Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da yamma kike gani na a nn ko during wkends" Aneesah tayi masa kallon sama da kasa snn tace "tab, amma daga wani state ka xo nn?" yace "daga kano nake ke fa?" Aneesah tace "to nn ina ne?" ya harareta yace "oh kina gari ma baki san ko ina ne ba?" ta ce "Allah ban san ina ne nn ba," yyi murmushi yace "lallai, to nn garin kaduna ne though but kauyen nn ix close 2 zaria" Aneesah ta yo waje da ido ta dafe kirji tace "Zaria kuma?" yace "eh mana, me ya faru?" ta dan yi yake tace "aa bkm, amma mai yasa kke behavin kamr dan kauye, ka dinga shan rake a hanya kuma kasa shaddodi daban daban," Mudatheer yyi dariya yace "tab, lallai ma yarinyar nn, baki yi biology bne ae dis is wat dey call adaptation, i adapted 2 my environment, ke ynxu ki gaya min meye a jikin ki?" Aneesah ta kalli jikinta da sauri, xani ce daban riga daban, ta fashe da dariya tace "kuma fa hka ne kam, amma naka yyi worst," yyi dariya yace "to ke daga wani state kike?" xata yi magana sae ga shatu ta bullo, shatu ta saki salati tana tafe hannu tace "ynxu Aneesah ke baxa ki ji maganar da na gaya maki ba ko, wae wacce irin yarinya ce ke, kin fi so kullum ina dukanki kamr jaka ko?" Aneesah ta mike da sauri ta kwashi iccen da ta tattara waje daya ta bar wajen, shatu ta bi ta da harara, shi dae mudatheer bae ko kalle shatu ba, bayan Aneesah ta bar wajen shatu ta galla masa harara tace "bnxa kawae, wllh baka fita harkar 'ya ta ba sae na sa su garbebe sun maka dukan fitan rai," tana kai wa nn ta juya fuu ta bar wajen tana cigaba da masifanta. Baffa ne xaune dakin Abdul dake ta faman busa sigari yana danna wayarsa, baffa ya dan yi gyaran murya yace "wajen ka fa na xo Abdul," Abdul ya dago jajayen idanunsa yyi masa kallon rainin wayo snn yace "to wae me xan maka," baffa ya dan fara kame kame "no ba komai xaka min ba son, kawae shawara ce na kawo maka, don me Abdul baxa ka koma bakin harkokin ka ba a can london idan aka ga Aneesah sae a tura maka ita kawae ta jirgi, kafa san tym nd tide wait 4 no man, kana nn ne kana bata lkcn ka kawae a bnxa, tunda dae ynxu kaga mun kusa samun nasara a kan case din nn ka daure ka koma bakin aikinka a london kar a sami matsala guy," sae da Abdul ya gama sauraran mahaifin nasa har ya kai aya snn ya mike a fusace yana huci yace "nonsense, bbu inda xanje malam har sae an bani Aneesah a matsayin matata, ka fini sanin abinda ya kamata ne xaka kawo min mgnr bnxan nn, ka rike mahaukacin shawararka kawae" yana kai wa nn ya jefar da guntun ta bar dake hannunsa yana bouncn ya fice daga dakin, baffa yyi murmushi yace "yaro man kaxa, amma nasan maganinka don ubanka," ya mike har lkcn yana murmushi ya fice daga dakin shima. Haydar ne xaune kan kujera Hajiyarsa da barrister umar tsaye kansa a gidan yari, duk ya xama wani iri da ganinsa kasan yana cikin tashin hankali, tunda aka kawosa wajen kusan sati biyu knn ranar ce rana ta farko da suka samu ganinsa don ba a barin kowa ya gansa, hajiya duk ta rude "nashiga uku haydar kaga halin da ka jefa kanka ko, wae kai wani irin taurin kan tsiya ne Allah ya xuba maka, don ma basa cin ubanka ko," shi dae murmushi kawae yyi bae ce komai ba, brrster umar yyi tsaki yace "ae hkn kafi so sae ka ta xama a nn," cikin tsawa hajiya tace "kasan kuwa me kke cewa umar, dan nawa ne xae ta xama a nn, Allah ya sauwake, mance wacece ni kayi ne," tayi dariya tace "muje dae xuwa ae ni ba a taba ni a kwan lfya" Hajiya ta ja kujera ta xauna tana kallon dan nata tace "ynxu ka gaya min meye matsalarka haydar meyasa baka son bamu hadin kai, me yasa...." ya katse ta da sauri yace "ni matsalata Aneesah, don ban san halin da take ciki ba ynxu," cikin tsawa Hajiyar tace "Aneesar taci ubanta, kaji min mahaukacin yaro, amma ba laifin ka bane dn ubanka," dn takaici ma barrister umar barin wajen yyi dn ji yyi kmr ya kwada masa mari, hajiya tace "kaji min gantalalle wae Aneesah ce matsalarsa, taci uwarta da ubanta, 'yar da ynxu na ganta bbu uban da xae hanani kasheta, wllh wllh wllh da xan ga tsinanniyar nn ynxu idan ban kasheta ba Allah ya hanani abinda nke nema duniya da lahira," Haydar ya bude baki da mamaki ya ma kasa cewa kmai sai kallonta da yake yi "kaji min wahalallen yaro, Allah dae ya kawo min prince lfya na kirasa yana nn tahowa wae, idan kaga dama kaci abincin, pretty ce ta girka maka idan ko baka ga dama ba ka bar shi a wajen ni kaga tafiyata," ta fice a fusace ita ma. . Yau ma kmr kullum Aneesah ta fita neman itacen girkin yamma ta hadu da Mudatheer, ta karaso karkashin bishiyar da yake ta xauna tana kallonsa tace "to baka fa gaya min gidan wa kke ba a nn kauyen" ya dago yana kallonta yace "ina yini?" tayi dariya tace "au na manta ina yini?" bae ce komai ba sae murmushin da yyi, snn yace "gidansu sanusi da lado nake ai kin sansu?" tace "lah wa inan kaxaman masu xaman kashe wando sae ji da kan karya, ko gona bnga suna xuwa ba" mudatheer yyi dariya yace "xasu maki duka kuwa idan suka ji ki" ta hararesa tace "tunda 'yar su ce ni ba, wae in tambayeka meysa su garbebe ke jin tsoranka toh?" nn ma yyi dariya yace "sbda mun taba gwada karfi dasu na raunata su gaba daya, daga nn suka gane ni wanene, kuma na samu kwanciyar hankali daga lkcn a kauyen." Aneesah ta dinga dariya har da buga kafa, yyi murmushi yace "yau ma sae shatu ta biyo ki koh, wae ma meye hadinki da mugayen mutanen nn marasu hali?" Aneesah tayi shiru bata ce komai ba, can ta mike tace "ni xan je neman woods na girki bye bye," ya mike da sauri yace "to bara na rakaki inda xaki samu woods da yawa," tace "to muje," ya shiga gaba tana biye da shi a baya. Da daddaren ranan tana dandali tana sayar da gyada wata 'yar makwabciyarsu shafa ta xo da gudu kiranta, wae shatu tace ta maxa ta dawo gida ko bata sayar da gyadan duka ba, Aneesah tayi ma kawarta karime dake saida xobo sallama snn ta dauki bokitin gyadar ta ta bar dandalin don abokinta mudatheer ma bae xo ba, tana isa gida taga wata tsohuwar mota da ta gama shan wahalar duniya tana neman freedom a fake a kofar gida, ta bi ta gefen motar ta shiga gidan, shatu ta gani xaune kan 'yar kujera, kan tabarma kuwa wani tsoho ne dake ta washe baki, gaban Aneesah yyi mugun faduwa ta dake ta karaso dan tsakar gidan da sallamarta snn ta shige bukkarsu, shatu na wagale baki tace "sannu da dawowa lu'u lu'u, in kin ajiye bokin ki fito ga malam tanko ku gaisa," Aneesah tayi kmr bata ji ta ba ta sulale kasa a hankali cike da tausayin kanta taji kmr ta fasa ihu, shatu ce ta shigo dakin da kanta tana ganin Aneesah a wnn hali ta hade rai, tace "ke ni fa ban son iskanci da rainin hankali, kina ji ina kiranki xaki yi bnxa dani ga bawan Allah can ya xo tun daxu yana jiranki, an gaya maki yana xuwa gun 'yan mata ne da sunan xance, wllh sae dae su suje gidansa su same shi, don mun samu ya tuko santaleliyar motarsa har nn shine xaki masa walakanci, maxa shafa jan baki da hoda ki fito yana jiranki," Aneesah ta mike tsaye da kyar tana kkrin mayar da hawayen da ya cika idonta, shatu na kallonta tayi duk yanda ta ce mata, snn ta sa ta yafa wani dan guntun mayafi, xata fita shatu ta jawo ta da sauri, ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace "ki tausaya min Aneesah idan muka rasa wnn daman mun shiga uku hka xamu ta tsaya wa a talauce har mu mutu, don Allah ki ba sa hadin kai, duk me yace maki kiyi, kinga ko sati biyu baxa a yi ba xa a daura auren ku, idan ma baki son xama wnn kauyen ne sbda 'yan sa ido kawae sae ki koma kauyen dake gaba da wnn yana da gida a can aka ce wae, ki rufa min asiri kar ki sa a mana dariya don ixuwa ynxu lbri ya gama baxuwa wae malam tanko na birni xae aure Aneesah, kar ki bani kunya don Allah," tunda shatu ta fara xancen ta kan Aneesah a kasa yake tana kukan xuci, har shatu ta sallameta tace maxa taje yana jiranta, ta fita jikinta a sanyaye ashe har ya fita kofar gida yana jiranta, tana karaso wa kuwa ya washe hakora yana murmushi yace "yauwa 'yan mata sannu da fitowa," ita dae bata ce kmai ba ta tsaya kanta a kasa, yace "to mu shiga cikin mota muyi hiran mana amaryata," ta dago cike da tsana tana kallonsa tace "A'a nn ma ya isa," yace "haba amaryata ae yawa ne a gan mu tsaye kmr yara a nn, ke dae shiga kawae,"ya bude motar yana kallonta, Aneesah tayi murmushin takaice tace "ni fa baxan shiga wnn motar ba malam," ya tsaya kallonta na kusan minti biyar snn ya bude motarsa ya shige ya ja ta yyi gaba, ta tabe baki a xuciyarta tace Alhmdllh ta shiga gida abinta, shatu na tsaye a bukkarta sae kai komo take ta kasa xaune ta kasa tsaye, Aneesah na shigowa ta riko hannayenta da sauri har wani bari jikinta yake tace "har ya tafi, nawa ya baki," Aneesah ta dan koma baya tace "wae fa mama sae na shiga motar da kila ko fitila ma bbu, ni ko nace masa baxan shiga ba shine ya wuce," shatu ta xaro kwala kwalan idonta ta daura hannu a ka ta kwala ihu tace "shiknn ta ja mana, Na shiga uku ni shatu don ubanki koransa kika yi sbda kin isa?? Na banu na lalace," Aneesah ta tsorata sosae da yanayin da shatu ta shiga, ta dinga komawa baya, cikin tsawa shatu tace "xo nn don ubanki shegiya mugu," . Aneesah ta fasa ihu ta durkushe wajen ganin shatu ta yo kanta, duka kam ta sha shi ranar don shatu komawa tayi kmr wata mahaukaciya, daga karshe ta saba gyale wae xata bi sa gida ta ba shi hkuri duk a rude take, Aneesah dae na durkushe tsakar dakin tana kuka, har shatu ta fita ta dawo kmr an hankadota cikin fushi tace "kuma maxa ki dauki bokitin gyadata ki koma dandali ki tabbatar kin sayar min gaba daya idan ko ba hka ba kar ki kuskura ki dawo min gida, shegiya kawae mugu 'yar bakin ciki," tana kai wa nn ta fice. Aneesah ta kife kanta a kasa tana kuka mai ban tausayi Amminta kawae take tunawa, da kyar ta lallaba ta mike ta dauki bokitin gyadar ta fita daga gidan, a hanya suka hadu da mudatheer ya kirata da kmr baxa ta je ba, har tayi gaba ta dawo, yace "shatu ta doke ki knn," tayi shiru bata ce komai ba tana goge hawayen fuskarta, ya nuna mata benchi ta xauna, bata yi musu ba ta xauna, yace "dandali xaki" ta gyada masa kai, yace "meyasa tun tuni baki je ba sae ynxu, gashi har kusan ten, ae an kusa tashi ma," bata ce masa kmai ba, yyi murmushi yace "me kika yi ta doke ki?" xata yi magana ta fashe da kuka, yyi shiru yana kallonta har tayi mai isar ta, snn ya sake tambayarta me tayi, ta kwashe duk abinda ya faru ta gaya masa, yyi dariya xae yi magana, ta mike a fusace xata bar wajen ya riko hannunta da sauri yace "Haba 'yar birni ni malam tanko ne ya ban dariya," tayi tsaki ta dawo ta xauna, yace "to wae baki gaya min hadinki da su shatu ba har ynxu" tayi shiru, yace "yau ma baxa ki gaya min ba knn" tace "sbda me kke son sani?" yace "i just want 2 knw a bit about yhu, kinga i may b leavin in 3dayz tym" ta wara ido tace "wucewa xaka yi?" yace "yes, na gama abinda ya kawo ni," Aneesah tayi shiru duk sai ta ji ba ddi, xata yi magana sae ga Zano da kawayenta sun dawo daga dandali, tana ganinta ta mike da sauri gabanta na faduwa tace "na shiga uku mudatheer xata gaya ma mama, kuma ban ma gama saida gyadar ba, ya ce nawa ne gaba daya, tace "dari uku ne ina ga," ya ciro dari biyar ya mika mata tace "aa ni ka rike kudin ka kawae," ya harareta yace "xaki koma ki kara shan wani dukan kuwa," ta karba tana kallonsa, tace "to gyadar fa?" ya ce "ki koma gida da shi, sae kice su garba ne suka baki kudin xata ji ddi tunda mayyar kudi ce," Aneesah tace "to bbu canji," yace "eh ki kai mata hka," tayi masa gdya ta mike jikinta a sanyaye ta kama hanyar gida, tana tunanin shawarar da karime ta bata ranan bayan ta bata lbrinta tun daga farko har ixuwa ranar da baffa ya kawota kauyen, karime tace ta gudu kawae amma ta kasa gudu wa daga kauyen kuma ta rasa dalili, kwata kwata bata sha'awar barin kauyen ita kam ta rasa meyasa, don wani lkcn ko tunanin gida bata son yi, a hka ta isa gida gabanta na faduwa a xuciyarta tana cewa "Allah yasa Zano bata gaya ma shatu ta gan ta da mudatheer ba, amma sae ta samu ma bata karaso gida ba, shatu na ganin dari biyar ta rikice ta dinga sa ma Aneesah Albarka ba tare da damu da inda ta samo ba ma. Washegarin ranar sae ga malam tanko ya xo da daddare, shatu ta lallabata ta fita, bata yi masa musu ba ta shiga rubabbiyar motar tasa, sae washe hakora yake yace "amaryata muje gun sule mai suya in dan siya maki nama," ta girgixa kai tace "bana ci," yyi dariya snn yace "to muje in xaga dake kauyen ko ya kika ga," gabanta ya dinga faduwa ga tsoran shatu, ba tare da ta sake wani tunani ba tace "toh," yyi murmushi yace "yauwa Amaryata, snn ya tada motar, ya ja ta," shatu na leke ta katanga, tana ganin hka ta sauke ajiyar xuciya ta daga hannu sama tace Alhmdllh bata tona min asiri ba, 'yar albarka. ~19~ .Aneesah dae bata tanka ma malam tanko dake ta sharara mata surutu a motar ba, hasalima kauda kanta tayi tana kallon glass din motar, ita duk kyankyamin motar ma ta isheta, yace "Haba amaryata ya hka ina ta magana kin min shiru," nn ma bata tanka saba, har suka isa gun sule mai nama, ya siya naman dari da hamsin ya bi ta shagon lado ya siya pure water leda biyu snn ya dawo ya shiga motar rike da naman da ruwan ya mika ma Aneesah yana washe rubabbun hakoransa, tayi kmr bata san yana mika mata ba, ya ajiye gefenta yace "sannu amaryata," ko kallnsa bata yi ba har yaja motar suka bar wajen, taga yyi parkin wajajen gonannakin mutane, ko ina duhu sae dan hasken wata, ya kamo hannunta yace"amaryata ci nama," ta fixge hannunta gabanta na faduwa tace"meye hka?" ya dan hade rae yace "nama nace kici," a fusace tace"ban ci, ka ci kayanka nace mka yunwa nke ji ne" tana fadin hka ya fixge dan mayafin dake kanta yace "ke kar fa ki kawo min raini, kin san ko ni wanene," ta fara kkrin bude motar xata fita ya fixgota yace "ina xaki," ta hankadesa da sauri tace "to motar ta ubana ne da baxan fita ba," yace "ae baki isa ba yarinya sae kin biya min bukatata yau, cikin kwanaki uku na kashe maku fiye da dubu daya, hakosu nace ina yi a rami" ta yo waje da ido a tsorace ta fara kkrin bude motar ya rikota yana kkrin yaga rigar jikinta tace "nashiga uku, meye hka, malam ka rabu dani ni ba 'yar iska bace," yace "ae nima din ba dan iskan bne, kudina da kuka ci xan amsa ta nn," bae ko damu da haukan da take yi ba ya matse ta yana kiciniyar cire mata kayan jikinta, ta fasa ihu, amma bbu mai jinta dan gurin kmr daji yake, ta wanka masa wani lafiyayyan mari tare da basa wani naushi a ido da karfinta, ba shiri ya saketa bayan ya saki 'yar karar axaba, hannunta na rawa ta shiga bude motar ya budu xata fita ya fixgota ta yakushi fuskarsa ta fice a guje, ko dankwali bbu a kanta, gudu kawae take a tsorace tana bin hanyoyin da ta san xae sada tada gida, garbebe da lado ta hadu da a wani corner suna ta tuntsirardariya suna lbrin irin bata wata yarinya hajjo da suka yi jiya da daddare, tana ganinsu ta juya da sauri ta canxa hanya, ji tayi lado na cewa kae garu ga 'yar birnin nn ita ce, suka ko bita a guje, ita magudun take kmr xata tashi sama, cikin ciyawa ta labe jikinta na rawa har suka wuce ta da gudu, gabanta ya dinga faduwa ga tsoran kar maciji ya sareta a wajen, ta kai kusan minti goma a cikinciyawar gudun kar ta yi gaba su hadu kuma, daga karshe wata hanyar ta canxa kuma, ta dinga gudu tana waige waige tana kuka kide kide ta dinga ji daga nesa alamar ta kusa dandali, ta tuna mudatheer yace ta xo dandali xae nuna mata abu, bata bi ta dandalin ma ba don bata san ko sun yi can ba ta sake canxa hanyatana dan tafiya da sauri da sauri tana waige waige, ji tayi ta ci karo da wani katon dutse ta fasa ihu tayi kasa xata fadi taji an yi saurin rikota su ka fadi a tare duk da bata wani buge ba dan kan wanda yakamota ta fada sae da ta fashe da kuka, taga ya ciro wayarsa da sauri yana kkrin haska fuskarta yace "Goddam Yhu baki kalln gabanki ne kina..." yana haska fuskarta da wayarsa taji ya dan koma baya da sauri yyi tsit, ita ma shirun tayi tana ta kallon fuskar dake gaban screen din wayar, ganin ya ki daina haska ta ne yasa tafixge wayar daga hannunsa ta shiga haska fuskarsa ita ma, wani kyakkyawan handsome guy idonta yyi tozali da, ta tsura ma manyan fararen idanunsa nata idon, ta saukar da kallonta kan pink lips dinsa dake ta kyalli, wayyo ya Haydar dinta exactly, fixge wayaryyi daga hannunta ita ma, ya tura ta ya mike tsaye yace "kina tafiyakmr wata mara saiti dubi yanda kika min da jikina," bata ce komae ba ta fara tafiya a sanyaye ya fixgota yace "cnt yhu thank me, da nabarki da kin fasa kai yarinya," ta fixge hannunta ya sake fixgota ya ja ta suka xauna kan dakalin da yake a xaune, yace "amma fa ke kyakkyawa ce, wait ko ma dae kece mudatheer yace na xo na gani a wancan gurin haukan naku?" ya fadi hkn yana nuna mata dandali,tace "lah kasan Mudatheer ne?" ya gyada mata kai yace "yea sch son dina ne muna sec sch, nn yake service ae, amma gobe xai gama shine yace na xo naga yanda kauye yake tunda ina garin," ke kuma naga baki yi kalan 'yan kauye ba, hw come kike kauye, ko daehutu kika xo kema, ya sunanki, me ma yake sa ki gudu da daren nn, baki tsoro baki dauki fitila ba Aneesah tace "kai wnn irin tambaya hka sae kace dan jarida," yyi dariya da ya bayyana dimples dinsa, tatsura masa ido tana kallo, Haydar kawae take tuna wa, ya daura hannu a kanta ya wara idonsa yace "ya dae" ta buge masa hannu tace "meye hka," yace "ohh sowie bby," ta tabe baki a xuciyarta tace"wnn dae dan iska ne dama yyi kama da su," ta mike xata bar wajenya fixgota har tana faduwa kansa yace "ke baki gaya min sunanki ba," tace "A'a meye haka malam," yace "sae kin gaya min sunanki xaki bar nn," da sauri tace "Aneesah,".Ya wara dara daran idonsa yace "waw sweet name Aneesah," Aneesah tace "to ka sake ni ai na gaya maka sunan nawa," ya xaunar da ita yace "No Aneesah tsaya mu dan yi hira, don Allah" xata yi magana ya daura yatsunsa biyu kan lips dinta yace "shhiii," tayi shiru tana kallonsa yyi murmushi yace "kina da kyau Aneesah," ta kauda kanta nn ma bata ce komai ba, ya kamo hannunta yace"hu2 kika xo yi nn Bby?" ta fixge hannunta tace "wae meye hka kke taba ni ne na sanka ne," ya kashe mata ido yana lasan lebensa yace "ni sunana Mujaheed Yusuf," tace "to naji," amma ka bar ni na koma gida, ya harareta yace "not until u tel me y u were running," ta dan marairaice fuska tace "wllh wasu mutane ne ke bi na," ya mike da sauri yace "su wa? A ina suke, me kika yi masu, xo ki nuna min inda suke," yana fadin hka xae fara tafiya ta riko hannunsa tana dariya tace "to me xaka masu?" yyi mata wani irin kallo yace "nuna min su kawae ki ga abinda xan masu," tana dariya tace "ae bn san inda suka bi ba," ya dawo ya xauna yace "da sun biyo ki har nn wllh da na cire masu hakoran bakunansu gaba daya," Aneesah tace"uhmm naga alama" Nan Mujaheed ya dinga mata surutu kmr da cansun taba sanin juna, ita ko ta biye masa sae dariya take yi, ana farafitowa daga dandali ta mike da sauri tace "kaga ni xan wuce gida kar yayyina su gan ni a nn," xae yi magana ta hangosu xulai ta juya da sauri ta fara gudu ta bar wajen, yace "shit ban san wacece ita ba," mudatheer ne ya karaso gurin yana kallon Mujaheed yace"kana nn har ynxu ashe big bro, da ka shigo da ka ji ddi, amma sae dae 'yar birnin bata xo ba yau" Mujaheed ya dan daga kafada yace"na ganta, ko ba Aneesah ba," mudatheer yace "waw ita fa, a ina ka ganta?" Mujaheed yace "she's such a beauty, ynxun nn ta bar nn wae kar yayyinta su ganta, da gske nn aka haifeta" Mudatheer yyi dariya yace "A'a ko wata uku bata cika ba a nn," Mujaheed yace "ni kam na xo kauye a sa'a don na samu mata, kaga xuwa nan ya kamani duk sati knn" Mudatheer yyi dariya ssae yace "gskya ne, ka ga ni xan tafi kai kuma ynxu kke xuwa, amma fa sae dae gidan da take a nn ba gidan mutunci bne don mutanen gidan kowa ya san suda halinsu a kauyen nn," Mujaheed yyi tsaki yace "dont tel me dat, ina ruwana da halinsu, as far as ba su suka haifeta ba its none of my bzz," mudatheer yyi dariya suka bar wajen yana cewa "kaga ina ta damunka kaxo kauye kana ja min aji ashe alkhairi xaka xo ka tarar a nn," mujaheed yace "yaushe xaka tafi," "gobe da safe," mudatheer ya ba shi amsa, Mujaheed yace "xan samu ganinta da safe kafin mu tafi don Abuja nake son wucewa direct," Mudatheer yace "yes of course amma idan kaje rafi," Mujaheed yace "ehh sae naje to meye a ciki?" Mudatheer yace "to xaka kwana nn ne ko fita xaka yi," Mujaheed yace muje motata ma tana nan ae, ba karamin tashin Hankali Aneesah ta tarar a gidan ranan ba daga shatu don kasheta ne kadae bata yi ba, kuma wae washegarin ranar a gun tanko xata kwana ko taki ko ta so tunda dae shi xae aureta wae, kuka kam ta yi shi har kusan asuba, Da safe ta je debo ruwa a rafi duk jikinta a mace ga yawan faduwar gaban da take yi ta hadu da su Mudatheer suna jiranta karkashin wata bishiya, tayi mamakin ganinsu a tare amma tayi kmr bata gansu ba tayi gaba mudatheer ya kirata da sauri taki juyowa, ya mike ya bi ta yana cewa "Aneesah yau fa xan tafi shine kike min wlknci?" ta juyo da sauri tace "da gske?" yace "ehh," ta ce "to baxa ka sake dawowa ba," ya juya yana kallon Mujaheed da ya kasa daina kallonta yace "yayana xae dinga kawo maki visit ae," ta kalli Mujaheed ya kashe mata ido, ta galla masa harara tace "bana son visit din," Mudatheer yyi dariya yace"yayana ne fa," bata tanka sa ba tayi gaba duk jikinta a sanyaye ynxu Mudatheer wuce wa xae yi ya bar ta, da rana Mudatheer ya bar kauyen duk da ya so ganin Aneesah amma bae samu ganinta ba, Mujaheed ya kai sa har tashan da xae hau mota a motarsa shi da ya kamata daga can ya kama Hanyar Abuja yace ina ae sae ya dawo yyi sallama da Aneesah. Aneesah dasu xulai da karime na dawowa daga kauyen dake kusa da nasu sunje saro ma shatu gyada, suna tafe suna hira banda Aneesah da tayi nisa a tunaninta,oh ita ynxu hka rayuwarta xae kasance a gantale knn, tana tuna abinda shatu tace mata jiya da daddare wae gidan tanko xata kwana sae taji wani hawaye na xubo mata, xulai taji tana cewa "lah ga abokan Aneesah xuwa," Aneesah ta dago kai da sauri ta ga shanaye ke tahowa ta inda suke, a rayuwarta tana bala'in tsoransu ba kadan ba, duka suka tuntsire da dariya, ita ko ta hade rae xata canxa hanya xulai ta rikota tace "ae baki isa ba sae kun gaisa yau," ihu Aneesah ta dinga yi tana dukanta ta sake ta amma taki, sae dariya suke yi, karime ce kadae ta hade rae tace "meye hka xulai ku kyaleta mana," ganin sun ki sakinta ne kuma ga abun da take tsoro sun kusa inda take yasa ta fixge hannunta daga rikon da suka yi mata a guje Ta afka dan titin motar dake wajen, suna ihu suna ga mota ga mota, amma ina bata ma san suna yi ba..Kamar daga sama Aneesah taji abu ya buge ta da karfi, daga nn kuma bata sake sanin abinda ya faru ba, karime da su xulai suka fasa ihu ganin abinda ya faru suna cewa "wayyo shiknn ya kashe mana Aneesar mu," mai motar ya fito daga motar da sauri yace"subhanalla hi,"ya durkushe gabanta ya dago ta, su karime duk sukaxagaye shi suna koke koken Aneesah ta mutu, ya tura xulai dake daf da kansa tana rusa ihu a fusace yace "ke da'alla ja can uban wayace maki ta mutu," xulai ta koma baya da sauri tana yarfe hannu tace "wayyo ashe bata mutu ba karime," daukar Aneesah yyi ya saka cikin motar ya dawo xae shiga driver sit, karime ta bisa da gudu xulai da yayarta Xano na biye da ita a baya, karime ta rike

Chapter 10 of 23