Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
motar tace "kai ina xaka kai mana 'yar uwarmu?" xulai ta fara kkrin bude motar a rude wae xata ciro Aneesah, ita kuma xano ta yi kauye da gudu neman taimako wae wani xae sace Aneesah a motarsa, shi ko ya fixge xulai daga jikin motarsa ya jefar snn ya bude motar ya shige, suka dinga ihu suna bubbuga motar da karfi, bae ko damu da hka ba ya tada motarsa ya ja ta ya bar wajen a fusace kuma da gudu don har yana neman buge karime. Shatu ta saki salati ta fito kofar gida a guje bayan lbrin abinda ya faru ya risketa tana cewa "wayyo shknn na shiga uku ni indo, ku ka ce me? Ya tafi da ita ina?" xulai dake ta rusa kuka tace "a motarsa ya tafi da ita," nn da nn lbri ya baxu kauyen wani mai mota ya kade Aneesah ya tafi da ita kuma a motarsa, mutane suka dinga fiffitowa da daddaya da daddaya aka taru kofar gidan shatu da ta xama kmr mahaukaciya wae an sace mata 'ya kuka har da majina faca faca, karime da mamarta ma na tsaye wajen ana ta jajanta abun sae kuka karime take yi, xano ta raka samarin kauyen xuwa gun da abun ya faru aka bi bayan motar amma aka rasa inda mota tayi, sae kusan maghrib kowa ya watse ya koma gidansa, aka bar shatu da 'ya yanta suna ta kuka, banda Xano da tace "to wae shatu sae kace uwarki ta bata ko 'yar da kika haifa a cikinki, tunda ba a ganta ba ba shiknn ba" tayi tsaki ta jawo kayan kwalliyanta xata yi shirin dandali, shatu ta sharbe majina tace "don ubanki da kin san abunda muka rasa ynxu da baxa ki ce komai ba," Malam mati ya shigo gidan da buhu a hannunsa, rabon sa da gidan yau kwana biyar knn don bae cika xama kauyen ba, yana shiga Bukkar shatu yace "ke shatu me nake ji a gari wae yarinyar nn mae mota ya gudu da ita, ina ya kai ta, kin manta jan kunnen da Alhaji ya mana, masifa kike son ja mana" shatu tace "to ba aikensu nayi ba malam,"yace "to shi mai motan daga ina yake kuma ina xa sa?" xulai tace"bakaken kaya ya saka gaba daya har takalmi da tabarau, kuma mu bamu san inda xa shi ba" Xano tace "kila ma dan yankan kai ne," shatu tace " lah! kuma fa wllh hka ne ya motar tasa yake?" xulai tace "katuwa ce motar ita ma bakakirin kmr kayan jikinsa," malam yace "shknn ae barka ma da ya tsaya a kanta," xano tace "shi dae na gani malam amma tun tuni shatu ta bi ta cika ma mutane kunneda kuka da sharban majina, sae kace uwarta aka sace," shatu ta sauke ajiyar xuciya tace "to idan shehu ya xo kauyen nn me xamu ce masa malam," mati yyi mata kalln bnxa yace "ba sae mu ce mun aurar da ita, a can wani kauye ba, kuma ba na ce maki ko sati biyu ba ayi ba da ya kira ni ta wayar Buba ba, yace idan ta addabemu mu kasheta kawai mu huta da jaraba, da na kawo maki xancen ba ca kika yi aa ba kina da babban shiri a kanta," shatu tace "hka ne malam to tanko fa, ynxu shknn munyi hasara knn?" yace "to ya xa ayi, ni dae daga yau bna sn na sake jin batun yarinyar nn a gidan nn, tunda ta bata ta bata, idan shehu ya xo iya ka nace masa ma ankasheta kawae," shatu ta mike tsaye tana gyara tsumman xaninta tace "to shknn, amma ni dae ba hka na so ba wllh, ga shi ynxu shknn mun rasa tanko, tunda dae bae ce yana son su xulai ba," A hankali Aneesah ta bude idonta ta tsura ma agogon dake manne a bangon dakin da take, karfe sha daya ta gani, ta shiga bin dakin da kallo kmr mai son tunano abu bbu tantama ta gane asibiti take, ta mike xaune a hankali tana kallon hannunta dake manne da alluran drip, taji an bude kofa, ta daga kanta da sauri tana kallon mai shigowa, ya tsakar mata murmushinsa mai kyau ya karaso gefenta ya xauna yace "bby kin tashi," kallonsa kawae take yi da mamaki, ya daura hannu kan goshinta ta cire hannun a hankali tace "ka mayar da ni gidanmu," ya harareta yace "kina under treatment xan mayar dake gidan naku?" tayi kmr xata yi kuka tace "xa ayi ta nemana fa don Allah ka mai da ni gida, ina mudatheer?" yace "oho! kuma naki mayar dake gidan karfe sha dayan daren xan mai dake gida," tayi shiru tana kallon agogo, yace "ynxu dae me xaki ci," ta daure fuska tace "ba komai," yace "gud, bari na kira maki Dr," yana fadin hka ya fice daga ward din ta bisa da kallo.. ~20~ A tare Mujaheed ya shigo dakin da likita, likitan ya karaso kusa da Aneesah yace "yan mata hope bbu inda yake maki ciwo ko?" ta gyada masa kai kawae, mujaheed ya harareta yace "ke dae ki fadi gskya," ita ma ta galla masa hararan bata ce komai ba, likitan yyi dariya yace "to a dae tabbatar ta ci abinci, anjima nurse xata xo bata allura," yyi masu sallama ya fita, Mujaheed ya juya yana kalln Aneesah yace "bbyna me xaki ci?" da mamaki tace "waye kuma bbynka?" ya kashe mata ido yace "ke mana," sae abun ma ya kusa bata dariya amma bata ce kmai ba, ya hada mata tea ya xauna kusa da ita yace "bude bakin na ba ki, bbu xafi," ta hararesa ta dan matsa tace "wae meye hka ni ka mai da ni gidanmu," yace "to tashi ki tafi," ta fara kkrin cire alluran hannunta ya rike ta da sauri yace"ke kina da hankali kuwa?" ya kwantar da ita yana kallnta yace"kwanta ki huta dear, kiyi hkuri gobe xa a sallame mu sae na mai da ke gida," hkn da ta ji ne yasa hankalinta ya kwanta tayi shiru, ya ajiye mata tea a kan table din dake kusa da gadon da take yace "to kiyi hkuri ki tashi ki sha tea kanwata," yana gama fadin hka ya kma kujera ya xauna yana danna wayarsa, ta mike xaune a hankali ta dauki tean ta fara sha har ta manta rabon da ta sha tea, ta sha rabita ajiye ta koma ta kwanta daga nn bacci ya dauketa, Nurse ta shigo tayi mata alluranta ta fita. Can kusan karfe daya Aneesah ta farka, Mujaheed na xaune har lkcn amma wnn karan waya yake, ya juya yana kallnta yace "xaki yi fitsari ne kanwata?" ta hade rae tace"nace maka?" ya taso ya xauna gefenta yace "Allah ya baki hkuri," ita dae bata ce masa kmai ba, ya tsura mata ido, tace "lafiya?" ya kashe mata ido yace "Allah kina da kyau," takaici ya sa ta kasa ce masa kmai wnn dae da ganinsa dan iska ne, ta fadi a xuciyarta, yace "wont yhu thank me," bata ko kallesa ba bare ta tanka masa yace "kin san me, Allah baki gaya min ke wacece ba baxan maida ke kauye ba, don Mudatheer yace kin ki gaya masa hadinki da mutanen da kike tare da a kauyen," Aneesah ta xaro ido tace "ina ruwanka da ko ni wacece ni dae ka maidani gidanmu malam," yace"tab ashe dae baxa ki koma gidan naku ba, don gudu ma xanyi dakedon ki sani," ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace "don Allah kayi hkuri," ya daure fuska yace "tohm nayi," oya tel me about yhur sef kuma bn da karya, don Mudatheer ya gaya min halin da kike cikia village din nn," tace "to me hkn xae kara ka da," yyi dariya yace"abubuwa da yawa kuwa, haba kanwata ni fa yayanki ne," Aneesah ta tabe baki tace "ni dae bacci nke ji ma," yyi murmushi yace "to kwanta," tayi kwanciyarta ta juya masa baya. Washegari da safe, Mujaheed ya siyo mata breakfst ta ci kadan, ya ci sauran, ita dae duk hankalinta yyi kauye kar ma ta koma shatu tayi mata duka shi yasa take Allah Allah ya maida ta da wuri, karfe tara ya xauna gabanta yace "oya ina jinki kanwata gari ya waye," ta fixge hannunta tace "kai malam ni ka rabu dani," yace "tab, wllh baki gaya min ko ke wacece ba baxan mai da ke gidan naku ba," tayi shiru tana kallnsa jikinta a sanyaye, da ta dau ma kanta alkawarin karime ce mutum ta karshe da xata san ko ita wacece, ga shi Mujaheed ya takurata sae ya sani, alhalin ko mudassir da suka shaku da ma bata gaya masa ba, hawaye ya cika idonta tuno rayuwarta da tayi, Mujaheed yyi murmushi, don yasan akwae abu a kasa dama, yace "ina jinki" xata yi magana wayarsa tayi ring ya daga, ta tsura ma kyakkyawan fuskarsa ido tana kallon lebbansa dake kyalli, bayan sun gaisa taji yace "in'sha Allah Mum yau xan shigo Abujan... No ki kyaleni da dan iska mara hankali, ya ci ubansada son yarinyar, yarinyar bnxa, wae ma shi uban yarinyar wanene a Abuja?" Aneesah dae kallon Mujaheed kawae take yanda yake yi sae abun ma ya bata dariya, taga yyi dariya yace "ki kwantar da hankalinki mum duk xasu cicci ubansu ina nn shigowa," yana kai wa nn ya kashe wayar yace "aikin bnxa kawae, ya ci uwarsa daga shi har shegiyar yarinyar, yarinyar bnxa" Aneesah tayi murmushi tace "xagi dae ba kyau," yace "ohh nayi xagi koh? Ni ban ma sani ba, wllh Aminina ne ke cikin matsala a Abuja, tare muka taso muka yi karatu da shi a holland, ynxu hka yana prison ana xarginsa da sace wata bnxa wae, shi da yake da big big babes a holland, ni fa shiyasa bbu ruwana da matan abujan nn dan 'yan iska ne, ynxu ma mum dinsa ce ta kirani, Allah kadae yasan idan ba plan bne wnn aka masa," Aneesah tace "Allah sarki, amma kar kayi saurin goya bayansa kila da gsken shi ya dauketa" Mujaheed yace "koma shi ya dauketa yyi min dae dae kuma xanje na karesa a kotu, don uwarta ba kwadayin abun duniya ya kaita soyayya da shi ba,kinsan ko waye shi kuwa," yyi kwafa yace "ki bari kawae ke dae," bck 2 bzz inajinki" ta dan yi shiru snn a hankali tace "Ni marainiya ce, baffa na neya kawo ni nn ya ajiye don kada dansa ya aureni, bn san kowa a kauyen ba, ya raba ni mamata ya kawo ni gun mugayen mutanen nn da ban sani ba ya tafi ya bar ni" tana kai wa nn ta fashe masa da kuka..Mujaheed ya gyara xama yana kallonta yace "inajinki" ta dago kai tana kallonsa hawaye kwancefuskarta tace "shknn," yace "karya kike," tagirgixa kai tana ci gaba da xubda hawaye tace"Allah gskyata knn nake gaya maka, baffa na neya kawo ni kauyen nn," Mujaheed yace "waye dannasa da baya son ya aure ki?" ta dan yi shiru snntace "su suna da kudi mu kuma talakawa ne shiyasa baya san dan sa ya aureni," Mujaheed yace"gud, to me ya hana mahaifiyar ki biyo ki nn?" Asanyaye Aneesah tace "bata san inda ya kai ni baai," Mujaheed yace "ku nawa ne a gurinta?"Aneesah tace "ni kadae ce, kanina ya rasukwanaki, dama mu biyu ne," Mujaheed ya girgixakai yace "Allah sarki, Allah yasa ya huta,"Aneesah tace "Ameen," "to shi baffan naki ya kuke da shi?" ya tambayeta yana kallon idonta,Aneesah ta sunkuyar da kai tace "yayan Abbanane," mujaheed ya gyada kai yace "yaushemahaifin naki ya rasu, kuma meye aikinsa kafinya rasu" Aneesah ta galla masa harara tayi tsakitace "ni don Allah ka kyaleni hka ka mayar da nigida, komai ne xan gaya maka, kuma mai hakanxae kara ka da" Mujaheed yace "tab, ba gida kikeson koma wa ba knn yarinya," Aneesah ta fasheda kuka tana kallonsa tace "don Allah kayi hkuri,nasan ana ta nemana a gida ynxu " ya dankwantar da murya yace "kiyi hkuri, kina ban amsata xan mayar da ke gida," Aneesah ta gogehawayen fuskarta snn ta gaya masa lkcn daabbanta ya rasu da aikin da yake yi kafin ya rasu,Mujaheed yyi shiru yana kallonta snn yace "to baebar maku komai bne, ko ko sun kare ne," Aneesahta gyada masa kai tace "ehh," yace "ok ynxu bakison xuwa gun ummarki knn, kin fi son xama damutanen nn su cuceki su yi maki auren dole?"Aneesah tayi shiru tana hawaye, yace "talk 2 memana," cikin kuka tace "ina son xuwa gunAmmina," Mujaheed yace "to kin amince na kai kigun Ammin ta ki ynxu?" Aneesah ta tsura masaido har lkcn tana kuka, Mujaheed ya kamohannayenta yace "dnt wrry kanwata, xan kai kigun Ammin ki idan kika yarda da ni, baxan bari kisake komawa kauyen can ba, am takin yhu homeAneesah trust me, nima ina da kanni kaman ki ,"Aneesah ta fixge hannunta tana kuka ssai tace"su mama xasu yi ta nemana kuma," a fusaceMujaheed yace "ita kuma mahaifiyarki batanemanki aka ce maki ko, sakayyar da xaki yimata knn, kinsan halin da take ciki ynxu na rashinki, ke daya fa kika rage mata, gujeta kike son yiko ko uban me ya hada ki da 'yan kauyen nnmarasu imani, consider yhur dear mum Aneesah,kar ki yi mata hka baki san halin da take ciki baynxu," kuka ssae Aneesah take ta kasa cewakomai, ya tsura mata ido bae hanata kukan basae da ta dan yi shiru snn yace "kin amince ynxuxaki gun Amminki?" a hankali ta gyada masa kaihawaye na xuba a idonta, yace "Gud Aneesah, inaxuwa" yana fadin hka ya mike ya fita daga dakinxuwa office din likita, Aneesah ta fashe da kukatace "ni baxan iya bin ka ba nasan su mama nacan suna nemana," tana fadin hka ta mike tsayeta gyara daurin dankwalinta ko takalmi bbu akafarta tayi gun kofa ta bude a hankali ta fita snnta fara neman hanyar da xata bi ta fita dagaasibitin, duk a rikice take duk inda ta bi ward ne,har daga karshe ta bi wata mata dake goye dayaronta suka iso har bakin kofar fita harabarasibiti, da sauri ta isa gate xata fita ta ci karo danurse din da tayi mata allura jiya da daddare,nurse din tace "ke ina xaki, an sallameku ne,"Aneesah ta fashe da kuka a rude tace "ehh,"nurse din ta riko hannunta tace "ban yarda ba,ina mutumin da ya kawo ki," dae dae nnMujaheed da likita da nurses har biyu suka fitoharaban asibitin, Mujaheed ya jingina jikin bishiyayana kallonta, kuka kawae take ta kasa daga kaita kallesa, ya karaso gabanta ya kama hannuntayyi ma nurses din da Dr. gdya snn yyi hanyarmotarsa dake haraban asibitin ya bude baya yasa ta shiga, snn ya xaga ya shiga ya tuka motarsuka fice daga asibiti.Sae da suka kai dae dae titin da xae yi lead dinka xuwa kauyen snn Mujaheed ya juyo yana kallon Aneesah da har lkcn ke kuka yace "aexaki gane gidan naku daga nn ko?" Aneesah ta kasa cewa komai sae kukan da take, yace "ohk, to sauka ki tafi, xan juya daga nn ne," cikin kuka Aneesah tace "to Ammina fa?" ya daga kafada yace"oho" ta hade kanta da gwiwa tana kuka, bae sake ce mata komai ba illa wayarsa da yake ta dannawa, ganin har kusan minti sha biyar bata ce komai ba kuma bata bude motar ta fita ba, yasa ya tada motar yyi driving dinta suka bar wajen, ta dago kai da sauri tana kallonsa tace "ka tsaya na sauka," yyi kmr bae ji taba, ya dingasharara gudu da motarsa, kuka ta dinga yi da ihu tana bubbuga motar wae ya bude mata ta sauka, tafiyarsa kawae yake bae tanka ta ba, har sae da suka shigo kaduna, snn ya juya yana kallonta yace "idan na kai ki gun Ammin ta ki, ki gudo ki dawo nn," bata ce masa komai ba sae dae a hankali take kukan ynxu tana kallonsa, daga karshe bacci ya dauketa ma. Ko da ta farka sun kusa shiga Abuja, yana kallonta ta madubi yace "me xaki ci kanwata nasan kina jin yunwa?" ta girgixa masa kai tace "ba komai," sae ynxu taji tana mugun son ganin Amminta, kewar ta ya isheta, amma a kauyeda ta fara tunanin amminta ciwon kai xae sa ta daina, ynxu Allah Allah kawae take ta ganta a gida kusa da Amminta, har haushin kanta ta dinga ji kan abun da tayi daxu. Karfe uku saura suka shigoAbuja, sae a lkcn tayi masa magana ganin hanyar da ya dauka tace"ba fa nn bane hanyar gidanmu yaya," ya ce "kin san me kanwata, kibari da daddare na kai ki, bna son kowa yasan kina Abuja ynxu," ta marairaice kmr xata yi kuka tace "dn Allah nayi missin din Ammita ka kaini gida kawae na ganta bbu wanda xae san na dawo," ya girgixa kai yace "No sae anjima xan kai ki kanwata," har tayi shiru sae kuma tace "to ynxu ina xaka kai ni?" a tsorace tayi tambayar, yace "gida xa mu," cikin tashin hankali tace "gida kuma, gidan wa?" suna shiga traffic ya juyo yana kallonta yace "gidanmu," ta fashe dakuka tace "A'a ni ba ruwana wllh, ka kai ni gun Ammina kawae," yace "haba kanwata baki yrda da ni bne, wllh xan kai ki gida amma da daddare sbda tsaro," a hka ya dinga kwantar mata da hankali yana lallabata har ta hkura, basu suka isa gidansu Mujaheed ba sae kusan hudu sbda traffic, Aneesah ta dinga bin anguwan da kallo, a xuciyarta tace kudi na inda yake, yyi horn a wani kantamemen gida mai kyan gske, mai gadi ya bude gate da sauri har yana neman faduwa, ya ja motar ya shiga haraban gidan dake kewaye da shuke shuke masu kyau, bayan mai gadi ya gaishesa dayi masa sannu da xuwa, a garage yyi parkin, snn ya juyo yana kallonta xae yi magana ta riga sa tace "to yayana su mommy baxa su yi magana ba," ya kwantar da murya yace "kin san me Aneesah?"ta girgixa masa kai tace "A'a," yace "gidanmu ne nn, amma su mommy suna Malaysia," bata bari ya karasa ba ta katse sa da sauri "to waye a gidan ynxu," yace "ba kowa," ta fashe da kuka tace"wllh ba ruwana shine xaka kawo ni gidan da ba kowa, ni ka kai ni gun Ammina kawae," ya harareta a fusace yace "baki yarda dani ba knn? Idan kina tunanin xan cuceki ne sae ki xauna da matar mai gadin don yana da mata, har lkcn da xan kai ki gidan," yana fadin hka ya bude mota ya fito yyi hanyar shiga gidan, ita ma ta fito jikinta a sanyaye tana kare ma gidan kallo, juyawa yyi ya ga tana biye da shi a baya, ya jirata har ta iso gunsa snn ya ci gaba da tafiya, ya ciro makulli a aljihunsa ya bude kofar shiga gidan ya shiga da sallama ita ma tayi sallamar ta shiga katon falon dake cike da kayan alatu na more rayuwa, ta tsaya a bakin kofa tana bin falon da kallo, shi ko har lkcn yana tsaye bayanta yana jira ta karasa ciki ya kullo kofar, ta juya da sauri tana kallonsa a dan tsorace tace "kulle kofar xaka yi?" ya ma rasa me xae ce mata don haushi, kawae ya hangame kofar gaba daya yyi gaba abinsa ya haura sama, ta karaso cikin falon a hankali ta dan xauna bakin kujera, ta kai minti ashirin xaune a falon bata ga Mujaheed ba har ta fara bacci ya dan bugi kujeran da take kai, ta mike tsaye a tsorace tana kallonsa, jallabiya milk colour ce jikinsa, da ganinsa kasan wanka yyi, kamshin turarensa ya baibaye ko ina ta dauke idonta daga kallon da take ma kyakkyawan fuskarsa, yace "xo ki ga," a dan tsorace ta bisa sama gabanta na faduwa, taga ya bude wani daki ya shiga, ta ki karasawa ta tsaya bakin kofar bae damu da hkn ba yace ni xan tafi masallaci, ki tabbatar kin yi wanka snn kiyi sallah bathrom na cikin dakin, yana kai wa nn ya fito ta ja gefe da sauri ya tabe baki yyi gaba, sae da taji tashin motarsa snn ta shiga dakin, tana bin ko ina da kallo daga gani dakin kanwarsa ce, ta kalli kayan da ya ajiye mata kan gado, snn ta bude kofar bathroom din ta shiga tana karanto adduar shiga bayi.. @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 . Na KHALEESAT HAIDAR. 21&22 ~21~ . .Aneesah na fitowa daga wanka ta sa kayan da Mujaheed ya fito mata da, ta dauki hijab din dake kan gadon ta saka, snn tayi salla kan darduman da ya shimfida mata a dakin, tana idar wa tayi jigumtana kare ma hadadden dakin kallo, ynxu kawae so take ta ganta kusa da Amminta, Allah Allah take karfe shidda yyi Mujaheed ya kaita gida, tana cikin tunane tunanen nn taji yyi sallama, ta gyara Hijab din jikinta da sauri tana kallon kofar dakin, ganin bae shigo ba har lkcn yasa ta amsa sallamarsa, sae a snn ya turo kofar dakin a hankali ya shigo, ya karaso gabanta ya durkusa, ta dan koma baya da sauri, ya ajiye ledan Hannunsa yace "ga abinci nn ki ci," yana gama fadin hka ya mike ya bar dakin, sae da ya kullo kofar snn ta bude ledan, abincin eatry ne da kaxa sae lemun kwali, ta danci abincin kadan ta mike ta dauko glass cup ta debi lemun ta sha snn ta tura ledan abincin. Karfe shidda nayi Aneesah ta mike da sauri ta harhada kayan da ta cire ta dauka ta bude kofar dakin a hankali ta fara saukowa daga stairs din har ta iso falon, yana xaune sanye da 3qtre da farar singlet yana danna laptop, ta juya dasauri kmr warce xata koma sama, ya mike tsaye yace "ya dae kanwata," ba tare da ta juyo ba tace "kace da Maghrib xaka kai ni gidanmu ai," yyi murmushi yace "hka ake Maghrib kanwata?" ta fashe da kuka tace "wllh gidanmu nake so na wuce yayana," bae ce mata komai ba sae kallonta da yake, ganin shirun yyi yawa ne yasa ta juyo a hankali tana kallonsa, suna hada ido ta juya da sauri tana kuka a hankali, yyi murmushi yace "to xo ki xauna na sa kaya sae mu wuce," ta juyo ba tare da ta bari sun hada ido ba ta rabe ta nemigu ta xauna a takure kan kujeran falon, shi ko ya haura sama, ko minti goma ba a yi ba ya fito sanye da kananan kaya hannunsa rikeda makullin motarsa yace "to muje kanwata," ta mike da sauri ta bi bayansa rike da kayanta a hannu, ya juya yana kallonta yace "a hannu xaki rike kayan?" ta gyada masa kai yyi murmushi suka isa garage ya bude mata mota ta shiga shima ya shiga mai gadi ya bude gate ya ja motar suka fita daga gidan, Hka ta dinga yi masa kwatancan anguwarsu har suka iso layinsu, Mujaheed yace "ina da wani aboki a layin nn da, amma ya tashi ynxu" Aneesah da farin cikiya isheta ga ta ga unguwarsu tace "haba dae da gske?" yace "eh wllh na taba xuwa nn sau daya kafin ya tashi," Aneesah tace "Allah sarki, a nn xaka yi park," ta nuna masa kofar gidansu, yyi parkin din snn suka fito daga motar, tayi kofar shiga gidansu da sauri yace"kanwata jirani mana," ta dawo cike da doki tace "to yayana," a tare suka shiga gidan, Aneesah ta karasa bakin kofar dakinsu da sauri tana cewa "Ammina, Ammina" amma shiru, ta tura kofar dakin da sauri taga duhu, ta fara kalle kallen tsakar gidan bata ga alamar damutum cikin gidan ba, bata san lkcn da ta fashe da kuka a rude ba, Mujaheed ya karaso kusa da ita da sauri yace "me ya faru kanwata," cikin kuka tace "Ammina bata ciki?" ya kunna fitilar wayarsa da yake gari ya fara duhu yana haska dakin, ko ina baja baja, ga hotuna ta ko ina a dakin, kuka sosae Aneesah ke yi a bakinkofar dakin, Mujaheed yyi sallama ya shiga dakin ta bi sa a baya, bbu alaman mutum na rayuwa a dakin a ynxu dae don ko ina yyi kura, ya juya yana kallon Aneesah yace "haba kanwata, ki kwantar da hankalinki Amminki na nn bbu inda ta je," bata ce masa komai ba sae dae har lkcn bata fasa kukan da take ba, ya durkusa yana kallon hotunan dake watse a dakin, ya dauki hoton yusuf yana kalloyace "ina kuwa na taba ganin yaron nn, he looks familiar" Aneesah ta durkushe gabansa da sauri tace "ka taba ganinsa ne," Mujaheed ya sosa kai yace "yea ina ga kmr hka," can yace "yes na taba ganinsa ranar da nace maki na xo anguwan nn gun frnd dina," Aneesah na murmushi tace "don Allah, a ina ka gansa toh?" Mujaheed yace "ball dinsa na taka da motata ranan," Aneesah tayi shiru a sanyaye tana kallon Mujaheed, Mujaheed yyi murmushi yace "he ix a vry brave boy, tun kan na fito yyi knck din min kofar motata, ina fitowa kuwa yace sabuwa xaka siya min ko gyaramin wnn xaka yi," Mujaheed yyi dariya ssae yace "kai yaban dariya ranan, don mamaki ma kasa ce masa komai nayi" yana ganin hka yace "to idan bnda kudi na tafi, amma watarana na kawo masa balldinsa," Mujaheed yyi murmushi yana kallon Aneesah da hawaye ya cika idonta yace "dubu biyu ke hannuna ranan, na dauka na basa yyi min gdya ya shiga gida abokanansa na ta dariya, a vry brave boy" can Mujaheed yyi shiru daga surutun da yake yace "hope ba shi bne ya rasu Aneesah?".Aneesah ta fashe da kuka tace " uhm shine," Mujaheed ya wara ido yace "innalillahi wa inna'ilaihi raji'un," me ya samesa?" ta kasa ba sa amsa sae kukan da take yi har da shessheka, ya dago kanta yace "ya isa Aneesah Allah ya sa ya hutu, kar ki sake kuka, Addu'a xa kiyi masa," kai kawae ta gyada masa, ya dago ta yace "ina kike tunanin ammi xata tafi ynxu?" ta girgixa kai tana hawaye tace"nima bn sani ba," ya ciro handkerchief ya goge mata fuskarta yace"wani neighbour ne kuka fi close da a anguwan nn muje mu ji ko sun san inda Ammi tayi," a hankali Aneesah tace "Anty Amina ce," ya kamo hannunta yace "to xo mu je gun ta," suka fita daga gidan ta nuna masa gidan matar, Aneesah ce ta fara shiga da sallama Amina na xaune tsakar gida tana alwala, ta amsa sallamar tana cewa "wanene," Aneesah tace "ni ce maman mubarak," sororo ta tsaya kallon Aneesah baki bude, Aneesah ta yi murmushin dole tana gaisheta, matar ta rike haba tace "anshiga uku ke Aneesah daga ina hka?" Aneesah bata ce komai ba sae murmushin karfin halin da take, Aminar ta ja ta da sauri suka shiga daki tace "ikon Allah Aneesah ina kika shiga, daga ina hka" Aneesah tace "maman mubarack Ammina fa?" Matar ta girgixa kai cike da jimami tace "ae Ammi rabona da ita yau kusan wata uku Aneesah ban san inda tayiba wllh, tun bayan sallaman da ta xo tayi min gashi ita ba waya ba, na kira su kaka a can gombe sun ce bata je ba, amma kuma suna waya ko ta yaya oho," Aneesah ta shiga xubda hawaye ba kakkautawa maman mubarack tace "ynxu me ya kawo ki nn Aneesah rayuwarki na cikin hatsari wllh kullum a kalla mutane fiye da biyar

Chapter 11 of 23