You Cannot Download this book untill you login but you can read it .
Login Register
idanunta tana kallonsa sannan ta sake fashewa da wani sabon kuka da take Jin radadinsu har cikin zuciyarta Nan take tausayinta yasa hawayen minister suka zubo bakinciki kamar ya Kai mumy lahira "kiyi hakuri ki kwantar da hankalinki Zainab wannan jarabawa ce daga Allah Babu Wanda ya Isa ya Hana Hakan faruwa ,ban son ki cigaba da tsananta damuwa domin zata jefaki cikin mummunar matsayi ki dogara da Allah shine zai magance komai mu ma godewa Allah da qaddara ce ta fad'awa tanweer ba bin Maza take ba.
" Aranshi yace Ina ma zan iya goge *kuskuren baya* dana aikata hakika na tafka kuskuren gashi ya shafi yaruwar dilon diyata .Ta goge hawayenta tayi iya yinta ta tashi zaune ta kasa yace karki damu da sai kin tashi yanzu kiyi kwanciyarki ki huta bari na kwaso magunhunaki naga Wanda ya dace ki Sha .
Ya mike da sauri wani duhu ya rufe idanunshi baya ganin komai sai wasu taurari dole tasa ya dawo ya zauna Yana furta hasbinallahu wa ni'imal wakil yayi ta maza ya sake mikewa mumy tace "ka zauna karkaje ka fadi ka nakasa bai kulata ba ya fice dan yafi bukatar rayuwarta akan tashi .
bai dade ba ya dawo d'akin da kwadon magungunanta ya zauna yana bincikawa jikinsa na rawa
Saboda bacin rai Amman haka ya daure ya d'auki kanta ya d'aura saman cinyarsa yana mata sannu ya goge mata kwalla sai daya kwantar mata da hankalin sannan ya mike ya nufi dakin tanweer cikin tsananin tashin hankali.
tana kwance tayi ruf da ciki ya tsurawa bayanta Ido daman wannan shine karshen masu halin munafurci irin nasa, karshen mai son zuciya kenan, Kuma duk Wanda yaci bashin Allah sai ga karshensa tun anan gidan duniya ,sannan karshen mai irin halinsa kenan dansani.
a yanzu ya gane kuskurensa da yayi tsawon shekaru yana aikatawa a boye ,ya goge kwallan data zubo masa ya kirasa sunanta "tan!
Ta juyo a natse tana fuskantashin "Tashi ki shirya muje hospital a cire miki cikin " da sauri ta shiga girgiza masa kai alamun bazata zubar .Wani irin juya ne ya soma dibarsa nan kuma ya shiga furta Kalmar Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun yana maimaitawa cikin haka mumy ta rarrafo ta shigo d'akin adaidaita lokacin da dady yake sake bawa tan umarni "ni dady Abar min abuna ina so ..."
"Kina son me dan ubanki ?"me zakiyi dashi ? kina hauka ne Ko kin fara Shaye shaye ne ?"tayi mata tmbyr ajere juya na sake dibarta kafin kace me tuni ta soma yin kasa da sauri tanwer ta sauko daga kan gado suka hadu da dady a lokacin da take kokarin kaiwa Kasa da kyar take fidda numfashi bakinta na rawa tace "tan..! tan !! ki amince a cire cikin ...."
Assalamu alaikum yan'uwa barkanmu da wannan lokacin jama'a , ku taimakawa wannan baiwar Allah Mai suna rukayya wacce ta kasance budurwa ce tana fama da ciwon no-no tsawon shekara daya Kenna saboda iyayenta basu da halin da zasu dauki nauyinta yasa brest dinta d'aya fara lalacewa , rukayya tana zaune ne a garin Kaduna a unguwar kanawa tare da iyayenta dan Allah ku taimaka mata saboda Allah da darajan fiyayyen halitta annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam ga masu bukatar taimakawa ga account number nan 1438775094 Aishat Abdullahi access bank .Domin Jin qarin bayani a tuntubi wadan nan numbobin
07039569430
07037450698
08059623096
Allah ya bada iKon taimakawa .
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
"Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan an tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️24
Mumy bata qarasa maganarta ba numfashinta ya sake tsarkewa idanunta na faman zubar da hawayen tashin hankali ," Ina ta ta'ba ganin balai irin wannan , Allah ya rufa maka asiri ka nemi ka tonawa kanka, dady kuwa duk ya rud'e ya gigice sai zufa yake fitarwa da kyar ya bud'e bakinsa yace "zainab ki rufa min asiri dan girman Allah karki d'aga min hankalinki da sannu zata fahimcemu ta janye kudirinta. mumy taja numfashi da kyar ta sauke ta sake fashewa da kukan bakinciki
ita abinda ya d'aure mata kai mai yasa tanwer zata ce abar mata cikin "?
"To tayi meye dashi ?" cikin muryar kuka tace "da kunnenka kaji abinda ta fad'a wai tana son abunta ". ta k'arasa maganar tana zubar da hawaye.
nan take tausayin mumy ya kama tanwer bisa kuncin data jefa mahaifiyarta muryarta na rawa tace "mumy kiyi hakuri " ta k'arasa maganar tana zubar da ruwan hawaye mumy ta sake matso ruwan hawaye "tayi hakuri akan me Kenan" ? " akan zata yarda a zubar da cikin Ko kuma bazata yarda ba ?"
"Sannu zainab komai zai daidaita inshaallahu tanwer yarinyar ce har yanzu batasan ciwon Kanta ba ,batasan rayuwa ba sai mun zaunar daita mun fahimtar daita illar abinda take son jefa rayuwata ".mumy ta sake runtse idanunta gam jikinta na wani irin rawa saboda bacin rai ."
Sallama suka jiyo daga parlour babu tantama muryoyin yan'uwanta ne take jiyowa bashir da Jamil da sauri dady ya jinginar da mumy ya nufi waje yana fad'in " gamu anan ku shigo ya fad'a tare da juya ya Koma d'akin ,suka biyo bayansa jugun suka ga yayartasu ta rasa kuzarinta. "yaya dai aunty meke faruwa dake ba dai jikin bane ya tashi ?sun fadi haka ne saboda zuciyarta data soma ciwo adalilin dauke tanwer .
dady yace "shine dai yake k'okarin tashi bashir , nan take suka zube gabanta kamar zasuyi mata kuka uncle Jamil ya d'auki Kanta ya d'aura akan cinyoyinsa yana cewa "sannu auntynmu !shima bashir sannu yake mata faman jera mata
sam hankalinsu bai ga tanwer ba ta matso kwalla ta dubesu d'aya bayan daya "kunzo lafiya ?"ya mantaku da yaranku suke "? suka had'a baki suka amsa mata da "lafiya suke sunce agaisheki "ina amsawa ta k'arasa maganar da kyar wasu sabbin hawaye na gangaro mata ta gefen Ido bashir ya goge mata kwalla ,Kannenta uwa d'aya uba d'aya itace babbarsu su hudu ne agurin iyayensu kuma sun mutu sun barsu maza uku ita kad'ai ce mace acikinsu shiyasa ma ta d'auki soyayyar duniya ta d'aurawa tanwer duk da bata rasa kulawa da gata da komai ba daga gurinsu dan sun maye mata gurbin komai duk abinda tace shi sukeyi kafin ma tace sunyi mata suna tsananin qaunar junasu ."
Ahankali suka dubi dady suka gaisa kafin su sake wata magana dady ya fad'a musu komai dake faruwa duk sukayi shiru tare maida hankalinsu inda tanwer ke durkushe tana kukan zuci .
Idanunsu na Kanta na tsawon lokaci kafin uncle Jamil ya dube uncle bashir sannan ya cire kan mumy ya d'aura a jikin dady ya k'arasa inda take cikin hanzari yasa hannu ya fizgota ba karamin tsoro ya bata ba ta kwalla qara tana rike cikinta
tare da furta "wayyo Allah cikina ". wani bakinciki ya qara turnukesu bai san lokacin daya buge mata baki ba yace "maza ki rufe mana baki shasha banza shashar wofi Kawai " .
da sauri tasa hannu ta dafe bakinta wanda take kyautata zaton hakoranta zasu iya ficewa su bar bakinta Idan bata dafe bakin ba "jawota yayi kiiiiiii bai direta akoina ba sai a gaban mumy ta zube har tana cin karo da gwiwar mumy ya zaro mata Ido kamar zasu fad'o waje mumy tace " matsa kusa dani dan zan iya shake miki wuya ki mutu na huta".
da sauri ta janye jikinta dan wani irin tsoron mahaifiyarta ne ya shigeta, a hankali hawaye ke ambaliya a fuskarta sun fi minti biyar jugun jugun babu wanda ya sake cewa komai saboda takaicinta.. "gbdy kina son ki rusa rayuwarki, ki lalata asalinki, me zakiyi da wannan ciki ?"bari kiji idan ma kin barshi babu abinda zai janyo miki sai bakin fanti da cila rayuwarki cikin garari , sannan babu mai aurenki da dan shegen 'yanta'ada dan haka wannan cikin dole a zubardashi tana jin haka ta sake fashewa da wani sabo kuka .
gbdy suka nemi natsuwarsu suka rasa ji suke Kamar zuciyarsu zata buga wallahi sun san da soja yana kasar to da sai ya balbalata yayi gudunwa gunduwa daita dan ya tsani ganin mumy cikin damuwa bare kukanta uncle Jamil jikinsa sai tsuma yake yana faman jan tsaki ."
A natse uncle bashir ya mike ya riko hannunn tanwer ya nufi waje daita , ta gaban abokan dady suka wuce dan suna zaune har lokacin a matukar firgice suka bisu da kallo "Kamar tanwer nake gani Ko kuwa idanuna ne?" inji cewar alhj Lawan Shuaib "ba idanunka bane itace "a'a to yaushe aka dawo daita da bamu sani ba ?" wa zai baka wannan amsar tunda duk yanzu muka ganta .?alhj rufa'i ya fad'a yana kwabe baki.
Kai tsaye part din mumy uncle bashir ya nufa daita ya murda handle din kofar suka shiga ya zaunar daita abakin gado shi kuma ya janyo karamar stood ya zauna ya fuskance na tsawon lokaci sannan ya fara magana jiki a sanyaye "tan....!
Ta d'ago runannun idanunta da suka kode tsabar kuka ta zuba masa tana jiran taji mai zaice "mai yasa baki son a zubar da cikin nan ? "tayi shiru tare da sunkuyar da kainta kasa wasu hawaye na sake gangaro mata suna diga a tafukan hannunta.
" kiyi hakuri my daughter a zubar da cikin nan babu abinda zakiyi dashi barinsa bai da wani amfani ,wannan cikin matsala ne a rayuwarmu gbdy".
on-expecting yaji sautin muryarta cikin dodon kunnensa "yanzu uncle bashir zaka jagoranci kisan kai ?" take zufa ya shiga tsatsafo masa hankalinsa yayi mugun mugun tashi", wannan cikin dole na haifesa domin yunkurin zubar dashi yafi samunsa barna da ta'addanci da tarin zunubi .
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ya dinga furtawa had'e da mikewa tsaye cikin tsananin tashin hankali ya shiga zagaye d'akin yana maimaitawa abinda ta fad'a gumi na sake karyo masa duk da gudun ac dake aiki a d'akin amman hakan gumi ke tarara ajikinsa kamar ruwa kwakwaluwarsa ta hargitse
tana hautsinewa cike da buguwar zuciya ya tsaya cak a tsakiyar d'akin yana kallonta tare da nazarinta a matsayinsa na barrister take ya hango wasu abubuwa a tattare daita a hankali ya lumshe idanunshi tare da sanya hannunsa a daidai saitin zuciyarsa ya dafe dan wani irin bugawa take saboda abinda ya zowa zuciyarsa ,still idanunta basu daina zubar da hawaye ba cikin kasa da murya ya kira sunanta "tanwer !
Idanunta ta sake da d'agowa wadan da suke cike da ruwan hawaye ta kalli uncle bashir murmushin takaici ya sakar mata wanda yafi kuka ciwo.
"ba cikin kike so ba wanda yayi cikin so Ko idan na kintata daidai ?"shiru tayi tana tunanin amsar da zata bayar kafin idanunta su sake Kawo wasu ruwan hawaye .
Ya numfasa ni kadai ne anan ki fad'a min gaskiya zan fahimceki. "wannan gaskiya ne uncle ina son shi sosai ,ina masa son da bazan iya zubar da gudan jinsa ba ". ware idanunshi yayi sosai akanta yana cewa "are you out of your sense dan fashin kike so tanwer? shiru tayi tana nazari cikin zazzafa murya yace "why tanwer ?"me yasa zaki mana hk ?mai yasa zuciyarki zata kamu da sonshi ?"a Ina ma kika san zaki qara ganinsa ?"mutane da ba guri d'aya suke zama ba Ke yanzu kina tuninin zamu yarda dashi ne ?"
Da sauri ta rike masa hannu tana cewa" dan Allah uncle ka taimakeni Adnan mutumin kirki ne qaddara ce take yawo a rayuwarsa, wallahi idan kagansa bazakace dan fashi bane,yana da kirki da kamala da tausayi ...."
"Tausayin banza da wofi yana tausayi ya kwana dake ?yayi maganar yana k'okarin cire hannunsa cikin nata ta sake rikewa gam"wayyolhhly Allah ka taimakeni uncle ta fad'a jikinta na rawa Ina son shi wallahi zan iya mutuwa akanshi, zaku rasani akanshi, ni dai ina sonshi .." da sauri ya runtse idanunshi kafin ya fizge hannunsa cikin nata, kuka take sosai tana rokonsa amman Ina a fusace ya juya ya bar d'akin zuciyarsa na bugawa da karfin gaske . "
A falo sukai cikibis dasu dady sun kamo mumy da sauri ya karasa ya sa hannu suka nufi d'akin dady daita, nan fa hankalin mutane dake zaune falon yayi kansu atare suka mike tsaye suna kallon juna "Ku da alamun gidan nan babu lafiya ,nima abinda na gani Kenan mu wuce Ko mu tsaya neman qarin bayani ?"gasky gara mu tsaya muji Ko meke faruwa suna cikin tautaunawa sai ga dady ya fito daman niyyarsa ya sallamesu kowa ya kama gabansa ,cike da damuwa suka matsoshi suna tambayarsa "fatan dai lafiya zainab take Ko jikin ne ?"eh jikin ne amman da sauki yanzu likinta nake shirin Kira "okay to Allah ya kara sauki inji cewar alhj rufa'i dady na gama magana ya nufi kofar fita dole tasa suka biyosa alhj hamisu yace"Ashe kuma tanwer ta dawo ?"eh! Kawai yace ya kara gaba ya nufi inda motarsa take fake ya shiga ya zauna tare da kunnata kamar zai fita hakan yasa kowanensu ya sha jinin jikinsa ya nufi inda motarsa take dan ga dukkanin alamun yana bukatar su bar masa gidansa dan haka suka soma k'okarin barin gidan zuciyarsu cike da sake sake Kala Kala .
yana ganin fitarsu ya fito daga cikin motar ya nufi cikin gidan
a falo suka hadu da tanwer tana daga kafafunta da kyar ,tana ganinsa taja ta tsaya ta kasa cigaba daga kafafunta da idanu ya bita yana matukar jin tausayin diyarsa dan bashir ya sanar masa da yadda sukayi daita ,jiki a sanyaye ya karaso inda take ya riko hannunta, zafin jikinta ya ratsa tafin hannunsa bai ce uffan ba ya shiga dakinsa daita .
Suna Shiga d'akin mumy ta mike zaune da kyar ta soma magana cikin zafin zuciya "wato burinki daman ki ruguza rayuwarki da taimakon kanki Ko? " wallahi danasan haka zaki dawo ki zame min da ban daga hankalina a lokacin da suka tafi dake ba ,Ke dama basu dawo min dake ba da sun rikeki kin cigaba da rayuwa agurinsu , wallahi idan kika bar cikin nan wulakanta zakiyi zaki wulakanta tanwer wannan abun kunya ne duk da qaddara ce ta janyo miki haka amman abun kunya ne mumy takarsa mgnr tana girgiza kai ".
"Dan Allah Zainab ki natsu ki kwantar da hankalinki ,wannan bashi bane mafuta dady ya fad'a "yanzu dai meye abunyi ?"Jamil ya fad'a dady yace "abun yi shine a zubar da cikin "wannan dole kam a zubar dashi Idan ita mahaukaciya ce mu da hankalinmu ai .
uncle Bashir ya gyara zama gaskiya bazata haifi cikin ba ta daurawa aunty ciwo Idan ita bata bukatarta araye mu muna bukatarta dan bamu da wacce yafita a zukatanmu ,bamu da Wani burin daya wuce mu rayu tare dake auntynmu kar bacin ran yasa ki dakatar mana da farincikinki .
Hawaye suka zubo ma mumy ucle Jamil yayi saurin rungumota jikinsa yana share mata hawaye "ki daina kuka idan kina kuka kina kara daga mana hankali ,ki daure awanni ne kawai sukayiwa cikin saura arabata dashi .
Tace "na gode kannena Allah yayiwa rayuwarku albarka kema tanweer zo kusa dani ta fad'a tana mika mata hannu, dady ya rikota ya kawota gurin mahaifiyarta mumy ta rike hannunta gam cikin nata "kiyi hakuri tanwer ki rabu da wannan ciki nayi Imani da qaddara kuma nasan komai daya faru dake qaddara ne bana jayayya da Ikon Allah sannan bazan juya Miki baya ba amman nayi bakinciki cikin nan duk da hallitar Allah ne, wallahi da zan iya dana bar miki duba da haihuwar muke so Ke kadai fa allah ya bani taya zan so ki cire ciki ?dole ce tanwer ,ki bari acire kinji Allah yayi miki albarka kuma Allah yayi muku albarka."
suka numfasa suka ce" ameen kuka tanwer take sosai Kamar ranta zai fita ta zura musu Ido hawaye nata zuba a idanunta
ta kasa cewa komai domin ita Kanta batasan me zatace ba game da matsayar ciki jikinta
ta rike hannun mumy gam tana kuka Kamar zai fada zuciyarta bakaramin rikita dady tayi ba dan bayason kukanta da sauri ya juya ya bar d'akin ya dawo falo yana cigaba da goge hawaye zuciyarsa nayi masa ciwo ,wani irin bakinciki yake ji a zuciyarsa da gangar jikinsa .
Jiki a sanyaye ta yunkura da kyar ta fito daga dakin zuwa nata zuciyarta cunkushe da bakinciki wayarta ta lalubo ta soma rubuta ma jaguwa sako Kamar haka .
_Slm Adnan I don't why my heart is telling me you can do that to me there's something behind, dan Allah ka kirani yanzu naji muryarka ina cikin tashin hankali mai tsanani muryarka Kawai bance ka aureni dole ba naji muryarka zai qara min kuzari da kwarin gwiwa idan baka kirani ba zan mutu 😭😭😭 Ina sonka banason na kai kararka gurinka_
Ta tura masa tare da rike wayar tana jujjuyawa ta rasa dalilin da yasa ta kasa fada masa cewar tana dauke da ciki ,wallahi da tana cikin haiyacinta baza taba daukar jikinta ta bashi ba dan tasan Ko tabashi ta dadin rai shima wulakanci zai zame mata, yanzu ma da fyade yayi mata tana gani jala inaga itace ta bashi da Kanta ,ita Kanta bata taba zaton zata tsinci rayuwarta haka ba Kusan minti talatin tana zaune tana jiran ta gani zai Kirata Ko kuwa , aikuwa yadda ya saba haka yayi mata yaki kira ta fashe da kuka ta sake tura masa wani sakon .
_sakomakon fyaden da kamin mahaifata ta d'auki cikinka sai ka Kira asan yadda zaa yi dashi_
Byn ta tura ta koma ta kwanta lamo tana tunani rayuwa tana fitar da mumfashi sama sama Kamar daga sama taji shigowar sako da sauri ta zabura ta mike ta zauna tana adduar allah yasa shine ilai kuwa sakonshi ne ya shigo sai dai ba abinda tayi tsammani ta gani ba dan cewa yayi .
_ai likita ce ke dan haka ki cire mana, meye ma na fad'a min cewar kina dauke da cikina?" ni babu abinda zanyi dashi kema kuma nasan babu abinda zakiyi dashi abort it_
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta tare da daura hannunwanta duka saman Kanta nan take ta shiga wani yanayi na kuncin rayuwa wanda ya wanzar mata da cututtuka masu yawa ajikinta kafin kace me tuni ta rikece ta sake tura
masa wani sako .
_Burinka dama ka rugaxamin rayuwa, burinka kuma ya cika sai dai kasani Ko sama da kasa zasu had'e bazan zubar da cikin ba tunda nasan abinda kike bukata Kenan na zubar da cikin jikina ,sai abu na gaba ka jira sanda zan haife abinda Ke cikina Idan ka ga dama ka karba danka Ko yarka Idan baka karba ba na kaiwa mahaifiyarka amman kasani Sai kayi nadamar abinda Kamin karshenka dana sani arayuwa Allah ya Isa tsakanina Da ka_
ta tura masa sakon tana goge kwallan da suka zubo mata bisa kuncinta sannan ta sauke numfashi ta koma ta jingine bayanta da abun gado tana tunanin mafuta dan dole ta samowa Kanta mafuta kafin gari ya waye Kwanciya tan tayi cikin tashin hankali da faduwar gaba tuni kwakwaluwarta ta amince mata da maganar mahaifiyarta "na amince azubar dashi mumy, kuyi hakuri mumy da jainja da nayi daku ku yafe min ..."
Tunda jaguwa ya karanta sakon tanwer na karshe sai ya dan shiga tashin hankali sbd jin zata kaiwa mahaifiyarsa amman kuma daya tuna batasan kowa bashi ba sai ya dawo daidai ya Shiga jan tsaki ,ya mike tsaye tare da doguwar mika mai isar da sakon gajiya, murmushin gefe baki yayi ya dan yi taku daya biyu ya tsaya yana furta" tanwer Kenan kina dauke da ciki kuma ba zaki zubar dashi ba to me kike nufi da ba zaki zubar ba?
"anas ya shigo dakin a lokacin da yake furta hakan a fili "Yaya dai mutumina ? naga Kamar kana cikin damuwa ?ya numfasa amman bai ce uffan ba "ya Ina Magana kayi banza dani lafiyarka Kake Magana kai kad'ai ? ya sake sauke numfashi yace "ina fa lafiya tanwer na dauke da cikina "
gaban anas yay mummunar faduwa"ci me .."?
"Wai ciki gareta kuma bazata cire ba."Anas ya saki baki yana masa kallon mamaki mai cike da tashin hankali ganin Kamar hankalinsa akwance.
jaguwa ya kwashe da dariya yana dafe goshinsa "meye abun daga hankali Kamar kai kayi cikin ?"
cikin tsananin tashin hankali Anas yace "ban sanka da rashin Imani ba kai din mutun ne mai tausayi da sanin yakamata dan Allah ka amshi cikin nan tunda tace bazata cire ba ka aureta Kawai karka ruguza mata rayuwa babu wulakancin da yafi wanda kayi wa tanwer Ko tanko gote bakayi masa wannan hukuncin ba ,ka barshi yana yawonsa son ranshi .
ya zauna kan kujera yana cewa "Na amshi cikin nayi me dashi ?
"me akayi dashi ?"idan baka so ka karba ka bani dan gsky aure zanyi tunda kai bakasan zuru ba an zura maka Ido aga ko zakayi amman sai wasu abubuwa kake ni zanyi aure ka amshi cikin ka bani". jaguwa ya bishi da kallo yana kada kai kafin daga baya ya kwashe da wata dariya "lallai Anas aure abun yayi min dadi a ina kasamo matar?"bansani ba dan rainin hankali Kawai ".
Aure zanyi na haifi ko d'aya ne kar na mutu bani da masu min addua samun sausauci .
"Matsalar Kenan Duk kwanakin da zarar ana magana zaka fara Kawo batun mutuwa ,zamu mutu amman ba yanzu ba anas ya bud'e baki zai yi mgn jaguwa yace "kaga malam karka ce komai ga sauran kazar da nacan na rage maka kaci kaji dadinka ya juya zai shige bedroom dinsa Anas ya rikoshi ya marairaice.
" dan Allah Adnan kayi hakuri ka lallaba yarinyar nan ta zubar da cikin ta dadin rai ,yadda kake mata din nan zai bugar mata da zuciya tana bukatar rarrashi da kulawa , jaguwa yay masa wani irin kallo mai hargitsa kayan ciki "dan Allah ba dan ita ba ."
Ya numfasa kana yace" naji zan kiranta "yauwa to Ko kai fa dan Allah ka lallaba ta kaji abokina. Baice komai ba ya wuce zuwa uwar dakansa ya hau kan katifa ya kwanta ya janyo blanket ya rufe rabin jikinsa sannan ya lalubo wayarsa ya ya fara neman layinta kira d'aya ta d'auka qirjinta na buga da sauri sauri tsayawa tayi batare da tace komai ba shima shiru yayi na kusan minti goma yana sauke mata numfashinsa a kunne kafin daga bisani yace "hello ..!
Shiru tayi tare da kasa kunne tana jin zazzakar muryarya mai kashe jiki ,a hankali ta dinga jin wasu abubuwa na yawo ajikinta cikin zazzakar muryarsa yace "ya kike ?"a hankali ta bud'e bakinta "yanzu Adnan ka kyauta min Kenan ? lafiya muka rabu da kai fa,a tunanina kira d'aya idan kagani da kowacce number zaka biyo Kiran a tunaninka ko nice amman sai kayi watsi dani.
cikin murmushin yace "kiyi hakuri yanzu ya kike jin jikinki ".
gumin dake tsatsafo mata a bisa goshinta ta goge tana sauke numfashi hade da cewa "gani nan dai sai hankali wahala nake sha gashi kace a zubar da cikin saboda baka qaunata sai dai ni bazan zubar ba ina son abuna .."
Naunayyen ajiyar zuciya ya sauke da karfi ya kamo lips dinsa na Kasa yana cizawa a hankali yana yabi yatsun hannunsa da kallo dan tunanin Kalmar da zai
Book Chapters
Chapter 31
Chapter 32Chapter 33Chapter 34Chapter 35Chapter 36Chapter 37Chapter 38Chapter 39Chapter 40Chapter 41Chapter 42Chapter 43Chapter 44Chapter 45Chapter 46Chapter 47Chapter 48Chapter 49Chapter 50Chapter 51Chapter 52Chapter 53Chapter 54Chapter 55Chapter 56Chapter 57Chapter 58Chapter 59Chapter 60Chapter 61Chapter 62Chapter 63Chapter 64Chapter 65Chapter 66Chapter 67