Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Ammi ta kasa gane kan Aneesah duk ita ma ta daga hankalinta, ita dae Aneesah jiran dawowar ya faruuq kawae take, da yamma tana share tsakar gida taji an bude kofar gidan ta mike da sauri a tunaninta Faruuq ne, pretty ce ta shigo gidan kmr mahaukaciya wasu mata na biye da ita a baya, gaban Aneesah yyi mugun faduwa, pretty ta karaso kusa da ita da sauri ta rikota ta fashe da kuka tace "me kika yi ma yayana Aneesah, ki gaya min me kika yi ma yayana," ta sulale kasa ta daura hannu a ka tana kuka mai ban tausayi tace "don Allah ki gaya min me kika yi masa," Hajiyar Mujaheed ta karaso cikin gidan ita ma a rude tana kallon Aneesah tace "ke ce Aneesah ko," Aneesah ta kasa cewa komai don tashin hankali, a hankali ta sami kanta da sulale kasa ta fasa wani ihu a tsorace, hajiyar ta durkushe gabanta a rude ta rikota tace "don Allah ki rufa mana asiri," don a tunaninta suma Aneesah xata yi, Ammi da bata gidan ta shigo dai dai lkcn, ta karaso a dan tsorace tace "me ya faru," pretty na kuka ssae tace "don Allah mama ki bar ta ta bi mu asibiti, kar yayana ya mutu ita yake ta kira," daya daga cikin matan da suka shigo gidan ta dago Aneesah tayi waje da ita, Hajiya na biye da su da sauri, duk da ganinsu kasan suna cikin tashin hankali, Aneesah komawa tayi kmr statue duk ta kasa wani kwakkwaran tunani da kwakwalwarta, ta xama kmr wata mutum mutumi, hawayenta ma tamkar sun kafe take ga, Amai ta shiga kwararawa cikin motar ba gaira ba dalili, don har lkcn ita bata gama fahimtan abinda ke faruwa ba, matan suka riketa a rude wata na xuba mata ruwa, sae a snn maganganun pretty suka dinga dawo mata, daga nn kuma bata sake sanin abun da ya faru ba, don sulalewa jikin matar da ke rike da ita tayi sumammiya.duk suka rude a motar wasu har da kuka, pretty nata kam ba a magana, suna isa asibitin ita ma aka shiga da ita da sauri. Ko da ta bude idonta pretty ta gani xaune gefenta tana kuka, pretty ta kamo hannunta cikin kuka tace "don Allah kar ki sake rufe idonki Aneesah ki tausayama yayana," wata nurse ta shigo ta janye pretty daga kusa da Aneesah da ta xuba mata ido kmr wata mara hankali, nurse din tasa duk matan dake dakin suka fita, Aneesah dae binsu kawae take da kallo, nurse din ta fita ta ja kofar, bacci mai nauyi ya dauketa daga nan . a hankali Aneesah ta bude idonta ta shiga kare ma inda take kallo, daga karshe ta sauke idonta kan drip din dake hannunta, ta fara kkrin mikewa xaune, taji muryan mutum a gefenta, ta juya da sauri taga Abdul ne, yace "ya jikin kanwata" tayi shiru tana kallonsa, ya mike ya fita ya shigo da nurse ta cire mata drip snn tace a bata tea ta sha, Abdul ya fita ya shigo tare da mum din Mujaheed ta karaso kusa da Aneesah tace "sannu kinji Aneesah," Aneesah dae bata ce komai ba sae kallonta da take, ta hada mata tea ta shiga bata da kanta, kadan Aneesah ta sha ta kauda mata kai Hajiyar tace "ki sha mana Aneesah," Aneesah ta girgixa mata kai a karo na farko muryarta a shake tace "ya Hydar fa," Hajiyar tace "ki daure ki sha sae na kai ki gunsa bacci yake," da kyar ta shiga kurban tean har tayi rabi tace ta koshi, wata nurse ta shigo da magunguna mum din Mujaheed ta karba tace "xa mu iya dan fita da ita nurse," Nurse din tace "idan har bata ganin jiri xaku iya fita da ita amma kar kuyi nisa," Hajiya tace "A'a bama waje xamu ba, ward din dake sama xamu," nurse din tace "ok," tana kallon Aneesah tace "hope bbu inda ke maki ciwo ynxu," Aneesah ta gyada mata kai nurse din ta fita, Abdul yace "mum ku bar Hydar ya huta kar a tada shi," hajiya tace "aa baxa mu tashe sa ba dama, da ya ma aka samu yyi baccin," hajiyar ta taimaka ma Aneesah ta mike tsaye ta bata takalmi ta sa, snn suka fita daga dakin, dakin da Hajiyar ke kwance ta fara kai ta, hajiya duk ta rame ta xama wani iri ita ma a daxun ciwonta ya tashi bayan an aiko mata da rasuwar sumy a can india, snn ga Hydar da aka rasa me ya samesa lkci daya, don lkcn bai ma san da mutuwar kanwartasa ba bare ace shine, Aneesah ta shigo dakin a sanyaye tana kallon hajiyar da ta mike xaune da sauri ganinta, ita ma ruwan ake kara mata, Ammi ma na xaune dakin, cikin murya mai ban tausayi Hajiyar ta fara magana tana kuka, "don Allah Aneesah ki yafe mana, ki tausaya ma rayuwata ki amince ki aure Hydar, shi daya nake da bana son wani abu ya samesa Aneesah, ban gama dawowa hayyacina daga mutuwar Sumayya ba sae ga na Hydar, idan wani abu ya sami Hydar ban san ya rayuwata xata kasance ba," kuka ssae Hajiyar take, Aneesah ma kukan take, duk mutanen dake xaune dakin sae da jikinsu yyi sanyi, Ammi ko kasa dago kanta tayi, Hajiya ta juya a sanyaye tana kallon mum din Mujaheed tace "kun ki gaya min halin da Aliyu ke ciki," mum din Mujaheed tace "nace maki bacci yake yi Hajiya," tana fadin hka ta kama hannun Aneesah suka fita daga dakin, wani ward din daban suka shiga gabanta yyi mugun faduwa ganin Hydar kwance ana kara masa ruwa har leda biyu, faruuq na xaune dakin da wani frnd dinsa, pretty ma na xaune gefensa kmr xata shige jikinsa, duk ta xama wani iri itama abun tausayi, Aneesah ta karasa kusa da shi da sauri ta fada kan gadon tana kuka, faruuq ya janyeta da sauri yace "kar ki tada sa Aneesah," ta koma gefe tana kallonsa tana ci gaba da kukanta mai ban tausayi, Mum din Mujaheed ta kalli Najeeb tace "na samu Mujaheed a waya daxu Najeeb, wae ashe ya koma holland ne, kaji tsiya ko ubansa fa bae sanar ma wa ba bare ni," Najeeb yace "ikon Allah, to kin gaya masa rashin lafiyar Hydar din ne mum," Hajiyar tace "eh na gaya masa, yace gobe xae juyo, yana can duk ya daga hankalinsa shima yau ya kirani yafi sau ashirin " a sanyaye pretty tace "nima yana ta kirana," Najeeb yace "dama kice masa mu hadu a Egypt kawae, can xamu wuce da Hydar gobe," Hajiyar tace "egypt kuma Najeeb," Najeeb yace "wnn Abdul din ne yace hka, shima likita ne ssae, kuma daxu ma wani doctor ya kirani office ya gaya min hka," Hajiyar tace "to mu dae ga mu ga Allah, Allah dae ya basa lfya, ku ba Aneesar kujera ta xauna," Najeeb ya jawo mata kujera ta xauna da kyar, Hajiyar ta juya ta fita, ana kiran sllhn isha duk suka fita yin sllh dakin ya rage daga Aneesah sae pretty, wata mata ta leko tace pretty taje Hajiya na nemanta, ta fita daga dakin tana kallon Aneesah kmr me tsoron kar ta ma yayanta wani abun, bayan ta fita Aneesah ta mike ta karasa kusa da gadon a sanyaye ta dafa gadon tana kallonsa hawaye na bin kuncinta, a hankali ta shiga kiransa ganin bae amsa ba yasa ta fada kansa tana kuka ssae, ranar dae asibitin ta kwana don likitocin ca sukayi ta xauna ko da xae farka ya xamana tana kusa da shi kuma a kanta xae daura ido kafin kowa, dole Ammi ta wuce gida ta barta, cike da tausayin Hydar, Aneesah dae na gefensa a xaune jira kawae take taga ya bude ido amma yaki budewa, hkn yasa ta kasa samun nutsuwa hawaye yaki tsaya mata, ba ita ba kowa ma abinda yake jira knn har likitocin amma shiru. * To nimadai bari natsaya anan kada nima kukan yazomin C U nXt 👉@ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAIYDAR 38➡40 Washegari friday aka fara shirin fitar da Hydar xuwa Egypt ganin har lkcin bae farka ba, bbu wanda hankalinsa yafi tashi irin Aneesah da mum dinsa, Aneesah na xaune gefensa ita dae gata nn, wani lkcn ma sae ayi ta mata magana bata san da ita ake ba, tamkar mai brain disorder ta koma, Hajiya ce ta shigo dakin don taga bbu abinda kwanciya xae mata dan ta na nn rai a hannun Allah, ta karaso cikin dakin a sanyaye tana kallon Aliyu, Aneesah ta mike xata bata kujera tace "yi xamanki Aneesah dama magana na xo muyi dake," Aneesah tayi shiru tana kallonta snn tace "to mumy ina jinki," Hajiya ta juya tana kallon Abdul dake xaune dakin, Aneesah ta gane me take nufi tace "kiyi maganarki mum, yayana ne," Hajiyar ta ja kujera ta xauna a raunane ta fara magana kmr mae shirin fashewa da kuka "Alfarma naxo nema gunki Aneesah, kuma nasan baxa ki hanani ba, Aneesah nasan Hydar na sonki ssae, ke dae ce ban san abinda ke xuciyarki ba, wnn rashin lfyar sbda ke yake yinta, kuma tun ba yau ba yake da hawan jini kuma ni kam nasan ta dalilinki ya samu hawan jini sbda yanda yake sonki, Aneesah ki tausaya mana don Allah don Annabi ki amince a daura maku aure da Hydar sae ki bi su can Egypt din har Allah ya basa lfya, kinga ni baxae yiwu na bi su ba, jiya sumayya ta rasu, kiyi hkuri ki taimake mu Aneesah hkn kadae ne xae dawo min da farincikin da na ko da ya warke ya ganki a matsayin matarsa" tana kai wa nn ta fara hawaye abun tausayi, gaban Aneesah ya shiga bugu da sauri da sauri ta kasa daga kai ta kalle Hajiyar sae hawayen da take ita ma, a xuciyarta tace wayace maki Hydar na sona ynxu, da knn amma ba ynxu ba, muryar Abdul taji yace "ki amince kanwata nasan Hydar na sonki ssae, kuma daga reactions dinsa jiya bbu tantama ta dalilinki hawan jininsa ya tashi, save lyf kanwata, dama Allah yyi shine mijinki" kuka ssae Aneesah take tana kallon Abdul, ya gyada mata kai alamar ta yrda da batun Hajiyar, hajiya sae hawaye take tana jiran cewar Aneesah, da kyar Aneesah ta iya ce mata "sae Ammina ta amince," ko minti biyar Hajiyar bata kara a asibitin ba ta sa aka kaita gun Ammi, Ammi ma ta kasa cewa komai jin batun da Hajiyar ta xo da shi, daga karshe da kyar ta samu na cewa tace to Hajiya ki bari muyi shawara da yan uwana da na ubanta, Hajiyar tace "ba komai 'yar uwa duk yanda kuka yi ina jiran bayani, kinsan kila yau xa a su fita, kuma ga abinda likitoci suka ce ya kasance tana kusa da shi xae far fado, shi yasa nake son ku taimaka nasan Hydar xae riketa amana, kuma son gskya yake mata" Ammi tace "xaki ji ni gobe Hajiya Allah dae ya bashi lfya," Hajiyar taji ddi ssae kmr an mata albishir da gidan Aljanna. Faruuq Ammi ta fara magana da kan batun da Hajiya ta xo da, yyi shiru na dan lkci snn yace "gskya yana sonta ssae Ammi ita fa ya dinga kira ko da muka isa asibiti jiya, sae dae ki fara tuntubarta kar a cuceta ita kuma, amma ya cancanci xama mijinta," faruuq yaje asibiti ya maido da Aneesh gida ranan, duk ta xama wani iri ta rame kamr ita ce mai ciwon, a nutse Ammi ta sa ta gaba ta shiga tambayarta ko tana son Hydar, ta fashe da kuka ssae tana girgixa ma Amminta kai, Ammi tace "kiyi min magana Aneesah kar ki ji komai" cikin kuka muryarta na rawa tace "to Ammi ya Mujaheed fa?" Ammi tayi shiru tana kallonta snn a hankali tace "shi kike so Aneesah?" Aneesah ta kife kanta kan gado tana kuka kmr ranta xae fita ta kasa ce ma Amminta komai, Ammi ta rasa me xata ce mata ita ma, duk iya yan da Ammi ta so jin ko Mujaheed din take so Aneesah kin cewa komai tayi sae kuka, dole Ammi ta kyaleta ta fita daga dakin, daga nn bacci ya dauketa. . Aneesah ta mike tsaye tana ci gaba da kukanta tana kallonsa, ya gyada mata kai da kyar cikin wani irin yanayi yace "yess Aneesah shine mijinki ba ni ba, amma karki manta dani Aneesah ki ci gaba da daukana a matsayin yayanki, Allah ya baku xaman lfya mae dorewa" yana kai wa nn ya dan yi shiru na wani lkci yana kallonta, har lkcn bata daina kukan da take ba kmr ranta xae fita, ya kauda kai yace "ki shiga ciki Aneesah kar Ammi tace kin dde its gettn late," Aneesah taki ko da motsi daga inda take tana kallonsa tana kuka, hkn yasa juya yyi hanyar motarsa snn ya daga mata hannu tare da sakar mata murmushi ya bude motar ya shiga yyi reverse ya bar anguwar, ta xube kasa tana kuka mai ban tausayi ya xa ayi ace ta auri Hydar da baya sonta, wayyo ta shiga uku, muryar faruuq taji yana cewa "haba Aneesah meye hka kike yi sae kace karamar yarinya, so kike ki daura ma kanki wani ciwon ko," ta mike tsaye tana kallonsa cikin kuka tace "ya faruuq ba sona fa Ya Hydar yake ba" faruuq yace "inji wa yace maki haka, Hydar kam yafi kowa sonki Aneesah," da kyar ya lallabata suka shiga gida. Washegari da safe Ammi ta hada break ta bata ta kai asibiti, tare suka tafi da faruuq, Hajiya ta yi murnar ganinta ssae sae nn nn take da ita, bata dde gun su Hajiyar ba tai ward din da Hydar yake gabanta na faduwa ta turo kofan a hankali ta shiga, Najeeb ne xaune dakin da Abdul ta gaishesu a sanyaye Najeeb ya bata kujera ta xauna, tayi shiru tana kallon Hydar din, Abdul ya mike yana kallonta yace "kinyi break kuwa Aneesah, duba fa yanda kika rame duk kin bi kin daga hankalinki," Aneesah tayi shiru bata ce komai ba Abdul ya ajiye mata fruit gabanta yace "ki ci wnn," ta dan yi murmushi ta dauki apple ta kai bakinta, tana nn xaune a dakin har kusan karfe sha biyu ita kadae don su Abdul sun fita, da rana Ameera ta kawo masu abinci, ta dan ci kadan ba dan tana jin ci ba don rashin kuxarin nata na yau yafi na kullum, ko me xae faru kuma yau oho, don indae taji hka a jikinta tasan abu na shirin faruwa Allah dae yasa alkhairi ne, ta juya tana kallon Hydar hawaye cike idonta, yini tayi a dakin daga ita sae shi, sae kuma wa inda ke shigowa dubasa su fita, Ammi ma ta xo ta dubasa ta koma gida, lkci lkci ta kan dinga tofa masa addu'a, duk da hankalinta na gun Mujaheed shi kadae take son gani amma har lkcn bae shigo ba kuma taji muryarsa yana magana da mum din Hydar, bbu abinda yafi daga mata hankali irin yanda taji ana cewa yau xa su wuce Egypt kuma da ita, to me xa ta je tayi masu a can, tana nn dakin a xaune har kusan karfe hudu sae dae in lkcn sllh yyi ta tashi tayi, ta gaji da xama ta daura kanta kan gadon da yake kwance, a yanda ta lura daga ita sae Hajiya da wata kawarta ne a asibitin su Najeeb duk basa nn, hka ma Mum din Mujaheed, motsi taga yana yi ta daga kanta da sauri tana kallonsa gabanta na faduwa, ta mike tsaye ta dafa gadon tana kallon fuskarsa, ganin bae sake motsin ba yasa ta shiga kiran sunansa a hankali kmr mai shirin kuka, ta kirasa ya kai sau uku snn taga ya bude idonsa a hankali ya daura kan fuskarta, ta toshe bakinta kar ta fasa kukan da take shirin yi, a hankali taji ya kira sunanta da muryarsa da baya fitowa. Ta fasa kukan da take hadiyewa ta fada kansa, dae dae nn aka bude kofa Mujaheed ya shigo dakin, ta mike tsaye da sauri tana kallonsa ya karaso kusa da gadon yana kallon Hydar da mamaki yace "waw, Alhmdllh, kin kira likita ne" ta girgixa masa kai ya juya ya fice sae ga shi ya dawo da doctor, doctrn ma kansa yaji ddi ssae don Hydar abokinsa shi dae Hydar tun daga sunan Aneesah da ya kira bae sake cewa komai ba sae binsu da yake da ido. Bbu wanda bae yi mamaki hade da farin cikin farfadowan Hydar ba, Hajiyarsa farin ciki da murna ba a magana ta kasa xaune ta kasa tsaye, Najeeb ya shigo dakin yana dariya yace "kai Hydar Anya kuwa?? dama jira kawae kke a daura ka farfado ko kai gayen nn da mugun wayo kke to dae ga ka ga Aneesah a matsayin taka na har abada idan Allah ya yrda," . Mutuwar tsaye Aneesah tayi daga inda take tsaye, ta kasa ko da kwakkwaran motsi idonta har lkcin na kan Najeeb dake ta faman surutu yana dariya, Abdul ya shigo dakin yana murmushi da fara'arsa ya karaso kusa da Hydar dake binsu da kallo bae ce komai ba, yace "congrat luver guy, ga ka ga Aneesah no more love sickness," Aneesah ta jingina jikin bango ta rumtse idonta cikin tashin hankali, taji kafarta ya kasa daukarta, wayyo ta shiga uku ita kam, bbu wanda ya lura da halin da take ciki kowa da abinda yake cewa, banda Mujaheed dake murmushi kawae, ta bude idonta a hankali ta daura kan Mujaheed dake tsaye gefen gadon, shi din ma kallonta yake yi, suna hada ido ya dauke kansa da sauri, taji wani hawaye mai xafi na bin kuncinta ta girgixa kai tayi hanyar fita daga dakin da sauri, Mujaheed ya bi ta da kallo abun tausayi, Abdul dake kallonsu shima yaji wani iri, suna hada ido da Mujaheed, ya dauke kansa ya karasa kusa da gadon da Hydar yake kwance, ana surutu amma Hydar shiru sae ido da ya xuba masu, da dan damuwa Najeeb yace "A'a wae ya dae ku kira likita naga yaki magana," ganin Hydar yaki ce masu komai sae kallonsu da yake har lkcn yasa Abdul ya karaso kusa da gadon yana kallonsa yace "ya? Kana jin mu kuwa Hydar," Hydar ya sauke ajiyar xuciya yace "ina jinku," snn ya fara kkrin sauka daga kan gadon, Abdul ya rikesa yace "ina kuma xaka," ya dan yatsine fuska yace "4 hw lng nake nn kwance" Najeeb yace "u've been here 4 d past three dayz, sae yau da Aneesah ta xama mallakinka don gulma ka farfado har da ana shirin fita da kai egypt," Hydar yyi shiru yana kallonsa, a hankali cikin wani yanayi me kama da confusion yace "Aneesah" Najeeb yace "yes," Hydar ya dafe kansa na kusan minti biyar snn ya dago yana kallon Mujaheed, Mujaheed bae bari sun hada ido ba, Hydar ya fara kkrin mikewa tsaye ya koma da sauri ta dalilin wani jiri da ya gani, Abdul yace "ya dae," ya koma ya kwanta da ganinsa kasan bae da karfi a hankali yace "baxan iya tashi ba," Mujaheed yace "bari a kira doctor to," ya juya ya fita, Hydar na kallon Najeeb yace "ku gaya min gskya don Allah da gske ne abinda kuke gaya min," Najeeb yace "gskya ne Hydar Aneesah matarka ta sunna ce ynxu," Hydar ya girgixa kai cike da takaici yace "meyasa xakuyi hka, meyasa kuka yi ma Mujaheed hka, bani take so ba shi take so," faruuq yace "Aneesah na sonka dan uwa ka kwantar da hankalinka, hka Allah ya so," Aneesah na fita haraban asibiti taci karo da Hajiya, a rude Hajiya tace "meye kike kuka Aneesah me ya faru kuma" cikin kuka Aneesah tace "wae mumy da gske ya Hydar mijina ne ynxu," Hajiya ta rungumota tace "to meye abun kuka Aneesah ko ba kya son sa ne," cikin kuka ssae tace "ba sona yake ba mumy, don Allah ku taimakeni," da mamaki Hajiya tace "wa yace maki hka Aneesah, ae duk duniya a yanda na lura bbu wanda Hydar yake so bayan ubansa kmr ke," Hajiya ta ja ta suka isa gun mota takira driver ba a jima ba ya xo tace ya kai su gida, har suka isa gida Aneesah bata daina kuka ba, suna fitowa daga mota Aneesah ta tuna lst tym din da ta bar gidan, Hajiyar ta ja ta suka shiga ciki mutanen dake cikin gidan na ta tambayarta ko Aneesah ce amaryar, ta dae yi murmushi tayi masu sannu da gida suka wuce sama da Aneesah ta kai ta dakinta ta xaunar da ita kan gado, ynxu kam Aneesah ta daina kukan da take yi sae na xuciya, Hajiya ta dago kanta tana kallonta tace "kiyi hkuri Aneesah amma don me kika yi tunanin Hydar baya sonki, sbda ke fa ya shiga halin da yake ynxu, shi yace maki baya son ki" Aneesah ta sunkuyar da kanta bata ce komai ba, nn Hajiya ta dinga bata baki tana mata 'yan nasihohi ita dae bata ce komai ba sae hawayen da take, tana dakin hajiya ita kadae bayan sllhn isha tana jujjuya lafiyayyan abincin dake gabanta Wasu mata biyu suka shigo dakin, dayar tace "amaryarmu baki ci abincin bane," Aneesah ta sunkuyar da kanta tace "na ci," matar tace "to sako hijabinki ki fito ana jiranki a waje xaku wuce gida," bata yi musu ba ta sa Hajib ta bi su a baya, ta shiga motar da aka nuna mata, matar ma ta shiga snn driver ya ja motar suka bar gidan, dae dae kofar gidansu drivern ya tsaya suka fito ita da matar suka shiga gidansu, Ammi na xaune daki da wasu 'yan uwanta har uku da makwabta, Aneesah ta fada kan Amminta tana kuka ssae Ammi ta dagota tace "meye hka Aneesah," daya daga makwabtansu ta dagota ta fita da ita daga dakin ta shiga da ita gidanta, ranar Aneesah bata yi baccin kirki ba bayan matar tayi ta mata nasiha ssae game da xamantakewar aure, ita dae jinta kawae take amma ta kasa gaskata wae ynxu ita matar Hydar ce, washegari da safe matar tasa Aneesah ta shirya bayan ta aika yarinyarta ta karbo mata kaya a gida, da kyar ta daure tayi break din da matar ta hada mata, karfe goma saura suka shiga gida gun Ammi har lkcn da mutane cikin gidan nasu, Ammi ta kasa ce ma Aneesah komai sae matan dake dakin ne suka shiga bata baki da yi mata Nasiha, ashe abinda bata sani ba shine ranar xata bar gidansu ta tare gidan mijinta. ~39~ Aneesah ta rasa me ke mata ddi a duniya, ita dae kawae jin abinda ake ce mata take amma bata fahmtar kmai, daga karshe aka dauki sadakinta dubu dari aka mika mata, daga baya xa a kai mta kayan daki dk da hjya tce su bari, ta fashe da kuka tana girgxa kai tana kalln kudin tce ni bana so abn ya ba mutann dake dakin dariya, wata mata tce naki ne wnn Aneesah, Aneesah ta girgixa kai tce na ba Ammina, matan dakin suka yi dariya snn wata tace Ammi dae xata rike maki, amma hakkin ki ne wnn," da kyar Aneesah tabi matar da suka xo jiya da wasu daga 'yan uwan abbanta guda uku suka fita daga gidan tana kuka ssae, duk daurewan Ammi sae da tayi hawaye, gani take kmr ta xalunce Aneesah ta yanke hukunci ita da yan uwanta ba tare da saninta ba, duk da tasan ya cancanci ta ba Hydar Aneesah, don yyi masu abinda 'yan uwansu na jini suka kasa masu a rayuwa, a yanda ta lura kmr Mujaheed take so ba Hydar ba, tausayin 'yar tata ya cikata. Karfe sha biyu suka isa gidansu Hydar, Aneesah ta fito daga mota a sanyaye wata na rike da hannunta suka shiga cikin gidan, mutane ne dayawa cikin falon, hkn yasa matar ta rungumota suka haura sama ta shiga da ita dakin Hajiya, Hajiya ta rungumeta cike da farin ciki ta xaunar da ita kan gado tanai masu sannu da xuwa, mutane nata shigowa ganin amaryar, wata daga kawar Hajiya tace "to Hajiya yaushe ne bikin," Hajiya tace "idan mijin nata yaji sauki ssae" duk suka dinga mata Allah sanya Alkhairi suna yaba kyan Aneesah da kunyarta don takurewa tayi guri daya, karfe biyar saura mutanen dake gidan suka fara raguwa, dakin ya rage daga Aneesah sae wasu mata biyu, aka turo kofan dakin pretty da Ameera suka shigo, Ameera ta sakar ma Aneesah murmushi, pretty kam bata ko kalleta ba ta karaso gabanta tace "sannu amaryarmu," snn ta ajiye farantin dake hannunta, tace "mu je Ameera," Ameera tace "mun gaishe da amaryarmu me kyau sae mun shigo anjima," suka juya suka bar dakin Aneesah ta bisu da kallo a sanyaye, hawayen da take son ji a idonta ma ta neme shi ta rasa, matan dake dakin suka ce ta sauka ta xuba abinci ta ci, bata yi masu musu ba ta xamo kasa daga kan gadon, duk da na daxu ma da aka kawo mata bata cinye ba. Bayan magrib Hajiya tasa ta shirya su kai ma Hydar abinci asibiti, ta shirya cikin wani material mae shegen kyau, ta sa Hajib dinta har kasa, bata yi wani make up ba, driver ya wuce da ita da kanwar Hajiya xuwa asibiti, a sanyaye gabanta na faduwa ta dinga bin matar da taji ake cema Anty farida xuwa ward din da Hydar yake, faridar ta riga ta shiga cikin dakin, ta shigo ita ma da sallamarta murya can kasa kasa, yana kwance amma idonsa biyu, ya rame ssae ba kadan ba, najeeb da wasu abokansa biyu na xaune cikin dakin, suna ganin Aneesah suka fara tsokanarta suna dariya, hkn yasa taji kmr ta fasa ihu ta saka masu kuka, hawaye ya cika idonta amma bata bari kowa ya lura ba,hydar kam dauke kansa yyi bayan ya gaida Anty farida dake ta dariya tana biye masu ta hanyr kare ma Aneesah, su ma bakinsu bae mutu ba su ka dai gama haukansu suka bar dakin suna dariya, Anty farida tace "da ku tsaya mana" sae a snn ta kalle Aneesah dake tsaye tace "A'a amaryarmu baki xauna ba," Aneesah ta kirkiro murmushi ta ja kujera ta xauna, Anty farida ta mike tsaye tace bari xan je siyo kati na dawo, tana fadin hka ta fice dakin ya rage daga Aneesah sae Hydar, ganin sun kai minti kusan biyar a hka yasa ta daure da kyar muryarta na rawa tace "ya jikin," sae da ya dan yi shiru snn taji yace "da sauki," ta daga kai tana kallonsa taga kallonta yake, ta sunkuyar da kanta da sauri tace "in xuba maka abincin?" ya girgixa mata kai yace "aa sae dae in ke xaki ci ki xuba," tayi shiru bata sake cewa komai ba, shima hka, kowa da tunanin da yake yi a xuciyarsa, a hankali taji yace "dan bani ruwan can," ta mike ta dauki ruwan ta bude ta dan dauraye kofin snn ta xuba masa ta karasa kusa da gadon tana mika masa, ganin bae karba ba yasa ta daga kai tana kallonsa ya sauke idonsa da sauri daga kallon da yake mata, ya mika hannu ta sakar masa ruwan ba tare da tasan bae rike ba, ruwan ya fada kansa yyi saurin daga kofin ta shiga goge masa ruwan a rude tana cewa wllh ban sani ba, ya kamo hannunta yana kallonta, wani iri taji daga saman kanta xuwa kasa, ta janye hannunta da sauri, yace "ba komai ba fault dinki bane," ta gyada masa kai ta koma xata xauna yace "plss ki je waje ki karbo min wayana gun Najeeb, xan kira mum xasu kawo min abu," ta juya da sauri ta fice daga dakin, ya dafe kansa da yyi masa nauyi, me yasa ya kasa daina jin haushin Aneesah, da ya tuna abinda pretty ta gaya masa sae yaji wani xaxxabi na neman rufesa, ya koma ya kwanta da sauri tare da lumshe idonsa baya son yana irin tunanin da yake a kanta, Aneesah kam na fita daga nisa ta hango Mujaheed ae kam ba sae an gaya mata ba tasan yanda Mujaheed ke tafiya, ta karaso da saurinta kmr mai shirin fadawa

Chapter 21 of 23