mutun ya shiga hankalinsa sam sam babu alamun wasa atare dashi kafa yasa mata sai gata ta zube kasa bisa gwiwowinta tana kallonsa cikin muryar kuka tace "ni kad'ai kake bi bare kayi tunanin nice na aikata abinda kake zargina? Ina Jin tsoron Allah Adnan bazan iya ......"shiiiiiiiii ! banason Jin komai d'aga bakin makira irinki ."
"Zahra!
ya kira sunanta muryarsa a tsarke ta zuba masa Ido tana amsawa da" Na'am "babu tsoron Allah"n daya halicceki acikin zuciyarki dan hk nasan zaki iya aikata komai akan cikar burinki ,masu kyakkyawan zuciya da tsoron Allah su suke tsoron aikata mugunta ke Kuma baki da ko daya aciki "yayi shiru yana numfasawa sannan ya cigaba da mgn "daga yau idan kika sake shiga harkata zan mugun baki mamaki kuma dan Allah karki cire hannunki akaina da duk wacce zaki ganni idan Kuma kinki yiwa kanki kiyamul lail zaki hadu da cuuttuka ,sannan zan ganar dake da yaren da zaki gane yana kaiwa nan yace " ki tashi ki bani guri bana son ganin wannnan fuskar taki ".
"naji zan tafi amman kayi hakuri kayi bincike sosai akai muddin aka tabbatar maka Ina d'aya daga cikin wad'an da suka aikata wannan laifin ka min hukuncin da yafi wannan "wani bincike zanyi bayan nasan babu me shegen naci a rayuwata kamarki ?ya matsota sosai ya cafki makoshinta idanunta suka yo waje "ki fad'a min gsky kece kikayi mata asiri ?ta shiga girgiza Kai alamun a'a "bazaki fad'a gsky ba ? girgiza masa Kai ta sake yi anas ya taso ya rikesa karka yi kisan Kai Adnan "ka rabu daita karka kashe yar mutane "kace mata ta fad'a min gsky da bakinta
"me yasa tayi wa yarinyar mutane asirin data kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? ya fad'a yana filinging daita sauran kad'an kanta ya bugi bango anas yayi saurin riketa yana bawa jaguwa hakuri .wani sanyayyayen numfashi Zahra ta sauke da kyar tana jin dadi aranta burinta ya cika tunda ya kusanceta rabuwarsu tazo duk nacinsa dole su rabu ,abokansa kuwa da Ido suka bisa suna mamakin jin furuncinsa ,me yasa kika yiwa yarinyar mutane asirin da ta kawo min kanta gareni na aikata abinda ban yi ra'ayi ba? suka tambayi zukansu suna dubansa fuskokinsu d'auke da qarin bayani .
"Anas kaji abinda yake fad'a , dan jarabansa ya ciyosa ya kwana da yarinyar mutane shine zai d'aura laifina akaina , kasani babu hannuna acikin wannan aika aikan " ,jaguwa juya mata baya ya tsuke fuska alamun bai son jin komai daga bakinta muryarsa a tsawace yace "anas ka sallameta daman Kaine kake gayyatota zuwa gidan nan " da sauri anas ya riko hannunta ya nufi kofar fita daita "anas ka sakeni na fahimtar dashi gaskiya "bazai ta'ba fahimtarki ba kije kawai dan Allah nima daga yau karki sake kirana na yanke muamula dake bazan Kara kiranki ba banason na samu matsala da abokina, aminina ,farincikin rayuwata .
fixge hannunta tayi daga cikin nashi adaidai lokacin da suka fito zuwa haraban gidan ta tsaya a hassale tana dubansa "ka dade baka daina kirana ba ,bazan kiraka ba shima bazan kirasa ba Amman na rantse sai Adnan ya dawo ya nemeni da kansa ka rubuta ka ajiye a Inda bazai goge ba ..."
Mmn sudais💗💗💗💗💗💗
KUSKUREN BAYA
💖💖💖💖
💗💗💗💗💗💗
PAID BOOK
FREE PAGE
WRITING BY
AYSHA .A BAGUDO
WATTPAD @HAUESH
bismillahirrahmanirrahim
Wannan littafin na kudi ne mai bukata karanta shi ya tura 500 ta wannan account number din 1438775094 Aishat Abdullahi Access bank ,Idan a tura sai a turawa wannan number+234 703 534 8686
alert domin tabbatar da an tura ko wannan number 08059623096 Idan Kuma vtu za'ayi sai a tura ta wannan number 08059623096 kada ayi vtu a number MTN ,domin sauraran littafaina a tuntubi Channel dina ta Hausa bakwai.
🅿️16
"Kenan da gaske kin aikata abinda yake zarginki akan shi ?" idanunta da suka rikid'e sukayi jazur ta cigaba da kallon anas wanda yake tsaye a gabanta yana huci kamar zaki dasu "eh na aikata Kuma bazan tsaya iya nan ba ta fad'a a matukar fusace " zan d'aura daga Inda na fara , zan tabbatar da na azabtar da yarinyar nan da azaba mafi muni , ba dai duk akanta ya mareni ba?" ya mareni akanta anas , ya ci mutuncina akanta ya wulakantani a rita lori akanta ,wallahi ya kwana da sanin zan fanshe duk abinda yayi min akanta 'zan mata azaban da rad'ad'insa yafi zafin dalma , zan rikirkita mata rayuwa zan....."saurin dakatar da ita yayi ta hanyar buga mata wata razananniyar tsawa yana cewa "enough !
"karki fara zahra dan bazaki ci riba ba , wad'an da ma suka fiki sunyi sun hakura sun barshi dan ba zasu iya ja dashi ba domin shi din dokin tsere ne bazaki iya karawa dashi ba ,shi guguwa ne idan ya tashi zai tashi da rayuwarki , zai juya rayuwarki daga sama zuwa kasa ki rasa gane kanki ......"ya k'arasa maganar yana nuna da yatsansa .
"Zahra !
Ya kira sunanta cikin tsananin 'bacin rai " ki tsaya daga Inda kike idan ba haka ba ki shiryawa gudun tsere da mutuwarki , dan akan ki ta'ba wannan yarinyar gara kin rungumi mutuwa da hannuwanki." Adnan yace bai sonki ya nuna azahirin bai sonki, tunda ba tare aka halliceki da soyayyarsa ba ya kamata ki hakura ki rabu dashi ki tsira da rayuwarki dan akan yarinyar nan ba zai raga miki ba zai iya destroyed din rayuwarki, ki manta da kin ta'ba muamula da Adnan a rayuwarki ". wannan shine abinda zan fad'a miki idan Kinga dama ki d'auka ki cire hannunki akan mugun nufinki ki zauna lafiya idan kinga dama ki cigaba kece zaki kare rayuwarki a nadama ".
Tunda ya soma magana zuciyarta ke bugu very fast ta kafe shi da idanunta ta cigaba da kallonsa ,a yau gbdy babu sauran burbushin tausayin data saba hangowa acikin kwayar idanunshi a duk lokacin da hargitse ya shiga tsakaninta da adnan , yau ce rana ta farko da anas yayi hannun riga daita . ka'fafunta ne suka kasa d'aukarta ta durkushe kasa bisa gwiwowinta tana wani irin kuka tana cewa "kasan kuwa yadda nake ji a zuciyata ? "maganganunka suna huda min zuciya, me yasa zaka nisantani da Adnan ? ya kalleta cike da matsanacin bakinciki dan gbdy ya fuskanci bata da niyyar saduda shi kuma a yau gbdy babu wannan tausayin da yake ji nata, da tayi silar rabashi da masoyinsa da yafi qauna akan komai a rayuwarsa gara ya yakiceta ta karfin tsiya sunyi hannun riga daita "amman kai kana ganin zan iya rabuwa da Adnan dan yace bai sona ?ko kana tunanin zan iya daina sonshi ne ? Me yasa zaka ce na manta da soyayyata ? "haba anas idan kayi min haka baka kyauta min ba ,yanzu adalci ne daka nuna kafi bukatar rabuwarmu dashi ?
ya gyada mata Kai alamar"eh! " cikin firgici da tashin hankali ta shiga girgiza masa kanta sannan ta cigaba da magana "ada tunanina kana sona da Adnan ne a she duk ba haka bane karya ne baka qaunata dashi ? to bari kaji in fad'a maka maganganunka ba zai sa na fasa duk abinda nayi niyyar aiwatarwa ba ko da kuwa zan mutu ." ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka "karki fasa zahra bazan baki hakuri ba kije kiyi duk abinda zakiyi amman Ina tabbatar miki wahalar banza zakiyi dan ba zaki yi nasara ba hasarar kudinki da lokacinki kawai zakiyi yana gama fad'ar haka yace ki tashi ki 'bace min da gani yadda Adnan baya son ganinki nima hakan take gareni ".
Batace masa komai ba ta mike da kyar ka'fafunta na rawa ta juya ta soma tafiya hawaye masu zafi da ciwo na sake zubo mata akan quncinta , zuciyarta bata ta'ba karaya ba atun sanda jaguwa yake furta mata kalma bai sonta sai a yau da anas ya sake maimaita mata , duk da ba yau ta saba jin kalmar baya sonta daga bakinsa ba amman ciwon na yau daban ne a cikin zuciyarta sannan ya mugu mugun tsaya mata arai ya d'aga mata hankali ya dagula mata lissafin tsarin rayuwarta data shirya dashi , Kuma duk runtsi duk wuya sai tayi abinda zai furta mata Kalmar so da bakinsa , sai ya dawo yayi kuka da idanunshi yana rokon ta amshi soyayyarsa, ko zatayi yawo tsirara sai ta aureshi idan Kuma hakan bai samu ba zata saka rayuwarsa ta quntata . "
anas ya yabi bayanta da kallon bakinciki ,ya rasa wani irin naci ne irin nata , mutun ya nuna miki da Ido ya nuna miki da jikinsa har ya fito ya furta miki amman ki tsaya kina hauka akanshi, tsaki yaja ya juya ya shiga ciki falon zuciyarsa cike da takaicin abinda zahra tayi . Inda ya bar jaguwa anan ya iskeshi tsaye a tsakiyar falon rungume da duka hannuwansa a qirji sai faman cika yake yana batsewa .
jikin anas a sanyaye ya samu guri ya tsaya kusa dashi ya dafa kafad'arsa, jaguwa ya juyo ya kalleshi yana cije lip's dinsa na kasa a hankali ya sake juya masa baya yana furzar numfashi kana yace "ka gama munafurcin ?wani irin bugu qirjin anas yayi da karfi " a hankali sautin muryarsa ya fito yana cewa"idan zanyi munafurcin kowa bazanyi naka ba, idan zan cuci kowa bazan cuceka ba, kama daina min irin wad'an nan abubuwan dan wallahi suna Kona min rai da mugun tayar min da hankali ".
Jaguwa ya waigo ya fuskanci anas sosai yana sake furzar da iska mai zafi daga bakinsa "muddin kana son zuciyata ta cigaba da amincewa da Kai sannan na daina fad'ar haka akanka anas ya zama dole sai kayi hannun riga da zahra bana qaunarta bana qaunar ganinku tare muddin zaka kasance dani sai dai ka za'ba ko ni ko ita ? taku daya biyu yayi ya matsa daga kusa da anas yana tafiya a hankali still yana rungume da hannunwansa.
"jaguwa !
anas ya kira sunanshi cikin yanayi na firgici da tashin hankali , idanu kawai jaguwa ya tsura masa batare daya amsa masa ba" shakka babu duk duniya nafi sonka akan kowa, Ina qaunarka fiyye da ni kaina maganar zabi ma bata taso ba dan kasan waye zabina" yayi mgnr hawaye na ciccikowa a idanunshi "Kai ne zabina Adnan Ina sonka fiyye da kowa da komai nawa " tautausan murmushi jaguwa ya sakar masa yana mai Jin sanyi acikin zuciyarsa , cike da farinciki ya mika masa hannunsa
da sauri anas ya mika masa nasa hannun suka rungume juna suna sakin numfashi atare , jabir , jubi ,kamil da suke zaune duk sukayi shiru suna dubansu dan ba wannan bane karon na farko da suke samun matsala a tsakaninsu kuma cikin kankanin lokaci suke daidaita kansu.
kuka sosai anas yake jaguwa na shafa bayansa kamar wani karamin yaro "is okay anas na sani , nasan kana qaunata da gsky kmr yadda nake qaunarka am really sorry for my active har cikin zuciyata nake jin qaunarka , Kai zinari ne acikin zuciyata Ina sonka anas "Nima Ina sonka kyakkyawan abokina had'e da qauna mai karfi , cikin kankanin lokaci komai ya daidaita a tsakaninsu suka samu guri suka zauna cikin sauran abokansa nan hira ta barke a tsakaninsu .
su jubi sun so kwarai su sake samun qarin haske akan maganar jaguwa ta d'azu akan yarinyar amman yaki bada dama amman duk da haka sai da kamil yayi magana Cike da kulawa kamil yace "anyi maka tambaya akan yarinyar nan ka wani share mutane " to me yasa meka a goshi Kuma ? ko baku lura da goshinsa ba ?ya fad'a yana kallonsu d'aya byn daya ,kun san halin miskilancinsa ai ba lallai ya fad'a ba ni tun jiya na gani sanin halinsa yasa na share inji cewar jubi .
"ku manta da wannan maganar idan akwai wacce ta fita mahimmam ku kawo muyi kawai " anas ya fad'a dan jaguwa wayarsa ya d'auka yana duba sakonin mutane , basu tashi a falon ba sai da suka tsara yadda tafiyarsu Ogun state zata kasance a gobe .
" Yadda suke tsara komai akan aikinsu haka Suma jami'an tsaro dana sirri suke shirya yadda zasu kamasu a yanzu ma Asst Commissioner of police ne ya kira layin d .c .p baba abare wato lawan numan byn ya d'auka suka gaisa ya fara magana cikin zafin rai " wannan mutumin bai kamata a barshi har zuwa wannan lokacin batare da anka mashi ba , yayi mgn tare da yin shiru "eh to haka ne amman abinda nafi bukata a Kara saka Ido sosai akan duk wani motsinsa da shiga da fitarsa bama iya rayuwarsa ta fashi ba hatta rayuwarsa ta duniya ma sai na tabbatar da ta ru'bance idan yazo hannu , sun dauki lokaci mai tsawo suna tautaunawa akan jaguwa da yaransa kafin daga bisani suka yi sallama. "
*****
"Nazifi haka mukayi da Kai ?a she baka da amana ban sani ba ? ya rufe shi da fad'a ta Inda yake shiga ba ta nan yake fita ba cike da matsanacin firgici nazifi yace "dady me nayi Maka ? bangane me kayi min ba ? ya tambayesa yana maxurai ",ni zakawa tambayar rainin hakali ? to yau duk a zaune naga Ibrahim alhalin na fad'a maka bana son ganinsa a zaune sai akwance dan lokacin tashinsa bai yi ba tukun "sai lokacin nazifi ya fahimci rashin amanar da yayi masa . ya shafa sumar Kansa yana cewa "Allah dady Ina iyakacin k'okarina Ina yin komai yadda ya kamata alluran da na saba yi masa shi nake masa haka zalika maganin da yake sha shi nake kawo wa ban canza ba ".
"wannan karya ne nazifi "da gaske dady baza yi maka haka ba ,ai duk abinda kace shi zanyi tunda ka zabi abarshi cikin wannan yanayin ni me zaisa naki?" ai ya zama dole nabi
duk wani umarninka bayan haka ma duk sati sakokan na shigowa account dina ,nafi tunanin yawon magani da allurar da ake masa ne yasa suka daina aiki ajikinsa Ina ganin me zai hana a canza masa ? ". ya fad'a yana tsine masa acikin zuciyarsa domin kuwa mutane masu hali irin na alhj Tahir sam basu ya kamata su haifi d'a irin Ibrahim ba. "to shikenan na d'auka kana cin amanata ne ?Ina ai bazan ta'ba cin amanarka ba wannan ai sirri ne a tsakaninmu " alhj Tahir yayi murmushin jin dadi yana cewa "to yanzu kana ganin idan an canza masa za'a samu me karfin na farko ?"sosai kuwa za'a samu zan duba me karfi wanda yafi na farko zuwa gobe sai nazo dashi "to shikenan na gode son Allah yayi maka albarka ya Kai hannu ya zagaye kafad'an nazifi yana tafiya dashi acikin falonsa" ka cigaba da bin umarninna ni Kuma bazan gaji da tura maka sakona ba "nazifi ya gyada masa Kai tare cewa "babu komai dady ai ko baka biyani ba ya zama dole nabi duk wani umarninka nasan kana da wata munafa me kyau akan ib shiyasa kake bukatar ganinsa akwance ?".
"yauwa nazifi a she kana da fahimta ?" shi yasa kullum kake kara burgeni saboda kaifin baseerarka" cike da girmamawa nazifi yayi sallama da alhj Tahir ya fito zuwa babban falon gidan Inda ya iske hajiya baseera zaune kusa da Ibrahim dake zaune akan wheelchair tana bashi abinci a baki tausayinta dana Ibrahim ya kamashi ,mace har mace me tausayi da biyayya amman batayi sa'ar miji ba "har ka fito nazifi ? "eh mumy na fito "to sannu da kokari Allah yayi muku albarka gbdy , yadda kake kula da abokinka baka gajiya Allah ya kula da lamarinka "Ameen mumy ai kula da ib ya zama dole , Ibrahim ya dubesa wuyansa a karye magana yake son yiwa amininsa amman ya kasa furta Komai so yake ya sheida masa Kiran daya samu daga bakin alqali a kwanakin da suka gabata .
sai da nazifi ya sake duba jikin Ibrahim sannan ya fito zuwa haraban gidan ya shiga motarsa ya zauna ya bata wuta, tafiya kad'an yayi ya gangara gefen titi yayi parking ya Kasa cire hannunwansa akan stearing motar ya shiga kogin tunani ta yarda alhj Tahir yake wa dan lelensa wanda shi kad'ai ya haifa a duniya mugunta.ji yake kamar ya tattara ib da komai nashi ya turasa zuwa kasar england domin ya samu kulawa daga manya likitoci , dan allurar da mahaifinsa yake sa shi yayi masa bata da maraba da poising me karya garkuwar jiki gashi sanadiyyar haka an tsaida komai nashi bayan shi din mutum ne mai qulafucin akan aikinsa"gbdy zuwa yanzu ya soma zargin manufar alhj Tahir akan d'ansa Ibrahim, idan kuwa haka ne babu shakka akwai lauje cikin nadi wato akwai saka hannun alhj Tahir cikin kidnappin din tanweer da yan fashi suka yi .
"haka ne ma zuciyarsa ta tabbatar masa da hakan , wannan dalilin yasa alhj Tahir baya son Ibrahim ya tashi bisa kafafunsa ya nemi tanweer da karfin da iKon da Allah ya bashi, tabbas Ibrahim nada gogewa da jajircewa da qulafici akan aikinsa da duk wasu masu laifi a kasar nan.
" idan ya gangara ta bangaren aikin sirri shine kan gaba saboda kwarewarsa ya iya binciken sirri tamkar aljani tare da abokan aikinsa har su gano me laifi yanzu abinda zai yi zai cigaba da boyewa alhj tahir tare da biye masa har sanda zai kammala komai akan abinda yake zarginsa akanshi tare da nemo sheidu masu karfi ta yadda za'a samu nasarar kamashi a sikwane , yana da tabbacin muddin aka kamashi za'a kama ragowar abokan sana'ar tasa dukkaninsu su girbi abunda suka shuka ya kusan awa d'aya agurin yana saka da warwara har hawayen tausayin Ibrahim ya zubar saboda rashin dacen mahaifi da yayi sannan ya tada motarsa zuwa office dinsa har ya Isa office tunanin aminisa yake .."
*******
Tanweer bata farka ba sai gurin karfe d'aya na rana ta farka cike da matsanacin azaban ciwo dan ta sha wahala sosai jikinta na rawa koina ciwo yake mata sai numfashin wahala take fitarwa , wani abu ya hadiye sannan ya matso kusa daita sosai ta bud'e idanunta da suka mata nauyi ta ga shine zaune a kusa daita wani marayan kuka ta fashe dashi tana shesheka, muryarsa a kasalance yace "lafiya kike kuka me ya sameki ? ya fad'i haka ne dan ya sake tabbatar da tana sane da abinda ya faru a daren jiya duk da baya doubt akan gaskiyar abinda baba ya fad'a masa .ta fashe da wani sabon kuka tana cewa "nima bansani ba amman duk ilahirin jikina ciwo yake min tunda nake ban ta'ba Jin irin wannan ciwon ba dan Allah ka taimakeni ka maidani gida ....." ta k'arasa maganar tana sheshekar kuka bai sake yin magana ba ya ɗauketa cak ya nufi bayi daita ya had'a mata ruwan zafi ya Kai hannu zai riko hannunta ta goce ya bita da wani kallo.
ta zabga masa harara tana hura masa hanci ,shiru yayi yana cigaba da kallonta yayinda kukanta yaki tsayawa ganin ko ya rarrasheta 'bata bakinsa zai yi yasa a hankali ya Isa Inda take jingine acikin bayin ,batayi expecting ba taji ya rungumeta ajikinsa tsam , ajiyar zuciya ta saki ta had'e rai sosai .
rarrashinta yake son yi amman yasan halinta ba lallai ta bashi had'in Kai ba zata iya butsare masa "tanweer ! ya kira sunanta muryarsa a sanyaye tana jinsa taki amsawa ta cigaba da kukanta "tanweer !" ya sake kiranta cike da rauni Yana shafa sumar kanta zuwa gadon bayanta " Kince jikinki na ciwo ? ta gyada masa Kai kawai " ki d'aure please ki shiga ruwan zafi zaki daina jin ciwon kinji "tayi masa banza tamkar ba da ita yake ba bare ta nuna alamun zata yi abinda ya bukata ,a hankali ta soma k'okarin kwace kanta daga jikinsa har ta zare ta tsura masa idanunta fuskarta babu annuri a kallon da take masa taga goshinsa ya dan kubura ta Kai hannunta ta shafa gurin batare da tace masa Komai ba duk da tmbyrsa bakinta yake son yi amman ta kasa sarrafa harshenta , hannunta ya kamo cikin nashi ya matse gam "ki shiga ruwan zafi zan gasa miki jiki ta yadda zaki daina jin ciwon komai ajikinki" girgiza masa kai tayi sannan ta motsa labbanta " ka fita kawai zanyi da kaina ba sai ka tsaya ba dan bazan iya tubewa agaban wani katon banza ba ta fad'a Kai tsaye taja ka'fafunta ta jingina jikinta da bango bayin ."
yayi shiru kawai yana kallonta maganarta ta sosa masa rai sosai azahiri ake iya hango hakan "idan Kuma bazaka fita ba bari ni na fita ta juya tana d'aga ka'fafunta da kyar ya nad'e hannun rigarsa ya kamo kafadarta bai tsaya wata wata ba ya d'auketa ya dannata cikin ruwan zafi wani qara ta saki mai sauti ta zabura zata mike ya sake dannata ta zaro idanuwanta gbdy hawaye na zubo mata , kallon juna suke wanda ita nata kallon na fita haiyaci ne shi kuwa na mugunta ne "muryarta a tsarke tace "Allah ya Isa ban yafe ba mugu azalumin kawai Allah ya Saka min nace maka zan gasa jikina dole ne da zaka wani sundumani cikin ruwan zafi dan mu...." ? bata k'arasa mgnrta ba ya dalle mata baki da yatsansa "har yaushe zaki daina yiwa mutane rashin kunya ?ya fad'a yana sake dannata cikin ruwan zafi har sai da ta sake sakin qara me sauti tana cewa " har sanda mahdi zai bayyana ta bashi amsa da haka tana marairaice fuska .
tausayinta yaji yana yawo a sansar jikinsa shiyasa ya rabu daita dan inya biyewa rashin kunyarta komai zai iya faruwa a tsakaninsu "ni ka barni haka zafi na ratsani dayawa "ta fada tana kallonsa "abinda kika fad'a nayi aiki dashi "to ni me na fada ?ta tambayesa muryarta cike da shagwa'ba tana turo masa karamin bakinta "muryarsa can kasa yace "kince jikinki na ciwo har kasanki ko ba haka ba ?tai masa banza tana bata fuska tare da d'aga kanta sama alamun tunanin tana son ta tuna lokacin da tace masa har da kasanta ke mata ciwo ita dai tasan tace masa jikinta "ko zan iya sanin abinda yasa kike jin ciwon jiki da kasanki? ya tambayeta yana k'okarin zare rigar jikinta , idanunta ta tsura masa tana kallonsa cike da mamaki hannunsa ya Kai yana shafa bakinta kafin daga baya ya maida bakinsa ya fara kissing dinta in a romantic way tun tana turjewa har dai ta hakura ta barshi bayan ya gama romancing dinta ya zare hannuwansa yana cewa "kiyi wanka ki had'a dana tsarki ".
zaro Ido tayi waje cike da mamaki tana maimaita abinda yace a zuciyarta " ki maida wadan nan idanun naki kiyi abinda nace yana gama fad'ar haka ya juya zai fita ya jiyo sautin muryarta tana cewa "akan wani dalili zan had'a da wankan tsarki ni ba janaba ba ?"ya juyo a natse yana kallonta tai saurin kare qirjinta da hannuwanta , ya kwa'be baki yana kashe idonsa d'aya a ransa yace" abinda na kwashe rabin dare Ina sarrafasu shine dan manufarci kike wani boyewa ,numfashi ya furzar ya sake juyawa yana cewa"kiyi k'okari kiyi wankan dana tsarki idan Kuma kin Isa karki yi zan gane "baza'a yi ba , babu janaba ajikina dan hk babu wani wankan tsarkin da zan yi daf da zai bar d'akin yaji ta fad'i haka "kwa'be fuska yayi " yarinyar nan da alamun sai na baki tarbiya kafin na maidake gidan ubanki dan kanki na mugun rawa."
d'akinsa ya koma ya shiga wanka sai daya d'auki minti ashirin yana bayi sannan ya fito yana goge jikinsa da karamin towel fari tasss yana tunanin tanweer, hakan nan yake qara Jin qaunar yarinyar na mamaye ilahirin jikinsa sai dai yayi ta k'okarin yakice hakan yana karyatawa , ya shirya kanshi cikin wasu Kanana kaya wando da riga farare sol ya feshe ilahirin jikinsa da turare , ya zauna a bakin gadansa ya d'auki d'aya daga cikin wayoyinsa ya kira number aliyu number bai shiga ba da alamun akwai matsalar network ya mike tsaye ya fito yana neman layin eku kira d'aya ya d'auka tare da cewa "boss Ina yini ?"Lafiya ya fad'a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 67