yi da Address din yayana," ya harareta yace "ina son nasan ko nasan anguwan ne," da kyar ta gaya masa Address din baffan nata, yyi mata sallama suka bar anguwar, ita kuma ta koma cikin gidan a sanyaye. Haydar yyi parkin dae dae kofar gidan Baffa yana kare ma gidan da anguwar kallo, sanye yake da suit baki har lkcn, ya kalli agogan hannunsa karfe biyar na yamma, ya karasa bakin gate din ya danna bell maigadi ya leko yana tambayar waye, a nutse Haiydar yace "nn ne gidan Alhaji shehu?" mai gadin yace "eh nn ne, akwae matsala ne, don baxa ka samu ganinsa ba ynxu bae jima da shigowa ba" Haydar yace "No ni wajen Abdul naxo ae yana ciki?" mai gadin yace "ko minti goma ba ayi da fitarsa ba sae dai in jiransa xaka yi a ciki," Haydar yace "eh ba matsala xan iya jiransa," mai gadin ya bude masa gate ya shiga gidan yana kare ma ko ina kallo yana murmushi har ya isa kofar shiga falon, ya tsaya ya danna bell, 'yar aiki ta taho da sauri ta bude kofar, yace "Alhaji shehu na ciki ko?" tace "eh amma hutawa yake yi," yace "kije kice masa ana nemansa urgently, a dan tsorace tace "A'a ni ba a bani ixinin hawa sama ba sae dae na kira maka kande, yace "to me kike jira," da sauri ta juya sae ga ta da kande, ya gaya ma kande abinda ya fada mata, ita ma a tsorace tace "aa ni iya ka ta kofar dakin Hajiya," cikin tsawa yace "eh kije kice da Hajiyar ana neman mijinta," ta dan koma baya tace "gskya baxan kuma hawa sama ba sae gobe don na gama duk ayyukana na yau," xae yi magana sae ga hajiya ta sauko, tana kallon yan aikin tace "me ya faru, wnn daga ina," kande ta durkusa da sauri tace "A'a ranki shi dde wnn bawan Allahn ne ke neman Alhaji wae," ta karaso cikin falon tace "akwae damuwa ne yaro?" Haydar yyi murmushi mai sauti yace "gun Alhaji shehu na xo," tace "in ji lfya" ya daga kafada yace "lfya lau, kan wani business ne," tayi murmushi tace "Ayyo xauna mana, bari na kirasa yana ciki," . Haiydar yyi murmushi ganin bata gane sa ba bayan ta bar falon xuwa kiran maigidan nata, bayan kmr minti biyar baffa ya sauko cikin bakar jallabiya, har lkcn Haiydar na tsaye a falon, ya karaso falon yana kallon Haiydar daga sama xuwa kasa yace "hw may i help yhu gentleman?" Haiydar ya gyara tsayuwa yana kallonsa da kyau yace "srry fa, hope am speakin 2 Alhaji Shehu," Baffa ya basa hannu yace "ehh ni ne, have a sit mana," Haiydar ya girgixa masa kai ya juya masa baya yace "ba xama ya kawo ni ba Alhaji Shehu, am barrister Aliyu muhammad," yana fadin hka ya juyo yana fuskantar baffan da dan fara'ar dake shimfide a fuskarsa ya bace da gudu, fuskarsa a daure yace "ehem hw may i help yhu? kana da matsala da ni ne?" Haydar ya girgixa kai a nutse yace "ko daya, i came on behalf of the late Alhaji mukhtar's family," baffa ya yo waje da tulelen idonsa a fusace yace "Alhaji mukhtar meye hadinka da mukhtar, da'alla malam fice min a gida, wnn ae xancen bnxa ne wae on behalf of Alhaji mukhtar, kasan alaka ta da mukhtar xaka xo kana gya min magana malam," Haiydar yyi murmushi mai sauti ya fito da takardar aljihunsa ya jefa ma baffan yace "gidaje biyar, motoci hudu, filaye hudu, 2 companies ba a maganar kudin da ya bari a acctn ma tukun, duk ka tattaro ka damka ma iyalansa nn da sati daya, if nt i will sue yhu, bnxa kawae jahili mara tunani masu cin haram" yana gama fadin hka ya juya yyi kofar fita, baffa ya bude baki yana kallonsa, dae dae bakin kofa Haydar ya juyo yana kallonsa yace "just a week," snn ya fice daga falon, baffa ya girgixa kai cikin tashin hankali ya shiga kwada ma matarsa kira, ta sauko da sauri tana tambayar lfya, me ya faru Alhaji, cikin in ina yace "wnn waye kika turo ni wajensa, kina da hankali kuwa, ni ni ya gaggaya wa magana hka ya fita, ta ina ya shigo gidan nn, yasan ko ni wanene ma kuwa" Hajia zuwaira ta rude tace "wllh ca nake business partner dinka ne Alhaji, mai yace maka?" baffa ya dinga kai komo a falon yana salati, "lallai sae nayi maganin tsinannun mutanen nn, nn ba da dde wa ba, ni xa su toxarta??" duk yanda Hajiya zuwaira ta so jin me bakon ya gaya ma mijin nata hkn bae yiwu ba don duk ya fita hayyacinsa, kira wnn a waya, kira wancan a waya, duk lauyoyinsa biyu sae da ya kirasu, daga karshe ya kira wani abokinsa Dpo, ita dae Hajiya duk inda yyi binsa take kawae a baya, gashi ya ki sauraranta, suna nan a wann hali Abdul ya shigo gidan a fusace, yana kiran abbansa, dad, dad, baffa ya juyo da jajayen idonsa yana kallonsa ba tare da ya amsa ba, "kana sane dae gobe ne daurin aurena da yarinyar nn ko?" Baffa yace "nonsense kasan tashin hankalin da nake ciki ynxu kuwa xaka min maganar auren wa inda suka sa ni cikin tashin hnkalin," cikin tsawa Abdul yace "ina ruwana da tashin hankalinka dad, ni kasan irin tashin hankalin da nake ciki, shit! dad wllh komai xae iya faruwa idan yarinyar nn bata xama matata gobe ba, idan ma kai baxa ka daura min auren ba sae na biya wani ya daura mana, wnn ae walakanci ne kke min dad" baffa ya xauna kan kujera ya dafe kansa yana girgixa kafa, Hajiya Zuwaira dae an sa ta a duhu ta rasa gane abinda ke faruwa, a nutse baffa ya shiga yi ma Abdul bayanin abinda Haydar ya xo yyi masa, Abdul yace "shit shine dad saurayin Aneesar ne, shine wanda nake gaya maka shekaranjiya, shine yyi min tijara daxu" Hajiya ta saki salati tana gwale ido tace "ban gane sa ba wllh Alhaji, ba ranar da naje gidan ba nima nace mka na ga wani a xaune a dakinsu, au shine ya xo yau, tab" abdul yyi tsaki yace "wnn duk ba matsalata bace dad, gobe nake son wnn mara kunyar yarinyar ta xama mata ta don na gwada mata hankali, period," yana kai wa nn ya haye sama yana huci. Baffa ya dafe kai yace "innalillahi wa inna ilai hi raji'un," Hajiya ta xube kan kujera tana kuka, baffa ya mike ya bar falon da sauri yana cewa "nasan abin da xanyi," Hajiya ta bisa da sauri ita ma. . Dai-dai bakin kofa Hajiya Zuwaira ta hadu da mai gidan nata yana kkrin fitowa daga dakinsa rike da makullin motarsa, da mamaki tana kallonsa tace "A'ah ina xuwa kuma Alhaji...." yyi saurin katseta ta hanyar daura yatsansa a baki yace "shhiii" alamar tayi shiru ta ja gefe ya fito daga dakin kmr mara gskya yana kallon kofar dakin Abdul, ya dan yi gyaran murya yace "guy kayi bacci ne!" duk da idon Abdul biyu bae tanka masa ba, baffa ya karasa har bakin kofar dakin ya tura kofar yana kallon cikin dakin, ya ga Abdul din xaune yana xugar taba, ga wine mai sanyi a gabansa, baffa yyi murmushi yace "ashe dae baka yi bacci ba, wae da fa fita xa muyi guy!" Abdul ya juyo da jajayen idonsa yana kallon uban nasa a walakance yace "mu fita muje ina?" baffa yace " No Alhaji kasim ne ya kira ni gidansa ba lafiya shine xan je ynxu," Abdul yyi tsaki yace "shine xan bi ka" baffa yyi murmushi mai sauti yace "mai da wukar Angon gobe, bari naje ynxun nn xan dawo muyi maganar yanda shirye shiryen bikin xae kasance gobe," Abdul yace "A'a ana daura auren a bani matata na tafi da ita kawae bbu wani bikin da xa ayi," " baffa yace "an gama guy, bari naje na dawo" snn yyi masa sallama ya fice Hajiya Zuwaira da hankalinta ya gama tashi jin mijin nata na xancen auren dan ta da Aneesah gobe, ta dinga binsa a baya har suka sauka kasa snn ta fashe da kuka ynxu Alhaji da gske aura masa shegiyar yarinyar nn xaka yi, yyi mata wani mugun kallo yace "da yake na ce maki mahaukaciya ce ta haifeni ba, ni shehu na hada zuri'a da tsinannun mutanen nan baki san ni bane Zuwaira, look ba lallai bne na dawo yau har sae na idda abinda na fita yi, kiyi min addu'a kawae kuma bana son Abdul ya gane ban kwana gida ba, be vry watchful," yana kai wa nn ya fice yana kiran driver a waya, ta bi shi da Allah ya kiyaye xuciyarta ya dan yi sanyi sanin mijin nata shaidanin gske ne. Kofar gidansu Aneesah drivern baffa yyi parkin dinsa, ya fito yana kallon agogo karfe goma da rabi na dare, yace ma drivern gashi nn fitowa ynxun nn snn ya shige gidan. ~14~ Aneesah na kwance bayan ta ci kukanta ta koshi tana ta kallon Amminta dake ta faman har hada mata kayanta don gobe xata wuce gombe wae, ta kauda kanta a hankali wata xuciyar na ce mata tafiyarki gombe shine kadae kwanciyar hankalinki, da ta tuna abinda Abdul ya xo yyi masu daxu da maghrib sae ranta yyi mugun bacewa, ta tsani Abdul ta tsane sa, da ta auri Abdul gwara ta shiga duniya ita kam, sam bata dace da shi ba, to idan da gske ne kmr yanda ya fada masu gobe ne daurin aurenta dashi ya xata yi, ohh da shiknn karshen rayuwarta ta xo, ko da yake ae gobe da asuba xata bar garin Abuja idan Allah ya yrda, tayi assure din kanta, hakan ya kara sa taji hankalinta ya kwanta ta samu kwarin gwiwa, damuwar ta daya basu yi sallama da ya Haiydar ba, ynxu sae dae ya xo ya ga ba ta, hkn yasa taji hawaye ya silalo gefen idonta, ta mike xaune a hankali ta goge idonta, Ammi bata ko kalleta ba tana ta faman hada kaya abun ta, Aneesah xata yi magana knn suka ji an banko kofar xaure da karfi aka shigo gidan, duk suka tsaya kallon juna har baffa ya turo kofar dakin yana huci yace, "maryam, maryam ina tsinanniyar 'yar nn take, maxa maxa ta tattaro kayanta ta fito daga gidan nn kar na balla ta, don na gaji da abun kunyar da kuke janyo mana a gari ko kuma nace kuke janyo min tunda shi ibrahim ba a nn yake ba, maxa ta fito da jakar kayanta bata sake xama a gidan nn," cikin tsawa yake maganr yana nuna Aneesah da ke xaune dakin tana kallonsa da mamaki, Ammi tace "kmr ya abin kunya baffa, wani abun tayi ko kuma....." ya daka mata wani mugun tsawa yace "ki rufe min baki bnxa dake kawae, nace fateema ta tattaro kayanta ta fito daga gidan nn ynxun nn ina tsaye idan ba hka ba wllh wllh xa ku sha mamaki na ynxun nn, matsiyatan bnxa kawae" kuka Aneesah ta fashe da tace "wllh bbu inda xan je daga nn Ammi," ya shigo dakin a fusace har yana neman faduwa ya gaura mata mari mai lafiya, "don ubanki tashi, tashi, nace ki tashi," ya fixgota da karfi, ta fixge hannunta tana kuka tace "wllh bbu inda xani ka kyaleni," ya fita a fusace sae ga shi ya dawo da icce, Ammi dake xaune ta kasa cewa komai sae hawayen da take yi ba kakkauta wa ta mike da sauri ta shiga tsakaninsu, "kar ka dukan min 'ya baffa, ina xaka kai ta da daren nn da xata hada kayanta?" yana huci ya nuna ammi da dan yatsa yace "ke,,, ke maryam ki fita idona kar na watsa maki mari munafuka kawae makira, maxa ta fito da kayanta yau kafata kafarta wllh wllh," Hka baffa ya dinga masu tijara daren ranar yana neman dukan Aneesar da bakinta ya ki mutuwa, Ammi tana kuka tace ta bi shi amma Aneesah tace bbu inda xata ita kam, da kyar Ammi ta lallabata ta hada ta da kayanta da take hadawa tace ta bishi, kuka Aneesah take kmr ranta xae fita hka baffa ya ja ta, yana rike da jakan kayan nata dayan hannunsa, ya wurga ta cikin mota da jakar tata, yace driver ya kula da ita kar ta fita snn ya koma cikin gidan yana huci, ya ciro dubu biyu ya jefa ma Ammi yace "ke ma maxa maxa gobe ki kama hanyar gombe da asuba don baxan tsaya da ku a garin nn ba ana nuna ni da dan yatsa, maxa ki tattara komatsan ki kiyi kauyenku kar naxo na tarar dake nn gobe," yana kai wa nn ya fice daga gidan ya shiga mota, driver na ta kokuwa da Aneesah dake neman ficewa daga motar ta karfin tsiya, baffa ya koma da sauri ya dauko iccen daxu ya dawo motar, Aneesah na ganin iccen ta fasa ihu "don Allah baffa kayi hkuri wllh na tsaya, wllh nayi shiru, ya kwale mata a ka yace "don ubanki da ke kabari ma kiyi mana," tsit tayi tana ajiyar xuciya a motar, ya shiga gaban mota driver ya ja suka bar anguwar suna hawa titi yace da driver ya shiga gidan mai xa su cika tanki, hka ko drivern yyi aka cika tankin motar snn baffa ya biya suka hau titi kuma, a ladabe drivern yace "to ina muka dosa mai gida," baffa yace "samu waje kayi parkin ka bani motar kawae baxa ka yi irin tukun da nake so ba, driver yyi parkin motar baffa ya dawo driver tsit shi kuma ya koma daya bangaren, snn baffa ya ja motar ya dinga sharara gudu kmr xasu ta shi sama, Aneesah kam duk ta tsorata kuka kawae take tana kiran Allah a xuciyarta, tun tana gane hanye har ta daina, taga sun soma fita daga Abuja, ta fara ganin daji da duhu, baffa ko tuki kawae yake kme xae tashi sama da motar, har baccin tashin hankali ya dauke Aneesh. . A tsorace Aneesah ta farka ta dalilin buga kujeran bayan motar da Driver ya dinga yi da nufin tada ta, ta fara waige waigen cikin motar xuciyarta na bugawa, xata tambaye Drivern ina ne nn suka kawota, baffa ya xagayo bayan motar a fusace yana cewa "kin fitowa tayi don ubanta," da sauri ta fito daga motar gabanta na faduwa daga ita sae dankwali tana kare ma inda suke kallo, ko ina tsit sae ciyawa dake ta bow down wa iskan dake ta kada su, ga uban duhu, crow din cock da ta dinga ji ne yasa ta gane Asuba tayi, cikin tasin hankali ta shiga tambayar kanta ina ne nn kuma baffa ya kawo ta, tsawarsa ta tsinta a tsakiyar kanta yana cewa "duk inda na bi ki bi, idan ba hka ba xan wurga ki cikin dajin can na bae ma macixae sadakar ki, kae kuma saleh ka jirani daga nn, ba jima wa xanyi ba," yana fadin hka ya bi ta dan wani hanya duk ciyawa, Aneesah ta bi sa a baya tana hawaye, da taimakn hasken wayar sa suka dinga ratsa grasses din wajajen ga hanyar duk cabi da ruwa, har suka bullo wata hanyar daban da karamar abun hawa xata iya bi, tafiya yake kmr xae tashi sama yana yi yana waiga bayansa ya tabbatar tana biye dashi, ita ko binsa kawae take tana hawayen tsoro, sun kusa minti talatin suna tafiya har daga karshe taga sun shigo wani dan karamin gari, abinda Aneesah ta fara cin karo da shine bukkokin mutane, abun yyi mugun daure mata kai ko ba a fada mata ba tasan kauye

Chapter 7 of 23