sannan jijiyarsa bata tashi amman da zarar ya kusanci Inda take sai ta mike ta tashi sosai shi kansa yanzu yasan idan ya mayar daita zai shiga damuwa ko dan abubuwanta .
****
Zahra ,hafcy no-no ,Saira suna zaune a falo sai sukaji knowking Saira ta tashi ta bud'e kofa police men guda biyar ta gani tsaye "muna son ganin "Zahra !
Saira dake tsaye tace "Zahra ! suka gyada mata Kai alamun "eh ! ta kauce ta basu hanyar shigowa dan batayi tunanin wata matsala bace a tunanin me gidansu ke son ganinta tunda tasan akwaita da kan masu kudi suna shigowa suka yi wuri wuri suna raba idanu suna son gano fuskar hoton da'aka basu.
cikinsu babu wacce bata tsorata ba most especially Zahra suna gama ganota suka tunkari Inda take zaune "are you Zahra? da kamar tace a'a sai Kuma tace" eh! "Okay muje me gidanmu na son ganinki tace "waye kenan me gidan naku ?"idan muje zakiga ko waye ki hanzarta please " ta mike ta d'auki karamin mayafi baki ta yane kanta dashi dan a shiryenta take ta fito suka wuce har suka Isa station tunanin waye wanda yasa a d'aukota take .
Kai tsaye office din dcp aka zarce daita suka Sara masa sannan suka ce "sir ga ta nan da hannu yayi musu alamar su wuce "ki zauna mana ya fad'a yana nuna mata gurin zama ta zauna a Inda ya nuna mata tana jira daga garesa qirjinta na dokawa da karfi byn kmr minti biyar ya dago yana cewa "Zahra ya jaguwa ? lumshe idanunta tayi sannan tace" yana gidansa "gud ko zan iya sanin halakarki dashi ?"eh to saurayina ne da na bukaci muyi aure dashi yaki "
ko kinsan aikinsa ?ta girgiza Kai da sauri ban ta'ba sanin aikinsa ba Sannan Ban ta'ba tmbyrsa ba "ya gyada mata Kai ",fashi da makami ne aikinsa "what ? Zahra ta furta a matukar firgice tana zaro idanuwanta waje "impossible gsky ban yarda ba, nan take ya shiga mata bayani a karshe ya kunna mata duk maganganun da sukayi dashi tabbas muryarsa ce babu mutsu muna son mu kamashi ko kinsan sirrinsa? tayi shiru tana nazarinsa " idan kika bayyana mana sirrinsa zamu baki million goma " ta sake yin shiru tana sauraronsa da tunanin million goma , ya cigaba da fad'a mata duk hanyar da suka bi amman basuyi nasara ba
"gbdy yadda kuka shirya gurin kamashi ba tsari bane "
" me yasa kika fad'i haka ? "tamkar kuna lalube ne cikin duhu , kun samu bibiyesa fiyye da sau hamsin amman bakuyi nasara akanshi ba saboda baku da wani Abu guda daya da zaku iya rikewa a matsayin hujja ko tabbacin yadda zaku kamashi byn muryarsa kunga har yanzu akwai sauran rina akaba kenan "
"nayi yawo guraren da dama akanshi duk Inda naje ba'a nuna min waye shi har sai da muka hadu da Kai yanzu sannan nasan waye jaguwa ,abinda wani malamina ya fad'a min jaguwa nada mugun asiri ajikinsa ya fad'a min cewar muddin ana son akarya asirin jikinsa sai an daidaici lokacin da bai tashi a bacci ba, ma'ana a rusashi yana kwance yana bacci akan katifarsa to fa a wannan lokacin dole asirin jikinsa ya karye kunga ku Kuma dole ya kamu a hannunku ni Kuma dole burina ya cika akansa amman matswar ba wannan lokacin ba asirinsa jikinsa bazai karye ba sannan batun diyar minister Shima malamina ya fada min ya kamu da balain sonta bazai iya rabuwa daita ba Ina ganin shine dalilin da yaki dawo daita ."
"yanzu me kika ganin za'a yi mu rutsashi yana bacci ?",dole sai munyi dogon nazari akan haka "Yanzu kirawo numbersa tunda kina daita muji ko zai dauka "wannan ma wani sabon tashin hankalin ne, yaushe rabon hakan a tsakaninmu dashi ?mutumin dake gudun haduwa dani sai dai duk every each hour Ina samu rahoto akanshi ."
"Shikenan yanzu ki bani numbersa "Taya zan baku numbersa byn Kun Saba tautaunawa dashi ?"duk sanda zai kiramu yana boye number ne,ki taimakawa kasarki kiyi aikin alkhairi ko sau daya arayuwarki, wannan mutumin dan ta'addane da bai dace ya cigaba da rayuwa ba shiru tayi kawai tana tunanin ta bayar ne ko karta bayar byn kmr mintuna shabiyar tace "zan baka Amman kasa baseera sosai dan yana da matukar hatsari "na dade da sani wannan ta Karanto masa number yayi dialing a wayarsa ya soma kira alokacin jaguwa na d'akin Jim dinsa yana motsa jiki yaji shigowar kira wani irin tsalle yayi ya danna bluetooth din dake ajiye a gefensa ya manna a kunnensa "hello.." jaguwa yayi shiru sakamakon ,jin muryar dcp bai gama tunanin Inda ya samu wannan layin nasa ba ya cigaba da Jin muryarsa "muna sane da halin da kake ciki yanzu amman ka sani karshenka yazo lokacin kamaka yayi."
"Kai ka tabbatar da hakan jaguwa ya fad'a tare da gyaran abun kunneshi ya kife hannuwansa duka akasa yana motsa jiki ?kwarai kuwa Kuma zaka gani , "meye abun maimaita magana daya Koda yaushe yalla'bai ?
"wai ma meye abinda kake gadara dashi da abinda yake baka wannna kwauri giwar da har kake aikata wadan nan abubuwan ?
"Ka sausauta yalla'bai wannan ba abun tada hankali bane ya fad'a yana mikewa tsaye ya kakkabe hannunsa "duk wani shirina na rigada nagama tsarawa aikatawa ce kawai ta rage min adadin mutane da zan yiwa fashi a lisafe suke ya fad'a tare da yin tsalle ya rike kerfe yana sama da kasa jikinsa na budewa " Ku daina bincike da bin kwakwafi akaina dan babu wani abu da zai amfana muku dan bazaku ta'ba samun komai ba sai darasin rayuwa kawai .
"ka kiyaye kanka dan randa zaka shigo hannunmu zakayi da kasani ....
"daga murya fa ba komai bane agurinmu, masu laifi ake d'agawa murya Kuma kunsan Inda suke , dcp yayi shiru yana furzar da iska sannan yace "me kake bukata zamuyi maka muddin zaka dawo da yarinyar nan ?"murmushin gefen baki yayi nasan karshe abinda za'a sake tmbyata kenan "me yasa sai akan diyar minister zaku kasa zaune zaku kasa tsaye ?"oho a she fa ita diyar me kudi ce ko ?
"ba wannan muka tmbyeka ba abinda kake bukata muke so jin ",ku shiga cikin gari akwai Yara irinta bila'adadin da akayi garkuwa dasu wasu sun mutu wasu suna raye zaku iya zuwa ku taimakawa wadan da suke raye, sau daya kawai kayi aikin alkhairi idan Kuma zaka had'a Kai dani ni din simple man ne ya karasa mgn tare da janyo rigarsa ya saka "kayiwa Allah karka manta kaifa Muslim ne"
"cikakke kuwa "to ka dawo da yarinyar nan "naji kubani lokaci na kammala abinda nake a karshe ma ni ne zan nemiku ba sai Kun Sha wahalar nemana ba yana gm fad'ar haka ya katse Kiran duk ya hada gumi tunaninsa Inda suka samu numbersa Kai tsaye ya fito cikin tsananin damuwa d'akinsa ya shigo ya wuce bayi ya tsaya cikin bathtube ya Kuna shawa a hankali ruwa ke sauka ajikinsa sosai ya shiga kogin tunani"Ina suka samu wannan number sosai kwalkwawarsa ta shiga lissafi ya dade ruwa na sauka ajikinsa sannan ya fito ya goge jikinsa ya zira jallabiyar deep blue ya fito falo ya goya hannuwansa duka abaya yana zariya ko cikakken minti goma bai yi ba anas ya shigo yana murmushi "mutumina sarkin soyayya wannan yarinya fa tayi win ... tayi galaba akanka yanzu muka hadu da pretty take fad'a min wai wulakanci kayi musu akanta "ba'a akanta bane kawai yanzu zinar ce bana so "
"karka wani waske kana fa son yarinyar nan da zarar anyi magana ka kama wani Shan kamshi amman kullum cike da yi mata biyayya kake da tattalinta "na sha fad'a maka babu soyayya a tsakanina daita kuma karka dameni da wannan maganar dan a halin yanzu bashi bane a gabana ba kwakwaluwata na bukatar tunani dan gano wani Abu me mahimmancin " "tunanin me zakayi ?Kuma me zaka Gano byn mun gano maka , munyi shekaru sama da goma tare taya zan kasa fahimtar abinda kake so Adnan ? tsaki yaja "ka daina fad'a min haka nace ba sonta nake ba bana sonta kawai dai tausayawa ce , taya za'a yi nayi soyayya daita gbdy zuciyata ta mutu babu wani abu soyayya bayan ta ahlina ,wallahi Ina balain tausayinta ne kuma ko tabar gidan nan zan cigaba da tausaya mata saboda na amshi budurcinta wanda yake da wuyar samu a wannan zamani yarinyar ta had'u ciki da wajenta tunda na Kusanceta na kasa cin kowace mace ilarta rashin kunya da rashin tarbiya .
"anas! Jaguwa ya kira sunansa gbdy yarinyar nan bata da manners "gaban anas ya fadi sakamakon ganin tanweer a tsaye a bayan jaguwa rungume da hannuwanta anas ya Kai hannunsa zai nuna masa bayansa jaguwa ya buge masa hannun "Kaine ka kawo maganar dan haka ka bari na gama kafin ka shigo da wata "sam sam yarinyar bata da tarbiya iyayenta basu koyar daita yadda ake girmama babba ba da kace mata cas zatace maka kul , ko da yake taya zatayi tarbiya haihuwa tayis reinon tayis tashin turai kasan baza'a sameta da cikakkiyar tarbiya amman Misali ace da gaske zan yi soyayya da wata mace da itace farko kodan disvarging dinta da nayi amman bazanyi ba yana gama fad'ar haka ya juya da niyyar barin gurin turus yayi zuciyarsa na karkarwa sakamakon idanunsu da suka tsarke cikin juna."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️20
.....juyowa yayi ya Kalli anas dake tsaye a bayansa yana tmbyrsa da kwayar Idanunshi dake cike da matsanacin firgici ko taji abinda ya fad'a , shima da kwayar Idanunshi ya bashi amsa alamun taji komai daya fad'a a yanzu ." ya subhanallah ya furta a kasan makoshinsa yana mai sake juyowa Inda take tsaye , tana nan tsaye kmr wacce aka dasata agurin sai dai zuwa wannan lokacin babu komai acikin kwayar idanunta sai tsananin firgici dake tattare da tashin hankali .
Muryarta na rawa tace "me naji ka furtawa abokinka yanzu ? "mafarki nake
ko kuwa karya ne ? "
taku d'aya ta K'ara tana sake cewa "kace karya kunnuwana suka jiyo min ba gaskiya ba ?" shiru yayi yana kallonta zuciyarsa na wani irin rawa dan gbdy ya gama rikicewa bai so taji abinda ya shiga tsakaninsu ba "ka fad'a min gaskiya Adnan da gaske kayi disvarging dina ? ta fad'a tana wani irin sheshekar kuka kmr ranta zai bar gangar jikinta "idan gaske ne kayi disvarging dina a yaushe kenan kayi da ni ban san da zaman hakan ba ?" still shiru yayi qirjinsa na cigaba da bugawa da karfin gaske , sai dai wannan karon yayi k'okarin Kai hannunsa jikinta domin kamota , tayi saurin buge masa hannu "dan Allah ka fad'a min cewar karya ne ba gaskiya bane dan zuciyata bazata iya d'aukar wannan sabon tashin hankalin ba ?".
ta k'arasa maganar tana cakumar wuyar rigarsa da hannuwanta duka ta matse masa wuya gam da iyakacin karfinta tana fidda zazzafan numfashi ."
anas na ganin haka ya lalla'ba sun sun ya gudu ya barsu su karata , dan bai san ta yadda zai shawo kan matsalar ba , shi da yayi silar amsar budurcinta sai yasan duk yadda zai yi ya shawo kanta ." Ka fad'a min cewar karya ne Adnan bakayi komai dani ba? dan Allah karka ce min kayi disvarging dina...." wannan kalmar kawai
take fad'a tana sake maimaitawa . rungumeta yayi tsam ajikinsa yana sakin numfashi babu shiri ta sakar masa wuya saboda ba karamin runguma yayi mata ba , ya Kai bakinsa daidai saitin kunnenta ya soma rad'a mata mgn cikin sanyayyiyar muryarshi me kashe gabobin jiki "da gaske ne tanweer amman kece silar Komai daya faru ,kece da kanki kika kawo min kanki batare da nayi niyyar aikata hakan ba".
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun ta furta cikin tsanani tashin hankali, zamewa tayi ajikinsa ta kwalla wata razananniyar qara mai sauti da tasa gbdy gidan ya amsa tana ihu ta zube kasa warwas tana kuka da birgima da sauri ya durkusa gabanta ya rikota gam jikinsa na rawa tamkar mazari yace "wallahi ba da son raina nayi ba kece kika bukaci hakan ".
"ni ....!
Ta furta a tsawace tana watsa masa wani mugun kallo ,ya gyada mata Kai alamun "eh !
"na shiga uku na lalace ni surayya Adnan ka cuceni taya zaka min haka? "taya ma zan kawo maka kaina wallahi ban san na aikata hakan ba karya kake min wallahi bazan ta'ba aikata hakan ba saboda Ina qaunar budurcina fiyye da komai dake cikin duniyar nan" .
kuka tanweer take sosai kamar ranta zai fita ya bar gangar jikinta ta mike tsaye ta soma tafiya cikin tsananin tashin hankali tsabar gigicewa hanyar special room dinsa ta nufa har tayi taku uku ya biyota da hanzari ya fixgota da karfi ya sake mannata a faffadan qirjinsa "am really sorry for....." ai bata bari ya karasa ba ta shiga dukan qirjinsa da iyakacin karfinta tana tsine masa tana mai sake fashewa da wani kuka . kamkameta yayi sosai ajikinsa duk ya rud'e ya gigice sai zufa yake fitarwa "ka sakar min jiki bana son kusancinmu tare , tsanarsa take son yi irin tsanar da bata ta'ba wani halitta ba amman tsanar taki sauka acikin zuciyarta ."
Muryarta cike da kuka tace "a tunanina na tsira daga kaidinka a she ban tsira ba ," me yasa kamin haka Adnan ? wallahi nasan bana haiyacina bancin haka babu abinda zai sa na baka kaina , Kuma ko duk duniya zasu taru akaina bazan taba yarda da nice na kawo maka kaina ba sai dai idan wani abu ka bani na sha har kayi nasarar akaina ".
shiru yayi kawai yana sauraronta yana tunanin yadda zai ku'butar da kanshi agurinta take ya tuna da cctv na bangarensa dan haka yay gauggawar zareta ajikinsa ya riko tsintsiyar hannunta ya soma tafiya daita nan fa ta turje tana cewa "babu Inda zani ka rabu dani wata hadaddiyar tsawa ya buga mata yana cewa "muje !
iya abinda bakinsa ya iya fad'a kenan ya cigaba da tafiya bai tsaya akoina ba sai a d'akinsa ya zaunar daita tana wani irin kuka me ta'ba zuciya ."
camerar part dinsa ya kunna yayi rewarning d'aga Inda ta shigo masa ya juyo da tv Inda take "ki bud'e idanunki da kyau ki Kalli komai daya faru "shiru tayi tare da tsaida kukanta shi kuma ya koma jikin bangon d'akin ya tsaya rungume da hannunwansa duka a saman faffadan qirjinsa sai dai gbdy hankalinsa da Idanunsa sun tattara ne akanta .
a hankali ta fara ganin komai tun daga shigowarta d'akin da yadda ta kunna wutar d'akin ta Isa Inda yake kwance tana shafa jijiyarsa har zuwa sanda ta d'auki bindigarsa da yadda ya amince mata ya kusanceta suman zaune tayi agurin , lokacin data ga yadda ya dinga sarrafa dukiyar fulaninta da yadda ya dinga tumurmusanta bata san sanda ta zamo kasa a gigice ba tana furta kalmar "inna lillahi wa inna ilaihi rajiun " me ya sameni haka ?"me ya shiga cikin tunanina ?"wallahi ban san na aikata haka ba, bansan abinda ya sameni ba "inna lillahi na shiga uku shikenan na rasa budurcina ?" wayyo Allah ni surayya ka kuwa san maseefar da ka jefani aciki ? me yasa kayi sex dani ? "yanzu me kake son nacewa mijin da zan aura ?hawayen ya zubo mata sharr ... akan quncinta take Kuma jikinta ya kama rawa "gbdy zuciyarta ta sake karyewa "me yasa baka dawo dani haiyaci ba a lokacin ?"wallahi bansan na aikata hakan ba Shima jikinsa rawa yake tausayinta ya kamashi gbdy ya manta wancan tashin hankali da dcp ya jefashi ciki ya matsota sosai yana me jimamin da nadamar abinda ya faru."
kusancin dake tsakaninsu yasa ta jiyo yadda qirjinsa ke bugawa da karfin gaske "dan Allah kiyi hakuri nasan bakya cikin haiyacinki lokacin da abun ya faru nayi k'okarin kar hakan ya faru a tsakaninmu amman saboda bakya cikin hayacinki burinki na kusanceki alokacin shiyasa nayi .
"me Ka bani wanda ya gusar min da hankalina ? girgiza mata Kai yayi alamun "Babu " Karya ne ka bani wani mugun abu idan ba haka banga dalilin da zai sa na kawo maka kaina ba kayi yadda kaga dama ba ta k'arasa maganar tare da fixgo numfashi da karfi ta fesar kmr me cutar asthma tayi shiru hawaye na xubo mata "kenan shiyasa a wacan ranar yayita matsa mata lallai sai tayi wankan tsarki ? ashe yasan mugun Abu da yayi mata ta zabura zata mike ya rikota gam ya makaleta ajikinsa yana shafa kanta zuwa bayanta yana jin kmr ya mutu , yana son ya fad'a mata cewar asiri akayi mata a waccen ranar yasa komai ya faru yana jin tsoron wani sabon tashin hankalin da za'a yi idan tasan da hakan.
"kiyi hakuri da abinda nayi miki nayi k'okarin gujewa hakan nasan illar abinda nayi miki tunda an ta'ba yiwa yar'uwarta
a lokacin ji nayi kamar na mutu duk yadda mutane ke bani hakuri akan nayi hakuri kasawa nayi har sai dana d'auki fansa da hannuna sannan ruhina ya samu salama " iya radadi naji a wannan lokacin ,qunar abinda na miki ya tsaya min a zuciya kullum dashi nake kwana nake tashi na zubar da hawaye sosai naji kamar na kashe kaina a ranar ,ki ya femin tanweer domin kece mace ta farko dana amshi budurcinta , bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta cewar ni ne mutumin dana amshi budurcin tanweer ba, kuma bazan daina ganin kima da martabarki ba ."
"Zaka cigaba da ganin kima da martabata ? ya gyada mata kanshi "amman kace bani da tarbiya ? shiru yayi kawai dan rasa abinda zai fada mata "haka kayita maimaitawa abokinka cewar ni mara tarbiya ce kuma nasan shima zai tsaya maka arai baza ka ta'ba ganina da wannan darajar ba ? " no karki ce haka ,kiyi hakuri da furucina na d'azu am really sorry bazan sake ba ya rike kunnuwansa da hannunwansa , "babu ruwana da nadamarka ka biyani budurcina kawai dan wallahi bazan yarda ya tafi a banza ba".
shiru yayi yana kallonta maganarta tayi matukar bashi dariya amman ya hadiye ,
yarinyata ne zalla atattare daita bancin haka taya zai biyata budurcinta daya amsa ?
Numfashi ya fesar kafin a hankali ya mike ya Isa gaban wani katon akwatin me ratsin baki da ja ya janyo akwatin zuwa gabanta ya bud'e dalolin kudin american ne cike dashi "bani da abinda zan biyaki dashi sai dai ..... "dakata ai kasan ni ba bakuwarsu bace dan zan iya baka ninkinsu abinda nafi bukata ka dawo min da budurcina na koma yadda nake Kuma a yanzu ".
tsura mata tsumammun idanunshi yayi kawai yana kallon karamin bakinta ,ya furzar da numfashi wanda hucinsa ya doki fuskarta ,a natse ya d'auke idanunshi akanta zuciyarsa na tafarfasa "yau tazo masa da abubuwa a cukurkud'e "Ina dcp ya samu numbersa da har ya kirasa yana masa barazana ? sannan da wannan tashin hankalin da furucin bakinsa yayi nasarar jefashi ciki ,taku biyu yayi ya tsaya jikin window d'akin tare da juya mata baya ,bayansa tabi da kallo batare tace uffan ba illa sheshekar kukan da take zuciyarta na hasko mata yadda ya dinga juyata .
A natse ta soma jiyo sautin muryarsa na shiga kunnuwanta "ki shirya gobe zan mayar dake gidanku nasan zakiyi farinciki da jin hakan sannan dashi kawai zan iya biyanki budurcinki dana amsa ya k'arasa maganar tare da juyo ya kafeta da Idanunshi yana ciza lip's dinsa na kasa da karfi ".
Wani sanyayyayen farinciki ne ya lullu'beta alokacin d'aya , duk cikin kalamansa babu wanda yayi mata dadi ya sanyaya zuciyarta kamar wannan "zani gida kace ?ta fad'a tana tsareshi da idanunta ya gyada mata Kai alamun "eh! gbdy taji raunin da yayiwa zuciyarta ya Kau hawaye ya gangaro mata amman wannan lokacin na farinciki ne, sosai take kuka wanda ya rasa dalili a tunaninsa murna da farinciki har ma da tsalle zatayi na barin gidan .
ta tsugunna kasa ta cusa kanta a tsakankanin cinyoyinta hawaye na cigaba da gangaro mata ya rasa ya zai yi daita abubuwa dayawa suka zo masa kukanta da rabuwar da zai yi daita rarrafowa yayi ya dawo gabanta ya kafeta da tsumammun idanunshi masu kashe mata jiki tun ba'aje koina ba ya soma Jin babu dadi a ransa ,ya bud'e baki da niyyar yin magana kenan kira ya shigo wayarsa ya janye jikinsa ya mike ya karasa Inda wayoyinsa suke ya d'auki wacce ke ruri ya duba sunan amminsa ne ke yawo a screen din wayar dan haka da hanzari ya danna Koren madanni tare da manna wayar a kunnensa ya soma tafiya yana Kiran sunanta "ammi!
bata daga Kai ta kallesa ba har ya bar d'akin kusan minti biyar da barinsa d'akin ta d'ago kanta ta bin hawayen dake zuba akan tafukan hannunta da Kallo.
a hankali ta soma share hawayenta zuciyarta na tsinkewa , ta tsaya shiru tana kallon d'akin har zuwa kan bed dinsa da komai ya faru sosai take tunani matsayar rayuwarta , kwakwaluwarta ta shiga tunani "shikenan ya amshi budurcinta zai barta ? " bana sonki amman budurcinki shine abinda yafi komai tsaya min arai har na mutu bazan manta da ni ne na amshi budurcin tanweer ba" kwakwaluwarta ta dawo mata da maganarsa "Adnan ka cuceni amman Kuma ka sake mamaye zuciyata da komai nawa , ka sake samun gurbi acikin zuciyata ,ka amshi abu me daraja da tsadarsa ya wuce komai acikin fad'in duniyar nan to me yasa har yanzu zuciyarka ta kasa amsar soyayyata ?why! why !! adnan kwalkwaluwarta ta toshe kanta ya cunkushe duk abinda ya fad'a rashin sonta daya furta shi yafi komai d'aga mata hankali "nima bazan manta da Kai ba har karshen numfashina ,Kuma har yanzu ban ji na tsaneka Ina tsananin sonka adnan nasan Allah yana da kyakkyawan nufi akan ni da Kai yasa ya had'amu , yadda nake sonka haka zalika Kai ma kana Sona duk da cewar kana boyewa , amman soyayyata ta gama fallasa kanta ajikinka tunda har abokanka suka san dashi , zan tafi na barka da dunbin qaunata daskare a zuciyarka , ba zaka gane hakan ba sai bayan bama tare idan Kuma hasashena dana abokanka bai zamo gaskiya ba " ya Allah ka jarabi adnan da mutuwar sona , yaji idan bai dora idanunshi akaina ba bazai iya rayuwa ba ,
ya kasa samun natsuwa ,ya kasa hutawa ,ya kasa tsaye ya kasa zaune har sai ya tunkareni da batu na soyayya , Allah kasa na zamo silar shiryuwarsa ya dawo mutumin kirki ...." ta k'arasa maganar tana mai runtse idanunta tare da jingina bayanta da abun gado tana sake zurfafa tunaninta tun daga farkon haduwarta dashi har zuwa wattanin da tayi a hannunsa ta fahimci abubuwa da dama akansa illarsa dai shan wiwi da sanar satar da yake bancin hk bashi da wata makusa ,yana qaunar ahlinsa da taimakon mutane gari yana kyautatawa duk wanda yake tare dashi gashi shi din me basera ne ta kowani bangare yana da matukar da basera akan komai ."
******
Bangaren hjy baseera kuwa tunda nazifi ya bar gidan alhj Tahir take cikin furgici da tashin hankali ta rasa samun natsuwar zuciya da kwanciyar hankali" tabbas allura na shirin tono garma domin kuwa bazata rungumi son ran alhj Tahir akan tilon d'anta ba ,bazata d'auka ba ,sam bazata zabi halin da yake k'okarin saka ita da d'anta ba akan cikar burinsa .
shiru tayi tana kallon celling falon tana nazari , tunanin abubuwa da dama suka dawo mata tana jin kamar karta amince da shawarar nazifi na guduwa da Ib zuwa wata kasa gara tayi komai ta ku'butar da rayuwar d'anta idan ma ta kama ta fito tayi gaba da gaba da alhj Tahir ta nuna
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 25 Chapter of 67