Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ANEESAH 🌹🌹🌹 Na KHALEESAT HAIDAR 👉1 A guje ta fado dakin ta xube kan Amminta dake linkin kaya tana sakawa cikin jaka, Ammi ta dago fuskarta a rude tana tambayarta "lfya? me yafaru?" tana mayar da numfashi a dan tsorace ta kasa ce ma Amminta komai, sae da Ammi ta maimaita mata tambayar a fusace snn ta fashe da dariya tace "wae Ammi yusuf ne xae dokeni, don mota ta take masa kwallonsa nayi dariya," Ammi ta haureta cikin fada ta fara magana "wae ke yaushe xakiyi hankali ne Aneesah, ba wanke-wanke na sa ki ba kika fita waje kina biye ma yusuf, shi yusuf din kike ma gudu idan ba wauta ba," ganin yanda Amminta ta fusata yasa ta mike tsaye da sauri ta marairaice murya tace "kiyi hkuri Ammi, amma idan na fita wllh dukana xae yi, kuka fa yake yi," Ammi xata yi magana sae gashi ya shigo dakin, da gudu tayi bayan Ammin tana cewa "wayyo ammi kin ganshi ko," Ammi ta dada mata duka snn tace "kai yusuf yayar taka xaka duka don ba ka da kunya," yyi ma Aneesar wani irin kallo yace "Allah ya taimake ki mutumin ya bani Naira ashirin na siya wani kwallon," Aneesah ta dinga dariya tana cewa "Naira ashirin" yace "eh mana" snn ya fito da sabbin dubu daya guda biyu, Aneesah ta xaro ido tana kallonsa, Ammi tace "kai yusuf wa ya baka wnn kudi hka," yace "mutum da ya fasa min ball da motarsa yace naje na siya sabo," Ammi ta juya tana kallon Aneesah, can tace "to kawo nn yusuf, anjima da kaina xanje kasuwa na siyo maka wani, amma kace masa ka gode ko?" yusuf yace "aa na manta, snn ya mika mata dubu biyun ya fice ya fice daga dakin," Ammi tace "oh Allah dae ya biya wnn mutumin, kmr yasan ynxu tunanin me xamu ci anjima nake Aneesah," Aneesah tayi murmushi tace "ki siyo kayan abinci kawae Ammi," ammi tace "hkn xanyi, bari na gama hada kayan nn sae na tafi kasuwa," Aneesah ta mike jikinta a sanyaye ta fita daga dakin taje yin wanke wanken dake tsakar gidan. . Aneesah na shirin islamiyya karfe hudu saura Ammi ta shigo gidan, ta karbi ledojin dake hannunta da sauri tanai mata sannu da xuwa ta fito mata da kujera waje snn ta debo mata ruwa a randa ta kawo mata, ta xauna gabanta tana tambayarta ya hanya, Ammi ta ajiye kofin ruwan dake hannunta bayan ta shanye ruwan tace "maxa ki tashi ki kama hanyar makaranta lkci na wucewa, ina yusuf?" tace "nace ya jirani yace shi su khabir xae bi," ta mike ta dauko goggen Hijab dinta da Nikaf ta saka snn tace "to Ammi sae na dawo," Ammi tayi mata Allah ya kiyaye ta fice daga gidan. Karfe bakwae saura su ka shigo gidan ita da kaninta, Ammi na share tsakar gida su ka yi mata sannu da gida suka shiga daki, tana gama cire uniform ta fito karbar sharan ammi tace "su yi sallah, ga abincinsu a kitchen," yusuf na ganin shinkafa da miyace ya dinga tsalle yana murna yau xa su ci shinkafa, Aneesah ta galla masa harara tace "yau ka saba cin shinkafa ne? wawa kawae," ya daga hannu xae kai mata kulli ta goce da sauri tare da kwala ma Ammi kira ganin wani kullin xae kai mata, Ammi ta shigo dakin da sauri ta raba ma kowa nasa tana masu fada snn ta nemi guri ta xauna tana kallon 'ya yan nata. Aneesah yarinya ce da bata wuce shekara 17 ba, sun taso cikin wahala da talauci tun bayan rasuwan mahaifinsu Alhaji Mukhtar, Alhaji Mukhtar shararren mai kudi ne a garin Abuja, Allah yyi masa rasuwa shekara takawas da suka wuce a hatsarin mota da yyi a hanyar sa ta dawowa Abuja daga kano bayan ya kai ma 'yan uwa da relatives ziyarar sallah, tun bayan rasuwarsa suka fara fuskantar kalubalen rayuwa duk da dukiyar da ya bari mai dumbin yawa don a lkcn ma gidajen da ya bari sun kai 6 bayan motoci da filaye, kiri kiri yayansa Alhaji shehu ya karbe komai nasa da sunan xae ajiye har sae yaransa sun mallaki hankalin kansu, Alhaji Mukhtar shine auta a gun mahaifinsu malam sule, da mahaifiyarsu saudat, su uku kadae Allah ya basu duk maxa, shehu, ibrahim da shi Mukhtar, tun yana primary Allah yyi ma mahaifiyarsu rasuwa, yana gab da gama secondary mahaifinsa ma ya rasu, tun daga lkcin komai ya tsaya masa don duk yayyinsa sun dauki karan tsana sun daura masa tun iyayensu na da rae bare ynxu da suka koma ga Allah, duk suka juya masa baya ga 'yan uwa ba xumunci, ya sha wahala sosae a rayuwa don da kyar da taimakon sana'ar da yake yi na wankin mota cikin ikon Allah ya kammala karatunsa ya sami aiki a House of Assembly Abuja. . Yan uwansa na ganin hka suka fara shisshige masa suna nuna masa so, da yake shi Allah yyi sa mutum ne mai son xumunci kuma mara riko, ko kadan bai kullace su kan abinda suka yi masa ba ya ja su a jiki ya sama masu aiki don dama duk buga buga suke, ya kuma taimaka ma yan uwa da dama tun daga kan relatives har xuwa wa inda ma bai hada komai dasu ba. Ana hka suka hadu da Mahaifiyarsu Aneesah Maryam a bikin wani abokinsa, sunyi soyayyar gskya wanda ya kaisu ga aure duk da dangin ubanta basu so hkn ba don auren xumunci suka yi niyyar mata, amma da yake Allah yyi shine mijinta a hka su ka yi aurensu wanda bayan shekra daya Allah ya axurta su da samun Aneesah, daga ita ko basu sake haihuwa ba har sae bayan shekara takwas, don kaninta yusuf na da wata biyu mahaifin nasu ya rasu, ba karamin girgixa Ammi mutuwar mijin nata yyi ba, kuma duk da tsanar da danginsa ke mata don ko kadan basa sonta a hka ta gwammace ta xauna ta tarbiyantar da 'ya yanta a gidan ubansu don iyayenta talakawa ne sosae snn tun tana da shekara goma mahaifiyarta ta rasu matar uba ta sa ta gaba, hkn yasa kakarta na wajen uwarta ta maidota wajenta har Allah ya hadata da Alhaji Mukhtar suka yi aurensu, kuma tasan ko ta tunkari gidan mahaifinta ynxu baxae karbeta ba don duk abinda matarsa ta gaya masa shi yake bi, kuma matar bata so ta auri mai kudi ba tunda yayanta duk ba masu kudi suka aura ba, to be continued. . .. . . insha Allah @ #dan_gogori1 Drop ur cmmn ANEESAH🌹🌹🌹 Na KHALEESAT HAIDAR. ~2~ Sallamar wata makwabciyarsu ne ya sanya Aneesah ta dago tana goge fuskarta, ta karaso cikin gidan Aneesah ta gaida ta ta amsa tana tambayrta ya karatu, ta shiga dakin ta gaida Ammi snn ta ajiye kwano tace "gashi a ba yusuf ya kara Ammi, bbu yawa," Ammi tayi mata godiya tana tambayrta danta umar, tace "yana can waje suna wasa" snn ta fice. Ammi ta jawo kwanon ta bude taga dumamen tuwo ne, tasan kila yusuf yace mata yana jin yunwa ne shine ta kawo abincin don matar tana da kirki sosae duk da su ma manage suke don sae mijinta ya fita yyi shoe maker snn suke samun abinda xasu ci suma , ta kira Aneesan su xo su ci, bakin ciki da takaici yasa taji ta daina jin yunwan ma kwata kwata tace bata ci, da kyar Ammi ta lallabata ta ci dn tasan halinta. Karfe sha biyu saura Ammi ta fito da dinkekken atamfarta da kakarta ta aiko mata da wani sllh, Aneesah ta tambayeta inda xata da shi ganin tayi shirin fita ne, Ammi tace "xan je kasuwa ne na sayar Aneesah kafin su Hajiya salamatu su dawo," Aneesah tace "haba Ammi ke knn kullum sayar da xani don Allah don annabi," Ammi tace "to meye amfaninsu Aneesah," ki kula da yusuf kafin na dawo don daga can xan siyo abinda ya sauwaka na abinci," bata jira cewar Aneesahn ba ta fita daga gidan. Tana tsaye bakin kofar dakinsu bayan ta gama shirin boko, yusuf yace "Anty mu wuce kar su Jamila da khabir su ruga mu yau ma," Aneesah ta jawo sa tace "kasan me yusuf, maxa ka bisu ni ina nn xuwa kaji," bae yi mata musu ba ya fice daga gidan, Ammi tace "to ke me kike jira Aneesah," Aneesah ta shigo cikin dakin ta xauna tana kallon Amminta tace "kudin waec nd Neco Ammi, kuma ance kar mu xo yau idan har mun san xa muyi kuma bamu kawo kudi ba," Ammi ta tsura mata ido tana kallonta tace "to yaushe ma ya bada kudin makarantar da har xa'a tunkaresa da wani kudin waec, amma dae ki shirya kije ki samesa ki gaya masa ynxu kila Allah ya daura ki a kansa Aneesah" Aneesah ta hade rai, can ta tabe baki tace "bbu inda xanje Ammi, gwara kar na sake xuwa makarantar ma kwata kwata," Ammi ta galla mata harara tace "to ki xauna," Aneesahn tace "to wnn mutum ne Ammi, ko fa naje ba bani xae yi ba sae dae ya walakanta ni ma, ba gwara kawae kar naje ba," Ammi tace "ko ma de mae xaki ce, yayan babanki ne, baffanki ne dn hka ki iya bakin ki, kuma ki tashi ki shirya ki tafi kafin ya fita," ta mike jikinta a mace ta tube uniform dinta, ta dauki wani material dinta ashe da maroon ta saka, duk da talaucinsu in ta fita baka taba cewa tana cikin wahala don kullum fes xaka ganta. Ammi ta bata kudin motar tace ta barshi kawae xata taka, dole ta tilasta ta ta amshi kudin dn can cikin gari xata da nisa sosai. Aneesah na isa gidan baffan nata ta danna kararrawa daga waje mai gadi ya leko ta gaishe shi ya bude mata gate din ta shigo, ta tambayesa ko kawunta na ciki yace eh, da kyar gabanta na faduwa ta shiga gidan da sallamarta ta gaida 'yan aikin dake ta harkar gabansu a gidan, snn ta karasa cikin falon ta xauna kasan tiles tana jiran fitowar baffan nata. . Aneesah ta kusan minti ashirin xaune a falon kafin baffan nata ya fito cikin shiga ta shadda green colour sae walkiya yake, ga kamshin turare ya baxa ko ina, yana ganinta ko ya hade rai cikin daga murya yace "dama kece ki ke nemana wae?" ta sunkuyar da kai tace "eh nice ina kwana baffa," ya amsa a dakile snn yace "lfya da sassafen nn hka," tace "A'a dama kudin waec da Neco ne aka fara karba a schl, shine naxo na gya mka don sun ce kar mu xo yau ma," sae da ya saurareta ta kai aya snn ya daka mata wani mugun tsawa yace "don uwarki ca nayi maki ina da kudi ynxu da har xaki xo da sassafe karban kudin waec da Neco, kin bani ajiya ne ko uwar taki da ta aiko ki ta bani," ta girgixa kai tace "naga dae Baffa ba mu da wanda xamu tambaya bayan kai, kuma in ma hka ne ni fa ba kudinka nace ka bani ba, daga cikin kudin mahaifina xaka bani naje na biya abinda xan biya, kace sae mun mallake hankalin kanmu Baffa to ni dae na mallaki hankalina, a raba mana gadon mu kawae ka huta da tambayarka kudi ko makamancinsa da muke yi" tun da ta fara magana ya bude baki kmr soko cike da mamaki yana kallonta, tana gama fadin abinda xata fadi ya daka mata tsawa yace "ohho dama rashin kunya uwar taki ta turo ki kiyi min fateema, ni kike gaya ma wa innan maganganun don baki da kunya" ya saka salati yana jijjiga kansa yana kallon ceilin, ta dan tabe bki tace "ni fa ba rashin kunya nayi mka ba baffa" "to wllh wllh kinji rantsuwar musulmi ko, daga yau xuwa makarantarki ta kare, don aurar dake xayi don ubanki, kuma daga yau ko tsinke na ya daina shiga hannunku, shi uban naki da yake da rai uban me ya tsinana ma mutane sae uban rowa duk dukiyar da Allah ya basa, don uwarki duk hidimar da na ke maku har ixuwa yau da kudina nace maku ina maku, ai ki bar ma maganar gado don ko dubu dari bae rage cikin accnt din ubanki ba, duk kun cinyesu," ta mike tana yi masa wani irin kallo snn tace " lbri ma knn, shi kuma wnn gidan da kke ciki da sauran gidajensa da motocinsa fa ba a mayi maganar filaye ba, idan ma kace mun cinye kudin acc, ae wa innan suna nn baffa," ya kwasheta da wani gigitattcen mari yana huci "ni kke gaya ma wnn maganar," dae dae nn matarsa hajiya zuwaira ta fito da sauri, tace "me ya faru Alhaji, me ya kawo wnn kuma da sassafen nn," cikin in ina don ransa yyi mugun baci ya shiga yi mata bayani, Aneesah dae na tsaye dafe da kuncinta tana kallonsu, matar tasa bata bari ya kai aya ba tayi cikin kitchen da sauri tana cewa "ka kyaleni da shegiyar Alhaji," Aneesah na jin hka ta fice daga gidan da gudu don tasan matar bata da mutunci, bata manta randa ta biyo ta da yaji ba, yau kuma bata jira ganin me xata je daukowa ba ta yi ta kanta, tana barin anguwan ta dinga kuka a hanya tana bakin cikin wnn rayuwa irin tasu, da kyar ta isa gida don har wani jiri take ji dn yunwa dama koko kadae tasha da safe. Ammi ta mike da sauri tana kallonta tace "ya akayi kika dde Aneesah, me ya sa ki kuka," ta girgixa mata kai tace "ban samu ganinsa da wuri ba ne Ammi," sae da ta nutsu snn tayi ma Amminta bayanin duk yanda suka yi da baffan nata, Ammi ta dinga mata fada kmr xata mareta wae tayi ma baffanta fitsara ita dai shiru tayi bata ce komai ba har Ammi ta gaji tayi shiru, sae a nn ta shiga bata hkuri tana kuka, Ammi ta goge hawayen fuskarta don ita ma kukan take tace "kinga kin ma kanki Aneesah, ynxu xaman gidan kika fi so," Aneesah tace "dama Ammi ni banga alamar xae biya min ba fa," Ammi tace "to shknn Aneesah," Aneesah tayi shiru kmr mai naxari snn tace "Ammi kinsan mene," Ammi ta girgixa mata kai tace "me", ta dan kwantar da murya tace "don Allah Ammi ki sama min inda xan dinga aiki ana biyana sae na tara kudin waec din ta hka, tunda naga sae nn da wata uku xa a xana waec din," Ammi ta galla mata harara tace "kina da hankali kuwa Aneesah," ta yi narai narai da ido tace "kiyi hkuri Ammi, amma hkn shine kadae mafitar mu" Ammi tace "baxae yiwu ba, sae dae kijira har wani shekaran sae ki xana abinki idan Allah ya hore mana," Aneesah ta fashe da kuka tace "haba Ammi, to meye a ciki don nayi aiki, mu fa ynxu bamu da gata sae na Allah, don Allah ki bar koma wani tunani kike yi Ammi kin manta ko wacece Aneesah ne Ammi, wllh xan tsare kaina baxan taba baki kunya ba, ki tausaya min ki bari na tara kudin jarabawa na don Allah Ammi," tana magana ne tana kuka, Ammin ma kuka take, ta rasa abinda xata ce ma 'yar tata, can dae tace "shknn Aneesah ki bari nayi tunani da kyau kar mu janyo ma kanmu xagi a gari," Aneesah tace "to shknn Ammi," snn ta mike a sanyaye ta bar dakin taje debo ruwa a waje don ba ruwa a gidan. . Bayan kwana biyu Aneesah na xaune gaban Ammi dake rungume da yusuf baya jin ddi tana basa ruwan tea, Aneesah ta kirata a hnkli tana kallonta, Ammi ta dago tace "meyafaru Aneesah," Aneesah ta sunkuyar da kai murya a raunane ta fara magana "Ammi har ynxu baki sake cewa komai kan maganar da muka yi dake ba, kince xaki yi tunani, don Allah Ammi ki bar ni na fara aiki, hkn xae taimaka mana sosai, gashi ynxu ko kudin da xa mu kai yusuf asibiti bbu" Ammi tayi shiru bata ce komai ba tana ta lallaba yusuf ya sha ruwan tean, hkn yasa Aneesah ta fara hawaye, Ammi ta dago kai tana kallonta, "meye na kuka Aneesah," Aneesa ta girgixa kai cikin kuka tace "to kin ki cewa komai Ammi," Ammi ta sauke ajiyar xuciya ta gyada mata kai tace "naji Aneesah," bata sake cewa komai ba daga nn, Aneesah ma tayi shiru tana tunanin wani irin rayuwace wnn da kowa kansa ya sani. Washegari laraba tun da sassafe Ammi ta fita xuwa gun wata hajiya xulfa da suke mutunci da, ta yi mata jagoran sama ma Aneesah inda xata dinga yin aiki don tana hulda da masu kudin cikin gari sosae kuma tana yawan kai masu 'yan aiki, karfe shidda na yamma Ammi ta dawo gidan a gajiye, Aneesah ta fito mata da kujera snn ta kawo mata ruwan sha a kofi, bayan ta sha take tambayar jikin yusuf Aneesah tace da sauki sosai don har ya fita wasa, sae da ta bar Ammi ta huta snn murya can kasa tace "Ammi ya hanya," Ammi tace "lfya lau, na samu inda xaki dinga aikin da kyar Aneesah, amma sae dae matar bata da mutunci ko kadan, bana tunanin xaki iya Aneesah barin ma ke da baki da hkuri, snn irin aikin da ta lissafo gskya bana jin xaki iya su sun maki yawa Aneesah, ki hkura kawae idan Allah yasa wataran Hajiya xulfa ta sake samun wani wurin aikin sae ki fara," Aneesah tace "haba Ammi ni wllh koma meye ni xan iya aikin nn, don Allah ki barni na fara kawae Ammi, nayi maki alkawarin baxan baki kunya ba kinji Ammina, " Ammi tayi shiru tana kallonta, can tace "shknn to Allah ya kai mu gobe," Aneesah tace "Ameen," cike da murna da jin ddi don ita so kawae take ta xana jarabawarta wnn shekaran da yardar Allah. Karfe goma da rabi Aneesah da Amminta suka isa kantamemen gidan da xata fara aiki a cikin garin Abuja, jikin Aneesah yyi sanyi sosai ganin gidan bana wasa bne don gidan ya hadu iyakar hadewa ga anguwar ma kadai abun kallone, maigadi da uniform din soja a jikinsa ya bude masu gate fuskarsa a tsuke yace "ku ne bakin da Hajiya tace xa su xo," Ammi tace "eh mune," ya nuna masu daga kusa da wani flower yace "to ku tsaya can tace ku jira ta a nn," Ammi tace "to snn suka dawo gefen shukan suka tsaya, Aneesah ta dinga masa wani irin kallo cike da jin haushin yanda yake masu maganar," yaje ya ba yaran gidan sako suce ma Hajiya masu aikin sun xo snn ya dawo bakin gate ya tsaya, Aneesah sun fi awa daya a tsaye wajen ga rana bbu hajiya bbu lbrinta, har sun firda ran fitowarta Ammi tace "muje kawae Aneesah," sae ga ta ta fito cikin shiga ta alfarma sanye da glass sae kamshi take a girme xata girme ma Ammi sosae ba kadan ba, ta dinga taku kmr baxata taka kasa ba ta iso kusa dasu tana masu wani irin kallon raini cikin isa da gadara tace "ina 'yar aikin," Ammi ta kasa cewa komai, sae Aneesah ce tace "gani," matar ta bude baki da dan mamaki tace, "wnn kwailar wani aiki xata iya hka, na yi xaton wata babba balagaggiya xaki kawo min malama," Aneesah ta dake tace "bbu abinda bana yi Hajiya, tun daga kan shara, wanke wanke, goge goge, girke girke, da duk aikin da kika sani Hajiya," Hajiyar ta tabe baki tace "yyi, duk wata dubu goma sha biyu nace xan dinga badawa kuma idan washing machine ya wanke ma babies dina kaya yau to gobe ita xata wanke masu, snn tun karfe bakwae xata xo aiki ta bar min gidana karfe shidda na yamma, ina fatan ku ba fulanin daji bne kun fahimce ni," Ammi tayi murmushi tace "mun fahimce ki Hajiya mun gode, amma karfe shiddan da kika ce Hajiya yyi dare don gidanmu da nisa sosai, ki rage kudin aikin in yaso sae ta dinga barin nn ko xuwa karfe biyar ne," hajiyar tayi masu wani kallo ta tabe baki tace "karfe biyar da rabi xata dinga barin nn period, idan hkn yyi maku to ta fara aiki daga dis vry moment, idan kuma bai maku ba ku ja tsumman rayuwarku ku fice min daga gida don ni bna kai wa wnn lkcn ina surutu da yan aiki talakawa irin ku," tana kaiwa nn ta juya ta shiga takunta cikin isa har ta hau balcony ta shige falo... @ #dan_gogori_ ANEESAH 🌹🌹🌹 . Na KHALEESAT HAIDAR .~3~ . Ammi ta girgixa kai a hankali tace "baxa ki iya ba Aneesah muje kawae," Aneesah ta xame hannunta a hankali daga rikon da Amminta tayi mata tace "xan iya Ammi, ki tafi gida kawae sae na dawo," bata jira abinda Ammi xata ce ba tayi saurin barin wajen ta bi kofar da Hajiyar ta bi ta shige cikin gidan tana karanto Addu'o'i cikin xuciyarta, ta ga kanta a wani makeken falon gske mai cike da kayan alatu da kayan more rayuwa " ya salam! Aljannar duniya knn," ta dinga bin falon da kallo a hankali gabanta na faduwa sae kace ba Nigeria ba, wnn wani irin aiki suke yi hka, gskya wasu kam sun more duniya, ta rasa inda xata bi don falon ba kowa sae karar Ac da wani ni'imantattcen kamshi dake tashi, ta kai minti kusan goma a tsaye tana naxarin komai na falon duk da wasu tana ganinsu falon baffanta, taji ana taka matakalan bene a hankali ana saukowa ta tsura ma stairs din ido tana jiran taga ko Hajiyar ce ke sauko wa, wata kakkyawar yarinya da baxa ta wuce ta ba ce ta sauko tana sanye da kayan bacci, yarinyar ta mitsike ido tana kallonta da mamaki, Aneesah ta kauda kanta, yarinyar cikin gadara tace "who re yhu," Aneesah tayi shiru bata ce mata komai ba sae wani irin kallo ma da take ma yarinya, yarinyar ta juya da sauri ta koma sama, sae ga ta ta dawo da momynta, Hajiyar tace "ohh House Maid dinmu ce pretty," Hajiya ta karaso kasa a walakance tace "bbyna xata xaga dake ko ina na gidan ta nuna maki duk aikin da xaki dinga yi, sae ki fara daga ynxu," ta kira prettyn tace "sauko bby ki nuna mata House chores din gaba daya," yarinyar ta sauko tana yatsine fuska tace "momy ni kayana xata fara wanke min kafin ta fara komai, don ni ynxu na daina gane wankin washin machine din nn, shi kuma iliya baya wanke min da kyau gugan ma na Hauka yake min," Hajiya tace "to maxa ki fito mata da kayayyakin taje bakin tap a kusa da garden ta wanke, ki hado mata da na sumy don naga kmr tana da kayan wanki ita ma," prettyn tace "na meenah fa," Hajiyar tace "A'a kinsan halinta tana iya cewa bata samu ba, kwaso mata naku dae kawae," prettyn ta juya da sauri ta haye sama, Aneesah dae binsu da kallo kawae take. Hajiya ma ta juya ta haye sama, bayan kmr minti goma sae ga prettyn da tulin kayan wanki ta watsa mata su a gabanta, Aneesah ta dinga bin kayan da kallo, cikin gadara prettyn tace "kuma yarinya ki tabbatar kin wanke mana kayanmu da kyau, suna bushewa kuma ki goge mana su, snn karki kuskura ki hada min fararen kayana da wasu kayan don idan suka dafe wllh sae kin siya min sabo," ta juya tana tana karkade jiki ta haye sama. Aneesah tace "hmm, ikon Allah," ta girgixa kai ta kwasa kayan da sabulae da omon da ta watsar mata ta fita daga falon ta shiga neman garden da kyar ta samo sbda girman gidan, ta ga bokitae da manyan robobin wanki a wajen ta tara famfo ba tare da bata lkci ba ta fara wankin, ba ita ta gama wankin nn ba sae kusan karfe daya, don kayan mugun yawa ne dasu, abun mamaki ma wasu bata ga alaman an sa su ba, ta juya bayan ta gama shanyan kayan tana kallon kudaden da ta dinga gani a wandunayensu da english wear tana ajiyewa gefe daya, ta kirga gaba daya kudin taga dubu

Chapter 1 of 23