Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sauka downstairs a tare, mumy tace ina xa ku, Mujaheed yace xamu dan fita ne, tayi masu Allah ya kiyaye, suka shiga mota Abdul ya ja ta. Sae da suka yi nisa snn Abdul yace "ina xamu?" Mujaheed yce waida inda Aneesah take xamu, amma mum ta hanani xuwa kuma ni bana tsallake umarninta," Abdul yyi tsaki yace "kai fa wani gara ne, ae ba kai xaka je ba kai ni kawae xaka yi, naga kanwata." . Mujaheed yyi shiru yana kallon Abdul, Abdul yace "yes, ae ba xuwan kanka xa kayi ba, rakani xaka yi," Mujaheed yyi murmushi ya ciro wayarsa, yyi dailn nmbr Hydar, ya shiga kiransa, tun bayan abinda ya faru tsakaninsu har yau basu yi cmmncate ba, har ya fidda ran Hydar xae daga ya ga ya daga, ba tare da bata lkci ba yace "dama na kiraka na gaya maka ne, mum din Aneesah na gida ynxu, ko xaka je ka dauketa daga inda take ka kai ta gida," Abdul ya fixge wayar daga hannun Mujaheed din ya katse kiran yace "ni ka bani Address din gidan naje na dauketa na kai ta gida, kila hkn xae sa ta daina min abinda take min, ta dinga ganin mutunci na," Mujaheed ya tsaya kallonsa yana doubt dinsa a xuciya, can dae yace bari kawae muje, xan ma mum bayani nasan xata yafe min, ko minti biyar ba ayi ba Hydar ya kira Mujaheed, mujaheed ya daga hydar yace "ban gane xancenka ba," Mujaheed yace "no barshi ma kawae," yana gama fadin hka ya katse kiran, suna isa gidansu Mudatheer, Mujaheed ya kirasa yace "ga su nn a kofar gida Mudatheer yace su shiga daga ciki don shi baya gida, Mujaheed bae lura da motar Hydar dake parke a waje ba ya shiga gidan, Hydar dake xaune kan kujera karkashen wata 'yar bishiya yana jiran Aneesah don shima shigowarsa knn gidan ya bi su da kallon mamaki, su kam basu lura da shi ba ma, Aneesah da tunda mai gadi yace ana nemanta taji gabanta na faduwa don tasan Hydar ne ita kuma tsoransa take ji ynxu ta fito a sanyaye bayan ta nemi ixini gun Momy, tana fitowa daga falo suka yi ido huda da Mujaheed a tsakar compound yana taho wa, Abdul kuma na bayansa, ko lura da Abdul din ma bata yi ba, ta yo waje da ido cikin wani mugun farin ciki tace "yayana," Mujaheed ya wara mata ido shima da farin cikin yace "kanwata," ta taho da gudu, ya buda hannunsa ta fada jikinsa ta kankamesa, ya daura bakinsa kan goshinta, kmr xata yi kuka tace "yayana, ina ka tafi ka barni," cikin rada yace mata "abubuwa ne suka min yawa kanwata," sae a lkcn ta lura da Abdul ya dan koma baya a tsorace tana kallonsa, ta kauda kanta da sauri tana shirin barin wajen gabanta na faduwa, cak komai na ta ya tsaya ta dalilin ido hudun da suka yi da Hydar, tuni jikinta ya dau rawa, ta fixge hannunta daga rikon da Mujaheed yyi Mata da karfi ta sulale kasa wajen jin kafarta ya kasa daukarta, Mujaheed ya durkushe gabanta da mamaki yace "me ya faru kanwata," ta fashe da wani matsanancin kuka tana kallon Hydar da ya mike da kyar daga kan kujerar da yake, yyi hanyar fita daga gidan, Mujaheed ya bi sa da kallon mamaki shima, Aneesah ta mike tsaye da sauri ta bi bayan Hydar din, Mujaheed ya bi ta da kallo xuciyarsa na tafarfasa, har hydar ya bude motarsa xae shiga Aneesah ta karaso kusa da shi ta durkushe gabansa tana kuka ssae tace "wayyoo ya Hydar wllh ban san....." mari mai rai da lfya ya watsa mata snn ya fincikota ya jefar da ita daga gabansa ya shige motarsa ya wuce, kallon kallo Mujaheed da Abdul suka shiga yi a tsakar gidan, a nutse Abdul ya karaso kusa da shi yana masa wani irin kallon yace "dama son Aneesah kke, kake amfani da ni wajen cimma burinka," to bari kaji na gaya maka, baka isa ka aure Aneesah ba, Aneesah tawa ce ba ta kowa ba, Abdul na fadin hka ya juya xae fita daga gidan Mujaheed ya riko hannunsa yace "ka cire Aneesah a ranka, she ix mine" yana fadin hka ya cika sa yyi hanyar fita daga gidan shima ~34~ .Mujaheed na fitowa kofar gidan ya tarda Aneesah durkushe kasa tana kuka, tana ganinsa ta mike tsaye tana share hawayenta, ya karaso gabanta yana mata wani mugun kallo yace "me yasa baki bi sa ba," ta girgixa masa kai tana kuka tace "yayana....." sae kuma maganar ya makale ta fashe da wani sabon kukan, Mujaheed ya girgixa kai ya daga mata hannu yace "kar ki gaya min komai, hold on 2 yhur crocodile tears, dama munafurta ta kika yi kika ce min Hydar baya son ki, don me kika min karya kikace bbu komai tsakaninki da Hydar, whereas masoyinki ne, why Aneesah?" kuka kawae take tana girgixa masa kai, ya kauda kansa ya hade tafikan hannunsa, can ya juya yana kallonta cikin tsawa yace "don me baki bi sa ba, nace don me baki bi sa ba, ae da kin bisa da kukan da kika tsaya kina ma mutane a nn, munafuka kawae" yana kai wa nn ya juya a fusace ya shige motarsa yyi gaba. Aneesah ta sulale kasa a hankali ta bi motar da kallo tana girgixa kanta, kukan ma wnn karan kasa yi tayi, wnn wace irin rayuwace, a hankali taji Abdul ya dafa kafadarta ta juya da sauri tana kallonsa sae a snn ta fashe da wani kuka mai ban tausayi, ya dago ta yana kallonta ya shiga share mata idonta yace "it's owkay Aneesah," bata ce masa komai ba ya dauko gyalenta ya mika mata ta karba hawaye na bin kuncinta, ya kama hannunta suka bar wajen, ita bata ma san binsa take ba suna tafiya, duk abun duniya ya isheta, har lkcn bata daina hawayen da take ba, sae da suka bar anguwar snn tayi saurin fixge hannunta ta shiga waige waigen inda suke tace "ina xa ka kaini?" yana kallonta yace "gurin babarki xan kai ki," ta girgixa masa kai tana kuka ssae tace "aa Ammina bata nn, ka barni na koma gida," ya kamo hannunta yace "kar ki damu Amminki na gida," ta juya da sauri tana kallonsa cikin muryar tausayi da rashin hope tace "da gske ya Abdul," ya gyada mata kai yace "eh, xan kai ki ki ganta ai," hkn yasa ta dinga binsa jiki ba kwari, suna ta tafiya a kafa, duk a rikice take don bata san ko Abdul gaskiya ya gaya mata ba, ita dae kawae ta ga Amminta, sunyi tafiya mai nisa, ta dan duka alamar gajiya, ya juya yana kallonta yace "me ya faru?" a sanyaye tana kallonsa tace "ruwa xan sha ya Abdul," yaji tausayinta ssae, ya dago ta yace "ba kudi hannuna Aneesah, bank nake dubawa ko xan samu mu cire kudi a Atm," ta gyada masa kai kawae, ya kama hannunta suka ci gaba da tafiyar, har daga karshe suka samu wani banki, ya ciri kudi a ATM tana gefensa a tsaye, sae da ya fara siya mata table water biyu snn, ya tsayar da taxi ya fadi anguwarsu Aneesar, hkn yasa taji mugun ddi, ta yrda ba cutar da ita Abdul xae yi ba, duk da a xuciyarta tana cewa wahalar bnxa kawae xasu je suyi, amma bata nuna masa sun je da Mujaheed Ammi bata nn ba, ko bakomai xata ga makwabciyarsu ta gaya mata ko suna communicate da Amminta, bayan minti talatin suka iso anguwar tasu, sae taji duk wani bakin cikinta ya yaye, hankalinta ya kwanta, Abdul ya nuna ma mai taxin inda xae tsaya dae dae kofar gidansu Aneesah. . Hydar yana kallon Mujaheed yace "ina kke tunanin xae kai ta?" Mujaheed ya girgixa kai cikin damuwa yace "wllh ban sani ba, gashi duk ya kashe wayoyinsa," Hydar ya dafe kansa yana kiran Allah a xuciyarsa, Mudatheer dake wajen a tsaye ya ma kasa cewa komai shima sae try din nmbr Abdul din yake, mujaheed yyi hanyar motarsa yace "ina xuwa" Hydar ya sha gabansa yace " ina kke tunanin xa ka? tun wuri lkci bae kure maka ba ka fito da Aneesah kar na baka mamaki, don nasan karya kke, karya kke, kai ka dauke Aneesah," Mujaheed yyi masa wani mugun kallo snn yyi kwafa yace "am on my own fa, kar ka tunxura Hydar, dont piss me off, baxae mana kyau daga ni har kai ba a nn," Hydar ya bugi kirjinsa yace "do yhur worst" Mudatheer ya shiga tsakaninsu yace "haba dis is nt a matter of quarrellin guyz, a bi komai a nutse xa a ga Aneesah idan Allah ya yrda," Mujaheed ya shige motarsa, yyi reverse, Hydar ma ya shiga tasa motar ya bi sa a baya, suka shiga tafiya, Hydar yyi mugun mamaki ganin Mujaheed ya sha kwanan anguwarsu Aneesah bayan tafiyar da suka yi mai nisa, ya na ta binsa har suka isa dai-dai kofar gidan snn duk suka fito daga mota, ko kallonsa Mujaheed bae yi ba ya shiga gidan, Hydar din na biye da shi a baya da mamaki, Aneesah na xaune tsakar gidan tana wanke wanke, Ammi ko na ta gyare gyare a daki wajen karfe biyar na yamma, wae yau ita ce ga ta ga Amminta a gidansu, Allah kadae yasan irin mugun farin cikin da take ji yau, wani lkcn sae ta ga kmr mafarki take xata farka, jin an shigo gidan ko sallama bbu yasa ta juya da sauri a dan tsorace tana kallon kofar soron, mikewa tayi da sauri ganin Hydar da Mujaheed, Mujaheed ya jingina jikin bango ya lumshe idonsa tare da sauke wani ajiyar xuciya, Hydar kam kasa daina kallonta yyi, ta juya a hankali tayi cikin dakinsu, Mujaheed ya bude idonsa yana kallonta, Ammi tace "kin gama ne Aneesah," ta girgixa ma Ammi kai a sanyaye tace "ya Hydar ne ya xo," Ammi tace "haba," ta gyada ma Ammi kai, Ammi tace "to ki ce ya shigo mana," ta girgixa mata kai tace "ba shi kadae bne," Ammi tace "to duk su shigo," ta mike ta fita tana kallonsu tace "wae ku shigo," Mujaheed ya juya yana kallon Hydar dake kallonta, da mamaki Hydar yace "Ammi na gidan nn ne?" kai kawae ta gyada masa yyi hanyar dakin, Mujaheed ya juya ya fice daga gidan. Hydar suka dinga hira da Ammi tana basa lbrin inda baffa ya kai ta bayan sun gama dogon gaisuwa, sae a snn ya shiga bata lbrin abinda baffan yyi masa shima, Ammi ta kasa cewa komai don tausayin hydar, ita ko Aneesah na tsakar gida a xaune don har lkcn ita bata ba ma Ammi lbrin irin abubuwan da ta fuskanta na rayuwa ba, Abdul ya shigo rike da ledojin eatry tana kallonsa har ya karaso gabanta snn tace "sannu da xuwa," ya gyada mata kai yace "Ammi fa," ta juya tana kallon daki alamar tana ciki, ya isa bakin kofar yyi sallama Ammi ta amsa, ya shiga, Hydar ya juya yana kallonsa, shi ko kallo daya yyi masa ya kauda kansa, ya ajiye ledan hannunsa yace "sae da safen mu," Ammi tace "to Allah ya kai mu mun gde Abdurrahman," ya gyada mata kai ya fita daga dakin, har lkcn Hydar bae daina kallonsa ba. . Hydar bae bar gidansu Aneesah ba sae kusan Maghrib, tana xaune har lkcn a tsakar gida amma wnn karan alwala take, bae ce mata komai ba ta bi sa da kallo har ya fita daga gidan snn ta mike a sanyaye ta shiga dakin, sae da ta idar da sllh snn Ammi ta kirata, ta juya tana kallon Ammin bayan ta amsa, Ammi tace "Aneesah dama abinda ya faru da ke knn, dama kauye baffanki ya kai ki, meyasa baki son gaya min irin abinda kika fuskanta Aneesah" Aneesah tayi shiru bata ce ma Ammi komai ba tana kallonta, Ammi ta girgixa kai hawaye cike idonta tace "Allah ya saka mana Aneesah, ba mu da abinda xamu ce da ya wuce hka" ta kamo hannunta a hankali tace "Aneesah ina fatan wahala bata sa kin yasar da mutuncinki da darajar ki a waje ba," Aneesah ta girgixa ma Amminta kai tana hawaye tace "A'a Ammi," Ammi tayi shiru tana kallonta, can kuma tace "to shi kuma wnn da suke tare da Abdul waye," Aneesah ta share hawayenta tace "ya Mujaheed sunansa, shi ya dauke ni daga kauye ya dawo dani Abuja, abokin ya Hydar din ne, yana da kirki Ammi," Ammi tana kallonta tace "da ya daukeki a kauyen ya dawo dake nn ina ya ajiye ki?" Aneesah tayi shiru tana kallon Ammi snn a hankali tace "gidansa," Ammi tace "gidansa? Kike me a gidansa?" Aneesah ta kasa cewa komai har sae da Ammi ta sake maimaita mata tambayar snn tace "Ammi ko ina nemana ake wae xa a kasheni ni bansan me nayi masu ba, harda Hajiyarsu ya Hydar ma, shine daga baya ya kaini gidan maman wani abokinsa nake tsayawa a can, suna da kirki gidan ssae Ammi," Ammi tace "kin kwana gidan nasa ne Aneesah kar kiyi min karya," da sauri ta girgixa ma Ammi kai tace "A'a" Ammi tace "to Allah ya taimakesa kmr yanda ya taimake ki," sallamar da suka ji daga bakin kofa yasa Aneesah ta mike da sauri tace "Ammi shine," Ammi na kallonta tace "to ya shigo," ta fita da sauri ta samesa tsaye, tace "wae ka shigo," ya bi ta a baya har suka shigo dakin, suka gaisa da Ammi da fara'arta tana tambayarsa ya gajiya, Ammi tace "a xubo maka abinci," Mujaheed na kallon Aneesah dake kallonsa yace "ehh Ammi a xubo," Aneesah ta mike ta kawo masa abincin ta ajiye gabansa ta koma ta xauna, hira suka dinga yi da Ammi yana cin abincin, sun yi hira ssae fiye da yanda suka yi da Hydar ma kmr da can sun saba da juna, Mujaheed bae bar gidan ba sae kusan karfe sha daya, Aneesah ta fita rakasa bae ce mata komai ba har suka iso bakin kofa snn ya juya yana kallonta bbu yabo bbu fallasa yace "ki koma gida," yana fadin hka ya fice daga gidan, ta juyo jikinta a sanyaye ta koma daki, Ammi tace "amma yana da kirki Aneesah, shima iyayensa a nn garin suke," Aneesah tace "aa yace min suna malaysia," duk surutun da Ammi ta dinga mata kan Mujaheed hankalinta baya gun, ta rasa dalilin da yasa suke mata hka, ganin Ammi na shirin kwanciya lura da tayi cewar 'yar ta ta ba jin yin hiran take ba, yasa Aneesah tace "kinsan me Ammi," Ammi na kallonta tace "sae kin fada," Aneesah ta dan yi shiru snn a sanyaye tace "shine fa wanda ya taba fasa ma Yusuf ball dinsa ya basa dubu biyu," Ammi ta tsura mata ido tana kallonta, Aneesah ta hau kan gado tana kallon Amminta tace "sae da safe Ammi," tayi kwanciyarta tare da lumshe ido. washegari tun da sassafe Abdul ya xo gidan, Aneesah na sharan tsakar gida ta mike tsaye tana kallonsa har ya karaso cikin gidan snn ta gaishesa, ya amsa ya tambayi Ammi fa, Aneesah ta nuna masa daki, ya gyada mata kai snn ya ciro wayarsa ya kira Mujaheed yace "hy ka taho gidansu Aneesah ynxu, just want 2 hand over d documents over 2 yhu" yana gama fadin hka yyi sallama ya shiga cikin dakin. Ko minti ashirin ba ayi ba Mujaheed ya taho, shima ya shiga dakin bayan sun gaisa da Ammi Abdul ya mika masa takardun hannunsa, Mujaheed na murmushi yace "no Abdul, sae anjima a kotu xaka fito da wnn," kan Abdul yace komai wayar mujaheed ya shiga ring da kmr baxae daga ba ganin Hydar ne sae kuma ya dan tabe baki ya daga, Mujaheed yace "what?" bayan ya gama jin abinda Hydar yace, ya mike tsaye da sauri yace "subhanallahi," Abdul na kallonsa yace "me ya faru?," hka ma Ammi. ~35~ .Aneesah da Amminta suka dawo gida jikinsu a sanyaye ranar daga kotu, Rayuwa knn dama watarana sae lbri, kuma Hkuri shine wadata, Abdul ne yyi drivin din a motar Hydar ya mayar da su gida, Hydar ko na xaune gefensa a gaba, Mujaheed dama daga kotu yana shiga motarsa yyi gaba, suna isa gida bayan Aneesah da Amminta sun shiga, Hydar ya juya yana kallon Abdul yace "kar ka damu frnd, nn da 'yan watanni sae mu sake tada case din, daga nn sae a samu dad dinka ya fito," Abdul yace "in shi ya fito sae wa ya shiga?" Hydar yyi murmushi yace "ba kowa idan Allah ya yrda" Abdul ya daga kafadarsa bae ce komai ba, Hydar ya fito shima ya fito suka shiga gidan, Abdul dae na xaune a tsakar gidan yana kallon Aneesah dake kkrin kunna wutan coal xata daura girki, yyi murmushi yace "na karshe kike yi hka ko me," ta juya tana kallonsa bata ce komai ba sae murmushin da tayi ta cigaba da abinda take, ita kam tausayi yake bata, ashe dama Abdul ba ruwansa hka, Hydar na daki xaune da Ammi, sae da ya bari ya gama jin batun Ammi dake masa magana a sanyaye snn yace "wnn ba matsala bane Ammi, nayi masa magana daxu a mota bae dae ce min komai ba, nace nn da 'yan watanni xa a sake dago case din," Ammi tace "amma ba ddewa xa ayi ba ko Hydar?" Hydar yace "sae nn da wata uku don yaji ya xaman prison yake, nxt tym baxae yi marmarin taba abinda ba nasa ba, ae dama rayuwar sae da had i knw" Ammi xa tayi magana ya riga ta da sauri don bae son jin abinda xata ce yace "to ynxu Ammi yaushe xa ku bar nan?" Ammi ta girgixa masa kai tace "A'a ni ina nn," Hydar yyi shiru snn yace "kar ki ce hka Ammi, muje ki xabi daga cikin gidajen da kike son ki xauna," Ammi tace "ni fa ina nn Hydar," bae sake ce mata komai ba, tace "kaje Asibiti kuwa yau," ya girgixa mata kai tace "sbda me Hydar? Wae me yasa kke hka ne Hydar?" yace "ae akwae mutane a asibitin, amma ynxu nake son tafiya dama," Ammi tace "to ka tashi ka tafi, kuma ka gaida mana su, Allah ya sauwake," yace "Ameen Ammi," snn ya mike yyi mata sallama ya fita, ya kalli Abdul da har lokacin ke kallon Aneesah tana ta aikinta yace "mu dan tafi Asibiti Abdul" Abdul ya mike yace "ni akwae wani allura ma da nake son ayi masu naga nn ko maganar alluran basa yi, amma tsada gare shi may b sae an fita da su," tare suka fita daga gidan Aneesah ta bisu da kallo, suna fita ko minti goma ba ayi ba Mujaheed ya shigo, ta juya tana kallonsa ta gaishesa murya can ciki, ko kallonta bae yi ba, kuma yyi kmr bae ji ta ba yyi sallama Ammi ta amsa ya shiga dakin, ya gaishe da Ammi ta amsa tana tambayarsa ya gajiya, yace "Ammi, wani gidan kike son a bude maku in ma da gyara ciki a yi sae ku koma," Ammi ta girgixa masa kai tace "A'a ina nn Mujaheed nn ma ya isheni," nn fa Mujaheed yace bae san xance ba dole sae sun bar wnn gida, Ammi tayi murmushi tace "to ka bari ba ynxu ba tukun, sae an sake baffansu," Mujaheed yyi shiru bae ce komai ba, bae kuma sake musu da ita ba yace xae tafi, tace "ka tsaya kaci abinci mana Aneesah ta kusan gama girki," ya dan kalli tsakar gidan snn yace "xan dawo Ammi," ya mike yyi mata sallama ya fita. Da yamma Hydar ya shigo gidan Ammi ta tambayesa ya jikin kannin nasa da babarsa, ya dae ce da sauki, Ammi tace "wae da tuwo nake girka masu ka kai masu," yace "to mun gde Ammi," karfe shidda ta gama hada Abincin ta basa ya kai masu, ya karba yyi gdya ya bar gidan, ranar da daddare Aneesah ta ci kuka jikin Amminta wae yau ga su ga dukiyar Abbansu a hannunsu, duk da a hkn ma ba duka ba, gidaje uku suka samu, sae motoci uku da filaye da dama, snn kudin dake accnt ma an basu kayansu, sae taji tausayin Abdul ganin ya dake bae nuna komai ba har aka yanke ma ubansa hukunci, duk da ta lura hkn ya girgixa sa. Washegari da safe Abdul din ya xo gidansu, ta hada masa breakfst a daki ta fita ta cigaba da abinda take yi don Ammi na makwabta, suna tsakar gidan su biyu a xaune tunda dae ba hira suka saba ba, sae dae ya kalleta ta kallesa Mujaheed ya shigo gidan, Aneesah ta mike tsaye tana kallonsa ta gaida shi, yana kallon Abdul yace "Ammi fa," Abdul yace "bata nn," Mujaheed yace "ok, xo muyi magana Abdul," Abdul ya mike ya bisa suka fita. Aneesah ta koma ta xauna a sanyaye kmr xata yi kuka, ita kam bata san me tayi masu ba duk basa amsa gaisuwarta, Abdul kadae ne ke amsawa. Maganar da Hydar yyi ma Abdul, shi Mujaheed yyi masa kan cewar xa a daga ca . Da yamma Hydar ya shigo gidan, Ammi ta ba shi abincin da ta girka ya kai asibiti, Hydar yace "Ammi da ma kin bar ba kanki wahala don ban tsamman suna iya cin abincin ba ma, wahalar da suka dauko ma kansu yafi karfin su ci abinci, ina ga da daddare ma xasu tafi india. " Ammi tace "wae kai meyasa kke hka Hydar, yau ko ba kanninka bane baxa ka ji tausayinsu ba bare kanninka uwa daya uba daya, haba Hydar" yace "a'a Ammi ni bance baxan kai masu ba ai xan kai," Ammi tace "to bana son kana irin wnn maganganun, Allah ne ya kaddara masu hkn," Aneesah dae na xaune tana kallonsu don ko da ya shigo ma yi yyi kmr bae ganta ba, Ammi tace "baki iya gaisuwa bne ke," ta dan wayance tace "A'a naga kuna magana ne," ta juya tana kallon Hydar din tace "ina yini ya Hydar," yace "lfya lau," Hydar ya karbi basket din da Ammi ta ajiye masa yace "to xan tafi Ammi, Allah ya saka da alkhairi," Ammi tace "da yaushe xasu tafi yau?" Hydar yyi shiru yana dan tunanin snn yace "ina ga xuwa bayan maghrib jirginsu xae tashi," Ammi tace "ummanka xata bi su ne," Hydar yace "A'a yayarta ce xata bi su da kanwar dad dina sae mum din Mujaheed," Ammi tace "to Allah ya sauwake masu ya basu lfya," Hydar yace "Ameen Ammi," Ammi ta juya tana kallon Aneesah tace "tunda yau xasu tafi da Aneesah kin shirya kuje ki gaishesu," gaban Aneesah yyi mugun faduwa ta kasa cewa komai sae kallon Amminta da take, shi kansa Hydar sae da ya dan ji wani iri, amma yyi saurin cewa "to ta shirya mu tafi mana," Ammi ta kalleta tace "ki shirya kuje Aneesah," Aneesah ta gyada mata kai, Hydar yace "ina jiranki a mota" snn ya fita, ta mike a sanyaye ta dauki Hijab dinta milk colour har kasa ta sa, snn ta dan gyara fuskarta, Ammi tace "amma fa kar ku dde Aneesah kinji, naga yana da kirki ne shi yasa nace kije," Aneesah tace "to Ammi" snn ta saka takalminta ta fita taje ta samesa a mota. . Aneesah ta kasa karasawa ciki har sae da daya daga cikin matan dake xaune a dakin tace "shigo mana 'yan mata," da kyar ta iya karasawa cikin ward din gabanta na faduwa har lkcn Hajiyar bata fasa kallonta ba, Hydar ya ja mata kujera gefen gadon ta xauna, muryarta na rawa tace "ina yini mummy, ya jiki," Hajiya ta sauke ajiyar xuciya a sanyaye tace "lfya lau Aneesah, ya gida," Hawaye ya cika idon Aneesah ta kasa cewa komai, Hajiyar ta mike xaune tana kallon Aneesah tace "kinga yanda rayuwa tayi da ni da 'ya yana ko Aneesah, kila ma hakkin ki ne ke bibiyarmu" Aneesah ta fashe da kuka tana girgixa kai ta kasa cewa komai, Hawaye ya cika idon hajiyar tace "ki yafe mana Aneesah, ki yafe mana, bamu maki adalci ba a rayuwa," kuka ssae Aneesah take ta fada kan Hajiyar tace "ni baku yi min komai ba mummy, nima ku yafe min," haka suka dinga kuka abun tausayi, Hydar ya mike ya fice daga dakin, da kyar matan dakin suka lallashi Aneesah tayi shiru, Hajiya tace taje ta duba su sumayya da Amina, ta mike a sanyaye, wata mata ta rakata, a hanya suka hadu da pretty, tayi mata wani kallon bnxa kmr bata san daga inda ta fito ba, Aneesah ta gaisheta a sanyaye, pretty ta wuce abinta tare da ce mata sannu, Matar da ke tare da Aneesah kanta bata ji ddin abinda pretty tayi mata ba, Aneesah dae ta dinga binta jiki ba kwari har suka isa ward din gabanta ya shiga faduwa don bata san me xata je ta tarar ba, a tsorace ta bi matar suka shiga dakin, ai kam tayi da ta sanin shiga don kuka ta dinga yi ssae don abin kam sae du'ai, matar tace "ba kuka xakiyi ba, addu'a xa kiyi masu Allah ya basu lfya," kai kawae ta gyada ma matar snn suka koma can dakin da Hajiyar take, xaune taga Mujaheed gefen Hajiyar yana hada mata tea, yyi mugun mamakin ganin Aneesah, ya kasa daina kallonta . Hello fans i think zan rage yawan rubutun ya koma ko 1 page ne saboda masu qorafin nasu baya budewa Luv U all! @ #dan_gogori_ 36&37 ~36~ Hydar ya shigo dakin ya karasa kusa da gado yana kallon Aneesah yace "tashi na mayar dake gida Magrib ya kusa," ya dauki ledojin da suka shigo da, da abincin da Ammi ta basa ya ajiye kan table yana kallon Mum dinsa yace "Mum din Aneesah tace a kawo maki," Hajiya tace "to ngdd ssae Allah ya biyata," ta juya tana kallon Aneesah tace "Allah ya baki miji na gari wanda xae rike ki amana Aneesah," Aneesah ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, Mujaheed ya mike xae fita Hajiya tace "har xaka koma ne Mujaheed," ba tare da ya kalleta ba yace "A'a ina xuwa," yana fadin hka ya fita, Hydar ya kalli Aneesah yace "mu tafi," Aneesah tayi ma Hajiyar da ta kasa daina kallonta sallama a sanyaye, suka fita daga dakin. Ko kallon Mujaheed Hydar bae yi ba yyi hanyar motarsa ya bude Aneesah na biye da shi a baya, tana kai wa inda Mujaheed yake ta kasa wucewa, ta tsaya tana kallonsa tace "ina yini ya Mujaheed," ba tare da ya kalleta ba yace "lfya," dae dae nn Hajiyarsa ta shigo asibitin, Hydar ya tsaya ta karaso suka gaisa tana kallon Aneesah tace "A'a surkarmu ne wnn mae kama da balarabiyan Aliyu," Hydar yyi murmushi bae ce komai ba, Aneesah ta gaisheta cike da jin kunya ba tare da ta dago kai ba, Hajiyar ta amsa da fara'arta tana tambayarta mutan gida, ta juya tana kallon Mujaheed tace "prince ashe dama kana nn," kai kawae ya gyada mata, ta shiga cikin asibitin, ba sae an gaya ma Aneesah ba ta gane Mum din Mujaheed ne sbda kamar da suke yi, Aneesah ta lura ita Hydar yake jira ta kalli Mujaheed a sanyaye tace "sae anjima yayana," ya dago yana kallonta ya kasa ce mata komai ta bude bayan mota ta shiga sae da Hydar yyi reverse snn a karo na farko yace ma Mujaheed "sae mun hadu anjima," ya ja motar suka fice daga asibitin, dae dae kofar gida Hydar ya ajiye Aneesah,

Chapter 19 of 23