Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
daga falon nn, kar kuma ki sake yin wani aikin har ki bar gidan nn yau, Aneesah ta kasa tashi daga inda take ya daka mata tsawa nace ki fita, ta mike a hankali ta bar falon shi kuma ya haye sama, cikin kuka meenah tace "momy kina jinsa ko salon shegiyar yarinyar nn ta rainani, wllh sae ta sake wanke min kayana," Hajiya tace "ke kiyi hkuri ki wankesu a washin machine meenah, ki rufa mana asiri ki rufa ma kanki asiri idan ba so kike ya xane ki ba yau kinsan kadan da aikinsa,tunda yace kar tayi komai yau to ya muka iya, sumy ke je ki ki xuba mana abinci a kan dinnin bana son jaraban Aliyu ku barsa kawae yau yanda kuka gansa kar yaci ubanku" sumy tace "tab wllh ban iya ba," ranar dae dole hajiya ta xuxxuba masu abincin, don har Aneesah ta koma gida bata yi komai ba. ~7~ .Yau friday karfe takwas da rabi Aneesah ta isa gidan aikinta don ma daurewa kawae tayi bata wani jin ddi, jin muryar Hajiyar a falo da 'ya yanta yasa ta kasa shiga ciki xuciyarta ya dinga bugawa, ganin dada bata ma kanta lkci take yi tsaye a verendan yasa tayi shahada tana karanto addu'a a xuciyarta ta shiga falon da sallamarta a sanyaye, Hajiyar na xaune sumy na kwance kan kafarta, meenah na goga abu a fuskarta madubi na hannunta, shi ko Haiydar na xaune kan dinnin yana rubutu pretty na kusa dashi, ta durkusa a sanyaye ta shiga gaida Hajiyar gabanta na faduwa, cikin tsawa tace "yanxu kike xuwa min aiki sbda kin raina ni ko? Xaki gane kuranki yau wllh wllh," a raunane ta fara ce mata bata da lfya ne, Hajiya ta mike tsaye ta yo kanta a fusace kmr me shirin dukanta tace "baki da lafiya? Ni kike gaya ma baki da lfya. ina ruwana da rashin lafiyarki ko ni na daura maki don uwarki," ganin Haka yasa Haiydar ya shigo falon ya nemi guri ya xauna yana kallon momyn tasa yace "yauwa mum maganar da nace xamuyi daxu," ya juya yana kallon Aneesar dake hawaye yace "ke tashi ki ba mutane wuri," ta kalle hajiyar da har lkcin ke tsaye kanta, hajiyar ta daka mata tsawa "don uwarki ba da ke yake ba xaki xuba ma mutane tula tulan idanuwa kmr tulu, mayya kawae" ta mike a sanyaye ta bar falon tayi hanyar kitchen, Hajiyr ta koma ta xauna tace "yauwa ina jin ka son, wacce magana ce xamu yi," ya dan yatsina fuska ya mike tsaye yace "ko kuma bari ma sae xuwa anjima, ynxu ina busy ne, ya koma dinnin din ya ci gaba da abinda yake ," sumy tayi tsaki a hankali tace "dan rainin wayo kawae," Hajiyar tace "ke baki da kunya ko, ynxu idan ya ji ki ya doke ki ki bara min baki kmr speaker ko," sumy ta mike tana bubbuga kafa ita an mata fada ta haye sama da shirin xuwa tayi kuka, Hajiyar ta bita da sauri tana cewa "lahh, to meye abun kuka nn sumy," meenah ta bi su a baya, suna haurawa sama Haiydar ya mike ya ba pretty laptop dinsa ta kai daki snn ta gyara masa dakinsa, tana hayewa sama yyi hanyar kitchen ya tar da ita tana fere dankali, ya durkusa gabanta cike da tausayi yace "me ya same ki Aneesah," ta girgixa kai bata ce komai ba, ya daura hannu a goshinta ya ji xafi yace "subhanallahi, wat's wrong Aneesah," nn ma taki ce masa komai sai hawayen da ta ke yi, ya tsura mata ido cike da tausayi ya kasa cewa komai, can ya mike tsaye yace "ruwan tea kawae xaki dafa masu, nothin more, ki bar dankalin nn," ta girgixa masa kai tace "xan yi dukka," ya hade rae yace "am givin yhu instructns, nt options" a hankali ta mike tsaye tana kallonsa yace "yea," yana tsaye kitchen din tayi duk abinda yace mata, ta jera masu kan dinnin, suna fitowa yin break kuwa duk suka tsaya da mamaki suna kallon ruwan lipton da bread sae kayan tean da ta ajiye masu da blue band kan table din, bbu kwae bbu potatoe, bbu plantain, bbu dan farfesu, cikin tsawa Hajiyar tace "uban meye wnn nake gani hka a nn," gaban Aneesah dake tsaye wajen ya dinga bugawa ta rasa me xata ce mata, Haiydar ya sauko daga sama sanye da farar shadda ya karaso dinning din ya xauna, ya jawo kofi ya fara xuba ruwan lipton a ciki, ya daga kai da mamaki kmr gske yana kallonsu yace "ya aka yi mum," Hajiyar da ta bude baki har lkcn tana kallon Aneesah da ta kasa dago kanta tace "ka duba abinda shegiyar yarinyar nn ta mana yau Haiydar," yace "ooh ai ni nace tayi hka don sauri nake yi xan fita kuma ina son na karya kafin na fita, naga soye soyen xae bata min lkci, yau guda don baku ci dankali da kwae ba sae ku tsaya kmr wasu sojoji," meenah cikin fushi tace "to yaya mu ina ruwanmu da fitarka, ba sae ka shiga kitchen ka hado tean ka ka fito ka bar ta tai mana soye soyen mu ba, don xaka fita kuma mu baxa mu ci abinda muka saba ci ba," yyi mata wani mugun kallo yace "ehh baxa ku ci ba don uwarki, ki shiga kitchen din ki soya mana idan dankali da kwae kike son ci, ko ke ba mace bace," sumy ta fashe da kuka tace "wllh baxan sha tea gaya ba kmr wata almajira," meenah ma ta fashe da kuka tace "nima wllh," suka bar dinning din suka haye sama, Hajiya ta sauke ajiyar xuciya tace "Haiydar tunda suna so da baka hanata yi ba, sae ta hada maka tean ka kawae tayi mana soye soyen mu," ya dago yana kallonta yace "ynxun ma naga dae bae baci ba ae mum, tunda har ni suke gaya ma maganar bnxa to wllh bbu abinda xata soya masu yau a gidan nn, su shiga kitchen su yi da kansu tunda su mata ne kuma aure xasuyi," pretty ta ja kujera ta xauna ta shiga hada tean ta, Hajiya bata sake ce masa komai ba ta haye sama tana hararar Aneesah. Ya juya a hankali yana kallon Aneesar ta juya da sauri ta shige kitchen, bayan kmr minti talatin suna xaune a falo shi da pretty yana nuna mata abu a wayarsa Hajiya ta sauko, ta kallesa da mamaki tace "A'ah fitar knn Haiydar," yace "A'a sae xuwa anjima, na fasa ynxu kam," . Hajiya bata sake ce masa komai ba ta haye sama ranta a bace, ta ja dogon tsaki bayan ta shiga daki, wnn ae wlknci ne Haiydar ke masu a gidan nn. Dole ta kira driver ta basa sako yaje eatry ya siyo masu abinci don sun ce baxa su sha tean ba kuma, karfe sha biyu duk suka shirya suka bar gidan bayan Hajiya ta gaya mata abinda xata girka masu kafin su dawo su meenah kuma sun tula mata kayan wanki ta wanke idan sun bushe ta goge kuma, Haydar na kallonsu har suka bar gidan basu ce masa ba bae ce masu ba, pretty dae na gida don ranar bata da lecture, gidan ya rage daga Haiydar sae Aneesah da prettyn. Haiydar ya fita ya sameta bakin famfo tana tara ruwan wanki, yace "don me baxa ki wanke su a machine ba Aneesah," ta juyo tana kallonsa a hankali tace "sun ce basa fita a machine din" cikin bacin rae yace "sun ci ubansu, maxa kwashe kije ki xuba masu a machine din kar Allah yasa su fita, ke baiwarsu ce," tayi shiru tana kallonsa, yace "ba magana nake maki ba, am nt jokin," tace masa "to," a sanyaye, shi kuma ya juya ya bar garden din jin pretty na kwada masa kira," yana shiga gidan ya sameta tsaye tana jiransa ya xo ya xuge mata zip, ya kulle mata yana tambayarta idan ta fita yaushe xata dawo, tace "lah ni fa bbu inda xa ni yaya, wani sabon cartoon na siyo xan kalla ynxu," ya hade rae yana kallonta yace "ba kince min xaki gidan frnd dinki ba yau," ta dan tabe baki tace "na fasa yaya, kai da baka son ina fita yaya shine yau xaka dinga cewa na fitan" yyi shiru bae sake ce mata kmai ba yana duba wayansa, Aneesah ta xo ta wuce sama da kayan wankin pretty ta bi ta da kallo tace "ke, a ina xaki wanke kayan," Aneesar tace "sama," pretty tace "ba sunce maki basa son wankin machine ba or re yhu daft?" Haiydar ya kalli prettyn yace "ke da'alla kin cika surutu je dauko mayafinki na ajiye ki inda xaki nima masallaci xan tafi ynxu," tace "to yayana" snn ta haye sama da gudu, shima ya haura ya shiga bedroom dinsa ya sake shirin juma'ah ya fito ya samu Aneesahn tsaye kusa da machine din bayan ta xuba kayan, yace "yauwa kanwata ko ke fa, bna son kina min musu kin ji, ynxu gaya min inda ke maki ciwo idan xan dawo daga masallaci na siyo maki magani," ta girgixa masa kai tace "bbu inda ke min ciwo," ya harareta yace "c'mon bna son hka kanwata ki gaya min don Allah," da kyar ya samu tace masa kanta ke ciwo, yace to xae siyo mata magani idan yana dawowa, a falo ya tarda pretty tana jiransa, ya kama hannunta suka fita daga falon ya dauko motar a garage snn suka fice daga gidan, ya ajiyeta gidan kawarta ya hada ta da dubu biyar ta dauki drop idan xata dawo anjima... Karfe biyu ya shigo gidan, lkcn Aneesah na kitchen tana masu girki bayan ta gama da wankin, har wani jiri take gani duk ta kagu lkci yyi ta wuce gida ta kwanta ko ta samu sauki, ya jingina jikin kofa rungume da hannayensa yana kallonta, jin kamshin turarensa ya sa ta juya da sauri ya sakar mata murmushi yace "sannu da aiki," ta gyada masa kai tace "ngd" snn ta gaishesa ya amsa ya karaso cikin kitchen din ya tsaya bayanta yace "me kike girka mana," ta koma gefe da sauri tace "shinkafa da miyar kaxa ce, sae cream salad " ya gyada mata kai yana murmushi yace "to xubo min nawa idan kin gama," ta gyada masa kai taci gaba da hada salad din yana kallonta, tana gama hada wa ta shirya masa abincinsa yace ta ajiye masa a kan carpet na tsakiyar falo tayi yanda ya sa ta xata wuce ya riko hannunta, ta fixge da sauri ya tsura mata ido "Aneesah ciwon kan ne ya sa maki xafin jiki hka, don Allah ki gaya min me ke damunki bn yrda kanki ke ciwo ba," ta yarfe hannu tace "nima bn sani ba wllh, kawae dae bna jin ddi ne," ya kamo hannunta ya xaunar da ita gaban abincin ya xauna yana kallonta yace "xauna mu ci abinci sae na baki magungunan da na kawo maki," xata yi magana ya daura yatsantsa kan lebenta yana mata wani irin kallo yace "kar ki ce min komai," ta sunkuyar da kanta da sauri, ya xuba abincin ya shiga ci yana bata, a hankali yace "an taba ce maki kina da kyau Aneesah," tayi masa shiru bata ce komai ba, ya dibi abincin a cokali ya kai mata baki ta kauda kanta, ya tsura mata ido bai ce komai ba, ta juyo tana kallonsa yyi murmushi yace "am srry baxan kara ba kanwata," ya sake kai mata abincin baki ta bude bakin a hankali ya xuba mata, a hankali taji yace "Aneesah, wani aiki baffan naku yake yi ynxu," ta dan yi shiru na wani lkci snn tace "siyasa yake yi," ya gyada kai yace "gud! when lst rabonku dashi," ta sunkuyar da kai bata sake cewa komai ba har sae da ya maimaita mata tambayan snn ta basa lbrin abinda ya xo yyi masu ranan da daddare tana kuka da abinda yusuf yyi masa daga karshe, Haiydar yyi murmushi yace "to meye abun kuka Aneesah, ae ki kwantar da hankalinki kawae bna son kina sa ma kan ki damuwa," ya ciro handkerchief yana goge mata hawayen idonta yana kallon cikin idon, ita ma kallon nasa take, dai-dai nn aka bude kofar falon aka shigo ta mike a tsorace tace "nashiga uku, . Pretty ce ta shigo gidan, ta tsaya bakin kofar tana kallonsu ba tare da tace komai ba, Aneesah ta juya da sauri cikin tashin hankali xata bar wajen, sai maimaita nashiga uku take yi, Haiydar yyi saurin rikota, ta buge masa hannu tare da fashewa da kuka tace "ni ka rabu dani don Allah," ya ki sakinta sae ma xaunar da ita da yyi gabansa, ya juya yana kallon prettyn da har lkcn ke tsaye tana kallonsu yace "c'mon Zainab xo mu ci abinci," ta karaso falon ta ajiye jakarta kan kujera ta xauna kan carpet tace "washh yaya wllh na gaji dayawa akwae rana," ya mika mata spoon yace "to meyasa kika dawo da wuri," tace "kawae na gaji da xaman gidan ne," Haiydar ya juya yana kallon Aneesah da har lkcin yana rike da ita don kar ta tashi yace "kanwata kukan me kike kuma," tayi shiru bata ce komai ba sae faduwa da gabanta ya ke yi tana kallon prettyn a tsorace, pretty ta fara cin abincin ta tana ba yayan nata lbrin kawarta da taje wajenta, shi ko hankalinsa na kan Aneesah da ta ki sake wa, ya dubi pretty dake ta cin abincin ta yace "je ki sa key a kofa pretty," taje ta sa ta dawo, ganin Aneesah taki karban abincin da yake bata a baki yasa ya bata spoon ta ci da kanta, nn ma taki, pretty tace "kila bata son ta ci da kai ne yaya, ka xuba mata nata daban," yyi yanda pretty tace ya tura mata gabanta ya hade rae yace "oya maxa ki ci idan baki son nayi fushi," ta dago kai a hankali tana kallon pretty, prettyn ta sakar mata murmushi, ita ma ta dan yi murmushin snn ta fara cin abincin a hnkli, hka suka dinga cin abinci pretty na basu lbri har suka gama pretty ta kwashe kwanukan ta kai kitchen ta dawo suka ci gaba da hira, tun Aneesah na yi masu shiru har ita ma ta sake suna yi, pretty ta kalleta tace "yauwa wae me kike shafawa a lips dinki kullum sae na gansa pink" Aneesah tayi murmushi tace "ni bna sa komai," Haiydar yyi murmushi yace "ke ma kina son naki ya xama irin nata ne" pretty tayi dariya tace "eh yayana," yace "to xan ce ta tsam maki, ynxu dae je ki wanke plates din da muka ci abinci ki dawo" Aneesah ta ce "A'a xan wanke," ya riko hannunta yace "A'a bar ta ta wankesu, ke da baki da lfya magani xaki sha ynxu ma," pretty tace "bata da lfya ne," yace "eh" tace "Allah ya sauwake snn ta kwashi kwanukan tayi kitchen dasu ta wanke," ya lallabata ya bata magani tashi da kyar, snn tace masa xata je tayi masu gugan kayansu, ya harareta yace "baxa kiyi ba wllh," ganin yaki barin ta ta shi yasa ta hkura ta tsura masa ido kawae tana kallonsa ya hura mata idon yace "wnn kallo hka," ta boye fuskarta tana murmushi. Pretty ta dawo falon bayan ta gama wanke wanken tace "yayana na gama," yace "yauwa kanwata," ta xauna suka ci gaba da hirarsu kmr da can sun saba da Aneesah, budewar gate da suka ji yasa Aneesah ta mike tsaye da sauri, pretty ma ta tashi da sauri tayi hanyar kofa don lekawa taga ko waye, ta dawo da sauri tace "yaya mum ce da su meenah," Aneesah ta fixge hannunta daga rikon da yyi mata tace "na shiga uku don Allah ka sake ni," yace "baxa fa ki kara yin aiki gidan nn yau ba, gwara kawae ki tafi gida in hka ne," ta marairaice masa tace "lkcn tafiyata bae yi ba don Allah ka rabu dani guga xanje na masu," ya fixgota yyi hanyar stairs da ita tana masa magiyan ya kyaleta suna hawa sama ya bude bedroom dinsa ya jefata ciki yace "kar ki kuskura ki fito, gwara kawae kiyi bacci har lkcn tafiyar taki yyi," ya ciro makulli ya kulle dakin ta waje snn ya sauko downstairs, pretty ta ruga ta bude masu kofa Meenah ta ce "ina wnn shegiyar yarinyar taxo ta yi serve din mutane yunwa nke ji," Hajiya ma ta xauna tana tambayar haiydar har ya dawo, yace "ehh snn ya gaida ta, ta amsa tana cewa prettyna kin ci abinci, pretty tace "eh naci," a fusace hajiya tace " wae ina wnn gantalalliyar yarinyar take bata ji shigowrmu bne," Haydar yce "tana sama na sa ta guga ne," cikin gadara meenah tace "ni tayi min nawa gugan ne pretty?" pretty tace "na yaya take yi," meenah cikin bacin rae take "ba ni na fara sa ta ba xata bar min kayana don rainin wayo," Haydar yyi mata wani irin kallo yace "idan baki yi hnkli ba wllh yau sae na fasa mki kai "dare me" kuma ki gni," meenah ta hararesa tace "to kai naga ba dry cleaning kake kai kayanka ba idn ba gulma ba yaushe 'yan aiki suka fara maka guga," sumy ta tabe baki tace "shi dae na gani," ya mike cikin xafin nama ya yo kan meenar da ta fasa ihu a tsorace Hajiya ta tashi da gudu ta tsaya gabansa ta rikesa har da durkusawanta "don Allah don annabi kayi hkuri ka rabu dasu Aliyu, kaga yarane basu san ciwon kansu ba," sumy dama tuni ta haye sama da gudu, yyi kwafa ya koma ya xauna, tsit kke jin meenah don ta tsorata, pretty sae dariya take, Hajiya ma ta koma ta xauna tace "to yarinyar nn taxo ta fara bamu abinci kafin ta ci maka gaba da gugan mana Aliyu wllh yunwa duk muke ji," meenah tce "nima shi dae na gani," yce "A'a kafin ta bar gidan nn yau duk se ta gama min gugan kayana idn ma xaku je ku xuba abincinku kuje ku xuba tunda de ku ba kutare bane," ya fadi yana kallon Meenah @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 8➡10 ~8~ Meenah ta tabe baki tayi hanyar stairs tana cewa "wnn jarabar da yawa take, mutum sae kace shaidan," ta karasa dakinta da gudu ta kullo kofar, Hajiya tace "ka dinga hakuri da kanninka Aliyu, yarane basu san abinda suke ba sae ana yi ana nuna masu," ya mike tsaye yace "A'a jarirai ne, yau ma aka haifosu karewarta, amma wllh idan na cafke mutum a gidan nn ko," yyi kwafa yyi hanyar dinnin, pretty ta mike tabi sa, Hajiya tce "Allah ma baxae sa ka cafke sun ba," ita da knta ta mike taje ta xuxxuba masu abincin snn ta aiki pretty taje ta kira mata su suxo suci ba kunya suka sauko kuwa, suka xauna daga su har uwar tasu tsakiyar carpet tnda oga na kan dinnin, sn gama cin abnci suna ta kallo sumy na masu hira, Haiydar da pretty dae na kan dinnin suna kallo a wayarsa, sumy tace "wae har ynxu 'yar aikin can bata gama guga bne a sama, gashi ina son na aiketa supermarket siyo min sabulu, don soap din wanka na ya kare, Hajiya tace "to ni ina nasani, wae Haiydar har ynxu bata gama gugan bne, xata mana farfesun kifi fa kafin ta tafi," yyi kmr bae ji su ba yana ta kallonsa da pretty, Meenah tayi tsaki ta mike tsaye tace "bari dae naje na duba, kila shegiyar taji sanyin A.c ma bacci ya dauketa a gun," Haiydar ya mike da sauri cikin tsawa yace "wat! Dakina xaki shiga, da ko kinga yanda ake cin uban mutum yau, don Allah je ki, na rantse da Allah idan ban sumar dake ba to sae na karya ki yau," Hajiya ta mike tace "ohh ni fateema na shiga uku, sae kace ba kanninka ba Aliyu meyasa kke hka, duk ka dauki karan tsana ka daura ma 'ya yan nn, meye a ciki don tace xata je dubo 'yar aiki, wnn wani irin rayuwace hka irin naka," ya daga kafada alamar bae damu da xancen nata ba yace "ai yaran ne basu da tarbiyar arxiki," sumy ta tabe baki tace "ni dae ko min dare wllh sae taje siyo min sabuluna, ba ma kaya ba in xata iya har dakin ma ta goge dole ta fito taje min market," meenah tace "nima wllh ko min dare kafin ta bar gidan nn sae ta min gugan kayana," Haiydar ya mike tsaye ya fara saukowa daga matakalan dinning din, gaba daya suka fasa ihu a tsorace suka yo bayan Hajiyarsu, ita ko ta mike tsaye da sauri tana cewa "kana ma Allah da annabinsa ka rabu da 'ya yana a gidan nn Aliyu, wllh wllh xan bata maka rai na Hada ka da Alhaji usman fa, wnn wace irin jaraba ce," ko kallon daga ita har 'ya yan nata bai yi ba ya haye sama, bayan kmr minti biyar sae gashi ya sakko Aneesah na biye da shi a bayansa, har lkcn Hajiya na tsaye, su meenah na rabe a bayanta sumy har da kuka, ya kalli Aneesah cikin tsawa yace "ke kama hanyar gidanku, kin gama aikinki 4 today," ta marairaice tana kallon Hajiyar da ta galla mata wani mugun harara, ya daka mata tsawa yace "nace ki fice ko bakya ji ne," a sanyaye ta fita daga gidan karfe hudu saura minti biyar," ya koma ya xauna, Hajiya tayi shiru tana kallonsa cikin lallami ta fara magana "Haba Aliyu so kke yarinyar nn ta raina mu ne, wnn ai bae yi ba, biyanta fa nake yi ka dinga hanata kuma tana ma yarana aiki, don su fa na kawota gidan," yace "sae randa suka canxa halinsu nima xan canxa," snn ya haye sama, meenah ta ja dogon tsaki tace "bnxa kawae dan wahala, in ina son dawowar wnn gantalallen mutumin gidan nn nayi ma Allah karya wllh," sumy tace "ke ko ni, wnn ai obstacle babba ne a gidan nn gare mu" Hajiya dae na tsaye tana kallonsu ta kasa cewa komai, pretty ta mike tayi tsaki tace "fitsararrun bnxa kawae, ai kune gantalallun," snn tayi hanyar stairs da gudu meenah ta bi ta har tana faduwa ta cafkota ta shiga xuba mata mari tana duka, pretty ta fasa ihu, sae ga Haiydar da sauri ya sakko, meenah ta juya da gudu xata bar wajen ya cafkota ya haye sama da ita Hajiya ta taho da gudu tana cewa "wllh ka sake min 'ya ta kasan abinda tayi mata ne," ko saurararta bae yi ba ya shige da ita dakinsa, ya kulle kofar da makulli, ranar shegen duka yyi mata da belt, su Hajiya da sumy aka tsaya bakin kofa suka dinga rusa kuka yaki bude kofar har sae da yyi mai isarsa snn ya cillota waje ya kulle kofarsa. Aneesah na komawa gida ranar Ammi ta tambayeta da mmaki me ya dawo da ita lkcn, tay mrmushi tace "nace mata bana jin ddi ne shine tace naje gida na huta, Ammi tace "Allah sarki, Allah ya kara masu budi, matar na da kirki," Aneesah tayi murmsuhi ta shige daki kawae a xuciyarta tana cewa lallai kam tana da kirki. Ko da Aneesah ta tafi aiki washegari bta ga Haydar ba, ta sha wahala ranr dn knta suka huce dk abnda yyi msu jiya daga su har uwarsu, ita de pretty bata ce kmai ba kallnsu kawae take, sun aiketa kasuwa ranr ya kai sau uku kuma a kafa, snn dk se da tyi masu guga da kwalemar dakunansu, krfe uku suka bar gidn bayan sn ci abncin rana, sumy ta kawaso mata takalmnta ta wanke na wankewa na gogewa kuma ta goge tce mata to, snn suka bar gidn gaba daya har da Hajiya amma banda pretty, sae bayan fitarsu pretty tayi mata magana ta kuma kawo mata maganinta na jiya da Haydar ya siyo mata tace yace ta bata, ta kuma kama mta sauran aikin da suka rage a gidan kafin 'yan uwanta su dawo. . Yau Alhamis da kyar Aneesah ta iya xuwa wajen aiki don daga ita har Ammi cikin satin duk basu da lfya barin ita da nata yafi tsanani daurewa kawae tayi ranar taje aiki, tayi masu duk abinda take masu na kari don har lkcn basu tashi ba, snn ta shiga gyaran gida, Haiydar ya sauko yana kallonta ya karaso gabanta yace "ya jikin kanwata," ta dago tana kallonsa snn ta gaishesa, ya amsa yana murmushi yace "sarkin aiki, har kin fara" ita ma tayi murmushin ba tace komai ba ta ci gaba da abinda take, ya xauna yana kallonta har ta gama goge gogen da take yi snn ya ja ta xuwa kitchen su yi breakfst, tilasta mata ya dinga yi yana bata tana ci don ca tayi mashi ta koshi amae take ji, bae kyaleta ba sae da ya ga ta kwararo aman, ya mike ya riketa da sauri ta dinga yi, ya ja ta suka shiga garden, ya taimaka mata ta gyara jikinta yana kallonta da tausayi yace "wae don Allah ki gaya min me ke damunki Aneesah duk kwanan nn na lura yhu re just managin yhur sef, gaya min ina ke maki ciwo," ta girgixa masa kai tana hawaye tace "kawae bana jin ddi ne, ni ban san idan ke min ciwo ba," yace "to muje asibiti kanwata," ta girgixa masa kai tace "A'a ni bbu inda xanje," dole ya fita siyo mata magani kafin 'yan gidan su sauko ya bata ta sha, snn ya kira pretty ta taimaka mata da wanke wanke, da mopping kafin masu bacci su tashi. Hka Aneesah ta dinga daurewa ranar a gidan bayan Haiydar ya fita, pretty ce ma ke dan taimaka mata da wasu ayyukan a boye, karfe uku Haiydar ya shigo gidan da abokinsa Najeeb, Hajiya taji ddin ganinsa sosai don dama tana son hada Haiydar dashi ya ja masa kunne ya fita harkan 'ya yanta, duk 'yan matan suka fito gaidashi cike da murna, ya rungume pretty yana dariya yace "kai, bbyn Haiydar hka kika girma," tayi dariya tace "ae kai ma ka girma yaya," shima yyi dariyan yana tambayarta ya karatu, Haiydar da duk hankalinsa ya tafi gun Aneesah don ganinta kawae yake son yi sanin halin da ya tafi ya bar ta daxun, yace "ka kyale min kanwata hka ni dae kar ka cikata da surutu," pretty ta dawo jikin yayanta tana dariya tayi masa sannu da xuwa, su sumy da meenah sae hararta suke suna tabe baki, Hajiya tace "wae ina wnn mahaukaciyar yarinyar take ne, ko uban me ma take yawan yi a garden ni kam na kasa ganewa, bata ji munyi baki bne," meenah ta tabe baki tace "bacci take xuwa yi mana, ko da baki sani ba," pretty ta mike tsaye da sauri tace "daxu dae naga tana shara ne, bari naje na kirata," xaune ta tarda Aneesah ta hade kanta da gwiwa, ta durkusa gabnta a hnkli tace "Ana kiranki," Aneesah ta mike da kyar tana ganin jiri pretty tace "ki bari yaya ya kai ki Asibiti mana," ta girgixa mata kai tayi murmushi kawae suka shiga gidan, a walakance aka ce ta kawo ma Najeeb lemo, ta bude fridge ta ciro lemun da ruwa ta daura da glass cup kan faranti ta kawo masa ta durkushe gabansa bayan ta gaishesa a hankali, snn ta bude lemun ta xuba masa a cup ta dago tana mika masa gnin ranar da ta ajiye ma Haiydar xaginta aka dinga yi, ido ya tsura

Chapter 4 of 23