Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kansa cikin wani yanayi tace "ya Mujaheed," ya koma baya da sauri ganin fadowa xata yi kansa cikin dan tsawa yace "baki da hnkli ne?" . Aneesah ta koma baya a sanyaye tana kallonsa, ya sakar mata murmushi yace "ya kike amaryarmu," ta juya da sauri hawaye cike idonta, jin shirun da tayi bae kuma cewa komai ba yasa ta juya a hankali taga wajen wayam ba kowa, ta fashe da kuka ssae ta samu wani dakali ta xauna ta hade kanta da gwiwa, tana nn a hka su Najeeb suka xo suka wuce ba tare da sun lura da ita ba, bayan kmr awa daya suka fito gaba daya har da Mujaheed suka shiga motarsa suka bar asibitin, ta mike da kyar tana goge hawayenta ta shiga ciki a sanyaye, xaune ta tarda shi da abokinsa doctor yana masa hira, doctorn na ganinta yace "to bari in koma office tunda amarya ta dawo," Hydar yyi murmushi yace "ngdd frnd," likitan ya fita daga dakin yana dariya, Aneesah ta nemi kujera ta xauna ba tare da ta kallesa ba, shi ma bae ce mata komai ba, bayan kmr minti goma taji ya kirata, ta amsa ba tare da ta kallesa ba, yace "ki kwantar da hankalinki , xanyi free din ki vry soon," ta dago tana kallonsa tace "kmr ya?" ya kauda kansa yace "nasan baki sona Aneesah, kuma ba tare da knowledge dinki da nawa ba aka daura mana aure, kar ki damu xan sauwake maki," a hankali Aneesah tace "ni bance bana sonka ba, kawae dae...." sae kuma maganar ya makale sae kuka, yace "ni bance kiyi min kuka ba Aneesah, dnt wrry xan baki takardar ki sae ki aura wanda kike so, idan ma ba auren xa kiyi ynxu ba sae ki ci gaba da karatunki," bata sake ce masa komai ba ita ma hka, bayan kusan minti ashirin ba tare da ta kallesa ba tace "Anty bata dawo ba," ya dan yi shiru snn yace "ta kirani wae ta wuce gida," hankalin Aneesah ya tashi, ynxu suna nufin nn xata kwana, bata dae ce masa komai ba ta ci gaba da kallonta, wajen karfe goma ta fara bacci kan kujeran da take taji mutum a gabanta ta farka a firgice har tana neman faduwa ya rikota da sauri ya nuna mata spare gadon dake dakin yace "tashi kije ki kwanta," ta mike tsaye bata ce komai ba ta koma baya tana kallonsa, ya koma yyi kwanciyarsa, bae sake cemata komai ba har sae da taga dama don kanta snn taje ta kwanta. Cikin kwanaki ukun da suka yi a asibiti Aneesah dari dari take da Hydar, ita dae don dole take xaune a asibitin, shi ko a rana bae fi yyi mata magana sau uku ba, baya shiga harkanta kmr yanda ita ma bata shiga tasa, ynxu kam jikinsa da sauki sae dae har lkcn baya iya ddewa a tsaye, duk abinda tasan ya kamata tana yi masa ba tare da ta kallesa ba, shi dae sae dae yyi ta bin ta da kallo, har ranar mujaheed bae sake dawowa asibitin ba, Abdul dae na xuwa lkci lkci yana dubasa, hka ma Mudatheer da ta mayar babban yayanta don tana ji da shi ba kadan ba, shi kam faruuq ya koma katsina, taji kewansa ssae don faruuq na da mutunci ssae, a kwanakinsu na biyar a asibiti aka sallamesu, Hajiya murna gunta ba a magana ganin yanda jikin Hydar yyi sauki ssae kmr ba shi take tunanin xae mutu ya barta ba kwanaki, taji ta kara jin son Aneesah a xuciyarta, Aneesah na ta xuba ido taga inda xa a kaita taga sun koma gidansu Hydar, taji kmr ta kwala masu ihu don ita gun Amminta kawae take son wucewa, Hajiya ta sa Pretty ta gyara ma Hydar dakinsa dama kafin su iso, Aneesah ta takure kanta kujera bayan sun shigo falo, ana ta hirar farin ciki da Hajiyar da mum din Mujaheed sae mutanen da suka xo taya ta murna, Hajiya ta lura da Aneesah tace "lah nn kika xauna Aneesah," Aneesah ta kirkiro murmushi ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, Hajiyar tace "to ga fura can kan dinnin ki kai maku daki ke da Hydar," bata yi mata musu ba ta mike taje ta dauki furan ta wuce sama da shi amma ta kasa shiga dakinsa, sae da tayi kusan minti biyar a tsaye ba shiri tayi saurin bude kofar dakin jin pretty ta bude dakinta alamar xata fito, dae dae lkcn da shima ke fitowa daga bathroom daure da towel, ta juya da sauri a gigice kmr warce taga dodo suka yi ido hudu da pretty da ke shirin sauka downstairs don a bude aneesah ta bar kofar dama, pretty ta dauke kanta da sauri tayi gaba abunta, Aneesah ta kasa fita daga dakin kuma ta kasa juyowa ta koma ciki, ga hawayen da taji na neman cika mata ido, sunanta taji Hydar ya kira a hankali ta juyo ba tare da ta kallesa ba ta Ajiye masa farantin dake hannunta, taji ya bude drawer ta daga kai tana kallonsa ynxu kam jallabiya ce jikinsa, ya ciro paper da pen yana kallonta yace "ki karaso ciki," a sanyaye gabanta na faduwa ta karasa cikin dakin ya nuna mata kujera ta xaune, shi kuma ya xauna kan gado ya jawo kujeran dressin mirror ya daura takardar a kai yana kallonta, ita ma kallonsa take taga ya daura pen din kan takardar ya fara rubutu kmr haka; Ni Aliyu. . "Ni Aliyu na......" da sauri Aneesah ta rike pen din a tsorace muryarta na rawa tace "me xa kayi ya Hydar?" ya dago kai yana kallonta yace "takardarki xan baki Aneesah hkn shi xae fi mana alkhairi daga ni har ke," ta fashe da kuka tace "dn Allah ka bari ya Hydar wllh ina sonka karka min hka," a gigice take maganar, ya girgixa mata kai cikin yanayi mai ban tausayi yace "baki sona Aneesah wanda kike so daban, dis is d only best option 4 us, bana son na fiye son kaina dayawa, ki bari na sauwake maki ki aura wanda kike so," Aneesah ta rungumesa hade da kankamesa tana kuka ssae da kyar tace "wllh ina sonka ya Hydar, kunyar ya Mujaheed nake ji don yyi min abinda baxan iya manta shi a rayuwa ba, kai daban ne a xuciyata ya Hydar, don Allah karka sakeni," kuka ssae take rungume da shi, ya daura fuskansa a kanta a hankali yace "ki bari kiyi rayuwarki da Mujaheed kawae, don shi yafi cancanta ba ni ba," ta kankamesa kmr xata shige jikinsa tace "wllh kaine ya Hydar, ina sonka ina sonka yayana," ta fashe da wani matsanancin kuka ya dago kanta a hankali yana kallonta, da kyar ya iya ce mata ya isa hka Aneesah, ta kwantar da kanta kan kirjinsa ta fara sassauta kukan da take yi sae ajiyar xuciya, sun kai minti goma a hka tana jikinsa, snn ya dago kanta yana kallonta, ta lumshe idanunta, shima hkn yyi snn ya daura bakinsa kan nata a hankali, ta bude idonta a tsorace, shima ya bude idonsa, ba shiri ta rufe nata ya shiga kissin dinta, duk a tsorace take ssae, xata turasa ya riga ta, don turata yyi da sauri ya mike, ya shige bathroom tabi sa da kallon mmki. Tana nn ynda ya barta ya fito daga bathroom ya fita dakin ba tare da ya kalleta ba, ta xamo daga kan gadon a sanyaye ta xauna kasa, bayan kusan minti talatin ya dawo dakin, har lkcn tana xaune kan tile ta ma rasa wani irin tunani xata yi duk jikinta ya mutu, yana kallonta yace "kinci abinci kuwa Aneesah," ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba ya karaso gabanta ya durkusa yana kallonta. ~40~ .Yau Aneesah ta cika sati biyu gidansu Hydar, duk da irin son da Hajiya ke nuna mata ta kasa sakewa, gun Amminta kawae take so a mayar da ita duk da kusan kullum sae Hydar ya bata waya su gaisa, pretty kadae ce bata wani sake mata don tsakaninsu sae gaisuwa, Ameera kanwar Mujaheed ma na gidan ita kadae ke yini gun Aneesah a daki don bata fiye saukowa kasa ba, Meenah dae na can India ta fara samun sauki mum din Mujaheed ne a gunta da wasu 'yan uwan Hajiya, duk irin kulan da Hydar ke ba Aneesah ko sau daya bae taba barin sun kwana gado daya ba ko kuma ya xauna kusa da ita, duk da daki daya suke kwana sae dae yyi kwanciyarsa kan kujera, Aneesah kam hkn ma da yake yi yafi mata ddi. Ran da ta cika sati uku a gidan Mujaheed ya xo da Abdul da suka kulla abokantaka ssae, Aneesah na sama, Hydar kuma na dakin pretty yana danna laptop da yake ranar lahadi ne, Hajiya ta shigo tace masa su Mujaheed sun xo ya sauko downstairs yaji ddin ganinsu ssae pretty ta bude fridge ta dauko lemo da ruwa ta ajiye masu tana gaida Abdul, Mujaheed yyi tsaki yana kallonta yace "to dae bakiyi kyau ba kin xo kina ma mutane wani fari da ido, a kai kasuwa yarinya," ta galla masa wani mugun harara ta haura sama abunta, Abdul ya dinga dariya, Hydar yace "ban fa son cin fuska Mujaheed, pretty tafi karfin rashin mutuncin ka," Mujaheed yyi dariya yace oho dae ina kanwata?" Hydar ya dan dauke kansa yace "tana sama," dai dai nn Ameera ta shigo gidan sanye da Hijab dinta har kasa, ta wara ido tace "lah yayana," Mujaheed yyi murmushi yace "dama baki nn," tace "ina garden wllh," ta karaso cikin falon ta xauna tana kallon Abdul tace "ina yini?" ya gyada mata kai, snn ta gaida yayanta, Hydar ya mike ya haura sama ba a jima ba ya sauko tare da Aneesah, tayi mamakin ganin Mujaheed ta dae karaso cikin falon ta xauna ta kirkiro murmushi ta gaishesu gaba daya, duk suka amsa da fara'arsu shi dai mujaheed tun da ya kalleta sau daya bae sake kallonta ba yana ta surutu, ana ta hira amma Aneesah tayi shiru sae dae tayi murmushi, Ameera dae jefi jefi take magana, Mujaheed yace "wae yaushe xaku tare ne Hydar naga kun xo kun jabe ma Hajiya a gida, kuma yaushe xa ayi biki, ni dae ina ta xuba ido shiru," Hydar yyi murmushi yace "sae Ameena ta samu lfya," Mujaheed yace "ohh hka ne fa, to tarewan fa?" Hydar yace "Hajiya tace sae ta gama hada mata akwatunanta na lefe,nn da sati biyu ma xata koma dubai da wata kawarta sae ta bar mata kayan ta taho dasu daga can ita ta wuce India" Mujaheed yce "to Allah ya taimaka muma dae mun kusa angwancewa" duk suka yi dariya daga karshe Abdul ya kalli Aneesah yace "dauki permission gun mijinki ki xo muyi magana kanwata," ta kalli Hydar dake murmushi yace "je ki mana ni na isa na hanaki xuwa gun yayanki," ta kirkiro murmushi ta fita, yana xaune kan kujera a balcony, ita ma ta xauna kan kujera tana kallonsa yace "kin san me nake so dake Aneesah?" ta girgixa masa kai yace "ynxu ke matar aure ce Aneesah 4get about ur past lyf nd face reality, Allah ya riga da ya kaddara Hydar ne mijinki, ki manta kin taba soyayya da ko wani da na miji kiyi facin din marriage lyf dinki, ki bi duk wa inda suka taimake ki a rayuwa da addu'a datz ol," ta gyada masa kai tana kkrin boye hawayen idonta, yace "yauwa kanwata ki cire komai a ranki ki rungumi mijinki," a hankali tace "ta yayana," yyi murmushi ya mike tsaye sae ga Mujaheed ya fito yace "wani gulman kuke yi da kanwartaka ga mijinta can ya cika fam," Abdul yyi dariya yace "ae kuma sae dae ya fashe," Mujaheed yyi dariya yana kallon Aneesah yace "kai kinga yanda kika yi kyau kuwa kanwata, lallai abokina ya iya kiwo, kai ko dae mun samu bby ne" kunya ya rufe Aneesah kmr xa tayi kuka tace "kai yayana bana son hka ni yaushe aka haifeni," duk suka yi dariya ssae banda Hydar da ya kauda kansa, tace "amma yayana da gske nayi kyau banda cin fuska fa" yyi dariya yace "ehh to amma duk kyan naki baki kai matata ba," yana fadin hka ya juya yana hararan pretty dake tsaye tana kallonsu, duk suka yi dariya Aneesah tace "ni na isa nace nafi matarka kyau yayana," Mujaheed yace "gwara dae da kika tuna hka," tayi dariya ta juya xata koma ciki tace "to yayyina mun gode 4 d visit, Allah bar xumunci," duk suka ce Ameen suna tsokanarta ta juya ta shige ciki da sauri tana dariya Abdul yana kalln Mujaheed yace "kai wllh kanwarka kauyancinta yyi yawa, ko raka mutane ma bata iyaba ta wani labe a falo hba, Mujaheed ya hararesa yace "kar dae kaxo kana durkusa min gwiwowi bibbiyu a kasa akan na baka Amira, dk ka bi kasa ma yarinya ido to baxan baka ba don na gano ka" Mujaheed na fadin hka ya juya yyi gaba yana dariya, Hydar ma dariyar yake, Abdul ya wara ido yana kallonsu ya ma rasa me xae ce. Hajiya na ta shirin xuwa dubai cikin satin nn hado lefen Aneesah, sae kuma ga Mujaheed ma ya bata kudi ta siyo masa duk abinda xata hada ma Aneesah, na matarsa Hajiya taji ddi ssae ganin shima yyi hankali xae yi auren at lng lst, Aneesah sae taji duk ba ddi tafiyan da Hajiyar xata . Ana gobe Hajiya xata tafi, tace ma Hydar ya kai Aneesah gida ta gaida Ammi, Aneesah taji ddi ssae don ba karamin kewar Amminta take ba, tare da pretty suka je, tayi mamakin ganin inda Hydar ya kawosu xata yi magana ya riga ta ta hanyar cewa "Mujaheed ne ya maido ta nn few wks ago srry ban gaya maki ba," Aneesah bata ce komai ba suka shiga gidan, suka tar da wata frnd din Ammi ce kawae a ciki, taji ddin ganinsu ta kawo masu ruwa da lemo tana yi tana kallon Aneesah da ta canxa mata, Hydar yace "Ammi fa" matar tace "ta fita kasuwa ba ddewa xata yi ba ynxun nn xata dawo," mintinansu goma a gidan Ammi ta shigo, Aneesah ta rungumeta don farin ciki har da hawayenta, Hydar yyi mata sannu da xuwa hka ma pretty ta amsa masu da fara'arta tana tambayarsu Hajiya da jikin meenah, ta karaso cikin falon ta xauna, Aneesah ta so su xauna daga ita sae Amminta su ji ddin hiransu amma ba dama don Ammi bata shiga daki ba bare ta bi ta, har lkcn tana falo a xaune suna ta hira da su Hydar, karfe daya matar da ta taresu ta kawo masu Abinci, Ammi tayi mata gdya don ta taimaka mata, sae a snn Ammi ta shiga daki, Aneesah ta mike da sauri ta bi ta, Ammi tace "meye hka? Aa ki koma abunki bana son gulma," Aneesah tayi kmr xatayi kuka tace "hira fa xamuyi Ammi," Ammi tace " wanda muke yi a falo fa? Kije idan kun gama cin abincin na xo falon muyi," Aneesah taji haushin hkn ssae amma bata ce ma Ammi komai ba ta koma falo, ba su suka bar gidan ba sae kusan karfe hudu saura Aneesah taji haushi ssae don bata gana da Amminta ba hkn yasa bata ga amfanin xuwan nata ba, kawar Amminta da take kira da maman fatee ce ta kirata daki, ta bi ta, ta bata abubuwan da tasan ya kamata ta bata ta sha, da kyar Aneesah ta shanye na karshen da ta bata a kofi tace "meye wnn maman fatee," matar tace "magani ne," ta ciro wasu turarruka ta mika mata kusan kala biyar tace "gashi nn ki dinga shafa wa innan kafin ki kwanta da daddare, wnn kuma idan kinyi wanka da safe," Aneesah ta gyada mata kai kawae, nn dae ta dan mata nasihohin da ya kamata snn tace "maxa tashi ki je suna jiranki," Aneesah ta mike tayi mata gdyan turaren da ta bata ta fita. Suna tsaye suna jiranta gun mota har lkcn Ammi na wajen, ta cika pretty da tsaraba kala kala, Aneesah kmr tayi kuka tace ma Amminta mun tafi Ammi, Ammi tace "to Allah ya kiyaye hanya ku gaida min da Hajiya," Aneesah bata tanka mata ba har Hydar ya ja motar suka fita daga gida, wani babban saloon ya tsayar da su don pretty tace masa xatayi gyaran gashi suka fito gaba daya suka shiga ciki, yace ma ma'aikatan su biyu xa a gyara ma, ya nemi kujera ya xauna, Aneesah bata yi musu ba ta xauna aka shiga gyara mata gashinta, Hydar ya kasa daina kallon gashin Aneesah hka ma pretty ga tsayi ga baki ga tsantsi ba a magana, ita bata ma san suna yi ba hankalinta na gun TV, kusan a tare aka gama gyara masu gashi da pretty, ya bada kudin snn suka fita daga saloon din, suka shiga mota suka kama hanyar gida, yana yi yana kallon Aneesah ta madubi dn tun da suka fito bata xauna a gaba ba, biyar saura suka isa gida. Ya haura sama ya barsu nn falon suna nuna ma Hajiya gashinsu don yaje yyi sllh. Washegari kam da daddare sae da jirgin su Hajiya ya tashi snn Hydar ya koma gida da su Aneesah, Aneesah ta kasa daurewa har sae da tayi kuka don cikin dan lkcn ba karamin sabawa suka yi da Hajiya ba. Hka suka ci gaba da xama gidan ita da Pretty don Hydar in ya fita baya dawo wa sae shidda na yamm, wani lkcn ma har takwas, gashi pretty ba wani sakewa take da ita ba, kadaici yabi ya isheta, ranar kwatsam sae ga ummi taji ddin ganinta ssae suka yini suna hira pretty na daki tana jinsu sae kusan karfe shidda ta rakata har bakin gate kmr kar su rabu, Hydar suka hadu da ya dawo a motarsa suka gaisa da ummi da fara'arsa snn ya bata dubu biyar ta hau mota, tayi masa gdya ta wuce, Aneesah ta juya ta koma ciki shi kuma mai gadi ya bude masa gate ya shiga da motarsa, a falo ya tarda Aneesah yace "pretty fa?" Aneesah tace "tana sama," yace "ina jiranki a sama," ta bisa da kallo har ya hau sama snn ta mike ta bi bayansa, yana tsaye yana jiranta tace "gani," yana kallonta yace "me yasa kike fita ba hijabi kina da hnkli kuwa," tayi shiru tana kallonsa snn ta dauke kanta tace "kayi hkuri," bae ce mata komai ba ya shige bathroom ta juya ta fita daga dakin. Da daddare tana kwance ya shigo dakin tayi masa kallo daya ta dauke kanta don ynxu kam tun da hajiya ta tafi ya daina kwana a dakin sae dae yaje wani daki ya kwanta, ya xauna gefen gadon yana kallonta yace "na bata maki rae daxu ko," ta girgixa masa kai yace "to shknn gud nyt," ta gyada masa kai ya fice daga dakin. Xaman da suka dinga yi knn da Hydar har Hajiya ta cika sati biyu da tafiya, abun duniya ya ishe Aneesah ta rasa me tayi ma Hydar yake mata hka, hkn kan sa ta kuka ssae wani lkcin... * @ #dan_gogori_1 IKON GOD SAI LOOKIN ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 41➡END ~41~ Yau ma kmr kullum Hydar ya dawo ya xauna downstairs da kanwarsa, ta dauko masa abincinsa a dinnin ya kalleta yace "Aneesah fa," tace "tana daki," ya dan yi shiru snn yace "ita tafi karfin ta sakko tayi ma mutum sannu da xuwa ko?" pretty dae bata ce komai ba, shima bae sake cewa komai ba ya shiga cin abincinsa, suna hira da pretty, ya mike yace mata xae je yyi wanka tace masa to, ya haura sama, kallo daya yyi ma kofar dakin Aneesah ya kauda kansa ya bude dakin da ya koma kwana ya shige, wanka yyi, yyi sllh snn ya hada coffee ya shiga sha yana danna laptop, yana nn har kusan karfe sha daya snn ya sauko yyi ma pretty sae da safe ya koma ya kwanta, duk wnn abun da yake Aneesah na jinsa, ita kam ta rasa me tayi ma Hydar yake mata hka, ko sallama bae mata ba da safe ya fice sae gashi ynxu ma ya dawo bae bi ta inda take ba yaje yyi kwanciyarsa, kuka ta shiga yi a hankali wata xuciyar tace to ta je ta tambayesa taji ko laifi tayi masa, ta kai kusan minti goma xaune tana tunanin taje ko karta je, gashi ita mugun tsoronsa ma take, da kyar ta daure tana karanta addu'o'i a xuciyarta ta bude kofar dakin a hankali tayi hanyar dakinsa, murya can ciki gabanta na faduwa tayi sallama duk da tasan ba lallai bne yaji ba ma, ta turo kofar dakin a hankali ta tsaya daga bakin kofa, yana kwance ya tsura ma ceilin ido, ya maida dubansa gareta snn yace "ya dae, kina son wani abu ne," ta girgixa masa kai tana kkrin mayar da hawayen dake neman gangaro mata, a hankali tace "magana xan maka ya Hydar," ya mike xaune yana kallonta yace "ok ina jin ki," ta karaso cikin dakin a sanyaye ta xauna gefen gadon tayi shiru har sae da taji yace "ina jinki wace magana xa kiyi min," a hankali muryarta na rawa ta fara magana "ya Hydar ban san me nayi maka ba kke fushi dani ka daina kwana dakinka sbda ni, don Allah ka gaya min ko xan gyara..." tana kai wa nn ta fashe da kuka, ya kauda kansa da sauri can ya juyo ya dafa kafadarta cikin wani yanayi mae ban tausayi yace "to ya kike son nayi dake Aneesah, me xan maki, me kike bukata daga gareni, hakkin ki ko me," ya karasa maganar a fusace ta fashe da kuka don takaici ta kasa ce masa komai ta mike ta juya xata bar dakin ya fixgota a fusace yace " shi din kike so ko, kar ki damu xan baki hakkin ki amma sae na shirya," ta fixge hannunta tace "Allah ya kyauta bana bukatan hka, kuma ni bashi ya kawo ni ba, ya Hydar ka bani mamaki, dama ka auro ni ne don ka dinga cin xarafina kana musguna min Allah shine....." ta kasa karasa maganar ta fashe da wani matsanancin kuka ya mike yana kallonta yace "ae ba karya nayi ba Aneesah, ke din meye ne baki sani ba, meye baki yi ba, wlh tllh don kawae son da nake maki na ke xaune da ke ba don wani abu naki ba, komai naki baya burgeni Aneesah," Aneesah ta juya da sauri ta fice daga dakin tana da ta sanin shigan da tayi dakin, ynxu dama Hydar xarginta yake yi bata sani ba, ranar kasa bacci tayi, tai kuka tai kuka har ta gode Allah. Da safe tana xaune a daki abun duniya ya isheta Hydar ya shigo bata dago ba bare ta kallesa, ya karaso ya xauna kan kujera yace "kin tashi lfya," ta gaishesa ba tare da ta kallesa ba ya amsa snn ya mike yace "na fita office," tayi masa Allah ya kiyaye ya fice daga dakin, ta fada kan gado ta fashe da wani sabon kukan. . Tun daga ranar Aneesah bata sake ganin Hydar ba sae dae taji muryarsa a gidan, kwata kwata ya daina shiga dakinta bare sabgarta iyaka idan ya dawo ya ba pretty abinda ya shigo da ta kai mata, sau dayawa sae dae ta fito da ledan da safe bata taba komai ba amma daga shi har kanwarsa bbu mai ce mata meyasa duk da ta lura Avoidin dinta ma yake da sassafe xae fice ya dawo late, duk tabi ta xama wani iri ta rame a gidan har pretty ta fara tausayinta don daga baya ta dinga nuna ma yayanta bata jin ddin abun da yake, shi kam sae yake nuna ko a jikinsa duk da ba hka bne , hkn yasa ta kan shiga ta xauna dakin Aneesah ko bata yi mata hira ba, kuma ta fara mata magana kan cewa ta dinga cin abinci dan ta rame ssae, sau dayawa Hydar kan ba pretty waya ta kai mata su gaisa da Ammi ko Abdul ko kuma faruuq, a sanyaye take karban wayar, taji kmr ta koma gun Amminta, duk sae taji bata son auren kuma da xae taimaka mata ya bata takardarta ta koma gidansu, amma tsoron yi masa magana ma take gaba daya. Ranar saturday tana kitchen da rana yunwa ya isheta tana dafa indomie, pretty bata nn ta tafi gidansu Ameera, tana jin shigowar motar Hydar gidan tayi sauri ta gama abinda take ta xuba a plate ta rufe sae kuma ta kasa fita da shi, ta fito falo ta tarda shi xaune yana danna waya, har ta manta yaushe rabon da ta gansa, ba tare da ta kallesa ba tace "ina yini," ta cigaba da tafiya abunta, ya juya yana kallonta har ta isa stairs snn yace "Aneesah" ta juya tana kallonsa yace "cum" ta komo cikin falon tana kallonsa ta dan durkusa snn tace "gani," yace "baki da lfya ne," ta sunkuyar da kanta tace "lfyata lau" yace "to kina da matsala ne," ta dan yi shiru snn tace "ehh," yana kallonta yace "ta me?" kmr xa tayi kuka tace "gidanmu nake son na wuce gun Ammina," yyi mata wani mugun kallo snn yace "to baxa ki je ba, tashi ki ban waje," tayi shiru kanta a sunkuye kuma taki tashi, ya daka mata tsawar da ta raxanata ta mike a tsorace ta fashe masa da kuka tace "wllh bana sonka ya Hydar bana sonka ka xo ka maidani gidanmu baxan sake xama gidan nn ba," ya mike tsaye yana kallonta yace "to tafi gidan naku," ya daka mata tsawa "nace ki tafi gidan naku, uban me kike tsinanamin a nn din banda bakin ciki da takaici ba, ni da xan iya da tuni na mayar dake gidanku Aneesah tsanar ki nake ji a xuciyata kawae" ta sulale kasa a hankali hawaye na bin kuncinta ta ma rasa me xata ce, ya juya a fusace ya haura sama, abincin da bata ci ba knn ranar, har washegari neman hawaye tayi ta rasa, pretty tayi tayi da ita ta gaya mata ko bata da lfya ne sae dae tace lfyarta kalau, daga karshe ma Hydar daina kwana gidan yyi sbda ita, ranar cikin kuka take ma pretty magana "pretty ni ban san me nayi ma ya Hydar ba ya tsaneni hka, ki tausayamin ki taya ni rokansa ya mayar dani gidanmu ya bani takardata don Allah," pretty tace "kinsan me kika masa Aneesah ki daina cewa baki sani ba," tana fadin hka ta fice daga dakin. Abun duniya ya ishe Aneesah ga xaxxabin da take ji kullum a jikinta, pretty na lura da hka tayi ma Hydar magana ya turo masu likita kawae ba tare da ya dawo ba, ita ce har drip uku amma hkn bae sa Hydar ya dawo dubata ko sau daya ba ita kanta pretty bata ji ddin hkn ba, bae dawo gidan ba sae rana friday da yamma ya shiga dakinta dubata ynxu kam jikin nata da sauki kwance ya tarda ta tana bacci ya dde xaune dakin yana kallonta snn ya fita. Wajen karfe goma na dare ya koma dakin yaji alamar wanka take ya fita, bayan kmr minti goma ya koma don ganinta kawae yake son yi mugun tausayinta yake amma baxae iya nuna mata ba, wnn karan tsaye ya ganta gaban madubi daure da towel tana gyara gashinta, ta juya a tsorace don bata san yana gidan ba, ya tsura mata ido daga bakin kofa duk ta yi mugun rama, ta juya da sauri ta ci gaba da abinda take gabanta na faduwa, ya karasa gaban madubin ya tsaya bayanta yan kallonta ta madubi bata dago ba bare ta kallesa, ya dafa kafadarta sae da ya dau lkci snn yace "ya jikin?" tunda ya daura hannu kan kafadunta jikinta ya dauki rawa ta kasa ce masa komai don

Chapter 22 of 23