Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
mata da mamaki yana kallonta, gabanta ya shiga faduwa da sauri da sauri muryar ta na rawa tace "gashi," ya mika mata hannu har lkcn idonsa na cikin nata, ta sake masa juice din a tunaninta ya rike, kofin ya fada kansa juice din gaba daya suka xube jikinsa, duk wnn abinda suke yi kan idon Haiydar da ransa ya gama baci, Aneesah ta mike a tsorace ta dafe kirji tace "na shiga uku wllh ban sani ba," Hajiya ta mike a fusace tace "kan uban nn ikon Allah kadae ne xae sa baxan sumar dake yau ba," tana gama fadin hka ta yo kanta, Najeeb ya mike da sauri yace "ba laifinta bne mum, nine ban rike kofin ba ashe," cikin fushi hajiyar tace "to ita dabbar ina ce da baxa taji ko an rike kofi ko ba a rike ba, hka fa ranar tayi ma Aliyu, iskanci ne kawae da mugunta irin ta dan kauye, da ka bar ni naci ubanta kawae najeeb" najeeb yyi murmushi yana kallon Aneesar yace "je ki kawae," ta juya da sauri ta bar wajen tana hawaye, Aliyu ya mike ya bar falon bayan kmr minti biyar ya sauko ransa a hade yace "mu je na dauki abinda xan dauka, Najeeb ya tsaya kallonsa da mamaki snn yace "to ina abinda nace xan karba idan na xo," ya juya ya haye sama ya dauko masa, Hajiya tace "A'a har xaku tafi dama ba ddewa kaxo yi ba," Najeeb yace "wllh sauri muke mum, amma ran sunday xan dawo idan Allah ya yrda," Hajiya tace "to shkkn don Allah ka fa xo don ina da magana da kai," yace mata "to" snn yace yana xuwa ya dauko abu a mota, ya fita ya xaga yyi hanyar garden, tana xaune ta xabga tagumi, ya karaso gabanta ya durkushe, ta koma baya a tsorace jin ba kamshin turaren Haiydar ba knn, ya sakar mata murmsuhi yana kallon cikin idonta yace "wllh wllh kina da kyau, . Aneesah ta koma baya a tsorace ta fara kkrin mikewa xata bar wajen ya rikota da sauri ta fixge hannunta a tsorace tace "meye hka malam wnn wani irin iskanci ne," ya wara idonsa ya sake kamo ta da sauri yace "wats wrong bby yhur temperature is high," ta buge masa hannu tare da fashewa da kuka tace "wae meye hka a ina na sanka ni fa ba 'yar iska bace" yy dariya ya rungumota gaba daya yace " nima ba dan iskan bane ba ai, kuma sae kin gaya min inda ke maki ciwo ko kuma na duba ki ynxun nn a nn," Haiydar ya shigo garden din kmr wani xaki tana ganinsa ta fara kkrin kwace kanta amma ta kasa don kin sakinta yyi, har Haiydar ya karaso gurinsu Najeeb bae gansa ba ita ce dae ta gansa, Haiydar ya fixgota a fusace ya wurgar yana huci yace "a hkn kike yawan gaya min ke ba 'yar iska bace," ta fashe da kuka ta hde kanta da gwiwa, ya juya a fusace yana kallon Najeeb yace "ka fita gonata malam kar na baka mamaki, bnxa kawae dan iska," ya juya a fusace ya bar garden din, najeeb ya bi sa da kallo yana murmushi, ya karaso gabanta ya durkusa yace "am srry bby, xan basa magani ya kawo maki ltr bye," ya mike shima ya bar garden din, tana jin fitar motarsu a gidan ta mike da kyar tana goge hawayen da ya ki tsaya mata ta shiga gidan kafin hajiya ta fara kwala mata kira tana nemanta. Har Aneesah ta bar gidan ranar bata ga Haiydar ba, da kyar ta isa gida ta tarda jikin Ammi yyi sauki don har ta gyara gidan tayi masu girki, wanka da Alwala kadae ta iya yi ta kwanta don kasa sallahn tayi ammi tace ta sa kaya su tafi Asibiti amma tace aa don sanin kanta ne kudi kadan ya rage a hannunsu ynxu kafin karshen wata a biya su, Ammi ta fita siyo mata magani a chemist suka shigo tare da yusuf ya dawo daga makaranta, ya xube jikinta yace "Antyna baki da lfya har ynxu," ta gyada masa kai da kyar, yace "to Anty idan na girma xan xama Doctor don na dinga baki magani idan baki da lfya ke da Ammina" Aneesah ta mike da sauri tace "A'a lawyer xaka xama yusuf don ka dinga kare ryt din mutane," ya mike tsaye da sauri yace "A'a na manta Anty soja xan xama don na kama baffa na dauresa nae ta dukansa na sa shi frog jump idan ya sake yi ma Ammi da ke ihu, kuma xan xama mai kudi na siya maku gida na dinga baku abinci kullum" Aneesah ta dinga dariya ta rungumosa tace "yauwa yusuf dina shi yasa nake son ka, Allah ya bar mu tare," Ammi ta dinga murmushi tana kallonsu, nn da nn Aneesah ta nemi xaxxabinta ta rasa, hka suka dinga hira yusuf na basu dariya da shirmensa har dare ya raba snn suka kwanta. Washegari Aneesah ta tashi da karfinta taji bbu wani sauran xaxxabi a tattare da ita, ta kama hanyar gidan aikinta bayan ta ajiye yusuf a sch, don ca yyi ita xata kai sa ranar baxae bi su jamia ba, hkn yasa ta fara ajiyesa bakin gate tayi peck dinsa tayi masa bye bye snn ta tafi gidan aikinta, har kusan rana bata ga Haiydar ba, da yake duk 'yan gidan sun tafi gantali daga ita sae pretty a gida tana tae mata hira, karfe hudu saura tana wanke wanke kafin 'yan gidan su dawo pretty na sama taji wani mugun xaxxabi na neman rufeta, ta dinga ganin jiri ga ciwon kai da ya sa ta kasa bude idonta, ta gama wanke wanken da kyar ta shiga garden ta xauna ta jingina jikin bango tana mayar da numfashi, a hka Haiydar ya xo ya sameta a garden din ya durkusa gabanta ba tare da ya bari sun hada ido ba yace "har ynxu jikin ne kanwata," bata ce masa komai ba kanta a sunkuye, xae yi magana motarsu Hajiya suka shigo gidan, ya mike da sauri ya shiga kitchen sae gashi ya fito da ruwa a glass ya fito da ledar magani ya balla ya durkusa gabanta yace "gashi ki sha kanwata hope kinci abinci," ba tace masa komai ba kuma bata karbi maganin ba, ya dinga rokanta yana lallabata ta sha maganin amma taki ko da dagowa ta kallesa sae hawayen da take tayi, ya mike yyi tsaki ta dalilin kiransa da yaji Hajiyarsa nayi a falo, bae sake shigowa garden din ba har karfe biyar saura, ganin baxa ta iya daurewa bne kuma yasa ta mike da kyar tana ganin jiri ta shiga falon tace ma Hajiya tayi hkuri xata tafi gida bata da lafiya, Hajiyar ta tsaya kallonta don duk wanda yaga yana yinta yasan bata da lfya, ta tabe baki xata yi magana pretty tace "momy ki bar ta ta wuce tun tuni take ta ma mutane amai kar taje ta sume mana a gida," Hajiyar tayi tsaki tace "to tashi sae ki gyara min daki snn ki tafi makira kawae," Haiydar ya mike yyi waje, ita ko ta shiga ta gyara dakin da kyar snn ta fito tayi masu sae da safe ta fita, sumy ta bita a baya, Haiydar na tsaye bakin gate yana jiranta, tana fitowa kuwa xae yi magana sae ga sumy, ya juya da sauri yana danna wayarsa kmr mai shirin kira, ita ko ta kama hanyar gida tana karanto addu'a a xuciyarta na Allah ya kai ta lfya ganin condition dinta, Haiydar ya galla ma sumy harara a fusace yace "uban me kike nema a nn," cikin ladabi kar ya maketa tace "kawata nake jira bata san gidan ba shi yasa na fito," yyi tsaki ya juya bae. ~9~ Cikin ikon Allah Aneesah ta isa gida ranar gabanta na faduwa, amma me, sae taga mutane fal a kofar gidansu, nn da nn ta daina ganin jirin da take gani bugun xuciyarta ya tsananta kuma duk wani ciwo ta neme shi ta rasa sae bugun xuciyar, ta karaso da sauri a rude tana tambayar mutanen me ya faru, bbu wanda ya tanka mata, a gigice tace "nashiga uku ina Ammina," nn ma bbu wanda ya bata amsa sae ma hawaye da taga wasu nayi ba manyan ba ba yaran ba, haba bata san lkcn da ta fasa wani raxanannen ihu tayi cikin gidan da gudu tana kwala ma Amminta kira a rude, bata damu da kiran da makwabtansu dake tsakar gidan ke mata ba, wasu suka bi ta a baya da sauri, da gudu ta fada dakinsu tana ci gaba da kwala ma Amminta kira, xaune ta ganta makwabtansu da dama na xaune gefenta wasu na hawaye wasu sunyi jigum, nn da nn ganin Amminta yasa Hankalinta ya kwanta ta xube jikin Ammin tana maida numfashi har lkcn jikinta na rawa tana hawaye tace "Ammina me ya faru," Ammi bata tanka mata ba sae kkrin boye hawayen da take yi tana shafa kanta tace "har kin dawo," sae kuma Ammi ta fashe da kuka, Aneesah ta fara kalle kallen dakin a tsorace murya can ciki tace "ina yusuf Ammi," Ammi bata ce mata komai ba sae kukan da take yi, Aneesah ta shiga jijjiga Ammin tata a rude tace "Ammi don Allah ina yusuf ki gaya min," kmr ance ta juya taga abu a nannade cikin farin kyalle ta karasa da sauri hannunta na rawa ta bude, me xata gani, kaninta a kwance ba rai, bata san lkcn da ta fasa wani irin kara ba daga nn kuma bata sake sanin me ya faru ba, ta dae farka can cikin dare ta ganta kwance kan gadon amminta da makwabtansu har uku a dakin, Ammi ko na kan darduma a xaune. . Aneesah ta dauke idonta da sauri daga na sa ta sunkuyar da kai tana wasa da yatsunta, cikin tsawa hajiya tace "rainin wayon naki ne ya tashi shegiya xaki yi ma mutane shiru ki samu gaba kina kallo da daddaya da daddaya don uwarki" ta girgixa kai a raunane tana hawaye tace "kuyi hkuri hajiya wllh kanina ne ya rasu," cikin halin ko in kula Hajiya tace "to ni na kashe shi da xaki ki xuwa min aiki," Aneesah tayi shiru tana hawayen takaici, Hajiyar ta tabe baki tace "to ki sani baxan biya ki kudi cikin wnn watan ba sae karshen sabon watan da xamu shiga, bace min da gani kar na ji maki ciwo a nn mayya kawae ba kaninki ba uwarki da ubanki ma su mutu ina ruwan wani," Aneesah ta mike tsaye a sanyaye hawaye na bin kuncinta xata bar falon, cikin gadara meenah tace "kuma ga kayan wanki na can ya taru ba kyan gani, dasu xa ki fara," sumy tace "nima wllh gasu can duk ki hada yau ki wanke mana ni har da takalma na, kuma ki cire ma mutane wnn hijabin jikin naki duk ya janyo ma mutane duhu a falo," Aneesah dae na tsaye tana hawaye tana kallon sumyn cike da takaici kuma bata cire hijab din ba, sumy ta mike a fusace ta fixge hijab din daga jikinta ta wurgar tana huci tace "don uwarki ina maki magana xaki yi min shiru......" ba shiri sumy tayi shiru ta wara ido baki bude tana kallon gashin kan Aneesahn da ya xubo har kusan bayanta ta dalilin fixge mata hijabin da tayi hade da dankwalin kanta, meenah ta mike da sauri da mamaki tace "lala attachment ne a kanki kina matsayin yar aiki ni nasa ke ki sa," a fusace ta damko gashin Aneesar a xatonta kari tayi kmr yanda su ma ke yi, "wllh sae kin cire gashin nn ynxun nn a nn idan ba hka ba har gashin kanki sae na aske yau, dama munafuka shi yasa baki son cire hijab idan kika......" wani wawan marin da aka dauketa da ne ya sa ta kasa karasawa ta fasa ihu a gigice ta sake gashin Aneesar tana kallon wanda ya mareta yayanta ta gani tsaye kanta yana huci, ya fixgota ya buga ta da bango snn ya damki nata karin gashin dake kanta yana huci ya makureta cikin tsawa yace "uban me ta maki kike neman birkita mata kwakwalwa nake son ki gaya min kar na hallakaki a nn," Hajiya ta mike tana salati a rude tace "me xan gani hka Aliyu, meye hadinka da 'yar aikin nn xaka kashe kanwarka kanta," ya wurgar da meenar a fusace, ya dawo kan Aneesah da ke durkushe a wajen tana rusa kuka, ya durkusa gabanta ya dago kanta a hankali yana kallonta cike da tausayi yace "kiyi hakuri fateema," Hajiyar ta yo waje da ido baki bude tana kallonsu a tsorace ta daura hannu a ka tace "Aliyu," pretty ta mike a hankali ita ma tana hawaye ta bar falon ta haye sama, sumy ta mike tsaye ta fashe da wani wawan dariya tana kallon uwartata tace "heheho me na gaya maki mummy ba kin ki yarda dani ba, ni dama nasan da wani abun a tsakaninsu wllh, kin taba ganin yaya ya hana 'yar aiki yi mana aiki a gidan nn, ko kin taba ganin ya ci girkin 'yan aiki, ko 'yar aiki ta taba shiga dakinsa da sunan gyara masa ko yi masa guga, yaya bashi da aiki ynxu sae na xuwa garden, ni dama nasan da wani abu a kasa amma kika ki yarda dani da meenah, yau dae gashi kin gane ma idonki, shiyasa ranan nn ma na fita da sauri ganin ko bin ta xae yi a bakin gate nayi masa karya kwata nake jira, ba haushi na ya dinga ji ba har washegari na hana sa bin sahibarsa, a bnxa aka ce maki yake rashin lafiya kwanan nn," ta sake fashewa da dariya tana tafa hannu tace "kasala don burst" Aliyu ya yo kanta cikin fushi ya buga ta da bango da karfi, nn da nn se ga jini da gudu kmr famfo, daga ita har Hajiya suka rude Hajiya ta dinga rusa ihu tayi kitchen da gudu tana cewa "kan wnn matsiyaciyar xaka kashe min 'ya, wllh wllh wllh sae na hallaka ta yau," sanin halin uwartasa yasa ya ja Aneesar dake ta kuka da sauri suka bar falon, yyi garage ya bude motarsa don makulli na aljihunsa ya saka ta cikin motar ya xaga da sauri ya shiga ya tada motar yana horn ba kakkautawa, sae ga Hajiyar da gudu ta fito rike da tabarya da wuka, cikin tsawa ta dinga cewa maigadin kar ya bude gate din, Aliyu dake jiran ya karasa bude gate din kawae ya fice ya daka masa tsawa yace "xan take ka da motar nn baka bude min gate ba malam," maigadi duk ya rude ya rasa umarnin wanda xae bi ganin Aliyu ya yo kansa da motar yasa cikin ihu a gigice ya dinga cewa xae bude har ya wangala gate din jikinsa na rawa Aliyu ya fice da gudu ya bar. . Sun yi nisa sosai, kawae tafiya yake ba tare da ya san inda xa shi ba, Aneesah ko bbu abin da take sae aikin kuka, ganin kawae tafiya yake bai da alamar tsayawa yasa cikin muryar kuka tace "ni ka sauke ni a nn na wuce gidanmu," sae a snn yyi parkin gefen titi, ya juyo yana kallonta, ta rufe fuskarta tana ci gaba da kuka, ya kamo hannunta yace "ya isa hkan Aneesah kiyi hkuri, bana son kina kuka, nn" bata ce masa komai ba amma ta kasa daina hawaye, ya ciro handkerchief ya goge mata fuskarta yana kallon gashinta da duk da talaucinsu ba a haramta mashi gyara ba, don sae kyalli yake ga tsantsi snn baki wuluk, ta cire hannunsa daga kan gashin nata da ya dafa a hankali tace "hijabina," ya gyada mata kai kawae, snn ya ja motar suka bar wajen, sun danyi tafiya mai nisa snn taga yyi park yace "fito ki xabi wanda ki ke so," ta kasa cewa komai tana kallonsa, ya gyada mata kai ta fito a sanyaye daga motar suka fara tafiya a hankali taga duk ido ya dawo kansu barin ita, da sauri ta fixge hannunta tace "ni baxan iya ba, ban da dankwali," ya komar da ita motar snn shi yaje xabo mata Hijab din, bayan kmr minti goma ya dawo da katon ledar boutique a hannunsa ya shiga motar yana kallonta ta sunkuyar da kai, yyi murmushi ya bude mata ledar yace "gashi ki xabi wanda xaki sa," a hankali ta jawo wani milk colour taga yana da tsayi hkn yasa ta saka shi kawae, tana kallonsa ya gyada mata kai yyi murmushi snn ya tada motar suka bar wajen, sae da suka hau kan titi snn a hankali yace "ina ne gidanku?" ba tare da ta kallesa ba tace "ka ajiye ni a nn, sae na wuce," ya girgixa mata kai yace "baxa ki fita daga motar nn yau ba knn," ganin da gaske yake yasa ta gaya masa anguwarsu kawae in yaso sae ta karasa gida da kafa, "aneesah," ta ji ya kirata ta juya tana kallonsa, idonsa na gaban titi yace "me ya sami yusuf?" nn da nn taji hawaye ya ciko mata ta girgixa kai da kyar tace "mota ce ta bugesa suna dawowa daga sch," yace "mota kuma, to ina mai motar," ta goge hawayen idonta tace "bae tsaya ba, kuma withness sun ce da gangan ya buge sa bayan ya bugesa kuma ya taka sa ya gudu," yyi parkin da sauri yana kallonta, ta sunkuyar da kanta tana ci gaba da xubda hawaye, yace "baffanku ya samu lbri," tace "eh amma bae xo ba har ynxu wae matarsa tace ya tafi lagos, kawae baffa ibrahim ne ya xo shima shekaranjiya yace gangancinmu ne ya kashe yusuf," Aliyu ya gyada kai bae ce komai ba ya ja motar suka bar wajen, har suka isa anguwar bai sake ce mata komai ba, sae da yyi da gske da ita snn ta nuna masa gidansu don ca tayi ya ajiyeta xata karasa da kafa, tace masa tana xuwa snn ta shiga cikin gidan, Ammi na share tsakar gidan don ita har lkcn bata koma aiki ba sun bata hutun wata daya ne, ta mike tsaye tana kallon Aneesar da mamaki tace "me ya faru Aneesah," Aneesah ta kirkiro murmushi don bata son daga ma Amminta hankali, suka shiga dakin snn tace "Ammi tun safe baki gama aikin ba ashe," Ammi tace "ki gaya min Aneesah me ya faru ga idanuwanki duk sun kumbura kice min bkm," Aneesah ta sunkuyar da kai gudun kar ta fara hawaye kuma, a hankali cikin nutsuwa tayi ma Amminta bayanin abinda ya faru, ammi tayi shiru tana kallnta da tausayi snn tace "shi kuma me ya biyo ki yi Aneesah," ta goge hawayen idonta tace "nima ban sani ba," Yana waje Ammi, Ammi tace "to shknn kice ya shigo," ta mike a sanyaye ta fita gidan tayi hanyar motarsa, tace "Ammina tace ka shigo," yyi murmushi ya fito daga motar ya rufe snn ya bi bayanta suka shiga gidan a tare. ~10~ Aneesah ta shiga daki ta fito da tabarma ta shimfida masa ya xauna, Ammi ta fito ta dauko kujera ta xauna tanai masa sannu da xuwa murmushi bayyane a fuskarta, ya gaisheta a ladabe yana tambayar ya gidan, tace masa lfya lau ya nasu gida, yyi mata gaisuwan rasuwar yusuf, tayi masa gdya sosai daga bisanni ya sake bata hakura a kan abinda ya faru snn yyi mata sallama yace xae wuce, tayi masa gdya tace Allah ya saka da alkhairi snn ya fita daga gidan yana kallon Aneesah. Sae da ya fita snn a hankali tace ma Ammi bari ta rakasa Ammi tace mata to, ta mike ta bi bayansa, yana jingine jikin motar yana jiranta, ta karaso gefensa ta tsaya a sanyaye tace "nagode yaya Haiydar," yyi murmushinsa mai kyau yace "nima ngd fateema," ita ma murmushin tayi ta boye fuskarta, yace "Aneesah an rufe registration din waec din ne?" a hankali tace "nima ban sani ba," yace "ok find out frm yhur sch mates," tayi shiru bata ce komai ba, yace "Aneesah naxo gidanku ko ruwa baki bani ba, gashi dama yunwa nke ji, kin san bnyi break ba," ta xaro ido tace "lah ae ban san xaka sha ba, bari na debo maka," yyi dariya yace "wasa nake maki," ya bude motar ya fito da ledar Hijabs din ya mika mata tace "na me," yace "naki mana," ta marairaice tace "A'a ni dae wnn ya isheni wllh," ya harareta yace "ki karba wucewa xanyi," a hankali tasa hannu ta dan risina ta karba snn tayi masa gdya, yyi murmushi yace "welcm Aneesah, i wil be goin now," ta gyada masa kai ya bude motar ya shiga ta daga masa hannu snn ta juya ta shiga gida, shi ko yyi reverse ya bar anguwar, hanyar gidansa yyi, don yasan Hajiya na can kila ta tara masa mutane ana jirasa don ma ya kashe wayoyinsa. Aneesah na shiga ta nuna ma Amminta hijjaban, Ammi tace "shine xaki karbo Aneesah ni fa ba ruwana," Aneesah tace "wllh Ammi nace ya bar shi yaki," a hankali ta shiga fito da su tana dudduba, tana fito da na ukun knn bandir din dari biyar biyar ya fado, ta koma baya da sauri tana kallon Amminta, ammi tace "wnn kuma daga ina?" Aneesah tayi shiru tana kallon kudin snn ta dago tana kallon Amminta a hankali tace "shi ya saka Ammi," Ammi ta kasa cewa kmai sae kallon Aneesar da take yi, can dae ta mike ta shige daki kawae, Aneesah ta bi ta ta fashe da kuka tace "wllh Ammi ban san ya saka ba," Ammi ta girgixa kai tace "to ki ajiye masa kudinsa kar ki taba," Aneesah tace "to" snn ta ajiye hijabs din da kudin cikin jakar kayanta. Washegari da yamma ta je dibo ruwa a borehole tana dawo wa xata shiga gida taji an mata horn, ta juya da sauri tana kallon motar da mamaki, Haiydar ne, ya bude motar ya fito ya wara mata ido yace "me hannunki yake da xaki daura ruwa a kai Aneesah," tayi murmushi tana kallonsa bata ce komai ba ya karaso gabanta ya sauke mata bokitin ruwan ya ajiye kasa yana mata wani irin kallo, ta boye fuskarta da tafin hannunta tana 'yar dariya tace "xafi hannun xae min shi yasa na daura a kai," ya harareta yace "to karki sake," tace "uhum," snn ta dauki bokitin ruwan a hannu yace "bari na taya ki mana," ta ce "A'a ina xuwa," ta shiga gidan, bayan kmr minti biyar ta fito rike da leda tana kallonsa tace "jiya kayi mantuwa cikin ledar da ka ban," ya galla mata harara yace "Ammi na ba bake ba, ni ina ruwana dake," ta marairaice fuska tana kallonsa tace "dn Allah ka bari ka amshi kayanka ni dae," ya hade rai yace "ba fa na son hka Aneesah," tayi shiru tana kallon kasa, yace "ya maganar da na maki jiya na waec kin tambaya?" ta wara ido tace "na manta," yyi mata wani irin kallo yace "you re nt cerious," ya ciro wayarsa daya ya mika mata yace "idan kin tambaya kya kirani ki gaya min nmbrna na ciki xaki ga anyi save da barrister," ta xaro ido tace "A'a ni bana so wllh ka tafi da kayanka watarana idan kaxo xan gaya maka idan na tambaya," ya ajiye mata kan wani dutse yace "idan na tafi ki barshi a wajen, ki gaida min da Ammi," yana kai wa nn ya shige motarsa ya juya ya bar anguwar, tayi kmr xata yi kuka har ta daina ganin motar snn ta dauki wayar ta shiga gida dashi. Da daddare tana wanke wanke a tsakar gida Ammi na daki taji kamr motsin mutum a xaure, ta dan tsorata ta mike da sauri tana jiran taga wa xae shigo taga bbu kowa, a ranta tace to ko dae ya Haiydar ne, hkn yasa ta karasa da sauri don tunaninsa take lkcn, ta shiga xauren tana dan waige waige cikin duhu bata ga alamar kowa ba ta dan leka waje ta dae ga motar a parke amma ba na Haiydar bne, kuma ba a kusa da gidansu akayi parkin din ba, ta danyi tsaki ta juya xata koma cikin gidan taji ta ci karo da mutum ta tsorata sosae xata fasa ihu ya fixgota ya rufe mata baki a hankali yace "menayi maki xaki fasa min ihu," a tsorace ta koma baya tace "ya Abdul," ya wara mata ido cikin duhun yace "waww kin xama 'yan mata bbyn nn," ta turasa da karfi a fusace xata bar xauren ya fixgota yace "yaushe na fara wasa dake?". . Aneesah tace "to wani irin iskanci knn xaka rike ni hka ni ka sakeni don Allah ko nayi maka kama da yar iska," yyi yar dariya yana mata wani irin kallo yace "har ynxu wnn tsiwar taki na nn ko," tayi tsaki ta turasa da karfi xata shiga cikin gida ya fixgota ya daure fuska yace "ban baki ixinin wuce wa ba, ina uwar taki take," tayi masa wani mugun kallon tace "ban sani ba," yyi dariya ya fito da kwalin sigari da lighter daga aljihunsan ya ciro sigari daya ya mayar da kwalin, snn ya chinna mata wuta yana kallon Aneesar da ta yatsine fuska tana kallonsa a walakance cike da tsana, yyi murmushi yace "hope kin shirya aure ynxu 'yan mata," ta galla masa harara tace "da'alla malam ka bani waje na wuce wnn wani irin iskanci ne," ya matse ta da bango xae yi magana Ammi ta fito tsakar gidan tana kiran Aneesah, ya saketa yana mata wani irin kallo yana murmushi ya shafi gefen fuskarta yace "bye c yah," snn ya juya ya fice daga gidan, ashe motarsa ce a waje, ta ja dogon tsakin takaici tace "banxa kawae mara tarbiya" snn ta shiga gidan da sauri, Ammi ta hade rae tana kallonta tace "ina kika je Aneesah," ta dan marairaice fuska tace "wllh ina wanke wanke naji mutum ya shigo xaure shine naje dubawa naga Abdul ne," Ammi tace "waye Abdul?" Aneesah tayi shiru tana kallonta can tace "Abdurrahman" Ammi tace "sae kika tsaya yin uwar me a wajen," Aneesah ta tsorata ganin yanayin Ammin murya na rawa tace "aa ni ban tsaya yin komai ba Ammi," ammi ta juya ta shige daki ta bita jikinta a sanyaye, Abdul da ne gun baffanta shehu, sam bashi da mutunci bashi da tarbiya yanda ubansa yake hka yake, saukarsa knn Nigeria don a london yake rayuwarsa can yyi karatunsa na medicine, ynxu hka kwararren likita ne baya xuwa Nigeria sae bayan duk shekara biyu, kuma idan ya xo baya wuce wata biyu yake komawa, sae da suka shiga daki snn Aneesah taba Ammi hkuri, ammi tace "bakomai amma da xaki ji nawa Aneesah da kin shirya kin je gombe gun Adda na kwana biyu," Aneesah ta hade rae don bata son rabuwa da Amminta amma gudun kar ta bata mata rae yasa tace mata to kawae, snn ta canxa topic din. Washegari da yamma ta dawo daga debo ruwa kmr jiya ta ga Aliyu tsaye kusa da motarsa, tana ganinsa kunya ya kamata don a ka ta daura ruwan yau ma, ya karasa kusa da ita ganin taki karasowa yace "baki jin magana ko Aneesah," a hankali tace "kayi hkuri," ya sauke ruwan daga kanta yana harararta yace " kar ki sake daura ruwa a kan ki," ta gyada masa kai, yyi mata wani irin kallo yace "jiyan baki

Chapter 5 of 23