atakaice , yana tafiya yana bashi umarnin ya d'auki kudi yaje adidas ya siyo masa abinci ya k'arasa maganar yana tura kofar d'akin da tanweer take ,Koda ya shiga d'akin tana kwance ta lullu'be jikinta da blanket kanta ne kawai a waje tana rawa sanyi .
gashin kanta yabi da Kallo bai ga alamun ruwa ba ya had'e fuska sosai ya k'arasa ya Kai hannunsa cikin sumar kanta ya cusa har yana ta'ba fatan kanta bai ji alamun ruwa ba ya cire hannunsa yana cewa "ke........" !
ta d'ago kod'ad'un idanunta ta zuba masa batare data amsa ba " wasa nake dake Koni sa'anki ne ?to ni me nayi Kuma nifa wallahi bana son takura tunda Kai ba sa'ana bane ka mayar dani Inda ka d'aukoni mana "tayi maganar jikinta na karkarwa ta janyo blanket ta sake rufe jikinta har kanta a zuciye ya fixge bargon yayi filinging dashi yana jan tsaki "ki tashi kije kiyi wankan tsarkin da nace ko na 'bata miki rai yanzu "kamkame jikinta tayi guri d'aya ta lafe akan katifa bata da alamun tashi ."
wata razananniyar tsawa ya buga mata wanda yasa tayi zumbur ta mike tsaye har hantar cikinta na kad'awa ta kwa'be masa fuska tana kallonsa, da yatsansa ya nuna mata hanyar bayi simi simi ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar dan kwata kwata bata ga al'amun wasa atattare dashi ba a yadda take kallonsa zai iya marinta har ma ya had'a da duka yabi tafiyarta da kallo gbdy yanayin tafiyarta ta canza kallo d'aya me hankali zai mata ya fahimci halin da take ciki ,bai d'auke idanunshi ba har sai daya shiga bayi ta bugo kofar da karfi .
numfashi ya sauke ya koma bakin gado ya zauna yana neman layin amminsa suna waya ta fito d'aure da towel tana rawar sanyi ya tashi ya rungumota jikinsa ya zaunar daita a gefensa ta rakube ajikinsa tana karkarwa ya janyo blanket ya lullu'beta tare da yi mata alamar ta kama kanta waya yake sun dade suna waya da amminsa tana sauransu Kuma duk akan maganar abinda za'a yiwa baqinsu masu zuwa neman auren shafiqa ne acikin satin ...
Lokacin da suka gama wayar tuni bacci ya d'auke tan ya kwantar daita ya tashi ya d'auko mata wata rigar ya dawo har zai Saka mata ya tuna da magani dan haka ya fita ko second biyu bai yi ba ya dawo rike da roba da gayen magariya yayi adduoi aciki ya shafa mata sannan ya Saka mata kaya ya lullu'beta ya kashe ac d'akin gbdy ya fita daga d'akin zuwa nashi ya kwanta a falonsa akan doguwar kujera."
Bai jima da kwanciya ba aka soma knocking kofar falonsa , yana daga kwance ya bawa mai yin knocking ɗin izinin shigowa eku ne ya shigo cikin falon hanunsa riƙe da farar leda, cike da girmamawa ya rusunawa ogan nasa a natse Jaguwa ya mike zaune ya zura silifas ya amsa ledar yana masa godiya eku ya juya ya fice daga falon.mikewa tsaye yayi ya fito ya shiga ɗakin tan batare da yayi knocking ba kamar yadda ya saba koda yaushe zai shiga Kai tsaye ne , sai kawai ya tura ƙofar ya shiga ciki, tun sanda ya kawota gidan yake jin haushi Kansa da bautan da yake mata amman a yau din jin zuciyarsa yake fessss akanta zai iya mata komai ciki kuwa har da zama bawanta .
Tana kwance akan gado ta kwanta ruf da ciki, bacci ta keyi har lokacin hankalinta a kwance, murmushin gefen baki yayi kamar tana ganinsa haɗe da aje ledar hannunsa" sarkin rigima da rashin kunya ya fad'a a ransa , har ya juya zai fita daga ɗakin kuma sai ya tsaya yana kallonta tun daga yatsun kafaunta har zuwa kanta komai nata abun burgewa ne , ahankali ya taka zuwa inda take kwance, tafin kafansa d'aya yasa ya ɗan shafa tsakiyar kafarta .
azabure ta farka ta zauna tana murza idanunta dan har lokacin Jan da sukayi bai baje ba , sake kallonta yayi, "Ki tashi kije kiyi wanka kiyi alwala kiyi sallah , ke fa na lura sallah bata dameki ba dan zaki iya wuni bakiyi sallah ba ki kuma kwana bakya damuwa" yayi mgnr yana mai tsareta da sexy eye's dinsa."
Tsura masa idanunta tayi tana kallonsa tana Jin haushin abinda yake mata sai ya fad'awa mutun mgn yayi kmr bashi yayi maganar ba, saboda yanda yake fizgo mgnr da kyar Kallon agogon d'akin tayi yanzu ne ma hud'u ta wuce muryarta a raunane tace "gara ni ko banyi sallahr akan lokaci ba zan rama Kai fa ?meye amfanin sallahrka akan lokacin tunda kana aikata aikin haram, wad'amuhu haramun ,washarabahu haramun wa guziya bil haramun wa'anna ....."ki min shiru anan stupid " ya fad'a a tsawace , ana tausayinki bakya tausayawa kanki "nace ka tausaya min ne? ko nace ka cigaba da rikeni dole ? Ko nace dole sai ka zau....."Idan kin sake furta wata kalma anan sai na tattakaki idan km kin mutsa bismillah kiyi " yana gama faɗan haka ya fice daga cikin ɗakin ransa a bace, gsky yayi mugun sakewa yarinyar dayawa shiyasa ta rainashi .
Saukowa tayi ta shiga bayi tai alwala ta fito tayi sallah tana idarwa ta mike ta Isa gaban mirrow ledan da ya aje mata ta ɗauka haɗe da buɗewa, robobin take away ne acikin har guda uku, ɗaukan ɗaya tayi haɗe da buɗewa ta soma ci, kad'an taci dan zazzzabi take ji sosai bata jin dadin bakinta ta sha ruwa kad'an .
kamar ta koma ta kwanta ta tsinci kanta da fitowa, kanta babu dankwali ta fito zuwa falo da kyar take taka ka'fafunta , yana tsaye agaban tv ya bawa cikin falon baya yana ƙoƙarin danna code din bude wayarsa , jin motsin mutun a falon yasa batare da ya juyoba yace. "waye ? "Waye byn wacce ka sato ka ajiye a gidanka ita ce ta fito ta sha iska tayi mgnr da kyar tana kokarin zama akan kujera "shekaru sun ja wallahi ya kamata ka tuba ka daina harkar fashi ,nasan da mahaifiyarka tasan wannan aikin kake yi da bata yi alfahari da Kai ba a karshe kashe kanta zatayi dan bakinciki ."
A matukar fusace ya nufo Inda take tamkar wani mayunwanci zaki ya damki wuyanta yana Shirin danne makoshinta ya fasa saboda zafin daya ratsa tafin hannunsa ya tsura mata Ido kawai yana kallonta "ka shaki ne mana ai ni yanzu a shirye nake da mutuwa gara min mutuwa akan cigaba da zama da Kai ,a farkon had'uwa ta da Kai naji duk duniya Kai mutumin kirki ne ,Kai ne mutumin da zuciya da gangar jikina suka mace akansa saboda a tunanin zuciyarka me kyau ce a she ba haka bane mugun ciwo ne daskare a zuciyarka wannan mummunar sana'artaka yafi min komai zafi acikin zuciyata wanda adalilin haka yanzu babu kyakkyawan zaton da soyayyarka acikin zuciyata sai zallar tsana ,na tsaneka tsanar da zan iya ganin bayanka ka rubuta ka ajiye muddin na bar gidan nan sai nasa ka shiga ha......."
"karya ne " ya fad'a a tsawace yana nuna ta da yatsansa "karya ne baki Isa ba , baki Isa kisa akamani ba how could you tell someone tanweer ?" you can't do that , bazaki iya ba sannan jaguwa ba zai kamu ba cikin sauki ba sai dai wani mutun dabam, da zan kamu da ban Kai iyanzu ba" yayi mgnr yana furza mata iska a fuskarta tayi saurin runtse idanunta gabanta na faduwa , ya juya mata baya tare da rike kugunsa da hannu d'aya ya fara zagaye falon zuciyarsa na tafarfasa can ya juyo a matukar fusace "and kikace me byn zaki sa na shiga hannu ?" Kin tsaneni tsanar da zaki iya ganin bayana Shima karya ne zuciyarki bazata iya rabuwa da soyayyata ba yadda kika furta cewar kina sona haka zaki tabbata da sona a karshe ciwon sona ne zai kasheki saboda Ina ranki ,na shigeki shigar da bazaki iya cireni a ranki ba ,zaki je gidan wani da tarin soyayyata gangar jikinki za'a Kai gidan wani zuciyarki kuwa tana nan ....."ya nuna qirjinta daidai saitin zuciyarta .
wani irin sarawa kanta ya dinga yi da karfi kmr zai ra'be gida biyu tayi matukar firgita da Jin mgnr shi , ta d'auka zai tsorata da maganarta sai dai taga sa'banin haka atattare dashi sam shi din ba matsoraci bane zuciyarsa a dake take ,kallonsa tayi tare da ciza lips dinta batare data sake yunkurin cewa komai ba "ki tashi ki 'bace min da gani banason ganin wannan banzar fuskarki, karki qara kuskuren zuwa Inda nake sannan duk abinda kikaga Ina yi miki karki d'auka so ne , ba so bane tanweer dan ko digo d'aya na sonki babu shi acikin zuciyata bakya cikin irin tsarin matan da zan so , idan Kuma kin koma gaban iyayenki dan Allah karki fasa idar da nufinki akaina kiyi Ina jiranki wani irin zafi da ciwo kai ne me karfi yayi mata diran makiya gbdy jikinta ya sake d'aukar zafi tayi karfin halin dafe kanta cike da sanyi jiki ta mike ta nufi hanyar komawa d'aki sai da tayi da tasanin fitowarta ."
da kyar ta dinga d'aga ka'fafunta da
idanu ya bi bayanta yana kallonta rai a 'bace har ta bace wa ganinsa sannan ya d'auke idanunshi yana fesar da iska zuciyarsa ban da zafi babu abinda take sai faman tsaki yake ja da karfi ya fad'a kan kujera ya runtse idanunshi tare dafe goshinsa cikin haka abokansa suka shigo suka samu guri suka zauna ganinsa haka yasa suka fara tmbyrsa abinda ke damunsa shiru yayi yaki cewa komai sai tsaki yake ja anas ya dafa kafadarsa "meye damuwarka Kuma ? Still shiru yayi yana ciza lip's dinsa jabir da jubi suka tashi suka fita dan sun San tunda yayi haka ba magana zai yi ba "ya kamata ka rage damuwar nan jaguwa nasan duk damuwarka bata wuce akan yarinyar nan ba "Ina matukar tausayin yarinyar nan anas amman ita burinta bai wuce taga bayana ba
yayi mgnr a fusace idanunshi sun yi jajur "kayi hakuri nasan da haka nasan kana tausayinta da qau...." wani irin kallo yayi masa wanda yasa anas ya hadiye abinda zai fad'a "na sha fad'a maka ka daina cewa Ina son yarinyar nan amman tunda haka kake tunani ka zuba Ido zan baka mamaki"
"yauwa haka nake so Ji abokina Ka bani mamaki ka rabu daita mu hutu tunda baka sonta banga amfanin zamanta damu ba dan kasancewarta damu matsala ne mu sallameta kawai anas ya fad'a yana cigaba da bashi shawara akan tanweer ..."
Ita Kuwa tanweer tana shiga d'akin ta shiga har gitsa d'akin tamkar mahaukaciya a karshe ta fad'a kan gado hawaye na zubo mata sharrrrr akan quncinta tasan hawayenta nada halaka da bakaken maganganun daya fad'a mata , zuciyarta ta karye madadin soyayyarsa ta bar zuciyarta kamar yadda take buri sai ta dawo mata sabo fil tunda take baa ta'ba kallon idanunta aka furta ba'a sonta ba sai Adnan shine mutun na farko jikinta ya sake d'aukar zafi sosai wuni ranar bai shigo Inda take ba har dare ita Kuwa zazzabi da dacin maganarsa da ciwon gajiyar sex din jiya suka hade mata guri d'aya tayi kuka har hawayenta suka kafe bai shigo Inda take ba ya kama kanshi dan yasan koya shiga gurinta wani rashin mutunci zata masa shi Kuma bazai dauka ba ."
washegari tun karfe goma suka bar gidan batare daya lekata ba , dan har lokacin haushin abinda tayi masa bai bar zuciyarsa ba Kowani titi jami'an tsaro ne over fiyye da duk wani abun hawa, duk motar data zo wucewa sai an tsaresa an bincika ciki da wajenta tun daga nesa suka hango motar jaguwa tun kafin motar ya gama karasowa garesu suka daga ma eku hannu alamar ya tsaya a hankali motar ta rage gudu tare da k'okarin yin gefen titi ,a hankali eku yayi waning glass din motar yana mazurai ,daya daga cikin police officer ya dan leko cikin motar, cikinsa ne ya duri ruwa sakamakon ganin pesto a hannun jubi , ya ware Idanunsa sosai yaga ak 47 akan cinyar eku dake tuki ya Kai Idanunsa baya nan yaga sabon tashin hankali domin kuwa manya bindigu ya gani akan cinyar anas da jaguwa wanda ya kawar da fuskarsa gefe yana kallon titi da sauri Police office's din da suke zagaye da motar suka yi baya jiki na rawa .
daya daga cikin police yace "sorry ban San ku bane you can be on your way " a hankali glass din motar ya fara yin sama motar ta fara move police sukayi sauri suka tsaida wani me adaidaita suka duba cikin motarsa kana suka bashi hannu ya wuce direct to Ogun state suka nufa basu suka dawo gidan ba sai daf da sallar magriba wanka ya fad'a tare da alwala ya fito ya soma k'okarin gabatar da sallah byn ya idar da sallah magrib ya nufo d'akinta hannuwansa duka zube cikin aljihun wandonsa ya hangota kwance tayi ruf da ciki ko motsi kirki bata iyawa , ganin yanayinta yasa qirjinsa bugawa da sauri sai dai bai nuna hakan ba a fili tun kayan jiya ne sanye ajikinta, harara ya wurga mata sakamakon tuno abinda tayi masa a natse ya qaraso Inda take ya Kai hannunsa wuyanta nan yaji wani zafi ya ratsa tafin hannunsa kmr ta buge masa hannu sai dai bazata iya ba dan jikinta babu karfi "baki da lfy ne ?ya tambayeta banza tai masa taki motsa labbanta "raguwa banza kawai ya fad'a acikin zuciyarsa ."
"Kinyi sallah ma kuwa ?
Still shiru tayi masa bai damu ba ya cigaba da mgn "idan kinyi sallah ki canza kaya ki sameni a falon dan naga alamun tun kayan jiya ne ajikinki yana gama fad'ar hk ya juya har ya kai tsakiyar daki yaja ya tsaya yana cewa "na sanki da shegen d'aurin Kan tsiya ,minti goma kawai na baki ki sauya kaya ki fito dan Allah karkiyi abinda nace ya cigaba da tafiya ya fice daga daki .
Babu yadda ta iya ta mike ta shiga bayi alwala tayi ta fito ta tada sallah byn ta idar taki sauya kaya kmr yadda ya bukata ta fito , yana tsaye tare da friends dinsa ta fito duk suka tsura mata Ido suna kallonta maganar jaguwa ta jiya ce ta fad'o musu sosai suka qura mata Ido
suna yabawa da kyawunta .
yaji motsin fitowarta amman yaki juyawa "muje ko yace daita sannan ya fuskanci abokansa "zan dan fita amman bazan dade ba zan dawo ya karasa maganar ya nufi kofar fita .."Tabi bayansa tana adduar Allah yasa gidansu zai kaita ta huta ..
suka bisu da kallo kowannensu na maganar zuci .yana gaba tana biye dashi abaya har suka ƙaraso inda motarsa ke fake eku na ganinsa ya taso da hannu jaguwa ya dakatar dashi ya buɗe murfin motar ya shiga itama ta shiga yayiwa motar key ya tada motar mai gadi na ganinsa yayi hanzarin tashi ya bud'e masa yana daga masa hannu ya fice ya hau kan titi tafiya kad'an yayi ya waigo gefen da take zaune cike da takaici"sai nace kisa seatbelt zaki sa kome ?" ya tambayeta cikin yanayi na ɗan jin haushi. Janyo belt tayi ta saka batare da tace umm ba bare Uhmmm sai qirjinta dake bugawa kamar zai fito waje.Sunyi tafiya me d'an nisa akan titi bata waigo ta kallesa ba, sai faman wasa take da yatsun hanunta tana addua acikin ranta ."
Kai tsaye 1829 plaza ya shiga har ya gama daidaita parking ɗin motar bata d'ago ba ya ciro wayarsa ya lalu'bo number aliyu yayi dealing ya manna a kunnensa maganar minti biyu yayi ya katse ya kira sadiq shima bai dade ba yayi disconnect din Kiran ya fito ya barta ya kulle motar gbdy, taja tsaki aranta ,shiru tayi tana zance zuci da dube dube da idanunta sai lokacin ta fahimci inda ya kawota, kallo d'aya tayiwa gurin ta fahimci gurin sun ta'ba zuwa da ib ta cigaba da zance zuci kmr ance ta Kalli kan kujerar daya tashi idanunta suka sauka akan wayarsa ta d'auka da sauri ta shiga daddana code din data ga ya danna jiya tana addaur Allah yasa haka ne 2020 ta danna sai ga wayar ta bud'e jikinta na rawa tashiga dealing number dad dinta kira biyu ya d'auka bakinta na rawa tace "dad ..."!daga can bangarensa a zaune yake amman sai daya mike tsaye cikin firgice yace"tan !!! where are you ? dad ka zo 1829 plaza ...." ai bata Kai karshen maganrta ba taga yana tahowa da sauri ta sauke wayar a kunnenta tana kokarin goge number ta kashe waya gby da sauri ta ajiye wayar zuciyarta na bugawa da karfin gaske ta sunkuyar da kanta tana danne kukan dake kokarin fito mata ".
ya bude murfin bayan motar ya jefa ledar hannunsa sannan ya bude banagaren mazaunin direba ya shiga yaja Kai tsaye fmc hospital ya nufa a hankali ta d'ago idanunta nan ta fahimci asibiti ya kawota yayi parking Yana kokarin fitowa yace "fito muje" ya faɗa yana ciccin magani .jiki a sanyaye ta fito daga cikin motar ya rike tsintsiyar hannunta gam cikin nashi suka jera koina hasken fitilu ne kowa ya gansu sai ya sake kallonsu dan bakaramin dacewa sukayi da juna ba zaka d'auka su din mata da miji ne ,yayinda gabanta ya dinga faɗuwa aranta tace "Allah Ka bani iKon tserewa yau daga hannunsa ".
Tafiya kad'an sukayi taga sun tsaya a bakin wani ƙofa ya Kai hannu yana knocking din kofar daga ciki aka bashi izinin shigowa." shiga muje "babu yadda ta iya ta shiga kmr zatayi kuka Sadiq na ganinsu ya miƙe yana fad'ad'a fuskarsa da murmushin jin dadi Dan bai taba ganin yayansa da wata mace ba sai yau shiyasa murnarsa a fili take da hannu ya nuna mata gurin zama ita Kuwa kallonsa take saboda tsananin kamaninsu zaka rantse tagwaye ne , babu shakka wannan mutumin dake gabanta dan'uwansa ne km na jini dan kamar ta baci a natse muryarsa ta fito tmkr ta dan'uwansa "father ya sunanta ne ?"ga tan a gabanka ta fad'a maka sunanta tunda shishigi kake son yi ".
sadiq yayi murmushi yana kallon tan wacce ta dago ta kalli jaguwa sannan ta d'auke kanta ita dai addua take har lokacin ,shi kuwa sadiq ya kasa hakuri hakan ya tsinci kanshi da cewa "aunty nah ya jikin naki?" ya sake tambayeta cike da kulawa." da sauƙi!" ta basa amsa murya a sanyaye a natse sadiq ya soma haɗa kayan aikin da zai mata amfani dashi yana gama had'awa yace "miko hnnunki shiru tayi Taki mika masa sadiq ya
kalli yayansa, jaguwa ya wani haɗe fuska yace "kiyi abinda yace mana karki batawa mutane lokaci "
Hawayen dake makale a kwarnin idanunta suka zubo duk da kasancewarta likita amman Allah yayita da tsananin tsoron allura muryarta na rawa tace "ni...ni banason allura a bani magani ".
"dole kiso allura ko mutuwa zakiyi sai an Miki " cikin sanyin jiki sadiq yace ", father ka bita a hankali kasan mata akwai su da mugun tsoron allura "rabu daita munafurcin ne kawai ita kanta likita ce mutane nawa tayiwa allura? murmushi sadiq ya sake yi yana cewa " aha ai likitocin nan sun fi kowa shegen tsoron allura ganin tana ta bata musu lokaci yasa jaguwa kamo hannunta tare da matseta gam ajikinsa "bismillah sadiq kayi mata allura " sadiq ya soma k'okarin tsira mata ta makale ajikin jaguwa sosai tare da sakin K'ara mara sauti ,wani irin harbawa jijiyar jaguwa tayi da karfi take yanayinsa ya sauya bayan hk wani sanyi yaji yana taso masa tarayyarsu ta shekaranjiya ce ta dawo masa a hankali tsigar jikinsa suka dinga mkewa gbdy ya nemi natsuwarsa ya rasa ana gama mata allurar ya saketa dan idan suka cigaba da kasancewa haka komai zai iya faruwa dan zai iya danneta a office din.
sadiq ya had'a mata maganunguna har dana zazzabi ya mika mata yana sake mata Sannu jaguwa yayi masa sallama suka fito kmr farkon da zasu shiga yanzu ma hakan ce ta kasance taji kmr ta fixge daga hannunta ta kwasa da gudu ."
suka karaso Inda sukayi parking suka tsaya abakin mota kamar ya sani ya bude mata sai data shiga ta zauna ya kulle sannan ya zagaya ya shiga bai zauna ba sai daya d'auke wayarsa
ya zauna yana danna gefenta yayi mamakin ganin wayar a kashe ya kunna ya ajiye a ma'ajinta tare da yiwa motar key ko cikakken minti biyar bayi da kunna wayar ba kira shigo da sauri zuciyar tanweer ya shiga bugawa da karfi .
ta kame guri d'aya ya d'auki wayar da hannun d'aya yana dubawa yayinda hannunsa ke kan stearing yana tuki sunan Abubakar Hamid ya gani yana yawo akan screen din wayar da yake yana da truculler a wayarsa ,bai gane ko waye ba ya dai d'auki wayar yana dauka yaji saitin muryar hade da Kiran sunan tanweer ...!wani wawon burki yaja a tsakiyar titi ya waigo yana kallonta "tanweer !!! are you okay ? shiru cikin tsananin tashin hankali minister yace "Talk to dady tan where are you ? "Inna lillahi ta furta a fili tare da juyowa da sauri Jin sautin muryar mahaifinta dake fita cikin tsananin tashin hankali .
Kit jaguwa ya katse Kiran tare da ɗauketa da barin makauniyar take hancinta ya balle da jini ,wani kuka ta saki mai ban tausayi ta bud'e baki zata yi mgn ya sake yarfa mata wani mari wannan karon gilmawar duhu ta gani acikin kwayar idanunta ta sake fashewa da wani sabon kuka tana neman d'auki tana kallonsa ya bud'e bayan wayar ya cire sim din ciki ya karya ya watsa a bakinsa ...."
💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686 alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️17
A matukar fusace ya bawa motar wuta gabansa banda fad'uwa babu abinda yake , ita Kuwa kuka take sosai kamar ranta zai fita .
zuciyarsa ke wani irin ciwo da zafi dan idan akwai abinda ya tsani gani shine zubar hawayenta sai dai a halin yanzu baya jin zai iya rarrasheta ,zai jure Jin zafin saukar hawayenta .hannunta ta Kai kan hannunsa ta rike gam hawaye shabe shabe kwance a fuskarta ,
da sauri ya waigo fuskarsa ya kalleta yana zabga mata katuwar harara ,gashi fuskarsa gbdy babu annuri , cikin muryar kuka ta kira sunansa "Adnan '!
Yana jin ta yayi mata banza tare da d'auke kanshi ya maida kan tukin da yake yana jan dogon tsaki "me yasa Adnan ? " me yasa bazaka maidani gidanmu ba ?"
Shiru yayi yaki ce mata Komai dan ko yace zai yi magana muryarsa bazata fito ba saboda 'bacin rai dake daskare a zuciyarsa ,zubewa tayi ajikinsa ta saki wani sabon kuka me tsuma zuciya tana cewa "kayiwa Allah da manzonsa ka maidani gidanmu nagaji ! nagaji !! " .
bai ce ta daina kukan ba haka zalika bai ce ta bar jikinsa ba ya barta tayi kukanta , shi Kuma ya cigaba da falfala gudu akan titi ."
Bangaren minister kuwa cikin lokacin da bai wuce minti biyu
da yaji wayar farko da sukayi da tanweer ta mutu ba ya soma neman number din commissioner batare da bata lokaci ba ya d'auka nan minister ya shiga zayyano masa abinda ke faruwa . cikin sauri commissioner ya katse Kiran ya kira dcp dake rike da halakin kula da binciken tanweer kafin kace me jimi'an tsaro sun hallara a gabansa ,cike da natsuwa ya soma magana "please ku maida hankali sosai yanzu nan minster yace sun gama waya da diyarsa tana 1829 amman ga number data kirasa dashi ya turo mana ku tafi kuna tracking din number ku samu location Inda gurin yake .
Nan take dcp ya amshi number suka fito cikin sauri suka shiga motocinsu suna tracking din number
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 67