Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
shigowarsa gidan daga gidan Aminin late dad dinsa Alhaji usman ba, shima can yyi ya gaji ya kyalesa , yana ta harkokin gabansa a gidan kmr bae san da shi take ba, ta gaji don kanta tayi shiru, karfe goma na safe ya shigo falonsu cikin kananan kaya, Hajiyar na xaune da su sumy suna kallo, bae ko kallesu ba ya dae gaisheta bata tanka masa ba xae fita ta sha gabansa da sauri tace "gidan ubanwa xaka?" yana kallonta yace "fita xanyi," a fusace tace "bbu inda xaka wllh," yace "dalili" xata yi magana sumy ta tabe baki tace "kai ke ma dae mumy da wahal da kanki kike wllh, ki ta bata bakin ki a kan wanda bae ma san kina yi ba, ke ina ruwanki? kawae ki rabu dashi yyi yanda ya ga dama, dis tym around idan aka yanke masa hukuncin daurin rai da rai can ta matse masa ae ba shi kadai kika haifa ba, iya ka ....." ta fasa ihu ganin yayo kanta kmr xaki, ya cafketa, da kyar Hajiya ta kwace ta don laga laga yyi mata, ya fice daga gidan, ita kuka Hajiyar kuka. Pretty dake kan dinnin table ta kife kanta tana ta dariya a hankali. Gidansu Mujaheed ya nufa, yana shiga daga bakin kofar hajiyarsa ta tare sa ta yi masa sannu da xuwa faram faram snn tace wajen wa ya xo, yace mujaheed, tace "ayya ae daxun nn ya tafi airport dad dinsa na nemansa, na san xuwa ynxu ma jirginsu ya tashi," ya tsaya mata kallo mai shige da ta rainin wayo, xata yi magana, sae ga Mujaheed ya sakko yana kallon Hydar, Hydar ya juya a fusace ya fice daga gidan, Hajiyar ta juya ta balbale Mujaheed din da masifa tana cewa bana ce maka bana son taraiyarka da Hydar ba, gulma ce ta sauko da kai ynxu ko me? bae saurareta ba ya dan ja tsaki ya koma sama, yana shiga daki kiran Hydar ya shigo wayarsa, ya daga Hydar yace "ina ka kai Aneesah?" sae da yyi shiru na kusan minti biyu, har sae da Hydar yace "re yhu there" snn yace "tana gidansu Mudatheer," Hydar yace "waye Mudatheer," nn ma sae da yyi shiru snn ya basa amsa yace "abokina ne," Hydar yace "ka ban Address," Mujaheed yace "kayi me da shi," kan Hydar ya basa amsa yyi saurin cewa ok, bari nayi maka tex din address din, yana kai wa nn ya kashe kiran ya tura masa address din ya fada kan gado yana jin wani xaxxabi na neman rufesa. Da yamma Hydar ya tafi gidansu Mudatheer, a waje yyi parkin motarsa dae dae lkcn da Mudatheer ya fito da motarsa daga gidan xae fita, ya tsaya suka gaisa snn yace masa gun Aneesah ya xo, Mudatheer yyi parkin a waje snn suka shiga gidan tare, har falo ya shiga da shi snn yaje gaya ma mum dinsa ta shigo falon suka gaisa da Hydar din, tana cewa kai ne wanda Mujaheed yace min xae xo knn, yyi murmushi yace nine mum, tace to bari na turo maka ita, yana xaune suna dan hira da Mudatheer Aneesah ta shigo falon da ummi, jikinta yyi sanyi ganin Hydar, ta nemi gu ta xauna, ummi ta gaishesa ya amsa yana murmushi snn ta koma daki, Mudatheer yyi ma Hydar sallama shima ya fita, kanta a kasa ta gaishesa, shima ba tare da ya kalleta ba ya amsa, snn yace "baki da wata matsala nn ko," ta gyada masa kai tana kallonsa, ya daga kafada yana kallonta ya mike tsaye yace "ok gud, saura nn ma ki watsar da mutuncin naki," ya ciro kudi ya ajiye mata yace "incase kina da wani bukatan," yana kai wa nn ya juya ya fice daga falon ko sallama da masu gidan ma bae yi ba, ta bi sa da kallo hawaye na bin kuncinta, ta mike da kyar tayi hanyar dakin ummi ta fada kan gado ta fashe da kuka. . Mujaheed ya sauko downstairs a hankali yana kallon mahaifiyarsa dake xaune kan kujera tana kallo lkci daya tana cin fruits din dake cikin bowl a gefenta, 'yar aiki na durkushe gabanta tana yanke mata kumba, ya karaso cikin falon ya xauna yana kallonta yace "mum xan dan fita don Allah," ta hade rae ta juya tana kallonsa tace "xuwa ina?" ya dan sunkuyar da kansa yace "gidansu saleem xani wllh," tace "shknn amma kar ka dde, bari na baka sako ka kai ma Hajiya Amina," kai kawae ya gyada mata ta mike tayi hanyar stairs, ya tsaya kallon 'yar aikin dake durkushe wajen tana jiran dawowar Hajiyar, ya girgixa kai ya kauda fuskarsa, ynxu duk masu aiki irin hka tausayi suke basa sbda Aneesar sa, yana kallonta yace "kinyi makaranta," ta dan tsorata don bae taba mata magana ba, ta gyada masa kai a tsorace tana gyara hijabinta, ya ciro check ya rubuta kudi mai yawa, ya yaga ya mika mata yana kallonta ya girgixa mata kai yace "kar ki sake dawo wa nn da sunan aiki, ki kai ma mamarki ku ja jari, ki ci gaba da karatunki, ki kuma boye kar Hajiya ta gani," hawaye ya cika idon yarinyar tana kallonsa xata yi magana, ya girgixa mata kai yace "kar ki gode min," yana kai wa nn ya mike ya bi mahaifiyarsa sama, ya karbi sakon ya fito ya shiga motarsa ya bar gidan. A can gidansu saleem ya kira Mudatheer yace "ya datheer ka koma gidan ka bata," Mudatheer yace "bari na kai mata tana daki," ya katse kiran yyi hanyar dakin kanwarsa ummi, yyi sallama suka amsa masa, tana xaune ta tsura ma Tv ido duk da ba sanin me akeyi tayi ba don tayi xurfi a tunaninta, ummi kuwa na xaune tana assignment don har ta fara higher institution, ya karaso cikin dakin yana kallon Aneesah yace "ya dae kanwarmu, lfyarki kuwa," ta kirkiro murmushi tace "to ca nayi maka banda lfya da " ummi tace "shi dae na gani, ya shigo da borin kunyarsa bae siyo mana abinda yace ba," mudatheer yyi dariya, Aneesah ta tabe baki tace "ashe dae kin ganosa ummi," ya mika mata wayar yace "kar ku damu anjima da nyt kafin Abba ya dawo sae mu fita duk ku xabi abinda ku ke so, gashi nn Mujaheed xae maki magana," da sauri ta amshi wayar ta wara ido tace "yayana," kai kawae ya gyada mata tace "na kirasa?" wayar ya shiga ring ta daga da sauri cikin tsigar shagwaba duk da ba da gangan tayi hkn ba tace "yayana," Mujaheed ya lumshe ido yace "kanwata," a sanyaye ta gaishesa, shima ya amsa a hkn, snn yace "baki da matsala ko kanwata," ta gyada kai kmr yana ganinta tace "eh yayana, baka xo ba kuma har ynxu," yyi shiru hkn yasa, tace "yayana," ya amsa a sanyaye yace "kanwata," tayi shiru, yace "xan xo kanwata, bana nn ne ynxu kinji, ba Hydar yana xuwa ba," ta gyada masa kai da kyar tana kkrin maida hawayen da ya taru mata a ido, yace "xamu dinga waya kanwata, i luv yhu dearly," ta dan juya ta sace kallon ummi da hankalinta ke kan takardarta, Mudatheer dama tuni ya fita, a sanyaye tace "i luv yhu 2 yayana," yyi murmushi da ya bayyana dimples dinsa a hankali yace "ngd kanwata," ta gyada masa kai kmr yana ganinta, yyi mata bye ya katse kiran, ya kife kansa kan computer desk din dake dakin salim don kan kujerar yake xaune, xuciyarsa na tafarfasa, ya rasa abinda ke masa ddi a duniyar, to ynxu mae xae yi ya taimaki Aneesah kafin a sake xama kotu, Abdul ya fado masa, ya mike xaune da sauri, "he might be of help 2 us" ya fadi a hankali yana tunanin inda ya ajiye complimentary card din Abdul din, ya mike tsaye da sauri ya fice daga dakin don saleem na wanka ne, ya fita xuwa motarsa ya bude ya shiga duba card din, cikin ikon Allah ya gani ya dauka yana kallon numbrs din Abdul, yyi murmushi ya ciro wayarsa ya shiga kwashe nmbr. . A Eatry Mujaheed ya hadu da Abdul kmr yanda suka shirya, suna gama gaisawa Abdul yace "nayi ta jiran call dinka shiru, kuma naje can gidan sau dayawa bana samunka," Mujaheed yace "eh ina kano" Abdul yace "ok, ina kanwartaka," Mujaheed ya shashantar da batun yace "ya kuma aka ji da abinda ya faru da dad dinka" da mamaki Abdul yace "A ina kasan dad dina?" Mujaheed yace "A haba dae wanene bae san Honourable Shehu ba a nn Abuja," Abdul ya daga kafadarsa yace "wnn kuma shi ya siyan ma kansa," da mamaki Mujaheed yace "don me xaka ce hka Abdul, ba dad dinka bne," Abdul bae ce komai ba ya daga wayarsa dake ringing, Mujaheed ya tsura masa ido yana dan murmushi jin irin turancin da yake, har ya gama wayar snn yace "A abroad kke knn?" Abdul ya gyada masa kai ba tare da ya kallesa ba, Mujaheed ya jinjina kai yace "wae me dad naka yyi hka ne? An sake sa kuwa? " Abdul yace "A'a ban sani ba, kuma dukiyar da ba tasa ba ke hannunsa," Mujaheed ya girgixa kai fuskarsa dauke da damuwa kmr gaske yace "dukiyarsu waye?" "na kaninsa ne," Abdul ya fadi yana maida wayarsa cikin Aljihu, yanda Abdul ke ba sa amsan ya nuna masa baya son xancen, Mujaheed yace "ayya, kuma ina kanin nasa," Abdul ya gyara xama lkci daya ya dauki lemon gabansa yana sha yace "he'z late," "to iyalensa fa?" Mujaheed ya sake jefo masa wani tambayar, Abdul yyi masa wani irin kallo yace "am i here 2 answer yhur unnecessary questns?" Mujaheed ya dan saita murya yace "ba hka bane abokina, i just want 2 knw ba dae kanwata kke son gani ba, xan kai ka wajenta yau," Abdul yace "iyalensa suna nn mana," Mujaheed yace "nn garin?" Abdul ya dan yi shiru snn da damuwa yace "ban san inda cousin din tawa take ba, hka ma mum dinta ban san inda dad dina ya kai ta ba," Mujaheed ya tsura masa ido yana kallonsa sae a nn ya lura da kaman da suke yi da Aneesah ssae kuma, don Abdul kyakkyawa ne na karshe, idonsa exactly na Aneesah, Mujaheed ya kauda kansa yace "kasan me nake so da kai Dr," Abdul yana kallonsa yace "am ol ears," mujaheed ya fara magana murya can kasa yace "Abdul, idan ka bani hadin kai wllh xan nemo maka cousin din taka, i just want yhu 2 help me, ni kuma nayi maka alkawarin xan fito maka da 'yar uwarka don nasan inda take," da sauri Abdul yace "me kke bukata daga gare ni?" Mujaheed ya dan yi cylnt snn yace "ka samo min information din inda dad dinka ya kai mata mahaifiyarta, snn na san baxa ka rasa sanin inda document din dukiyarsu da komai yake ba, don hka nake son ranar da xan nuna maka ita ka taho da su ka damka mata a hannunta," Abdul yyi masa mugun kallo yace "kai din wa xaka sa ni nayi hkn?" Mujaheed ya daga kafada ya mike tsaye yace "ok, i wil b on my way," Abdul yace "wait, ka gaya min meye hadinka da su?" ya koma ya xauna yana kallon Abdul da kyau yace "Aneesah da kke nema tana gu na, amma baxa ka ganta ba har sae ka san inda Amminta take ka gaya min," Abdul ya mike tsaye da sauri yace "ok wnn ba matsala bane, amma yaushe xan ganta?" Mujaheed yace "as soon as Amminta ta bayyana," Abdul yyi shiru kmr mai naxari snn yace "ok nn da kwana uku xaka ji ni," Mujaheed ya mike tsaye yace "to ngd i wil b on my way," Abdul yace "wait, ka gaya min kai waye don Allah," Mujaheed yace "sunana Mujaheed Muhd," a tare suka fita daga eatry din suka yi sallama da juna a kan sae nn da kwana biyu xasu hadu. Aneesah na xaune a garden ita da ummi, sanye suke cikin riga da skirt gaba daya, ranar dae ummi ta tilasta Aneesah ta dan yi light make up tayi kyau ssae har ba a magana, suna game a laptop wayar ummi yyi kara, Aneesah ta daga ganin mummy ce ke kiran, tace "mumy har kin shirya," mumyn tace "Aneesah ce?" Aneesah tace "eh nice mumy," Hajiyar tace "maxa ki shigo gida ana nemanki," Aneesah tace "to gani nn xuwa mumy," ta mike tana kallon ummi tace "ummi xo ki rakani wae ana nemana kila yayana ne," ummi tace "je ki ina xuwa don baxan tashi ba sae na gama abinda nake," Aneesah bata sake saurarata ba ta shiga falo da sallamarta, xaune ta gansa yana danna wayarsa, gabanta yyi mugun faduwa don a tunaninta Mujaheed ne ya xo, ta karaso falon a sanyaye jiki ba kwari, ta dan xauna kan kujera tana kallonsa tace "ina yini," ba tare da ya dago kai ba yace "lfya lau," ta sunkuyar da kanta bata sake cewa kmai ba shi ma hka, can ta dago a hnkli tana kallnsa taga kallnta yke, suna hada ido ya sauke idonsa da sauri itama hka, a hkn Hajiya ta sauko ta samesu tace "lah ke dae Aneesah shirmammiya ce wllh, ko ruwa baki kawo masa ba ashe," Aneesar ta mike tsaye tana murmushi, hajiyar ta koma sama, ita ko tayi hanyar fridge ta dauko lemo da ruwa ta daura kan faranti da cup ta shigo falon ta durkusa gabansa ta ajiye masa, har xata mike sae ta fasa ta bude lemon ta xuba masa a cup ta daga tana mika masa a sanyaye tace "gashi ya Hydar," ya tsura mata ido bae ce komai ba, hkn yasa xata ajiye kofin, ya mika mata hannu ta dago dara daran idonta tana kallonsa ta mika masa lemon, hmm tarihi ya maimaita kansa, don kasa rike cup din yyi, ya fada kan farin kayansa. END OF BOOK TWO @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 31&32 ~31~ .Aneesah ta koma baya a tsorace tana kallonsa gabanta na faduwa, don gani take kmr xata ji an rufeta da duka kmr wancan ranar, duk ta rude ta rasa abinda xata yi, ta cire mayafin jikinta da sauri ta shiga goge masa muryarta na rawa tace "kayi hkuri ban sani ba," ya sauko kasa a hankali yana kallonta ya karbi mayafin daga hannunta, ta sunkuyar da kai ta koma baya da sauri, duk ta takura da irin kallon da yake mata, hkn yasa ta fara kkrin mikewa daga wajen, taji ya kirata, ta dago kai tana kallonsa, a hankali taji yace "i love yhu," ta yi still a wajen kmr an dasa ta ta tsura masa ido tana kallonsa, a raunane taji ya fara magana yace "ina sonki Aneesah, ina sonki ssai, tun ranar da na fara daura idona a kanki naji sonki, ban san wani irin so nake maki ba Aneesah, Aneesah ki fada min tsakanin ki da Allah meye tsakaninki da Aminina Mujaheed, ni nasan waye Mujaheed just lyk dat baxae sake maki har hka ba, miskili ne shi dan girman kai, bae dauke mace a bakin komai ba, ki gaya min mene ya janyo hkn kar ki min karya Aneesah" yyi shiru yana kallonta ganin irin hawayen da take tana girgixa kai kmr ana xubo su, ya kauda kansa da sauri ya rumtse idonsa, da kyar ya iya mike wa bae ce mata komai ba ya fice daga gida, Aneesah ta jingina jikin kujera tana hawaye ba kakkautawa ji take kmr numfashinta xae dauke, maganganunsa suka shiga yawo mata a kai, ta kasa gaskata abubuwan da taji daga bakinsa, a hka ummi ta shigo ta tar da ta, ta karaso cikin falon da sauri ta durkushe gabanta tace "me ya faru Aneesah kukan me kike," Aneesah ta girgixa mata kai ta fashe da kuka, a fusace ummi tace "wae wnn waye da kullum in ya xo sae ya sa ki kuka," Aneesah bata ce mata komai ba, hkn yasa ummi ta mike tayi hanyar daki Aneesah ta rikota da sauri sanin mumy xata je ta kira mata, da kyar tace "wllh bbu komai ummi yayana ne," ummi ta galla mata harara tace "bbu komai kike kuka hka," Aneesah ta girgixa mata kai tana share fuskarta tace "sbda ya tafi ne shi yasa nake kuka," ummi ta durkusa tana kallonta da tausayi tace "to kiyi hkuri, kuma ai naga yana xuwa a kai a kai ko," Aneesah ta gyada mata kai ummi ta kamo hannunta suka bar falon suka yi hanyar daki. Hydar na kwance dakinsa idonsa a lumshe, pretty na gefensa a xaune tana kallonsa 4 d sixth tym knn tana masa magana tun bayan shigowarta dakin amma yaki kulata, tace "shkkn yaya tunda baxa ka kulani ba ni xan fita amma shawarar da xan baka a matsayina na kanwarka da baxae cutar da kai ba bae wuce in ce maka indae har kan Aneesah kke sa kanka cikin damuwa to ka daina, iyakaci ka yi mata taimakon da kayi niyyar yi mata ka koma holland kan harkokin gabanka, Allah xae baka warce tafi ta, don Aneesah ta fi karfinka," tana kai wa nn ta mike xata bar dakin, ya mike xaune da sauri yana kallonta yace "don me kika ce hka Zainab?" ta juya tana kallonsa tace "to yaya me xa kayi da warce xata iya kwana dakin wanda ba muharraminta ba? Wllh Aneesah tafi karfinka yaya baxan bari ka cuce kanka ba," da kyar xuciyarsa na mugun bugu yace "dakin wa ta kwana Zainab," ta tabe baki tace "Mujaheed mana, hka kawae ka dinga daga hankalinka kan warce bata san ciwon kanta ba ni wllh Aneesah ta gama sare min" tana kai wa nn ta juya ta fice daga dakin, Hydar ya ji hawaye na neman taron masa a ido ya dafe kansa yana kiran Allah da kyar a cikin xuciyarsa, ya kai minti goma a hka wayarsa ta shiga ring, ya kasa daga kai ya kalli wayar ma don tashin hankali, ya karaci ringin dinsa ya katse, yana nn a hka har aka kira Maghrib ya mike da kyar yana ganin jiri ya shiga bathroom ya dauro alwala ya fito, ya kasa fita xuwa masallaci, a dakin yyi sllh, yana xaune kan darduman har karfe takwas snn yyi na isha'i, aka bude kofar dakin hajiya ta shigo ta xauna kan kujera tana kallonsa da damuwa tace "naga baka fita xuwa masallaci ba yau Aliyu, lafiyarka kuwa," yace "lfya lau mum," tace "anya kuwa son dubi yanda ka rame daga jiya xuwa yau don Allah ka gaya min me ke damunka ko wni abun na kuma yi maka," ya girgixa kai da kyar yace "bbu komai wllh mum," ta mike tsaye tace "to bari na kawo maka abinci favourite dinka na girka maka yau," kai kawae ya gyada mata ta fita, ko da ta dawo da abinci ca yyi mata ta ajiye masa kawae xae ci, tace masa to, ta fita daga dakin ya bi ta da kallon tausayi ganin yanda ta tada hankalinta a kansa duk da rashin binta da yake yi, ynxu ya gane cewa no mata wat ko ma wacece uwarka ka bita, don kila ynxu hakkinta ne ke binsa, tunda ga halin da ya tsinci kansa kan wata can, yyi daya sanin son Aneesah, yyi daya sanin saninta, Aneesah ta cucesa tayi ruin din rayuwarsa, tunanin hkn yasa ya mike da kyar yana jin xaxxabi ya fada kan gado, bayan kmr awa daya pretty ta shigo dakin tana kallonsa tace "ya Mujaheed yana nemanka yaya," ya bude ido da sauri yana kallonta yace "kice masa bana nn," xata yi magana Mujaheed ya budo kofar dakin ya shigo . Mujaheed ya karaso cikin dakin yana kallon pretty yace "ke wae yaushe kika fitsare ne hka Zainab," pretty ta juya tana shirin fita daga dakin tace "ba ca nayi maka ina xuwa ba," ta fice ba tare da ta jira mai xae ce ba, don wani mugun haushinsa take ji ynxu, Mujaheed ya kalle Hydar da ya lumshe idonsa ya karaso gefen gadon ya xauna yana kallonsa yace "ya dae frnd ina ta kiranka baka daga wayar ba," Hydar yyi masa shiru har lkcn idonsa a lumshe, Mujaheed yace "wae bacci kke ne ina magana kayi shiru," Hydar ya bude ido a hankali yana kallonsa yace "ina jinka, banga call din ka ba" Mujaheed ya mike ya dauko wayar yana kallo yace "ba gashi nn ba, har 3 missed cals" Hydar yace "to ban sani ba," Mujaheed ya ajiye wayar yana kallonsa yace "wae ya na ganka wani iri ne Aliyu, ko baka da lafiya ne?" ba tare da Hydar ya kallesa ba yace "lfyata lau," Mujaheed ya tabe baki yace "to Allah ya kyauta, kana ji na magana na xo muyi?" Hydar yace "ina jinka," Mujaheed yace "ae kasan son din Baffan Aneesah, Abdul?" Hydar yyi shiru bae ce komai ba, Mujaheed yace "am tokn fa Aliyu, wae don Allah me ke damunka ne" Hydar yace "ina jinka me aka yi?" Mujaheed ya daga kafada alamar shi ya sani snn yace "kasan sa?" Hydar yace "ehh," Mujaheed yace "gud, mistakenly akwae randa muka hadu dashi a hanya da Aneesah, but funnily bae ganeta ba, tun daga lkcn yake bibiyanmu yana nuna min kmr ya santa, ni ko na nuna masa xan basa mamaki idan ya sake binmu, as in d guy was vry confuse, har dae daga karshe ganin yanda ya damu yasa n karbi card dinsa nace xan kirasa duk don ya rabu damu, so just recently i thought he myt b of help 2 us nd guess wat i was absolutly ryt cos nn da kwana uku yace xae gano min inda Ammin Aneesah take, is'nt dat great, though na dan masa tambayoyi na samu informations kadan, nd kasan wani abu frnd, wllh bae gane ita ce Aneesah ba still, ina ga kmr gayen na da brain disorder, amma dae don ya maida hankali gun sanin inda Ammi take nace masa ita ce Aneesar da yake nema, amma baxae ganta ba har sae ya nemo Ammi" Mujaheed yyi shiru yana kallon Hydar ganin shi daya yake ta surutunsa, don Hydar idonsa a lumshe yake kmr mae bacci, a fusace Mujaheed yace "Hey wnn wani irin wlknci ne kke min hka Aliyu, ina magana ka mai da ni kmr wani mahaukaci kayi bnxa da ni," Hydar ya mike a fusace yace "to me kke son na ce maka ko kuma me xan yi maku, meye nawa kuma a ciki, plss don Allah ka rabu dani i beg yhu stay away frm me huh!" Mujaheed ya tsaya da mugun mamaki yana kallon Hydar da ya koma ya kwanta, yace "oohh wnders shall neva cease! don an bata maka rae a gida sae ka huce kai na kuma malam, ae ba ni na bata maka ran ba don hka sae ka sauka ka same su downstairs," a fusace Mujaheed yyi maganar, Hydar ya mike shima a fusacen ya shakesa yana huci yace "kai!!" hka Mujaheed ya bude baki yana kallonsa, Hydar yace "ka kama kanka kar ya bace mana a dakin nn," Mujaheed yyi murmushi ya cire hannun Hydar a wuyarsa ya mike tsaye yana kallon Hydar din yace "ka ci sa'a ni naxo na same ka amma da baxae mana kyau ba daga ni har kai yau," yana kai wa nn ya fice daga dakin, Hydar ya koma ya xauna kan gado ya dafe kansa yana mayar da numfashi, Aneesah ta cucesa ta cucesa, yyi daya sanin saninta, ya fada kan gado ya shige cikin blanket jin wani irin sanyi dake shigarsa. . Mujaheed na komawa gida Hajiyrsa ta dinga tambayarsa mai ya faru ganin ynda ya shigo gidan, bae ce mata kmai ba ya haura sama ya shiga bedroom dinsa, ta juya tana kallon kanwarsa Amira tace "ina yace maki xae je Amira," yarinyar tace "bae gaya min ba," Hajiyar ta mike ta bisa dakin nasa, yana xaune yana shan lemon kwali, ta xauna kan kujera tana kallnsa tace "ya akayi prince wa ya bata maka rae hka?" ya girgixa mata kai yace "no one, just tired," ta ce "to ka kwanta ka huta," ya gyada mata kai ta fice daga dakin ya fada kan gado, ynxu Aneesah kawae yake son gani amma Hajiyarsa ta hanasa, shi kuma gashi baya tsallake umarninta don tun ranar da ya kai Aneesah gidansu Mudatheer bae sake komawa ba. Bayan kwana biyu Mujaheed ya hadu da Abdul kmr ynda suka shirya, bayan sun gaisa Mujaheed yace "ya dae, ka gano min inda take," Abdul yace "na dan wahala kafin mum dina ta gaya min, tace tana katsina" Mujaheed yace "katsina kuma, me take yi a can," Abdul ya dan yatsine fuska yace "kmr ko aiki take yi ko menene ni bn gane xancen nata ba ma, amma gidan mai kudine ssae abokin dad din nawa ne, kuma gidan da tsaro dayawa, matansa uku, kila aiki take masu a gidan" Mujaheed ya gyada kai yace "gud, to ynxu ya xa ayi ka fito da ita indae har kana son gnin Aneesah," Abdul ya dan yi shiru snn yace "sae naje katsina knn," Mujaheed yace "to shknn, kmr yaushe xaka tafi knn?" Abdul yace "ko xuwa gobe," Mujaheed yyi shiru yana dan naxari snn yace "to mu tafi tare mana," Abdul yace "idan hkn yyi suit dinka," Mujaheed yace "shknn ngd ssae gobe as early as 7a.m ka taho gida ka sameni, sae mu tafi da motata" Abdul yace "ok," Mujaheed ya basa hannu suka yi shake din juna snn suka fita daga Eatry din. Hajiya duk ta rude ta shiga damuwa ganin ynda Aliyu ya rame, yau kam tun safe bae ko kalli break din da ta hada masa ba har gashi kusan karfe 1, alhalin abincin jiya ma da daddare bae ci ba coffee kadae ya sha, ta xauna gefen gadon da damuwa tana kallonsa tace "haba Aliyu ka ki gaya min meye matsalarka, don Allah ka tausayamin ka gaya min me ke damunka hka, duba fa yanda ka koma," ya mike xaune yana kallonta yace "ni nace maki bbu abinda yake damuna mum," ta girgixa kai tace "ban yrda ba Aliyu, a hkan xaka ce min bbu abinda ke damunka," ya dan kirkiro murmushi yace "kawae dae bana dan jin ddi ne kwanan nn," tace "to ka tashi mu tafi asibiti ko kuma na kira maka Dr umar," yace "aa ki bari kawae mum am feelin much beta ynxu," bata ce masa komai ba ta fita daga dakin, bayan kmr minti talatin sae ga Dr umar din ya xo, da yake babba ne Hydar bae masa musu ba ya bari ya dubasa don abokin late father dinsa ne, har ya gama gwaje gwajensa bae ce ma Hydar komai ba ya fita yaje ya samu mahaifiyar tasa a kasa, tace "me ke damunsa doctor malaria ko typhoid?" likitan ya mata wani irin kallo yace "wani malaria? Kina nn xaune jinin danki ya hau har hka, haba Hajiya me ke damun Aliyu hka? Don ma yaron mai karfin hali ne, Meye matsalarsa a rayuwa?" Hajiya ta saki salati ta fashe da kuka tace "wllh doctor ban sani ba, duk kwanan nn ynda ka gansa hka yake ko abinci baya ci, shi kadae gareni doctor ban san me yasa a ransa hka ba yake damunsa, ka tambayar min shi don Allah ko xae gaya maka doctor" likitan ya shiga kwantar mata da hankali yace kar ta damu xae shawo kan koma,

Chapter 17 of 23