Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
yana kallon cikin idonta yace "to bude baki na sa maki plantain sai ki wuce," ta fara waige-waige a tsorace tana kkrin barin jikin fridge din don dab da ita yake har tana iya jin breathin dinsa a fuskarta, yyi saurin sa hannu ya tokare hanyar da xata bi, ta marairaice murya kmr xata yi kuka tace "A'a ni na koshi," yace "ashe dae baxa ki bar nn ba yarinya," ganin da gske yake yasa ta bude bakin a hankali yana kallon kwayar idonta ya saka mata plantain din a baki, ta shiga taunawa a hankali yana mata wani irin kallo, ya matsar da ita daga jikin fridge din, ta fixge hannunta da sauri xata bar wajen, ya maxa ya rikota yace "baki isa ba tukun," ya na rike da ita ya bude fridge din ya dauko chill hollandia yoghurt, snn ya maidota jikin fridge din ya jinginar, ya bude drink din ya xuba cikin glass cup, ya kai mata baki, ta kauda kai da sauri ya hade rai yace "Allah baxa ki bar nn ba idan baki sha ba" kuka ta dinga yi tana rokansa ya kyaleta ta wuce, amma yaki sakinta wae sae ta sha hollandian, ganin ba sarki sae Allah ne yasa ta bude bakin a hankali ya shiga bata drink din tana sha, muryar Hajiya suka ji daga sama tana cewa " wae Aliyu ya fita ne meenah," a tsorace Aneesah ta turasa ta durkushewa wajen tace "nashiga uku na lalace," shi kuma yyi saurin juyawa ya koma dinnin ya xauna, dae-dae nn Hajiyar ta karasa saukowa da meenah, idonta ya sauka kan Aneesah da har lkcn ta kasa mikewa tsaye daga wajen, cikin tsawa tace "ita kuma warcan me take min jikin fridge hka," Haydar yyi saurin cewa "No ni nace ta bude ta kawo min drink, tace "Ayyo" snn ta karaso dinning din ta xauna tana cewa "har yanxu baka gama cin abincin ba son," Aneesah ta dauko hollandian da ya ajiye mata gabanta duk ta rude tama rasa abun yi ta hado da cup din ta dan risina ta ajiye masa gabansa kan dinin table din ya kashe mata ido ya bita da kallo ta bar wajen da sauri har tana tuntube. Ranar cikin rashin kuzari ta isa gida ta xube kan katifa, Ammi ta tambayeta lfya, tace kawae kanta ne ke ciwo, Ammi ta bata magani bayan ta sa ta gaba taci tuwon da tayi masu, snn taje tayi wanka tayi sallah ta koya ma yusuf assignment dinsa, ta danyi karatun qura'ani har karfe takwas, snn tayi sallahn isha tayi ma Ammi sae da safe ta kwanta duk da ba bacci take ji ba, kawae abun duniya ne ya isheta, ita kam duk aikin ma ya gama sare mata xuwan Haiydar, su dinga dabi'a irin ta nasara kmr wa inda basu da ilimin addini, ita a al'adarsu ta hausa fulani bata ga namiji na taba macen da ba muharramarsa bace, gskya ta kara tabbatar da cewar gidan nn basu da tarbiya, in Allah ya yarda aikinta ya kusan xuwa karshe a gidan, xata sa Ammi ta samo mata wani wajen daban da xata dinga aiki, baxata je ya cuceta a bnxa ba don bae mata kama da mai kamun kai ba. Hka Aneesah ta dinga aiki a takure a gidan, don Hydar duk ya bi ya sa ta gaba, indae yana gidan to bata da kwanciyar hankali don kawae sae dai taji mutum tsaye a bayanta, in tana garden to shima yana can, shi dae kawae so yake yaji lbrinta wae bata yi kama da 'yar aiki ba, kuma yasan tana da ilimi both, sau dayawa ya kan mata turanci don ta maida masa, amma ko sau daya bata taba mayar masa ba, sae dae ma tayi kmr bata ji mai yace ba, da ya kawo mata xancen yana son sanin ko ita wacece sae tace masa ba matsalarsa bace wnn, in kuma ta tashi serve dinsa abinci to sae ya tilasta mata ta ci abincin da ta xuba mashi, duk ya bi ya tsorata ta a gidan kuma duk wnn abun da suke ko sau daya Hajiya bata taba lura ba, hka ma yan matan gaba daya, yau ma kmr kullum tana xaune garden tayi xurfi cikin tunaninta bayan ta gama duk aikin da xata yi a gidan, ita kam kila yau ce rana ta karshe da xata kara aiki a gidan, don bata ga dalilin da Haiydar xae takura mata a kan sae yasan ko ita wacece ba, ga abun Hajiya sae gaba yake karawa ta rasa abinda tayi masu ba ita ba ba 'ya yanta ba, in ta tashi tafiya yau kawae ce mata xatayi ta bar aiki, ta gaya mata ranar da xata xo ta karbi kudun aikinta na rabin watan da tayi, idan kuma tace baxata bata ba, shkkn ta bar masu, tayi tagumi tana kallon tsuntsaye tana tunanin ko shawarar da ta yanke yyi taji hannun mutum a wuyanta, ta juya a fusace ta dan matsa cikin fada ta fara magana "wae meye hka malam, bana son iskanci ka rabu dani nasha gaya mka ni ba 'yar iska bace," ta mike ta shige kitchen ya bi ta da kallo, ko da ta shiga gidan ta tarar su Hajiya sunyi shiri xasu fita, tana cikin goge masu takalman da xasu sa ya shigo falon, fuskarsa a daure ya xauna kan kujera Hajiya ta shiga tambayarsa me yafaru bai tanka mata ba, tace "xamu fita son amma ni ba dde wa xanyi ba ynxu xan dawo," ya gyada mata kai kawae yana kallon Aneesah da gabanta ya shiga bugu da sauri, suna fita kuwa ita ma xata bar gidan tana gani, ya hade rai yace "ya ma kike da suna" ta juya tana kallonsa tace "Ni," hajiya ta haureta tace "to da uwarki ce idan ba ke ba" a hankali tana hawaye tace "Aneesah," yace "gud, bedroom dina xaki gyara min idan kin sallamesu,". . Aneesah ta dago a hankali tana kallonsa hawaye na bin kuncinta, shima ya tsura mata manyan idonsa, Hajiya tace "idan kinga dama kina gama gyaran bedroom din ki girka mana fried rice da cream salad sae farfesun naman rago da coconut drink, kuma kiyi dayawa don xan yi baki daga lagos anjima, muryarta a dashe tace "to Hajiya," su meenah dama tuni suka fita suna jiran Hajiya a mota, Hajiya ta juya tana kallon pretty dake kwance gefen yayanta tace "ke baxaki je bne bby," ta dan yatsine fuska tace "na fasa xuwa momy xan taya yayana hira," Haiydar yyi saurin cewa "A'a nima fita xanyi, tashi kawae ki bisu," ta xumburo baki tace "to ba sae mu fita tare ba," ya galla mata harara yace "nace ki tashi ki bisu don bbu inda xan kai ki," gaban Aneesah dake durkushe bayan ta gama goge ma Hajiya takalmanta ya shiga bugu da sauri, lallai suna fita kuwa ita ma xata bisu a baya don bbu abinda xae kai ta dakinsa, dama yau ai take son ajiye aikin, Hajiya ta bude baki tana kallonta bayan ta gama sa takalminta cikin tsawa tace "wae kina nn xaune ne har ynxu wnn dabbar yarinyar," ta mike tsaye da sauri jikinta a mace tayi hanyar kitchen, ta sake mata wani uban tsawan tace "gidan ubanwa xaki," a tsorace tace "girkin xan daura," ta fixgota a fusace ta kai mata mari tace "don uwarki kin gyara masa bedroom din ne," cikin kuka tace "A'a ynxu xan gyara," Hajiyar ta wurgar da ita hanyar stairs tace "kuma ki bari na dawo naga bbu girkin da na saki wllh sae na kusan sumar dake yau tunda kince ke bakya jin magana," duk wnn abun da suke Haiydar na kallonsu bai ce komai ba, tana kuka ta hau stairs din tayi hanyar bedroom dinsa da kyar don har wani jiri take gani don tashin hnkli, tana shiga bedroom din ta ga ko ina a gyare, TV na aiki hka ma A.c dakin sae kamshi yake, sae laptop dinsa da files dake kwance kan gadon, tun bayan ranar da xae dawo da ta gyara masa daki bata sake shigowa dakin ba sae yau, kullum da safe pretty ce ke gyara masa daki don yarinyar na bala'in son yayanta, Aneesah ta goge hawayen da ya kasa tsaya mata, tasan ba alkhairi yake nufi da ita ba, tana jin budewar gate alamar su Hajiya sun shiga mota xasu fita ta juya da sauri ta yi hanyar kofar dakin don dama hka take jiran ji kafin ta fita daga dakin daga nn kuma ta bar gidan ma gaba daya, tana isa bakin kofa ya riga ta bude kofar ya shigo dakin, ta fasa ihu a tsorace ta koma baya tana xaro ido, bae juyo ya kalleta ba har sae da ya kulle kofar dakin, ta fashe da kuka tana komawa baya murya a raunane ta fara magana, "don Allah don Annabi don darajar iyayenka ka tausaya ma rayuwata ka rufa min asiri wllh ni marainiyace, ka taimake rayuwata ka ceceni ka kyaleni, nayi maku alkawarin xan bar maku gidanku plss am beggin" tana magana ne tana kuka sosai tana komawa baya shi ko binta kawae yake har ta isa jikin bangon dakin ta sulale kasa ta sa hannu ta rufe fuskarta jikinta na rawa tana ci gaba da rusa kukanta, ya durkusa gabanta yana kallonta snn yace "idan kin gama kukan, tashi ki xauna nn magana xa muyi," ta dago kanta a tsorace tana kallonsa ya nuna mata kan gado, ta girgixa masa kai ta kasa cewa komai, hkn yasa ya koma kan gadon ya xauna, ya danyi shiru na wani lkci snn yace "idan kika bani hadin kai nasan ko ke wacece ba ddewa xakiyi a dakina ba, don hka kiyi save din tym dinki duk tambayar da nayi maki ki bni amsa, kuma ki bar tsorona ni bbu abinda xan maki, ko da me kike tunanin xan maki??" tayi shiru kanta na kasa sae hawayen da take yi, ya mike tsaye ya dago ta ya xaunar kan gadon ya ciro handkerchief ya goge mata hawayen fuskarta yana kallonta yace "tell me about yhur sef, am ol ears," tayi shiru taki cewa komai har sae da yace "kin yi shiru kanwata," ta dago a raunane tana kallonsa a hankali tace "to me xance," yace "to ya sunanki," ta sunkuyar da kai tace Aneesah mukhtar, yace "i mean yhur real name," ta dan yi shiru snn tace "fateemah Muktar," yyi murmushi yace "nyc name, momyna knn, but y re yhu nt in sch, kuma parent dinki fa?" @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 NA KHALEESAT HAYDAR 6&7 ~6~ Aneesah tayi shiru tana kallonsa ta kasa cewa komai, ya gyada mata kai yace "am ol ears," ta sunkuyar da kanta a hankali tace "Abbana ya rasu, Ammi ta ce kawae sae kanina yusuf" sae ga wani sabon hawayen tana yi, ya girgixa mata kai yace "a'a bance kiyi min kuka ba Aneesah," ya sa handkerchief ya goge mata fuskar snn yace "go on momyna" ta sunkuyar da kanta a hankali ta fara basa lbrin rayuwarsu tun daga rasuwar abbanta har ixuwa ynxu da yake xaune kusa da ita, tayi kuka sosai kmr ranta xae fita, ya xuba mata ido yana kallonta ya kasa cewa komai, ta goge fuskarta ta mike xata bar dakin ya kamo hannunta ya maido da ita ya xaunar, a hankali cikin nutsuwa ya fara magana "shi baffan naku a wani anguwan yake, snn relatives dinku mae suka ce dangane da abinda yyi, kuma wish din Abbanku knn ya rike maku gadon ku har ku mallaki hankalinku ko tsarinsa ne, snn me abokanan abbanku suka ce game da hkn, Abbanku na da lauya ko bae da??" Aneesah tayi murmushin da bata shirya ba xata yi magana suka ji muryar Hajiya downstairs, ta mike a tsorace tana kallon agogo, karfe uku har ya wuce, tace "nashiga uku na lalace," ya mike da sauri ya koma kan kujera yace ta cire bedshit din, jikinta na rawa ta cire bedshit din, dae-dae nn Hajiyar ta shigo dakin tana kallonta da mamaki cikin tsawa tace "ynxu shegiyar yarinyar nn baki girka abinda nace maki ba, gyaran dakin ne tun daxu," Aneesah ta fara kame kame a tsorace xata yi magana Aliyu ya riga ta "A'a aikenta nayi mum, bata dde da shigowa ba nace ta wanke min bathroom kafin ta gyara dakin," Hajiyar tace "Ayyo," snn ta galla mata harara ta ja kujera ta xauna tana kallon Haiydar din da damuwa tace "wae son ya maganar companies din Abbanku na lagos ne, kasan fa mutane basu da tsoran Allah tun da mahaifinku ya rasu Haiydar sau biyu ka waiwaye lagos," cikin fada ya fara mgana yana kallonta "to wae mum so kuke na kasa kai na ne, meye hadin barrister da wani bussiness can, ni ynxu cases din dake gabana ma sun fi karfina, su Amina da sumayya uban me suke yi ba abinda suka karanta ba knn, sun gwammace su yi ta gantali a garin Abuja," ya jawo laptop dinsa ya kunna ba tare da ya kara kallonta ba, tace "to kayi hkuri kuma fa gskya ne," Aneesah ta gama gyara gadon ta fita ta bar masu dakin tayi hanyar kitchen daura girkin da aka sa ta. Karfe shidda ta dauki hijab dinta tasa xata tafi gida, ta durkusa gaban Hajiya gabanta na faduwa ta dai yi shahada tace "Hajiya ina son ajiye aiki daga yau, idan yaso sae ki gaya min randa xan xo karban kudi na na rabin watan da nayi aiki," Hajiyar ta shiga mata wani irin kallo snn tace "gidan uban wa xaki da xaki ajiye aiki," ta girgixa kai a hankali tace "ba inda xani," cikin tsawa Hajiyar tace "baki isa ba to muguwa, a gidan uwarki ake hka, kinsan xaki tafi tun da can baki gaya min ba na samo wata sae ynxu da rana tsaka, kuma wllh baki karasa min aikin wnn watan gaba daya ba baxan baki kudin rabin watan ba, snn sae kin tsaya har an samo min wata yar aikin idan ba hka ba in na maki Allah ya isa sae ya biki wllh, tunda ban san ubanda xai dinga min aiki ba idan kika tafi bbu wata," a hankali tace "to xan jira ki samo wata 'yar aikin," Hajiyar tace "oho dae ya rage naki muguwa kawae" jikinta a sanyaye ta fita daga gidan, ta tarda Haiydar bakin gate a waje yana tsaye da alamar ita yake jira, ya karaso kusa da ita yace "lemme drop yhu," ta hade rai tace "A'a ngd" ya harareta yace "baki isa ba," tace "Allah bana so" bata sake jiran me xe ce ba ta kama hanyar gida da sauri da sauri. Tana isa gida tayi wanka tayi sallah ita da Amminta da yusuf, suna cikin cin abinci karfe kusan bakwae da rabi, suka ji ana bubbuga kofa daga can waje kmr xa a balla, duk suka yi tsit suna kallon bakin kofar dakin, aka shigo gidan aka banko kofar dakin, baffa shehu ne, ya tsaya yana hura hanci yace "ikon Allah, na sami lbrin abin kunyan da kuke yi a gari ke da tsinanniyar 'yar ki maryam, ynxu sbda tsabar butulci irin naku da rashin godiyar Allah duk abinda nake maku sae kin tura yarinyar nn karuwanci," Ammi tace "karuwanci kuma yaya, to Allah ya saka mana," cikin tsawa yace "sharri nai maki munafuka, idan ba shi kuke yi ba ubanwa ke ciyar daku tunda ni dae na fi wata uku bnga kun xo gu na maula ba, kuma a gari naji wnn xancen ana ta yayada wa, kuma gashi na xo na gani da idona wae kune da cin shinkafa da miya da nama yau," Aneesah dae abincin ta kawae take ci, Ammi ta goge hawayen dake xubo mata tace "in'sha Allahu sae Allah yyi mana shari'a daku ranar gobe kiyama," haba kamar kar ta fadi hka baffa ya dinga bala'i yana yo wa kanta kmr xae mareta, ita dae kanta sunkuye yake tana hawaye, hka ma Aneesah da ta kasa daure wa ta fashe da kuka, kmr daga sama suka ga an wullo torch light ya kwalesa da karfi a ka, ya dafe wajen yana salati a gigice, yusuf ne ya jefesa yana huci yace "xan fasa maka kai na cire maka hakori idan ka sake sa Ammina da Antyna kuka," ya karasa bakin kofar da gudu ya rufe masa kofar da karfi a fuskarsa. . Ammi ta mike da sauri ta fixgo yusuf tayi masa rankwashi cikin fada tace "kana da hankali kuwa xaka jefi babanka," yusuf yace "eh, kuma idan na girma ma dukan tsiya xan mashi wnn ba babana bne," Aneesah tayi saurin kamo shi kar Ammi ta dokesa tunda dae gskya ya fada, baffan ya bude kofar hannunsa har lkcn na goshinsa yana kallon yusuf din yace "ni xaka duka idan ka girma ko," yusuf yace "eh, idan har baka daina ma Ammina ihu ba," ya gyada kai ya fice daga gidan ba tare da ya sake cewa komai ba, Aneesah ta rungume yusuf tace "yauwa kanina shi yasa nake son ka," nn fada ya dawo kanta, Ammi ta dinga mata fada wae basu da respect tunda ubansu suke ma fitsara daga ita har yusuf, Aneesah ta mike ta wanke hannunta ta dauro alwala, taxo tayi slln isha snn ta jawo kaninta suka kwanta. Washegari Ammi ta dinga fushi da ita da yusuf, ita dae bata san me tayi ba kuma har ga Allah taji ddin abinda yusuf yyi, ta xauna gaban Ammi ta marairaice murya tace "don Allah kiyi hakuri Ammi, kin ga fa jiya bayan kinyi bacci nayi ma yusuf fada Ammi," hka Aneesah ta dinga ba Amminta hakuri ta kira yusuf ma ya bata hakuri snn Ammi ta sauko, ta shirya yusuf ya wuce sch, ita kuma ta kama hanyar gidan aikinta, hka ma Ammi don gidan da take ma aiki sun dawo, ranar through out bata ga Haiydar ba sae taji wani iri, yau Monday tana isa breakfast ta fara hada masu ganin karfe takwas ya kusa sbda pretty mai xuwa makaranta don duk sauran sun gama ita ma a Higher institution take, har lkcn 'yan gidan basu tashi ba, tana cikin wanke wanke taji mutum a bayanta ta juya da sauri, yana sanye cikin bakin suit da tie yyi kyau sosai ga briefcase a hannunsa kamshin turarensa ya gauraye ko ina, ta tsura masa ido tana kallonsa yau kwana biyu knn bata gansa ba, ya sakar mata murmushi yace "Gud mrnin," ta kauda kanta tace "ina kwana," ya gyada mata kai ya dawo gabanta ya tsaya "ke kin karya ne," ta juya bata sake tanka masa ba ta ci gaba da abinda take yi, ya juyo da ita yace "me kika hada na break," tace "suna can dinnin" yace "to debo min nawa ki kawo nn," ya fadi yana nuna mata dinnin din kitchen, tace "to ai bn san yanda kke hada tean ba," "ki hada yanda kike tunanin ya kamata amma kar ki cika min suger, jez cube biyu yyi," tace "uhmm" snn ta fice daga kitchen taje hado masa nasa tean a kan table, ko da ta dawo kitchen din yana xaune kan dinning, yace "to hado min coffee plss," ta hado masa ta ajiye gabansa xata wuce ya fixgota ya xaunar kan kujera yace "ni bana break a gida ran monday, amma yau sbda ke xan yi don tare nake son mu ci," xata yi magana ya sa mata dankali a baki yace "kar ki ce min komai" hka Haiydar ya tilasta ta suka ci duk abinda ta kawo masa a tare, tean ma kanta yasa ta hado ma don coffee kawae ya sha, gabanta ya dinga faduwa kar Hajiya ta sauko ta gansu a hka, ta marairaice fuska kmr xata yi kuka tace "wllh na koshi, na fa karya a gida" ya mike yana kallonta ya kashe mata ido yace " ai de kin ci, sae na dawo, kiyi min ginger drink kanwata," ta gyada masa kai kawae, ya kalli agogon hannunsa ya bi ta garden ya tafi garage xabar motar da xae fita da. Tana gama gyara inda suka yi break din Hajiya ta sauko tare da pretty dake cewa "momy yayana ya wuce ne, wae fa da droppin dina nake son yyi tunda driver baya nn," hajiyar tace "nima wllh ko sallama bai yi min ba bby," ki karya sae nasa sumy ta ajiye ki tunda har ynxu tsoran drivin kike yi, Aneesah ta risina ta gaida su, snn ta hau sama ta gyara masu dakunansu ta wanke bathroom, tana gamawa suka tula mata kayan wanki ta wanke, ba ita ta gama wankin nn ba sae kusan karfe biyu, bbu kowa gidan duk sun fita, ta shiga kitchen a gajiye don ta girka masu abinci kafin su dawo, karfe uku saura ta gama girkin ta jera masu kan table, ta tuna Haiydar yace tayi masa ginger drink, ta koma kitchen da sauri ta shiga hada masa drink din, tana gama hada drink din ta xuba cikin jug ta saka cikin fridge snn ta juya xata bar kitchen din ta gansa jingine jikin kofa yana kallonta, yyi murmushi yace "sannu da aiki kanwata," ta gyada masa kai ta gaishesa ta fice daga kitchen din, shima ya fito ya haye sama ganin meenah a falon tsaye tana ma Aneesahn magana cikin gadara, "ke meyasa xaki hada min wanki da fararen kayana," Aneesah tace "Aa su na fara wanke wa, bn hada su da komai ba," meenah ta kai mata mari tace "karya kike munafuka, ki tabbatar kin sake wanke min su kafin ki bar gidan nn yau," tana kai wnn ta haye sama tana xage xage, Aneesah ta bi ta da kallo hawaye na bin kuncinta, ganin Haiydar na saukowa yasa ta juya da sauri xata bar wajen ya kirata, ta tsaya har ya karaso kusa da ita yace "me kika yi mata?" tayi shiru bata ce masa komai ba, ya kwala ma Meenar kira ta sauko tana kallonsa tace "gani," ya hade rae yana kallonta yace "me nace kiyi min jiya kafin na dawo," ta yatsine fuska tace "oho na manta," ya kai mata tagwayen mari masu rai da lafiya. . Meenah ta dafe kuncinta tana kallonsa da mamaki, "yaya ka mareni??" ya fixogta ya watsa mata wani marin yace "an mareki don uwarki, nxt tym idan na sa ki abu baxa ki manta ba," ya cillar da ita cikin tsawa yace "bace min kar na taka ki," ta mike tsaye ta fasa ihu ta haye sama da gudu tana kuka tana kiran momynta, Haiydar ya juya yana kallon Aneesar dake tsaye a wajen har lkcn ya kashe mata ido yace "ya dai kanwata kin ga mun rama ko," ta juya da sauri ta bar wajen ta shige kitchen ya bi bayanta, yana shiga kitchen din yace "kanwata ki hada min lunch dina ki ajiye kan dinnin din nan, sae ki shiga bedroom dina xamu yi magana, ranar bamu gama ba mum ta dawo" ta xaro ido tace "A'a ni mun gama magana kuma Hajiya ma ta kusan dawowa ynxu," yyi shiru yana kallon cikin idonta ta sunkuyar da kanta da sauri ya karaso gabanta ya tsaya, ya dago kanta a hankali yana kallon fuskarta, murya can ciki yace "yhu're a damsel Aneesah," ta kauda kanta da sauri ya juya ya bar kitchen din ta shiga yin abunda ya sa ta. Sae da yyi wanka yyi sllh, yyi shiga cikin kanan kaya snn ya sauko falon, har lkcn meenah ta cika masu gida da kuka tana yi tana kiran momynta, ya tabe baki ya shige kitchen din bai ganta ba yasan tana garden, ya karasa cikin garden din ya jingina jikin kofa yana kallonta, tana xaune ta tsura ma sararin samaniya ido, jikinta ya bata ana kallonta ta juya da sauri suka hada ido ta kauda kanta tace "na xuba maka abincin," yyi murmushi yace "ohk xo ki gani," ta mike ta bisa a baya har suka shiga kitchen din, yace "xo mu ci oya," ta xaro ido tare da girgixa masa kai tace "aa ni naci nawa," ta juya xata bar kitchen din yyi saurin fixgota har tana neman fadawa kansa, yace "ai baki isa ba idan baxaki ci ba to kwashi abincinki nima baxan ci ba," kmr ko da yaushe hka Haiydar yyi forcin dinta yana bata abincin, har da hawayenta, har dae suka gama ci snn ya mike ya bar kitchen din yana dariya, ta bishi da harara snn ta mike ta shiga gyara table din, ta gama wanke kwanukan knn Hajiya da sumy suka shigo gidan, Hajiya ta rude jin kukan meenah tun daga waje ta shigo falon da sauri tana cewa "me ya faru meenah ta," meenah na jin muryar uwarta ta sauko da gudu ta xube kasa tana ci gaba da rusan kukanta, Hajiya ta rikice ta shiga tambayanta menene, cikin kuka tace "Haiydar ne ya dinga mari na bn san me nayi masa ba," Hajiyar ta gintse fuska tana kallon sama tace "baki yi masa kmai ba ya dinga marinki," tace "eh" hajiya ta shiga kwala masa kira a fusace, ya sako yana kallnta yce "sannu da dawo wa," bata damu da amsa masa ba cikin fada tce "me meenah tayi maka xaka mareta Aliyu ni fa wllh baxan dauki wnn ba, so kke ka illata mata fuskar ko me, wnn ai mugunta ce, ni gskya idan takura ma 'ya yana xaka yi ka tattara ka koma gidan ka kawae, ka dinga xuwa kana kawo mana xiyara," ya sa kafa yyi ball da meenar da har lkcn ke xube a kasan tiles yace "don uwarki na mareki din, ke wacece da baxan mara ba ohh ashe bbu ddi," ya juya a fusace yana kallon uwartasa yace "duk kin bi kin lalata yara basu da aiki sae na lalaci da iskanci, wnn wni irin abu ne, ita 'yar gidan uban wacece da ban isa na sata aiki tayi ba, kuma ta iya sa wani yyi, ni bama sae kince na koma gida na ba xan koma don baxan iya ci gaba da xama a gidan nn ina kallon tabarar da yaran nn ke yi ba,tunda na dawo bn ga shegen da ya dauki buta ko sau daya da sunan xae yi sllh ba, idan basa gaban t.v suna gidan party," tunda ya fara magana Hajiya tayi tsit ta marairaice fuska tana kallnsa can ganin ba shiru xae yi ba se dada tona ma 'ya yanta asiri da xe tayi yasa tace "to kayi hkri Aliyu ban san laifi tayi maka ba, ke kuma meenah me ya kai ki yi ma yayanki fitsara, meyasa ba ki jin magana," meenah ta xumburo baki taki cewa komai, yyi tsaki ya haye sama, sae a nn meenah ta mike cikin tsawa ta shiga kwala ma Aneesah kira, Aneesah dake kitchen ta fito da sauri ta durkushe gabansu tace "ga ta," "don ubanki ki je ki kwashe duk kayan da kika wanke min ki sake wankesu don basu fita ba," Haiydar ya sauko kasa cikin tsawa yace "ae baki isa ba don uwarki, kmr yanda ban isa na sa ki ki yi ba, to karya ki ke ki sa wani yyi," ya kalle Aneesar dake durkushe har lkcn gabnsu yace "ke tashi ki fita

Chapter 3 of 23