bani numbarka zan nemeka idan ka shigo ,"Aa yallabai ni ne zan kiraka ka bani number wayarka ,to shikenan ka rabuta commissioner ya karanto ma jaguwa numbersa yana maimatawa anas kuma na rubutawa sannna ya katse wayar ."
commissioner ya kalli mataimakinsa yana sake yi masa bayani abinda jaguwa ya fada masa "ya kake gani zamu yi yanzu "kwanta kwata yallabai ni ban yarda da wannna mutamin ba "taya yasan labarin mutuwar honorable abdulaziz da mutanen da suka kashesa da inda aka binne gawarsa byn har yanzu ana kan bincike ne baa gano inda gawar take ba su kansu abokansa sunki amsa laifin su suka kashesa dan haka ni ban yarda dashi ba karka sauraresa."
“amman kuma gaskiya ya fad'a mana tunda duk abinda ya fada haka ne kuma da alamun zai yi matukar yi mana amfani," nan dai suka cigaba da tautaunawa shi dai commissioner ya yarda da maganar jaguwa kuma idan dai har ya kirasa zai bari su hadu ya bashi bayanai akan komai bayan mataimakinsa ya tashi ya koma office dinsa kira ya shigo wayar hannu ta commissioner yana dauka ya fahimci mai magana "me kuma kake so daga gareni ?
"so nake idan na shigo mu hadu da kai kai kadai na baka sheidu masu matukar mahimanci idan kuma hakan bazai yiwu ka hadu dani kai kadai ba shikenan sai na tattara sheidun na watsasu a ruwa daman yanzu adalci yayi wuya ayi sharia a lahira a inda babu wanda ya isa sai allah ,ya tunhumeku akan abinda kukayi ,ni da zaku fahimceni ma bayan wannan mahiman bayanan akwai wasu akan masu safar miyagun kwayoyi wanda dayansu polisawa ne duk zan baka amman kai kadai ,dan da kai kadai kawai na yarda ."To shikenan ai kuwa daka taimaka mana yanzu dai ka sake kirana nan da awa uku zan fada maka inda zamu hadu jaguwa najin haka ya dunkule hannunsa yana jin dadi ya katse kiran ya zauna yana cewa "shikenan tarkona bai kama dcp ya kama commissioner ,sai yanzu hankalina ya kwanta"ya karasa maganar yana sakin murmushi.
“ya yarda zaku hadu kenan ?da alama tunda yace na kirasa byn awa uku zai fada min inda zamu hadu kasan fa shi wannnan commissioner din rikitaccen tsoho ne ina ganin ma a karshen shekara nan zai yi ritiya ,zan bika muje tare ."baka da hankali bakaji nace babu inda zakabini ba , ance maka haduwa da commissioner abu ne me sauki ? ka barni kawai naje ni kadai idan ma matsala ce ta tsaya iya kaina ban da kai ya karasa maganar tare da mikewa ya nufi bathroom dan lokacin sallah laasar yayi ."
Bayan jaguwa ya fito Ana's ya tashi ya shiga bai bata lokaci ba ya fito alokacin jaguwa ya tada sallah ya karaso ya bishi jim'i byn sun idar suka sake zama sai lokacin jaguwa ya tuna da jama'arsa dake kofar gida gashi ya soma jin alamun hadari ya kuma san muddin bai bada sakonsu ba anan zasu wuni har sai sun ga fitowarsa "anas kira sky kace ya sallama mutanen dake waje ,numfashi ya sauke "gsky kam dan wasu da wannan kudin daake raba musu kullum suke cin abinci batare da bata lokaci ba ya kira layin sky ya bashi umarnin ."
Suna hira suna duba lokaci a hankali har akaci awa daya acikin awa ukun da commissioner ya bayar dan haka suka cigaba da hirar yadda jaguwa zai hadu da commissioner "tunanina idan na kira shi zai ce mu hadu dashi a hotel ko gurin shakatawa ba lallai mu hadu dashi a gidansa ba , nima gaskiya bazan so ku hadu a gidansa ba akwai hatsari gara ku hadu a waje zai fi ,muna haduwa a yau ina tabbatar maka a yau scorpion zai fito domin bazan sausauta masa ba."
suna cikin hirar wata awa daya tazo ta wuce karfe shida daidai kenan cikin haka hally ta kira layin anas ya zaro wayarsa yana dubawa "my princess ."
Ya fada yana dauka "wa'alaikis salam matata fatan kina Lfy?alhamdulillahi kinji shiru ban kiraba ko ?sorry my princess inshaallahu bazan jima ba zan shigo sukai sallama ya maida hankalinsa ga jaguwa wanda ya dauki sigari ya kai bakinsa "kasan yanzu hatta sigari ina kyamar shanta saboda banason matata taji warinsa ajikinsa ".
Wannan kuma damuwarka ce ni dai ko zan rabu da komai ban da sigari ina mugun qaunarta murmushi Ana's yayi "wallahi adnan ina maka kwadayin aure da zarar kayi aure gbdy rayuwarka zata canza zaka rage wasu abubuwa tunda ga zahiri na gani akaina idan akace zan daina shan giya da neman mata zan karyata sai gashi hatta sigari ina neman barin ta "kai dan allah tashi mune garin ma ya sake hadewa da hadari nasan muna kan hanya lokaci zai yi na ajiyeka agida na kara gaba da motarka ."
Mikewa yayi ya shirya kansa sosai tare suka jera har suka karaso haraban gidan babu kowa acikin abokan aikinsu sai mai gadi kadai zaune akan farar kujera mai zaman mutun daya dakin ajiye makamansu ya wuce ya dauki bindiga masu lafiya guda hudu da harsashi ya zuba cikin karamar jaka ya fito inda motar anas take fake ya nufa Ana's ya ciro keyn mota a aljihunsa ya mika masa sannan kowannensu ya bude murfin bangaren da zai zauna ya shiga ya zauna jaguwa ya waiga ya ajiye jakar abaya ya sanya key ya tayar da mota suka bar gidan ."
Suna barin gidan cid ya soma kai kawo a haraban gidan bashi wannan lungu bashi wancan lugun wanda a garin leke lekensa yasan adadin mutanen dake rufe acikin gidan babu wanda ya bashi tausayi kamar alqali mutumin dake kan aikinsa shima fa da asirinsa zai tono wannan ne hukuncinsa agurin jaguwa tunda ya fahimci basa kisa sai izaya suka iya ."
A halin yanzu shi kansa ya matsu wa'adinsa ya cika ya tattara ya bar gidan domin yana matukar jin tsoro yana cikin tafiya yana dube dube kamar ance ya daga idanunshi sama ya hangi wata tukunyar kasa yar karama acikin tsakankanin fulawas din dake shuke a gurin ,bai yi sanya ba ya juya zuwa daki ya kira number dcp ya sheida masa ,"okay to shikenan amman ban zan samu damar fita ba yau dana zo da tukunyar ,no bai nan yanzu ya fita tare da amininsa ."
"Gaskiya bana tunanin suna zargina ,"okay to shikenan sai dai nayi haka ya fito yana waige waige babu kowa ata bangaren da yake dan haka ya dauki kujera ya kai daidai inda yaga tukunyar ya lallaba ya ajiye ya kara tsayi daita yayi bismillah ya dauko tukunyar ya ajiye yana kallon tukunyar babu komai acikinta sai kahon rago da madubi aciki sosai tsoro ya kamashi ." amman hakan bai hanashi yayi fitsari acikinta ba kamar yadda dcp ya fad'a masa ai gama fitsarinsa ke da wuya wani bakin hayaki ya tashi yayi sama ya dauki tukunyar ya mayar inda ya ganta ya lallaba ya bar gurin ."
Jaguwa kuwa tunda da suka shiga mota hirar yadda haduwarsa da commissioner zai kasance suke har suka hau kan babban titi ilu peju a lokacin garin ya sake hadewa da hadari "idan ruwan sama ya sauko allah kadai yasan lokacin da zai tsaya ,nima tunanina kenan ga aiki mai girma agabana fatana na samu nasara haduwa da commissioner suna tafiya ruwan sama ya tsinke kamar da bakin kwarya gbdy jikin anas yayi sanyi dan haka ya dif ya daina magana yana kallon motocin dake falla gudu akan titi ."
wata mota kirar farari baka wuluk ta wucesu da mugun gudu akan titi ilu peju tafiya kadan motar tai ta tsaya a gefen titi direban dake tuka motar ya waigo alokacin da matan daya tuko suke kokarin tmyrsa dalilin tsayuwarsa a halin yaga ana ruwan sama "tayar motar ce ta samu matsala bari na fita na duba na gani ya fad'a yana kokarin fita cikin ruwa , acikinsu babu wacce tayi kokarin hanashi fita sai hirarsu da suka cigaba da yi gashi mutumin ya dan manyata ,tsohon direbansu ne minister ma ya so kwarai ya ajiye aiki amman tsohon yaki a cewarsa zai iya kuma tabbas yana kokari idan gurin tuki ne ."
Boot din motar ya bude ya dauko wani karamin akwati dake dauke kayan gyara ya bude sannan ya duba tayar tan take ya gano matsalarta notikan tayar ne suka dan sake abun daure taya ya dauka ya tsugunna ga ruwan sama na dukansa amman bai damu ba ya fara aiki."cikin haka motarsu jaguwa ta karaso har ta gotasu kadan ya dawo baya yayi parking yana cewa"Ana's "bari na taimakawa tsohon can ya gyada masa kai kawai ,ya fito yana tare ruwa dake dukan fuskarsa da hannunsa har ya karaso gurin tsohon ya tsaya tsayuwa irinta ingarman namiji mai tattare da natsuwa da Kamala, a hankali ya motsa lips dinsa yana cewa "baba kawo na taimaka maka ka koma cikin mota ,tsohon ya dago yana yarfe ruwan dake dukan fuskarsa ya tsurawa jaguwa ido yana kallonsa yana ji dadi acikin ranshi yace "yaro na gode Kwarai da gaske allah yayi maka albarka amman kayi tafiyar zanyi da kaina ."
"karka damu baba ka kawo ya kai hannu ya karbi karfen hannunsa shi kuma tsohon ya shiga cikin mota ya zauna "har ka gama baba ?Aa wani dan albarka na samu zai taimaka min ban taba tunanin har yanzu akwai mutane masu kirki haka a cikin wannan duniyar tamu ba ,shiru tayi hakan nan taji gabanta ya shiga duka uku uku bata sake cewa komai ba ,"Jaguwa ya tsugunna a inda tsohon ya tashi ya kwance tayar motar kadan ya sake daureta tanwer dake zaune bangaren da tayar ta samu matsala kamar tayi warning din glass amman ta kasa aiwatar da hakan sai dai ta kasa dauke idanunta daga kallon gurin ga wani faduwar gaba daya dabaibeyeta ."
Bayan ya gama ya tattara kayan aikin da yayi amfani dashi ya nufi byn boot nan ma zuciyarta ta bishi da kallo sai dai bata dago ba ya bude boot din motar ya mayar masa da akwatin kayan aikinsa ya maida murfin ya rufe yana dagawa tsohon hannu dake kallonsa ta cikin mota sai alokacin tanwer ta waigo sosai ta bayan motar domin taga wanda ya taimaka masu ana tsaka da tsuga ruwan sama byn ga motaci nata falla gudu akan titi karaf idanunta ya sauka akan jaguwa ,gbdy kayan jikinsa ya jike sharkaf har sun bayyana tsayayyun nipples dinsa."
ta kasa dauke idanunta akanshi shima idanunshi
ya tsaida akanta cike da mamaki yake kallonta dan tsantsar mugunta da zalumci shine ta bar tsohon mutane cikin ruwa ita tana hakikce abayan mota lunshe idanunta tayi tana kokarin fitowa daga cikin mota sai dai kafin ta fito har ya juya bata damu ba ta fito cikin ruwan tana kiran sunansa da sauri ruky tabi bayanta da kallo ."
Cikin sauri tanwer tasha gabansa tana sauke numfashi "haba adnan ka tsaya mana ." ransa yayi mugun baci akan wanda yake ciki " me yasa ta fito cikin ruwa tana kiran sunanshi gashi ta jawo duk jikinta ya jike da ruwa har ya nuna sha shin jikinta ?a kallon da yake mata ta fahimci abinda yake nufi yana da tsanani tausayi da kulawa ,tausayinsa ya kamata shi din mutun ne me matukar tausayi ga mutane matsalarsa dai taurin kai idan ya tsaya akan abu babu wanda ya isa ya kawar dashi ko tsaida shi ,tarasa me zatayi domin ta canza shi ya dawo mutumin kirki a idanun duniya ."tsaki yaja sannan ya riko tsintsiyar hannunta cikin nashi atare qirjinsu ya buga da matsanancin karfi ,ji yayi wani shock ya caki jikinsa da duk wasu jijiyo dake aiki ajikinsa,itama haka taji a sansar jikinta,”
maganad’insun son junansu ne ya shiga yawo a jijiyoyin jikinsu sai dai babu wanda yayi magana acikinsu har sanda ya soma tafiya daita bai tsaya akoina ba sai ajikin motarsu ya bude murfin motar sai lokaci yaga ashe ba ita kadai bace aciki ita da ruky cousin dinta ne ,ta bude baki ta gaishesa amman yayi mata banza tamkar bai ganta ba da hannunsa ya nuna mata cikin motar sannan ya raba gefenta ya cigaba da tafiya ya karasa inda motarsu take ya shiga yajata da mugun gudu yana jan tsaki ".
"Lafiya !?Anas ya tmbyesa "wacan motar dana taimakawa tsohon can ashe tanwer ce zaune a bayan motar tsabar rashin Imani da tausayi ta bar tsohon mutane ya fito cikin ruwa ita da cousing dinta suna hakince abayan mota shiyasa naji motar tayi nauyi ya karasa maganar yana murza sterimg yana jan tsaki ."kai adnan tanwer din da consin dinta guda suke da zasuyi nauyi ?bai sake cewa komai ba dan haushi sannan bai tsaya ba sai akofar gidan anas .
“Sauka mana na qara gaba Ana's yace "ka shiga ka sauya wasu kaya mana ."ya girgiza masa kai ya kara gaba da gudu shi kuma anas ya shiga gidan ya zauna a falo sharaf yana jiran princess dinsa ta fito tayi masa sannu da zuwa wacce lokacin tana can tsaye gaban mirrow tana tsara masa kwaliya."
byn ta gama ta karasa wordrobe dinta ta dauko daya daga cikin kayan da ammi ta dinka masu ita da shafiq ta saka ,ta dauko dan karamin akwati dake dauke da sarkokinta kowanne na cikin gidansa tare da dan kunnensu ta dauki wanda take son sakawa ta fara saka dan kunne ta dauki sarka wuya zata saka kenan Ana's ya shigo dakin bakinsa dauke da sallama ."
A hankali ta motsa bakinta ta amsa masa tana sakar masa murmushi ya tsaya a bakin kofar dakin yana kare mata kallo tsab dan ba karamin kyau tayi masa ba ,naunayen ajiyar zuciya ya sauke sannan ya tako zuwa inda take tsaye ya tsaya ta bayanta tare da riko kugunta da hannunsa daya ,Kallo daya tayi masa ta cikin mirrow ta fahimci yana cikin damuwa dan haka ta juyo gabadaya ta zuba masa ido tana sake karamtarshi ,meke damunka ka fita cikin damuwa ka dawo min da damuwa ? girgiza mata kanshi yayi alamun babu ya kai lips dinsa ya tsotsa bakinta kadan ya zare bakinsa ."
Wani wahalallen numfashi ta sauke wani irin zazzafan soyayya take masa tana kallonsa ya karbi sakar dake rike a hannunta ya makala mata a wuya tare da shafa gefen wuyanta sannan ya zagaya da hannuwansa duka saman cikinta cikin kasalalliyar murya yake mata magana acikin kunnenta "my princess kina da kyau sosai a duk sanda na kalleki sai nayiwa allah godiya daya azurtani da samun salihar mace irin ki dan allah ki soni duk runtsi karki barni ".
Murmushi tayi masa ta dago idanunta suka tsarke cikin nashi "nima ina alfahari da samunka matsayin miji ,ya sake riketa gam yana lunshe idanunshi yana busa mata numfashinsa ta hanyar shinshina wuyanta a karshe ya zira harshnesa cikin kunnenta gbdy ta wani rikice tsigar jikinta suka shiga mikewa ta soma kokarin zare jikinta shima a rikice ya sake riko kugunta sosai yasa dayan hannunsa ya hade fuskokinsu guri daya hade da daura lip's dinsa akan nata kasa jurewa tayi dan haka ta sakar masa jikinta ta soma maida masa da martani daga cikin salon data koya agurinsa sun dauki sama da minti shabiyar suna tsotsan bakin juna tunawa da amininsa yasa yayi saurin zare bakinsa cikin nata atare suka sauke numfashi ".Adnan ya tafi ya hadu da commissioner zai dawo ko bazai dawo bai sani ba tharoom dinta ya shiga ya dauro alwala ya fito ya dauki carbi ya zauna ya dan jingina da abun gado yana já ita kuma ta fita daga dakin.”
Bangaren jaguwa kuwa yayi tafiya me nisa daga gidan Ana's sannan ya samu guri yayi parking a daidai Devol hotel dake kan titi alabi ,yayi baya da kujerar da yake zaune ya koma ya kwanta ya runtse idanunshi tanwer kawai yake gani cikin kwayar idanunshi shigar abaya da tayi yayi matukar masa kyau , kowani kaya ta saka sai ya zauna ajikinta ,
bude idanunshi yayi yana tunaninta yana duba lokaci har awa uku ta cika ya kira commissioner Kira biyu ya dauka ya fada masa inda zasu hadu , suna gama waya ya canza fuska ya shirya bindigarsa mai cin harsashi goma ya soke biyu ajikinsa ya sake shirya biyu ya soke a kafafunsa yayi wa na karfasa shiri me kyau sannan ya dauki hanyar water park daman yana kusa da gurin tafiya kadan yayi ya karaso gurin yayi parking ta kofar baya ya fito ya shiga cikin inda mutane suke wasu da rigar wanka wasu kuma suna zaune akan kujeru na alfarma da kaya ajikinsu shima ya samu guri ya zauna ya kirasa a waya "na karaso okay sir ".
Ko cikaken minti talatin bai yi da kashe wayar ba ya soma jiyo qarar jiniya daman yayi tunanin bazai zo shi kadai ba dole sai da masu tsaronsa nan take ya tashi ya boye har suka karaso ciki tare da masu tsaronsa yana maboyarsa yana kallonsa daga inda yake ya kirasa a waya yana kallo aka mika masa wayarsa "kana ina gani nazo ?"Okay sir ina bayan ta gurin swiming pool " kai kadai fa nace zazo ? "karka damu ni kadai ne .jaguwa yayi murmushin gefe baki yana kallonsa yayiwa masu tsaronsa magana wasu suka biyosa ,wasu suka tsaya gbdy ya gama tsara yadda zai kawar dasu ya damki commissioner yana zaune commissioner ya karaso daga nesa jaguwa ya daga masa hannu alamun shine commissioner bai karaso ba ya samu wani guri dabam ya zauna jaguwa ya karaso a natse cike da girmamawa kafin ya zauna
abinda yayi tunani shine ya faru masu tsaron commissioner mutun biyu da suka biyosa suka fara kokarin duba jikinsa sai dai basu ga komai ba boyayyar ajiyar zuciya ya sauke sakamakon basu tabo bidigir dake boye a kafafunsa ba ,commissioner ya nuna masa gurin zama yana cewa "ina bayyana mutuwar honorable Abdulaziz da inda gawarsa yake ?wondonsa yayi sama dashi kadan sai ga wani abu kamar roba shima yayi sama dashi sai ga bindiga ta bayyana muryarsa can kasa yace "ga bayyanan anan " ya fada yana sauke wondonsa yana dubansa a tsanake ".
"Jaguwa !?
Commissioner ya furta ahankali ta yadda babu wanda zai ji dan tun ganin bindiga yanayinsa da komai nasa ya canza jaguwa ya lumshe masa idanunsa yana cewa " nasan ka girgiza da ganina ko ?amman karka girgiza ,nayi haka ne saboda banason na rasa wani na kusa dani ,ku kuma burinku na rasa kowa nawa ciki kuwa har dani kaina, yanzu yanzu ka sallame masu tsaronka kafin muyi mutuwar kasko dan ni da ka gani mutuwa bata tsoratani da shirinta na fito ."
dago kai commissioner yayi yana basu umarni su matsa daga guri babu shiri suka yi nesa dashi jaguwa na ganin haka ya zaro bindiga ya soke ajikinsa yace "oya tashi ko "! kamar wani karamin yaro commissioner ya mike tsaye suka jera ta baya yabi dashi inda motarsa take "banason na taba lafiyar tsoho kamarka amman fa sai kayi abinda nake so zaka tsira da ranka da lafiyarka ."
Cikin mintunan da basu wuce uku ba jaguwa ya fice da commissioner suka nufa inda motarsa yake ya bashi umarnin ya zauna a bangaren direba shi kuma ya shiga baya "ka ja motar muje suka bar area gurin gbdy shi kuma yana baya hakince ya saita kan commissioner da bindiga ,babu wanda yaga saita kan commissioner da jaguwa yayi kasancewar glass din motar baki ne "idan kayi aiki acikin second daya, kaima zan barka acikin second daya kayi tafiyarka ka cigaba da rayuwarka cikin koshin lafiya .”commissioner bai ce komai ba saboda matukar girgiza da yayi ,bama dansa ko wani nasa ba ,ko cikin yaran aikinsa zaa danawa tarko ba shi da kansa ?
"lallai wannan barawon ya wuce yadda suke tsammani"kasa a sako min yarona a yanzu nima na sakeka yanzu Idan wani abu ya samu yarona lallai kasawa ranka mutuwa, ban taba kashe kowa ba amman zan fara akanka muddin wani abu ya samesa ba ."
"Babu abinda zai samesa amman kai ka mika kanka zuwa ga hukuma tunda daman an kamashi ne saboda ya bada bayanai akanka ,idan ka mika kanka nayi maka alkawarin zansa a maka hukunci mai sauki , lokacin dana fara alqallarta kasani ko na nemi shawarka bare yanzu ka bani shawara na dauka"?ni nan da kake gani kamani zai yi matukar baku wuya saboda nayi rayuwa acikinku nasan in and out dinku kai bakayi mamakin yadda na samu number office dinka ba "?"Ace baka bani number ba zan samu kuma cikin sauki kuma na tare da kai ne zasu bani dan haka babu ruwanka kayi abinda nake bukata kawai ka tsira da ranka ,babu waya a hannuna da me zan kira headquarters? sun yi tafiya me nisa sannan jaguwa ya tsaidashi alokacin duhun dare ya shigo dan bakwai da wasu mintuna sun wuce .
Yayinda water park na can ya hargitse adalilin neman commissioner da akayi aka rasa kafin kace me headquarters ya samu labari aiko nan ma ya hargitse ska soma Kokarin baza manya ma'aikata titi titi lungu lungu domin bincike kowace mota jaguwa ya kira number Ana's kira daya ya dauka yana tambayarsa halin da yake ciki "nayi nasarar kamashi abokina kasan na fada maka rikitaccen tsoho ne gashi ma na sashi yin abinda ya jima bai yi ba sai dai ayi masa ,tuki mana ai shi ya tukoni ,sai anjima daman na kiraka né kasan ina cikin koshin lfy dan nasan hankalika bazai kwanta ba yana gama wayar yace "wa zaka kira acikin wadan da suke karkashinka ?
"Mataimakina !"
Ya fada yana sauke numfashi "ina jinka karanto numbersa bai bata lokaci ba ya kirawo masa number sai da jaguwa ya boye number sannan ya kira tare da sata a hands free ,kira biyu cikin na uku A kwantagora ya dauka jaguwa ya manna masa wayar a kunnensa cikin harshen turanci yace "hello kwantagora ni ne commissioner hope baka cikin mutane ?okay abinda nake son fada maka rayuwata tana cikin hatsari ,yanzu abinda nake da kai ka faki idanun kowa ka fito da yaron jaguwa da'aka kama idan ba haka ba sai dai ku tsinci gawata okay!!!
jaguwa ya katse wayar ya gyara zama .
Bayan kamar minti talatin suka sake kira "sir gashi na fito dashi ina zan kai shi ?kaje under bridge din iyanapaja zan turo wanda zai daukesa yaji sautin wata muryar amadadin yaji ta commissioner bance karaka ka tafi da ma’aikatan sirri ba kaje dasu ni kuma nan zanji da commissioner. babu wanda zanje dashi dan allah karku taba lafiyrsa dan ….”
Jaguwa bai tsaya jin me zai ce ba ya katse kiran
Hankali a tashe kwantagora ya figi mota ya dauki hanyar iyana paja shi kuma jaguwa ya kira layin eku ya bashi umarni zuwa iyana paja cikin mintuna talatin kwantogora ya isa sai dai dole yayi parking ya jira kira daga jaguwa ,alokacin shima eku ya karasa ya kira jaguwa ya sheida masa nan take ya kira number kwantagora yana dauka yace "kana daidai ina ?
"Ina daidai inda ake shiga motar ondo ,da uniform ne ajikinka ?eh !Ya katse kiran ya kira eku sukayi mgn sannan ya sake kira kwantagora yace ya bawa scorpion waya ya mika masa wayar sukayi mgn suna gama waya kawai yaga scorpion ya fito daga cikin mota yana dingisa kafasarsa tun yana iya hangosa har ya daina akan titin mowe ibafo jaguwa ya ajiye commissioner ya kara gaba ."
A tare jaguwa da eku suka karaso gida gbdynsu babu wanda bai yi mamaki ganin Scorpion dan basusa rai zai fito acikin kwana daya ba ,lokacin da jaguwa ya fad'a musu abinda yayi kafin scorpion ya dawo sunyi matukar jinjina masa,a daren ya kira likitansa tazo tayi masa allura ta rubuta masa magani sannan eku ya taimaka masa ya shiga bayi yayi wanka dan jikinsa Kmr gyenbo yake jinsa.
kwana daya kawai da yayi a hannun police yaji kamar kwanaki dubu yayi ya kalli jaguwa da idanunshi daya kunbura "police basu da Imani a gobe suke shirin min izaya ta karshe duk da bansan wacce irin izayya zasu min ba a fadar wani police naji
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 55 Chapter of 67