Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kke," Mujaheed yyi fullstop dae dae kusa da dressin mirror, cikin daga murya sallau yace ka kwanta kasa kar na harbeka kar kuma ka dago kanka, Mujaheed ya sauke hannunsa a hankali yyi kmr xae kwanta kmr yanda sallau yace yana durkusawa ya tsuri kwalban humra dake gaban Madubi da sauri cikin second da bae wuce shidda ba ya jefi bala dashi, tas kke ji dae dae goshin bala kwalban ya tarwatse sae ga jini kmr famfo bala ya fasa ihu ya dafe kan yana neman faduwa tuni jini ya bata masa fuska, Mujaheed bae wani bata lkci ba ya isa kusa dashi da sauri ya murde hannunsa ya karbe bindigar ya nuna sallau da shi, sallau da ya shiga karkarwa a tsorace ya nuna ma Aneesah dake kwance a sume wajen fankon bindigarsa, Mujaheed yyi murmushin mugunta ya karaso kusa da shi sallau yyi karfin halin cewa kana matsowa ina harbeta wllh, Mujaheed ya buga masa bindingar da karfi a ka yace harbeta, sallau ya sake bindigar jikinsa ya dau bari, tun shigowar Mujaheed ta reaction din sallau ya gane ba komai cikin bindigar hannunsa, ya shake sallau da karfi ya buga sa da bango, bala na ganin haka ya fara kkrin guduwa daga dakin Mujaheed ya sa kafa ya kwashesa snn ya rufe kofar dakin, duk sae da ya sumar da su kmr yanda suka sumar da Aneesah don dukan fitar hankali yyi masa. Sae da ya gama dasu snn ya durkushe gaban Aneesah da sauri ya dago ta yana kiran sunanta, wayarsa ya dauka da sauri ya kira wani frnd dinsa likita yace yana bukatansa urgently, ko minti goma bae cika ba Doctor din ya shigo gidan don basu da wani nisa, Mujaheed yace ya hayo sama ya shigo dakin baby, likitan na bude dakin ya kasa shiga ya tsaya daga bakin kofa baki bude ya firffito da ido yana kare ma dakin kallo, Mujaheed dake rungume da Aneesah har lkcn yace "da'alla ka shigo ka tsaya daga bakin kofa," likitan yace "meye hka nake gani Mujaheed?" Mujaheed yyi tsaki a fusace yace "ni ka xo ka duba min yarinyar nn Aminu," da kyar doctorn ya shigo dakin ya tsallaka su bala ya karaso kusa da Mujahee d da sauri yace "wacece wnn kuma jaheed , me ya faru? Su waye kwance a nn" Mujaheed yace "ka duba min ita da'alla can," Aminu ya shiga dudduba Aneesah yana kallon Mujaheed yace "ae suma tayi," Mujaheed ya daga ta ya daura kan gado yana kallon Aminu yace "to ae sae ka farfado da ita ka tsaya kana kallona," ~25~ Likitan yace "to ina kayan aikin da xan duba ta da?" Mujaheed ya hararesa yace "dole sae da kayan aiki kawae ka duba min ita malam," Aminu ya girgixa kai yana kare ma su bala dake kwance shememe a tsakar dakin kallo ya karasa kusa da Aneesah ya kara dubata snn yace "ka kwantar da hankalinka yallabae tsorata ce kawae tayi ba wani abu ba, basu taba ta ba ina ga, wae yan fashi ne wa in nan koko?" mujaheed yace "oho," snn ya ciro wayarsa ya kira wani abokinsa dan sanda yyi masa bayanin abinda ya faru, dayake dan sandan babba ne yace to gasu nn xuwa, ya katse wayar yana kallon Aminu yace "don Allah kaje gida ka dauka su stesthoscope da allurori ka farfado min da yarinyar nn Aminu," Aminu yyi dariya yace "asibiti ma gaba daya xan dauko," yana fadin hka ya fice daga dakin yace "ina xuwa," mujaheed ya bi bayansa yace "ni ban ma je na duba mai gadin nn ba," suna fita suka tura dakin mai gadi suka tarar da shi a kwance an xuba masa cocaine, da sauri Mujaheed ya kullo dakin kar shima ya shaka yace "Allah sarki," ya bubbude windows din dakin don warin ya fita snn ya koma ciki bayan fitar Aminu da kamr Minti sha biyar 'yan sanda suka shigo gidan, suka shiga yi ma Mujaheed tambayoyi yace "ni fa ban san ko suwa ye ba" nn dae yyi masu bayanin abinda ya shigo dakin ya tarar yyi defendin din kansa kuma, suka kwashe su bala da bindigoginsu suka saka cikin motarsu mujaheed yace ma su gobe xae xo station din snn suka wuce, suna barin gidan Aminu ya dawo, yyi mata allurori, snn ya taimaki Mujaheed suka gyara dakin, bayan kmr minti ashirin ya duba ta yace "kaga ynxu bacci take, at anytime xata iya farkawa ga magunguna nn ka bata idan ta tashi ni xan koma gida," Mujaheed yace "haba dae it's too late ka bari gobe mana," Aminu yace "aa bbu koma ae da mota nake," Mujaheed ya rakosa waje ya nuna masa mai gadi, shima yy masa alluran snn yace "ka bar kofar dakin a bude gobe xae dawo hayyacinsa shi kuma," Mujaheed yace "ok," snn ya rakasa ya shiga mota ya dawo ciki ya kulle gidan yana mamakin me ya hana mai gadi kulle gidan da wuri, bae san tun karfe tara su bala ke labe a anguwar ba, suna ganin mai gadi ya fito suka shaka masa cocaine suka shiga da shi dakinsa suka kulle, snn suka fita daga gidan suka rufo gate, sae daxun nn suka shigo. Mujaheed na komawa dakin ya yaye bargon da ya lullube Aneesah da ya tsura mata ido yana kallonta daga ita sae inner wears, tausayinta ya cikasa, ya rumtse ido rufeta ya koma gefen gado ya xauna ya dafe kansa, yana xaune wajen har kusan karfe daya ya ga tana motsi, ya juya da sauri yana kallonta a hankali ta bude ido tana kare ma dakin kallo, lkci daya ta fasa ihu, ya mike da sauri ya karasa gabanta ya riketa yace "menene kanwata" ta fashe da kuka tana kkrin mikewa xaune ya rikota yace "haba Aneesah nine fa yayanki," ta kankamesa tana kuka tace "na shiga uku yayana," ya rufe bakinta da sauri yace "sun maki wani abu ne kanwata," kuka kawae take kmr ranta xae fita bata ce masa kmai ba, hankalin Mujaheed ya tashi yace "haba kanwata kiyi min magana mana, sun maki wani abu ne," ta girgixa masa kai da kyar tana kuka tace "wae kasheni suka xo yi," ya rungumota da sauri yace "bbu wanda xae kashe min ke kanwata sae lkcn ki yyi, bana son ki sake wnn kukan" gyada masa kai kawae take tana hawaye yace "xaki sha tea na baki maganinki" ta girgixa masa kai da sauri tace "aa," yace "to ina ke maki ciwo ynxu kanwata," bata ce masa komai ba sae ajiyar xuciyar da take, ya sake tambayarta ta girgixa masa kai tace "ba ko ina," ya dago kanta yana kallonta yace "ki kwanta kinji kanwata," ta kankamesa ta fashe da kuka tace "wllh ni baxan kwana cikin dakin nn ba tsoro nake ji don Allah kar ka tafi ka barni," yace "haba kanwata, add'ua fa xaki yi ki kwanta, baxa su sake dawowa ba, nasa an tafi da su station," cikin kuka tace "wllh tsoro nake ji ka kaini gun Ammina," Mujaheed ya rasa me xae ce mata yyi shiru yana kallonta, a hankali tace "yayana kar ka tafi ka barni don Allah ina rokanka," yace "to naji, kiyi kwanciyarki a kan gado ni sae na kwanta a kasa," ta rikesa tace "A'a wucewa xaka yi ka barni yayana," a hankali yace "shekaranki nawa Aneesah," ta na goge hawayen fuskarta tace "16" ya mike tsaye ta rikosa da sauri tana kuka tace "wayyo yayana wucewa xaka yi," ya girgixa mata kai yace kaya xan dauko maki ki sa, ita ma ta mike da sauri ta bisa ya juya yana kallonta bae ce komai ba ya fito mata da wani gown mara nauyi ya mika mata tana rike da shi duk don kar ya fita ya barta ta sa rigan, ya koma kan gadon tana biye da shi a baya ya kwantar da ita ta riko hannunsa tana sabon kuka har wani rawa jikinta yake tace "wucewa xaka yi ka barni yayana?" ya girgixa mata kai ya kwanta ta daya side din yace "kiyi baccinki bbu inda xa ni kinga na kwanta," ta gyada masa kai ta matso kusa da shi a hankali ta kwanta tayi lamo a bayansa tana sauke ajiyar xuciya, ya juyo yana kallonta da kyar yace "kinga Aneesah idan baxa ki kwanta a can ba ni xan bar maki dakinki," . Aneesah ta girgixa masa kai da sauri tace "A'a kar ka tafi ka barni yayana," a hankali yace "to koma can," ta koma inda ya nuna mata tana hawaye ta kwanta, ya juya mata baya, Mujaheed ya kasa bacci, kuma bae sake juyawa ba bare ya kalli inda take, a hankali yaji ta birginowa kusa da shi tayi lamo a bayansa, ya rumtse idonsa bae dae ce mata komai ba, har bayan kusan minti talatin snn ya juyo a hankali yana kallonta ta takure kanta amma bacci take, ya mike xaune a hankali kar ta tashi, ya kusan minti biyar a xaunen daga bisani ya mike ya shige bathroom dae dae lkcn da agogon dakin ke struck din 2 o clck ya dauro alwala ya fito, ya dauki darduma ya shimfida ya fara sallah, ya kai kusan minti sha biyar yana sllh Aneesah ta farka a tsorace ta mike xaune da sauri cikin kuka tace "na shiga uku yayana ina kke," tayi shiru hankalinta ya kwanta ganinsa yana sllh, ta bar kan gadon ta dawo gefensa da sauri ta xauna, can dae ganin ba gama sllhn xae yi ba, ta tashi ta shiga bathroom ta wage kofar yanda xata dinga ganinsa da kyau tayi alwala ta fito ta dauki hijab dinta ta fara binsa sllhn ita ma, daga karshe gajiya tayi da binsa ta sallame ta kwanta kan darduman a bayansa nn da nn bacci ya kuma dauketa, ba shi ya idar da sllhn ba sae kusan karfe hudu, ya mike ya dauko bargo ya lulluba mata snn ya koma kan darduman ya xauna yana addu'a, daren ranar dae Mujaheed bae yi bacci ba asuba tayi xae tafi masallaci ya tuna kar Aneesah ta tashi ta dinga rusa mashi ihu a gida hkn yasa yyi sllhn a dakin, snn ya tasheta ita ma tayi sllh, har gari ya waye bata bar gefen Mujaheed dake duba wani littafi ba, can ya juyo yana kallonta yace "kin tashi lfya kanwata?" ta dan yi murmushi ta sunkuyar da kanta a hankali tace "ina kwana yayana," yyi murmushi ya gyada mata kai ya mike yace "kije kiyi wanka, nima shi xanje nayi, da wuri xamu fita yau don sae mun fara xuwa station," ta marairaice fuska tace "aa ni yaya kar ka tafi ka barni," yace "to je kiyi wankan ki fito ina jiranki, baxan tafi ba," ta mike jikinta a sanyaye ta shiga bathroom ya bi ta da kallo yana murmushi, bayan kmr second talatin ta budo kofar ta ga ko yana nn har lkcn, ta rufe da sauri ganin yana nn, shi ko yyi murmushi sae da ya ji ta bude tap snn ya bude kofar dakin a hankali ya fice, ko da ta fito bata gansa ba ta fashe da kuka ta fice daga dakin da sauri tayi hanyar dakinsa, ta jirasa xaune a dakin har ya fito, yana ganin ta yace "xan fa bata maki rae kanwata baki shirya ba xaki fito," muryar ta na rawa tace "tsoro nake ji," ya harareta yace "tsoron idonki ba," ya rakata ya tsaya daga bakin kofa ta sa kayan snn ta fito da sauri, tana xaune ya shirya a dakin, snn suka sauko falo tare, coffee kawae ya sha ita ko ya tilasta ta ta ci tea da bread snn suka bar gidan bayan Mujaheed ya duba mai gadi, a hanya ya kalleta yace "Aneesah su waye mutanen jiya," nn da nn hawaye ya cika idonta tace "nima ban sani ba, amma jiya na gansu a supermarket, kuma naga kmr suna biyo mu har muka kai gida snn suka canxa hanya," yyi parkin da sauri yace "wat, shine baki gaya min ba Aneesah," ta fashe da kuka tace "ni ban san da gske binmu suke ba ashe," mujaheed yace "to me suka ce maki?" a hankali tace "sunce aiko su akayi su kasheni," Mujaheed ya gyada kai yace xasu ci ubansu, snn ya ja motar suka bar wajen, kin shiga station Aneesah tayi tace xata jirasa a waje, ya shiga shi daya, bae fito daga station din ba sae kusan karfe tara, yace "srry kanwata kin gaji da jira ko," ta girgixa masa ka kawae yyi reverse suka kama hanyar gidan yari, bae ce mata komai ba ita ma bata tambayesa ya akayi ba, ko da suka isa ba su sami ganin haydar a lkcn ba, aka ce masu sae eleven, suna xaune suna jiran eleven din yyi Aneesah tace "yayana tsoro nake ji gabana sae faduwa yake ban san meyasa ba," ba tare da ya kalleta ba yace "kiyi ta addu'a," a hankali tace "yaushe xaka nemo min Ammina yayana," ya juya yana kallonta yace "vry soon," tace "yayana amma ba gidan nn xamu kwana ba yau ko?" yyi murmushi yace "eh" ba tare da ya kalleta ba, karfe sha daya aka basu ixinin shiga gun Hydar, Mujaheed ya juya yana kallonta a sanyaye murya can kasa yace "tashi muje kanwata," Aneesah ta xaro ido tace "aa ni baxan shiga ba yayana tsoransa nake ji, ba kace yarinya ya sace ba," Mujaheed yyi murmushi ya kamo hannunta yace "c'mon sharri aka masa abinda ma xae ga yarinyar ynxu," bae jira me xata ce ba ya ja ta tana nonnokewa kmr xa tayi kuka suka shiga inda Hydar yake. . Haydar ya dago kai yana kallonsu, har lkcn Aneesah na labe bayan Mujaheed wae ita tsoro take ji, Hydar ya hade rae yana kallon Mujaheed ganin ba shi kadae bne don a xatonsa daya daga gantalallun 'yan matansa ya taho masa da, Mujaheed ya kyaleta ya karaso kusa da Haydar ya xauna yana kallonsa, kasa karasa wa Aneesah tayi ganin Hydar bayan Mujaheed ya bar ta gun a tsaye, ji tayi kafarta ya kasa daukar ta ta durkushe wajen jikinta na rawa, hkn ne dalilin da ya sa Hydar dago kansa yana kallonta don har lkcn bae kalle da warce Mujaheed ya shigo ba, ya mike tsaye a hankali yana kallon Aneesah da mugun mamaki, Aneesah ta fashe da kuka tana kallon Mujaheed da ya tsiri danna waya tace "wayyo Allahna ya Hydar me kke yi a nn," Hydar ya juya yana kallon Mujaheed da alamar tambaya, amma ya kasa cewa komai, ba tare da Mujaheed ya kallesa ba yace "ita ce Aneesar da kke gaya min ko," Hydar ya koma ya xauna da kyar yana ci gaba da kallon Aneesah da mamaki yace "ina ka samo ta Mujaheed," Mujaheed ya juya yana kallon Aneesah dake kuka ssae tana kallon Hydar, bae ce komai ba ya ci gaba da danna wayarsa, Hydar ya karasa kusa da Aneesah ya durkushe gabanta yana kallonta, ta dago kai ita ma tana kallonsa, a hankali yace "Aneesah," ta girgixa masa kai ta fashe da wani sabon kukan ta fada kansa, ya dagota ya girgixa mata kai yace "No Aneesah," muryarta na rawa tace "ya Hydar me kke yi a nn dama kai ne yayana ke fada min," ya tsura mata ido yace "waye yayanki," ta juya tana kallon Mujaheed da har lkcn idonsa na kan waya bae ko kalle inda suke ba, Hydar ma ya juya yana kallonsa, mujaheed dae bae ce masu kmai ba, Hydar ya dawo da dubansa ga Aneesar yace "ina ya kai ki Aneesah?" ta goge hawayen fuskarta tace "wa?" yace "baffanki" ta dan yi shiru tana ci gaba da goge hawayen da yaki tsaya mata tace "can wani gari ya kai ni," Hydar yace "gun wa?" ta fashe da kuka tace "ban san su ba, can wani kauye ya kai ni a kaduna," Hydar yyi shiru snn yace "Ammi fa?" cikin kuka tace "ya Hydar ban ga Ammina ba amma yayana yace xae samo min ita," Hydar yace "gun wa kike ynxu?" tace "gun yayana," yace "waye yayanki," ta juya tana kallon Mujaheed, wnn karon dae Hydar bae kallesa ba, Hydar bae sake ce mata komai ba ya kauda kansa, ganin yyi shiru ne ya sa tace "ya Hydar ka gaya min wa ya kawo ka nn, me kayi?" ba tare da ya kalleta ba yace "ca akayi na sace ki," ta fashe da kuka tace "wa yace hka ya Hydar?" Hydar yace "baffanki," kuka ta shiga yi ssae, ya dagota ya sa hannu yana share mata hawayenta yace "kar ki damu Aneesah, in'sha Allah komai ya xo karshe ki kwantar da hankalinki," ta gyada masa kai kawae, ta juya bata sake ganin Mujaheed ba, ta tsayar da kukanta ta mike tsaye da sauri tace "ya Hydar ina yayana?" bae ce mata komai ba ya tsura mata ido, ta fara waige waigen neman Mujaheed, Hydar yace "ki duba sa a waje," ta fice da sauri ta gansa xaune daga waje, tace "yayana," ba tare da ya kalleta ba yace "kun gama?" ta gyada masa kai, ya mike ya shiga inda Hydar yake yace "sae mun hadu a kotu ran monday," Hydar yyi shiru yana kallonsa ganin ya juya xae wuce ne yasa yace "so early?? Bbu bayanin komai jaheed?" Mujaheed ya juyo yana kallonsa yace "bayanin me?" Hydar yyi shiru yana kallonsa can kuma yace "shknn Allah ya kiyaye hanya," har mujaheed ya juya xae wuce sae kuma ya fasa ya juyo ya dawo ciki yana kallon Hydar yace "kar ka damu Aliyu gobe xan dawo a kwae lbri, ynxu sauri nake wllh" yana gama fadin hka yyi murmushi yyi pat din shoulder dinsa yace "c yah," snn ya juya ya fita Hydar ya bi sa da kallo, Mujaheed ya kalli Aneesah dake tsaye daga bakin kofa a hankali yace "ki je kuyi sallama," tace "to ka jirani" ya gyada mata kai ta karasa kusa da Hydar a sanyaye tace "ya Hydar mun tafi," yyi shiru yana kallonta snn yace "ina xaku ynxu?" ta sunkuyar da kai tace "ni da yayana xamu wuce gida," ya dauke kansa yace "ok," Aneesah ta juya hawaye cike a idonta ta fita ta samu Mujaheed tsaye a waje ya jingina da bango idonsa rufe yana jiranta, tace "yayana," ya bude idon yana kallonta bae ce komai ba yyi gaba tana biye da shi a baya har suka fita ya bude mata mota ta shiga snn ya xaga ya shiga driver sit ya ja motar suka bar wajen. Happy weekend to all my lovely fans @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 26&27 ~26~ Mujaheed na gama parkin Aneesah ta bude motar xata fita ya kirata a nutse, ta koma ta xauna tana kallonsa, yace "kinji ddin ganin Hydar yau ko?" ta sunkuyar da kai bata ce komai ba, ya kira sunanta ta dago a hankali tana kallonsa yace "magana nake maki" tace "yayana a ina ka san shi to" yace "ki amsa min tambayata," ta dan karyar da kai ta marairaice tace "ehh mana ssae ma," ya gyada kai yace "to yyi kyau," ya bude motar ya fito ya bar ta a ciki, ta bishi da kallo har ya shiga cikin gida snn ta fara kuka, tayi mai isarta ta fito ita ma ta shiga gidan a sanyaye, yana kwance falo ya lumshe idonsa, ta karaso falon kmr bata son taka tiles din dake shinfide a falon, ta isa gabansa ta sulale kasa tana kallonsa a hankali ta shiga kiransa "yayana," ya bude ido yana kallonta, ta sunkuyar da kai hawaye na xuba idonta, ya mike xaune yace "ya akayi," ta girgixa masa kai bata ce komai ba, yace "ko na sake maida ke gun Hydar din ne?" ta tsura masa ido tana kallonsa bata ce komai ba, ya mike tsaye yace "fine! Sae ki je ki harhada kayanki," yana kai wa nn ya juya ya bar wajen da sauri ya haura sama, ta fashe da wani sabon kukan ta kife kanta kan kujera. Baffa ne xaune hankalinsa kwance a falonsa yana kallon tashar bbc, Hajiya zuwaira na xaune gefensa tana waya, Abdul ya shigo falon da jakar kayansa ya xaune kan kujera yana kallonsu, shehu yace "ya dae guy na ganka da katuwar jaka hka?" ba tare da ya kalli mahaifin nasa ba yace "yau xan kama hanyar london ne dad," baffa ya dan sace kallon Hajiya da ta kauda kanta tana dan murmushi yace "a haba dae guy, har ka gama hutun," Abdul yace "ni nama rasa me ya xaunar da ni har ixuwa ynxu a Nigeria yau fa watana kusan biyar," Hajiya tace "ae shine son, kar ma kaje ka samu matsala gurin aiki," baffa yace "shknn son Allah ya kiyaye, kana bukatan wani abu ne?" Abdul ya mike ba tare da ya kallesa ba yace "ba komai," ya ja jakarsa ya fice daga falon, baffa yace "amma driver ne xae kai ka airport ko?" basu ji ya ce komai ba, Hajiya ta juya tana kallon baffa, tayi dariya tace "ya kaga aiki na Alhaji," cike da jin ddi yace "yana kyau matata, shi yasa nake bala'in san ki wllh," ta mike tana dariya tace "bari naje muyi sallama mai kyau da dana," karfe hudu Mujaheed ya sauko kasa tun bayan hawansa sama, har lkcin Aneesah na xaune inda ya barta, ya karaso cikin falon yana kallonta yace "kin gama hada kayan," ba ta kallesa ba kuma bata ce komai ba, ya xauna kan kujera yace "na fa gaya maki ki je ki hado kayanki na kai ki gun Hydar din ki xauna," ta tashi tsaye tana kallonsa tace "ae ba da kaya naxo gidan nn ba," tana fadin hka ta juya tayi hanyar fita daga falon, ya mike tsaye da sauri yace "ke ina xaki" bata ko juya ba bare ta tanka sa, ya fito shima da sauri yana kiranta, har ta kusa gate, mai gadi na sllh dakinsa don hka kawae ta bude gate din ta fice, tana fita ta saka gudu sanin Mujaheed xae biyota, ko da ya fito kofar gidan tayi nisa, yace "ya salam," ya koma ciki da sauri ya dauko makullin mota ya bude gate ya bita, ya rasa hanyar da ta bi don hanyoyin daban daban ne, Aneesah gudu kawae take tana kuka ba tare da ta san inda xata ba, ta isa titi xata tsallaka wani mai taxi ya tsaya yace "tafiya ne Hajiya," bata ce masa komai ba ta bude bayan taxi ta shige, ya ja taxin yana tambayarta ina xata, tace "can gaba," sae da yyi nisa don har sun fito babban titi snn tace "malam banda kudi fa?" ya juya yana kallonta snn yyi parkin yace "to fita," tace "to ngd," snn ta fito ya ja motarsa yyi gaba, ta fara kalle kalle ta rasa inda xata yi ta fashe da kuka, xata tsallaka titi kmr daga sama taji mota ya bugeta ta fasa ihu ta durkushe wajen don bata wani bugu ba amma ta tsorata, mutane suka taru gun suna mata masifa bata kallon inda xata wae, mai motar ma ya fito yana kallonta a fusace yace "ke wace irin mara hankali ce kina tafiya hankalinki na karkashin takalminki haka kurum ina xaman xamana ki ja min sittin," Aneesah ta dago da sauri jin muryar mae maganar, dae dae nn kuma Mujaheed ya shigo crowd din. . Abdul yyi tsit daga masifar da yake yi yana kallonta kmr mae son tuna Abu ya dafe kansa, can ya durkusa gabanta yana kallonta yace "sannu baki ji ciwo ba dae ko," ta mike da sauri tayi gefen Mujaheed da ya kasa ce mata komai sae kallonta da yake cikin bacin rae, ta kamo hannunsa a rude tana kuka tace "yayana mu tafi gida don Allah," ya fixge hannunsa yace "ki dae tafi inda xa ki" ta juya da sauri xata wuce ya fixgota a fusace yace "na ga alamar baki da hankali," Abdul yace "ka bi ta a hankali mana," Mujaheed bae ko kalli Abdul ba yyi hanyar motarsa da ita, ya bude bayan motar ya jefata ciki, snn ya xa ga ya shiga driver sit ya ja motar suka bar wajen, Abdul ya xaga ya shiga tasa motar ya bi su a baya, kuka kawae Aneesah take a bayan motar, duk a tsorace take ganin Abdul, Mujaheed bae ko kalleta ba bare yace mata komai, kamr ance ta juya taga Abdul biye da su a baya, ta fasa wani raxanannen ihu, Mujaheed ya taka burki da sauri ya juya yana kallonta da mamaki yace "ya salam wae kina da hankali kuwa Aneesah?" ta nuna masa baya a tsorace ya juya yana kallon motar Abdul da ya tsaya, mujaheed ya kalleta yace "meye wnn?" cikin kuka tace "bin mu yake," Mujaheed ya bude mota ya fito yana kallon motar Abdul, Abdul ya fito daga tasa motar Mujaheed ya karasa gunsa yace "malam kana da matsala da mu ne?" Abdul yace "A'a just want 2 make sure she's alryt don na bugeta ssae," Mujaheed yace "dnt bother xan kai ta asibit," Abdul yace "dama ka bari na dubata nima likita ne," xae fito da I.D card dinsa mujaheed yace "nace maka karka damu malam," Abdul ya daga kafada alamar ok, snn yace "kanwarka ce," ba tare da mujaheed ya kallesa ba ya juya xae koma motarsa yace "matata ce," Abdul yace "matarka? karya kke wnn bata yi kama da matar aure ba, ina tunanin ma kmr na taba saninta," Mujaheed ya dawo da sauri ya cakume Abdul yana huci yace "kai! Wllh xan iya kasheka a kan wnn yarinyar, ka kama hanyar ka kar kasa nayi maka dukan fitan hankali a nn," bae jira cewar Abdul din ba ya turasa da karfi yyi hanyar motarsa ya shiga yyi reverse ya fasa komawa gida duk da sun kusa gidan tunda a layinsu yake, bae damu da irin kukan da Aneesah take ba har sae da yyi nisa ssae snn yace "waye wnn mutumin Aneesah," cikin kuka tace "yayana ne," ya taka burki da sauri don bbu motoci a titin anguwar yana kallonta yace "yayanki kuma?" ta gyada masa kai tana ci gaba da kuka tace "dan baffana ne," Mujaheed yace "wat?" ya sanki ne?" ta gyada masa kai nn ma tace "shine wanda ke son aurena baffa ya dauke ni ya kai ni kauye," Mujaheed yace "innalllahi wa'inna ilaihi raji'un," ya ja motar suka bar wajen snn yace "to ya akayi bae gane ki ba?" ta goge fuskarta tace "nima ban sani ba," bae sake ce mata komai ba har suka isa wani gida, yyi horn mai gadi ya bude gate ya shiga yyi parkin ya fito ya bude mata mota tace "ina ne nn yayana?" yace "nn ma gidanmu ne," tace "me xamuyi a nn?" ya kauda kansa yace "ae ya riga da ya san anguwarmu hatsari ne babba idan muka ci gaba da xama a can, shi yasan me yasa yyi pretend kmr bae sanki ba, kuma nasan xae kai ma ubansa information," Aneesah ta gyada kai tana hawaye tace "haka ne," yyi hanyar shiga gidan tana biye da shi a baya. Abdul na shiga gida mahaifansa suka tsaya kallonsa da mamaki, na farko a tunaninsu kmr yanda yace masu xae je gun abokinsa yyi sallama da shi ya ajiye motarsa a can snn ya wuce tashar jirgin sama, na biyu kuma ya shigo masu a hargitse kmr mahaukaci, baffa ya mike da sauri yana kallonsa yace "ya akayi son,

Chapter 14 of 23