Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gudu tana tsine masa, Hydar ya girgixa kai cike da takaici don yasan xa ayi hkn, ya shiga motar abokinsa suka bi ta a baya. Kuka Aneesah ta dinga yi tana ce ma Mujaheed ya ajiyeta kawae ya tafi, bae ko saurareta ba ya ci gaba da sharara gudu har yyi ma Hajiyar nisa ko hangota baya yi, yyi tsaki yace "Allah ya sauwake," ta madubi ya lura kmr bakaken motar dake bayansa shi suke bi, ya canxa hanya ya ga sun biyosa, bae gama tabbatar da shi suke bi ba sae da yaga wani na neman shan gabansa, ya taka burki da karfi, hkn yasa Aneesah ta fasa ihu don ta xata Hajiyar ce ta riskesu, taga wasu kattin mutane biyar sun fito suna nuna masa bindiga wae ya fito ga layi bbu kowa, Mujaheed ya girgixa kai yace "ya salam," yyi wani irin reverse ya canxa hanya kmr xasu tashi sama, mutanen suka shiga tasu motocin su ma suka bi sa da gudu, tunda take bata taba ganin tashin hankali irin na lkcn ba kuka take tana ihu tana rirrikesa wae ya bude mata motar ta fita, ya rasa da wanne xae ji kuma hkn da take yi xae iya sa ya sake motar su lula wani gun daban hkn ya sa watsa mata mari, ba shiri ta nutsu ta sulale daga kan kujeran, ya dinga sharara gudu suna binsa a baya, har cikin ikon Allah ya samu taxara ssae tsakaninsu shima ta dalilin wata mota ce da xata juya, yaga wani guri da ake parkin mota yyi reverse da sauri ya dawo ya shige tsakanin motocin dake wajen ya kashe motar ya dafe kansa, yana ganinsu suka xo suka wuce da gudu, ya juya yana kallon Aneesah da har lkcn ke kuka, bae ce mata komai ba, ya ji an kwan kwasa motar ya xuge glass, mutumin dake tsaye kan motar yace "biya fa ake malam ba kyauta bane parkin din," ya ciro dubu biyu ya mika masa ya ja motarsa mutumin a tunaninsa gyara parkin din xae yi sae kuma yaga yyi gaba, Mujaheed bae ce ma Aneesah komai ba drivin kawae yake a hankali, yana share xufar dake keto masa da handkerchief wayarsa tayi ring ya duba ya ga Mum dinsa ce. . Ya daga kiran da sallamarsa, maimakon ta amsa kawae sae ta hau sa da bala'i, "prince dama ka komo Nigeria ne don ka dauko ma ni da ubanka magana ko, wacce yarinyar ce kke tare da ynxu, har ynxu halin bnxan nn naka na tare da kai ko, to wllh tun kan raina bai gama baci ba na kamo hanya ko kuma na hada ka da ubanka maxa maxa ka rabu da yarinyar nn, umarni kuma nake baka ba shawara ba, mutumin bnxa kawae" bae ce mata komai ba ya tsura ma titi ido har ta kashe wayarta snn ya juya a hankali yana kallon Aneesah da ta hade kai da gwiwanta, yasan Hajiyar Hydar ce ta kirata, ya tada motar a sanyaye ya bar wajen, yana isa gida yyi horn mai gadi ya bude gate yyi parkin ya fito ya xaga ya bude mata mota yana kallonta bata dago kanta ba bare ta fito, ya dagota yace "Aneesah mai yasa kike tada min hankali ne, ki barni naji da abunda ke gabana mana," bata ce masa komai ba sae kukan da take, hkn yasa ya kamo hannunta ya fito da ita daga motar ya kulle, snn ya ja ta suka shiga gidan, a bude suka tar da gidan, bae yi mamakin hkn ba sanin Hydar nn xae yo dama, suka shiga falon suka tarda shi kwance kan doguwar kujera yana sanye da kananan kaya, lemo a gefensa kan table yana danna wayarsa, ya juya yana kallonsu har suka karaso cikin falon, Mujaheed bae ce masa komai ba ya ja ta suka yi hanyar stairs, ta juya tana kallon Hydar da ya bi su da kallo, har suka haura stairs din, dakinsa ya shiga da ita yace "kallon me kike masa hka?" ta girgixa kai bata ce komai ba, ta xauna kan kujera, ya xauna kan gado yana kallonta tace "yayana su waye mutanen nn," ya kauda kansa yace "mum dinsa ce ta tura mana su na sani," bata sake cewa komai ba ya durkusa gabanta yace "am srry kanwata kinsa na mareki daxu," tayi murmushi bata ce komai ba, ya mike yace "kije kiyi wanka kiyi sllh, i will also do same," bata masa musu ba ta fita daga dakin tayi hanyar dakin da take taje tayi wanka tayi alwala ta fito ta canxa kaya tayi sllh, tana xaune kan darduma ya shigo yace "Hydar kadae a falo, je ki taya sa hira" ta girgixa masa kay bata ce komai ba ya jawo hannunta suka sauka downstairs, yana xaune ya tsura ma TV ido, Mujaheed ya xauna gefensa yace "yau sae kaji daban ko Ali?" Hydar ya dan yi murmushi bae ce komai ba, Aneesah ta xauna kan carpet din tsakiyar falon tana satan kallon Hydar, shi din ma satan kallonta yake suna hada ido ta dauke kanta da sauri, shima ya kauda kansa ya ci gaba da kallonsa, can yace "naga kun dde" Mujaheed yace "ba dole mu dde ba, mun tsallake rijiya da baya ne fa," Hydar yace "me ya faru?" nan Mujaheed ya sanar da shi duk abinda ya faru tun bayan fitarsu kotu, Hydar ya girgixa kai bae ce komai ba don takaicin hali irin ta uwarsa, can yace "to ina Aneesar take kwana ynxu?" Mujaheed yace "nan gidan," Hydar yace "kai fa" Mujaheed yyi masa wani irin kallo snn yace "ina xan kwana da ya wuce nn," Hydar bae sake cewa komai ba ya ci gaba da kallonsa, bayan cylnt na kmr minti goma Mujaheed yace "bari xan je eatry na dawo ynxu Hydar," Hydar yace "ok" ya mike yana kallon Aneesah yace "tashi mu je kanwata," ta dan sace kallon Hydar dake kallonta ta girgixa kai da sauri tace "yayana na gaji, ni tsoro nake ji" Mujaheed ya tsura mata ido yana kallonta, ita ko ta cigaba da kallonta bata bari sun hada ido ba, Hydar yace "ku je mana Aneesah," ta girgixa masa kai bata ce komai ba, Mujaheed ya juya ya fice daga falon, ya shiga motarsa ya fita. Bayan kmr minti biyar Hydar yace "me yasa baki bi sa ba Aneesah," bata ce masa komai ba sae kukan da ta fara yi, ya dawo gabanta ya durkusa yana kallonta yace "kuka kuma Aneesah me ya faru" ta dago kai tana kallon kyakkyawar fuskarsa, ya tsura mata ido yana kallonta, ta sunkuyar da kai da sauri tana ci gaba da kukanta a hankali yace "ya isa hka Aneesah, ko Mujaheed din xaki bi" ta girgixa masa kai, ya xauna yana kallonta snn yace "wen lst kika yi cmmncate da Ammi," ta girgixa masa kai tana hawaye tace "tun ranar da baffa ya daukeni da daddare bayan mun dawo daga shoppn da kai da pretty," Hydar yyi murmushi yace "kar ki damu tunda yana hannu ynxu xae fadi idan ya kai Ammi," ta gyada masa kai kawae, ya sakar mata murmushinsa mai kyau ta sunkuyar da kanta da sauri, duk a takure take xaunawan da yyi kusa da ita sae gyaggyara hijab take, da ya lura da hkn sae ya koma kan kujera ya xauna, sae faman satan kallonsa take, da ya juya sun hada ido sae ta sunkuyar da kai da sauri, ana hka Mujaheed ya dawo, ya ajiye ledojin hannunsa kan dinnin bae ko kallesu ba ya haura sama, ta bi sa da kallo snn ta juya tana kallon Hydar dake kallonta ta kauda kanta da sauri, ganin Mujaheed ya ki saukowa har na kusan minti talatin yasa ta mike ba tare da ta kalli Hydar ba tace "xan je in kwanta, bata jira cewarsa ba ta haye sama, tayi dakin Mujaheed, yana kwance kan gado ya lumshe idonsa, ta xauna gefensa tana kallonsa tace "yayana," . Mujaheed ya bude ido a hankali yana kallonta fuskarsa a daure, a hankali tace "ka gaji ne yayana" ya mike xaune yace "bana ciki da gulma, ki koma inda kika fito, ina ruwanki da gajiya na?" yyi tsaki ya mike tsaye ya fice daga dakin, ta bi sa da kallo da mamaki, bata san lkcn da ta fashe da kuka ba, shi ko downstairs ya sauka, ya dauko ledan abinci ya ajiye gaban Hydar yana kallonsa yace "nasan ka kwan biyu baka ci irin wnn ba frnd," Hydar yyi murmushi bae ce komai ba, Mujaheed ya dauko plate a kitchen ya xuba masu, ya fara cin nasa, Hydar ya sauko daga kan kujera ya dauki spoon yace "Aneesar fa, ita baxa taci bne," batare da Mujaheed ya kallesa ba yana cin abincinsa yace "ae nn na bar ku, ban san inda take ba," Hydar bae sake cewa komai ba ya shiga cin abincin gabansa a hankali, har suka gama bata sauko ba, Hydar ya mike yyi hanyar stairs, Mujaheed ya bi sa da kallo har ya haura, snn yyi tsaki ya mike ya fice xuwa balcony, kwance Hydar ya tar da ita a daki tana kuka, ya karaso kusa da ita ya dafa gadon yace "me ya same ki Aneesah? Kukan me kike yi," ta kasa ce masa komai sae kukan da take ssae, ya xauna gefen gadon yana kallonta, ta mike xaune tana kallonsa tana kukan, ya girgixa kai yace "bana son Hka Aneesah, ki gaya min kukan me kike hka, an maki wani abun ne," ta girgixa kai da kyar cikin kuka tace "ni ban san me nayi ma yayana yake fushi dani ba," Hydar ya tsura mata ido yana kallonta ya kasa cewa komai, can ya kauda kai a hankali yace "to ki tambayesa mana," ta girgixa kai tace "baxae kulani ba," Hydar bae sake ce mata komai ba ya mike ya bar dakin, ta bisa da kallo tana ci gaba da kukanta, balcony ya tarda Mujaheed yace "Aneesah tace bata san me tayi maka kke fushi da ita ba, tana can tana kuka," Mujaheed ya mike a fusace yace "sharri xata min wae ina fushi da ita," ya shiga gidan a fusace, Hydar ya bi sa da kallo, yyi hanyar dakin da take, tana nn yanda take, ya karasa cikin dakin yana kallonta yace "me nayi maki Aneesah kke kuka?" bata ce masa komai ba ya xauna gefenta ya dago kanta yana kallonta, yyi murmushi yace "to yi hkuri kanwata ni banyi fushi dake ba," ta girgixa kai ta fada kansa cikin kuka tace "Allah fushi kke dani yayana," ya rungumeta yace "A'a kanwata ni banyi fushi da ke ba," dai dai nn Hydar ya shigo dakin yana kallonsu, kasa karasowa cikin dakin yyi ya dauke kansa da sauri, Aneesah ta fara kkrin free din kanta daga rungumar da Mujaheed yyi mata, ya sake ta ya dago kanta yana goge mata fuska yace "kaga Hydar na lallashe ta," Hydar ya gyada masa kai kawae da kyar ya fita daga dakin, tare suka sauko kasa, Hydar na xaune ya jingina kansa kan kujera, Mujaheed ya dauko mata abincinta yace "maxa ki ci abinci kanwata nasan kina jin yunwa," ta jawo abincin a sanyaye tana kallon Hydar tace "ya Hydar kaci," kai kawae ya gyada mata, snn yace "Mujaheed ka ban makullin mota, xan fita ne," Mujaheed yace "ka je ina? Ae kai da fita sae bayan kwana biyu, Hajiya kadae ma ta isheka ynxu," ya girgixa kai yace "ba gida xani ba," Aneesah ta marairaice tace "ya Hydar kar ka tafi don Allah, bana son a sake kama ka," bae ce mata komai ba Mujaheed yace "to kaji dae," shi dae bae ce masu komai ba idonsa na sama, aka ring din bell din gidan, gaba daya suka juya suna kallon kofar, Mujaheed ya mike ya isa bakin kofar yana leka ta glass yaga ko waye, ya bude kofar yana murmushi yace "bbyn yayanta," ko kallonsa bata yi ba ta shigo falon ta taho da gudu ta fada kan yayanta ya rungumeta yace "prettyna daga ina hka," tana murmushi tace "daga gida mana yayana, nayi missin dinka ssae," yace "nima nayi missin dinki kanwata," Aneesah tayi murmushi tace "pretty ranar ko sallama bbu kika wuce ko," ko kallonta pretty bata yi ba, ta shiga bude ma yayanta abinda ta kawo masa a leda, jikin Aneesah yyi sanyi ta juya tana kallon Mujaheed dake danna wayarsa, fura mai sanyi ta kawo ma yayanta, da kanta ta dauko cup a kitchen ta xuba masa ya karba yana murmushi yace "ngd kanwata," ya juya yana kallon Aneesah yace "xo ki diba fura," pretty tace "bae fa da yawa yaya" Aneesah tace "aa nama koshi," Mujaheed ya kalli prettyn yace "yayanki kawae kika sani a nn ko Zainab," ko kallonsa bata yi ba bare ta tanka masa, tace "yaya don Allah ka wuce kaduna ko xuwa anjima, sbda mummy, ~29~ Hydar xae yi magana Mujaheed ya mike yana kallonta yace "tashi ki fita," ta watsa masa harara tace "bbu inda xanje," Hydar yace "bana son rashin kunya pretty ban san ki da hka ba," bata ce komai ba ta xauna gefensa tace "kaji yaya, bna son kana saka kanka cikin matsala a bnxa a hofi, dubi fa yanda mumy da Abbansu Najeeb ke fushi da kai," Hydar yace "naji Zainab, xo ki wuce gida kar maghrib yyi," bata yi masa musu ba ta mike tace "to yaya xan tafi, sae na dawo kuma," tana kai wa nn ta juya tana kallon Mujaheed tace "sae anjima ya Mujaheed," yyi bnxa da ita tayi gaba abunta, Hydar ya mike ya bi ta, har suka fita snn yace "me yasa kika ma Aneesah hka Zainab," tace "ni me nayi mata yaya, kawae fa gaskya na fada, Allah furan bai da yawa," Hydar yace "ki wuce gida direct," tace "to yaya," ta daga masa hannu ta fita daga gidan, bae tarar da kowa a falon da ya shiga ba, ya xauna kan kujera ya dafe kansa, yana nn a hka shi daya a falon har lkcn sllh ya kusa ya mike da kyar ya haura sama ya shiga dakin Mujaheed, yana xaune kan kujera ita ko tana xaune gefensa a kasa suna kallon wani American film, Hydar na shigowa ta dan matsa da sauri daga kusa da Mujaheed, shi ko yace "har ka gama hutawan," Hydar bai tanka masa ba ya shiga bathroom, Aneesah ta mike tana kallon Mujaheed tace "xan je nayi alwala," ya gyada mata kai ta fice. Tare suka fita masallaci da Mujaheed, suna dawowa gida kuma Mujaheed ya koma siyo masu abinci, Hydar na xaune falo ta sauko downstairs tana kallonsa tace "ya Hydar kun dawo," yyi mata shiru bae ce mata komai ba, hkn yasa ta juya xata koma sama ya mike tsaye ya kirata ta juya tana kallonsa ta kasa karasawa, ya karasa gabanta yana kallonta a nutse yace "ina tarbiyar da Ammi ta maki Aneesah, ina kika ajiye "ni ba 'yar iska bace," da kike yawan gaya min a baya, don baki tare da Ammi sae ki watsar da tarbiyan da ta maki ki maida kanki jahila, wawiya, kmr baki taba karatun addini ba," ta girgixa kai a tsorace tace "me nayi ya Hydar," ya watsa mata mari yace "tambayeta kike me kika yi," ta tsorata ssae ta koma baya ta fashe da kuka, ya fixgota a fusace yace "ki bani amsa ta," cikin kuka tace "wayyo kayi hkuri ni ban san me," bae bari ta karasa ba ya kai mata wani marin. . Aneesah ta fashe da kuka a rude dafe da kuncinta tana kallonsa ta durkushe wajen, ya durkusa shima yana kallonta a nutse, fuskarsa daure yace "Mujaheed Muharraminki ne?" ta girgixa kai a tsorace tana kuka, ya daura yatsunsa biyu kan bakinsa alamar tayi shiru, ba shiri ta hadiye kukan sae hawayen da take yi, ya kauda kansa da sauri idonsa ya kada yyi jajur, hkn yasa ta shiga komawa baya a hankali tana hawaye, ya juyo yana kallonta a raunane murya can ciki yace "ban san xaki iya ajiye tarbiyarki mai kyau aside ba ki dauko wani daban Aneesah, ban san ke wawiya bace sae ynxu, kin ban mamaki Aneesah, ke ma ynxu kin xama 'yar iskar da kike yawan ambatar min ke ba ita bace a baya, Why Aneesah, don baki tare da Mahaifiyarki? Kin mata adalci knn " ta fashe da matsanancin kuka tana girgixa masa kai muryarta na rawa tace "wllh ya Hydar ni ba 'yar iska...." ya daka mata tsawa ya dakatar da ita, tayi tsit tana shesshekar kuka tana girgixa masa kai, ya mike a sanyaye ya hau sama, ta bi sa da kallo ta kife kanta a gun tana kuka ssae, a hka Mujaheed ya dawo ya sameta, ya durkushe gabanta da sauri bayan ya ajiye ledojin hannunsa yace "Aneesah me ya faru?" bata dago ba bare yyi tunanin samun amsa, duk ya rikice mata ya dinga tambayarta mae ya faru, me ya sameta, amma taki dagowa sae kukan da take kmr ranta xae ita, ya dagota yace "haba Aneesah tok 2 me don Allah, me aka maki," ta turasa da karfi ta fashe da wani sabon kukan tana komawa baya tace "kar ka taba ni," ya tsaya kallonta da mamaki, ya matso kusa da ita ta mike tsaye da sauri cikin kuka tace "ni ka rabu dani don Allah," yyi shiru yana kallonta, ta koma jikin kujera ta sulale ta hade kanta da gwiwa tana ci gaba da rera kukanta abun tausayi, bae sake ce mata komai ba yyi hanyar stairs a sanyaye, kuka kam ta yi shi ranan har ta gode Allah, tana xaune kusan karfe goma ita daya har lkcn a falo ta yi tagumi don hawayen ma har ya gaji yaki fitowa, Hydar ya sauko bae ko kalleta ba ya shiga kitchen ya hado tea ya dawo falo ya xauna yana sha yana kallon News, Mujaheed ma ya sauko yana kallon Aneesah da ta sunkuyar da kanta, ya karaso cikin falon ya dauko ledan da ya shigo da daxu, ya bude ya ciro mata abincin ya durkusa gabanta yana kallonta a hankali yace "kanwata ki ci abinci kije kiyi sllh ki kwanta," ta koma baya da sauri ta fashe da wani kukan muryarta a dashe tace "ni ka kyaleni nace maka" ya tsaya yana kallonta da mugun mamaki, ya juya yana kallon Hydar da idonsa ke kan T.V, ya mike a fusace ya karasa kusa dashi ya cakumesa cikin tsawa yace "me ka yi ma Aneesah? ka gaya min me kayi mata" Hydar ya mike tsaye yana kallon Mujaheed din a nutse yace "free me,", idan banyi ba fa? Mujaheed ya tambayesa yana huci, Aneesah ta mike tsaye jiki ba kwari tana hawaye tayi hanyar stairs. Mujaheed ya sake Hydar din yana masa wani irin kallo, Hydar yyi hanyar stairs ya shige daki, Mujaheed ya xube kan kujera ya dafe kansa, ranar dae a falo ya kwana ido biyu, ita kanta Aneesah bata yi bacci ba sae kusan asuba, Hydar ma da yaga baccin ya kaurace masa sllh yyi har kusan 3 snn ya kwanta. Washegari da kyar Aneesah ta tashi ta iya yin sllh, tana kwance dakin har kusan goma na safe har wani jiri take gani don yunwa, ganin ba sarki sae Allah ne yasa ta mike da kyar ta sauko downstairs suna xaune, Hydar na danna laptop Mujaheed na gefensa xaune idonsa kan na'urar shi ma, duk da gaba dayansu fuskarsu bbu wani annuri, ta kauda kai da sauri ganin duk sun dago ido, tayi hanyar kitchen a sanyaye tana shiga ta sulale kasa, ta kai minti biyar a hka, ta ga bbu abinda xata iya yi a kitchen din hkn yasa ta bar kitchen din ba tare da ta kallesu ba ta haye stairs ta koma daki, kuka ta fashe da ssae tana tausayin rayuwarta ba Amminta, bbu abinda xae sa ta sake kwana gidan nn gwara kawae ta je duk inda Allah xae kai ta, tana kwance a hka har kusan sha daya taji an danna kararrawan downstairs, hkn yasa ta tuna abinda pretty tayi mata jiya hawaye mai xafi ya sulalo mata, tasan ita ce, bayan kmr minti biyar aka budo kofar dakinta ta daga kai da sauri taga ko waye, Mujaheed ne, ya karaso cikin dakin yana kallonta yace "hurry up, ki sa hijab dinki ina jiranki," ya fita da sauri ta bi shi da kallo, can sae gashi ya dawo rike da makullun mota cikin fushi yace "wae bakya ji ne," a hankali tace "ni bbu inda xani," ya karaso cikin dakin ya fixgota ya dauki Hijab dinta ya ja ta suka fice daga dakin tana kuka, tsaye taga Hydar a bakin kofa, yana kallon stairs alamar jiran ganinsu kawae yake, sae a lkcn ta lura cewa har lkcn ana danna bell din gidan dis tym around ba kakkautawa, tana kuka Mujaheed ya ja ta suka shiga kitchen ya bude kofar kitchen din suka fita ta baya, Hydar na jin rufewar kofar kitchen din ya bude kofar falon. . . Mujaheed yyi ma Hajiyar bayanin halin da Aneesah take ciki bayan sun gama waya da Mudatheer, snn ya fadi mata alfarmar da yake son tayi masa na cewar Aneesah ta xauna gidan har xuwa lkcn da Amminta xata bayyana, Hajiyar tace "bbu komai Mujaheed, tayi xamanta a nn, meye a ciki, kawae dae Allah ya shiga tsakanin mugu da na gari," Mujaheed yace "Amin mum, ngd ssae," tayi murmushi tace "meye abun gdya Mujaheed, Allah dae ya kyauta" nn suka dinga hira har Mudatheer ya shigo gidan, ya xauna yana murmushi bayan ya gaida Hajiyarsa da ta mike ta basu waje, yana kallon Mujaheed yace "ya dae fada, daga ina hka, yau ka tuno da son dinka knn," Mujaheed yyi dariya yace "ba dolena ba, yah ka fara aiki ne?" Mudatheer ya daga kafada yace "nn da sati biyu, dad ya samar min a wani company assistant Director," Mujaheed yace "waow congrat, Allah ya taimaka," Mudatheer yace "Amin," dae dae nn ummi da Aneesah suka sauko, baka taba tunanin Aneesah na cikin wani abu wae shi damuwa don lebbenta dauke yake da murmushi, sanye take cikin kayan ummi da lkci daya suka saba kmr da can sun taba sanin juna, Aneesah ta wara ido tana kallon Mudatheer tace "lah dan kauye ashe ka dawo," yyi dariya da mamakin ganinta, shima yana kallonta yace " kai! Ashe tare kuke da 'yar birnin nn Mujaheed," Mujaheed ya kirkiro murmushi bae dae ce komai ba, Aneesah ta xauna tana kallon mudatheer tace "ashe dae ka iya sa kaya, shine a kauye kke shiri kmr dan kauye," ummi ta dinga dariya tana kallon yayan nata da ya kasa cewa komai sae murmushi yake yana kallon Aneesah, can yace "ke ko!! ya kika baro su mama shatu," Aneesah ta rufe fuskarta tana 'yar dariya tace "kai ya ka baro su," shima dariyar yyi Mujaheed ya mike yana kallon mudatheer yace "kayi min sallama da mum, xan koma ne," mudatheer yace "a haba dae har xaku koma, yaushe kuka xo," da sauri Aneesah tace "A'a ni nn xan xauna, da ummi," Mujaheed ya juya ya mata wani mugun harara, ummi tace "uncle ka bar ta nn ta xauna mana, tace xata xauna nn har lkcn da Amminta xata dawo," Mujaheed ya kirkiro murmushi bae ce komai ba, Mudatheer ya tafi kiran Hajiyarsu, ta shigo falon tace "har xaka koma Mujaheed," yace "eh mum da inda xanje ne wllh," tace "ko abinci baxa ka ci ba" ya girgixa kai yana murmushi yace "sae dae wani lkcn mum, ynxu sauri nake," tace "to shknn Mujaheed, Allah ya kiyaye," yace "Amin ya mike tsaye yana kallon Aneesah," bata ko kalli inda yake ba, Mudatheer ya kalleta yace "to 'yar birni sae ki tashi ko nn xaki xauna," tace "A'a a nn ni xan tsaya da ummi," ya juya yana kallon Mujaheed da har ya kusa bakin kofa, xae yi magana Hajiyar tace "to fateema ki je kuyi sallama da yayan naki mana," a kunyace ta mike ta bi bayansu, Mujaheed bae ko kalleta ba ya shige motarsa Mudatheer na yi masa sallama, ta dan tabe baki, ta juya ta koma cikin gidan abun ta. Mudatheer yyi murmushi, Mujaheed ko yyi horn ya ja motarsa ya fita daga gidan, throughout ranar Aneesah na dakin mumynsu ummi, ji take kmr Amminta ce, ta mance duk wani damuwa dake xuciyarta, gashi matar tana da kirki ssae, duk kyanta 'ya yanta uku suka biyo barin Mudatheer, Mudatheer ne babba sae kanwarsa dake aure a kaduna, snn autansu Ummi, da yamma tare Aneesah suka yi girki da ummi, tana daki da daddare ita da ummi suna lbri, Hajiya ta shigo tace "suje su gaida Abba ya dawo," suka sauko xuwa falonsa yana xaune yana kallon News, yace "A'a yau bakuwa mukayi a gidan," Aneesah tayi murmushi ta gaida sa, ya amsa da fara'arsa yana jansu da wasa ita da ummi, sae a snn taji ashe uba ma na da ddi a rayuwa don bata taso ta ga nata ba, don hka bata taba experiance din son uba ba da carin dinsa, nn ya sallamesu yace suje su kwanta xae kalli news, suka masa sae da safe suka bar falon nasa. Mujaheed na koma wa gida ya tar da Hajiyarsa ta dawo da kanninsa biyu, sae yaji shakkar karasawa falon ganin yanda mahaifiyartasa ta hade rae ssae. Ya fita balcony ya kira Hydar yace "guy, meyasa baka gaya min su Mum sun dawo ba," Hydar yace "shima bae sani ba, mujaheed ya tambayesa yana ina, Hydar yace ina gidansu Najeeb sae mun yi waya, yana kai wa nn ya kashe wayar daga jin yanda yake wayan ransa a bace yake, Mujaheed ya shiga falon ba tare da ya kalle mahaifiyartasa ba yyi mata sannu da xuwa xae haura sama ta daka masa tsawa tace ya dawo ~30~ Hajiyar ta mike tsaye tana kallon Mujaheed da ya tsaya dai dai kusa da stairs yana jiran cewar Mahaifiyartasa, ta karaso har gabansa tace "daga ina kke Mujaheed?" ba kasafae Hajiyar ke kiran sunansa ba sae dae tace prince, hkn ya nuna masa lallai tayi fushi da shi ssae, ya dan yi shiru snn yace "daga office nake," tayi masa wani mugun kallo tace "ubanka xaka raina ma hankali ko?" bae ce mata komai ba sae kallonta da yake yi, a nutse ta fara magana tana kallonsa da kyau tace "wllh wllh ka sake sa hannunka cikin case din yarinyar nn ko kuma ka sake xuwa gunta Allah ya isa ban yafe maka ba Mujaheed, kuma ka wuce ka hada kayanka nn da kwana biyu ka bar country din gaba daya dad dinka yace kaje ka samesa, ni dama shi yasa bana son kana hulda da wnn mai taurin kan Aliyu da bae maida mahaifiyarsa komai ba, don influence din min kai yake kai ma ka gagaremu kmr yanda ya gagare uwarsa," Tunda ta fara magana Mujaheed ya jingina jikin stairs ya lumshe idonsa har ta kai aya snn ya bude idon da kyar yana kallonta yace "mum, wllh marainiyace yarinyar ku tausaya mata......" ta daka masa tsawa a fusace "bace ka ban waje kar ka dada bata min rae," bae ce mata komai ba ya haura stairs din, yana bala'in respectn iyayensa yana gudun bacin ransu barin mum dinsa, bambancinsa da Hydar knn, don shi ba ruwansa inda ya sa kansa nn yake dosa bbu wanda ya isa ya hanasa. Hydar kam bae ko kalli Mahaifiyarsa dake ta masifa tun bayan

Chapter 16 of 23